Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
su dan ta basu labarin abinda ya faru,dan suma sun jinjina lamarin na su Reena. Cike da tashin hankali Ummah ta kalli agogo dake nuna ƙarfe goma na dare gashi dama suma sun yi kiran na sa layuka shiru har su Sir sun gwada dukkanin su dai hankali tashe dan yayi abin da bai saba ba.Ya tafiyar sa babu Sallama. Gashi bayan haka sai da su Reena suka ƙara kwata wani damben gurin bada haƙuri da Ummah ta saka suyi wa juna,su yafewa juna.LINA uwar rashin haƙuri daga kawai REENA ta share ta shikenan ta fara ƙoƙarin kaima ta duka,A fusace,duk da tana cike da tausayin ta,kuma tana son bata haƙurin Allah ya sa Ummahn tana kusa,sai faɗan ya tsaya nan, sai dai har yanzu babu mai yiwa wani magana a cikin su sai gidan ya koma babu daɗi daga ita sai su Rabi ne suke ɗan sakewa suma ba wai suna jin daɗin bane saboda dama su LINA ke ƙawata gidan yau gashi kowaccen su kamar an mata mutuwa. Ga tashin hankalin yadda ya yan na su yake ciki dan haka estate ɗin ta koma ko ina shiru dan tun rana suke kiran layin sa daga ƙarshe suka bar shi haka tun da sun binciki yaran sa since lafiya lau yake. Yana bacci koda suke kiran bayan isar su,sunyi hakan ne suma ba tare da suna da tabbacin bacccin yake yi ba. " Yanzu ya za,ayi a fito dashi ina tsoron kar ace wani abun ne ya same sa,bari na kira Abban su kawai AB ". Ummah ce ke zancen cike da wani irin raunin ta da ya bayyana. AB yana niyyar ƙara furta wata magana sai ya ga an buɗe ƙofar bedroom ɗin dan haka ya ce ma Ummah " Ya fito he's fine " kafin ya katse kiran yana sara masa (Solidarity)cikin girmamawa. Numfashi Ummah ta sauke mai nauyi kafin ta ja ajiyar zuciya tana tunanin yadda zata kira Abban su ta tada masa da hankali duk da ta san shima ɗin zai iya kira kowane irin lokaci ƙila ma ya kira bai same sa ba. Daga chan ɓangaren kuwa kallon AB yayi kafin ya ɗauke kan sa dan ko bai tambaye sa ba ya san da wa yake waya ganin yadda ya natsu dan suna mugun girmama Ummah suna jin ta kamar mahaifiyar su saboda mutuncin ta ga kowannen su sun ɗauke ta kamar uwa. Direct kan dininng ya nufa tea ya haɗa kawai mai kauri ya sha sannan ya miƙe ya dawo falon yana sauke numfashi.Tashar labarai ya kunna ko hakan zai rage masa Damuwar da yake ciki.Mayar da hankalin sa yayi ga labaran da ake haskawa a tashar sai dai ba wani fahimta yake ba,dan hankalin sa na ga su REENA yana son ya ji ya ƙannen na sa suke amma ya san yanzu sun isa yin Bacci saboda da wuri suke kwanciya bacci saboda school. Ganin babu abinda zai fahimta a cikin tvn hakan ya sa ya miƙe ya koma bedroom ɗin sa.A chan ma ya daɗe zaune kan cusion kafin ya miƙe ya doshi bed ɗin sa, zuciyar sa daƙushe.Dan tunda suka iso ɗin ya shige ya rufe kan sa saboda damuwa,chan yayi sallolin sa,ko abinci bai ci ba sai shayin da yasha yanzu ko shi saboda yaji yunwa na neman illata sa ne.Duk ya tuna da yadda ya daki Lina sai zuciyar sa ta yi zafi saboda ya san bata kai ta samu irin wannan ba duk da chan baya yayi bugun ta amma chan bata yi hankali ba yanzu kuwa ta san zafin jikin ta.Dukkanin su rarrashi suke so saboda yarinta ce dukkanin su ke damun su amma ba yadda zai yi dashi har mahaifiyar su haka, Allah ne ya basu nasu yan biyu ɗin haka.Numfashi ya sauke mai karfi yana kawar da duk wani tunani tare da yin addu'ar bacci take kuwa bacci ya ɗauke sa mai nauyi. *** Tun da ya shigewar sa bedroom ɗin na sa ya faɗa toilet saboda haka kawai yake jin jikin sa babu daɗi yar tafiyar nan da suka yi ko ina tsami yake masa saboda yanayin tafiyar hanyar duk da manya motoci ne ba gane yanayin hanya suke yi ba amma shi duk ya gaji haka yake ji dan haka ya cika ƙaton bathtub ya faɗa ciki da ruwa masu ɗumi da ƙamshi yayi haka ya kai sau uku kafin ya fito bayan ya ɗauro wanka tare da yin alwallah. Tsaye yayi gaban mirror madaidaicin jikin sa mai cike da ƙira wadda take mummurɗe ya ke ƙarewa kallo kafin ya fara murza mayukkan sa masu ƙamshi yana bin ko ina na jikin sa da su a hankali. Turarukkan sa ya shafa masu ƙarfi da kyau.sannan ya tada Sallah bayan ya saka Jallabiya mai kyau da tsari. Cikin natsuwa ya gabatar da Sallah azahar da ta fara gota lokacin ta saboda ya daɗe toilet bai lura da lokacin ba. Yana gamawa duk da yunwar da yake jin akwai ta acikin sa dan ko breakfast bai yi ba haka ya haye lafiyyayen gadon sa bayan cire Jallabiyar da yayi ya koma da ga shi sai short, duvet ya yi cover dashi mai taushi fari ƙar dashi kafin ya ƙara gudun ac daga kwancen sannan ya rufe idanun sa take bacci mai nauyi ya kwashe sa. Mubarak da ya san tabbacin sai yayi baccin nan na Hutu dan haka shima ya wuce na sa gefen ya huta kamar yadda ya huta ɗin dan shi ma ya ɗan gaji dan su suka yi yawon ma,sai dai duk ya tuna da Shatou da mai gidan na su sai yayi guntun murmushi ya girgiza kan sa ya rasa dalilin da ya sa yarinyar ta kasa fice masa arai amma ya san tabbacin MAHAJ ya manta da wata halitta ita Shatou dan sun ji sunan ta bakin Iro.Ya rasa har yanzu dalilin da ya sa ya kula yarinyar shi da ko su Sajida da Salma da ba su ishe shi kallo ba duk da kuwa gida ɗaya suke zaune dasu kuma yan uwan sa ne.Amma ita har ya kula ta gata wata figaggiya da ita dan ya san a ƙalla ba zata wuce shekara goma ba ma a duniya dan bai tunanin ta ma hau da sha ɗaya saboda yadda take yar cukul da ita ga rashin tsawo ga rashin jiki. "Amma Ya MAHAJ ya dawo fa tun ɗazu " Wata yarinya ta furta mai matsakaicin jiki sai dai ita ma a kallo ɗaya zaka san tana da yarinta dan zata kai shekara sha uku. Kallon ta matar da aka kira Amma tayi kafin ta furta " shine bai shigo ba kuma har yanzu Samra " " Amma akwai gajiya kin sani ko Amma ai na san zai shigo dan bana jin ko gefen Ayya ya shiga,Nima ga Yaya Muby na gani yanzu yace ai sun dawo ". Kai matar ta gyaɗa kafin ta ce " Sun kwaso gajiya kamm gashi ko breakfast ɗin sa bai yi ba gashi har lunch ya gota,ban san ƙiyayyar sa da abinci ba,haka yayi tafiyar nan ". Ta kai ƙarshen zancen tana cigaba da ɗan duba saƙonni dake shigowa a wayar ta. Yarinyar da aka kira da Samra kuwa ɓata fuska tayi tace " Amma dagaske bai yi breakfast ba,kuma shine har yanzu bai fito yayi lunch ba ". Murmushi Amma tayi kafin ta ce " To Sarkin kuka kar ki fara yi mini kuka gurin nan idan kuma Ayya ta isko ki babu ruwa na ke da ita ne,wanda kike Tausayin ko ajikin sa hasalima ɗabi'ar sa ce hakan,gwara kiyi shiru yadda muka saka masa ido ki saka masa,idan ya ga dama zaki gan sa ya fito yanzu ". Takai ƙarshen zancen tana share ma Samra hawaye dan har sun fito kuwa dan tana mugun son ɗan uwan ta da Tausayin sa shi ya sa a duk lokacin da yazo nan take cikin farin ciki duk da basu wata magana dashi amma wulgawar sa na saka ta farin ciki.Ko fitar nan ba ta so ba saboda ta san zai sha wahala, Allah ya ɗaura mata ƙaunar ɗan uwan ta,Ammah har cewa take yi ta fi son sa fiye da ita sai tayi dariya dan ita ta san tana son kowa a cikin yan uwan ta bare ma mahaifiyar ta. Miƙewa Samra tayi da sauri. " Ina zaki je Samra kuma ba dai gurin shi zaki je ba " Cewar Ummah ganin ta miƙe tsaye kamar an tsikare ta. " Gurin Ayya zani ko zata iya Fiddo da Ya MAHAJ ya yi lunch kar yunwa ya kama sa " Shiru Amma tayi kamar zata hana ta sai dai ta san ko ta hana ta tunda tayi niyya sai ta kai jiki dan haka ta ce " Samra ki bari zai fito kinji ba sai kin je wajen Ayya ba ". Ai ko Samra bata ma jira ta kai ƙarshen zancen ba ta falfala da gudu tana dariya. Da sallama ta shiga wani ƙaton falo wanda ƙofar shi take a cikin ƙaton falon na Amma dan ƙofofi ne gasu nan birjik wasu sama wasu ƙasa ta Ayya tana ƙasa saboda tsufa. " Ke lafiya kika faɗo mini falo babu Sallama,ita Maryam bata ga fitowar ki haka bane,kamar zaki je gasar Guje Guje " Yar dattijuwar tsohuwar da Hutu da kwanciyar hankali ya ratsa ta tayi furucun,sai dai daga nin ita fitinannun tsofaffin nan ne masu rigima.Dariya Samra tayi kafin ta haye kan rugs na ƙaton falon na Ayya sannan cike da tausayi ya yan na ta ta ce " Ayya Yya MAHAJ yau gaba ɗaya bai saka abinci a cikin sa ba fa,gashi sun yi tafiya sun dawo kuma bai nemi abinci ba,dan Allah ki je ki tado dashi ko bacci yake yi ".Ta kai zancen tana ɓata fuskar ta tare da riƙe hannun Ayya ɗaya. Ayya kuwa da sauri ta kaɓe hannun ta tana furta " ke tafi chan yar neman ga,Wanda bai san ciwon kan sa ba zaki saka kan ki dole kula dashi,shekarar sa nawa,Mahajjaci ai ba yaro bane,ada na wahala dashi amma yanzu babu garjejen ƙaton da zan wahala akan sa ta tafi ta bar mana jaraba,duk halin uwar shi ya gado " mstww taja mugun tsaki tana juyar kan ta gefe taana cigaba da kallon tsohon Film na hanyar Kano da ake haskawa a tashar ta Saira movie tana jan charbi a hannun ta. Samra hawaye ne suka wanke mata fuska nan ta fashewa Ayya kuka,dama ta san ba lallai ta samu magana mai daɗi ba amma ta san yadda yake mugun jin maganar Ayya akan takowa a gidan.Ba ta san dalilin da ya sa Ayya take tsangwamar sa ba tun bata gane abun da ke yi wa ya yan na ta ba daɗi har ta kai ta fahimci inda ta dosa dan kai tsaye take nuna bata son sa duk da irin biyyayyar da yake mata saboda rabin rayuwar sa a hannun ta yayi ta,kuma tun yana ƙaramin sa yake cikin matsin Ayya har bai gane ba ya gane dan haka dai dai da rana ɗaya bai taɓa nuna damuwa saboda kallon uwa yake mata koda yaushe. Miƙewa tayi da sauri bata ƙara cewa komai ba ta fice daga sashen tana Sharar hawaye.Sai dai tsaye tayi ganin wanda ya ke tunkare gaban ta,ta tare da jin ƙamshin sa da ya mamaye ko ina.Shi ɗin ne dai ya ke saukowa yana zuba ƙamshi ya sanya wasu irin kaya masu kyau da tsari kamar dai na sport riga da wando ash color da suka ƙara haska farar fatar sa mai sheƙi da ɗaukar ido.Cike da murmushi take bin shi da kallo har ya sauko.Ɗan sake fuskar sa yayi dake ɗaure kafin ya sakar mata lafiyyayen Murmushin sa yana shafa kan ta cike da son yar uwar ta sa da yake jin mugun Tausayin ta saboda yadda ta ke damuwa da lamurran sa dan ta kawai wasu lokuttan yake fitowa ya saka ma cikin sa wani abu dan ya san ta da naci yanzu haka ma.da ya ga hawaye a fuskar ta ya san daga inda ta fito dan haka babu tambaya,ya nuna mata shafaffen tumbin sa da kai kace bai taɓa samun wani abu a cikin sa ba.Fahimtar alamar da yake mata ya ci abinci ya sa ta sakin yar dariya ta jin daɗi ko bata tambaya ba ta san Chocolate ya ci saboda akwai shi da shegen son kayan zaƙi fridge ɗin sa duka sune shaƙe aciki babu kalar da babu.Ficewa yayi saboda yayi shirin sa tsafff dan zai ɗan motsa jikin sa ne da yake jin har yanzu yana masa babu daɗi.Dan haka yana tashi daga bacccin mara nauyi,ya ƙara watsa ruwa dan akwai wanka kamar moɗa.Chan baya inda field ɗin wasa yake ya nufa yana ɗan haɗawa da ɗan gudu.Dai dai lokacin suma su Salma da Sajida sun fito daga gurin sun gama buga ball kowaccen su da ɗan guntun wando.Kai ya ɗauke daga gare su tun kallon da yayi musu na farko.Su ko tsaye suka yi cike da jin haushin sa na share su da yayi gashi har haɗa baki suke yi wajen faɗin Sunan sa dan basu san ya dawo ba sai yanzu da suka gan shi.✍️ Duk abinda kuka gani kuyi Haƙuri ko editing na tafi ɗaya tafi uku nayi saboda yau ban samu na zauna ba.ngde WANNAN LABARI NA KUƊI NE A MANHAJAR WAHTSAPP *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Commente,and like pls 🙏 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P..1️⃣7️⃣ *BOOK ONE* PAID *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* Not edited🥺 ✨✨✨ Cike da murna ta faɗa ɗayan falon na Amma da yake ta upstairs ɗin da yake gefen hagu.Ganin ta hakan ya tabbatar ma Àmmah da ta samu abun da take so dan haka ta girgiza kai cike da murmushi dan ba ma sai ta mata bayani ba ta fahimci komai. Ƙaramin tsaki Sajida ta saki,ita kuwa Salma murmushi ta yi na farin ciki ko ba komai ai sun samu ganin sa tunda tsada yake yi dan shi ma suke yawan fitowa wajen wasannin basu san dalilin da yasa bai sake musu fuska kamar yadda yake sakewa Samrah ba har Sajida zata bi bayan sa Salma ta riƙo hannun ta tana girgiza mata kai.Kallon ta tayi kafin taƙwace hannun ta tayi gaba hasale dan ta ji zafin wulaƙancin da yayi musu,ita ba kowane ta ke ɗauka ba dan ma bata ga fuskar raini ba da tuni MAHAJ ya ga rainin ta. *** A ɓangaren SHATOU yau ta tashi da wani irin mahaukacin ciwon ciki da ya ke neman ganin bayan ta,duk murnan bikin sunan da zasu tafi na maman ramata bata sami zuwa sabo da yadda ciwon ya sako ta gaba ko maƙiyin ta sai ya tausaya mata. Ta zama Abar Tausayin Inna ni da Baffa na iya kar ƙoƙarin su kawai suke yi har ɗan chemist da suke dashi ya je ya siyo maganin ta sha banza dan yana lafawa da mintuna ƙalilan yaƙara tashi dan haka suka zuba ma sarautar Allah ido domin kamar ciwon bai jin magani gashi baiwar Allah duk ta ƙara lanƙwashewa.Shatou tayi Kwana kusan huɗu tana fama da wannan ciwon babu wani sauƙi sai ana biyar ne ta samu da ƙyar ta miƙe ta shige toilet wajen fitsari bayan ya ɗan lafa mata sai dai,me ƙara ta saki ganin abinda yake fita a jikin ta bayan fitsarin.Inna Ni dake tsakar gida cikin ɗan jin daɗin miƙewar da tayi ta taso da sauri dan ita kaɗai ce a gidan,sai SHATOU. " SHATOU lafiya kuwa,ko jikin ne ".Inna ni ta furta bayan samun kan ta tsakiyar makewayin. Miƙewa tsaye Shatou tayi dan kamar an zare mata ciwon jikin ta lokaci ɗaya haka ta ji sai ta ɗan samu sauƙi. Idanu Inna ta zaro cike da farin ciki kafin ta riƙo hannun ta tana ayyana wa aranta wata sabuwa.Dan wani sabon aiki ne ya same ta bata taɓa tunanin Shatou zata iya shiga wannan yanayin yanzu ba ta yi tunanin sai shekarun sun ƙara yin gaba duba da yanayin ɗan jikin na ta. " Ji rani nan " Inna ni ta furta fuskar ta cike da murmushi.Kafin ta fice daga bayin. SHATOU kuwa hawaye ne har yanzu suke silalar mata duk da yanzu ta tuno da wani karatu da wani malamin su yayi musu kan wannan abun da ya same ta sai hankalin ta ya ɗan kwanta yanzu ƙyanƙyamin kanta take yi sosai dan haka take tsaye hawaye na silalar mata musamman ganin yadda jinin ke bin ƙafafun ta saboda na farko ne yana mugun rushing sosai. Ɗauke da wando ta shigo tare da Wani ƙaton tsumma da ta yanko wani zanen ta wanda bai ji jiki ba. Nan ta kimtsa Shatou da ke ta hawaye bayan ta bata izinin yin wanka dan har da ruwan wanka ta haɗo mata tana gama yin wankan ta saka komai gaban ta kamar yadda ta nuna mata.Ganin hawayen yaƙi tsayawa ya sa Inni ni furta " Ni fa kin ishe Ni,haba,Girma fa ne ya kama ki,dama so kike ki ƙara girma ai, yanzu zai zo lokacin sa yazo,tunda baki son ana ce Miki ƙarama " Ta kai ƙarshen zancen tana sakin yar guntuwar dariya.Baki Shatou ta turo gaba tana jan majina.Kafin tayi gaba ta baro Inna ni cikin toilet ɗin tana wanke kayan ta da ya lalace wando da rigar. Ɗaki shatou ta shige ta yi kwanciyar ta saboda duk jin ta take yi a takure kamar an manna mata wani mugun abu ganin take yi motsi kaɗan zai iya saka abun ya faɗo dan haka ta takure waje ɗaya. Maganganun Inna ni kuwa da ta yi ta jera mata suna dawo mata kan kunne.Zantuka ne masu cike da gargaɗi da tsoratar wa.Dan haka taji ko wajen bata son fita domin Inna ni ta nuna mata kuskuren da ke ciki koda ace hannun ka ka bari wani ya taɓa wanda ya wuce Bibu da Baffa na. Duk dai wani yanayi da kuka sani farin shiga yana samun kan sa ciki haka SHATOU ta tsinci kan ta cikin yanayin mai takura.Tana cikin tunanin zantukkan ne wani irin bacci ya kwashe ta. Inna ni kuwa cike da tausayi haka ta wanke kayan na Shatou ta cigaba da ayyukan gaban ta dan ta samu ɗan kwanciyar hankali ko ba komai ciwon ya tafi tunda dama wannan ne dalilin wahalar ta ta ita bata ma lura ba tunanin ba bai zo ga kan ta ba a tunanin ta ko ma wani abun ta ci a waje basu sani ba. A haka koda Baffa na ya dawo shida Bibu sun ji daɗi sosai ganin Yadda Inna ni ta sake Sosai babu wata damuwa kan fuskar ta hakan ya tabbatar musu da Shatou ta samu lafiya,dan haka ya jikin ta kawai suka ƙara yi mata sannan.Nan ta sanar musu da ta ji sauƙi ta samu bacci ma suna tsaka da zancen kuwa sai ga ta ta fito tana yaƙune fuska tana wani haɗe ƙafafu.Duka zuba mata idanun su kayi cike da tausayinta ganin yadda ta ƙara yin fayau da ita har ja ta ƙara yi kamar wadda aka kwalhewa jinin jiki. " Ya jikin SHATOU "? Cewar Baffa na. Cike da murmushi ta amsa masa tana zaro ido jin kamar abinda ke fita jikin ta zaya zubo ƙasa saboda yadda yake mata rushing. " Adda SHATOU lafiya kuwa kike zaro ido haka kamar wacce ta yi ƙarya,gaban mai gari " Ya kai ƙarshen zancen yana sakin ɗan guntun murmushi. Hararar sa ta yi kafin ta mayar da kallon kan Inna ni da take ta kallon ta tana tsoron ta ce musu wani kan halin da take ciki dan haka ta zuba mata idanu tana fatan kar Surutun ta ya kai ta sanar da su duk da ta san dole ma zasu iya sani wata rana.Duk da ba abun ɓoyo bane. Kai Inna ni ta juyar gefe kamar bata ga yadda take zaro ido ba yanzu dan ta fahimci halin da take ciki dan haka tace " Wuce ki samu waje ki zauna " Sai dai bata kai ga rufe baki ba Shatou ta faɗa Makewayi a Guje bayan ta runtumi buta.Sai da ta ɗan jima sannan ta fito tana ɓata fuska dan sabon tsumma ta chan za tana jefar da wanchan dan nan Inna ta ajiye mata kayan ta san zata buƙace su. Inna ni kai kawai ta girgiza kafin ta zubo musu abincin a waje ɗaya dan wasu lokutan tare Baffa na yake cin abin cin sa da ya yan na sa. Koda Shatou ta fito har sun fara ci sun yi fiye da rabi da sauri ta nemi waje kusa da Baffa na ta zauna.Sai dai har ta ɗora hannun ta akan filet ɗin ta cire tana ya ƙunar fuska wasu daga cikin spoon da Inna ni take da su ta ɗauko ɗaya cikin su duk da kasancewar su yan ƙanana.Babu wanda ya ce mata ƙala daga Inna ni har Baffa na da yake nuna musu cin abinci da hannu ya fi lada da albarka. Tare suka cinye abincin sai dai suna cinye wa itama ta miƙe dan jin cikin ta famm duka kallon ta suka yi cike da mamakin ɗan abincin da take cewa ta ƙoshi kan sa. Bibu ne ya ka sa haƙuri yayi wa Baffa na rigaye da yake son yi mata magana " Adda SHATOU wannan ɗan abincin zai ishe ki keda bakya zama sai kinji ko ina tab". Ya kai ƙarshen zancen yana kallon ta yar Hararar wasa tayi masa dan Dagske dai ta ƙoshi ɗin bata jin ma zata iya cin abincin dare dan ji take ko ina yayi mata baƙebaƙe.Inna Ni dai bata ce komai ba dan ta san hakan bai rasa na saba da yanayin da take ciki dan haka mutun yake komawa kamar mai lauyayi a wannan lokacin bare mata shine farkon ta.,dole zata samu ire iren waɗannan abubuwan. Ganin Dagske ta ƙoshi ɗin dan kai tsaye ta cewa Bibu " Wallahi Allah Na ƙoshi ko Baffa n,a shafa ciki na kaji ". Ta na sauke ayar zancen tare da kamo hannun Bibu da yake kusa ƙwace hannun sa.Yana ɓata fuska saboda ganin ya kw yi kamar har yanzu jikin ne dan duk da yake bata da lafiya da ta farfaɗo sai ta ɗan zubawa cikin ta ko ba da yawa ne,amma gashi yau ta ji sauƙi sosai ta kasa cin abincin. Baffa na ne yayi Murmushi tare da shafa kan Bibu yana cewa " Habibullah bafa koda yaushe mutun yake zaune akan halayyar sa ba a wasu lokuttan ya kan iya aro na wani,dan haka ka daina damuwa Addan ka zata samu ta samu lafiya,gata nan komai tanayi,akwai abinda ya sauya mata cikin ." Kai Bibu ya gyaɗa cike da tausayin yar uwar ta sa. Ruwa ta sha kafin tayi gyatsa tare da yin godiya ga Wanda ya ƙara tabbatar musu da ƙoshin ta. zaman ta nan gurin tayi tare da Inna ni da ta rage a wajen saboda sun tafi cire kaya su watsa ruwa su huta. A ɓangaren su ALINA kuwa yau kusan kwana biyar babu mai iya yiwa wani magana acikin su dukkanin su sun koma kamar wayen da basu da lafiya saboda yadda suke azabtuwa da rashin kula junan su, ALINA tana son yiwa REENA magana sai ta kasa musamman dan ta bata haƙuri da Auntyn su tace ta bata saboda itace ƙarama idan ma faɗa su kayi komai zai wuce kasancewar an ga sun dai na ko chachar baki ne a aji babu mai kula kowa.REENA tsoro ne maƙil a zuciyar ta ga Tausayin yar uwar ta da ta san ya damuwar bugun da BILAL yayi mata a matsayin ya tsane ta ta tabbatar ko kashe ta zai iya yi in ya samu dama a ƙuruciyar ta dan haka ta sha alwashin babu ita babu magana da ya'yan na ta idan ma ya zo ba zai ƙara ganin ta ba har ya koma gurin aikin sa,tun da bai son ta,dan a zuciyar ta cewa take yi bada gangan tayi wa REENA haka ba ita kan ta bata iya cewa ga yadda aka yi ta mata wannan dukan abun da kawai ta sani shine ta hau ruwan cikin ta da faɗa ya fara. Yau ne suka ɗan sake dan kowaccen su ɗakin ta take bacci ita ɗaya a wahalce Umma tayi rarrashi ta saka musu ido. Tana son sanar da Bilal sai dai shima har yanzu ba wani sakewa yayi ba duk daya

Chapter 13 of 39