Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
YA SA KUKA JI SHIRU,KUMA IRIN ZAZZAƁIN NAN NE MAI TAKURA🥲😔.ALLAH KA BAMU LAFIYA MAI AMFANI.🤲 Masoyan SHATOU a yi haƙuri zamu koma gefen ta a next page in sha ALLAH. Like share,and comment 🙏 Wannan littafi na kuɗi ne. Amma in sha Allah Zan baku page goma sha biyu free kamar yadda nayi niyya.. Masu son fara yin payment zaku iya farawa ga details a ƙasa👇 *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh 💞 *TAFIYAR TA DABANCE SAI AN BIBIYA AKAN GANE HAKAN.✍️* _Typing_ *💋KURMAN ƘADDARA💋* *©®Faiza Almustapha Murai* *FA'EEH BG*✍️ *BOOK ONE* free pages👌 P..0️⃣7️⃣ >>>>>>>>>>>> > >>>>>>>>>>>>> *CONTACT DIS LINE 👉08069059746 FOR ADVERT.* *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* Channel link https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y Posting room link https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn *LITAFFAN MARUBUCIYA* *A MAFARKI NA SANTA* *RAYUWAR MU A YAU!* 🎀🎀🎀 ***Sai da suka ci girkin Inna ni sannan suka watse kamar kar su rabu. Dare nayi hankalin Inna ni ya fara tashi ta san cewa SHATOU dole sai ta fita, fira suke yi amma hankalin ta na kan ta har suka ɗauko abun karatun su Baffa na ya fara bita musu bata natsu ba.Kamar kullum sallar isha'i ce ta sanya su miƙewa domin gabatar da sallah akan lokacin ta,musamman ta isha da take mai nauyi. A tsakar gida tayi Sallah tare da Inni amma duk da haka hankalin ta ba a kwance yake ba,Suna gama wa Nan bacci ya ɓingire ta wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar inni ni ganin baccin take yi Dagaske.Gyara mata kwanciya tayi ta ɗan sha iska kafin su tashi ta mayar da ita ɗakin ta. Addu,oin ta ta cigaba da yi bayan ta gabatar da shafa'i da wutiri. A haka su Bibu suka dawo daga masallaci suka tarar da ita tana baccin ta cike da natsuwa. Murmushi Baffa na yayi yana gyara mata hannun ta ɗaya daya lanƙwashe. Sannan ya furta " Shatouwa da bacci da wuri yau,halama dai A'ie Addu,a kika mata ta bacci da wuri ".? Inna ni dariya tayi tana furta " gata nan dai,nikamm babu ruwa na Allah dai ya dubi zuciya ta ya kwantar muna da ita da wuri yar neman,dan haka karku ƙalubalance ni" Ta kai ƙarshen zancen tana Murmushi tana miƙewa ta zubawa Bibu abincin sa da ya bai ci ba ɗazu yace ya ƙoshi sun ci abinci a makaranta kuma cikin shi ya cika sosai. Dan haka kowa yaci nashi ba dashi ba. Fira suka taɓa kaɗan kafin aka mayar da Shatou ɗakin ta,Sannan dukkanin su kowa ya koma na sa ɗakin bayan sunyi wa juna sai da safe. Kamar ko da yaushe bayan dukkanin sawu ya ɗauke ta miƙe bayan tabbatar da Baffa na yayi bacci ta miƙe ta haɗe kai da gwiwa ta fara wani irin kuka mai tsuma zuciya,kuka ne mai fitowa daga ƙasan zuciyar ta wanda yafi na ko yaushe,yau zantukan SHATOU sun ƙara mata wani irin rauni a cikin zuciyar ta,ta kusa ɗaukar Awa tana yin wannan kukan mai cike da rauni da kewa sannan ta share hawayen ta ganin tana neman jazawa kan ta ciwon kai. Miƙewa tayi ta fita da zummar wanke fuskar ta sai dai Turus ta ja ta tsaya domin kuwa bakowa taci karo dashi ba face Baffa na fuskar shi cike da tausayi idanun sa sunyi jazir dan akwai farin wata sosai. Kan ta ta sauke ƙasa,ta raɓa shi tayo alwallah.Shi ma bai ce mata ƙala ba har sai da ta kusa shigewa ɗakin na ta sannan ya ambaci sunan ta cike da tausayin ta. " Komai yayi tsanani maganin sa Allah,hakan da kika yi shine dai dai, Sannan ba zan gaji da maimaita Miki ba A'ie ki fito ki faɗi wata maganar da zata sa mu fahimci wani abun da yake damun ki,zancen da kika bani a baya ba zai iya saka a fahimci komai ba,har a san abun yi,amma kiyi tunani ina son sanin komai dake faruwa,amma ba zan matsa Miki ba ina jiran ranar da kika tashi faɗa zan saurare ki ". Yana gama maganar sa ya shigewar sa ɗakin sa dake kusa da nata kaɗan. Jikin ta ne ya ƙara mutuwa wani sabon kukan na son ta so mata dan Dagske tana cikin damuwa,kuma tana buƙatar mai Rarrashin ta. Shigewa tayi ta shimfiɗa sallaya ta tayar da sallah sai da tayi raka'a shida sannan ta fara kai kukan ta ga Ubangiji hawaye na kwaranya a cikin idanun ta. " Allah idan har abun da mutanen Shatou suka faɗa gaskiya ne Allah ka kare mini su,a duk inda suke,Allah ka bata lafiya,Allah ka yaye mata,Allah bani da tsimi bani da dubara Allah ka yaye mini damuwa ta,Allah ka kawo mini mafita,Allah ka kare mini rayukkan su a duk inda suke " Kuka ne ya ƙwace mata mai zafi da raɗaɗi da ƙuna sai da tayi mai isar ta anan sannan ta kwanta nan kan sallaya bacci ya kwashe ta mai nauyi. Baffa na dake tsaye bakin ƙofar ɗakin ne da ya ji komai da take faɗa ya koma ɗakin sa da sauri cike da tambayoyi a cikin zuciyar sa ya je da zummar ƙara bata baki ya ji abinda bai san inda zai saka kalaman na ta ba da ba komai ya fahimta ba sai dai ya sanya su a cikin zuciyar sa cike da mamakin mutane shatoun da ya ji ta faɗa wanda shi dai duk iya sanin sa da yar ta sa ba ta da wasu mutane tun da basu taɓa tashi ba bare a gan su. Addu,ar kwanciya bacci yayi bayan ya ƙara tofekke su Shatou da Addu,a ya sayo gidan sannan ya kwanta shima cike da tunani a haka har bacci ya kwashe sa jiki mace. Yau Litinin hakan ya sa tun da suka tashi sallar asuba basu koma bacci ba,saboda yin ayyukan gidan da wuri da kuma zuwa makaranta akan lokaci tsaf suka shirya bayan sun jido ruwa tare da yiwa Inna ni share share,karin kumallo suka yi sannan suka fice a tare bayan yiwa iyayen na su mun tafi.Addu,a suka bisu da ita.Ba a ɗau lokaci ba shima Baffa na ya fice kasuwa dan yana da ɗan ƙaramin shago a kasuwa yana siyar da kayan farauta duk wani nau'in kaya na farauta,da kuma Ganyen shayi ko wane iri ne ana samun sa a wajen sa. Tun da suka isa makaranta tsirarun yaran da ke wajen ke kallon su musamman shatou sai su kalle su suyi dariya sai suyi gaba.Tun abun na bawa shatou mamaki har ya daina bata.Bata ce ma Bibu komai ba haka shima sai dai kowa ya shigewar sa aji cike da mamakin kallon da ake musu. Da shigar ta Ajin su ta ji ƙana nan maganganu na tashi sama sama gashi sai kallon ta suke yi.Kamar ance ta kalli allo saboda ta iya karatun Hausa tsafff ta zaro ido tana kallon Allon da ya ƙunshe da rubutu kamar haka " daga yau ni Shatou suna na ya koma Kosongo,ko shatou kosongo ". Abun gugar allo ta ɗauka tana furta " Uban wa yayi wanann rubutun nayi imani da Allah ko waye yayi shi sai ya ɗan ɗani azaba ta sai ya gwammace Ni shatou banzo duniya ba ". Tana yin maganar cikin ɓacin rai da haushi tana gugar rubutun,su dai sauran yan Ajin su kowa zuba mata ido yayi wasu kuwa dariya suke yi ƙasa ƙasa ba damar a fitar an san halin ta. Sai da ta goge Allo tass sannan ta dawo tana nishin Masifa tana kallon yan Ajin na su,Amina ta hango daga gefe wadda tayi tagumi dan ta san yau akwai matsala taso ta goge rubutun wasu yan Ajin suka hana ta,ashe ma a banza dan kowane aji dake makarantar anyi rubutun,rubutun da ma yake chakuɗe kamar na yan koyo. " Amina wa yayi rubutun nan,waya tsokano fitinar da tafi ƙarfin sa,na rantse da Allah idan kin san kowaye karki ɓoye ni,dan idan na gano wallahi sai na bar ƙawance dake " Tayi hakan ne dan ta san yadda Amina ta tsani kalmar ta san dole in ta sani ba zata taɓa ɓoye mata ba. Idanun Amina cike da hawaye ta ce " Wallahi na yi miki rantsuwa da Allahn da ya halicce ni ban san wanda yayi shi ba nidai ko da na zo na tarar dashi na so na goge suka hana ni,Kuma Kiyi haƙuri gaba ɗaya ajujuwan makarantar nan aka yi rubutun amma ni da su Ramata mun goge shi wanda koda muka goge wasu sun riga sun gani ". Ran shatou ne ya ƙara ɓaci kamar ta fasa kuka dan da gaban su Inna ni ne da ta yi kuka sosai yadda ran ta yake ɓace ko zata rage hasahi. Zama tayi bata cewa kowa ƙala ba har su Ramata da suke son cewa wani abu,amma bata basu dama ba. Ajin sai kallon ta suke yi kowa na son ya maimaita sunan yana gudun ruwan masifa dan daga Mazan har matan su babu wanda take shakku. Har malamin su ya shigo yayi karatu bata sauko ba duk yadda yake jan ta da magana saboda tana cikin ɗalibban Ajin masu hazaƙa tana da kai, sosai take gane karatu both Arabi da boko. Har aka tashi makaranta shatou bata wani gane ma kan ta ba saboda yadda ta sanya son gane wanda yayi rubutun ta rasa wanda zata hasasowa gaba ɗaya kan ta har ya fara ciwo saboda tunani. Ko ba,ayi ba daga makarantar ta kama hanyar gida,daga zuwa fitsari,da shigar ta ko sallama ba tayi ba ta shige ɗakin ta, littafan ta na makaranta ta janyo tun na aji ɗaya da suke ɗauke da sunayen halittu a bayan su saboda Amina ta faɗa mata ance mata wata dabbace ake kira haka mai Shegen gudu. Tana cikin dubawa kuwa taci karo da ita mummunar halittar dabbar ran ta ne ya ƙara ɓaci har wani numfashi ta ke sauke wa na yadda zuciyar ta take cike da Masifa.Kuka ta fashe dashi na yadda aka haɗa sunan ta da dabbar.kukan ta ne ya ankarar da Inna ni Dawowar ta, kasancewar tana sallah koda ta shigo.Kuma cikin natsuwa ta shigo babu guje guje. Cike da mamaki ta faɗa ɗakin na ta zaune ta isko ta haɗa kai da guiwa ta na ta darzar kuka. " Ke lafiya, , wa ya mutu ne,ina kika baro mini yaro na " Inna ni ta jero kalaman cike da son samun amsar su. " Yana makaranta ni dawowa nayi saboda kaina na ciwo yake ". " Shine saboda kan ki na ciwo shatou sai ki zauna kiyi ta kuka".takai ƙarshen zancen cike da tausayin ta dan a tunanin ta Dagske zazzaɓin ne. Ficewa tayi sai gata ta dawo tare da magani da ruwa. Ɓalla mata tayi ta bata babu musu kuwa ta karɓa dan ta san halin inna ni yanzu sai ta hasala dan tana da saurin hasala dan kamar duk ita ta biyo. " Sannu,yanzu ki tashi ki watsa ruwa sai ki samu ki ci abinci ki kwanta ko ". Kai shatou ta gyaɗa kafin ta miƙe ta cire kayan jikin ta nan gaban Inna ni ɗin ta koma daga ita sai ɗan kan fai dan babu ruwan ta Indai ta so cire kayan jikin ta kowa ke wajen tana iya wa sai dai bazata cire gaba ɗaya ba,gaban Inni ni kuwa zama take da ɗan kanfai.Inna ni tayi faɗa amma ta kasa bari,har gaban Bibu wata rana ta kan cire kayan jikin ta. Shi ko yayi ta tsokanar ta da "Adda SHATOU ƙatuwar banza mai cire kaya a gaban mutane ". Daga haka kuma suyi ta zagayen gidan har su gaji. Kai Inna ni ta girgiza tana murmushi ganin yadda ƙiren dangin na shatou suke maƙale a jikin ta,lallai girma yana hanya. Jikin ta ne ya mutu mutus hakan ya sa ta fice daga ɗakin tana share hawayen da suke son silalo mata masu zafi cike da tausayi Shatou. Ruwan wanka ta haɗa mata ta kai mata makewayi. Shatou na fitowa ta san cewa ta kai mata su chan hakan ya sa ta wuce makewayin. Sallamar su Amina ce da Bibu ta cika gidan. Amsa musu Inni ni tayi fuskar ta wanze da murmushi ta furta " Ya na gan ku fuskokin ku kamar babu lafiya ". " Eh dama Shatou ce " .... Amina ce ta fara maganar sai kuma ta yi shiru. Cigaba da maganar ki. Nan ta kwashe komai ta faɗawa Inna ni. Kai Inna ni kawai ta girgiza ita sai ma abun ya bata dariya wai shatun ta ce ake kira da kosongo sunan ma abun dariya. Yar dariya tayi kafin ta furta " Oh ni indo kowa ye da wannan ɗan yen aiki " ita kuma shine ta dawo ta zauna tana rusar kuka saboda sakalci ". Ku tafi kawai sata sauko kunji. " Toh " suka haɗa baki wajen faɗa kafin suka bata jakar ta suka fice daga gidan. " Inna ni,Adda Shatou fa na san bazata bar zancen nan ya tafi ba sai ta nemo wanda yayi aikin nan ".Furucin Bibu. Kafin ta basa amsa sai ga shatou ta fito tana bin su da kallo dan taji duk taji komai. Alwallah tayi bata ce komai ba ta shige ɗakin ta. Da kallo duk suka bita ganin yadda ran ta yake jagule har yanzu. Murmushi Inna ni tayi tana furta "Lallai ran maza a ɓace yake,Bibu kuka fa ta zauna ta shara,dole na taka mata burki ta haƙura. Ɗakin ta bi shatou tare da jakar ta sallah ta tarar da ita tana yi,aje mata jakar tayi tare da zaunawa har sai da ta gama sallar tayi Addu,oin ta, Sannan ta kamo hannayen ta,ta ce " Shatou na kiyi haƙuri kinji koma wane ne ki bar shi da Allah,zai saka Miki,kuma ma shatou ai ba abun tashin hankali bane tun da bakalar dabbar zaki koma ba.Ta kai ƙarshen zancen tana sakin yar guntuwar dariya tana kallon yar Tata cike da ƙauna. Kallon Inna ni tayi kafin ta furta " Toh " tana cewa haka bata ƙara cewa komai ba. " Allah yayi Miki albarka " Inna ta furta cike da murmushi tana ficewa daga ɗakin tare da sanar da ita abincin ta Bibu zai kawo mata idan ta ci ta kwanta ta huta kafin lokacin makarantar su yayi.✍️ *** " Hhhhh ki bar wannan aikin kawai an riga ki,kuma anyi aikin mafi hatsari,aiki ɗaya za,a Miki yanzu shine ƙara hana su kusantar juna,wannan shine kawai zaki yi " Cike da mamaki take kallon Bokan na ta da ke zaune kamar wani malami sai buge buge yake yi a ƙasa. " Amma Boka Gangaro yaushe hakan ya kasance dama an daɗe da yin aikin ne ". Matar da ke zaune gaban sa tayi kamar wata baiwa tayi Furucin tana sanye cikin kayan alfarma da mayafin ta na manyan mata,mai tsada. " An daɗe da yin sa,ya fi ƙarfin shekara goma,anyi shi tun kafin zuwan su duniya,kuma yana nan yana bibiyar su gaba ɗayan su,ki bar aikin a hakan karki shiga cikin wannan gamami aiki ne babba da ya ci shekaru dan haka ki fitar da hannun ki ". " Boka Gangaro ko zan iya sanin wanda yayi aikin ". " A'ah karki matsa kar ki jamin bala'i,aiki ne na duhu baƙaƙen Aljannu ke riƙe da shi ,Idan kika matsa zamu halaka mai aikin fitinanne ne,ki iya tunanin ki kar ki ƙara maganar kuma kar ki sanar wa da wani ki bar shi a cikin ki domin zaki iya shiga haɗari,ke kan ki,aiki nane ya cece ki da tuni an gama dake ". Idanu ta zaro cike da tsoro kafin ta miƙe bayan karɓar yan ƙulle ƙullen na boka Gangaro sannan ta fice da baya daga ruɓaɓɓiyar rumfar sa,bayan ta ajiye masa manyan kuɗaɗe kamar yadda ta saba. Sai da tayi tafiya mai nisa Sannan ta fice daga cikin ƙungirmin dajin.Motar ta,ta hau ta tada tana ƙara jan Niƙaf ɗin ta. Sai dai zuciyar ta cike take da mamaki da al'ajabi me ya sa bata taɓa sani ba sai yau.To waye ne yayi mata rigaye gashi ya ce aikin ya daɗe wane mara imani ne wannan.Lallai dole ta ƙara riƙe Boka Gangaro kar ta rasa rayuwar ta. Wal, iyazubillah 😭 Hmmm.🙄 Hmmmmm Kuna ganin haƙurin nan, na Shatou ya kai zuciya kuwa ? Wa kuke tunanin ya aikata wannan aiki ? Gaskiya duk wanda ya tado muna da rigima bai kyauta ba.🚶😂 Like share,and comment 🙏 Wannan littafi na kuɗi ne. Amma in sha Allah Zan baku page goma sha biyu free kamar yadda nayi niyya.. Masu son fara yin payment zaku iya farawa ga details a ƙasa👇 *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh 💞 *TAFIYAR TA DABANCE SAI AN BIBIYA AKAN GANE HAKAN.✍️* *_Typing_* *💋KURMAN ƘADDARA💋* *©®Faiza Almustapha Murai* *FA'EEH BG*✍️ *BOOK ONE* free pages👌 P..0️⃣8️⃣ >>>>>>>>>>>>>> > >>>>>>>>>>>>>>> *CONTACT DIS LINE👉08069059746 FOR ADVERT.* *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* Channel link https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y Posting room link https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn *LITAFFAN MARUBUCIYA* *A MAFARKI NA SANTA* *RAYUWAR MU A YAU!* 🤳🤳🤳 Har ta isa aka wangale mata ƙaton gate ɗin gidan zuciyar ta cike take da mamaki mai yawa.Ta so kiran ƙawar ta ta sanar da ita sai dai ba zai yiyu ba saboda gargaɗin da Boka Gangaro ya mata dan haka ta kame bakin ta tayi shiru. *** A ɓangaren su LINA kuwa bedroom ɗin su suka koma kasancewar lokacin makarantar islamiyya yayi suka yi shiri kafin Yayan su ya kora su da kan sa dan ya saba musu hakan idan suka buga latti saboda mafi yawan lokutta suke tsayar da yan uwan na su,kasancewar a tare ake kai su makarantar islamiyya dan dama dalilin raba su shine fitina da suke yawan yi a mota. A jere suka fito cikin shirin su kowacce riƙe da jakar ta mai ɗauke da Alqur'ani da sauran littafin sanin addini saboda makarantar suna karatu sosai gashi ana zube kuɗaɗe masu tsoka a cikin ta. Gwanin burge wa kowaccen su ta sha niƙab da Safa saboda bin ƙaidar dokar makarantar amma duk da haka LINA wata rana haka take shiga makarantar,ko yanzu ma bata ɗaura nata ba,ƙiri da muzu wai takura ta yake yi tun malamman basu fahimci halin ta ba har suka fahimci haka take idan suka ce su tilasta ta mata saka wa dole za,a samu matsala domin zata iya hinjire musu shi yasa suka saka mata ido sai gashi abun ya zame mata shan ruwan tsuntsaye wata rana ta saka wata rana ko ta ƙi sakawa. Ya'u ne driven su shine mai haƙƙin kula da kai yaran islamiyya hakan ya sa ya ke shirin sa da wuri amma duk da haka sai sun ɓata ma kan su lokaci da shi.Yau dai Allah ya taimaka saboda kasancewar wanzuwar ya yan nasu hakan ya sa kowaccen su tayi shirin ta da wuri.Koda suka fito sun tarar da Hamrah,da Nina kowaccen su ta hakimce a kujera suna taɓa fira kaɗan kaɗan. Cikin washe baki REENA ta ambaci sunayen su,suma haka cike da ƙuruciya suka amsa mata suna matsa mata space alamar ta shigo bayan kusa da su duk da motar irin mai seat da yawa ce prado new design.Da sauri kuwa ta shige tana zama tsakanin su. Ita kuwa REENA bata cewa kowaccen su ƙala ba haka su ma sai ma wani haɗe rai da tayi tana bin su da Harara daga cikin niƙaf ɗin da ta saka yanzu,dan duka haushin su take ji akan su Yaya B ya taɓa tabkar ta.dan ko wancan zuwan na sa ya tabke ta akan Hamrah da ta zaga kafin kuma ta hau ruwan cikin ta tana ta nusa.ba,a ma zancen Nina da basa ga maciji dan itama fitinanniyar kan ta ce duk da wata rana tana shayin REENA dan ta taɓa cire mata haƙori a achan baya,Allah ya taimake ta lokacin suna fira ne. Tana zama ya'u ya Kalle ta yana washe baki yana ɗan gyara sumar kan sa a madubi kasancewar sa saurayi mata shi ya furta " Yan matan Ummah yau waya taɓa mu " Dan shi dai haka kawai Allah ya ɗaura masa son REENA tana matuƙar burge shi yana son mace yar tujara,kamar ta. Mugun kallo ta jefa masa kafin ta taɓe bakin ta ta mai da fuskar ta kan glass tana ƙarewa haɗaɗɗiyar estate ɗin ta su kallo da koda yaushe ƙara kyau take yi kamar kullum ake renovation nata. Murmushi ya ƙara saki kafin ya furta "Allah ya huci zuciyar Hajiya ALINA SS ". Murmushi ne ya suɓuce mata jin ya kira ta da sunan manya wanda ya sanya ta jin kanta yayi wani ƙato. Sai dai bata kalli ko gefen da yake ba ta cigaba da kallon wajen. Haka ya tada mota yabar estate ɗin bayan wangale masa ƙaton gate da aka yi. Wani tunanin da ya shige sa ne ya san ya shi jan mugun tsaki yana bin motar da ƙwafa dan duk abinda ke faruwa a ciki Yana gani saboda ba tinted glass bane da motar ta su.Lallai dole ya taka wa wannan Drivern burki ya fara wuce gona da iri akan ƙannen na sa. Shigewa yayi part ɗin da babu kowa a cikin sa sai kayan dake zube na alfarma a ciki da wani irin ƙamshi. Da shigar sa ya nemi waje ya zauna yana sauke ajiyar zuciya,abubuwa da dama suna dawowa masa aƙwakwalwa hawaye ne masu zafi suka silalo masa kafin ya yi ƙarfin halin share su yana ambaton sunayen Ubangiji zuciyar sa na cigaba da ƙuna da raɗaɗi wanda ya daɗe yana dunƙula na rashi,shekara da shekaru a duk lokacin da ya tuno da abun da idanun sa suka gane ma sa sai yaji wata iriyar zafi ta mamaye zuciyar sa baida tabbacin abinda ya gani.Dan haka tsawon wannan shekarun ya rasa wazai tun kara da wannan maganar wa zai masa fashin baƙi akan ta.Sai dai kunya da nauyin maganar sun sa ya kasa iya kallon kowa da ita kuma ya hana zuciyar sa saka masa mugun dafi mai illa a tsakanin makusan tan sa.Kuka ne ya ƙwace masa mai zafi sai da yayi mai isar sa sannan ya miƙe ya shige wani haɗaɗɗen bedroom da yake ƙal ƙal saboda kullum cikin gyaran sa ake,saboda umurnin sa ne. Kwanciya yayi akan gadon inda take bacci ya kwashe sa anan cike da tunani iri iri mai cike da mafarkayya masu daɗi da marasa daɗi. Shine bai farka ba sai ana kiraye kirayen sallar la,asar a Babban Masallacin dake cikin estate ɗin. Miƙewa yayi da sauri ya faɗa toilet wanka ya ɗauro tare da alwallah sannan ya chanza kaya saboda yana da wasu sutura anan.Wani ƙaramin frame yayiwa kiss sannan ya fice zuwa masallacin da ke cikin estate ɗin ta su. Bayan fitowar su Sallah kuwa sai Alokacin ya fara kame kame ganin yadda Mai gayya Alhaji Sada tsohon Arziki wanda dukiya ta ƙara wa tsufan sa kyau yake kallon sa yana taɓe baki.Kafun ya ɗauke kan sa daga idanun sa yana mayarwa kan Junaid da yake gayar da shi cike da girmamawa. Murmushi ya ƙaƙalo dan ya san cewa yayi laifi tun safe ya shigo bai neme sa ba sai yanzu da sallah ta haɗa su.Babu ma.wanda yaje ya gayar a cikin iyayen na sa duk da ya san suna nan kuma yana da niyyar yin haka zuwa dare. Junaid ma cike da farin ciki ya matsa kusa da ɗan uwan na sa da ya lura da shi yanzu ya rungume sa yana masa sannu da zuwa kasancewar ya ga alamar sa a cikin estate ɗin ga sojojin sa na birjik. Waye Alhaji Sada Saleh( SS ) *TUSHE* SS Babban ɗan kasuwa ne da yayi gwagwarmayar rayuwa da turawa iri iri a fannin kasuwan cin sa kuma shine magini na arzikin wannnan zuri,a,shida ɗan uwan sa. Sada Saleh,Haifaffen garin Kaduna ne su biyu suke ga mahaifin su shida ɗan uwan sa,Usman Saleh tun farkon asali mahaifin su yana ƙaramin kasuwan cin sa a ƙofar gida irin na ƙaramin shago haka kafin A hankali Allah ya buɗe masa ya cigaba ya mayar dashi kasuwa daga nan ne komai ya fara chanza wa cigaba ya samu mai yawa.A lokacin kuwa Sada da ɗan uwan sa basu wuce shekaru bakwai, shidda a duniya ba,dan babu tserewa a tsakanin su mai yawa, dan haka suka taso cikin Gata saboda sune ƙwal a gun iyayen su,sune kyautar da Allah yayi masu bayan barowar su mahaifar su,dan Saleh mata ɗaya yake da ita Aisha,Sada Saleh shine Babba sannan Usman Saleh.Iyayen su irin fulanin nan ne da suka baro garuruwan su saboda tsaro suka fara gina kan su a cikin birni cike da gwagwarmayar rayuwa. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya ana ta samun cigaba ta ko ina,su Sada da Usman kuwa suna cigaba da samun ingantaccen kulawa da ilmi mai kyau.Kwatsam ana zaune wata rana Saleh Ya tsiro da zancen ƙarin Aure A'isha bata tada hankalin ta ba kasancewar ta mace mai alkunya da haƙuri duk yadda yake ɗarare da zancen amma ganin yadda ta kwantar da hankalin ta dan shi kan shi bai san abun da zai sanya shi ƙarin Auren

Chapter 6 of 39