Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
" Reena ta furta tana Murmushi. Murmushi yayi mai sanyi ya ƙara shafa kan ta kafin ya furta cike da jin daɗi " Na ji sauƙi mata ta " Sannan ya ƙyafato Leena yana furta " waton ke wannan ja'irar matar ta wa baki yi kewa ta ba "..Ai ko kamar jira take yi ta washe baki ta matsa kusa da shi da ɗan gudu tana dariya tana girgiza masa kai. Dariya yayi yar ƙarama sannan ya ce " to me zai sa a share ni,sai na yi magana,ga ɗayar mata ta harda mini ya jikin tsufa ". Ido ta ɗaga ta ɗan saci kallon B Dake zaune yana ɗan taɓa wayar sa fuskar sa kwance da murmushi na ganin dattijon ya samu lafiya dan kwana biyu yana yawan zuwa duba sa kusan kullum sai ya zo duba sa tun da ya dawo musamman ma da ya tarar jikin sa, sai a hankali Ummah ma tana zuwa duba mahaifin na ta duk bayan ɗan lokaci Haka Abba ma da su Dada,Sir suna ɗan leƙawa dan basu yar da Zumuncin ba duk da yar uwar su ta tafiyar ta amma ai Zumuncin su na nan ya riga ya haɗu gasu harda jikokin su jini ɗaya. Fahimtar cewa BILAL ya gargaɗe su ne ya sa Baba mai Billions bai ƙara cewa komai ba sai ma shafa kan ta da yayi yana murmushi yana tofa musu addu'oi na kariya ba ta re da sanin su ba sai da ya gama sannan ya samu waje ya zauna tare da kowaccen su a gefen sa. " Ya Mahaifiyar ta ku,tana lafiya ko ".?? Ya tambaya bayan Bilal ya gayar da shi da jiki cikin girmamawa duk da wasan jika da kaka da suke yi hakan bai hana sa bashi girman sa ba da daraja sa kamar yadda yake bawa sauran manyan mutanen da bai san su ba. " Ai jiya Abban na ku yazo ya jima nan bayan fitar ka ". Murmushi BILAL yayi yana jin daɗi har cikin ran sa. " Ke yar gurguwa ya ƙafar da sauƙi ko ?" Ya faɗa yana kallon REENA da take ta murmushi dan indan kewar sa sunyi kewar sa dan tun da ta kwanta ciwon ƙafa basu leƙo shi ba gaba ɗayan su Bilal shi kaɗai yake tahowar sa. Baki ta tura gaba fahimtar da ita yake Kafin hawaye suka cika idon ta tuno azabar da ta sha kafin ƙafar ta samu sauƙi " Ya isa haka Allah ya tsare gaba a ƙara kulawa da hanya " Ya furta yana wanzar da guntun murmushin sa kasancewar ya san komai duk da Bilal ya ɓoye masa amma ya ji komai gurin Samira jiya da ta zo gai she da shi itama gurin Hamida ta ji komai dan ta je gidan wayewar safiyar da abun ya faru ne ta ji komai bakin Ummah. " Yaushe zaka koma aiki na san hutun na ka ba mai yawa bane ko " ? Yayi maganar yana kallon Bilal da ya ajiye wayàr ta sa yana kallon kakan na sa. " In sha Allah zuwa farkon azumi zan koma,duk da hutun ba mai yawa bane dama na ɗauko ". Kai Baba Mai Billions ya gyaɗa yana murmushi kafin ya kalli Leena ya ce " Matas shirun dai yau babu magana " Murmushi tayi kafin ta ce " Akwai magana man mun kusa zama manya daga wannan shekarar sai wata zamu je senior section " Ta kai ƙarshen zancen tana Murmushi. Reena kuwa dariya ta yi itama mai haɗe da murmushi tana furta " Muma mun kusa zama irin su Anty Hamida da Samira mu riƙa fita mu kaɗai ba tare da kowa ba ". Dariya mai nuna jin daɗi Baba mai Billions yayi yana kallon su. " Ashe amare na sun kusa tare wa, na ku sa zama Sabon Ango na yar da Kaka tsohuwa " Shigowar Kaka dai dai tsakiyar falon ne da ta shige Bedroom ɗin ta bada jimawa ba ya kai ƙarshen maganar yana sakin murmushi. Murmushi Kaka tayi tana ɗan hararar Baba mai Billions cike da murmushi ta furta " ai mu tsohuwar zuma ce,sai dai ayi da mu a bar mu,idan muma aka matsa mana sai muyi sabon Aure,ga ango na nan a hannu ",ta nuna Bilal dake zaune yana murmushi fuskar sa sai sa. Dariya Baba mai Billions yayi yana furta " Tsohuwar zuma sai da wuta".Dariya Kaka tayi tana zama kusa da Leena. " Ni ba zan iya Auren Tsohuwa ba,na bar wa Baba mai Billions yayi ta kaya mu sai masu jini a jika ". Hararar shi tayi haka ma Baba mai Billions dariya ya saki yana kallon su. Kafin ya furta " Ko dambe aka haɗa mu sai mun chanye ka Indai gasa ce,dan mu rainon tuwon dawa ne bana ice cream da indomie ba " Dariya Bilal yayi haka ma Reena ganin yadda B B yayi da hannun sa alamar yana da ƙarfi irin mugun ƙarfin nan.Ita ko Leena kallon su kawai take yi dan ta kasa sakewa. Haka suka cigaba da ta ɓa fira cike da barkwanci da sakewar su har Hamida ta shigo aka cika taro da ita tare da Samira wadda ke ta rawar ƙafa tana bawa BILAL kulawa yana share ta ko kunyar su Kaka bata ji.Sun daɗe a wajen sa kafin suka shiga suka gayar da Mahaifiyar su Samira da sauran jama'ar gidan sannan suka yi Musu Sallama. *** Ƙamshin sa ne ya zagaye makeken falon kafin ta kon tafiyar shi mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali ya fara shiga kunnen Abbu da Mubarak da ke zaune suna magana wanda baka jin abinda suke faɗa sai kukan Ac da ke tashi haɗe da sanyin turare mai daɗi da yake garwaye da falon, dan musamman Abbu yau ya tare falon bayan ya tado sa dan in bai fito ba ya koma ya sako shi gaba,dan tun safe yake son ya fito da shi zuwa ƙauyen su Shatou duba aikin da ake yi ya san halin shi tsaf zai kasa yin tafiyar kamar kwana biyu da suka wuce ya zille wa tafiyar wadda sai yau Allah ya nufa za,ayi ta dan Abbu da kan sa ya shiga bedroom ɗin sa ya tado shi dan haka kyakkyawar fuskar nan ta sa take a ɗaure dan gaba ɗaya ji yake an takura masa ba yanzu ya so yin tafiyar ba.Murmushi Abbu yayi yana kallon sa ganin yadda ya tura bakin sa gaba kamar wani ƙaramin yaro ɗan goye.Sanye yake cikin wasu haɗaɗdun riga da wando masu kyau yan Companyn le vanor tsadaddu yana sanye da riga ruwan shuɗi da Black blue jeans sai p cap da yaɗaura akan sa mai ɗauke da rubutu kamar haka ANGEL.cikin tsari mai kyau da burgewa kwantaccen gashin kan sa ya kwanta luff agefe da gefen cap ɗin sa Black blue,sai takalmin sa rufaffu suma masu tsada da kyau blue Black. Murmushi Mubarak yayi ganin yar hararar da ya sauke masa ta gefen ido wadda ba kowa zai iya lura da yayi masa ita ba. Abbu cike da sakin fuska da murmushi ya furta " Masha ALLAH bayan ya gama ƙarewa ɗan na sa kallo ya so ace shigar manyan kaya yayi amma ko hakan babu laifi ɗan na sa kyakkyawa ne Masha ALLAH. Cike da ƙasaita da natsuwar sa ya ƙara sa saukowa fuska ya shagwaɓe a hankali yana zama kusa da Abbu da yake ta murmushi. Kan sa ya shafa a hankali sannan ya ce " Masha ALLAH,Allah ya tsare muku hanya yayi albarka ya baku iyalai masu albarka " . Cike da farin ciki ya amsa da Amin sai dai Abbun ne kawai ya ji shi dan akan laɓɓan sa yayi ta. Addu'ar Abbu ta ƙarshe kuwa bata samu amshi ba sai ma lumshe idanun sa da yayi hakan da yayi ya sa Abbu girgiza kan sa kawai yana cigaba da murmushi shiko Mubarak cike da jin daɗi yake Amsawa da Amin yana yin ƙasa da kan sa a addu'ar ƙarshe ta Abbu da ya ɗan jima kunya. Miƙewa yayi a hankali bayan ware idanun sa sannan a hankali ya furta " Abbu sai mun dawo ". " Allah ya tsare hanya banda rigima da ƴaƴan mutane ". Abbu ne yayi Furucin yana sakin ƙayataccen murmushi wanda MAHAJ da maganar ta bashi mamaki yake ɗan satar kallon Abbun na zancen sa mai haɗe da murmushin sa da ke nuna farin cikin sa a fili,kan shi ne ya ɗan ɗaure masa yana mamakin yadda aka yi Abbu ya sako wannan zancen sai dai kamar zai ce wani abu bayan ɗan ƙara waigowa da yayi ya ɗan ƙara satar kallon Abbun,sai kuma ya sa kai ya fice yana baza ƙamshin sa a ko wane saƙo da lungu. Muby kuwa ƙaramar dariya yayi fahimtar inda furucin Abbu ya nufa kafin shima yayi wa Abbu sallama tare da bashi tabbacin zasu kula da hanya.Addu,a ya ƙara bin su da ita yana Amsawa da Amin har ya fice daga ƙaton falon gaba ɗaya. Murmushi ne ya cigaba da wanzuwa akan fuskar Abbu kafin ya ɗan girgiza kan sa ya miƙe yana gyara zaman hular sa door ɗin da zata sadaka da part ɗin Aiyah ya shiga da Sallama ɗauke a bakin sa. Zaune ya same ta kan darduma tana lazimi dan gama sallar walhan ta kenan dan Aiyah akwai ibada matuƙa. " Aiyah Barka da safiya " Abbu ya furta a natse yana mai tanƙwashe ƙafafun sa kusa da sallayan ta mai taushi da take kai. Kasancewar ta saba bayan gaisuwar bayan Sallahn Asuba idan zai fita irin wannan lokaci dole zai shigo yayi mata ina kwana tare da mata ya fita ta yi masa addu'a. Shafe addu'a tayi tana sakin fuskar ta a hankali ta amsa masa tana furta " Har za,a fita ".Da murmushi kwance akan fuskar ta. " Eh Aiyah zamu yi meeting da shugaban ƙasa ne by 10" Kai Aiyah ta jinjina cike da sakin fuska ta ce " Allah ya taimaka ya bada nasara ya sa awanye lafiya ". " Amin ya hayyu ya qayyum " Abbu ya amsa cike da jin daɗi kafin a hankali kuma murya cike da raunin da yake ɓoyewa ya furta " MAHAJ ma sun fita ƙauyen chen duba aikin nan da ya fara ". Ya kai ƙarshen zancen kamar mai jin tsoron ƙarasa zancen ko tsoron abinda Aiyah zata tai masa. Aiyah kuwa take fuskar ta ta chanza ta haɗe rai kamar an mata saƙon mutuwa shiru ƙaton Falon na Aiyah da ya ke tsit ya ƙara ɗauka sai sautin AC da ke ɗan tashi.Kafin a hankali jiki mace Abbu ya miƙe ganin bata da niyyar cewa komai. " Na tafi sai na dawo " Abbu ya furta a hankali jikin sa mace. " A dawo lafiya ". Aiyah ta furta ba tare da ko ta kalli fuskar Abbun ba dan ta tsani ganin Damuwar sa ko kaɗan shi ya sa ma take ragawa mahaj a gaban idanun sa. Har ya cire rai da tsammani ya kai tsakiyar falon jikin sa mace yana gyara Babbar rigar sa ya tsinkayo Muryan Aiyah na furta " Allah ya sanya albarka ". Ajiyar zuciya ya sauke a hankali kafin ya furta Amin yana ficewa daga sashen gaba ɗaya dan ya san da wa take wannan addu'ar,wanda ita kan ta Addu'ar ya san bata da zaɓi ne yanayin sa ta duba Damuwar da ta wanzu akan fuskar sa. Sashen Ammah ya shiga bai jima ba sai gashi ya fito dan dama sunyi Sallama ya shiga ya ƙara duba jikin Samrah ne da take fama da mura kwana biyu na sanyin ice cream da MAHAJ ya ke ɗan fita da ita tana jido shi. Direct yana fitowa ya shige ɗai daga cikin danƙara danƙaran motocin sa da suke Parkey a gefe gwanin burgewa.Bayan motar ya shige kamar ko yaushe bayan bude masa motar kafin suma suka fice tare da mota ɗaya ta sauran masu kula da shi da suka rage. A ɓangaren MAHAJ kuwa yana fita mota ya faɗa yana gyara zaman sa tare da jingina da seat dan dama masu wankin motocin sun gyara komai an kimtsa sa da duba lafiyar su dan fitar ta su da ta Abbu ɗin. Muby kuwa da zuwan sa shima fuskar sa kwance da murmushi ya shige motar tare da kunna ta suka bar harabar compound ɗin tare da mota uku sai budaɗdiya guda da Abbu ya tilasta masa fita da su dan kariyar lafiyar gudan jinin sa abun son sa da farin cikin sa. A jere suka fice gwanin burgewa bayan wangale musu ƙaton gate ɗin da aka yi koda suka iso dai dai fankacecen gate ɗin estate ɗin take aka wangale musu shi ganin tambarin motar ta sa da duk inda ta shiga sun san mallakin ta duk da ƙarancin shekarun sa ko Amma suna bashi girma sosai kasancewar sa mutun mai tsare gida da kame kan sa ga kowa bayan mahaifin sa. ***A ɓangaren Shatou kuwa yau tun safe ta tashi da fitina dan abinda bata taɓa yi ba yau shi ta yi dan tun gama ayyukan gidan na su da suka zama na ta ne ta shirya ta fice makaranta,makarantar da aka fita da Haushin malam Abu,da Haushin faɗan da Inna ni ta yi mata dan Bibu ta samu ta narka abinda bata taɓa yi ba tun fara wayon ta ko kan ta ta hana dukan Bibu bare wani yau sai gashi daga kawai ya tsokane ta da wasa ta fara jibgar sa bayan kai shi ƙasa dan ma ta shan ma ce sa ne dan Bibu Badai jiki ba yana da ƙirar ƙarfin sa gwargwado,shima da abun ya bashi mamaki sai ya sakar mata jiki ta yi ta kilma da ya ga dai abun na yi ne hakan ya sa ya saki kukan azaba ta yadda Inna ni da ke kusa ta jiyo ta yo kan su cikin mamaki take kallon su kafin ta ɗaga Shatou jikin sa ta na mata faɗa cike da ɗaga murya da ɓacin rai da tsoron da ya dabaibaye ta na wannan sabon abun da ya faru. " Daga kawai na ce mata nan gurin Shanaye bai sharu ba shikenan ta hau ni da bugu,kuma ma tsokanar ta nake yi ". Inna ni kai ta girgiza bayan gama sauraren Bibu da ya kai ƙarshen zancen yana Shesshekar kuka. Ita kuwa bata ce ƙala ba har Inna ni ta gama faɗan ta kafin ta bar wajen,ta wuce ɗakin ta tana kumburan baki. Inna ni kuwa da ke jin kamar ta riƙo ta ta kai mata bugu ko ta jibge ta kai kawai ta girgiza dan ta san ba lallai shatoun ba ce haka kawai jikin ta ke nuna mata kamar ba asalin shatoun ta bace sai dai bata da ikon yarda da hasashen ta dan haka ta Rarrashi Bibu ta taimaka masa ya shirya ya wuce makaranta dan yau bai ko tsaya jiran Shatou ba Inna ni tace ya wuce,ita kuwa tana gama shiryawa cike da kumburin ta,ta bar gidan ba tare da tayi wa ko Inna ni sallama ba,sauƙin ta ma an gama mata ayyukan ta. Dan shi Baffa na yau da wuri ya fita kasancewar yau ranar kasuwa ce. Wannan kenan. Tunda ta isa makaranta bata kula kowa ba har su Amina duk yadda suke ƙoƙarin jan ta jikin su amma abu ya ƙagara dan haka suka zuba mata ido ganin abun bana wasa bane kamar harda cika take tana batsewa kuma hasale take rigima take nema ido rufe dan haka kowa ya sha jinin jikin sa cikin su cike da tsoron abinda zai je ya dawo. Koda aka tashi tara ƙin fita tayi ta hakimce akan yar kujerar su koda suka dawo su Amina ta cinye kusan filin mutun biyu kuma fuskar nan a haɗe babu alamar zata iya sauraren maganar wani,dole suka bar mata seat ɗin gaba ɗaya. Malaman su duk wanda ya shigo yayi Magana bai samu kulawa ba sai su fita iskan ta.A haka aka tashi makarantar sai dai koda aka tashi duk itace ta ƙarshen fita su Amina bayin Allah kusan ƙarfe uku haka suka zauna zaman jiran ta kamar abun dole.✍️ Update zai riƙa sauka a koyaushe harmu kammala Book iñ sha ALLAH. Sai kunyi haƙuri yanzu yadda kuka san mai Aljannu barci haka nike kamar kar mu gama exams da ciwon da na tashi wallahi yanzu da anyi sallahn isha Bani kai 😹🥺labari sai barci dan haka kuka ji shiru shekaranjiya.Wayan ma sai dai mother ta kwashe ta in kwana ya debeni ba ayi hakuri da duk yadda page ɗin ya zo naso ace yafi haka yawa. Ina alfahari da ku.💃👌🤝✍️ Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________3️⃣7️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* 🕳️💕🕳️💕🕳️ Koda ta fito haka ta yi gaba ta bar su tsaye kafin cikin shakkar ta suka bi bayan ta,shima Bibu kasa tafiya yayi,har sai da Shatou ta fito sannan ya bi bayan ta abun ka da ɗan uwa sai gashi ya jera da ita har ya manta abun da ya faru ɗazu kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kan ta. A gida kuwa hankalin Baffa na da ya dawo ya tarar babu kowannen su gida kasancewar lokacin tashi yayi hankalin sa ya tashi,dan koda yayi wa Inna ni zancen rashin dawowar ta su su biyu da wuri wanda itama tana cike da tashin hankali musamman da ta san yanayin da Shatou ta fita sai dai tayi ƙoƙarin dannewa tana kwantarwa da Baffa na hankali. Har fita yayi niyyar yi zuwa nemo su Inna ni ta hana tace suna hanya. Su Amina kuwa jikin su a sanyaye suke bin bayan Shatou da Bibu da Tayi masa kallo ɗaya ta ɗauke kai kamar taga kashi tunda ga lokacin jikin shi yayi mugun sanyi dan haka ya haɗe dariyar da ya zo da ita da murmushi a haka suka cigaba da tafiya kafin kuma yaji ta ja tsaki ta ja burki kallon ta suke yi dan tunanin abun da zata yi kafin su ankara ta yanka a Guje sai dai ƙurar ta kawai suka hango Bibu haɓa ya riƙe sai dai bai yi mamaki ba dan ba yau ne farau ba sun saba sai dai yanayin na ta akwai ban mamaki da tsoro a cikin sa dan ko magana bata yi da kowa ba tun wadda suka yi da safe ta koma Kurman karfi da yaji. Su Amina ma da su jawairiyya basu yi mamaki ba sai dai su Abin ya basu dariya mace kamar mai Aljannu sai dai yau sun ƙara tabbatar da hasashen su Shatou na da iska akan ta dan gaba ɗaya yanayin nata da masu ƙwankwanmai yayi kama dan haka basu bi ta ba suka cigaba da tafiyar su kafin kowaccen su ta iso kofar gidan su ta shigewar ta rai jagule. Bibu kuwa shima ta fiyar shi ya cigaba da yi a tsakanake yana mai cigaba da mamakin sabon halin Addan sa Shatou sabon hali man dan bugun da ta masa da safe bata taɓa masa shi ba tun suna wasan ƙasa na yara kuwa bare yanzu da suka fara hankali da wayau irin na manya. Koda Shatou ta isa gida haka ta faɗa babu sallama tana nishi sai dai tana shiga ta yanke jiki ta faɗi cike da tashin hankali Baffa na da Inna ni suka yi kan ta,Inna ni cikin zuciyar ta kuwa take ayyana dama ta sani sai dai tana fatan kar shatou ta furta komai a gaban Baffa na dan bata shirya Son ya san wani abu ba game da abinda bata da tabbacin shi a yanzu, abinda ta ke yiwa kallon labarin ƙanzon kurege,labarin hikaya,domin kuwa har yanzu kan ta ya kan cigaba da ƙullewa a duk lokacin da ta tuna da zantukan Shatou ɗin sai dai zuciyar ta na bugawa da damuwa a duk sa,a da daƙiƙar da ta tuna kalaman nan taya zata gasgata su,taya zata gasgata zancen Mutanen ɓoye,Halittar da suke da muguwar ƙarya a doron duniya,dan kaso ɗari cikin maganar su kashi biyu ƙarya ce. Numfashi ta sauke mai zafi tana cire wa Shatou Guntun hijab ɗin ta bayan Baffa na ya ɗaura ta akan tabarman da yake kai bayan ya tallabo ta. Hankali tashe Baffa na yake kallon Shatou cike da mamakin yanayin ta da bai saba gani ba sai yau kuma bai taɓa ji ba ko a bakin Inna ni dan su ɗin ma basa zuwa a gaban sa. Idanu ya zuba mata yana ƙare mata kallo kafin ya sauke a jiyar zuciya da numfashi yana jin jijiyoyin jikin sa na kuncewa da ɗai ɗai musamman na kansa da tunani yake neman tarwatsawa a dai dai wannan lokaci.. "akwai matsala,Indai har abun da nake zargi ne ". ya furta a ƙasan zuciyar sa wani irin damuwa na bayyana akan fuskar sa.Addu,oi ya fara tofa mata ganin yadda idanun ta suka kakkafe lokaci ɗaya sannan jikin ta ya ɗauki ciccira kamar mazari.Inna ni wasu hawaye ne take dannewa gudun kar ta nuna damuwar ta fili raunin da take ɓoyewa ya bayyana Baffa na ya fahimci wani abu hakan ya sa ta rintse idanun ta da ƙarfi tana haɗiye ajiyar zuciya ran ta a jagule wata sabuwar damuwa na samun matsugunni a cikin zuciyar ta wadda take ƙara girmama a duk lokacin da Shatou ta samu kan ta a wannan yanayi.A hankali bayan Baffa na ya yayyafa mata ruwan addu,an da yayi yanzu jikin ta ya fara lafawa daga girgizan da yake yi sai dai jikin na ta ya gashe kamar ana rura wuta a cikin sa har hucin yana dukan fuskokin su. Cike da tausayin ta Baffa na ya shafa ma idanun na ta da suke kafe Ruwan Addu'a kafin suka koma yadda suke sai dai basu rufe ba gaba ɗaya suna ma ɗan yin blinking kaɗan. " SHATOU wa tahh " Baffa na yayi zancen cikin sanyin murya mai haɗe da damuwa. Ko motsi bata yi ba duk da cewa ta ji cewar Baffa na ne dan da alama bata dawo hayyacin ta ba har yanzu. Baffa na ganin haka ya sa ya ƙara furta cikin son tabbatar da zargin sa. " Wace ce domin na san wannan ba shatou bace zaki yi magana ko sai an ɗauki mataki yanzu ". Ya kai ƙarshen zancen yana kafe Shatou da ido.Aiko yana aje ayar zancen ta Gwale manyan idanun na ta masu haske ta ɗaura kan sa kai daga nin yadda take zare su ka san ba lafiya ba. Murmushin gefen baki ta saki kafin ta juyar da ƙwayar idanun ta kan Inna ni da take makure idanun ta Sun rikiɗe sun sauya ga hawaye kwance cikin su wanda kowanne irin lokaci tana iya fashewa da kuka. Idanu Inna ni ta saka cikin na Shatou ɗin duk da idanun na ta kallon su ciki da ciki akwai tsoro domin ko ƙyafta su bata yi. Kai Inna ni ta girgiza mata,bayan hango bakin ta na motsi kamar kullum idan sun zo da magana.Sai dai ba zata so ta ji komai ba a gaban Baffa na ba domin dole ne ya san abun da ta furta mata. Aiko kamar ta fahimci abinda Inna ni ke nufi sai kawai ta ɗauke idanun ta,ta mayar kan Baffa na sai da ta masa kallon yan seconni kafin a hankali ta mayar da kan ta gefen Inna ni sai kuma ta fashe mata da kuka. Wani irin bugawa ƙirjin Inna ni yayi wanda har sai dai Baffa ba ya ga alama dan idanun ta sun fito waje sosai na tashin hankalin da ya bayyana a gare ta domin kuwa ta san kukan na Shatou Ko tace mutanen Shatou bana lafiya bane,kuka ne da ke nuna akwai matsala daga abun da take faɗa mata wanda har yanzu ta ka sa gasgata lamarin dan bata san ta inda zata fara ba,domin kuwa abune mai ɗaure kan mai tunani da hankali. Baffa na kuwa haka kawai ya samu kan sa da kafe Inna ni da idanun sa yana kallon yanayin ta da karantar sa kafin a hankali ya ɗauke kallon sa daga gare ta yana sauke numfashi sai dai zuciyar sa ta fara masa wani zancen kamar na da walakin akan yanayin da Inna ni ta shiga dan bai taɓa ganin ta a wannan

Chapter 29 of 39