Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nufa sai da ta fara leƙa bedroom ɗin REENA da ita ma ta yi shirin baccin cikin yar guntuwar riga da wando kamar na LINA dan itama tayi shirin baccin har hular ta ta sanya. Murmushi tayi ta shafa kanta tare da ƙara shafa mata Addua,a sannan ta fice. Bedroom ɗin ta ta wuce itama direct toliet ta wuce,wanka ta,ɗauro tana fitowa dai dai lokacin da wayar ta take rurin neman taimako.Da sauri ta ɗaga tana Murmushi cike da farin ciki. Sallama tayi cike da kulawa da natsuwa. A chan ɓangaren ne a aka furta " Ina yan biyu ko sunyi bacci,ya suke ? ". " Haba Abban su Ni ba zaka yi ta tawa ba sai ta ya yan ka,Ni nayi ma fushi ". Murmushi aka yi daga chan ɓangaren kafin ya furta " A gafarce ni Uwar Soja ai kina raina,ban samu 'okaci bane ko yan uwan ki duk yanzu nake son kiran su,ya kike Amaryar ta ya gdn "? Shiru tayi jin furucin sa kamar bazata amsa ba.Sannan ta sauke Numfashi tana haɗiye wani abu mai nauyi tana furta " Duka muna lafiya,ya aikin ". Haka suke cigaba da firar cike da kulawa sai da suka yi kusan mintuna talatin sannan suka yi sallama rabin firar kuma duk ta su LINA ce da yadda yayi kewar su " .Sallama suka yi cike da kulawa sannan ya yi hanging kiran. Yana mai da kiran kan Momy. Numfashi ta sauke wani abu na sauka mai nauyi acikin zuciyar ta,wanda ya ke maƙare da maƙoshin ta tun lokacin da firar ta su tayi tsawo. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta miƙe ta saka kayan barcin ta yi shirin ta tsafff,Addu,ar kwanciya bacci tayi bayan ta sanar da BILAL idan ya dawo ya rufe part ɗin ta shige. Wuraren sha ɗaya na dare ta farka tana lalaba gefen ta sai dai wayam babu komai a wajen buɗe idanun ta tayi da sauri tana bin ɗakin da kallo tana duban inda zata ganta.Miƙewa tayi ta buɗe toilet sai dai babu ta ciki.Fahimtar ba nan ta kwana ba hakan ya sa ta ta saka bedroom silifas na ta ta fito dan ta san inda zata same ta.Dan baya iya kwana ita kaɗai sun saba da kwana a tare da juna komai faɗan da aka yi,idan sama suke son yin Bacci sai sai su kwana na ɗaya jibi na ɗayar su. A falon ta tarar da dashi yana wani aiki a system ɗin sa akan business idanun ta ta murza ganin dai shi ɗin ne hakan ya sa bata ce komai ba ta raɓa shi ta wuce idanunsa ya sauke da sauri bayan abinda idanun sa suka ƙyallo masa,ya cigaba da aikin sa yana girgiza kan sa dan shi har ya nzu mamakin yar uwar ta sa yake yi yadda faɗa baya damun ta. Bedroom ɗin REENA ta faɗa tana kunna haske ganin ta tayi tana sharar bacci ta hankali kwance.Hararar ta tayi kafin ta kashe hasken ta kwanta kan gadon bayan REENA.Ta na kwantawa kuwa bacci mai nauyi ya kwashe ta. A ɓangaren BILAL kuwa bai tashi daga aikin ba sai kusan ƙarfe ɗaya na dare sannan ya miƙe ya cire system ɗin sa daga Chaji sannan ya wuce sashen sa dake cikin part ɗin. 🍃🍃🍃 Aɓangaren SHATOU kuwa tun da aka yi Sallar Isha take ta mutsuniyar yadda zata samu ta fice saboda dukkanin su suna zaune a tsakar gida suna shan Iska.Inna Ni na lura da ita dan haka ta ka sa ta tsare cike da kulawa.Har wani jan jiki take ƙara yi saboda kawai ta ƙi fitar dan ta fahimci yan kame kamen da take yi da salo. "Inna ni yau zan je makarantar dare Su Amina sun ce zasu biyo mini kuma basu zo ba ". Murmushi irin na yarinya yarinya Inna ni tayi mata dan ta fahimci nufin ta.Sannan ta furta " Sai ki haƙura kawai " " Na haƙura fa Inna ni Kinga mun kwana biyu bamu je ba ya kamata mu koma " " To yanzu ya za,a yi kenan ". Cewar Inna ni. " Ki bari mu tafi tare da Bibu kawai Inna ni ko Baffa na " Tayi zancen tana kallon Baffa na da Bibu. Murmushi Baffa na yayi dan ya fahimci shirin ta sannan ya furta " Ya kama ta kam SHATOU na ".Ya san Indai da Bibu za,a je to rigimar daƙyar ayi ta. Numfashi kawai Inna ni tayi kafin ta furta " Kuje kuma idan an taso kar ayi biye biye nan dare ne yanzu ba rana ba banda rigima ". Tsalle SHATOU tayi tana murna tana cewa " to Inna ni ". Bibu da bai so fita ba baccin sa ya so yayi ya miƙe yana saka takalmin sa. Babu littafin karatu babu komai haka ta fice kuma Inna ni ta gani sai dai kawai ta girgiza kan ta tana fata da Addua,a Allah ya dawo mata da su lafiya babu wata rigima.Dan ta san asalin inda za.,aje ba makarantar ba kawai. Makarantar daren suka fara zuwa basu ko yi mintuna goma ba ta nemi izinin zuwa gida wai kan ta ke ciwo haka aka saka Bibu ya raka ta. Tun a makarantar yake kallon ta yana son ya ce wani abu sai da ya bari sun fita sannan ya ce " Adda SHATOU ƙarya fa kika yi,kwanan nan sai zuba ƙarya kike yi ". " Eh nayi ai ƙarya akwai inda ta halasta " " Yawwa Bibu fili zamuje in zaka je idan kuma ba zaka je ba ka ce Baka da lafiya sai kayi gida kace shine ya sa ka dawo,ni kuma sai na zo daga baya " " Kuma dan Allah Karka faɗawa Inna ni na tafi Filin wasa ". Baki Bibu ya turo gaba kafin ya ce " Ai tare muka zo tare zamu koma Ni bazan koma nikaɗai ba mu tafi na yi kallo ko na shiga nima kuyi dani ". Dariya tayi tana laƙƙamo hannun ta wuyan sa shima ya laƙƙaama na sa sannan tace " Yawwa Bibu na kusa zama SHATOUn birni haka nake jin kamar zan tafi,kuma Allah Dagske haka nake ji ". Dariya yayi kafin ya ce " Babu inda zaki je Adda SHATOU,to me zaki je yi chan ". " Oho Nima ban sani ba,Allah ya sa alkhairi ne na siyo maka Raken birni mai ƙara wa kan ta zaƙi da ragewa ". Dariya Bibu ya ke ce da ita yana furta " Kai Adda SHATOU ya sifn ban yadda akwai wannan raken ba ke har kin yarda da maganar Iro ,ance shi ya kawo zancen nan wai akwai wannan raken ". " Mtsww" taja tsaki jin an ambaci sunan maƙiyin ta kafin ta furta. " Eh lallai ƙarya ne Bibu amma zan maka tsara ba mai kyau kana so ko ". Kai ya jinjina mata cike da Murmushi haka suka cigaba firar su har suka isa chan firar wata shirme wata dai dai. Koda suka isa filin cike take yara na ta wasa sai yan manya irin su Iro gefe ɗaya suna shan rake suma taɓa firar su suna kallon abun da ke waka na. Cike da farin ciki sauran yaran suka tarbe ta suna kiran sunan ta. Wasar yar jari ri bisa gado suka cigaba da yi inda aka yiwa SHATOU ta4fna ta dariya sai dai rabin hankalin ta na na ga kan jama'ar dake wajen dan akwai hasken kara da aka kunna. Bibu ma cikin maza irin sa ya shige suka cigaba da wasa. Ita kuwa SHATOU a jirgi na tara ne da aka wulla ta baya a lilon da suka koma yi yanzu ta hango dai dai kalar yaguwar dake ga rigar da ta gani a barcin ta.Hakan ya sa cike da sauri ta ce su ajiye ta dan tabbatar da abun da ta gani.Wanda ke sanye da rigar ya juya baya yana Marmara gyaɗa.Cikin azama suka sauke ta ganin yadda take ta ɗaga musu murya dan har sun tsorata.A hankali take sanɗa dan fara ganin wanda yayi aikin da kyau.Aiko sai aka yi sa,a dai dai lokacin da ya juyo da fuskar sa...✍️ Wannan littafi na kuɗi ne akan1000 *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh 💞 *_Typing_* *💋KURMAN ƘADDARA💋* *©®Faiza Almustapha Murai* *FA'EEH BG*✍️ *BOOK ONE* *~Paid~* *Second to the last free pages*👌 P..1️⃣1️⃣ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting room link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn *LITAFFAN MARUBUCIYA* _*A MAFARKI NA SANTA*_ _*RAYUWAR MU A YAU!*_ _*SHAGALI💃💃💃💃nace!! Ina yan kasuwa manyan Hajiyoyi masu Capacity nace ga damar ku tazo domin kuwa muna tallata muku hajar ku,kowace iri ce a farashi mai sauƙi idan ki/ka na buƙata,sai ku tuntuɓe mu wannan lambar +234 808 750 4734 dan tallata hajarku.Sai kun zo.*_ 🪐🪐⚡🪐🪐⚡🪐🪐 A hankali take sanɗa dan fara ganin wanda yayi aikin da kyau.Aiko sai aka yi sa,a dai dai lokacin da ya juyo da fuskar sa yana kallon ta jin sauran Abokan su na maganar nufowar ta wajen su dan yace kowannen su ya fita iskan ta sai an manta sai su rama abun da ta musu.. Idanu ta ƙara buɗewa da kyau dan tabbatar da zargin ta shi ɗin dai ne dan tass haka fuskar shi ta bayyana gare ta.Cike da wani irin haushi da baƙin ciki take kallon sa sai dai ta kasa cewa komai sai ma Riƙe ƙugu da tayi ,tayi tsaye tana ƙarewa dukkanin su kallo.Bibu ne ya matso gurin da sauri gudun faruwar wani abun hakan ya sa ya riƙo hannun ta yana furta " Addah SHATOU lafiya ".?? Ƙin bashi amsa tayi sai bin hannun ta da ya fara jaaa da kallo tayi kafin ta yi murmushin da ita kaɗai ta barwa kanta sani.Su Amina ma duk zuba mata idanu suka yi haka ma sauran abokan na Iro sai Surutun su suke wasu suna hayayyaƙo mata na lafiya kallon da ta ke yiwa Iro,Wanda wasun su har sun fara kiran ta mayya mai cin naman mushe Indai Iro ne kurwar sa tafi ƙarfin ta. Bata tan ka ma kowa ba har ta daina ganin duhun jama'ar wajen dan kai tsaye Bibu hanyar gida ya nufa kuma bata hana sa ba dan ta riga ta sha alwashin ta ƙara tabbatar da shi ne sai ta masa wulaƙancin da bai zata ba. Sai da suka kusa isowa gida ne suka lura da su Amina a bayan su.Ashe tun ɗazu suna biye da su.Dakatawa tayi tana furta " Ku kuma lafiya kuka sako mu gaba ".? Amina ce cikin ɗan ƙarfin hali ta furta " Dama mun ga kamar ba lafiya ba ne SHATOU shi ya sa nace bari mu biyo bayan ku " "Idan na faɗa muku kuna iya ɗaukar mini mataki "? Tayi furucin tana kallon Amina. Kai Amina ta girgiza kafin ta furta " Indai wanda bai fi ƙarfi na ba zan iya SHATOU Ni kaɗai ma ". Murmushin na samu banza SHATOU tayi kafin ta furta " Yawwa Iro nake son Ki tsaya gaban sa ki zazzage sa saboda ya ci mutun cin ƙawar ki ". Idanu Amina ta zaro ba ita ba har Bibu da ke kallon Shatoun.Haka ma su Ramata. " Adda SHATOU kin san dai abun da ke tsakanin ku da shi,to ma ai bai Miki komai ba kuma naga yanzu bai ma kula ki ba ". Hararar Bibu tayi sannan tace " Shine fa yayi rubutun nan a makarantar mu,kuma wallahi ba zan yafe masa ba sai na rama dan ma kar wanda ya dakatar da ni Gara ma Karka faɗa a gida kayi shiru da bakin ka ". Ta kai ƙarshen zancen a hasale kafin ta ƙara furta " Mafarkin sa nayi jiya,da kayan da ke jikin sa,Dama neman mai kayan nake yi sai gashi a she shine dai dan da farko nayi zargin sa. Idanu da baki dukkanin su suka saki suna kallon ta kafin Amina cikin ƙarfin hali ta furta " SHATOU mafarki fa ba gaskiya bane,sheɗan na iya zuga ki Shine ya nuna Miki Iro,nidai Dan Allah kiyi haƙuri ki bar zancen nan ko kuma ki bari mu tabbatar da gaskiyar ta fili ". Kallon Amina tayi tana gyaɗa kan ta,ta san gaskiya take faɗa amma tabbas tana buƙatar Son yin maganin sa idan dai har shi ne.Dan haka zata yi binciken kamar yadda ta tsara tun farko da ta tabbatar da shi ɗin ne sai ta masa wulaƙanci. " Naji " kawai ta furta ta cigaba da tafiyar ta har ta shige gida babu wanda ya ce ƙala a cikin su sai dai suna mamakin yadda zaka ga abu a mafarki kuma kace zaka yarda da abun da ka gani.Gashi Malamin su ya sha faɗa musu bakowa ne mafar ki ne gaskiya ba wani mafarkin sharrin shaiɗan ne kawai. Sallama Bibu yayi musu ya wuce gida sannan suma suka juya suka yi gida kowace zuciyar ta cike da zullumi. Jawairiyya ce ta furta " Ni dai ko da an ƙara kirana shaidu zance ban da lafiya gaskiya dan na san sai an yi rigima babba akan wannan zancen dan ba barin sa zata yi ba ". " Nidai tsoro na kar su bata kashi,na san idan dukkanin su suka dake ta mutuwa zata yi " Amina tayi furucin tana jin hawaye ya cika mata ido. " Ke Amina ba dai daga magana ba har kin fara hawaye " Cewar Ramata dake kallon ta cikin hasken farin wata. Dariya ta kece da ita tana furta " shi ya sa duk SHATOU ta fi raina ki wallahi ". Tsokanar ta suka dinga yi har suka iso gida kasancewar gidajen su suna kusa da juna kowaccen su tayi shigewar ta. Koda suka shigo Inna ni ce kawai zaune a tsakar gida tana jiran su hankalin ta ba kwance ba ganin lokacin ta shin na su yayi amma ba su iso da wuri ba. Numfashi ta sauke mai nauyi bayan shigowar SHATOU gidan sannan Bibu. Bata ce musu komai ba sai umurnin kowa yayi Alwallah ya je ya kwanta tare da tunatar da su mahimmancin Addu,ar kwanciya bacci. Haka suka shigewar su ɗaki kowa ya kwanta bayan yin Addu'a. A ɓangaren Inna ni itama da baffa na sai da safe suka yiwa juna kafin suka yi Sallama. Guraren Ƙarfe Biyu ta buɗe idanun ta da suka gagara rufuwa da bacci,dan ta daɗe haka kwance.Miƙewa tayi zaune tana kunna fitilar ɗakin na ta.Idanun ta da suka yi nauyi ta ƙara buɗewa kafin hawaye suka silalo mata masu zafi.Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi kafin Kuka ya kubce mata mai tsuma zuciya kamar ko yaushe sai da tayi mai isar ta sannan ta share hawayen ta. Tana nan zaune yadda take bacci ya kwashe ta. " Yadda suke kuka suna ƙoƙarin rungume ta ne ya sa ta zuba musu ido tana kallon su ta kasa rarrashin su wata mata ce da baƙin mayafi fuska a rufe ta zo da sauri ta janye su jikin ta da ƙarfi wanda ita kan ta har da zabura tayi " Wanda ya sa ta miƙe firgigit daga zaunen da take tana buɗe idanun ta daga nannauyan baccin da ya ɗebe ta.Duk yadda take son tuno fuskokin da ta gani yanzu a mafarkin na ta a bin ya gagara dan haka ta miƙe ta fice alwallah ta ɗauro ta sallah tayi addu,oi sannan ta miƙe ta koma kan ɗan madaidaicin gadon na ta. Yau an tashi da abun farin ciki a cikin kauyen kasancewar zasuyi manyan baƙi domin ɗan gidan babban ministar ne na Abuja zai zo duba yadda tsarin makarantun su yake kafin a fara wani abun.Dan haka yau ta ko ina su SHATOU basu samu sauƙi ba tun da suka je makaranta sai aikace aikace suke yi.Tana son guduwa gida abu ya gagara dan yunwa take ji dan haka saboda Abar ta taje ta san malamin su ba zai hana ba idan ta tafi tare da su Ramata ta san zai yarda zata dawo.Da ƙyar da rarrashi ta roƙe sa ya bar su suka fice daga makarantar da zummar zasu dawo. Sai dai Shatou ba yunwar kaɗai ba ce ke damun ta ta gundura da aikin ne kawai a cewar ta dan wani banza zai zo sai a saka su aiki kamar tumakai dan duk da aikin nata na shan ruwan tsuntsaye ta cire jin Haushin aikin da aka tataro musu ba, dan har da su cirar yana da cire ƙananan hakukuwa,duk yadda prefect suke matsin lamba da malammai amma ita tana gefe tana ragwanci bakin ta ture kaɗan take jira ayi ta ruwan masifa tsakanin ta da prefect ɗin sai dai fahimtar halin da take ciki sai suka fita iskan ta bayan malamin su ya basu umurni kuma ko ba dan haka ba sun san halin ta. *** " REENA kin san jiya mafarkin me nayi,mafarkin fuskokin mu nida ke nayi,muna kuka muna miƙa hannayen mu ga wasu hannayen da ba,a ganin fuskokin su wai muna kuka suma suna kuka ". LINA ce ta yi Furucin bayan sun gama sallar asuba. Kai REENA ta ɗaga alamar tunani kafin ta furta " Me yasa baki bari kika ga ko su waye ba kafin ki farka ".ta kai ƙarshen zancen cike da yarinta kamar yadda LINA tayi zancen. " Mtsww ke fa Wawuya ce waya ce Miki ana iya saka wani abu a mafarki,kai ba sai dai ka gani ba ne ". LINA tayi Furucin tana cigaba da tofa Addu'a. " Mtsww Ni dai ba Wawuya ba ce wallahi,idan kin san Wawuya nake mai ya kawo ki bedroom ɗina ai da sai ki tsaya naki". REENA ta kai ƙarshen zancen tana ɓata fuska kamar zata yi kuka. " Uban me zai shigo da ni nan ni ma ban san wanda ya kawo ni nan ba,da ba zan kwanta a wannan banzan gadon ba " Ta kai wa bed ɗin bugu kamar irin zai ji. Kuka REENA ta fashe dashi kafin ta furta " Wallahi ki ka ƙara dakar mini bed Allah ya isa na muguwa ". Dariya LINA ta ƙyalƙyace da ita kafin ta miƙe ta na wani irin ja baya sannan ta kai wa bed ɗin mugun shuri da ƙafar ta,ta dama har da yin suluka kamar wata Chinese sannan ta haye bed ɗin. Kuka ne ya ƙara ƙwace wa REENA har da murje murjen ƙafafu an daki gadon ta. Tana furta " bai yafe ba wallahi,kuma sai na rama ma sa ". Miƙewa tayi tana cire hijab ɗin ta dogo har ƙasa kafin ta haye gadon ta faɗa kan LINA da ke ta tsalle tana dakar bed ɗin tana dariyar ƙeta jin REENA na ƙara giyar kukan ta. Tana hayewa kan gadon kuwa kamar dama LINA jiran ta take ta faɗa mata aiko ta hau dakar abar ta har sai dai ta kai tun REENA na ƙara ta kai Muryar ta bata fita kafin ka a an kara ta sume ga jini ta bakin ta yana gangara kaɗan. Ummah da take jin hayaniyar su ƙasa ƙasa ne ta leƙo tana tambayar lafiya. " Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un " " LINA me nake shirin gani,Allah ka rabani da mugun ji da mugun gani Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un LINA kashe kashe mini ita zaki yi ".? Ummah tayi furucin Ganin Yadda LINA take jibgar REENA dake kwance a Kasan ta bata motsi kuma duk da haka bata daina jibgar ta ba kamar Allah ya aiko ta. LINA da bata fahimci aika aikar da tayi ba ne saboda yadda idanun ta suka rufe ta juyo da sauri tana kallon Ummah kafin ta mai da idanun ta kan REENA dai dai zaro idanun ta da faɗuwar ƙirjin ta ganin yadda jini ke zuba bakin yar uwar ta hannu ta aza a kai ganin babu numfashi a jikin ta.Miƙewa tayi tana sauka daga kan ta kafin kuma wata irin juwa ta kwashe ta ta faɗi ƙasa yaraff babu numfashi. Ummah dake riƙe da REENA hankalin ta ƙara tashi yayi hakan ya sa ta miƙe cike da sauri tafi ce tana ƙwala kiran Sunan Soja. BILAL da bai daɗe da shigowa bane bai ko isa sashen sa ba ya ji kiran mahaifiyar ta sa cike da tashin hankali.Juyowa yayi da sauri yana dosar sama dai dai lokacin da itama ta iso ƙofar ɗakin REENA ta nuna masa da sauri ta ma kasa magana. Shigewa yayi da sauri cike da tambaya sai dai bata bashi amsa ba. Abun da ya ci karo da shi ne ya tayar masa da hankali ganin REENA kwance kamar gawa fuskar ta ta kumbura lokaci ɗaya ta chanza kamanni kamar wadda ta yi dambe a filin dambe. Kan ta yayi da sauri yana ɗan marin fuskar ta yana kiran sunan ta sai dai ganin bata motsa ba ya sa shi tunani wata mafita kallon bedroom ɗin ya fara kafin ya hango LINA itama yashe a ƙasa idanun sa ya waro wani sabon tashin hankalin na mamaye sa ga tambaya rass dafe da zuciyar sa babu amsa.Ummah ce ta shigo da ruwa mai sanyi a hannun ta.Hankali tashe ruwan ta yayyafa ma LINA har sau biyu sannan ta miƙe a razane sabo da tashin hankali ne ya kai ta ƙasa da tsoro. Miƙa ma BILAL ruwan ta yi ya yayyafa ma REENA baiwar Allah tana jin sanyin ruwa ajikin ta ta buɗe idanun ta a galabaice sun yi jawur da su na azaba. Hawayen ma sun ƙafe.Zama take son yi amma ta kasa, fahimtar hakan ne ya sa BILAL miƙa ta hannun Ummah bayan ya ɗago ta, toilet ya faɗa ya haɗa ruwan masu ɗan ɗumi da zasu taimaka mata sannan yadawo ya ɗauke ta ya shige toilet ɗin da ita. Bayan shi Umma ta bi cike da tausayin REENA babu wanda ya kula halin da LINA take ciki dan kuka take ta rizga harda shiɗewa. Ganin Ummah bayan sa ya sa shi ɗan kallon ta ƙasa ƙasa kafin ya baro toilet ɗin yana mamakin wasu halaye da Ummah take nuna wa duk da alƙawarin da ya ɗaukar mata a chan shekarun baya da suka wuce. Ummah kuwa kan REENA tayi bata ma kula da shi ba.Cike da tausaya wa ta ke ɗan gasa mata fuskar ta da ruwan ɗumi bata fito daga cikin bahon ba sai da tayi kusan mintuna goma sannan Ummah ta chanza mata wasu ruwa tare da yi mata wanka ta ɗaauro mata towel suka fito. Koda suka fito BILAL ya fita ɗauko first aid kit.yana shigowa kuwa kallo ɗaya yayiwa LINA da ta ta kure waje ɗaya alamar bata da gaskiya.Zama yayi bakin gadon yana Fiddo da maganin kashe zafi da su pain relive na oral,Tare Da maganin da zai taimaka mata tayi bacci dan ta bugu,BILAL duk da bai san abun da ke faruwa ba amma zuciyar sa ta riga ta gama amince masa aikin LINA ne musamman yadda ya ga ta takure gefe ɗaya sai satar kallon sa take yi tare da REENA da ke ta sauke nishin azaba. Shayin da Ummah ta haɗa mata yanzu ta sha kafin ya miƙa mata maganin ta sha kamar zata dawo dashi dan itama bata wani son magani.Duk da tafi LINA ita da wuya a bata magani bata zubar ba,ko ta ɓoye. Kwantawa tayi ya lulluɓe ta da blanket yana mata sannu.Kai kawai Take iya ɗagawa sai hawaye da suke sauka kaɗan a gefen idanun ta.Cike da tausayin ta ya fice daga bedroom ɗin. Fitar BILAL ta sa LINA jin sauƙi a zuciyar ta,dan wata irin masifa ta hango cikin kwayar idanun sa a kallon da yayi ƙara yanzu kafin fitar sa. Ummah kuwa yana fita ta fara mata faɗa cike da ɓacin rai ta inda take shiga bata nan take fita ba.Shigowar BILAL ce da wata iriyar bulala mai harshe biyu ya sa Ummah yin shiru tana kallon sa kafin ta furta me zaka yi BILAL.... ______________ 🍀🌻🍀🌻🍀 A ɓangaren SHATOU kuwa gidan su ka wuce suka ci suka ƙoshi kafin suka fito suna firar su da wasannin su a hanya harda yan guje guje,Suna tsaka da tafiya su huɗu manyan danƙararrun motocin da ke ƙoƙarin mamaye yar hanyar suka ratso kusa dasu dai dai wata babbar mota mai walƙiya kamar an ƙera ta da zinari wacce duk tafi sauran kyau kuma itace a tsakiya tayi wa su Amina da Ramata, jawairiyya wanka da ruwan kwatar dake zube a wajen saboda akwai kwata wajen dan ƙofar gidan suna niƙan injin na ruwa ko wane kala sai ya zama wajen ya tara ruwan kwata,gashi ba,a tsaftace sa. " Kutumar Uban nan,Amina kunji wanki ". Ta furta ganin yadda duk aka wanke musu jiki ita kaɗai ce ruwan bai sama ba.Amma taji kamar itace dan cike da masifa da ɓacin rai tayi zancen ganin ko ta kan su ba,a bi ba kamar ba mutane aka yiwa haka ba. " Yau ko uban waye sai ya yi bayanin abun da ya aikata sai ya baku haƙuri ko shine ɗan gidan

Chapter 9 of 39