Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kun san ba akan dai dai kuke ba.Mu daina zubar da ya ya dan Allah.Ciki kona halal ne zubar dashi bai dace ba._ Allah ya sa mudace ya nisan ta mu daga aikata Zina._ _Ya shiryar da masu yin ta._🤲🤲 _Allah ya shiryar damu ya shirya muna zuri'a.Amin_.🤲 ~~Kuyi haƙuri na cika muku page da surutu.~✍️🙏🙏 *Mu koma cikin labari.* 🔥💋💋💋🔥 Numfashi malam Abdul Basiɗ ya sauke bayan tsaida zancen zucin sa , Yana ƙara jin Tausayin jinjirin sannan yayi murmushi yana furta " Muje ba sai an sanar musu ba,ya kamata shima likito su duba shi idan lafiyar shi ƙalau kamar yadda muke hasashe Dan alamun sa sun nuna cikin ƙoshin lafiya yake,Kalli yadda yake waro ido ɗan neman ". Ya kai ƙarshen yana dangwaro Hancin sa a hankali cikin yar ƙaramar dariya ganin yadda Muhammad ɗin yayi kamar yaga abinda yayi masa ya zura masa idanu kamar yana ganin sa.Suma su malam Rabu'u Dariya suka yi kafin suka fice zuwa a sibitin,bayan Sun sayo gidan. 💃💃💃💃💃💃 Alhamdulillah na san yau zanga react na murmushi da na soyayya masu kuka sai ashare hawaye Nadiya'r mu ta dawo kun san koni ina gefen ta. Like,share and comment.✍️✍️✍️🙏 Daga Alƙalamin ✍️✍️ *Fa'eeh BG* *FIRST LADY 🙌* *GIMBIYAR TASKIRA 👑* *_Typing_*📱 https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y _Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_ *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim *✍️TEAM TAURARI HUƊU✍️* ⭐⭐⭐⭐ _Fa'ee BG_ *RAYUWAR MU A YAU* _Matar Habibi_ *NIKEH DA IKO* _Haandy_ *NIKKAH ( MARRIAGE FOR RENT )* _Oum Amjad_ *RAYUWAR JANNAH* 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ P.34 A dai dai lokacin da su Suka gama waya da Malam Abdul basiɗ a dai dai lokacin ne kuma Tanim ya isa office ɗin da ya kasance Mallakin mahaifiyar sa bayan yayi ta zuba ido ya ga ta inda zai ga Najiba ,ko ta ɓullo sai dai har ya gama zagaye bai gan ta ba kuma bai tambayi kowa b.Kawai ya yi amfani da sunan Da ke Ɗauke a jikin office ɗin ya kutsa kan sa da sallama ɗauke a bakin sa,hakan kuwa sai da ya san ya shi jin wani iri kasancewar ya kwana biyu bai yi sallama bar ba ma ga shi kuma a inda bai taba tunanin zai samu kan sa a ciki ba. Idanun ta, ta zuba mishi ƙirjin ta na ƙara bugawa tabbas hasashen ta gaskiya ne yanzu ta ƙara tabbatar da abun da ta gani da idanun ta.Ko rantsuwa tayi ta san bazata taɓa yin kaffara ba Wannan Muhammad ɗin nata shine Mahaifin Ɗan Nadiya domin kasancewar shi a gaban ta ya ƙara tabbatar mata da lissafin ta Dan yadda ta sunɓulo shi yana karami haka ta ga Muhammad ɗin Nadiya sak kamar an tsaga kara. Numfashi ta sauke mai zafi duk da tana cike da mamakin yadda hakan ya kasance sai dai kasancewar ta san da Auren sa ya sa ta bar shi a matsayin Matar shi ce. To shiko Ya sayyadin da ta taɓa furta Miki fa. Zuciyar ta ta tambaye ta,shiru tayi tana jin ɗayar zuciyar ta na bata amsa,da ina ga sunan Soyayya ne ta bashi,bata iya faɗin sunan sa.Wannan tunanin ya sa Murmushi suɓuce mata wanda bata taɓa tsammanin fitowar sa ba. Inda ya bayyanar da zallar farin cikin da take ciki. " Seat " Ta furta cikin bashi umurni. Kan sa ƙasa cikin wani irin yanayi ya kai zaune bata re da ya bari sun haɗa ido ba saboda wani irin kwarjinin ta da yake ƙara ta so masa da wani irin ɗauki na ta da ya daɗe bai ji sa ba.Tun yana matashin sa a lokacin da yake ƙoƙarin cika shekara Bakwai. Ajiyar zuciya ya sauke yana ƙara yin ƙasa da kan sa. Numfashi ya sauke itama haka kafin ta furta " Matar ka ta haihu,sai dai ban san dalilin ka na ƙin zuwa nan ba,kuma kana kusa ". Ta yi zancen kai tsaye ba tare da jin komai ba,kamar chan baya da take kasa magana dashi sai ta ji kamar an rirriƙe ta. Idanun sa da suka ɗan ƙara rikiɗewa ya ɗago ya zuba mata su kafin ya sauke Ajiyar zuciya.Sannan ya ce " Ta haihu ɗan ya koma ,kuma ta bi shi haka na samu labari gurin Najiba". Ya bata amsa kai tsaye Dan bai yi mamaki ba saboda ya san likita ce ta yuyu ta san komai game da Nadiya,duk da yasan bata taɓa ganin ta ba matsayin matar sa,Wanda har yanzu yake mamakin yadda ta ke magana kai tsaye kamar babu wani abu a tsakanin su. Shi kan shi ma da yake tsaye gaban ta abun ya bashi mamaki dan a chan baya bai iya ko kallon ta a matsayin mahaifiyar shi. " Son ". Da ta ambata ne murya a karye cikin wani irin yanayi ya sanya shi ɗagowa ya zuba mata idanun sa sai dai ya kasa iya amsa wa dan wannan ne karo na farko da ya ji ta ambaci hakan tun ta shin sa kuwa bayan shuɗewar shekarun baya. Hawaye ne suka cika idanun ta na farin ciki jin ya amsa mata sai dai sama sama dan baida wani zarran da zai iya Amsawa da iya ƙarfin sa ta yadda zai gamsar da ita. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya yi ƙasa da kan sa.Jikin shi na ƙara yi masa wani irin sanyi. " Me ya hana ka zuwa asibitin matar ka na naƙuda, ". Ta yi masa tambayar tana kallon sa. Rasa abinda zai ce mata yayi sai ya yi shiru. Sai dai ta ƙara maimaita masa sannan ya sauke numfashi yana furta. " Na raba igigiyoyin ". Fahimtar abun da yake nufi hakan ya sa bata ce masa komai ba sai ma idanun ta da ta rintse da ƙarfi ƙirjin ta na wata irin harbawa me ya sa zai aikata haka me ya sa ya samu matar sa ta shiga tsara mai mutunci,to amma yaushe ya Auren na su ya mutu. Ta ƙara tambayar kan ta sai dai bata da mai bata amsa. " Me ka sanar mata da yayi sanadin halin da ta shiga a gadon asibitin ". Shiru yayi mata babu amsa Dan bai san yadda zai sanar da ita.Shi ya san cewa bai duba wa lamarin ba,kamar babu imani a cikin sa. Ganin Hakan ya sa ta miƙe ta fice inda shima. Ya biyo bayan ta yana sauke ajiyar zuciya ganin ta share zancen. Su malam Rabu'u da ke tsaitsaye da jinjirin a hannun su suna nuna wa Su Mama Laure da bakin ta yake washe kamar gonar Audi ga Dan tunda ta samu labarin Tashin Nadiya sai kukan ya ƙafe ƙaff sai Hamdala take ta Zubawa.Haka ma Mama Hasiya dukkanin su mamaki suke yi da al'ajabi na yadda komai ya kachame daga baƙin ciki zuwa ɗimbin farin ciki sai dai sun yarda da cewa lallai Allah mai girma ne shi yake yin yadda ya so ga bawan sa cikin ikon sa yau ga Nadiya da Muhammad a cikin jerin mutanen da ke rayuwa a doron duniya,duniyar da aka cire musu rai Duniyar dasuka bari ana tsakaa da ƙaunar su. Har sujudu shukru sai da suka yi cikin farin ciki Bayan isowar su malam Rabu'u ɗin. Tun da ta doso wurin take kallon yadda Mama Hafsatu ke bin jinjiri da kallo a hannun ta sai kallon sh take yi kamar ta samu hoto tana sakin murmushi hakan ya sa da azama ta ƙara sa gurin kasancewar ba chan zata je ba zata shiga ɗakin da Nadiya take ne. Turuss ta ja ta tsaya tana bin kowannen su da kallo ganin abun take yi kamar mafarki,kumatun ta ta buga kaɗan Dan farin ciki yana neman suƙe ta lokaci ɗaya,yana neman yaye mata duhun da take ciki na wannan rashi musamman yanzu da ta ƙara tabbatar wa da kan ta Nadiya surukar ta ce matar Muhammad ɗin ta ce namiji ƙwal ɗaya a cikin ya yan ta kuma shi ɗaya tak a gidan Mahaifin sa Alhaji Abdulkarim. Kallon ta Malam Abdul basiɗ yayi ya lura da yanayin da ta shiga sai kuma idanun sa suka sauka akan Tanim dake bayan ta shima jikin sa na wani irin Amsawa. Kan sa ya ɗauke da ga kallon sa yana mamakin kamannnin sa da likitar kafin ya furta " Likita Kinga ikon ALLAH ko ". " Ashe Muhammad na da sauran shan ruwa kamar dai mahaifiyar sa ". Nan ya labarta mata duk yadda aka yi. Wani irin farin ciki ne ya mamaye Dr Abida ba ita kaɗai ba harta Tanim dake tsaye ya kasa iya furta komai sai shawagi zuciyar sa ke yi na abinda ya aikata. Tare da wata irin nadama da ta shige sa lokaci ɗaya na tausayin Jinjirin nan da ya yanzu yake kallo akan fuskar sa kasancewar Dr Abida ta karɓe shi bakin ta washe.Godiya take ta zabgawa gurin Ubangiji inda sai hawaye suka wanke mata fuska. Shiko Tanim ya kasa matsawa ya karɓi jaririn gani yake kamar kowa ya san rashin imanin da ya nuna mata ta hanyar sakin ta kan gadon asibiti,asibitin ma a gurin haihuwa,kan dokin naƙuda mai wuyar fita,da kuma cin zarafin da yayi mata. Mama Hasiya kuwa dake bin shi da kallo a fakaice ba ta iya cewa komai ba sai ma ɗan bin shi da take yi da kallo shi da Dr Abida abinda ta gani take son tabbatar wa dan in ba idanun ta suka nuna mata ƙarya ba wannan jinin Dr ne daga goshin su da hanci zaka gane jini ɗaya ne ke aiki a jikin su ko haka ma ga kama nan ta bayyane,kamar dai shi jaririn. Juyawa Tayi a hankali kasancewar yana bayan ta ta miƙa masa jinjirin duk da yadda take jin wani irin Haushin sa da kuma wani irin ƙololon da ya farmata na sakin da yayi babu wani lissafi bata san abun da ya shiga kansa ba har zai saka shi ya yanke irin wannan ɗanyen hukuncin da kake yin nadama a take, dan haka zata sa ya mayar da Auren idan komai ya lafa. Karɓa yayi yana jin hannun sa na rawa musamman da yanzu duk suka Zuba masa idanu iyayen Nadiya ɗin da duk ya san fuskokin su ta Mahaifiyar ta ce bai sani ba dai yanzu wanda ya gane hakan ne ta hanyar kamar da suke yi da junan su ta yanayin fata da komai. Suko kallon mamaki dukkanin su suke bin Dr Abida da ta miƙa masa shi sai dai babu wanda ya iya furta komai,sunyi mamakin yadda ta san shine mijin Nadiya ɗin dan su sai yanzu suka Ganshi ma.Ita ko Mama Hasiya murmushi kawai tayi da yafi kuka ciwo haka ma Malam Abdul basiɗ da su malam Rabu'u da Malam Adamu kai kawai suka girgiza Dan suna zargin wani abu sai tsakanin sa da Dr ɗin ganin kammanin su bayyane da ita.Sai kuma yanayin gashi da Tanim ya shiga kamar wanda ya aikata wani abu a ranar da ya kamata yayi farin ciki. Wandon sa da yake a saɓule yayi azdown ya ɗan gyara a fakaice saboda yadda yaji nauyin shigar ta sa a yau kurummm Dan ma Allah ya sa yau ya cire sarkunan da ya ke maƙalawa a wuya kamar wani mickel. Sai dai kuma su yan kunne suna nan maƙale A kunnen sa Tatto ɗin sa kuwa tafiyar da yayi kwanan baya ya sa an cire masa shi haka kawai ya ji baya ƙaunar sa.Sai sarƙunan sa da yake jin nauyin su yanzu kamar ya ɗakko kaya masu nauyi. Saboda duka na gold ne mai kyau. Zuba ma yaron idanu yayi cikin yar natsuwar da ya samu Dan su Malam Adamu sun ɗauke idanun su kan shi suna masa fatan shiriya Dan sun san ƙaddara ce kawai ta haɗa Nadiya da Auren sa saboda ba mutumen ƙwarai bane tun binciken farkon su suka gane hakan sai dai basu san yadda aka yi ba komai ya juya ya koma.yadda ba su tsammana ba sai dai sun bar shi hakan sun san hakan Allah ya rubuta mata wanda gashi harda Rabo a a tsakanin su,dama rabon ne ƙila yake kira sai dai suna mishi fatan shiriya.Allah ya kimtsa wa Nadiya shi ya koma mutumin kirki kamar yadda suke son sa. Idanun sa ne yaji sun cika da hawaye ganin yadda yaron da yaji an kira da suna Muhammad yake ta kallon sa kamar yana gane ko wanene shi kamar yadda shima yake kallon sa cikin son shi da yake kutsa jinin sa.Da Tausayin sa da na Mahaifiyar sa da yake jin lokaci ɗaya ya mamaye sa ba kamar da ba wanda har yanzu yake cikin shakkun lamurran sa da suke a bai bai bayan munanan ɗabi'un da yake yi ace harda kawar da kan sa ga mahaifiyar sa yadda yake rayuwar sa ba tare da ya damu da ita ba kamar bata cikin duniyar sai dai ba haka bane, ayanzu yana jin kamar akwai abinda ba dai dai ba tabbas. Ajiyar zuciya ya sauke tuno warin da sauran Abokan na su suke yi wanda ya ji har yanzu babu wanda yayi maganar ya ji a jikin shi ko wani ya daɗe hanci inda hakan yayi masa wani irin daɗi sai ya samu kan sa da gode ma Allah da kuma jin wata irin nadama na mamaye sa domin ya san wannan duk da ga cikin hukuncin Ubangiji ne daga cikin laifukkan su da suke aikawata duk da ya san bai daɗe yana aikata ɓarna irin ta su ba yayi zaton ya samu irin na su hukun cin sai dai Allah mai jin roƙon bayin sa ne sai ya tsame shi daga hakan,domin kuwa Addu o,in da Mahaifiyar sa ke masa ba da dare ba rana basu rasa na saba da tsirar sa daga wannan mugun warin da ya shaƙa wanda har yanzu bai daina jin tashi tashin sa ba kuma har yanzu zuciyar sa tana ɗagawa daga warin kamar zai amayar da komai na sa ya rasa gane wane irin wari ne wannan.Hawayen da suke neman zubo masa ya san ya hannu ya goge da sauri yana hana su zuba a karo na biyu zuciyar shi tayi wani irin yaushi nadama kala kala tare da Tausayin yadda rayuwar shi zata kasance,Musamman yanzu da ya tuna yadda ya zalunci Nadiya ya san Allah bazai taɓa barin haƙƙin wani akan wani ba.Numfashi ya sauke yana miƙa ma Dr Abida Jinjirin da yake jin kamar kar ya rabu dashi cikin begen sa. Ita ma Murmushin ta yi mai haɗe da hawaye ganin Muhammadu Tanim na zubar da ƙwalla abinda bata taɓa gani ba ta san hakan bai ra sa nasaba da nadamar da ta fara shiga jikin sa ta sakin Najiba da bata san ko nawa bane har yanzu.Tausayin sa ne ya kamata idanu kawai ta zuba masa ta na ƙare masa kallo shi ko kan sa ƙasa.Ɗakin yara ta wuce da Muhammad ɗin tana bin shi da kallo cike da soyayya da tausayi ba komai yasa take jin tausayin shi ba kamar yadda yanzu wai iyayen sa basa tare,ta rasa yaushe aka yi sakin da bata jiya ba,koda yake ta ya zata jiya in ba ma idanun da ta sanya suka kawo mata rahoto ba.Take aka fara duba Muhammad ɗin sai dai cikin ikon Allah babu wani abun da yake damun sa kamar an yaye masa komai lafiyar shi garass a yanzu kamar yadda ake haifo kowane jariri mai lafiya,sai wuntsila ƙafafu yake yi yana buɗar idanu kamar yana gane wane abun. Duk ya zuba ma Dr Abida idanu wadda ke riƙe da hannun sa ɗaya ido sai ta saki Murmushi tace Kasan Granny Jazlan. Sai ta ƙara sakin murmushi idan ya ɗan rufe idanun sa kamar ya ce mata eh. Sai dai ganin yana lumshe idanun sa hakan ya sa ta ta gyara masa kwanciya take bacci ya kwashe sa.Ɗauko shi tayi,bayan sun tabbatar da Babu wata matsala sannan ta kai shi ɗakin da Nadiya take,inda ta ɗaura shi akan ɗan ƙaramin gadon yara kusa da na mahaifiyar shi dake ta shan bacciin wahala na Alluran da suka bata. Ficewa tayi daga ɗakin Dan zuwa duba Najiba dake ɗakin haihuwa wadda ta dubo bada daɗewa sai dai Midwives dake gurin sun tabbatar mata da naƙudar ta kwanta dama akwai abun da ya tayar mata da ita. Ganin komai lafiya lau,sai Bp ɗin ta da ya ɗan hau ne wanda suka bata allurar bacci. ya sa tayi Hamdala tare da ficewa daga ɗakin. Midwives dake kula da ita ne suka je suka sanar da su Mama Hasiya halin da ake ciki dan yadda sabon EDD ɗin ta ya nuna sai wani sati irin rana wata yau. Cikin farin ciki suka yi musu godiya. Inda sai godiya suke ga Ubangiji da ni'imar da yayi musu. A ɓangaren Tanim kuwa haka kawai yake jin wani irin nauyi yana dabaibaye shi ga yanayin jikin shi yana jin ya chanza masa tun kwanakkin baya yake fama da ɗacin baki da rashin kuzari sai dai ya kasa zuwa asibi,kuma yana shan maganin maleria duk da bai haɗa hanya da ita ba sai dai kamar abun na ƙara yin gaba.Hakan ya sa ya fice daga cikin asibitin ba tare da sanin Dr Abida ba. Sai dai bayan fitowar ta samun shi wayam babu halittar sa a gurin ya sa bata damu ba sai dai kuma tana son sanin dalilin sakin nasa,da kuma nawa ne yayi a yanzu amma zata bari har Nadiya ta farka taji komai. Sai da ta tabbatar komai yazama normal sannan ta koma gida ta bar bakin zata dawo Anjima. A ɓangaren Najiba tun da ta dawo hayayyacin ta,bayan bacciin ya sake ta kasancewar allurar ba mai ƙarfi ba ce kamar ta Nadiya kuma jinin ta na da ƙarfi.Tun farkawar ta take zaune jugum kamar wadda ta rasa duk wani jin daɗin ta. Babu abun da take yi face tunanin wai yar uwar ta ta fi sai hawaye shar suka,wanke mata fuska kafin kuka yaci ƙarfin ta mai mugun karfi,ga wata irin tsanar Tanim da take ji lokaci ɗaya. Nurse ɗin da ke kula da ita kuwa kallon ta take yi tun ɗazu kamar tayi magana kuma sai kuma ta fasa, sai kuma yanzu da ta ga Kukan da take yi ya fara yawa kar ta ƙara janyo wa kan ta ciwo dan ta kukan bai wuce na zancen mutuwar yar uwar ta ne da ta farfaɗo ita da abun cikin na ta wanda suke tunanin sun rasa dukkanin su a farko. " Kiyi haƙuri yar uwa,Komai yayi tsanani yana tare da sauƙi,Ki godewa Allah ba kuka ya kamata kiyi ba murna ce ta dace dake,domin kuwa baƙincikin da kuke ciki ya yaye dan Yar uwar ki ta dawo duniyar mu dama Doguwar suma ce tayi,haka ma.jinjirin ta wanda har an masa wanka sai dai cikin ikon ALLAH ya farfaɗo shima cikin ƙoshin lafiya " Kalaman wannan nurse sun mata wani iri Dan haka ta zuba mata idanu sai dai kan da ta gyaɗa mata dan tabbatar mata da zancen ta hakan ya sa ta sauko daga kan gadon da sauri. Har nurse ɗin na ce mata bi a hankali kar ki ƙara tado da naƙudar tayi zancen tana sakin ɗan murmushi. Najiba kuwa bata saurare ta ba sai ficewa da tayi da ɗan saurin ta Nurses basu hana ta ba kasancewar sun san inda zata je kuma tana da sauran ƙarfin ta suka bita kawai da idanu. Zancen ya kasa ɗaukar ƙwaƙwalwar ta Dan haka ji take kamar ta yi ƙara duniya ta ji gaba ɗaya yadda zata tabbatar cewa ba hauka ke shirin kama ta ba domin ko afilm bata taɓa jin wannan labari ba ace dukkanin su sun rayu lallai Allah azimun ne.Yanzu Nadiya'r ta zata iya numfashi tayi magana ,kamar kowa hakan ma.Jinjirin zai girma idan Allah ya rubuta masa. Wani kuka ta ɓarke dashi bayan gama jin bayanin da Mama Hafsatu take mata bayan isowar ta gurin.Haka ma RALIYA da ibrahim ya kawo yanzu wadda Mama Hasiya ta kira, kukan take yi mai cike da zallar farin ciki da godiya ga Ubangiji domin hakan babbar ni'ima ce a gare su. Haka aka taru ana ta Rarrashin su har suka lafa,sannan aka fara yiwa Najiba ya jiki.Jamil da yanzu ne isowar sa shima Dan Najiba tun ɗazu ta kira shi sai dai yana hanya lokacin ya kwaso jama'a. Kallon ta yake ta yi cikin tausayi sai dai ya kasa matsawa kusa matar sa saboda iyayen su dake gurin wayen da ya gaisa dasu cikin mutunci. shima ya shiga shock sosai na wannan lamari ashe bai sani ba har Rashi aka yi wanda ya koma samu lokaci ƙalilan. Jaje yayi musu bayan jin yadda komai ya wakana cikin tausayin Najiba da ya san yadda tsakanin su yake da Nadiya. Gida aka ce gaba ɗayan su su koma.saboda jikin su yayi nauyi duk yadda Najiba ta nuna naci haka iyayen su suka saka mazajen su suka mayar dasu gida badan dukkanin su sun so ba. Wanda ya zamo an bar Mama Hasiya Kawai da Mama Hafsatu. Sai gab da Bayan Isha ta koma gida ko shi da faɗa da tsawatarwar malam Abdul Basiɗ sannan ta koma gida Dan ba haka ta so ba dan taso ace ita zata ragargaji uban kayan jinya da aka kawo daga gidan su Tanim ɗin inda Dr Abida ta shiryo su ita da Sahiba da mai aikin su ga kayan shayi nan zube suma duk wani abun buƙata dai an kawo musu.Dangi kuwa babu wanda bai zo ba matan dama suna mugun ƙaunar ɗan uwan na su dan haka suka masa kara babu wadda bata je ba ita da iyalin ta suka ga ɗan sa sai dai shi uban gayyar babu shi a wurin tun fitar da yayi.Hakan sai ya ƙara ɓata ma Mama Hasiya rai tana son yiwa Dr Abida magana wadda ke ta kai kawo sai dai ta kasa,mamakin ta har yanzu shine bata ji zancen sakin da ya faru yan daƙiƙu da suka wuce bakin ta ba sai ma kamar tana cikin farin ciki fiye da yadda su suke,Wanda ta tabbatar da cewa ɗan ta ne bayan zuwan yan uwan sa mata da suke ta yabon Nadiya ɗin a yanzu dan suma sun san tana haƙuri dashi saboda duk wanda zai iya zama da mashayi kuma mazinaci a jinjina masa dan basu taɓa tsammanin zata zame masa ya ba shi ya sa bayan Auren da suka ɗauko ta mahaifiyar su tayi ta kwaɓar su akan kushe gidan da Nadiya ta fito ita fatan ta da burin ta shine Ya samu wadda zata zamo sanadin shiryar sa,ya koma cikakken mutun domin duk wani abu da yake yi yana sane a tafin hannun ta yake abu ɗaya ne shine wannan ƙungiyar ta su itace bata san da ita ba dan bai daɗe da shigar ta ba,Amma shaye shayen sa da neman matan sa babu wanda bata sani ba,har ciwo take kwantawa kan halin da yake cikin sai dai bata gajiya da masa Addu'a, dare da rana

Chapter 29 of 39