Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ni ta ji tunda har ta ji danshi kamar kuma hawaye a kan fuskar ta. Kuka ta ƙara fashewa dashi. Wanda da ƙyar Inna ni ta rarrrashe ta tayi shiru.. " Je ki kiyi Sallahn ki in sha ALLAH ba zaki mutu ba sai kin haifa mini jikoki ". " Ba zaki tafi ki barni ba cikin wannan duniya mai abun tsoro shatou ina ji a jiki na kece haske na,da zai yaye mini duhun da nake ciki ke ce zaki kai mu ga hasken da zamu yi farin ciki a tare ".Ta yi wannan furucin na biyu a cikin sauti mara fita wanda shatou bata ji ba. Shiru shatou ta yi tana sauke ajiyar zuciya tana jin wani sanyi a ranta. " Ki cigaba da na na ta Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un kinji wannan abun da kike ji zai daina babu komai in Sha ALLAH Alkhairi ne,bana son wannan yawan shiru shirun yanzu idan kin gama Sallah kije ki same su wajen farautar " Aiko da sauri shatou ta washe baki tana furta " Dagaske Inna ni "? Kai ta gyaɗa mata itama cikin Murmushi mai haɗe da wani irin rauni da mugun tausayi. Aiko cike da ɗan kuzarin da shatou ta samu ta yi alwallah sannan tana gama sallah ta yi addu'a Sannan ta fice dan dama tace zata je Inna ni ta hana saboda bata son tana Guje guje kuma ta san muddin suka fita sai ta yi gashi dai ta fara zama yar budurwa duk da ƙirjin na nan shafe har yanzu sai tsawo da take ɗan yi. Da kyawun ta dake ta ƙara bayyana fili makerin kyau na ta aikin sa. Ficewa tayi daga gidan bayan ta yiwa Inna ni sai ta dawo,yanzu bata ma yin fargaban fita saboda ta san Iro na kare ta dan duk inda ya san Shamsu yake yana bibiya.Da ya ji labarin zai je wajen ta sai ya tare shi su yi ta rafka artabu tsakanin su. Kuma tun daga wannan rana sai Shatou ta saki jikin ta,saboda yadda maganar Inna ni ta mata wankin Damuwar da take ji a jikin ta da wani irin tsoro da ke shigar ta. Duk da wani gefe akwai ɗan tsoro sai dai mara yawa. " Wallahi ni bana jin tsoron ka,dan haka baka isa ka kashe ni ba,sai lokaci na yayi ". Kallon ta yayi da kyau ganin yadda ta riƙe ƙugu.Babu tsoro ko ɗar akan fuskar ta ko da chan tana shanye abun ta bai ta ɓa ganin Zallar tsoron sa ba a idanun ta Wata muguwar dariya ya saki kafin ya ce " Ke ni zaki saka a tozar ta gaban abokai na ". " Wallahi sai na illata ki,sai na cusa Miki baƙin ciki ". Dai dai nan Iro ya bayyana yana furta " Allah kaɗai ah haka ". Kallon sa Shamsu yayi kafin ya ja tsaki yana jefa masa muguwar Harara. Cikin rashin damuwa da son ƙara ƙure Shamsu ya ce. " Shatou na ina zaki je ne " Baki ta fara turawa gaba jin sunan da ya kira ta da shi da ta mugun tsana wai shatou na.Mugun jin zafin sunan take yi bata da yadda zata yi ne da ta hana shi kiran sunan ta ma gaba ɗaya. " Wajen Baffa na zanje farauta ". Ta bashi amsa. " To tafi,kuma ki kula da hanya ". Ya furta mata yana sakin murmushi yana ƙara washe bakin sa ganin ta gyaɗa masa kai kamar irin yana da mugun iko da ita. Hmmm.😏 IRO yan love manya.LOl🤪 Bari dai nayi shiri kar shatou's fan su wullo mini daƙuwa.😂🤗 ...Bai bar wajen ba sai da ya ga shatou ta ɓace ma ganin su haka ma Yaga hanyar da Shamsu ya bi wanda ya cika ya batse. A ɓangaren shatou kuwa take ta saki komai da ya faru ta cigaba da falfala gudun ta har ta isa wajen su Baffa na aikuwa take ta ƙarasa wartsakewa tana ta tsalle tsalle harda gasa suka yi da Bibu wanda ya cinye ta kasancewar kwana biyu ya daina zuwa Farauta,aiko tana ta matsar hawaye Baffa na kuwa murmushi kawai yake yi yana kallon su Bibu kuwa dariya yake ta mata. Daga ƙarshe itama nan ta saki jiki har suka yaɗa zango suka gasa wani ƙaton Zomo na daji su ka ci nan sannan suka yi wa Inna ni guzuri suka yo gida. ***Yau an tashi da shirye shirye, su mai gari sai kai kawo ake yi da su Baffa na a fadan mai gari ta shirye shiryen zuwan su Abbu domin ƙaddamar da ayyukan cike da farin ciki domin kuwa abun fari ciki ne Babba a gare su da cigaba a ƙauyen su,kowa ka kalli fuskar sa zaka gan ta sake saboda farin cikin samun wadattun ruwa domin mafi ya wan su chan suke yini suna kallon wajen suna jin daɗi. A ɓangaren Abbu kuwa suma sun shirya tsaf dan zuwa wajen ƙaddamar da ayyukan sai dai duk yadda ya so suje tare da Mahaj ya ƙi hasalima Bacci yake sha kuma Abbu baya son ta dashi dan haka ya cigaba da shirin sa suje tare da Mubarak. Suna gama shirya wa suka fice kowannen su cikin shiga mai kyau babu ma kamar Abbu yadda kuka san wani sabon ango. A ɓangaren MAHAJ kuwa bayan fitar su daga kwancen da yake ido rufe kamar mai bacci ya miƙe yana sauke numfashi da a jiyar zuciya. Ƙaramin tsaki ya ja wanda ya tsaya iya kan laɓɓan sa kafin ya miƙe ya zare kayan jikin sa ya ɗaura towel ya shige toilet bai jima ba ya fito yana tsane jikin tsaf ya shiryawar sa cikin wata irin shiga ta alfarma yau kayan mu na Hausa ya saka Black jampa da takalmi masu kyau da tsada white color,sannan ya ɗaura agogon sa mai kyau ya fesa turare mai ƙamshi sannan ya kwashi wayoyin sa ya fito. Tun da ya doso ƙamshin sa ya mamaye ko ina har ya fice ya dawo ya zari wani a bu a wata yar kwalba sannan ya shige sashen Aiyah. Zaune ya same ta ta miƙe ƙafafun ta kan doguwar kujeran ta tana kallon tashar labarai. Sai wata lafiyayyen madara dake kusa da ita a cikin wani cup na tangaran mai kyau. Haɗe fuska ta yi dan gaisuwar ma ciki ciki aka amsa mishi ita.Duk da dama shi take zaman jira yau bai shiga gai da ita ba jiya, tana jiran ya cika na uku ta musu tass shi da uban shi dan ko chan baya kafin a zumi sai da ta zazzaga ma MAHAJ ta yaɓa ma MAHAJ mugayen kalamai mara sa amfani,wasu ma ita kan ta bata san amfanin faɗar su ba. Daga gaisuwar nan kuwa bata ƙara ce masa komai ba haka shima. Miƙewa yayi ya na mata sallama. " Ga madara nan ko zaka sha ". Ta furta masa ba ta re da ta kalle sa ba. Ɗan kallon madaran yayi wadda yake ta satar kallo tun shigowar sa saboda ya san tana da madara mai kyau da take sa ake nemo mata,yana son ta sosai lokacin da yana ƙarami har shan ta yake yi a sace bata sani ba. *WAIWAYE,MU KOMA FARKON LABARI* Daji ne dake cikin garin suleja wanda ake kira ƙare kukan ka. Babu abun da ke tashi sai kukan tsuntsaye kala kala sai kuma yana yin yadda itatuwa ke kaɗawa suna bada iskan hunturu mai daɗi kasancewar lokacin sanyin da ake ciki. Matashiyar budurwa ce ke tafiya cikin dajin a hankali da wani irin tulelen ciki a jikin ta da alama cikin zai kai kamar wata shida haka ko bakwai.Hawaye ne jage jage a kan fuskar ta ga idanun ta sunyi wani irin jaaa tafiya ce ta ke yi wadda bata san inda take jefa ƙafafun ta ba.Yadda take tafiyar kai kan ka zaka shaida a gajiye take kuma a galabaice.Kukan karnuka da taji a bayan ta ne hakan ya sa ta fara sauri tana ƙarawa tafiyar ta sauri kafin ta haɗa da gudu domin kuwa ko ba,a faɗa mata ba ta san ko suwaye kuma suka cimma ta rayuwar ta na cikin galalari domin kuwa kisa ne mai zafi zasu aiwatar akan ta domin yadda suka yi neman ta a chan nan ma hakan ne zai kasance.Cikin wani irin gudu haka take kutsa ƙafafun ta cikin ramukkan dake gaban ta da tulelen cikin na ta ga wata irin Hajijiya da ke kama ta wadda ba ta san mafitar ta ba.Sai dai tana fatan da irin wannan yanayi gwara mutuwar ta domin kuwa wata irin azaba ce ke ta so mata na gudun da take yi dan gudu ne bana wasa ba.Tana kawowa dai dai bakin wani ƙaton rame mai kama da kogo ta faɗa nan domin tsira da rayuwar ta da abinda ke cikin na ta tana sauke haki kafin kuma kan ta ya buge da wani irin ice da bata lura dashi ba A cikin kogon wanda hakan ya sanya ta fara ganin dishi dishi kafin kuma Numfashin ta ya ɗauke ɗiif. Wani irin zabura tayi ta miƙe daga kan haɗaɗɗen royal bed da take kwance Numfashin ta na wani irin sama yana ƙasa kamar zai tafi da rayuwar ta ga zuciyar ta dake wani irin bugawa kamar zata faso ƙirjin ta lokaci guda ta haɗa wani irin zufa. Sunan ta da aka kira ne cikin ɗan tsoro da tausayi yasa ta fara samun natsuwa tana lumshe lulu eyes ɗin ta da suka tara ruwa kamar na hawaye sai dai ba su kai ga saukowa ba. "ALEESHAT ''!!! Zubawa matar idanun ta tayi da taƙara kiran sunan ta,tana ƙoƙarin haɗiye hawayen da suka cika mata ido sai dai abun ya ci tura domin kuwa a hankali ta ɓarke da wani irin kuka mai tsumaa zuciyar mai saurare.Dafa ta Babbar matar tayi wadda ke sanye da shiga ta ado ta alfarma ita ma idanun ta sun sauya jikin ta yayi sanyi alamar damuwa.✍️ Rikicin cim kenan yau kuma ina muka samo Alishat.🤔? Shin ya kuke jin tasirin maganganun Shamsu ? Wace irin manakisa yake shiryawa Shatou? Lallai zamu tsunduma filin watse Gara ku gyara zama.💃💃💃💃💃💃💃💃 Zaku fahimci komai,a hankali zamu war are komai na san zaku yi mamakin yadda aka yi muka koma farko,haka tafiyar take haka labarin ya zo,muna ni da ku. Fatan zaku jure mu cigaba da wannan gwagwarmaya a tare.Allah ya biya kowa da gidan aljanna.🤲🤲🤲 Ba zan gaji da faɗa muku ba mun kusa kammala Book One,two and three paid ne.Ongoing 800 Complete book idan mun gama 1k Masu buƙata Ga numban da zaku tuntuɓa *08069059746* Ko ki saka kuɗin direct to my opay 8069059746 Sai ki tura payment receipt naki ta Wannan ñumban. *+234 808 750 4734* Note : idan kin san ba zaki iya jurewa karatun shafi shafi ba Ban ce ki saka kuɗin ki ba,kar ki zo kina matsa mini da yaushe za,a gama ku raba mini hankali biyu.Na kasa concentrating akan gyara muku labarin na yi ta sauri mu kashe tafiyar a zo a yi ta zagina.Lol✍️ *FA'EEH BG CE✍️* SHARE FISABILILLAH.... REACT AND COMMENT PLS 🙏🥰💕 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣8️⃣↔️4️⃣9️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Second to the last free page.* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ # Alishat # Asad # Mamma # Alhaji Mamman # Fa'eeh BG # ✨✨✨ Rarrashin ta matar ke yi cike da tausayin ta. Sai da tayi shiru ne sannan ta sake ta ta juya ta ɗauko mata ruwa mai sanyi a cikin wani ƙaramin fridge dake a cikin bedroom ɗin ta ba buɗe mata. Ruwan ta miƙa mata babu musu kuwa ta kafa kan ta a hankali ta sha dan su ta fi buƙata a yanzu,a hankali ta sauke a jiyar zuciya da numfashi a tare tana sauke goran a bakin ta jin sun ratsa ta ta ko ina. Lumshe idanun ta tayi tana buɗe su. Yaron da ke gaban ta da ya dunƙule waje ɗaya ta kalla wanda a ƙalla zai kusa kai shekara biyar a duniya. Baccin sa yake sha hankali kwance kusa da ita dan ajikin ta ma rabin jikin sa yake. Itama matar shi ta kalla kafin ta ce " Sannu mafarkin ne ? ". Kai Budurwar da aka kira Alishat ta ɗaga kafin ta ce cikin natsatsiyar Muryar ta mai sanyi da taushi " Mamma me ya sa wannan mumman tarihi ya kasa barin idanu na da tunani na,me ya sa zan dinga mafarkin sa haka? ". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta yi shiru tana sauke numfashi jin wasu Sahabban hawaye na neman sauko wa tare da wani sabon kukan da ke bayyanar da ƙunar da zuciyar ta ke yi. " Ki cigaba da Addu'a In Sha ALLAH daga wannan ba zaki ƙara yin sa ba da yardan Ubangiji,kuma hakan ba komai bane sai yadda tsoron yanayin ya shige ki,kuma ki yi ƙoƙari ki daina tunawa kar ki haifar wa kan ki wani sabon ciwo kin san dai yadda kike fama idan ciwon ya tashi ". Matar da aka kira Mamma tayi furucin. Ajiyar zuciya Alishat ta sauke kafin ta ɗan shafa kan yaron da ya fara motsawa kasancewar lokacin sallar Asuba yayi ta zo ta tada yaron su wuce masallaci shida mai gidan na ta.Alhaji Sama'ila da suke kira Abbi wanda kuwa Ba kowa ta ya raɗa masa shi ba sai Wannan yaron. " Asad ! Asad ! " A hankali kuwa ya fara washe manyan idanun sa dake cike da bacci kasancewar jiya bai kwanta da wuri ba sai da ya yi ta rigimar da ya saba wadda har yanzu sun kasa samo masa mafitar ta.Dan haka wasu lokutan tare suke shan kukan su ita dashi abun tausayi dan ita kan ta da take mahaifiyar sa ba zata iya yi masa abun da ya ke nema ba hasalima ba ta san inda ta dosa a abin da yake buƙata. Zuba wa Alishat ido yayi yana kallon ta wadda ko makaho ya shafa ya san ɗan ta ne amma ba zaka taɓa cewa ita ce ta haife sa ba. Kiran sunan sa da ta ƙara yi ne cikin murya mai taushi ya sanya shi ɗan Lumshe idanun sa masu cike da bacci kafin ya ɓata fuskar sa ganin tana Murmushi tana nuna masa Mamma dake tsaye tana murmushi itama tana kallon sa. Da sauri ko ya ja tattausan duvet dake kan gadon ya rufe fuskar sa. Aiko da sauri itama ta riƙe duvet ɗin tana Murmushi mai bayyanar da side dimples ɗin ta. Jan sa ta yi baya tana furta wa a hankali cike da Rarrashi " Come on my baby wake up pls ". " Ummieeey ". Ya furta kamar ya fashe da kuka ɗaga shi tayi tana Murmushi. Mamma ce ta ce " Asad Abbi na jiran ka fa kaga an fara Salloli ". " Mamma Basshi ". Ya bata amsa kamar zai saki kuka. Yar dariya tayi ganin ya tsayu kan ƙafafun sa da taimakon mahaifiyar sa. Alishat ce ta furta " Mamma ce Abbi ya tafi kawai kar ya makarar da shi ". Murmushi Mamma tayi kafin ta ce " Ɗan nema yau Abbi fushi zai yi da kai ". Ta fice tana Murmushi. Shiko Asad jikin Alishat ya shige daga tsayen da suke. Hannun sa ta riƙa tana Murmushi sannan suka shige toilet guntun wandon dake jikin sa kawai ta cire masa ta masa wanka da brush sannan suka ɗaura Alwallah tare suka fito bayan ta ɗaura masa towel karami. Koda suka fito short kawai ta saka masa na yara mai kyau da tsada sannan ta saka masa jallabiya mai kyau itama ta saka ta ta a bayan akan rigar ta ta barci mai tsawo da take da ɗan buɗaɗɗen gaba wanda har albarkatun ƙirjin ta da suke a tsaye chik suka bayyana.Ɗan kwallin ta yana akan ta kafin suka kabarta Sallah a tare a natse daga ita har shi suka yi sallar sannan suka sallame,a tare suka yi addu,a gwanin burgewa. Karatun Alqur'ani ta fara bita masa yana Amsawa bayan sun yi azkar a tare na safe. Sai da suka karanta kusan page biyu sannan suka rufe qur'ani. Dai dai lokacin kuma Momma ta shigo ɗakin da sallama ɗauke a bakin ta murmushi kawai ta saki kafin ta ce " Allah ya sa yau an muna Addu'a ".? Ɗan guntun murmushi Asad ya saki kasancewar ya san da shi ta ke kafin ya ce " Na Miki kuma har da Dady na ma ". Ya kai ƙarshen zancen yana washe bakin sa da yake ɗauke da yan tsirarun haƙoran sa da suke fara re sol kasancewar yana fira. Zuba masa ido dukkanin su suka yi babu ma kamar Alishat ƙirjin ta da ya buga ne ya sa ta haɗiye wani abu mai nauyi a zuciyar ta kafin ta sauke numfashi ba tace komai ba sai ma Wayar ta da ta ɗauka a gefen bedside drower da ta sanya Chaji da dare. Zama tayi bakin gadon tana kunna wayar ta ba tare da ta ƙara kallon gefen da Asad yake tsaye ba dan a duk lokacin da zai yi maganar mahaifin sa jikin ta mutuwa yake yi ta kan ji wata irin kunyar sa kunya mafi hana motsi domin kuwa duk duniya yanzu ba ta da kamar sa shine kawai abun da take kallawa tayi farin ciki sai kuma su Mamma da suka zame mata bango.Domin bata san ainahin abun da zata ce masa a kan mahaifin sa ba. Mamma kuwa numfashi ta sauke kafin ta saki murmushi ta ce " Me ka roƙa mini " ? Ta tambaya tana kallon kyakkyawar fuskar sa dake shar da ita. " Na ce Allah ya sa kar ki tsufa " Dariya Mamma tayi kafin ta ce " Yau wannan na samu kuma, toh nagde,Amma fa Asad tsufan nan sai ya zo wa Mamma ". Shi dai murmushi kawai yake yi yana kallon Mamma dan shi yaro ne da bai cika hayaniya ba. Ummiee yau ba zan je school ba ko "? Ya furta yana mayar da kallon sa ga Alishat. Ɗan ɗagowa tayi a hankali ta Kalle sa da idanun ta da suka ɗan sauya kafin ta ɗan yi luu da su kamar zata rufe sannan ta buɗe ta girgiza masa kan ta tana sakin guntun murmushi. Ɓata fuskar sa yayi hakan ya sa itama ta ɓata Tata fuskar kafin ta ce " Asad yau fa akwai wasa ". Cike da murna Asad yayi tsalle yana furta " yeeeh zan yi wasa da su Chuchu ". Dukkanin su dariya suka yi mai Sauti. Sai lokacin ne kuma Alishat ta kalli Mamma cike da murmushi ta ce " Mamma good morning ". " Wannan yaron naki Mamma ya sa na manta bamu gaisa ba ". Dariya Mamma tayi tana riƙo hannun sa ta ce " Shi ɗin ma yau bai gayar da Mamman sa ba ". Murmushi Alishat ta saki a hankali tana kallon su musamman Asad dake ta miƙa ma Mamma hannu ta ɗauke sa. Yana furta " Mamma Good morning ". Cikin yar maganar sa ta yara da har yanzu bakin sa magana bata wani zauna ba. Ɗaga shi Mamma tayi tana Murmushi kafin ta ce " Fine,good boy, hope ka yiwa kan ka Addu'a kai ma ".? Kai ya jinjina mata kafin ya ce " eh kuma har da Dady na na yiwa Addu'a ". Kallon sa Mamma tayi tana Murmushi kafin tace " good,Allah yayi maka albarka ". " Amin " Ya amsa yana jan jelar jallabiyar sa. Ficewa da shi Mamma tayi zuwa na sa ɗakin dan shirya sa kamar koda yaushe. Har suka fita yana ɗagawa Ummieen sa hannu yana murmushi sai kace wanda zai je wani wajen.Itama murmushi kawai ta Bisu da shi kafin ta ajiye wayar ta kwanta kan gadon tana sauke ajiyar zuciya ta tsirawa pop dake shimfiɗe a rufin ɗakin. Wayar ta ce da ta ɗan yi ƙarar shigowar saƙo ne hakan ya sa ta ɗan kalli inda ta jefa wayar kusa da ita kafin ta janyo ta a hankali. Ƙaramin tsaki ta ja tana wurgar da wayar kafin ta rufe idanun ta tayi shiru kamar mai yin Bacci. Miƙewa tayi zaune kamar an ce mata ta shi zaune. Wayar ta janyo ta duba notification na saƙuna da suke kan shigowa wayan rutu tu da su musamman na new numbers. Wani saƙo ne da ya shigo yanzu ta zubawa ido '' Yau ina son haɗuwa dake Dan Allah, wallahi ina son ɗanɗana zumar ki,ko nawa ne zan zube Miki,zan sakar Miki Naira kinji tauraruwa ta" Sai daga ƙasa aka rubuta Alhaji Mamman. Wani irin murmushi ta saki kasancewar ya fi sati biyu yana bibiyar ta kuma har yanzu ma ta kasa yin saving number sa,A hankali ta shiga what'sapp ɗin ta ƙara kalla saƙon da kyau.Tana jan Numfashi. Fitowa cikin chat ɗin tayi inda ta fara bin sauran saƙunan da suke kamanceceniya da wanda ta karanta yanzu. Sai da ta gama karance su tsaf sannan ta a jiye wayar gefe. Alhaji Mamman kuwa dake zaune ya saka tumbin sa gaba a ƙaton bedroom ɗin sa ne yana jiran reply na ta ya ja ƙaramin tsaki yana fatan ganin wani alama bayan na duba saƙon da ta yi ma sa sai dai har ya ci zaman sa bakin gadon har ya miƙe ya fara Zarya babu alamar zata bashi amsa hakan kuma Bai dame sa ba domin kuwa ya ji labarin ta tsaf da izzar da take da ita da jan ajin ta dan bata hurɗa ma da ƙananan mutane sai manyan Alhazzawa dan ko yanzu labarin ta a bakin wani abokin sa ne minister ne na security. Kuma tun da ya ga ƙirar ta shekaranjiya ya ji gaba ɗaya ya kasa zama kurumm dan haka yayi duk yadda zai yi har ya samu ñumban ta da bayanan ta shi ji yake ma zai iya auren ta idan ta bashi dama tun da Ance bazawara ce mai lasisi ba dole sai ta bariki ba. Wayar ta sa yayi wurgi da ita kafin ya miƙe ya faɗa toilet har ya saka wa jikin sa kumfa ya fito da sauri jin motsi a ɗakin kuma ya san bata wuce matar sa ce ba aiko da kumfa da komai haka ya fito yana bin bango tare da kiran sunan matar ta sa yana furta bani wayata kasancewar wayar ta shi bata da password a kan ta dan haka ya yi azamar fitowa gudun tonon asirin sa. Sake da baki matar ta sa ke kallon sa data zo sanar masa da lokacin breakfast yayi ta zata bai ma tashi ba. Salati ta rafka kafin ta kalli wayar dai dai lokacin shima ya sanya wata Babbar rigar sa pitch color ya rage kumfar. Wayar ya janyo jikin sa na rawa,sannan ya juya hanyar toilet jikin sa na ra wa. Hakan kawai jikin ta yake nuna mata akwai matsala mijin na ta bai da gaskiya. Dan haka ga zuba masa ƙofar da ya bi da kallo. Ƙyafci ta yi kafin ta ce " Alhaji breakfast ya zama ready ". Daga chan ya amsa mata da ya ji. Hakan ya sa ta ficewar ta Alhaji Mamman dake tsaye bakin ƙofar toilet ne ya buɗe ƙofar ya leƙo ganin Babu kowa a cikin hakan ya sa ya fito da sanɗa ya ajiye wayar ya koma. Aiko yana shigewa ta fito babu wahala sai gata cikin saƙonnin sa na what's app. Aiko ƙirjin sai da yayi muguwar daka kamar zai fito daka ƙirjin ta sunan take ta nanata wa. A bakin ta. " Leesha " Inda ta taɓa jin sunan take son tunawa sai dai ta kasa dan haka jin motsin alamar fitowa zai yi hakan ya sa ta yi sauri ta ajiye ta fice cikin sanɗa tana nazarin sunan da ya tsaya mata a ƙirji. Kitchen zata koma amma ta kasa dan haka bedroom ɗin ta,ta koma ta ɗauki wayar ta wata number ta yi dialing ringing ɗaya biyu aka ɗaga cike da azama bayan sun gai sa ta ce " Anty Ruƙy wai ni ko kamar na taɓa jin kuna labarin wata yarinya yar bariki haka na ga sunan a wayar Alhaji da chat da yayi mata,shine nake son tabbatarwa idan ita ce ". Daga chan ɓangaren ne aka furta " Leesha kike magana kenan "? Wani irin faɗuwa gaban ta ya cikin mazarin baki ta lailayo ashar ta sauke kafin " tace ita fa,ita nake nufi ". Murmushi ta wanchan ɓangaren a kayi kafin ta ce " Makiyya ki raba kan ki da yarinyar nan dan bomm ce ina faɗa Miki zata iya rabaki da Alhaji Mamman wallahi rabuwa ta har abada,ki bi komai a hankali a rabu lafiya,duk yadda kike tunanin yarinyar nan ta wuce haka,ita nata jawarcin mai lasisi take da barikin ta,dan haka ki bar komai hannu na". " Wai ni me take dashi haka suke ta tura kan su gare ta haba wallahi dole mu ɗauki mataki ". Hajiya Makiyya ta yi furucin a hasale. Ta ɓangaren Anty ruƙy kuwa numfashi ta sauke

Chapter 37 of 39