Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yanayin ba tun bayan Samun lafiyar Shatou ɗin da ita kan ta na doguwar jinyar da tayi. Kuka ne Shatou take yi wanda ke fitowa daga ƙasan zuciyar ta jikin ta har girgiza yake yi gashi an kasa samun mai rarrashin ta a haka Bibu ya same su kowa yayi jigumm ga shatou na ta darzan kuka. " Adda shatou "! " Me yake damun ki,?Baki da lafiya ne,ina yake Miki ciwo " ? Wayen nan sune tambayoyin da yake ta jerawa Shatou bayan shigowar ta sa hankalin sa ta she ya matsa kusa da ita kamar zai fashe da kuka shima idanun sa har sun cika da hawaye na Tausayin yar uwar ta sa. A jiyar zuciya dukkanin su suka sauke ganin tayi shiru bayan zaman Bibu kusa da ita.Dan kuwa shima idanun ta zuba masa har sai da ya ɗan tsorata kafin ta janye su kan shi hannunn sa ta riƙo " kafin a hankali ta ƙyafato shi tana nuna masa ya karo kunnen sa kusa da bakin ta dan da alama shaƙaƙƙiyar murya ga re ta ko gare shi Dan har yanzu Inna ni bata san wane jinsin bane na mace ko namiji amma tafi masu kallon mace. Karo kunnen na sa kuwa yayi kafin a hankali ya tsinkayo yar ƙaramar Muryan ta da bai fita sosai ciki ciki take sai ma kana da lafiyayyen kunne zaka ji ta furta. " Ka yi haƙuri ba da gangan na dake ka ba,kuskure ne,Kar ka sanar wa da Baffa na abunda nace amma kana iya faɗawa Inna ni,idan kuwa ya matsa yana son ji ka faɗa masa ". Hawaye ne suka cika idon Bibu a take kai ya girgiza mata share hawayen sa yayi kafin ya yi kokarin riko ta, ta tashi zaune sai dai kamar dutse haka ya ji dan haka ya sake ta yana sauke a jiyar zuciya fuskar sa cike da damuwa dan duk shi ganin yake yi duk shiru shirun da ta koma abun da ta masa ne ke damun ta. Idanun ta ta mayar kan Baffa na kafin a hankali ta masa wata alama kamar ta kurame.Sak kuwa ya fahimta alamar zasu tafi ne suke masa dan haka bai ce komai ba.Kan Inna ni suka juya kafin suka ƙara kallon ta sannan ta fara rufe idanun ta bayan ta sakar wa Inna ni murmushi mai nuna tabbacin akwai damuwa sai dai tunda ta fahimci Inna ni bata son sanin komai ne ne gaban Baffa na sai ta haɗiye komai shine dalilin sakin kukan na baƙin cikin duk da ta san ko faɗawa Inna ni tayi babu abinda zata iya,amma ta san addu'ar ta kamar dafi ce akan abinda ta zo dashi. A haka bacci ya kwashe Shatou jikin ta ya saki sai numfashi da ta fara saukewa a hankali. Baffa na ganin haka ya sa ya sauke ajiyar zuciya kan shi kuwa da yake har yanzu a kulle ya dafe kafin ya miƙe ya fice daga gidan jin kiran Sallah la,asar da ya karaɗe ƙauyen bayan ya sanar da fitar ta sa. Inna ni ma numfashi ta sauke da ajiyar zuciya mai nauyi kamar wadda ta haɗiyi zuciya damuwar ta na sake dawowa sabuwa Badan komai ba sai dan rasa jin abinda suka zo da shi a yau ɗin wanda ta tabbatar babu lafiya tunda ga yanayin Aljannun na Shatou.A haka ta gyara mata kwanciya ta miƙe tare da ɗaga Bibu tana cewa. " Muje ka watsa ruwa kayi Sallah kaci abinci ka kwaso yunwa,Addan ka ta samu bacci ". Babu musu kuwa ya miƙe yana share hawaye. " Baccin ta samu fa kuma zata tashi kaji ". Inna ni ta furta jikin ta a sanyaye ganin yadda Bibun ya kasa sakewa. Kai Bibu ya ɗaga kafin ya shige ɗan ɗakin sa ya cire kayan sa ya canza da wasu sannan yayi alwallah ya wuce masallaci yana dawowa sannan ya shiga ya watsa ruwa yana gama shirya wa ya zauna cin abinci kuma har lokacin Shatou bata farka ba yana yi yana kallon ta har ya gama cin abincin sa. Baffa na kuwa wani uzuri ya hana sa dawowa gidan bai dawo ba sai Gab da magriba kuma yana shigowa ana kiran Sallah dan haka kai tsaye ya yi alwallah ya wuce masallaci tare da Bibu da ya ke ta yiwa Shatou Fifita tana shan baccin ta hankali kwance. Dai dai fitar su kuma Shatou ta fara motsi alamar tashi a hankali kuwa ta fara ware manyan idanun ta da suka ƙara girma da haske tar kuwa ta ware su akan Inna ni dake zaune akan yar zuƙunno ta buga ta gumi tana kallon ta. Ya mutsa kyakkyawar fuskar ta tayi da ta ƙara yin fayau farin ta ya ƙara bayyana sai shinning take yi kamar yadda kuka san fatar nan ta yan Korea mai walƙiya kamar suna wanka da mai na madara. Murmushi ta sakar ma Inna ni kafin ta miƙe zaune cike da kuzarin ta,tana jan doguwar miƙa tare da Nanata addu,ar tashi daga bacci. Inna ni ma Murmushin ta sakar mata tana jan ajiyar zuciya tare da riƙo hannun ta ɗaya.Bata ce mata komai ba sai da ta dangane ta da ɗakin ta,da taimakon ta shatou ta cire kayan jikin ta Sannan ta ɗaura zanen da take wanka dashi. Fitowa Inna ni tayi ta haɗa mata ruwan wanka ta kai mata makewayi. Ɗan leƙawa tayi bayan ta kai mata ruwan ta ce. " Kije ki watsa ruwa na kai Miki ki samu ki yi Sallolin ki,dan ban samu ta da ke daga bacci ba ". " Touh ". Shatou ta furta a hankali babu musu kafin ta fito daga ɗakin,makewayin ta shige ba tare da ta ce wa Inna ni komai ba da ke alwallah. Sallah ta kabbarta bayan gama alwallah. Koda Shatou ta fito Inna ni na Sallah bata ko gama magriba ba. Ruwan Alwallan da ta zuba mata a wata ƙaramar buta ta ɗauka kafin ta yi alwallah sannan ta shige ɗakin na ta.Bata jima ba ta fito ta sanye da wata yar kodadddiyar riga da take mugun so ta roban gwanjo da Baffa na ya taɓa siyo mata da yayi tafiya.Dan rigar da jan ta take yi amma yanzu ta ɗan shige mata dan haka take jan ta tun Inna ni na dariya idan ta sako har ta daina. Kusa da Inna ni ta tsaya ta sanya hijabin ta ta kabbara Sallah lokacin Inna ni ta sallame magriba zata fara nafilan bayan magriba. Magriba ta fara yi kafin ta ranka la,asar A tsanake tayi Sallolin ta koda ta gama su Baffa na sun shigo suna zaune gefe shida Bibu akan yar tabarmar kaba sun zuba mata ido babu ma kamar Baffa na sai dai fuskokin su cike suke da annuri ganin ta zaune harda sallah.Samun kan ta tayi da sakar musu murmushi haka suma. " Ya jikin ki Adda shatou " ? Bibu yayi maganar yana kallon ta. Kai ta girgiza masa kafin ta ce a hankali " Lafiya ta lau fa barci ne kawai ya kashe n,kuma Inna ni bata tashe Ni Sallah ba,gashi sai dai nayi ranko ".Tayi zancen kamar zata fashe wa da kuka dan bata son fashin sallah ko kaɗan ta san zunubin da mutun ke samu wasu malammai ma sunce ba,a karɓanta.Haka malamin su ya sanar musu dan haka take jin tsoron fashin sallah wanda zai saka ta tarikussalah ba tare da dalili mai ƙarfi ba.Na daga cuta,ma,ana rashin lafiya ko tafiya.d.s. Shiru gurin yayi Baffa na kuwa ajiyar zuciya ya sauke domin kuwa abun da yake zargi ne ya ga ya tabbata dan har yanzu ko kwanto yake yi. Inna ni kuwa ba tace komai ba itama sai cigaba da jan charbin ta da tayi tana sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. Shatou kuwa daga gama maganar Addu'oin ta, ta fara yau babu wanda ya ji abinda take cewa dan cikin zuciyar ta take yin abarta. Yau Baffa na sai ya ga kamar ta ƙara hankali dan haka ya ke satar kallon ta kafin a hankali murmushi ya ɗan suɓuce masa na gefen baki. Bibu shiru yayi yana mamakin ta kafin kuma ya miƙe ya ɗauko Kitabul azkar na su bayan Baffa na ya bashi umurni sannan ya dawo ya zauna. Baffa na ya cigaba da bita masa haka Shatou jikin ta har rawa yake yi ta zo ayi karatun da ita aiko tana gamawa ta dawo kusa da Baffa na bayan ta gayar da Inna ni da ta amsa mata fuska sake. Haka shima Baffa na tayi masa ina yini duk mamaki suka yi dan ba kasafai take wannan gaisuwar ba Ƙiriniyar ta bata barin ta gaisuwar maraice ta safe ce kawai wannan babu fashi dan Bibu yafi ta ƙoƙarin musu ina yini bayan Sallahn magriba. Daga shi har Inna ni murmushi suka yi Acikin zukatan su dan mamakin ta sai dai sun shanye abun su ba zaka taɓa ganewa ba. A haka Baffa na ya cigaba da bita musu azkar ɗin suna sakawa akan su har suka yi wanda ya wadata kowannen su ya bita da kan sa zuwa lokacin kuwa an kira sallahn Ishai.Baffa na da Bibu masallaci suka wuce su kuwa suka tada Sallahn su anan take. Koda suka gama Sallah Shatou ka sa haƙuri tayi dan haka ta buɗe bakin ta tace " Inna ni wai banda lafiya ne,naji Bibu nace wa wai Ya jiki na,kuma lafiya ta ƙalau bacci kawai na sha ". " Sai kuma kema ɗazu da na tashi naga kamar kinyi kuka wani abu ya shigar Miki ido ne " ? Haka ta jerawa Inna ni tambayoyin wadda ke jan charbin ta hankali kwance. Ɗan kallon ta Inna ni tayi kamar bazata tanka mata ba sai chan ta ce " wai dukan da malam Abu ya Miki ne ya ke Miki ya jiki kan sa,Nima kuma ɗazu wani abun ya faɗa Mini ido kamar kin sani da ƙyar ya fita ido na ". Kai shatou ta gyaɗa cikin yarda ta ce " Sannu " cike da tausayin mahaifiyar ta ta. kafin kuma ta ƙara furta " Inna ni Zanje Dandali yanzu ". " Da wuri haka ". Inna ni ta furta tana jin babu daɗi dan bata son fitar ta gaba ɗaya kwanan nan an ma yi sa,a yau ta tambaya da sai dai a neme ta a rasa ta ja Bibu sun fice. " Ehh wasan gala gala zamu yi,kuma yau bana son Rakiyar Bibu yayi baccin sa ". Kai Inna ni ta jinjina tana sauke ajiyar zuciya kafin ta ce. " Abin cin kin fa ba,ba kya jin yin wa ne " ? " Eh na ƙoshi sai na dawo ". Kai Inna ni ta girgiza kawai kafin a hankali ta furta. " Ki kula in kika fita kuma banda yin dare ". Cike da farin ciki Shatou ta ce. " Tau zan kula ". ko gama Addu,an bata yi ba kuwa ta miƙe ta chanzo riga yar doguwa ta atamfa da ta ɗage mata sannan ta ɗauro ɗankwali irin dai shigar da kuka san matan ƙauye na zuwa dandali da ita ta fice bayan ta yiwa Inna ni sai ta dawo. Koda ta fita Inna ni ajiyar zuciya ta ƙara saukewa tare da bin ta da addu'ar kariya. A ɓangaren Shatou kuwa tana fita gidan su Jawairiyya ta fara shiga da ke kusa da su maman Jawairiyya da gama sallahn ta kenan ta kalle ta da mamaki ta ce. " Wai dandali za,a je yanzu da wuri haka,Amma dai A'i bata gan ki bata san kin fito ba ko,wannan irin sako haka " ? " Sai da na tambaye ta sannan ". Shatou ta bata amsa tana cunno baki gaba. Kai maman Jawairiyya ta gyaɗa bata ƙara cewa komai ba dan dama ita bata tauye yar ta abu ɗaya ne bata so shine ta yowar dare,dan ma dai kawai ta san dalilin da ya sa Inna ni take yi wa Shatou katange ya sa yanzu tayi mamakin fitowar Shatou haka da wuri dan haka ta shanye mamakin ta da amsar da shatoun ta bata. A haka suka shirya cike da murna da sakewar da shatou tayi haka suka fice da Jawairiyya daga gidan, gidansu Amina suka wuce nan ma maman ta sai da ta magantu amsa ɗaya ta bata itama dan haka itama Amina da take cike da tunanin shatoun ta yi ta murna maman ta kuwa abun har mamaki ya yi ta bata dan da ta dawo harda kuka tayi mata na yadda Shatou ta share su sai gata kuma ishain farin ta zo da sakin fuskar ta kamar ba ita ba. Suna fita suka yi gidan su Ramata chan ma basu jimaba sun same ta har sun gama sallah dan haka a take su ka yi dandali su hudun su a jere suna wasannin su har suka isa duk da suna ɗan shakkun Shatou ɗin amma sun sake ganin yadda ta wartsake musu kamar ba ita ba. Sune farkon wayen da suka buɗa dandalin yau dan haka suka samu waje suka zauna suna yan wasannin su na hannaye a haka wajen ya fara cika da jama'a yan yara matasa irin su kafin suma Mazan su fara zagaye wajen suna zama akan ɗan dakali da ke wajen wasu akan kara wasu jingine a kan bangon dake kusa da wajen na tsohon gidan mai gari. Waje na cika dan har su iro sun cika wajen suka fara wasannin su cike da nishaɗi da burgewa. Ita da Nazihwa kamar ba su yi faɗa ba suka sake ma juna aka cigaba da wasa sai dai shi Shamsu fa ya riga ya ƙullaci Shatou da gaske dan haka ya ke Binta da ido duk motsin ta yana kallo dan yau ya sha alwashin sai yayi maganin ta cikin daren nan dan bata isa ta taɓa masa Nazihwa ba ya ƙyale.Shi ko Iro ganin an ɗan kwana ya sa ya share da zancen Shamsu dan tunanin sa ya bar maganar duk da ya san halin sa mugun mutum ne Shamsu ko tsakanin su ta haɗa su sai anyi da ƙyar yake saki maye ne ɗan Bala'i dan sun tabbatar da ace Shamsu maye ne duk wanda ya kama sai buzun sa. A haka suka yi wasannin su cikin sakewa cikin ikon Allah yau har an ka gama ba,ayi rigima da kowa ba an wanye lafiya. Suna gamawa kowaccen su ta kama hanyar gida Iro hankalin sa ya ɗauku saboda wata gardama da suke yi a tsakanin su har Shatou da yake ta bi da ido ta bar wajen bai lura ba, yau ba ma hanya ɗaya suka bi da su Amina ba kowa ta sa ya kama dan haka tafe take tana juya ɗan karen dawar ta,da ta samo a wajen dandalin tana yan waƙe waƙen ta.Sai dai Turus ta ja ta tsaya ganin mutun gaban ta kamar an jeho sa. Wata irin ƙatuwar sanda dake hannun sa ta tsirawa ido kafin ta kai kallon ta kan fuskar sa da take babu annuri ko magana bai yi ba ya ɗaga ƙatuwar sandar yana neman Kaita jikin Shatou wadda ta waro idanun ta da ƙarfi ganin da Dagske a jikin ta zata sauka ga wani tsoro da ya saukar mata ganin bata da mace ci sai Allah bata kuma da abun kare kan ta sai dai ba zaka taɓa gane cewa a tsorace take ba ta shanye harda riƙe ƙugu irin in ka isa ka taɓa ni,ai kuwa akan ta ya sauke sandar da wani irin ƙarfi sai dai wani abu ta ji ya tokare mata akai sandar bai sauka akan ta ba hakan ya sanya ta buɗe idanun ta da ta rufe ruff tana jiran tsintar kan ta wata duniyar mai cike da wahala. Iro ne ta gani gaban ta yana zare ido cikin ɗan hasken farin watan da ke zagaye da su ga hannun sa ɗaya akan ta riƙe katuwar sandar Shamsu da ya fara kiciniyar sai ya sauke ta jikin Shatou ɗin ran sa ɓace dambe ne ya kachame tsakanin su ita kuwa Shatou cike da mamakin yadda akayi Iro ya san ta nan ta biyo ta matsa baya tana haɗiye tsoron ta tare da ɗan jin sanyi a ranta na zuwan Iron dan ta san da yau sai su Baffa na sun yi kukan rasa ta. Ganin yadda dambe ya kachame tsakanin su hakan ya sa da baya baya ta fara tafiya kafin ta ɗaga ƙafa ta yanka a Guje tana ɗan waigen su. Su ko su Iro abokan sa ne da suka biyo bayan sa suka raba faɗan dan dama wani daga cikin su ne da bai je da wuri ba ya sanar da Iro ya ga shatou a wannan hanyar da zai taho nan dan haka ya biyo bayan ta sai sai dai kuma ya tarar da shamu ya tare ta yana batun mata illa dan ya san ya aje wannan sandar ta sa jikin shatoun sa sai ya mata illa ƙila ma ya karya mata ƙashin baya. Da ƙyar suka raba faɗan abun ka ga ƙarfi da ƙarfi sai da suka yi da ƙyar suka raba dan kowannen su yaji jiki babu wanda yake baya wajen ƙarfi da rigima. Gida suka wuce da Iro sai dai ya zille sai bin bayan Shatou da yayi yana huci. Sai dai har ya kusa isa gidan su bai ga mai kama da ita ba dan haka ya tabbatar cewa ta isa gida lafiya.Sannan ya wuce gida yana jin yar natsuwa na saukar masa. Shiko Shamsu wata sabuwar gobarar ƙiyayyar Shatou ce ta ƙara ruruwa a cikin zuciyar sa nan yayi ta shan alwashin illa ta ta, ta hanya da ban da ban.Sai da ya zage ta tass ita da Iro kafin ya wuce gida yana ƙara jin zafin ta har Iron musamman ganin bakin san ya fashe dan ya shafo jini ga shi yana jin zugi kaɗan kaɗan. A ɓangaren shatou kuwa a Guje ta faɗa gidan Baffa na da ke zaune yana duba wasu littafan sa dan jiran Dawowar ta saboda hankalin sa da ya ƙi kwanciya ya ɗaga ido ya Kalle ta dan abinda Inna ni tayi bai masa daɗi ba amma ya san tana da dalilin barin ta fita gashi ba ta ma san rigimar da aka yi shekaranjiya ba.Dan ya san da ta sani da ba zata barta ta fita ba gashi shi da na shi dalili mai ƙarfi da bai son yawan fitar ta ta dan haka ya ke ƙoƙarin saka mata ido akan komai da take yi. Inna ni da ta fito wanke hannu kasancewar tana ɗakin ta ne ta ɗauke kallon ta daga kan Shatou da ta gama ƙare ma kallo wadda ke ta sauke numfashi daga inda take tsaye. Sai kuma a hankali kamar wadda aka matsi bakin ta,ta ce " Lafiya kika faɗo haka babu sallama ".?Ta yi mata tambayar ba tare da ta kalli ƙwayar idon ta ba. " Inna ni faɗa fa ake yi da Iro da Shamsun mai guru ". Sai da ta yi zancen sannan ta rufe bakin ta tana zare ido dan ta san dole za,a tambaye ta dalilin faɗan na su wanda dole zata ce itace sila gashi Inna ni bata san farkon rigimar ba,haka ma Baffa na wanda bata san ya san komai ba. Hmmm kawai Inna ni tayi kamin ta ce. " Ki wuce ki kwanta ki tabbatar kinyi addu'a kafin ki kwanta,abincin ki na nan ki tabbata kin ci ". Kai ta gyaɗawa Inna ni kafin ta wuce sum sum alamar rashin gaskiya.Inna ni idanu kawai ta bi ta da su tana girgiza kan ta haka ma Baffa na ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani tunani akan wannan rigimar na ɗarsar masa.A haka ya gama duba littafin na sa ya shige bayan sun yi sallama da shatou da ta masa sai da safe haka ma Inna ni dan Bibu yayi baccin sa tuni tunda suka dawo ya ji labarin shatou ta fice kuma ta ce ta yau bazata je da shi ba yayi alwallah ya shigewar sa yayi baccin sa hankali kwance bayan ya ci abincin daren sa. Miƙewa Baffa na yayi ya saya gidan kamin ya shige shima. Sai da yayi ta juye juye kamin bacci ya kwashe sa, ya daɗe yana tubka da warwarar yadda zai yi da rigimar da ta shiga tsakanin Shatou da shamsu sauƙin ta ma ta samu mai tare mata duk da bai son wannan shisshigin na Iro amma yakan ji daɗi da kariyar da yake bata. Inna ni yau ma ta daɗe zaune kafin ta kashe haske ta kwanta bayan ta yi addu'a cikin yardan Ubangiji kuwa bacci ya kwashe ta mai daɗi sai dai bacci ne mai cike da mafarkai. A ɓangaren shatou kuwa bayan ta gama cin abincin ta,wanda ta ci kadan ta sha ruwa,ta kwanta,ta daɗe tana tunanin wannan ƙarfin hali na Iro duk da ta ji daɗin yadda ya shige mata faɗan matuƙa dan ta san ko giyan wake ta sha bazata iya dambe da Shamsu ba. A haka cikin tunanin bacci mai nauyi ya kwashe ta kasancewar tayi Addu'an kwanciya bacci. ***Yau Shatou a sake ta tashi cike da fara,a dan haka suka yi duk wasu ayyukan da suka saba yiwa Inna ni ita da Bibu kafin suka fice makaranta bayan sun yi wa Inna ni da Baffa sai sun dawo kasancewar Baffa na yau bai fita da wuri ba ya ɗan tashi da ciwon kai. Koda suka isa makaranta kowa ya san yau Shatou ta dawo ta asali ba shatoun jiya ba ce. Dan haka kowa yake kokarin shige mata aka cigaba da yadda aka saba farin cikin Amina ya kasa ɓoyuwa dan koda ta zo makarantar a tsorace take ta yi zaton Shatou ta chanza musu sai ta tarar da aka sin haka dan haka take jin daɗi kamar ta goye shatoun kuma Shatou ta fuskan ci hakan da dukkanin su ma sai dai bata tambaye su ba ta share. A haka aka tada su tara suka fito gida kowannen su gida yayi dan an basu dama yau ɗin dan haka Shatou tana cikin masu zuwa gidan su Amina kuwa duk basu je ba dan sun san dole zasu yi latti a zane su Gara ita sun san bata jin tsoron bulalan sosai dan tana mazewa kar a raina ta. Gidan ta wuce sai da ta ci abinci Inna ni nata mita sannan ta fito ganin tana neman yin latti. Koda ta fito gida ta ci karo da Iro.Yana ganin ta ya washe baki.Gaba tayi kamar ba zata tanka masa ba da sunan ta da ya kira. Har ta ɗan yi gaba ta tuno da taimakon da yayi mata jiyan sai ta ɗan ji Tausayin sa hakan ta sa ta ja burki tana juyowa tana kallon sa,sama da ƙasa ta gama ƙare masa kallo kafin ta yatsine fuskar ta sannan kuma ta sake ta. Sannan a hankali ta amsa da " Na'am " bayan ya ƙara kiran sunan ta har da wani haɗawa da ta.Na nata sunan ta yi wai Shatou ta sannan ta ja ƙaramin tsaki iya laɓban ta shi ko sokon sai ya ga kamar tayi masa wani ɗan style na murmushi daya ga ya ƙara mata kyau. A haka suka jera suna tafiya Iro na jin kan sa sama sai washe jajayen haƙoran sa yake yi.Dan Shatou hakan ne kawai take ganin mafitar rabuwa da iro lafiya,musamman da ya fara yi mata amfani ko dan haka yanzu dole ta ƙara sake masa dan ya dagargaji maƙiyan ta dan shatou ba dai wayau ba shi ya sa yanzu ta saki fuska tana sauraren labarin faɗan su na jiya da yake bata wani abun tayi murmushi wani ta ɗai juya kai. *A ɓangaren su MAHAJ kuwa kasancewar suna da lafiyayyun motoci basu wani jimaba suka iso ƙauyen. Kasancewar ba baƙi suke ba Mubarak da sauran drivers sun san inda ake aikin ya sa basu tafi wajen mai gari ba direct suka kama hanyar wajen. Jingine yake da seat ɗin motar kamar yadda suka fito da Bluetooth a kunnen sa yana sauraren ƙira'ar minshawi idanun sa a lumshe p cap ɗin sa ya juyar da kan ta baya ya sanya haɗaɗɗen radon sa baƙi wulik mai kyau da ya ƙara wa fatar sa armashi da kyaun sa da yake fitar da wani annuri na haske na Hutu,arziki,da lafiya. Gudun motar ta su Muby ya rage kasancewar ya hango ta tun daga nesa haka kuma ya gane wanda take tare dashi ɗin dan haka ya ɗan saci kallon MAHAJ ta glass ganin bai lura da ita ba ya sa da gangan Muby ya ci wani irin burki wanda ya saka MAHAJ

Chapter 30 of 39