Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haske a cikin rayuwa ta Ɗan Baiwa kar ka bari nayi ƙwalla,Kar ka bari yar Baiwar ka ta zubda ƙwallla hhhh " ta kece Da dariya sai gata iya karta kaɗan da tafiya bakin bukkar ta sa ta ɓace ɓatt. Dariya ya kece da ita yana cewa " ta Baiwa kin Halaka kin halaka " .Kafin ya ɓace ɓatt daga shi har bukkar ta sa wurin ya koma filin Allah fallau kamar ba,a taɓa zama wajen ba ga wata irin rana da ta buɗe ta yi wani irin tsayi. " Ninah zo ki dubo mini Junaid na aike sa ya nemo mini magani na ina jin kamar Bp na na son ya tashi,na duba ashe maganin ka sun ƙare mini ". " To Ummah amma na Ga kamar kina cikin damuwa me yake damun ki ". " Bana son yawan tambaya Ninah zaki nemo mini shi ko naje da kaina ". Ɓata fuska Ninah tayi kafin ta miƙe ta bi wata hanya da ta shiga kamar lungu. Kasancewar yau weekend ce dukkanin su suna gida lokacin islamiyya bai yi ba..✍️ *To fa jama'a wace ce wannan Ta Baiwa bari na sha cuppy na ɗan samu relief tunani ya min yawa kar brain tayi Bosting wajen zaƙulo muku wacece ta Baiwa,Allah na ƙagu na san wacece wannan mata.🚶😮‍💨🚴🚴🚴🚴* Me kuke hasashe akan ciwon ISHAA. wai chakwakiya....🚴🚴 # Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣3️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* ☘️☘️☘️ Junaid kallon ta yake yi bayan ya kawo mata maganin ta sha gaban sa. Numfashi ya sauke kafin ya ce " Momcy wai me yake damun ki ne,Babu dalili BP yayi ta hawa,kuma anyi tambaya kice babu komai dan Allah idan wani abu na damun ki,ki faɗa mini Momcy ". Hajiya Ramlat kai ta sauke ƙasa bayan ta gama ƙare ma Junaid kallo da saurarar furucin sa kafin ta ƙara kallon sa tana galla masa Harara. Sannan cikin shan toka ta ce " Wai ni,Junaid ba zaka rage yawan yi mini tambaya ba,na sha faɗa maka babu abinda ke damuna,amma da alama baka yarda,Hawan jini ba ciwo bane da Allah ka jarabtar bayin sa da shi,ko ance maka sai akwai damuwa yake samuwa ". Ta kai ƙarshen zancen tana jiran jin amsar sa bayan ta ƙara zuba masa idanu. Junaid bai ce komai ba sai kai da ya sauke ƙasa cike da natsuwa ya ce " Allah ya baki haƙuri Momcy,kuma ya baki lafiya ". " Amin " ta furta ba tare da ta ƙara bi ta kan sa ba kasancewar ya miƙe jiki a sanyaye ya bi hanyar da zata sadaka da nashi bedroom. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana haɗiye wani irin abu mai nauyi a cikin zuciyar ta wanda take faman haɗiya shekara da Shekaru tun shigowar ta gidan. Tsaki ta ja mai ƙarfi tana furtawa a fili " Dole na ƙara sanin abun yi ba zai yuyu ba wallahi na zuba ido,idan har na ga babu cigaba a aikin da ya zo a ɓagass,ba zan taɓa yarda na faɗi warwass ba,dole na ƙara buɗe wuta ". Ta kai ƙarshen zancen tana ƙara jan mugun tsaki da yafi na daa girma. Miƙewa tayi a ɗan gajiye ta shige ɗakin ta kasancewar bata daɗe da fitowa ba ma daga cikin sa dalilin fitowar ta rashin ganin maganin ta ne da ta lura ma sun ƙare. Reena shiru tayi tana tura bakin ta gaba da Leena tayi wa mugun bugu a yanzu bayan ta ce mata Allah ya isa saboda ta taɓa mata littafin da take yan zane zane saboda tana son zane sosai, sai dai har yanzu bata wani ƙware ba. Hawaye ne suka silalo mata a hankali kafin ta buɗe bakin ta ta ƙara furta " Allah ya isa na ". Aiko Leena da ke ciccika kamar jira take yi ta ƙara kaima bakin na ta bugu inda take ya fashe da jini Kuka Reena ta saka ganin jini bayan ta shafo bakin aiko giyar kukan na ta ta ƙara tana ƙoƙarin kaiwa Leena bugu.Abba ne da ya shigo yanzu ya katsa musu tsawa dan hakan ne kawai zai an kararar da su da faɗan da in suka fara sai ka tsorata dan ma yanzu an samu sa,a Reena na ɗan ƙwatar rabon ta dan haka kare jini biri suke yi sai dai duk da haka itace mai shan wahala dan ƙarfin ba ɗaya ba,Leena kamar ƙarfin maza haka take damben babu ji babu gani,ranar da suka fara yin irin damben Gaban Abba sai da ya shiga tashin hankali matuƙa dan sai dai ya ji labarin anyi bayan sun ɗan fara tasawa,basu cika yi gaban sa ba. Sakin juna suka yi kowace na ciccira kamar ta kashe yar uwar ta.Reena ga bakin ta har yanzu jini yake yi kuma bata fasa shesshekar kuka ba.Wanda yake ratsa ƙwaƙwalwar Leena saboda daɗi dan yanzu mugun jin daɗin take ta ga tana kuka,in ta buge ta sai dai har yanzu idan wani ya taɓa Reena daga waje rigima ake yi Babba. Tsitt falon yayi sai numfashin su dan ko Reena yanzu ta yi shiru ganin yadda Abba ya zuba musu idanun sa ya rungume hannuwan sa. " Kowaccen ku ta je ta ɗauko mayafi na baku mintina biyu ". Ya furta musu cikin tsare gida. Babu musu kuwa suka wuce kowaccen su ta yi bedroom ɗin ta.Ba,a jima ba sai gasu a shirye Leena ce ta farko,kafin Reena saboda ta tsaya goge bakin ta da kuskure sa.Tare da wanko fuskar ta. Mayafi ɗaya dukkanin su suka saka dama shigar iri ɗaya ce,ta riga da siket yan janyo masu kyau. Bayan sa suka bi bayan ya gama ƙare musu kallo yana sauke Ajiyar zuciya da numfashi. Drivern sa ne ya taso da sauri ya buɗe masa bayan shigewa yayi itama Reena shiga tayi bayan sai dai a tsorace take da Abban yau. Ita kuwa Leena gaba ta shiga fuskar ta a ɗaure da ka gan ta kaga ruwan masifa dan haka driven da ya san halin kayan bai ce mata ƙala ba dan yana ɗan tsokanar ta wani sa'in. Securites ɗin Abbu da suke kula da shi ne suka taso su uku zasu shiga Mota ya hana su yana furta " Ba nesa zamu je ba ". Daga haka driven ya ja motar suka bar haɗaɗdiyar unguwar. Sun yi tafiya mai ɗan nisa har suka bar unguwar ta su kafin suka shiga wata unguwa itama dai gwargwado mutanen ta akwai dan hali a ciki ga jama'a nan sai harkokin gaban su suke yi. Dai dai wani ƙaton gate Drivern ya dakata bayan bin umurnin Abba. Fitowa yayi suma haka bayan an buɗe masa kofar. Wani ɗan dattijo ne da ya ke ɗauke da gemu mai ɗan tsawo fari ya fito daga yar ƙaramar kofar gate ɗin da alama fita zai yi ganin Abba ya sa ya washe bakin sa yana cewa " A'ah Saleh yau kaine a nan " . " Ehh malam " Abba ya faɗa cike da girmamawa. " Madallah to ku wucekke,har da manyan baƙi ake yau ". Murmushi Abba ya sake yi yana kallon su Reena da suke ɗan satar kallon Abba ɗin su ga ko ya chan za fuskar sa da take haɗe. Sai ko Gashi yanzu sun ga ya saki dan haka suka fara samun natsuwa a zukatan su.Suka fara sakin jiki babu ma kamar Reena Ita dai Leena bata wani saki fuskar ta ba. Zama suka yi a wani Madaidaicin falo da yake ɗauke da tarin littafan addini ya sha gyara sai ya zama ko ina yayi haske dakin babu hayaniya daga kujeru sai carpet da littafan addini da suke a tsare jere gwanin burge wa. Gaisawa suka yi cike da girmama juna.Har yana tambayar Abba Ina Sir da yake abokin su Sir ne da Dada sun yi gwagwarmaya tare anan.Malan Sunan sa shine Hambali.Ana kiran sa malam ne gaba ɗaya yanzu saboda ya zamowar sa Babban Malamin Addini shi ya sa da wuya kaji wani ya ambaci sunan sa sai dai malan ɗin. Gaisuwar su Leena ce ta maido da hankalin sa kan su.Zuba musu idanu yayi kamar yana karantar wani abu akan su kafin ya saki ɗan murmushi yana amsa musu Gaisuwar cike da sakin fuska. Yana cewa " Yan biyu an girma " Yayi zancen yana sakin ɗan murmushi.Baki Reena ta washe cike da jin daɗi tana gyaɗa masa kai. Ita kuwa cike da jin haushi ta sakar wa Leena harara bayan sun haɗa ido ganin ta ɗaga masa kai. Abba ne ya fara magana yana cewa " Dama Malam ya ran nan ne abun yake damuna shine nake son ka ƙara dubamin su idan ta dace ko raƙiya a musu a gani,Ni lamarin su tsoro yake bani,babu mai son ɗan uwan sa ya shiga inuwar sa,chan baya mun zo kace babu komai Malam dan Allah ina son a kara duba mana yanzu ko akwai iska a kan dayan su ". Abbu ya haɗiye wani abu mai ɗaci yana ajiye ayar zancen wanda ke nuna maka yadda abun yake damun sa. Kai Malam ya gyaɗa dan an taɓa kawo masa su chan baya kuma ya duba su kuma tun a wancan lokacin ya ga abun da suke tare da shi sai dai bai sanar ma da kowa ba ya ce babu komai a tare da su. Wanda bamu san dalilin sa nayin hakan ba.Zuba musu ido ya sake yi musamman Leena kafin ya saki guntun murmushi ganin tana ɗauke idanun ta akan sa bayan sun haɗa ido. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kalli Abba dake jiran jin yace akwai iska akan Leena ɗin dan ayi mata ruƙiyar. Sai dai jin ya ce " Babu komai kawai ƙuruciyar su ce haka,kar ka damu da sannu zasu daina in Allah ya yarda ". Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yana fatan hakan ya tabbata tun da wanchan karon ma haka Malam yace masa dan ko wancan lokacin shi ya kawo su da kan sa. Har malam ya ce masa idan ta sake faruwa ya kawo su nan a gani ko akwai ɗin dan yan zu babu alamar komai a tare da su lafiyar su ƙalau. A yanzu ma Malam ne ya katse masa tunani da tausayin ya yan na sa da ya ke so fiye da shi kan sa a cikin duniyar nan.Yana cewa " Idan abun yayi ƙamari ka ƙara kawo su sai a basu magani na miyagu,kar ka kai su wani wajen a wahalar da su kaji,Saleh zasu daina in Sha ALLAH ". A jiyar zuciya Abba ya sauke dan haka aka yi a wancan karon kafin ya ƙara tsintar Muryan malam da yake magana da ita anatse cikin natsuwa da kamala ya furta Yanzu zan basu ruwan Addua, kowaccen su ta sha sai ta shafa ". Wata ƙatuwar Jarkan zam zam ya jawo daga gefen sa sannan ya bude ya tsiyaya a wani ɗan ƙaramin cup sai da ya cika sa tab sannan ya rufe Jarkan yana mayar da ita inda take. Ya daɗe yana tofa ma ruwan Adduo,i kafin ya ɗago kan sa ya ɗauki ruwan ya raba biyu inda ya zuba a wani cup irin wannan Sannan ya miƙa ma kowaccen su cike da murmushi yana cewa suyi Bismillah su sha.Amsa suka yi sai dai kafin su amsa sai da Leena ta zuba ma ruwan idanu kamar ta ce bazaa ta sha ba sai kuma ta karɓa jikin ta na yin sanyi ƙalau Bismillah tayi ta kafa kai bata tsaya ba sai da ta shanye komai sannan ta sauke cup ɗin tana yatsinar kyakkyawar fuskar ta mai cike da ƙuruciya. Malam ma Numfashi ya sauke da ajiyar zuciya kafin ya ɗan matsa kusa da su ya fara tofa musu Addu,oi sai da ya daɗe yana yin su sannan ya shafa ma Reena akai ita kuwa Leena A ƙafafu.Hakan da yayi sai ya bawa Abba mamaki amma sai dai ya kasa tambayar sa dalilin yin hakan.su kan su su Leena sun ga abun da yayi sai dai basu kawo komai ba saboda ƙuruciyar su basu ɗauka akwai dalili ba. Godiya Abba yayi wa malam kafin ya sauke masa manyan kuɗaɗe yace a yi sadaka. Duk yadda malam ya nuna ya bar su haka Abba ya tule masa su yana Murmushi tare da ƙara yin godiya. Har gate ya raka su tare da yiwa Abba kyautar zuma mai kyau wadda sai da ya shiga Mota sannan ya bawa driver saboda ya san halin sa ba lallai ya karɓa ba."Ka gaishe mini da Sada da Usman".Malam ya furta yana ɗaga musu hannu ta glashin motar. Hannu suma suka ɗaga masa kafin driver ya tada motar suka bar bakin ƙofar gidan. Numfashi Malam ya sauke da ajiyar zuciya kafin ya furta wa kan sa a hankali murya a karye cike da tausayin Saleh da Su Leena " Ba yanzu ne lokacin da zaka ka san komai ba,Saleh bana jin zuciyar ka na iya ɗaukar wannan ƙaddarar a karo na biyu,a sannu komai zai warware kan sa,tabbas ya' yan ka suna cikin matsala Babba amma faɗar matsala ce a cikin rayuwa ta, ka gafar ce ni Saleh,amma muna ta ya ka yaƙi muna kai wa Allah duk dare,komai zai zama tarihi za,a wayi gari mai aikata wannan aika aikar ya bayyana da kan sa,kafin mu" Ya kai ƙarashen zancen yana sauke ajiyar zuciya yana komawa cikin gida jin kan sa na sarawa dan ya ji fitar ma ta fita ransa.Abubuwa da dama na dawo masa a kai har bai son yana tunawa saboda yadda zuciyar sa take tsinkewa da rayuwar duniyar. Abba kuwa umurni.ya bawa Driven na sa ya kai su Wani haɗadden mall Inda ya zuba musu Leena siyayya kamar bai san darajar kuɗi ba saboda adalci haka ya siya wa su Hamrah harda Ninah da ba yar sa ta cikin sa ba.Siyyaya su kayi mai Shegen yawa kafin ya biya kuɗin aka saka musu kayan a mota.Sannan suka yi gida kowaccen su tana ta faman sakin murmushi dan kwana biyu ba su je ba dama yaya Bilal ne yake kai su sai Abba wata rana amma ya kan daɗe.Cike da farin ciki suka yiwa Abba godiya Saboda koyar war Ummah ce wannan. Ajiyar zuciya Abba ya sauke yana zuba ma Reena idanun sa wadda ta ke ta faman shan ice cream ɗin ta hankali kwance bai san dalilin da ya sa yake jin ƙirjin sa na faɗuwa ba idan ya tuna yadda malam ya shafa ma ƙafafun ta Addu'a sai ya rasa samun natsuwa sai dai bai jin zai iya maganar da kowa saboda haka kawai yake jin akwai wani ɓoyayyen lamari da yake a jiye a duhu da Allah kaɗai ya bar wa kan sa sani,ba zai zargi malam ba amma zuciyar sa sai kai kawo take yi akan maganganun malan. Kallon sa ya mayar kan Leena itama dai anatse take shan ice cream ɗin ta tana sakin murmushi.Murmushin ya samu kan sa da yi yana jingina kan sa da seat. Tare da rufe idanun sa wani shuɗaɗɗen lokaci na dawo masa a kai samun kan sa yayi da sakin murmushi a karo na biyu kan sa ya girgiza sannan ya buɗe idanun sa ya shafa kan Reena. Dai dai sun kawo gida inda aka wangale musu ƙaton gate ɗin. Shigowa motar tayi bata tsaya a ko ina ba sai bakin sashen Hajiya Asma'u. Kayan Hamrah da na Ninah suka fito da su inda suka shige ciki.Ba tare da sun jira Abba ba. Hamrah dake falon tana kallo ne tare da mahaifiyar ta ta daka tsalle tana murna ta karɓe kayan.Tana tambayar waya siyo muna. Reena ce ta bata amsa baki washe tana faɗin " Abba ne ". Hajiya Asma'u dake zaune ce ta ɓata fuskar ta tana haɗiye wani irin ƙololon baƙin ciki kafin ta saki fuskar ta ganin Abba ɗin ya shigo. Gayar da ita su Reena suka yi cike da bata girma,sai dai ita Leena gaisuwar bata ma yi niyyar yin ta ba.Haka kawai jinin ta bai haɗu da na Momy ba. Zama Abba yayi yana sauke numfashi kafin ya amsa gaisuwar da Momy ke masa wadda kowa ya san itace mace ta farko a gidan na sa sai.Ita ce uwar gida.Sai dai ya ɗaya gare ta. " Abban su daga ina haka,sai ga yara sun shigo da kaya Masha ALLAH "? Murmushi Abba ya ɗan saki kafin ya furta. " Sun raka ni,na gano malam shine sai na biya da su aka yo siyayyar nan ". Wani irin raɗaɗi zuciyar Momy ta ƙara yi jin yana faɗin rakiya dan son kai ai ya san yar ta Na nan mai ya sa bai je da ita ba ta yo siyayyar da kan ta sai yan son sa,zata yi maganin sa da shi har uwar su take ayyana wa a ranta.Inda maganar Abba ta katse mata shirun na ta yana cewa " Kuje ku kaiwa Ninah nata ku dawo ko ".Kai suka jinjina masa kafin suka miƙe cike da murna suka fice har Hamrah tare da kayan Ninah ɗin a hannun su. Bayan fitar su kuwa Momy cike da kisisi na ta miƙe tana furta. " Angode ƙwarai Abban su,Bari na kawo maka ruwa " Dan bata saka kowa aikin mijin nata ita take yi da kan ta komai yawan sa. Kai ya jinjina mata yana yin balance akan kujerar da yake kai fuskar shi na sauya wa da damuwa dan har yanzu ya kasa sanin tunanin da zai yi. Ruwan ta tsiyayo masa sannan ta zo da lemu na kwali mai tsada haka ta ɗauro kayan akan tiren da ta ɗauro su.Lemun ne take ta faman girgizawa. Tana ɗan satar kallon Abba da ya rufe Idanun sa.. "Abban su anya kuwa lafiya lau kake naga kamar fa akwai damuwa akan kyakkyawar fuskar nan taka" ? Ta furta tana ɗan nuna damuwar ta. Murmushi ya saki kafin ya buɗe idanun sa . Yace '' Babu komai Asma'u,Bacci ne kawai nake ji jiya ban kwanta da wuri ba saboda ayyukan da na ke son na kammala a office da ban samu nayi ba ".kai ta jinjina tana fara miƙa masa lemun mai sanyi da tsiyaya masa. Karɓa yayi yana kaiwa bakin sa cike da Bismillah. Cije baki Momy tayi kafin ta tsiyaya masa ruwan suma tana sakin Murmushi ganin ya shanye duka. Ajiyar zuciya ya sauke jin yadda sanyi ya ratsa sa. Bai ma sha ruwan ba ya miƙe yana faɗin " bara naje na ɗan kwanta kafin a yi sallah ko kan zai rage mini ciwo su idan sun dawo kice musu na wuce ". Kai Momy ta gyaɗa kafin ta sauke ajiyar zuciya tana masa sai anjima. Duk da anjima kaɗan zai dawo part ɗin na ta saboda itace da shi anjima,har nan da kwana biyu. Murmushi ta saki wanda ita kaɗai ta san ma'anar sa sannan ta kwashi kayan da aka kawo na Hamrah ɗin bayan ta gama sakar musu harara kamar sune Abba ɗin da su Leena ƙwafa tayi tana wuce wa Bedroom ɗin ta. A part ɗin Momcy kuwa Ninah kawai suka tarar anan falon itama cike da farin ciki ta karbe kayan tana tambayar wa ya siyo musu. " Abba ne " suka haɗa baki wajen faɗa aiko cikin daka tsalle da murna ta ke furta " thanks you Abba ". Hayaniyar ta ce ta sanya Hajiya Ramlat fitowa wadda har ta ɗan fara bacci bayan shigar ta. " Ke lafiya kika cika mini gida haka "? Kayan ta ke nuna mata fuskar ta wanze da murmushi. Washe baki Momcy tayi kamar ta yage sa dan murna dama mace ce mai shegen son banza. Karɓan kayan tayi tana dubawa dukkanin su babu ƙarami kaya ne masu tsada dan kowace riga da wando zasu kai kusan dubu arba'in ko fiye da haka takalmin ma masu tsada ga chocolates nan suma zube masu yawa. Fuskar ta cike da murmushi ta ce " Abba ya kyauta kamm yana ji da ya yan sa,kuce an gode Allah ya saka da Alkhairi " " Bari ma na haɗa ku da faten wake da nayi ɗazu na san yana son sa sai ku kai masa ". miƙewa tayi ta shige kitchen bayan gama maganar ta jima a ciki sai gata ta fito bakin ta washe hannun ta rike da yar wata kula mai kyau ta silver da ta haɗa da golden.Miƙa musu tayi suka karɓe kuwa Ninah ma ta karɓa sannan suka fice daga part ɗin. Koda suka shiga Part ɗin Momy basu tsaya jiran komai ba ganin baya nan haka ya tabbatar musu da ya koma part ɗin Ummah sai Reena ta karɓo Coolern saboda Hamrah ta san halin mahaifiyar ta sai ta mata faɗa saboda bata, bata izninn fita ba. Ganin bata falon ya sa ta miƙa ma Reena Ita ta wuce bedroom ɗin Momcy ta ƙara ganin kayan ta dan ta san suna wajen ta... 'Tunda suka dawo daga makarantar ƙirjin ta yake wani irin bugawa ba tare da ta san dalili ba dan in ka lura da kyau zaka iya ganin yadda ɗan hijabin ta yake ɗagawa. Duk yadda su Amina suke son ta saki jikin ta ta kasa ƙarshe ma kuka ta saka musu abinda bata cika yi ba.Bibu hankalin sa tashi yayi shima ganin yadda take kuka wiwi kuma a iya sanin su babu abinda aka yi mata har aka tashi daga makarantar.Da ƙyar suka rarrrashe ta suka samu ta yi shiru sannan ta miƙe suka cigaba da tafiya wadda ake yin ta yau kamar masu koyo dan Shatou bata iya cewa ga inda take saka ƙafar ta.Su suke kula da duk tafiyar ta ta har suka iso gida zuwa lokacin magriba ta gabato.Sak Inna ni tayi ganin yadda SHATOU ta koma kamar marainiya dan ko lokacin da ta samu kan ta acikin baƙon wata a matsayin farin ta, bata yi hakan ba,cike da mamakin yanayin na ta take kallon ta cikin ɗan hasken da ya rage.Kafin ta iya furta wani abu sai ga Baffa na ya shigo cike da sallama.Bibu ne ya amsa masa sai Inni ita kuwa SHATOU kuka ta ƙara fashewa da shi tana dafe ƙirjin ta,da yake cigaba da bugawa tana durƙushewa wajen kan ta Bibu da Baffa na suka yi cike da kulawa.✍️ Anya kuwa Momcy 🚴🚴🚴🙆‍♀️Wannan matar nason kunce mini ɗaurin kaina. Malam ma haka jama'a me yake faruwa wai🤨an bar mu cikin duhu.🚶🚶😂🚴🚴 Shatou me yake faruwa hiliss ki daina karya muna zuciya.🥺 # Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣4️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* # Shatou # Baffa na # Iro # Leena SS # Reena SS # Mamy # Samir IS 🍂🍃🍂🍃🍂🍃 ***Kukan ta sake ɓarkewa dashi kafin ta lafe jikin Baffa na dake tambayar ta lafiya bayan ya rugume ta jikin sa yana share mata hawaye shida Bibu.Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sauke kallon ta kan Inna ni da ta gama furta Bata son sakalci Kafin ta furta a hankali. " Inna ni zuciya ta fa nake jin kamar zata faso ta fito,duba yadda riga ta ke ɗagawa,Allah kamar zuciya ta bata da lafiya,baki ji yadda take bugawa ba,kamar ana kaɗa ganga". Ta kai ƙarshen zancen tana ƙara dafe ɗan ƙirjin na ta da yake ɗauke yan ƙanana halittun da suke manne akai. Sai hawaye shar suka zubo mata.Dan son tabbatar wa hakan ya sa Inna ni ɗaura hannun na ta a dai dai in da ta dafe kallon ta tayi kafin ta ce " Ki riƙa Nanata Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un da ambaton sunan Allah ". Kama wa kuwa ta yi a hankali tana faɗa bakin ta yana ɗan motsawa ahankali cikin yardan Ubangiji kuwa sai taji sauƙin yanayin idanun ta,ta ɗan rufe a hankali ta buɗe tana kallon A halin na ta da duk fuskokin su suke cike da da damuwaa babu ma kamar Baffa na dan fuskar shi ta fi nuna zallar damuwar da yake ciki. Miƙar da ita Baffa na yayi yana sauke ajiyar zuciya yana furta. " Shatouwa ki riƙa Addu,a kinji Allah ya sa alkhairi ne ke tun karo ki damu baki ɗaya ''Kai ta jinjina

Chapter 18 of 39