Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya'ya Abdul Shine fa kafin mu fice ta ganmu ta ƙalla sau ta tace sai ta bimu,muka ce ba zamu je da ita sai kuka,sai aka sa,a Dada ya fito ya motsa jiki shine ya saka mu dole muka fita da ita aiko munyi dana sani dan mutumin nan ya ji haushi sosai yana fama da kan sa shi kaɗai ya san halin da yake ciki amma yarinyar nan saboda rashin ta ido ta fara sakar mai dariya tana nuna yadda motar ke rawa " . Har Hajiya da bata wani shiga firar ba bayan zaman ta wajen yanzu dariya tayi tana furtawa A ranta Allah ya shirye ku Albasa bata yi halin ruwa ba Leena mahaifiyar ku mutuniyar kirki koda yake ba haushe yace kana haihuwar ɗane baka haifi halin sa ba addu,a ta cigaba binsu da ita duk su duka tana rokon Allah ya ƙara shirya musu zuri,ar su. Samir bayan ya tsagaita da dariyar sa ne ya kalli Leena da ta haɗe rai tuno yadda Ayman ya janyo ta ya rufe glass kafin ya balbale ta da faɗa dan haka tun da suka yi mata haka dan shima Abduljabbar ya taɓa faɗan ta rufe komai. Hannayen ta ya riƙo kafin ya kalli fuskar ta yana jan kumatun ta take kuwa ta washe baki tana dariya kamar Ba ita ba dan tana mugun shiri da Samir sosai idan ka ga dariyar ta da ya Samir ne a irin mabanbanta lokuttan. Ƙarar wayar shi ce ta sanya shi dakatawa yana kai duban sa ga screen murmushi ya saki kafin ya ɗaga kiran. Da sallama ɗauke a bakin sa ya ɗaga tsadaddiyar wayar ta sa ya saita a kunne. Daga chan ɓangaren Amsawa aka yi kafin cike da barkwaci ya ce " Allah ya taimaki soja ni na 'isa " " ai Reena mutuniyar kirki ce gasu nan ma kusa muna fira ,kuma an kawo mini ƙarar ka daga jarumar gidan nan ". Ban san abinda aka faɗa masa ta chan ɓangaren ba naga ya saki murmushi yana shafa kai kafin ya kalli Leena ya ce " Mu dai Dan Allah kar a ƙara taɓa mu kaga ka sa ka mu fushin ka da yawa " Fahimtar da wa ake yin waya hakan ya sa Leena ɓata fuska sai hawaye kafin ta miƙe tana shirin fita daga part ɗin gaba ɗaya hannun ta ya riƙe da sauri yana girgiza mata kai.Kafin ya kafa mata wayar a kunne. " Kin gama fushin,ko da saura na ƙara miki lokaci " ? Shiru tayi tana haɗiye kukan ta jin yadda yayi magana cikin kakkausar muryan sa da babu wasa a cikin ta kafin ta ce komai ta kara tsinkayar Muryan sa yana cewa " Sakaryan yarinya kawai,Mara hankali,zanyi maganin ki duk abun da ke kan ki sai na cire Miki shi mark my word " kafin ya ja karamin tsaki yana kashe kiran . Ai Leena bata san ta saki wayar ba tana ɓarkewa da kuka kafin ta kai ƙasa harda murje murje kamar yar shekara huɗu.Kan ta suka yi ganin abun na ta kamar mai Aljannu dan ta birkice dagaske hankalin su ne ya ɗaga jin tana kuka kamar ranta zai fita,sai an samu ta rage sautin kukan bayan ya dago ta ya rungume ta kaɗan sai kuma da ta tuna kalaman sa sai ta ji wani irin baƙin ciki tana ji ina ma ba Ya Bilal Bane ta masa rashin mutunci kuka tayi mai isar ta ana Rarrashin ta.Shiko Samir hankalin shi duk ya ta shi dan haka ya ce " B da yace zai bada haƙuri ashe wata rigimar zai tsokano mana ya bar mu da rigima ". " Cewa fa yayi na baki ya rarrrashe ki ya baki hakuri ". " To ba ce min yayi Sakarya ba kuma wai duk abin d ke kaina sai ya cire mini,kenan yana nufin ina da aljanu Ni wallahi lafiya lau nake,wai sai yayi ta haɗa Ni da Aljannu " ta ƙara fashe wa da kuka cike da sangarta itama Reena ganin kukan Leena abun ka da ɗan uwa tuni ta fara tsiyayayar da hawaye itama kafin ta ɓarke da kukan haka suka jeru su biyu Ninah babu batun dariya ga abun dariya dan haka ta zuba musu ido kawai kamar ta samu tv. " A yafe ma yya B kinjin my baby shi fa big brother ne duk abinda yakeyi saboda ke ne da samun kammaluwar ki,You should not be like that hakuri zaki yi kinji Babyn SS kin san Ya ce ke ce matar ta sa Farko ba Hajo ba " Cike da barkwanci Samir ya kai maganar ƙarshe.Dariya duk suka sanya kafin suka tsinkayo Muryan ta tana shesshekar kuka bayan gama yar dariyar da tayi yanzu tana cewa bata son Sir ya mata tsufa " Ya Samir fa harda mara hankali ya kira mini wallahi kuma Ni ba mahaukaciya bace ai dai ka sani ko " Kai ya ɗaga mata kawai har ta gama maganar ta yana murmushi ganin hawaye sun ƙara silalo mata hakan ya sa ya ƙara janyo ta jikin shi ya yi wiping tears ɗin.Yana furtawa common is ok chill up my baby a hankali. Su ko Su Abduljabbar da Ayman yar dariya kawai suke yi wa Reena da ta lafe gefen sa itama idanu sun yi jazir wanda har yanzu idanun ta hawaye suke yi sai dai basu kai na Leena ba.Ta tsani ganin yar uwar ta cikin damuwa ko ƙalilan ta dan haka kukan ta bai da wahala akan abun da ya shafi Leena ɗin. A haka suna nan aka kira Sallan azahar dan haka suka miƙe kowa yayi wajen Sallah ,Su ko Su Leena Sashen Ummah suka koma da niyyar zasu dawo haka ma Ninah tare suka fice tayi na su sashen. " Na ra sa yadda zanyi da matar nan wállahi ta san bana buƙatar ganin ko ɗigon jinin ta ne a kusa dani amma wallahi saboda muguwar gulma da munafunci musamman take Turo su gaisuwa waje na har Babban su,Shin dole ne bana so wallahi bana kaunar ta ko kaɗan da ina inada yadda zan yi da ita da tuni nayi ". Hajiya Sa'ada ce ke zancen tana kishingide kan mahehen gadon ta na alfarma daga ita ɗan towel wanda ya rufe mata jiki da alama daga wanka ta fito sai hular wanka akan ta. Ban san abinda aka furta mata ta chan ɓangaren ba na ga tayi dariya kafin ta sake cewa " Ki bar Ni da ita wallahi zan yi maganin ta,ke ni har mai gidan ma yanzu mugun Haushin sa nake ji yayi tafiya Lagos kwana biyu da suka wuce da ya dawo ɗaki na ya kamata ya sauka amma wallahi Sashen matar chan ya sauka da na kalubalance shi sai ce mini yayi ai ya'yan sa kawai ya je gani da yayi kewa kiji munafunci fa,Sai yanzu nake jin dana sani matuƙa akan ƙwayoyin hana haihuwa da na yi ta bankawa kaina,wallahi tunda likitota suka ce sai an cire mahaifa ta ta lalace nake cike da tashin hankali haryanzu da aka zare ta bana samun isasshen bacci mai daɗi Mabaruka " Handsfree ta saka wayar ta sauko ta zauna kan mirror da ke wadace da kayan gyara fata sannan ta cigaba da sauraren maganar da ake yi ta ɗayan ɓangaren " Sa'ada sai da nace Miki kar ki yi,amma kika rufe ido bakya son haihuwa da wuri yanzu gashi nan ai mu kan mu kin barmu cikin damuwa, kuma nace ki karɓa yara ko na dangi ne yan ƙanana ki raina kin kasa kin fison baƙincikin Barirah da wannan su kai ki ƙasa,ki na kallo zata kwashe komai ita da ya'yan ta ga dukiya har ba a san iyakar ta ka ba amma babu magajin ki ai na yi baƙuncikin wannan lamari ". " Hmmm Ba zaki gane ba ne,Bana son sai na gama wahala da yaya su koma gun mahaifiyar su ne su bar Ni da ciwon zuciya da ƙunci shi ya sa kawai na karɓi kaddara ta hannu biyu,kuma bana fatan wata rana Saleh ya san da wannan maganar tunda bai san komai ba akan hakan sanin sa kawai bana haihuwa dan haka na haɗa baki da likita ya faɗa masa " " Allah ya kyauta ai Bama zai sani ba '' " Yanzu dai zamu yi magana zuwa gobe in Sha ALLAH idan na samu time zan shigo sai mu ga abun yi dan matar nan da alama ba tsaye take ba Bayan saye zuciyar shi da ya'ya har da wani sharrin da ban Dan Barirah da ganin ta nan macijin sari ka noce ce,zan shigo dai zamu yi magana " " Tau yayi yar uwata Nagode ki gaida Alhaji Mamman da yara " " Zasu ji in sha ALLAH bye " Daga haka suka yanke kiran. Tsaki ta ja tana cigaba da mirza mayukkan ta hankali kwance. Numfashi ya sauke da ajiyar zuciya tun bayan sauke wayar kunnen sa yake kallon wayar yana jin sautin kukan nata har tsakiyar kan sa.Murmushi ya saki a hankali kafin ya furta " Ni kowa ye zai kwashe mini wannan rigimammiyar ƙanwar ta wa,hankali sai baya yake yi " " Allah ya shirya mini ku twins " Miƙewa yayi ya shige rooms ɗin sa dai dai nan Ab ya shigo da Aiken da yayi masa. Wayar sa ya kira hakan ya sa ganin Ab ne ya ɗaga " shigo " Kawai yace masa ya katse kiran. Cikin haɗaɗɗun Rugs dake wadace da falo mai kyau da ya ji dark purple light rugs and curtain komai sai san Barka ko ina tar ga wata haɗaɗɗiyar tv dake ta aiki. Sara masa yayi kafin ya miƙa masa wata yar takarda. Karba yayi yana dubawa ya ja tsaki bai ce ma AB komai ba yayi gaba ya shige Bedroom ɗin sa, Ab kan sa kawai ya girgiza ya fice dan shi kam bai san amfanin aikin da ogan sa ya saka shi ba shi inda ma ya ga yarinyar da zai iya ma binciken ƙwaƙwaf amma ba kowace asibiti ne suke iya bada bayan nan mara lafiya ba,saboda doka ce bare Babbar asibitin SHAHABS ta manyan mutane. Aiken da BILAL yayi wa Ab kuwa shine tura sa asibitin ne ya nemo masa bayanan wannan mara lafiya ɗin dan mugun tausayin ta ne ya ɗar sa masa lokaci ɗaya ya kasa samun natsuwa yana son tallafa mata ya kai ta wajen wani Babban likita a Chaina,kafin su koma Lagos ya so su gama komai da ya dace.Sai dai yanzu bayan zuwan AB ya samu labarin an sallame ta sannan sun hana bayanai dan komai nata da ban yake hakan ne ya sa ran BILAL sosuwa ya ta shi ya shige daki yana jan tsaki mara sauti da tunanin shisshigin me zai kai sa dan haka take ya watsar da maganar bin ta da addu'ar samun lafiya. Shiru ya zuba ma wani hoto guda biyu da ke a jiye da bandan ɗaya na mace ne tana sanye cikin farar abaya ta yane kan ta da veil ɗin sa tayi kyau sosai a kallo ɗaya zaka mata san cewa Babbar mace ce sai na biyu hoton shima dai Hoton Matashin magidanci ne sanye da ƙanana kaya yana ɗauke da briefcase yana murmushi an masa hoton kamar dai wajen taro aka ɗauke shi ma a hoton. Wani irin abu ya haɗiye mai kauri a maƙoshin sa wanda yake ta kai kawo tun zuba ma hotunan biyu idanu.Hawayen da suka cika idanun sa ne ya shafe kafin ya fashe da wani irin kuka mai cike da kewa da raɗaɗi da baƙin cikin da yake jin ba zai taɓa gushe masa ba,wazai tun kara ya warware masa wannan lamari,me ya sa sai shi mai ya sa,zuciyar sa ta kasa gasgatawa me ya sa ya furta a bayyane da ƙarfi yana buga kan sa da kan gado kafin ya mike cike da ƙunar zuciya ya shige toilet kan sa ya sakarwa ruwa yana yi hawaye na silalar masa wani irin raɗaɗi a zuciya na sake mamaye sa. *Wani irin kaɗawa iskan wajen keyi tana bada wani irin ƙamshi mai narka zuciya da ruhi yadda wajen ya wadatu da shuke shuke da yanayin ruwa dake gudana a ƙasa zaka tabbatar ta Babban waje ne baida hayaniya ko kaɗan a wajen kowa yana harkan gaban sa ne babu ruwan kowa da kowa,a gefe akwai hadaɗden restaurant dake tsare gwamnin burge wa. Zaune yake daga shi sai guntun wando ya mike ƙafafun sa ɗaya akan ɗaya kan yar rumfar da yake cikin ta ya ɗaura hannayen sa kan ƙeyar sa idanun sa kuwa sanye da wani irin faskeken rado mai kyau black wanda ya ƙara bayyanar da ainahin zubin kyaun sa. Wayar sa ce tayi ringing kusan sau uku kafin ya ɗan ɗago ya zuba mata idanun sa wani kiran ne ya sake shigowa dan haka a hankali ya miƙa hannun sa ya zari wayar. Abbu shine abun da ya furta a ƙasan laɓɓansa sa. Goshin sa ya ɗan dafa dan bai yi zaton Abbu bane yayi zaton Mubarak da zai zo yau ne yayi zaton ya iso yana tunanin ya je ya dauko sa ne kamar bai san hanya ba. Sai da kiran ya katse sannan ya bi bayan sa. " Assalamu alaikum Abbu " Shine abinda ya furta kafin yayi shiru. Abbu cike da farin ciki ya amsa yana sauke ajiyar zuciya tare da sakin Murmushi mai sanyi. " Shine bazaka neme ni ba yau kusan kwana biyar MAHAJ kamar ba ka ma yi kewa na ba ". Murmushi ya saki mai sanyi kamar yana gaban Abbu sannan ya ce " Abbu kana lafiya ai Mubarak yana faɗa mini komai na shiga busy ne saboda mun fara preparations na presentations ɗin da zamuyi " shiru yayi har Abbu ya fidda rai da zai kara magana ya ce " Abbu ai kana raina daga ku har su Ayya ". Murmushi Abbu yayi sai kuma ya ji hawaye sun tarar masa na tausayin ɗan na sa da yake cikin kewa ta kulawar mahaifiya da bai samu ba. Ajiyar zuciya MAHAJ ya sauke dan shi da Badan mahaifin sa ba sai Samrah da babu abun da zai saka shi yawan komawa gidan ma Hutu sai dai yayi zaman sa nan.Amma ko yaya ne yana duba farin cikin da zai gani akan fuskokin Wayen nan mutanen guda biyu. " Aikin Ƙauyen ne an fara shi tun kwana biyu da suka wuce,na san kana da labarin komai ". Shiru yayi ma Abbu hakan ya sa Abbu sakin guntun murmushi dan ya san ba tan ka masa zai yi ba. " Allah ya sa ka da Alkhairii,ya sa matar Auren ka ta zame maka ta gari,ya baka yaya masu albarka da maka biyayya kamar yadda kake yi mini ". Haka kawai ya ji bakin sa yayi masa nauyi dan haka ya kasa Amsawa da Amin.A duk lokacin da mahaifin sa yayi masa irin wannan addu'ar wani yanayi yake tsintar kan sa ko yanzun dai hakan ya samu kan sa.Yana jin kamar yana yiwa mahaifin sa zagon ƙasa domin duk wannan zancen na mahaifin sa babu shi Aran sa ko nan da shekara goma ne,ba zai so rayuwar da ya ta so ta kaɗaici ya yan sa su yi ta ba dan haka bai shirya ma zuwan kowa karƙashin sa ba hasalima private life ɗin sa itace yake ganin tafi dacewa dashi har ƙarshen rayuwar sa saboda yadda ba ya son takura. Abbu bai ji komai ba na kin amsawar ta sa , sai murmushi da yayi bai yi masa maganar ya amsa ba yau kamm, shi kan sa Mahaj murmushi kawai ya yi cikin mamaki ya ɗan sauke wayar sai kuma ya tsinkayo Muryan sa yana furta " Mubarak zai sauka in the next thirty minutes in Sha ALLAH ka tura a ɗauko sa ko kaje da kan ka ". Baki ya tura gaba kamar Abbu na ganin sa jin shirun sa ya sa Abbu dariya kaɗan ya ce " kun fi kusa,ka kula da kan ka bye,Allah yayi maka albarka". " Amin " ya furta a ƙarƙashin laɓɓansa sa da suka ƙara yin jaaa sosai dan sai ɗan taunar su yake yi a hankali miyan bakin sa na ƙara musu sheƙi da nuna Zallar yadda suke a taushi. Headphones ya makala dake gefen sa bayan ya sauke ajiyar zuciya yana ƙara zuba wa wayar ta sa manyan idanun sa. Ɗan lemu dake gefen sa kan wani table ya ɗan yi sipping wanda ke a kan wani haɗaɗɗen cup yanayin dai na turawa haka irin wanda ake saka mocktail,jaaa yayi kaɗan da straw ɗin ya ajiye yana mai da idanun sa ya rufe ruff iskan da ke shiga jikin sa na ƙara masa wani jin daɗin wajen dan yadda ta garwaye da turaren sa mai Shegen ƙamshi sai kayi zaton shine mallakin wajen gaba ɗaya. A ɓangaren shatou dukkanin kwanakkin nan da suka shuɗe kullum sai Iro ya tare ta a hanyar makaranta ko aika,har ta kai yanzu ba ta son fita farautar ma da ta ke yawan matsawa idan ba,a je da ita ba yanzu bata zuwa,su Baffa na sun sakawa ikon Allah ido dan kowa ya fahimci Iro dai son Shatou yake yi duk da taƙi barin sa ya faɗa ɗin ma dan ga tsau ga tsau haka take jefa masa magana mara daɗi amma duka ya shanye.Yau ma daga wajen farauta ta fito saboda ta gaji sai ta baro su Baffa na chan Ita dai saboda gajiyar da ta kwaso bata san cewa akwai mutun bayan ta ba hakan ya sa ta ke tafiyar ta hankali kwance dan ta rage guje gujen yanzu. Ta kawo wajen wata bishiya kenan kawai ta ji mutun bayan ta ya ce "keeeh " Irin abun nan na ka bawa mutun tsoro cikin soyayya shine Iro ya yi mata aiko ta zabura ta zunduma a Guje ko waigen sa ba tayi ba, shima bayan ta ya bi yana ƙwala mata kira yana dariya cike da nishaɗi. Fahimtar shine hakan ya sa ta ƙara giyar gudun cike da Haushin sa.Su Ramata ne suka tare ta da Amina suka shaaa gaban ta hakan ya sa ta dakata dan har ta yi niyyar wuce su.Sai kuma ta ci burki tana Hararar su.Dai dai nan shima Iro ya iso wajen yana sauke numfashi yana cewa " Haba Shatou ke ko tausayi na baki ji kin fa gane Ni amma kike cigaba da gudu na haba Shatou na". Wata uwar Harara ta jefa masa kafin ta kalli su Amina da suka yi tsuru tsuru suna kallon Iro ganin yadda ya ƙara komawa kamar ba shi ba abokin faɗan Shatou wai yau shi ke kiran Shatou da shatoun sa. Dariya suke son yi babu dama dan shatou bata ƙaunar ko tsayuwar su ne duk sun shaida hakan yadda take tserewa kafin a tashi makaranta saboda shi har wajen wasannin su ta daina zuwa sosai saboda shi dan duk wata hanya da ya san zasu haɗu sai ya bita,ƙofar gidan su idan ya je zai gaji da tsayi yayi gaba. '' Nifa wallahi Iro ka fara isata wallahi zan kai ka ƙara wajen mai gari haba duk ka bi ka ta kura mini kamar bani da gata saboda jarabar ka ko kofar gida ta daina burge ni,ni kan wallahi ga mai gari zan kai ka ya ƙara mana kashe di "ta kai ƙarshen zancen kamar zata saka kuka musanman da ta ga ko ajikinnsa sai ma Murmushi da yake ta saki dan shi wata dama ya hango a nan take wajen.✍️ # 2025 # Hausa novel # Love,and romance story # Labari mai tafiyar saƙar gizo gizo # Soyayya mai tsayawa a zuciya # Kaddara mai cike da ƙalubalen rayuwa # zamba ma yar aike ce. # Cuta mai mai ban tsoro. # Mummunan Zuciya kai bawa mahalaka # All in one story ~*KURMAN ƘADDARA*✍️~ # Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣7️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* ♣️♣️♣️ Fuuu haka ta wuce ta bar su nan shi da su Amina ana kallon kallo kafin ya ɗan bi bayan ta da sauri sauri sai dai kafin ya an kara ta zunduma a guje dan ta fahimci muddin ba haka ta yiwa Iro ba,ba zata zauna lafiya ba.Dan bata taɓa jin zata iya tsayuwa dashi. Koda ta shiga gida babu sallama Inna ni na aikin wanke kayan da ake zubawa shanayen Baffa na abinci wayen da suka yi datti.Dan tun safe bayan Shatou ta gyara musu wajen su ta ce ta wanke su amma bata yi ba saboda shiriritar ta,sai ta ɓuge da bin su Baffa na Farauta. Kai kawai Inna ni ta girgiza bata iya ce mata komai ba sai cigaba da aikin ta dan ko bata tambaya ba ta san cewa Iro ne ta ke yiwa wannan guje gujen.Ta rasa dalilin da ya sa shatoun bata ƙaunar Iro ko kaɗan domin ga alama nan ko tsayu wa ta arziki ta ka sa yi da shi,itama wani farin ciki take ji duk da bata jin zata yi mata auren wuri kamar yadda ake yi a Ƙauyen na su duk da ƙalubalen da zasu fuskanta tana son Shatou tayi karatu mai zurfi ta taimaki mutanen wannan ƙauye ta mayar da kyauta da karamci. Zaune ta kai daɓass tana huci da sauke numfashi kafin ta ce ''Inna ni dubi dan Allah yadda Iro ya sako ni gaba wallahi na kusa kai shi ƙara wajen mai gari " " Aah ba ayi haka ba,kefa matsala ta dake rashin wayau shi iron ne meye dalilin zuwan sa wajen ki " ? Ƙin bata amsa Shatou tayi dai zumɓura baki. Murmushi Inna ni tayi kafin ta ce " to tunda kin san abinda ke kawo ɗan mutane ai sai ki bari ki ji abun da zai faɗa daga baya sai ki san abun ce masa,kuma banda wulaƙan ta wa Shatou rayuwa bata da tabbas karki wulakanta kowa domin baki san ɓoyayyen Alkhairii sa gare ki ba,sannan baka san mai taimakon ka ba dan haka idan ma tsayawa ne ba kya son yi dashi ki gaya masa ke an hana ki tsayuwa da kowa a gida faqat ". Bakin dai ta ƙara tun zurawa gaba bata ce komai ba. Chan kuma kamar an tsakure ta,ta mike tsaye ta kalli Inna ni ta ce " amma ai ni Inna ni bana son sa kuma ni ba a ƙauyen nan zan yi aure ba miji na birni yake shi ya sa bana kula shi duk ga su Amina nan amma sai ni da ya raina ". " Sannu matan ɗan birni,Haba SHATOU Soyayya ce fa " Baki ta kara turawa sai kuma kunya ta kama ta tayi kasa da kan ta tana dariya da ɗan murmushi Inna ni dai bata ce mata ƙala ba. Sai kuma ta matsa ta fara ɗauraya wa Inna ni kwanonin tana yi tana langaɓe kai maganar Inna ni na bata dariya wai Sannu matar ɗan birni,soyayya ce fa. A haka suka gama aikin tare. Su ko su Amina gaba suka yi kowacce su tayi gida suna ƙara mamakin Iro suna zuwa gida kuwa kowaccen su ta fara bawa innar ta labari suna dariya suma iyayen na su dariya abun ya basu duk da sun san haɗin mai wahala ne sai suka bi Su da addu'ar fatan Alkhairi. " Ina su Baffan naku,ba tare kike da su ba " ? " Ni na gaji ne shi yasa na tafowa ta " " Shine wanchan uban nacin ya biyo ni". Shatou ta bawa Inna amsa tana ƙara tura baki gaba. Komai Inna ni bata ce ba sai karɓe wanda yayi saura a hannun Shatou dan ta kasa dauraye shi sai juya shi da ta keyi har ta fara jiƙe kayan jikin ta. A tare suka kaiwa Shanayen da sauran dabbobin abincin su dan tun da safe sunyi gyaran wajen ita da Bibu saboda babu makaranta yau ɗin. Mubarak kuwa ya sauka ƙasar Beijing china lafiya dan sanin da yayi wa Ogan na sa kuma aminin sa da yake ma kallon ɗan uwan sa na jini ko ya kira sa ba lallai ya samu zuwa ɗaukar sa ba hakan ya sa koda ya fito

Chapter 21 of 39