Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dasa aya tayi shiru,kuma take suka karɓa dan kan ta na mugun jaaa dan tun da suka fara wannan program tana cikin wayen da ba su taɓa yin carry over ba,ba a class na su. Daga nan suka fara haɗa bayanai suka haɗa komai Aleeshat ma tun kafin a tashi kiran Alhaji Mamman ya fito da ita wanda bata ma yi niyyar ɗagawa ba amma saboda yadda wajen ya dame ta sai tayi amfani da damar kar su ga kawai ta fita bata cewa komai ba. Aiko tana fito wa ta yanke kiran Alhaji Mamman da kan ta.Tana jan mugun ƙaramin tsaki. Sai ga kira ya shigo wayen ta daga teacher ɗin su.Asad. Cike da sauri da wani irin mugun tashin hankali ta faɗa motar ta kafin ta kunna ta, ta fige a tsiyace ta bar school ɗin baki ɗaya bayan yanke kiran. Idanun ta ne suka rikiɗe lokaci ɗaya damuwa ta bayyana ƙara ra akan fuskar ta sa. Gudu ta ke tsugawa bana arziki ba dan cikin abun da bai wuce min tuna goma ba ta isa bakin gate ɗin wata haɗaɗɗiyar asibiti da ta amsa sunan ta asibiti dan asibiti ce ta a manya sai dai ko talaka gwargwado zai iya kai kan sa Amma tabbas asibitin manyan mutane ce kama da ga yanayin zubin ta da Nairan da aka kashe mata. MMG Hospital shine sunan wannan asibiti a taƙaice. Kamar kullum sashen yara ta nufa bayan yin parking motar zuciyar ta na wani irin rawa da harbawa kamar Ance mata Asad ɗin ya Mutu. Idanun ta har dushi dushi suke gani saboda tsabar tsoro da firgici da ya shige ta da tashin hankali. Kafaɗan wani da ta buga ce ta sanya ta ɗan dawowa hayyacin ta kafin ba tare da ta tsaya kula wanda ta buge ɗin ba ta cigaba da tafiya,cikin kiɗima. Su biyu ne a tare ɗaya da kayan likitota ɗaya kuma sanye cikin kaya na alfarma mutun mai kamala da natsuwa daga nin sa dai ba ƙaramin mutun bane. Ɗan juyawa yayi ya Kalle ta kafin ya ɗauke idanun sa kan ta.Yana furta astagfirullah a cikin zuciyar sa. " Sorry M Ina ga tana da patient ne a ciki shi ya sa, hankalin ta na kan sa ".Ya kai ƙarshen maganar yana sakin murmushi ganin yadda Mutumin ya nuna babu komai yana sakin guntun murmushi kafin ya ce " Babu komai na ga alama kammm,Allah ya basu lafiya ". Amin wannan likitan ya furta. " Ammm Jibi zai shigo ko gobe,zamu yi magana in sha ALLAH idan ya amince,Ba abun damuwa bane Mahuta. ". Godiya wannan Dr da sunan shi ke maƙale a jikin rigar sa shine Dr Sada sabo Mahuta,Amma an fi kiran sa da Doctor Mahuta.Kayan sa da suka zube suka duƙa suka kwashe tare kafin suka yi musabaha da wannan likitan sannan ya raka shi har mota suna ƙara tattaunawa kan maganar da suke yi ɗin kafin su fito yanayin su dai kamar a bokai ko mutanen da suka shaƙu da juna sai dai akwai ɗan nuna girma ga likitan zuwa ga mutumen da ya kira M.Yana barin asibitin shi kuma ya juya ya koma cikin asibiti. Haka kawai yake jin ƙirjin shi ya buga da ya tuno da yanayin gefen fuskar ta da yayi arba da ita duk da ba sosai ya gani ba saboda saurin da take yi. Wani tunani ne ya shigo masa akai sai dai da sauri ya furta " No impossible gaskiya ". Haka ya cigaba da tafiya har ya isa inda zai je. A ɓangaren Aleeshat kuwa kasancewar ta san room no.nasa dan komai Anty prise ta sanar mata a waya hakan ya sa ta tura ƙofar jikin ta na rawa. Ko Sallama babu haka ta faɗa ɗakin ,wannan Aunty ta su Asad mai suna Anty Prise sai ganin ta tayi tsaye kan ƙafafun ta.. Zuba ma Asad idanun ta tayi da suka sauya kamannin su sai ga wasu hawaye Sun Silalo mata musamman ganin sa haka kwance marabin sa da gawa numfashi,gashi numfashin na sa ma har yanzu bai dai dai ta ba. Bacci yake yi kai daga nin sa kasan ya na shan baƙar wahala. Kujerarar da ke kusa da shi ɗayar ta zauna tana haɗiye kukan da ke shirin ta so mata. Tana taɓa hannun sa dake maƙale da drip. Kan ta ta kife akan cinyar ta saboda ta kasa jurewa musamman ganin sa yayi wani sharr da shi kamar wanda baya da jini a jikin sa.Ɗan ɗagowa tayi ta duba ɗakin tsitt wanda har Malamar ta tafi kasancewar dama mahaifiyar sa take jira duk da suna da clinic a school Amma na sa ciwon bana treating bane clinic dan wanccen karon clinic aka kai shi dan abun ya fara ta sar masa a makaranta gadan gadan,sai dai na yanzu ya fi worse,dan haka suka nemi asibiti mai kyau mafi kusa.Duk da lokacin da ya na ɗan shekaru biyu ya yi ciwon ya fara nuna alamar sa a jikin sa. Sai dai ba su taɓa kawo cewa abun zai zamo haka ba dan dukkanin su tsorace suke tun karɓan report na sa na farko da aka yi masa bincike a school clinic... Numfashi ta sauke mai nauyi kafin ta ɗago kan ta ta ƙara kallon Asad da har yanzu ko motsi bai yi ba. Wasu hawaye ne masu zafi suka ƙara biyo wa ta fuskar ta damuwa ta ƙara bayyanar ma ta da tashin hankali. Sai alokacin ta lura Aunty prise ta wuce.Shiru ta yi cike da tunani kala kala tana kallon Asad zuciyar ta cike da wani irin zafi da ƙunci.Tana nan zaune sai ga nurse ta shigo ta sanar da ita Dr na neman Iyayen Asad Jibril. Aiko babu musu ta fito bayan ta yi wiping tears nata da wata hanky ɗin ta mai kyau fara tass. Asad kuwa ta bar shi hannun Nurse dan dama jinyar mutun ɗaya ke yin ta,idan ya kasance ku zaku yi jinyar abun ku ba nurse ba. Cikin sanyin muryan ta tayi Sallama zuwa cikin office ɗin. Ɗago idanun sa yayi ya zuba mata ido dan koda basu ga fuskar ta ba ya gane shigar ta. Masha ALLAH ya furta a cikin zuciyar sa sai da ya ƙare mata kallon tsafta sannan ya ce " Bismillah ga seat ".Ya furta yana nuna mata seatt ɗin. Aleeshat kuwa babu musu ta nemi waje ta zauna tana sauke ajiyar zuciya,haka kawai take son jin wani abu da ban bayan report na farko na Asad ɗin dan haka ta ƙagara ya sanar da ita komai ta san halin da Asad ɗin ta yake ciki. " Ammm ke wacece a gurin Asad F Jibril ".? Yayi mata tambayar duk da cewar ya ga yanayin kamannin su amma yana son tabbatarwa ko ƙanen ta ne ko ɗan ɗan ta dan daga yanayin shigar ta baiga alamar matar Aure bace ko kaɗan. Ɗan jimm tayi tana wasa da zoben ta na azurfa mai kyau da ya ƙara yiwa yatsun ta kyau ta ce " Ɗa na ne " . Daga haka bata ƙara ce masa komai ba. Kai ya jinjina yana saka record ɗin a system dake gaban sa.Sai dai mamaki ya kashe shi daga zaune,sai dai ya shanye abun sa tun da su likitota ne sun saba ganin abun mamaki wanda ya fi wannan su haɗiye. " Kece Mahaifiyar sa kenan miss " Kai ta jinjina masa. " Sunan ki fa ".? " Aleeshat Jibril Farauta ". Ta bashi amsa.Cike da fara jin ta ta kura daga yanayin tambayoyin da yake mata gashi tana jin ɗan kallon da yake mata ƙasa ƙasa.Dan abun da ta tsana shine kallo a yanzu. Shima kan sa ya jinjina mata kafin ya ce " Wa yake da Ashthma a cikin a halin ku ko na mijin ki "? Wani irin bugu ƙirjin ta yayi mai mugun zafi dan numfashin ta ne yayi yunƙurin ɗaukewa na wuccin gadi da taimakon Allah da taimakon da ya bawa wanin sa dama ta samu dai daiton numfashin ta domin kuwa wannan tambaya da ta sako kalmar mijin ta,ta girgiza ta matuƙa wani irin tsoro ne da tashin hankali ya bayyana kan fuskar ta.Take idanun ta suka sauya kala. Asthma ta na na ta akan laɓɓan ta kafin ta ji wasu irin hawaye na neman wanke mata fuska domin kuwa abun da suka gani kenan a binciken farko da aka yi masa a makarantar su. Hawayen da take ƙoƙarin riƙewa ne ya silalo mata ƙoƙarin ciro hanky ɗin ta take yi a daga cikin jakar ta sai dai ta ji saukar wani Hanky a hannun ta mai taushi yana ta ƙamshi. Ɗan kallon sa tayi,shima ita yake kallo kafin ya jinjina mata kan sa. Bata yi masa musu ba Ganin handky ne lafiyayyen mai tsafta kamar sabo hakan ya sa ta fara goge hawayen. Sai da ta goge su tsaff sannan ta sauke numfashi. Dr Mahuta na kallon ta kafin ya yi gyaran murya sannan ya ce " Yana ɗauke da Asthma ne kun san da hakan ko kuwa sai yanzu " ? Kai ta jinjina masa da tabbatar masa da sun sani. " An taɓa bamu report na sa a school na su ". " A lokacin bamu yarda ba gaskiya ". " Duk da a lokuttan baya mun ga wasu daga cikin alamomin irin cutar a gare sa ". Dan bazata manta ba lokacin yana shakera ɗaya da wata takwas yayi ta samun matsalar ɗaukewar numfashi,tun ma dai yana jaririn sa da wannan matsalar ta fara ganin sa Numfashin sa samaa sama bata taɓa zaton zai rayu ba sai gashi Allah yayi ikon sa. Numfashi ta sauke a hankali tana kawar da tunanin baya dake da alaƙa da maganar ta su. Kai Dr Mahuta ya jinjina mata yana ɗauke kallon sa daga kan ta ganin yadda take ɓata kyakkyawar fuskar ta alamar kallon na damun ta.Murmushi ya saki kaɗan sannan ya cigaba da rubuce rubucen sa. Ɗan ɗagowa ya ƙara yi kafin ya ƙara maimaita tambayar da ta fi komai ɗaga mata hankali " Mahaifin sa ke da Asthma ko ke ,idan shine ya kamata ya zo nan ".?Wani irin faɗuwa ƙirjin ta ya ƙara yi cike da wata irin rauni ta ce " Mahaifin sa ne, Asthma itace silar mutuwar sa ".Ta kai ƙarshen zancen hawaye Masu zafi na Silalo mata.Wani irin Tausayin ta ne ya ƙara kama Dr Mahuta.Ita kuwa kuka ne ta ɓarke da shi a hankali na ƙaryar da ta yi wadda bata taɓa sanin cewa ta iya ta ba yanzu.Wadda rashin mafita ya saka ta furtawa bata re da ta shirya wa hakan ba.Zuba mata ido yayi kafin ya sauke numfashi ya ce " Ayyah Sorry may his soul rest in perfect peace ". Bata tanka masa ba sai kukan ta dake cigaba da fita a hankali cikin wani irin rauni da ƙuncin zuciya." Calm down Miss Aleeshat Jibril Farauta.,Ba wani abun tashin hankali bane Asad zai samu lafiya idan an ƙara dagewa da bin dokokin mu ". ✍️ A hayyyye inji ɗan Daudu😅💃💃💃💃Biki buduri yau dai cikin Yardan Uban giji mun samu kammala Book One cikin iyawar ubangiji.. Ƙanwa ta tace ɗan da ƙyar😏😏😅🤣🙏 Ina godiya gare ku masoya wannan labari na nesa da na kusa.Ƙaunar da kuke nuna mini da goyon bayan ku shine ƙwarin guiwata.Allah ya sakawa kowa da Alkhairii.Allah ya kuma haɗa mu a gidan aljanna baki ɗaya. Sai mun haɗe book two and three. Na amanata.🙏🙏🙏🙏 Kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke tafiya ce mai ban mamaki,al'ajabi,tausayi zazzafan soyayya mai cike da ƙauna,sadaukarwa,Zamba,cuta mai ban mamaki,zumunci mai abun burgewa. Lallai kar ki bari a yi babu ke 💃💃💃💃💃Takwaran Shatou dai ta ce " Ko da bashi sai na shiga paid group " 😂😂😂🤔Niko nace hmm😇😒😏😂 Jama'a kar in cika ku da surutu.🤗 Na san akwai tambayoyi masu yawa a bakin ku dan haka paid group ne mafitar ku.😎💁 INA LABARIN SHATOU,WAIT WAIT IDAN SHATOUN MU TA ZO BIRNI TA YAYA,TANA INA ?KO TA CIKA BURIN TA NA ZAMA YAR SANDA 🤭🤭 SHIN KO SHAMSU YA CI GALABA KAN MUGUN BURIN SA. WAYE MAHAIFIN ASAD ? INA LABARIN SU INNA NI..? WACECE ALEESHAT? INA LABARIN SU ABBU DA ƊAN SA ? INA LABARIN TA BAIWA MAI CAPACITY 😏😒😂? INA LABARIN MA'ISHAT,TA WARKE KO TANA NAN HAR YANZU CIKIN CIWON TA ? ME YAKE SANYA BILAL YAWAN DAMUWA ?Ina ma labarin sa ? WA KUKE GANIN YAKE YIWA SU ALEENA,SARINA MAƘARKASHIYA ? Me malam Hambali yake ɓoyewa ga Abba???? Na san akwai wasu tarin tambayoyi a cikin zukatan ku..🤎😇🤔 HMMM WANI ABU SAI A PAID GROUP.Da Naira #800 sai ki samo amsoshin ki 😇😇☺️😌🥰 ZAKU IYA SAKA KUƊIN KU TA 8069069746 OPAY FAIZA ALMUSTAPHA. SAI KU TURA SHAIDAR BIYAN KUDIN KU TA WANNAN NUMBER. 0808 750 4734 Mutanen NIGER(500 CFA) ZAKU IYA MAGANA DA WANNAN LAMBAR.08069069746 Dan biyan kuɗin ku,ko tura shaidar ku. Koda katin Airtel ne za,a karɓa.Mungode! Note:idan kika tura kuɗin ki ta vtu,ko kati kin yiwa Fa'eeh sadaka.Babu refunding.😜 And ba zamu jira kowa ba zamu cigaba da update.Idan kin shirya sai ki saka kuɗin ki. Masu neman complete Book yanzu muke typing. A taƙaice babu complete book. Idan mun gama zaku same sa complete book 1k✍️ Allah ya haɗa mu da Alkhairi.🙏 Fa'eehn ku ta amana,na godiya mai tarin yawa.Love You all my esteem fans 🥰🥰💕🌹 FA'EEH BG CE ✍️✍️✍️ SHARE FISABILILLAH. LIKE,REACT,VOTE AND COMMENT PLS🙏 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 39 of 39