Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ruwan duste ya sha,Ni duka ma wayen nan kayan zaƙin bamu iya shan su ba sai dai ku masu shuni Yan gayu,ƙila ita Raliya nan gaba ta iya shan su da cin su amma Nikam ina ga tsufa na tasowa ka halaka kan ka da ɗan kanoma tun da sauran ka. " Ta kai ƙarshen zancen tana sakin murmushi na jin yadda zuciyar ta tayi mata sanyi na yadda ta samu ta mayar mata da zancen itama duk da tana mugun ganin girman ta. Shiru Mama Hafsatu tayi kamar ruwa ya cita sannan tayi ɗan murmushin yaƙe tana furta " To ba matsala ai shikenan Amma kam bazai ji daɗi ba ba,a mayar da hannun agogo baya da kin karɓa mata ta yuyu tana so '' " Ah ah Mama Hafsatu Nagode kawai kicewa Yaya Nadiya ta mayar masa ". Raliya ce tayi furucin cikin sanyin ta tana tana cigaba da duba wasu littafan ta na islamiyya da ta ɗauko a yanzu. " Yo to ai kun san ba,a mai da hannun Agogo baya da an mayar masa amma duk da haka bari kawai abawa yar uwar ki ta ƙara tun da ita kam Nadiya na da su har da na sadaka ma buhu buhu suna nan Ajiye wasu ma bata sakawa ". Mama Hafsatu ta ƙara yin furucin bayan gama sauraren zancen Raliya da kuma zancen Mama Hasiya dake cin ran ta. " Hmmm Yaya kenan ai duka ɗaya ne da kai da wuya duka mallakar kaya ne kowa ya ɗauka acikin su ai naki ne babu damuwa,Mun gode,kayan maƙu kashe da kayan Fulawa kuma a ƙara ayi ta ci,ko Ban za kin huta da loda tuwon ". Inda Takai ƙarshen zancen tana jan carbin ta tare da cigaba da Azkar ɗin ta. Mama Hafsatu kuwa miƙewa tayi cikin ɗan murmushin yaƙe ta furta " to sai an jima Raliya ". Ta fice tana sakin murmushin nasara domin dama da gangan tazo tun farko tasan cewa bazasu karɓa ba ta san Halin Mama Hasiya tsaf. " Wallahi Hasiya taƙi karɓar mata wai ki ƙara kawai a yi masa godiya ". Ta yi zancen a fuskar ta tana nuna bata ji daɗin hakan da Mama Hasiya tayi ba. A zuciyar ta kuwa farin ciki ne fal musamman da ta san yadda Nadiya ta nuna son rigar wanda kowa ya ganta yasan ba ƙarama ba ce. Nadiya kuwa ba kunya ta karɓe a barta tana murna duk yadda mahaifiyar ta ke ɗan shaguɓar ta da idanun ta akan Najiba da tayi kamaar ba ta san abinda ake yi ba a yanzu ta kama wayar ta tana ta chat da ita. Ciye ciye suka fara sai da sukayi nak itama dai Najiba haka ta ɗan saki jiki ta ci ta ƙoshi Sannan suka maida sauran kayan masu lalacewa a cikin fridge.Sannan suka taɓa yar fira kafin malam Abdul Basiɗ ya shigo suka watse kowa ya kama gabansa kowa yayi ɗakin sa dukkanin su *** " Gariti Ina cikin tashin Hankali Wallahi wai kasan yau Ni da kaina nasan tawa ta ƙare,kasan Gwaska ashe Saurayin Yar uwar Najiba ne da yake ban taɓa haɗuwa dashi ba sai yau ashe shine saurayin ta,nifa na ɗauko shi daga cikin ɗai daga motocin nan da ya turo a jiyan kasan da ita na fita yau ɗin saboda koda na fita ban ka nan kuma koda na dawo ban tarar da kai ba, Shiyasa na kasa tsaye na kasa zaune zagaye na huɗu toilet Gariti ". Yakai ƙarshen zancen kamar zai fashe da kuka sai zufa yake haɗawa kamar wanda ya haɗiye kunama. Saurayin da aka kira gariti ne ya kece da wata mahaukaciyar dariya ta ƙeta kafin ya furta " Ikon ALLAH kace yau dara ta ci gida,to ya kayi da ka ganshi amma ka bani tausayi wallahi Jamilu sabuwar mota ma da ko lasisi ba ayi mata ba na kamfanin nasu shine ka fita da ita dan gyara shiryayyer ƙarya,To wai ya abun ya kasance ma " " Wallahi mota na faɗa da sauri A lokacin da na hango shi na maƙala facemask, Sai dai daga yadda naga ya Amsa mini gaisuwar da nayi masa inajin kamar ya gane ni wallahi ". Jamil yayi furucin cikin fargabar da ke cin sa. " Tab wallahi ya ma gane ka kace ya ce Jamilu ko ". Kai Jamil ya ɗaga masa kafin ya furta " ALLAH yasa kar ya gane komai ". " Hmm na rantse maka da Allah ya gane kasan Gwaska Tanim mugun gari ne idanun sa Asake suke,ya gane abinda kayi gajiya ya rufa maka asiri ne ne kawai amma Ni nasan akwai magana kuma bari kaga ya gama hutawa idan ya shigo zaka ji an neme ka a office ". Wani tashin hankali ne ya ƙara mamaye fuskar Jamil jin kalaman gariti wanda shi kan sa tuannin da yake yi kenan ya gane sa Sai dai rashin disga sa da bai yi bane abun ya bashi mamaki ko nuna wata alama ta cewa ya san shi musamman kasancewar shi ƙaramin ma,aikaci a kamfanin nasu na motoci. Da ƙale kiran da ya sake shigowa wayar sa yayi domin baya jin yau zai iya yin wata firar arziki da masoyiyar sa wanda yasan sai ya sha tambayoyi idan taji sa shiru,saboda bata son damuwar sa ko kaɗan.Wani kiran ne ya sake shigowa inda ya miƙa wa Gariti da ke kallon sa kamar ya kwashe masa da dariya sai dai ganin da yayi tabbas atsorace yake kuma yasan magana ce Babba hakam ya sanya shi yin shiru yana kallon sa." Karɓa kace mata na shiga meeting na dare da ma,aikatan kamfani na ". Waro idanu gariti yayi kafin ya furta '' Wai dama abun da ka furta mata kenan cirrr ƙarya bala'i wai daɗin mi gare ta da ka dage kana ta ɓoye ɓoye kai ɗan talakan ka,Ka ɗaukar wa kan ka rayuwar wahala,wallahi Jamilu ka gyara kar ka zo kayi nadama abun da ba,a so,ka fito ka faɗa mata kai talaka ne in tana son ka Toh ko Babban ta ne mai kuɗin duniya bazata rabu da kai ba". Yakai ƙarshen zancen yana sakin dariya. Kafin ya ƙara furta " wallahi abun naka ya bani dariya Jamilu mutumen da ke nan ya na tsuwwa r sa Bai da kuɗi sannan yake biɗa ga Allah wai shi ke furta yana da kamfani ƙila ma wata ƙaryar da ka ke yi mata bata sallah ". Yakai ƙarshen zancen yana sakin dariya. Wani kiran ne ya ya sake shigowa inda Jamil dake kallon sa yayi fuskar tausayi yana jin kamar ya rusa kuka ya furta " Don Allah gariti ka ɗaga kiran nan kace P.A. ɗin yallaɓai Jamil ne ''. Riƙe dariyar dake son kubce masa yayi jin wata shiryayyer ƙaryar da ya haɗo yanzu yanzu wai yace P.A ɗin sa ne har da wani yallaɓai. Sannan A hankali cikin natsuwa yana katse dariyar sa ya ɗaga kiran " Wa alaikassalam '' A ɓangaren Najiba dake ta kiran sa suyi fira ta ɗan rage dare ne tayi ta kira bai ɗaga ba sai dai kamar ta sha re ayanzu sai ta ƙara kiran layin nasa .. Jin an karɓa mata Sallamar ta ne bayan ɗaga kiran hakan ya san ya ta ɗan miƙewa daga kwancen da take akan yar ya buɗaɗɗiyar katifar da suke kai jin wata murya da ban bata sa ba. Cikin mamakin wane ne wanda ya karɓa mata sallamar ta ƙara tsinkayar Muryar sa yana furta " Allah ya taimaki Hajiya Ni suna na Gariti men yah ". Najiba Dake Jin sa sai da ta ɗauke wayar sannan ta tuntsire da dariya tana mai do ta kan kunnen ta sannan ta furta " Gariti men yah wane suna ne haka " ? " Ehh to Hajiya karki damu da suna na,Amma dai ya samo asali ne daga Americano A lokacin ina chan tare da Yallaɓai Jamil kafin ya baro chan kin san mun fi shekara Goma Achan nida shi,to nan ne turawa suka laƙa mini suna kamar shi ma yallaɓai da suka yi masa nasa sunan suna kiran sa da Boss Jamilo gen ".Yakai ƙarshen zancen yana ƙunshe dariyar dake ta so masa na iyayin da yake yi. Shi kan sa Jamil duk da yanayin da yake ciki sai da ya tuntsire wai Gariti men yah. Da ido yayi masa alama da ya taimaka ya katse kafin ta gano wani abu kar yaje ya kwafsa. " Eh Hajiya ki gafarce ni na cika ki da surutu,kamar yadda na faɗa Miki suna na Gariti men yah,Ni ne P A ɗin yallaɓai Jamil a kamfani yanzu haka yana meeting da wasu turawa da suka zo tun jiya akan wata sabuwar mota da za,a kawo Nigeria". Kai ta jinjina cikin nishaɗin da tasamu Agurin Gariti,da kuma farin cikin jin har da turawa yake meeting d su kenan wani shege ne domin ita shaida ce yadda ya ke zuwa da mota kala kala gurin ta. Cikin sakin fuska ta furta " Ayyah P.A Gariti men yah nagode sai da safe ka kasanar dashi na kira i Dan ya fito daga meeting ɗin nasa". Ka tse kiran tayi tana dariya bayan tuno da sunan nasa wai Gariti men yah. *** A ɓangaren su Gariti kuwa Bayan gama wayar Dariya sai da ya kai ƙasa yana furta Ashe shima ya iya tsara ƙarya. " Wallahi kuma mutuniyar ka ta hau arado yadda ta ƙume daɗin ta Ance Jamil na gurin meeting ". Yakai ƙarshen zancen yana miƙewa daga ƙasan da yake a zube. Jamil shima dariyar yake yi sai dai ta Gariti ta fara ƙular dashi sai ya tsuke fuska yana hasko ma kanshi rigimar gobe yadda zai fuskan ci Tanim. *** " Kayi haƙuri malan komai zai wuce wata rana za,ayi kamar hakan bai faru ba,Najiba kuma Bazan so mu matsa ma taba kabar ta har lokacin da taga dama ita da kanta zata dawo muna in Sha ALLAH " Mama Hasiya ce ke furucin cikin Tausayin mijin nata da kullum maganar sa ɗaya ce akan su Nadiya da Najiba sai dai bai iya attaka komai ayanzu na yin hani a gare su ko saka su abu kamar abun magani da shi da yayan nasa malam Abdul basiɗ kowa an rasa gane ma kansa,tunda agaban su komai yake faruwa. Hawaye ya share kafin ya furta " ALLAH ya sa su bijiro da maganar Aure azukatan su sai ayi musu hankalin mu ya huta,A yanzu babu wanda na ke tausayi irin yaya Abdul Basiɗ.Allah kayi muna maganin wannan jarabawar ya Ubangiji '' " Amin " Mama hasiya a furta cikin Tausayin mijin nata kafin sukayi Addu'a suna kwanciya bacci. *** A ɓangaren tanim nan bacci ya kwashe sa wanda koda ya tashi karuwar tasa ta ƙara gaba da ma ranto ta yayi daga wani gidan karuwai dake sabon Gari na Kano. Haka ya cigaba da baccin sa babu magriba babu isha'i. *** " Kin fi son rayuwar yaran nan ta ta ta tarwate Hafsatu tarbiyyar da muka musu ta tafi abanza. Kiji tsoron Allah ki bar ƙara ingiza su ga wahala ko nace ga zuba yaran akwai ranar ƙin dillaci,ina tsoratar mik ranar da Zakiyi kuka da hawayen ki" Shiru Mama Hafsatu tayi tana sauraron malan Abdul basiɗ dake zuba bayani. Ɗan Jim tayi cikin mamakin zancen nasa Sannan ta furta " Tsaya malam me kake nufi yau ka samu damar magana shine kake ya ɓa mini magana haka kenan Ni ce gishiri da miyar su Nadiya,ko Ni na ɓata su me kake son ka faɗi ban gane ba,kuma da kake cewa hakan naga dai Yaran nan ba wani mugun abu suke aikatawa ba,Ɗan abun nan da kuka kasa sama musu ta wajen ku waton arziki shi suke fita su nema ba wani abu ba ko so kake suma su ƙare kamar mu da kuka zo kuka jibge kuna ɗura muna baƙi da Cott da sitati ( Tuwon Dawa da masara ).Dan haka kar ƙaara yi mini irin wannan zance ina zaman zama na ka bata rai kasanya Ni kwana da tunanin zancen nan,naga dai ai in sun fita suka baka karɓewa kake yi to me ye na conhilan ( Complain ). Tana gama zancen ta juya kwanciyar ta tana bashi baya tare da jan guntun tsaki.✍️ Wayar sa take ta kira sai dai ba,a ɗaga ba domin kuwa bacci ne ya dauke shi bana wasa ba gashi da nauyin bacci ganin ba,a ɗaga ba hakan ya sa ta hakura kawai ta ajiye wayar. Ɗan juyowa tayi jin Najiba shiru abayan ta sai dai samun ta yi har tayi bacci inda itama take baccin ya fara haɗe idanun ta sai bacci. A gafarce ni dama ban muku Alƙawarin samun update nashi a koda yaushe ba.✍️✍️✍️Ban da time ne. Asuba ta gari🙏 Masoyan Rayuwar mu ayau 🌺🌺🌺 Ko ya zata iya tsakanin Tanim da Jamil ?? Me yake damun iyayen su Najiba maza shin kodai zancen Mama hasiya gaskiya ne akwai wani lamari aƙasa.??✍️✍️✍️ Ku cigaba da bibiyar Alƙalami na✍️✍️ Dan jin yadda zata kaya. Kudai yi react na channel pls 🙏 Masu Wattpad ayi vote 🙏 Kuyi sharing pls 🙏🙏🙏🙏 Daga Alkalamin F'aeeh Bg✍️✍️✍️ GIMBIYAR TASKIRA 👑👑👑 SHARING DA REACT SHINE ABUN DA ZAI BANI DAMAR ƘARA MUKU YAWAN PAGE ✍️✍️✍️ Firstlady 🙌🙌🙌🙌🙌🙌🙌🙌🙌🙌 Vote pls,And sharing,and following pls 🙏 Zaku ji Ni shiru hakan yasamo asali ne da jarabawar da zan rubuta. Ina godiya masoyana🥰🥰🙏 masu bibiyar RAYUWAR MU AYAU da kuma A MAFARKI NASANTA BOOK. Soyayyar ku da ban ta ke agare ni kune ƙwarin guiwata🥀🥀🥀 🌸*RAYUWAR MU AYAU*🌸 Ƙarya ko sakin Aure Short story Labari da rubutawa Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> 💤A MAFARKI NASANTA WRITER 💤✍️ P6. *Alhamdulillah mun dawo kan aiki .Allah ya Bamu ikon kammala shi lafiya.* *Naga Addu,oin ku Nagode sosai*🤲🤲 <<<>>><<<>> Yau tun safe yake jin faɗuwar gaba tun bayan kiran sa da aka ce ogan nasu nayi. Sai kai da kawo yake yi kamar wanda ke Aci ki n matsananciyar damuwa. " Jamilu wai lafiya kakasa zaune ka kasa tsaye tun ɗazu nake lura dakai tun da aka ce maka oga na kira ka susuce,wai me yake faruwa ne kuma ka ƙi magantuwa,kar dai ace zan cen da kake faɗa mun ne ".? Furucin Gariti. Shiru yayi masa sai dai zufa kawai da yake ta faman sharcewa.Zuciyar sa ta kasa tsayuwa waje ɗaya bare ya samu natsuwa ya rasa abun da yasa ogan nasu ke neman sa a yanzu da sanyin safiyar nan. " Wallahi hankali na tashe yake Gariti ban san me zan tatar ba haka da safe,kai da jin irin wannan kira na tun da safe haka ka san ba lafiya ba bare ma Ni da nasan abun da ake ciki kan abinda ya faru juya". Ya bawa Gariti Amsar tambayar sa. " Ohh wai neman ka da yake yi ne ɗin dagaske ya ta yar maka da hankali,kawai kayi kamar wani abu bai faru ba kawai shine abinda zai saka ka samu natsuwa wallahi,tunda komai ya riga ya faru yanzu haka ma Alkhairi ne ke bin ka,Ni ina da tabbas ba abinda zai faru sai alkhairii ". Ɗan Nisa wa yayi bayan gama sauraren Bayanin gariti inda yake tuno da maganar da yayi masa jiya da yace ya gane sa ashe kuwa da gaske ya gane sa gashi yau tun da safe an neme sa a office. Ɗan rufe idanun sa yayi kafin ya miƙe yana furta " Gariti Gwaska Tanim fa Shegen kanshi ne ina tsoron naje na tarar da kora shine abinda ke tayar mini da hankali,Amma zan bawa zuciya ta natsuwa na tafi haka". " Lallai kam Gara ka tafi kafin ya ƙara yin wani aike ". Gariti ya furta fuskar sa babu wani alamun dariya ko ko tausayi domin a ganin sa ko me ne shi yaza jawa kanshi. *** Zaune yake kamar wani mai mulki sai juyi yake yi kan kujerar sa a cikin office ɗin nasa.Kamar ko da yaushe cikin shigar sa ta ƙananan ƙaya sai dai yau babu p - cap akan sa sai uban ƙitson nan da yake kama ta na zare irin na mazan nan wanda bai wuce tsoro goma ba haka.Sai sarƙunan dake wuyan sa na zinari da kuma na Hannun sa.Fuskar nan Babu wani annuri acikin ta. Sallamar da yayi ce cikin office ɗin ta bashi damar ajiye wayar tasa bayan sanar masa da zuwan sa da a kayi inji secretary nasa. Tsaye yayi kamar wanda aka tsamo a cikin ruwa kuma a tsorace bayan tsintar kan sa cikin ƙaton office ɗin. " Seat ". Ya furta masa a taƙaice yana mai nuna masa kujerar da ke facing ɗin sa a gurin zaman client. Zama yayi mamaki na ɗan son shigar sa. Shiru office ɗin har sai da aka ɗauki tsawon Minti uku haka kafin Jamil ya buɗe bakin sa daƙyar ya furta " Yallaɓai gwaska ka neme ni kuma har yanzu haka ce komai ba. " Numfashi Tanim ya sauke kafin ya ɗan kalli jamil ɗin wanda har sai da ya ɗan tsargu sannan ya fara magana yana furta. " Jamilu Dama wasa da hankali kake mun da boutique da motoci,motocin ma masu tsada,nayi bincike yau da safe na gano aikin ka kenan yawo da motocin kamfani a gari yau da wacchan gobe da wannan,kai ko tsoro baka ji ƙaddara ta hau kai Asamu matsala kuma kasan Bama ɗaukar ƙadara in yazamo incident ɗin da gangan ya faru,Haka ma Zubair shima kaya kake aro namu gurin sa,wanda wannnan harda laifin sa da bai baka ba gobe baza ka dawo ba". Ɗan shiru yayi kafin ya cigaba yana kallon Jamil ɗin da zufa duk ta gama wanke masa fuska duk da A C dake office ɗin tana ta aiki "Me ye Amfanin ƙarya Jamilu rayuwar da ka ɗaukar wa kanka ba mai kyau bace ƙarya ba da wata rana kunya ake ji alokacin da komai ya ƙure". " Yallaɓai gwaska kayi haƙuri ". Jamil yayi furucin cikin ɗar ɗar da tsoro da mamakin wa,azin da yake jin ogan nasa na ƙoƙarin yi masa wanda yake ji kamar ya juya sa kan sa kan tasa ɗabi'ar da tafi tasa muni ba kaɗan ba tunda duk sun san halin ogan nasu. " Babu batun bada haƙuri Jamilu wannan abun kamar karye muna Alkadarin Company ne yanzu wani yagan ka da motar nan da nagan ka da ita jiya,yazo saye kuma ya same meta a kasuwa bazai ɗauke ta ba ,sai ma yaje ya yi ta yaɗawa muna hawan sabbin motocin mu kuma mu siyarwa da mutane haka nan,wani ma zai ce sabon fenti muke musu mu siyar bayan mun take su ". Ɗan shiru ya sake yi kafin ya cigaba da magana. " Me ye dalilin ka na yin ƙarya irin wannan ga Najiba ".? Ɗan shiru yayi kafin ya sauke numfashi yana furta " Najiba yar masu kuɗi ce kasani yallaɓai bana son ta fahimci cewa Ni talaka ne ta guje ni shiyasa nake ta ƙoƙarin yin yadda zanyi na same ta nasan da na same ta shikenan komai zai zo da sauƙi koda wani abun ya taso an riga an gama,ina son Najiba so bana wasa ba yallaɓai son Aure nake mata son ta zamo uwar ya ya na ".Yakai ƙarshen zancen dake fitowa har cikin zuciyar sa.Yana sauke numfashi. Tanim dake kallon sa kuwa wani irin murmushi ya sauke yana gyaɗa kan sa fahimtar komai da ke faruwa tsakanin Najiba da Jamil ɗin ƙaryar ƙarya ce tsakanin su kowa baya da gaskiya babu wanda yasan ɗan uwan sa wane ne da alama ko ƙofar gidan su Najiba bai sani ba tunda har ya iya furta yar masu kuɗi ce. Tsaida murmushin sa yayi yana kallon Jamil ɗin da shima shi yake kallo ganin yana murmushi. Ɗan gyaran murya yayi kafin ya furta " Na fahimce ka Jamilu kuma in dai haka ne zan taimaka maka ka samu cikar burin ka ". Ɗagowa yayi da sauri ya zubawa Tanim idanu jin furucin sa da kuma tabbatar wa idan da gaske yake yi. Kai Tanim ɗin kuwa ya ƙara girgiza masa dan ƙara tabbatar masa kafin ya ya ƙara furtamasa " I mean it ". " Sannan yanzu zan taimaka maka da wasu suturu haka akwai wayen da nazo da su daga America Sababbi da wasu na nan da na bari zan fitar dasu zan fitar maka dasu sai ka ƙara sai maganar mota zan riƙa Ara maka motor biyar haka zan fitar dasu sai ka riƙa hawa idan zaka fita,sai kuma Maganar kuɗi zan baka miliyan ɗaya sannnan zan Ara maka kayan lefe zan saka ayi maka ordern su daga America a shagon mi dake chan,Bayan Ɗaurin Aure sai akwashe zan saka a shiga da dare sai a kwashe komai zasu shiga a matsayin ɓarayi masu kwasar kayan,Sai maganar gida shima zan baka aro ma sati biyu haka sai ka koma wanda ka ta nadar muku ''. Haka yake sauraren sa har ya gama zancen nasa.Zaune yake kamar mutun mutumi bayanin na ogan nasu ya gagara fahimtar sa ko bashi Ma'auni. Numfashi ya sauke yana jin wani sanyi na ratsa zuciyar sa domin kuwa yaji farin ciki sosai ko ba komai Asirin sa zai cigaba da rufuwa har cimma burin sa.Wani Farin ciki ne ke ƙara shigar sa. Bai taɓa tsammanin haka uban gidan nasa yake da tausayi ba da duba lamarin wanin sa. " Nagode sosai Gwaska Allah ya saka da Alkhairii yasa Afi haka ya bada mata ta gari,kuma ya ƙara arziki mai Albarka,Naji daɗi sosai wallahi kuma in sha ALLAH zan kula maka da motocin ka ". Amin Tanin ya Amsa cikin jin daɗin Addu,ar ta Jamil. Sannan ya furta " ka biyo ni yanzu kaje ka karɓa,bar shi ma kawai muje tare ka haɗo kayan ". " Nagode yallaɓai ". Ya ƙara furtawa cikin ɗan murmushi,Bama abinda ya ƙara jin daɗin sa irin kuɗin da zai basa yanzu ya samu na sayin fili ranar da ya samu sai ya fara gina gidan sa. Bayan Auren nasu. Bin bayan sa yayi suka fice. A tare motar Tanim suka shiga wadda drivern sa ya ja sa inda shi ya kasance a extra seat na kusa da driver Tanim kuwa a baya hakimce. Yana fata da tuannin Allah yasa maganar da suka ƙara furtawa kafin fitowar su,A yanzu da Alƙwarin da ya ɗaukar masa kar ya buɗe sa wata rana gun Najiba har maganar ta fita... Jamilu shima dake zaune tunanin maganar yake tayi Amma yadda ga ɗau Alƙawari kamar yadda ogan nasa ya rufa masa asiri shima zai rufa masa nasa har Kowannen su ya samu abun da yake so kamar yadda ya roƙe sa.Sai dai ta wani ɓangaren Nadiya ta bashi tausayi domin bata san irin mijin da zata Aura ba bata.Duk da ya na ganin kamar ta sani tun da shi kan shi shaida ne abun da ya faru atsaakanin su acikin mota ranar wanda duka kamar kanwar ɗaya ce.Sai dai daga yadda Ogan na sa ya ke zance ya fahimci babu abinda ya shiga tsakanin su. Numfashi ya sauke yana juyar da kansa gefen titi tare da kallon ababen hawa dake wucewa. ☘️🌸☘️ " Malam Abdul basiɗ Barka ". " Barka Malam Nasiru ya kasuwa ya hidima kuma ya lokaci "? '' Alhamdulillah lafiya lau malam Abdul Basiɗ ". " Magana ce nazo da ita mai mahimmanci,naga ya kama ta na faɗa maka ita da wuri ku ɗau mataki ". " Ba komai malan Nasiru Ina sauraren ka ". " Eh to maganar akan yar wajen ka ce Nadiya ". " Ina sauraren ka malan Nasiru,dama nasa n maganar gizo bata wuce ta ƙoƙi ". Malam Abdul basiɗ

Chapter 4 of 39