Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haka aka musu bayani kasancewar bashi kaɗai ne boka anan ba,amma an tabbatar musu da nasa aikin kafin isar ka gida ma an gama shi na kai tsaye ne. A haka suka ciga a da kutsa kai cikin rumfar da ke ɗauke da sassan jikin ƙwarangwal sai reto suke yi da wasu irin ɗaure ɗaure nan suma Babu kyan gani,da rubutu ka takarda wasu ɗauke da sunan ayoyin Allah wasu ɗauke da wani rubutu shi ba larabci ba shi ba namu Yaren ba.Abundai ba,a cewa komai. Da baya baya suka fara tafiya dai dai sun kawo cikin bukkar da kana tafiya kamar kana dawowa baya.Basu damu da hakan ba dan an musu bayanin komai.Hakan ya sa suka cigaba da tafiya suna yi suna tsine ma bokan Albarka kamar yadda aka sanar musu ƙaidar shiga gurin kenan idan ba kayi wannan tsinuwar ba tare da zagi mafi muni gare sa ba zasu taɓa ganin sa ba ya bayyana a gaban su ba.Haka ko suke ta auna masa zagi abun haushi abin dariya da baƙin ciki,Wani zagin bai da ko daɗin ji.Kamar yadda aka sanar musu kuwa bokan nan bai bayyana ba sai da ya ji zagin da suka masa ya shige sa sosai sannan ya bayyana a gaban su yana hurar hanta kamar jakin da ya ci wahala. Sai kuma ya ƙanƙame jikin sa da Numfashin sa kamar yadda kuka san jaki ya samu alewa.😅Kun san jaki zaƙi illata sa yake yi,gaskiya duk wanda aka kira jaki an cuce sa cuta mafi muni,kun san saboda sakarcin jaki da wawancin sa,idan aka bashi Alewa saboda gudun daɗin ya ƙare sai ya daɗe duk wata ƙofa ta iska a jikin sa daga nan kafin a an kara ya kai ƙasa ya kashe kan sa,saboda kawai kar zaƙin ya tsere ta wata hanya,yallaɓai ya toshe hanyar numfashi.🤣🤣🤣 Da nayi zancen Jaki sai na tuno da malam da yan bidi'a suka saka masa sunan jaki😥,kan kawai ya faɗi gaskiya da tsantsar tauhidin sa. Allah ya jiƙan Dr Idris Abdul Aziz Dutsen Tanshi.Allah ya cigaba da haskaka makwancin sa.🤲 Sakin jikin na sa yayi tare da sauke wata irin atishawa ta bayyanar da wani irin mugun tumbin sa da basu gan sa ba sai yanzu, dan yanzu ya bayyana wanda yake dai dai da cikin wata tara yau ko gobe baƙi ƙirin da shi.Ƙara hura Hancin sa yayi sannan ya fara yan tsibbace tsibaccen sa kafin ya Kalle su daga zaunen da suka kai cikin farin cikin da ya mamaye su sun san tabbas wannan hatsabibi daga Nin sa za suyi na sara, ga dariyan na cin su ta gefe ɗaya tana tun ƙuro su saboda cikin na sa abun adara ne sai hurar hanta yake yi shi irin ba wasa kuma riƙaƙaƙen boka. Take bayan ya gama ƙare musu kallo ya sanar da su abinda ya kawo su.Cikin sauri suka ɗaga masa kai alamar haka ne. Wasu irin ƙwaryayya ki ya janyo wasu da ruwa a cikin wasu babu,mai ruwan ya janyo gaba,yayi wasu ƴan surƙullen sa sannan ya basu bayan ya haɗa da jinin da ya ɗan Yanko ta ciki ya zuba daga hammatar sa da yayi amfani da rexo wadda take cike da tab da gashi kamar kan mahaukaciya,kuma jinin na gama zuba ya koma kamar ba,a fasa ba. Duk suna kallon sa kuma basu ji komai ba Haka suka karɓe jinin dan shan sa ba wani baƙon abu bane tun wanchan bokan na raye suke wa jini shan kunu ko shayi dan cikar burikkan su. Ba su ji ƙazanta ba ganin inda jinin ya fito suka kwankwaɗe abun su daga cikin ƙwaryar da ya zuba sa wadda take ta mugun ɗoyi da alama akwai wani abun bayan jini a ciki kuma yafi jinin muni. Abun da basu sani ba ita dai wannan ƙwarya ta Wannan boka da ake kira hatsabibi ta kasance Ƙashin sa yake jiƙawa wanda yake yi idan yayi ya bushe sai ya jiƙa sa ruwan sune yake tarawa a cikin wayen nan ƙwaryaye dake kusa dashi kamar dai wannan da ya basu,kuma hakan shi ne ke saurin wanzar da aikin sa kamar yadda sheɗanun baƙaƙen ƙazaman Aljannun da ke masa aiki ke buƙatar hakan.Duk yadda suke jin zukatan su na na tashi haka suka shanye ruwan nan ɗai bayan ɗaya. Sannan suka dire masa ƙwaryar. Suna direwa kuwa ya keta wata irin mahaukaciyar dariya ya na cewa " Zaku daina wari,zaku daina wari,Zaku daina warin mushen Alade domin shi ne kuke yi a yanzu ina mai tabbatar muku ko gida ba zaku koma ba zaku daina wannan warin dan Kutumar Uban..🤭". Yana cikin zancen ya saki wata arniyar tusar da ta kusan sumar da su domin warin ta ya ɓace.Yana sakin tusar sai ya ƙara shan mur daga dariyar da yake yi.Yana zare zaren ido bakin sa kamar bolar ƙazamai. " Wannan warin tusar da qarnin da kuka ji warin jikin ku sai ya fishi da baku zo nan ba,Ɗan duhu da ƙazami sun gama aiki zaku wala kamar kowa wannan ruwan da kuka sha muddin kuka samu kuka kusanci yaron nan daga komawar ku komai ya kammala cika aikin mu gama wanzuwa,daga shi har uwar sa babu wanda zai ƙara numfashi,Sannan ɗan sa ma zai tagayyara rayuwar sa zata zamo Abar tausayi,iskancin da zai tashi da shi sai yafi na turawa hhhhhhhhh Ɗan duhu,ƙazami "....Ya kai ƙarshen maganar yana ɓaɓɓaka dariya kamar taɓaɓɓe sabon Kamu. " Ku tashi ku fice Yan iska,Masu zuciyar Fir'auna,masu gadon mutanen luɗu,Mazi nata yan wahala,Masu Auren Junan su ƙazamai Masu asarar Rayuwa Jakuna a cikin al umma, Dabbobi,ku tabbata kun tsotsa bakin ɗan Ɗan duhu da ƙazami kafin ku wuce,Suna son hakan,idan ba kuma baku aikata ba Ko na lafira sai ya fiku jin daɗi ". Rarraba ido suka fara yi daga tsayen da suke kowacce kamar zata yi fitsari a wando jin furucin na sa na ƙarshe ga kuma wani zance da ya sako ciki wanda basu taɓa tunanin akwai wanda ya sani ba face Allahn su amma gashi boka na faɗa. Tashin hankalin da suke ciki ya mantar da su cewa boka ne fa suke tare da shi mai aiki da aljanu.Mushriki. Yadda yake zarar idanu zai tabbatar maka da tabbacin zancen nan na sa ga ƙaton tunbin nan na sa kamar ana ƙara masa girma ganin yadda Shegen ya cunno bakin sa da dauɗa ta dafe ya sa su kallon juna Dan dama suna tunanin ya zasu tsotsi bakin aljani a she aljannin a jikin sa yake ana su tunanin. Hakan ya sa da sauri Jaruma ta matsa ta haɗa bakin ta da nasa ta fara tsosa jiki na rawa har ta kai ta kasa ɗauke bakin na ta saboda garɗin da take ji a ya mutsasin miyan bakin sa da warin su da qarnin su kan iya hanaka cin abinci na kusan sati ɗaya,Domin bakin na sa dauɗa ta ci uban sa sai wani kauri da suke dashi abun dai ba,a cewa komai.. Sai da ta sha miyan sa kamar ta samu ruwa sannan ta saki bakin tana sauke numfashi.Shi ko ko ajikin sa yadda kuka san dutse haka yake sai cikin sa da ke ture yana faman zarar ido. Haka Jamcy ta matsa itama sai dai ita kamm haka kawai take jin ƙyanƙyamin bakin na sa musamman da ta ga wasu irin miyagun Saliva sun diro daga bakin na sa da warin sa ya fara har gitsa ta bayan matsawar da tayi yanzu. Dariya ya fara gaggaɓawa ganin bata son matsawa hakan ya sa ta ƙarfi ya tara miyan da bata san ya akayi suka taru abakin na sa ba kusan jarka ɗaya ta swan ya juye mata a baki kafin ya fara tsutar bakin ta kamar ya samu alewa dama idan baka so haka suke maka.Kuma suna yin hakan ne dan kan ka sai ka dawo saboda Saliva n da ya ɗura mata a matsayin ruwa yanzu zasu hana mata jin daɗin ko ɗanɗanon kowa ne ruwa dake cikin duniyar nan idan basu ba saboda yadda aka Yadda ɗan duhu da ƙazami suka saka musu wani mugun daɗi a gare su.Wannan shine muguntar da yake yiwa masu irin nuna ƙyamar sa a fili.Daga haka kuma kina zuwa zuwa zai haiƙe Miki ta ƙarfi ko baki so.Ba Damuwar sa bace,A yanzu ma akwai dalilin da ya sa ya ƙyale su.Saboda shima zai ci riba muddin suka yi tarayya da Tanim Kamar yadda ya faɗa shi kan shi idan suka dawo ya ɗan ɗana kowace zai ci riba matuƙa ga su Dan duhu. Haka ya saki bakin Jamcy dake mai da numfashi ga kuma kwanyar ta da ke jin wani iri saboda daɗin Saliva na sa da ya ɗure mata har tana jin kamar tace ya ƙara mata wasu,har ta matsa da niyyar kamo bakin sa ya sakar mata wata irin tsawa kamar arado haka suka ji saukar ta.Sannan ya fara tsigar su zagi ta uwa ta uba. (Wal iya zubillah😭😭Allah ka yi muna tsari daga bin bokaye,Allah ka ƙara muna ƙarfin imanin ka hana zukatan mu kai mu inda zamu halaka duniyar mu da lahirar mu,Masu bin bokaye kuma Allah ya shirye ku,ya ganar da ku)😭😭🤲🤲🤲SHIRKA BALA'I CE.Allah ka nisan tamu da aikata.🤲 Kuɗaɗen da ya zara da kan sa a jakunkunan su ba tare da sanin su ba duk da sunyi mamakin bai tambaye su kuɗi ba. Ya janyo kusan bandir biyar na yan dubu ɗari har da wasu chanji sama. Sannan ya bisu da kallo har suka fice suma suna ɗura masa zagin. Ɓatt ya ɓace bayan ya daina ganin su yana gaggaɓar dariyar sa da sautin ta ke zagaye dajin. Sai da suka yi ta fiya mai nisa sannan suka dakata suna sauke numfashi kowaccen su kamar tayi gudun da yayi kilometer ɗari. Dai dai wata yar bushiyar mangwaro suka dakata Jaruma ce ta kalli Jamcy Sannan ta furta " Kin so ki ja za muna bala'i kina ganin wannan hatsabibancin sa da ban yake ban taɓa haɗuwa da boka mara mutunci kamar sa ba ". Tana cikin zancen bata ko ƙara sa ba suka ji an kece da wata mahaukaciyar dariyar da ta sanya su runtuma a guje kamar wasu mahaukata mayafi a hannu kowace kamar doya saboda kowaccen su da ƙibar ta kuma mai muni,dai dai wata kwanar Da zata kai su ga titi Jamcy ta sha mugun kaye sai da ta wuntsila tayi ta gangara kamar kayan wanki,yadda take wuntsilawa idan ba Allah ya tsare ba ta samu matsala abayan ta domin kamar ƙwallo na gudu a ƙasa haka take juyi tayi buɗi buɗi kamar kura. Dariya kuwa Jaruma tayi ta kamar zata haukace ga tsoron da ya kamata idan ba aljanun bane su ɗan duhu suka biyo su ganin yadda kawar ta ke ta mulmula kamar dawo.(fura) Dai dai wata itaciya Allah ya taimake ta ta tokare nan tana sauke numfashi tana gode ma Allah da ya sa jirgin na ta ya tsaya nan. Cikin sauri Jaruma ta matse dariyar ta ta isa kusa da ita tana mata sannu.Sannan ta taimaka mata suka fara takawa ga dariya ga tsoro haka suka fice daga dajin. Isowar su a wata hanyar ne da take kusa da titi dan kana hango titi ya sa suka dakata suna samun waje suka zauna.Jamcy duk ta galabaita sai wash take yi bayan ta da alama ta bugu kamm. Ƙishirwa take ji matuƙa dan haka ta cewa Jaruma ruwa take so.Da ƙyar jaruma ta samu ruwan ta bata sai dai warin su take ji matuƙa. Jamcy dai rarrashin da Jaruma ke yi ma hakan ya sa ta matse ta sha ruwan bayan ta daɗe Hancin ta dan dagaske warin su take ji.Tana sha kuwa ta dawo da su saboda rashin daɗin su da taji.Cikin mamaki Jarumai ta kai ruwan bakin ta bayan ta sunsuna domin lafiyayyen ruwa ne da ta ɗebo a wani rafi dake gefen titi kusa da su kuma taga ruwan tsaftatacce ne mai kyau.Duk da mamakin da taji hakan bai hana ta shan ruwan ba tana jefar da ɗan ƙoran da ta samu wajen,tana mamakin yadda Jamcy zata ce ruwan ba daɗi,bayan gasu ta ji su da mugun garɗi kamar yadda ruwan rafi suke. Sun yi zaman jiran mota yafi na minti goma kafin suka sami mota. Tunda suka shiga motar suka ga mutanen ciki kowa ya rufe Hancin sa da fuskar sa,sai jikin su yayi sanyi sai dai tuna zancen boka suka basar,sannan sun san haka mutanen nan suke yin wannan rawanin suna rufewa fuska kasancewar su mafi yawa buzaye sai basu damu ba saboda kuma sun san al'adar su ce,suna da tabbacin ma sun daina warin, duk da ko motar da suka biyo daga Nigeria zuwa Niger wahalce suka biyo domin kan ta suka shigo irin motocin nan na ɗan gote masu ɗaukar kayan masa rufi domin duk motar da zasu tara driver na tsayawa yaji warin nan zai ce yana da passengers haka Suka yi ta guduwa daga ƙarshe bayan kanta suka shiga suka yi tsaitsaye. Ko zuwan su Chadi a yau ɗin motar shanu suka samu suka biyo Sai yanzu ne Allah ya haɗa su da motar ƙwarai gata mota mai kyau har nishi take yi. Sai dai ko nisa ba,a yi ba da tafiya Wani irin bacci ya kwashe su. Basu farka ba sai wajajen Asuba.Sanyin Asuba ne ya farkar da su.Haka suka tashi suna bin wajen da kallo domin kuwa mutane ne ga su nan kowa kwance a ƙasa da ƙatuwar bindiga wanda kamar jira kaɗai suke yi a ce tak basu harba bindigar su ba.Cikin matuƙar tashin hankali suke bin ƙasurgumin dajin da kallo mai ɗauke da bukkoki na darnin kara sai manyan bishiyoyi Sai namun Daji da ke ta zagayen wajen basu damu da mutane wajen ba kamar ma suna gadin su ne. Hankalin su ya ƙara shiga jikin su bayan jin iska tayi yawa a jikin su kamar babu sutura a jikin na su.Hakan ya sa cikin tsoro suka kalli juna suna mayar da idanun su ga jikin su dake sake kamar haihuwar uwar su.Jikin su ne ya ɗauki rawa tuno sharaɗin boka sai kuma ga wata ta faru,yanzu shi kenan duk burin su ya tafi a banza.Idan ko har abinda suke zargi ne ya faru dasu.Akwai babbar matsala. Cikin tashin hankali suka fara ƙoƙarin tada hargowa dan sanin makama. Wani ne ya taso da alama idanun sa biyu,ko dama su yake jira ya furta " Hajiya,Me kuka yi wa Ogan mu da mai bi ma oga Yanzu haka suna chan rai hannun Allah,Saboda Abinda suka yi da ku ". Cikin waro ido da tashin hankali suka furta mun shiga uku dagake dai ta faru.Jaruma ce ta fara fashewa da kuka domin har yanzu bayan ta bai da zafi ba ga wata ta auku ba su ko bar garin ba. Wannan wace irin musiba ce.Ta faɗa a cikin zuciyar ta. Jarumai.itama hankali a tashe ta furta " Ku su waye ". " Mu yan daba ne da suka yi hijira a wahalce daga Nigeria,A wani hari da aka kai a shekaru ishirin da uku zuwa da huɗu da suka wuce inji sojoji a mulkin wani soja na Arewa,Jabir Muhammad Soja,(Dady soja)Tare Da Wata Captain Zainab Adeleke(A MAFARKI NA SANTA). wadda ta Auri Ɗai daga cikin masu riƙe da dabobin mu masu ɗaukar nauyin komai,Mun zo nan a matsayin baƙi ne nan,babu wanda ya san cewa mu biyar mun kuɓuta kowa tunanin sa an gama damu tun da tabbas mun shiga Niger lafiya,Dan mune na farko mu biyar ni da sauran wasun mu,Na bayan ne aka kame aka kakkkashe kusan su ɗari uku,har da wayen da suka shigo nan ɗin ma an gama dasu. ".Ɗan shiru yayi kafin ya cigaba da magana. " Ni tuni na haƙura da wannan sabgar shi ya sa tun da muka haɗu da su nan suka ƙara sanar damu yadda suke komai na su anan sai ban matsa ba ko fita zasu yi sai dai nace abarni tsaro sauran huɗun kuma sai suje tare da shugaban su anan saboda su suka ɗauki shugaban ci Dan ƙasar su ce a haka muke zaune tare da su har ila yau duk da wasun mu sun mutu sai mu biyu muka rage a tare da na nan Niger,Amma me ya kawo ku nan,kuma kar ku ji tsoron na. ''.? Shiru duk suka yi masa kafin ya ƙara furta " Ina son mu gudu daga nan na daɗe da son barin nan sai dai na san ba mai yuyuuwa bane,Kashe Ni zai yi ogan mu kamar yadda ya kashe yan uwan mu guda uku,Ina son ku tsira Nima ku tseratar dani bana son na mutu a acikin wannan daji ina son na ga na da yan uwa na da mahaifiya ta,idan tana raye " Ɗan nunfasawa yayi ya cigaba da faɗin. " Ga suturar ku domin dama Ni aka baiwa tsaron ku sauran sunyi man kass wasu kuwa suna tare da su oga,zan kwance ku muyi ta kan mu kafin gobe a kashe ku nasan muddin su oga suka mutu,mutuwa ce zata wanzu a gare ku, Dan haka ku tashi muyi ta kan mu bana tunanin su oga su rayu ". Yana kai ƙarshen zancen sa ya kwance su sannan suka mayar da suturar su,ba tare da tsoron wannan mutumen ba duk da tsorace suke amma zancen kashe su ya shiga jikin su,kuma ya tabbatar da Babu abinda zai musu.Haka suka fara ɗibar hanya duk da agajiye suke kasancewar ya san takan dajin take suka fice daga dajin. Suna fita kuwa kan titi suka samu motar Akori kura mai ɗaukar dabbobi zasu kai su Nigeria. Wajen biyan kuɗi sai da akayi rigima domin babu kuɗi ko sisi a jakar su sai yan hassin hamsin boka ya kwashe duka maduƙan kuɗaɗen da suka zo da su wanda basu hankalta ba sai yanzu,sai mamakin su ya shan ye na rashin tambayar su kuɗi.Dan basu san haka yake amsar na shi ba.Taimakon su wannan mutumen yana da kuɗi a hannun sa dan ya ɗebo su da yawa jaka guda yayo.Shi ya biya kuɗin suka faɗa cikin shanu suka yi tsaitsaye kamar suma a halin Adam ne. " Amma Hajiya wane irin wari ne kuke yi haka,haƙuri nake ta yi,amma ko Ni da bana wanka kullum bana yin sa,amma ku daganin ku Masu Naira ne amma duk inda kuka kasance sai wari kamar na mushen Alade,mun taɓa kashe alade haka yake wari idan ya tsima ". Shiru da dukkanin su suka yi kowa da abinda take saƙawa zuciyar su cunkushe... *** Yadda take juya kan ta zaka san agalabaice take gashi babu mai shiga gurin ta,sai ƙishirwa take faɗa tana ji,kuma ko an bata ruwa bata ko iya haɗiye su saboda warin su.Duk yadda Likitota suke son su taimake ta sun kasa.Haka suka.kulle ta cikin ɗakin suna jin ta tana neman agaji sun kasa.Anyi baɗa turare amma kamar ana ƙara ma ɗakin wari.Ga ƙafarta ta rure cikin abinda bai wuce sati ba,duk wani taimako Likitota sun bata kafin komai ya rinjaye su domin warin ya ya zamo na fitar hankali take ya ke kumbura ciki ya zamo illa idan aka shaqe sa shi ya sa ko wurin doctors da Nurses basa son matsawa ward servant ne masu ɗan kai mata ruwa ko abinci alamar yadda aka bada kuɗin kula.da ita. Ta fita hayyacin ta babu abinda take da burin so kamar Saliva na boka su kaɗai take jin zasu magance mata ƙishirwar da take damun ta..Hannun ta ɗaya da yayi saura gundululu take ta kallo hawaye na zubar mata.Babu mugun ciwon da ya yi mata saura a zuciya yanzu face yadda Alhaji Abdulkarim ya ka sa zuwa ganin ta sammam har yanzu bata ga idon sa ba,duk an faɗa mata an sanar shi ya zo da su asibitin shi ya bada komai na kula da ita.Mugun zafin rashin Dawowar sa take yi ga kewa da jimamin rashin Jaruma wanda shima sai da tayi ƙaramar hauka bayan jin labarin Jaruma ta daɗe da kwanta dama. Domin ita take ta mutu bata ko shura ba.Na manta kan sa sai da aka karkare sa a cikin kwalta.Hawaye ta share masu zafi cikin tsoron da ya shige ta na irin mutuwar da ƙawar ta ta yi.Kuka.ne ya kubce mata inda ta ɗaga ƙafar ta ɗaya mai ɗauke da ɗauri kuma ta rure sai wari take yi wanda muddin ba,a yanke ta ba sai ta cinye naman cinyar gaba ɗaya,kallon ta tayi da kyau wasu sababbin hawaye na silalo mata,na damar da ta fara shigar ta da baƙin cikin rashin nasarar da suka samu. Abinda bata sani ba a ranar da suka yi mugun accident bayan shigowar su garin Kano,Alhaji Abdulkarim da ya dawo daga tafiya Jigawa yaga an yi dafun fun da jama'a ga mota babba da shanu a gefe ta kama da wuta wasu sun fita wasu basu fita ba. Hakan ya sa ya faka motar sa gefe yana alaawadai da dabi'un mutane na rashin taimakon gaggawa a yanzu sai an gama ɗaukar Hoto da video kowa dai ya tara followers a social media. Hakan ya sa ya kutsa kai yana faɗa da abinda ake kafin aka tabbatar masa da ankira ambulance suna hanya. A farko bai gane Jamcy ba, ba,a ma maganar Jaruma domin ta daɗe da tafiya duk yadda kake son gane ta baza ka iya ba kan ta ma da ya fita ba,a san inda ya faɗa ba. Da taimakon mutane aka samu aka ja motar gefe saboda ta tare hanya.Sannan ne aka gano kan Jaruma nan ne Alhaji Abdulkarim ya ga ne ta cikin ruɗu da tashin hankali ya kira sunan ta. Yana furta ai wannan ƙawar matar sa ce. Jama'a da suka ji haka sai suka fara nuna masa ɗayar matar Dan ya bincika ko itace. Ƙirjin shin ne yayi mugun bugu ƙasa yake batun kaiwa sai dai da taimakon jama'a da suka riƙe sa ya tsayu yana mai nanata innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un.Cikin tashin hankali yake neman ba,asin wayen da suka ga komai sai dai ya kasa cewa komai mamaki danƙare da zuciyar sa.Kamar shi Alhaji Abdulkarim mai kuɗin da bai san iyakar ta ba wai matar shi ce ta shiga irin wannan buɗaɗaɗar motar da ake lodo dabbobi,Gashi babbar masifar da Jamcy take ciki bai san da tafiyar ba shima yayi tafiya wani aiki anan Jigawa,kuma ba gurin ta yake ba shi ya sa bai lura ba da ba gida ta kwana ba saboda ta saba rufe part ɗin ta haka kawai idan baya shashen ta har sai ta ga damar budewa,shi ya sa bai matsa ba da yaji shiru. Cikin jimami da tashin hankali yasa aka karkare naman Jaruma aka zuba akwali aka bashi sannan aka saka Jamcy a ambulance da bata san wanda ke kan ta ba hannunta ɗaya ya cire ɗaya yana reto itama ƙafa ta yi sumtun kuma harda kariya ciki ga bayan shima ya bugu. Haka aka wuce da ita asibiti ita kuwa Jaruma nan gurin aka ɗan yayyafa mata ruwa yan ƙwarorin jama'ar dake gurin suka sallace ta aka rufe ta aka watse. Ko kafin a gama yiwa Jaruma sallah da rufe ta motar ta kama da wuta gaba ɗaya ta cinye wannan mutumen da ke ciki yana neman taimako kasancewar babu mai jin sa dan anyi ta nema ko za,a ga wani a ciki ba,a gani ba har driver ma ba,a gani ba. Har wuta ta cinye gaba ɗaya,duk kururuwar da yake yi babu wanda ya jisa Dan duk sun bar bakin motar. Bayan gama kawar da Jaruma ne aka tsinci driver a wani ice rigar sa ta Manne da icen yana ta lilo abun mamaki abun al'ajabi kuma cikin ikon ALLAH yana numfashi haka aka saka ma Alhaji Abdulkarim shi a mota ya wuce da shi. *Abinda ya faru a da su Jamcy Shine lafiya lau suke tafiyar su duk da wannan mutumen nayi yana zubar da miyau saboda warin da ya dame sa. Har suka shigo Nigeria kowa da abinda yake saƙawa tsakanin su babu ma kamar Jamcy da Jaruma. Sai dai suna cikin murnan sun kusa san Barka sun hango gida su da wannan mutumen,cike da tabbacin burikkan su zasu cika, sai ga wata ƙatuwar mota ta da tafi tasu girma kai ma ta su mugun bugu a cewar mai motar bai ga tahowar ta su ba.Haka motar ta kife bayan ta wujijja sannan ta watsar da na watsar wa wanda su Jaruma na ciki da Jamcy da driver da aka cilla gefe saboda yana da sauran shan ruwa duniya.Haka mutane suka taru kan su.shanun

Chapter 35 of 39