masa faɗa bayan fitowar su saboda shima yana da mugun jinini kuma ganin sa a bunda Suhail yayi wauta ce kawai da rashin hankali dan haka gudun kar ya maimaita yake ta nanata masa illar abun da yayi.
Zama yayi kusa da kujerar da ke kallon ta su Amoh.
Yace " Amoh ya ƙarfin jikin ki,ki yiwa Yaron nan magana ya riƙa kulawa da lafiyar sa ".
Ɗan Hararan sa Suhail yayi da ya ɗaura kan sa jikin Amoh.
Yana sauke ajiyar zuciya jin Uncle Yaqub bai tona sa kai tsaye ba.
Yar ƙaramar dariya uncle Yaqub yayi.
Amoh kuwa ce wa tayi " ka riƙa kulawa sosai Baba na ka ji ".Tana shafa sumar kan sa.
Kai Suhail ya jinjina mata yana ƙara shigewa jikin amoh.
Ko da Dady ya dawo haka ya isko su kowa dai zugum sai a hankali tun daga nan ya fahimci akwai matsala dan haka bai tambayi kowa ba ya dai yiwa yar sa addu'a cike da tausayin ta bayan ya leƙa ta window ya gan ta cikin yanayi na tausayi dan har da ƙwalla ya fitar mata.
💫💫💫
*A ɓangaren Abbu bai samu ganin Mahaj ba sai bayan sallan Magriba.
Da sallama ɗauke a bakin sa ya shiga room ɗin sa kasancewar ya gan sa masallaci kafin ya ƙara sauke kallon sa kan sa ya ɓacewa ganin sa.
Dan haka ya kasa hakurin ya isko sa ya same sa da kan sa.
Kunya ce ta kama Mahaj ganin Abbu dan haka ya sunkuyar da kan sa ƙasa bayan yiwa mahaifin na sa kallo mai ɗauke da soyayya da ƙauna irin ta ɗa da uba.
Dan shi da ya ji knocking a tunanin sa Mubarak ne.
Zaune yake kan ɗai daga cikin rugs dake ƙawace da Falon na sa ya sha baƙar jallabiya yar Moroccco Black color ta masa kyau matuƙa kyau ya haɗu da kyau.
Sai da Abbu ya gama ƙare masa kallo sannan ya saki ɗan guntun murmushi dai dai lokacin da Mahaj ya ɗaga idon sa ya kalle sa ganin bai zauna ba har yanzu ga shi yana jin idanun mahaifin na sa akan sa.
Ɗan lumshe idanun sa yayi a hankali ya buɗe yana zubawa mahaifin sa su da bashi da na biyun sa a wannan duniyar mamakin murmushin da yake ta saki yake yi gashi ya kasa magana bare shi kan shi ya yi magana dan murmushin ya bashi mamaki taya za,a yi mutun yayi ta Murmushi haka babu dalili duk da ya san abbu mutum ne mai sakin fuska amma ya san akwai wata ƙasa.Anya kuwa Abbu lafiya yake zuciyar ta furta masa.
Shima kan sa murmushin ya jefa shi wani irin yanayi sai dai ba zaka iya gane hakan ba kai tsaye dan fuskar sa babu wani alamar murmushi a cikin ta sai dai a sake take.Kasa haƙuri yayi cikin sanyayyiyar Muryan sa da take fita cike da natsuwa da sakewa irin ta ɗa da mahaifi da yar chakuɗaɗɗiyar Hausar sa ya ce " Abbu wani abu ya faru ne " ?
Kai Abbu ya girgiza yana ƙara faɗaɗa murmushin sa kafin a hankali shima ya ce " Kawai farin cikin ganin ka nake yi nayi kewar ka ,shine da ka dawo daga masallaci mai makon ka fara zuwa ka ga sanyin ranka ka shige ".
Murmushin gefen baki ya saki wanda Abbu ne kawai yake samun sa yana yin ƙasa da kan sa.
Riƙo hannun sa Abbu yayi wanda ya san ba zai ce masa komai ba a bazata kuwa ya ji ya ce " I'm sorry bayan isha'i na so naje wajen ka ".
Murmushi ne ya ƙara fita akan fuskar Abbu.
" Bani labari ya komai yake tafiya "
Cewar Abbu kafin ya ƙara furta " Da abun da ya faru da wanda bai faru ba "
Ɗan kallon sa Mahaj yayi yana zuba masa idanu kamar mai nazari kafin ya janye idanun sa akan Abbu.
Abbu kuwa ya lura dan haka ya ce " Kai nake jira malam ".Ya na haɗiye dariyar sa.Ganin kallon da yake masa.
Shiru ne ya biyo baya kowa da tunanin da Yake a ransa Abbu na jiran amsar da ya san ba samu zai yi ba har a zuciyar sa ya sani babu abin da zai faɗa masa.
Shi ko mahaj haka kawai zargin Muby ya ɗarsa masa amma sai ya haɗiye komai bai nuna ya ɗan fahimci abun da Abbu ke son ji ba.
Abbu kuwa cike da tsokana ya ce " Ni fa yarinyar nan shatou nake son jin labarin barafasar da kuka sha,Ance ...."
Shiru Abbu yayi yana rufe bakin sa domin ya san kai tsaye zai zargi Muby ɗin.Wanda bai sani ba tuni hakan ya faru dan yana jin sunan ya fito bakin abbu sai da ya furta a cikin zuciyar sa I know.
Ɗan lumshe idanun sa yayi kafin ya buɗe su ya ce " Wa yace Abbu " ?
Ɗan shiru yayi kafin kuma ya ce " Wace ce Shaaaa touuu " Ya kai ƙarshen sunan A rarrabe kamar mai tsoron kiran sunan.
Yana sauke Numfashi.
Abbu kuwa zuba masa ido yayi sai dai murmushin sa ko kaɗan bai bar kan fuskar sa ba mai cike da kamala da dattijan ta ka.
" Manta kawai ".
Cewar Abbu.
" Shatou kake tambaya ta,ai ka fi ni sanin wace ce hakan,ko ba haka ba ".?
Shiru yayi wa Abbu yana ƙara yin ƙasa da kan sa.Sai dai Abbu na lura da shi domin kuwa bakin shi ya tura gaba da jan guntun tsakin kan leɓɓen sa na tuna riginar su da shatou ɗin yanzu,wanda Abbu ya ji fitar sa a kunnen sa dan haka ya tabbatar da rainin hankali ne kawai na ɗan sa tun da ya mayar da shi abokin wasan sa dan haka ya share zancen yana cigaba da sakin murmushi inda ya canza wani zancen daban.
Mahaj kuwa tunda Abbu ya chan za magana ya ɗan saki jikin sa suka fara yar fira irin ta ɗa da uba wadda ta shafi rayuwar su ta baya da ta mahaifiyar Mahaj ɗin.
Suna a hakan a ka kira sallan Isha'i a tare suka fice kasancewar dukkanin su sunada Alwallan su.
Suna gama Sallah muby ya riga kowa fitowa daga masallaci haka kawai baya son haɗuwa da mahaj ɗin musamman yanzu da ya ganshi tare da Abbu.
Ai ko MAHAJ da yake lura dashi bai ce masa ƙala ba har ya fice yana gama addu'ar sa kuwa shima ya fito.
A nan Babban falon dukkanin su suka hadu har Aiyah da take dan jifar shi da harara.Dinner zasu yi wadda dama haka suke yi Shine kawai yake tsame kan sa saboda wasu dalilai bayan takurar idanun Aiyah a kansa da na wasun ta dan mutun ne da ya tsani kallo yana cikin dalilin da ya sa baya shiga mutane sosai bayan rayuwar kaɗai ci da ya ratsa jikin sa.
Ɗunguma suka yi zuwa kan Dinning hannun sa riƙe da na Abbu shi da kan sa ya ja masa kujera ya zauna yana furta " Yau ɗure zanyi wa wani babu ruwa na "
Shi kuwa sai ƙara ɓata kyakkyawar fuskar sa yake yi dan ji yake cikin sa cike yake saboda ya sha chocolate a ɗazu bayan ya farka daga bacci kafin aka kira sallah ya fice bayan yayi brush da watsa ruwa,bayan tashin sa daga baccin wuraren ƙarfe shida da yan mintuna.
Abbu kuwa ko a jikin sa kuma bai damu da idanun Aiyah da yake ji kan sa ba.
Dan shi ganin Mahaj yake yi yana rama bai sani ba ko idanun sa ne kuma ya san cewa rashin saka abinci ne isasshe a cikin sa.
Kasancewar ya san yanayin tsarin cin abincin sa ya zuba masa kunnun gyaɗa mai kyau da basa rabo dashi a koda yaushe kan dinning saboda Abbu da yake mugun son sa duk da shima Mahaj ɗin yana son sa amma saboda bai damu da cikin sa ba anfi yiwa abbu dan haka koda yaushe ake masa shi a duk girkin da masu aiki zasu yi sai sun yi shi.
Ajiye masa cup ɗin yayi gaban sa yana furta " Shaaa yanzu kuma bana son ganin komai sai cup idan ba haka ba zan saka Samira da Salma su matse mini kai na yi maka ɗuri ".
Haɗe rai yayi jin sunayen da Abbu ya ambata yana tura bakin sa gaba kamar yaron da ke shan nono.
Yar ƙaramar Dariya Samrah ta yi wadda ta warke har ta koma ayyukan gaban ta dan har school ta koma.
Yar hararan ta yayi kafin ya ɗauki cup ɗin ya na zuba masa idanu,daddaɗan ƙamshin sa ne ya daki hancin sa hakan ya sa ya ja ɗan numfashi yana kai cup ɗin bakin sa bayan yayi bismillah.cike da kulawa Amma ta ce " Yau dai wani zai ci dole ".
Ɗan kallon ta yayi bai ce komai ba bai kuma nuna alamar ya san da shi take ba.
Inda sabo Ammah ta saba da hakan dan haka cike da rashin damuwa ta kalli fuskar Abbu dake ta sakin murmushi yana kallon MAHAJ dake shan kunun sa a hankali.
" Kuna damuwa da wanda ko ciwon kan sa bai sani ba,idan yunwa zata masa illa me ye naku a ciki da har ake maganar yiwa garjejen ƙato ɗura ". ta kai ƙarshen maganar tana jan ƙaramar tsuka.
Furucin Aiyah ne ya sa shi ɗan dakatar da shan kunun sa kafin ya ɗan saci kallon ta dan haka kawai kwana biyun nan yake shafa ma kan sa lafiya ya daina leƙa wajen ta kwana biyu kuma cike take dashi a kan hakan jira take ta samu dama ta masa tass shi da uban sa dan a cewar ta shi ya ɗaure masa.Abbu ɗan ɓata fuskar sa shi yayi sai dai bai ce komai ba.
Dan baya da amsar bata sai dai ya san shi ke da komai a ciki kuwa domin shine wanda zai fi kowa fita hayyacin sa idan ciwon yunwa ya kama masa ɗaan sa abin son sa farin cikin sa.
Shiru wajen yayi kasancewar kowa ya fara cin abincin sa da aka yi serving ɗin sa.
Su Samira da Salma kuwa dukkanin su wani irin kallo ne suke jifan MAHAJ da shi wanda Ni dai Ban gane ma kan sa ba kuma yana ɗai daga cikin dalilin da ya sa baya son zaman kan dinning ɗin tare da su.
Yana jin idanun su jikin shi sai dai bai nuna yama lura da su wajen ba koda Abbu ya saka su cikin zancen sa kuwa bare yanzu.
A haka aka gama dinnern inda shi ya riga kowa ta shi duk yadda Abbu ya so ya ƙara saka wani Abbu ya ƙi dan kuka yake neman ma sa a cewar sa ya ƙoshi da ƙyar ma yake numfashi.
Ganin hakan ya sa Abbu bai matsa masa ba ya masa sai da safe yayi hayewar sa.
Koda ya shige ɗakin direct jallabiyar ya cire dan dama bai fita da wayan sa ba towel ya ɗaura ya shige wanka bai jima ba ya fito bayan ya ɗauro Alwallan kwanciya bacci.
Wasu riga da wando ne ya saka na bacci silky masu kyau guntun wando maroon color kafin ya ƙara gudun Ac ya hayewar sa kan bed ɗin sa bayan kashe hasken ɗakin da barin bedside lamp na gefe ɗaya.
Bacci dai ya ƙi zuwa duk yadda ya shirya yin sa yanzu kasa ɗaukar sa yayi domin kuwa sai juye juye yake yi wanda shi kan sa bai san dalilin ba ƙaramin tsaki ya ja yana jan ƙaton duvet na sa mai taushi blue color mai kyau ya rufa jikin sa tun daga kan fuskar sa har ƙafafu yana turje turje shi kaɗai tare da jan tsaki.
zaune ya miƙe yana hargitsa gashin kan sa dake ta walƙiya A hankali ya furta " Ya rabb.."
Idanun sa ya lumshe a hankali wata sabuwar Addu'ar ya ƙara yi kafin ya kashe light ɗin gaba ɗaya.
Ya kwanta babu abin da ke tashi a dakin sai ƙarar aikin na'urori da sanyayyen ƙamshin sa dake maƙale da ɗakin yana a hakan bacci ya kwashe sa rungume da filon sa wanda inda sabo ya saba hakan tun bayan da ya zamana yana kwana shi kaɗai ya saba wa kan sa da hakan ko da ya manta ne sai ya farka ya rungume filon sa yana jin hakan a matsayin cewa kamar mahaifiyar sa ce ya rungume duk da bai waye ta ba.
A suba ta gari ɗan Abbu.✍️
Mun kuwa komawa in da muka fito.
Masu niyyar fara payment su fara ba zamu jira kowa ba wayen da suka biya sun yi hakuri matuƙa dan haka babu jira in sha ALLAH.
Kuna da wani page an jima In Sha ALLAH.
Na yau kenan wannan bashin jiya ne.🤭🙏🙏
Kuna ƙwarin gwiwata readers Allah ya sakawa kowa da Alkhairi.
Masu bibiyar wannan labari na cikin group da na waje,mutanen facebook,mutanen Wattpad,mutanen Arewapens ina yiwa kowa fatan Alkhairi.💔🙏✍️💫
To subscribe yours contact this number
08069059746
_*KURMAN ƘADDARA*_
*_©®Faiza Almustapha Murai_*
_*FA'EEH BG*✍️_
P________4️⃣ 5️⃣
*BOOK ONE*
*_FREE_*
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t
_*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_
*Wannan shafin naki ne kacokam Uwata*
*_(Maman Abba)_*💕💕🥺kiyi yadda kike so dashi.Shatou na godiya.🙏🙏
***
A ɓangaren Abbu ma sai da safe kawai yayi wa Aiyah ya shige da matar sa.
Yau ko yar firan da suke taɓawa as a family ba,ayi ta ba saboda yadda Aiyah ta ɓata mood ɗin Abbu.
A ɓangaren shatou kuwa suna gama cin abinci kowa ya watsa ruwa kafin suka fice zuwa makarantan islamiyya.Abin mamaki yau bata tsokani kowa ba har aka tashi dan sai da Inna ni ta mata kashe di ashe kuwa ya shiga kunnen ta.
A haka aka rabu lafiya da su malam Abu.
Bayan sun dawo makaranta kuwa sun samu Baffa na baya gida yana kasuwa dan haka suka shirya suka same shi Chan kasancewar an kusa Magriba hakan ya sa ya sako su Gaba suka yo gida yana jin daɗin firar su da ya yan na sa musamman shatou.Wadda ke bashi labarin yadda taga malam Abu na zare ido wanda ke jiran tayi masa laifi yau ya dake ta.
Alwallah kawai Baffa na yayi ya wuce masallaci shi da Bibu bayan isar su gidan.
Ita kuwa shatou tare da Inna ni suka yi sallama kafin suka cigaba da aikin da suka tarar Inna ni nayi na fige ganyen zogala da Baffa na ya tsinko musu daga daji.
Shigowar su Baffa na ce ta dakatar da su inda dama Kowa Inna ni ta ajiye Musu abincin su a tare suka ci suka ƙoshi sai dai ita kamar koda yaushe bata ci nata nan ba a ɗaki ta ci abin ta kafin ta fito suka cigaba da taɓa yar fira.
A hakan Kiran Sallahn Isha'i ya same su kowa ya yi wajen Sallah.
Suna dawowa kuwa karatu Baffa na ya ƙara bita musu sai da ya tabbatar kowa ya iya sannan ya bar su.
A ɓangaren shatou hankalin ta ya rabu gid a biyu domin kuwa tana son fita dandali tana tsoron abun da kan iya biyo wa baya kan rigimar ta da shamsu maƙiyinta.
Wata zuciyar ta ce mata kije da Bibu shiru tayi kafin wata zuciyar ta bata amsa da zai iya masa illa idan ke bai same ki ba.
To ai kina da mai kare ki baga iro nan ba.
Wata zuciyar ta ƙara furta mata.
Kafin ta yi shiru jin ɗayar zuciyar na ce mata ki rufa ma kan ki asiri yanzu idan baku haɗu da iron ba ke dai zauna gida bari ƙura ta lafa.
" Ke lafiya ,me kike tunani haka " ?
Inna ni ce da ta zuba mata ido tun ɗazu ganin ta lula wata duniya abun har mamaki yake bata wai kamar shatou da tunani.Me take tunani wata zuciyar ta tambaye ta dan haka ta furta mata tambaya kai tsaye.
Bayan zuba mata idanun na ta.
"Babu komai Inna ni "
Shatou ta furta wadda maganar zucin ta tsaya chak kan tambayar da Inna ni ta mata.
Murmushi ta ƙara saki tana Kallon Inna ni da tayi alamar rashin yarda ga shatou ɗin.
Dan kai kawai ta girgiza.
Baffa na da ya lura bai ce komai ba sai yar dariya kawai da ya saki.
Yau shatou da wuri bacci ya kwashe ta ko firar basu gama ba dan ta bi maganar zuciyar ta.Aiko ba,a daɗe ba bacci ya ɗebe ta Inna ni ce ma dole ta tashe ta ta kai ta tayi fitsari saboda tana da gigin Bacci kafin ta taimaka mata tayi tsarki ta kai ta ta kwanta tayi mata Addu,a ta shafe ta ta ko ina, bisa ga Bibu da yaje da ƙafafun sa dan idanun sa biyu shikam.
---------Abba na gama cin abincin sa ya miƙe ya dawo falon dai dai lokacin da Leena ke fashewa da kuka kasancewar ta ƙoshi amma B ya ƙi daina bata sai ɗura mata tea yake yi ta kasa samun fuskar da zata masa magana kai tsaye.
Dan haka Ganin Abba sai ta fashe da kuka tana furta " Abba na ƙoshi ".cike da shagwaɓa
Murmushi Abba yayi yace '' Ai bani zaki faɗawa ba ".ya nuna mata B dake ƙara haɗe fuskar sa ganin abun da ya rage kawai cikin cup ɗin wanda ya kamata a ce ta shanye sa.
Zuwan Ummah ne wajen wadda ta tsaya kimtsa dinning ɗin tare da taimakon masu aikin ta.
Ya ƙara bawa Leena damar fashewa da kuka ganin bata ci nasara wajen Abba ba.
" Ummah zan mutu idan na shanye wannan abun,Dan Allah Kice Abar shi haka ".
Ummah cike da kulawa ta matso wajen da sauri tana furta " oh ohh my Baby yanzu wannan hawayen duk na tea ne" ta kai ƙarshen furucin tana shafo hawayen dake silala.Cike da tausayin ta ganin ta ɗaga kan ta ta ce " Soja ya isa haka kar ka saka mini ya amai "
Ta rungume Leena jikin ta.
Shiru Leena tayi tana sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin sanyi a ranta.
Idanu suka haɗa da B da ya haɗe fuskar sa yana Hararar ta yana kallon cup ɗin aiko da sauri ta rufe idanun ta tana sauke numfarfashi a jere.
Abba cike da tausayin yar sa ya yi dariya ya ce " Kun fi kusa ai ".
" Ni ba zan iya saka baki a rigimar da bata shafe Ni ba " dalilin da ya sa bai kula ba dan ya san tana bukatar abun da zata sanya wa cikin ta ne dan suna bukatar abinci bayan kulawa Saboda yanzu da ka kalli fuskokin su da ke sanya shi a wani irin yanayi mai cike da kewa bege wanda baya da maganin sa sai hakuri zaka san sun faɗa sun yi yar rama kowaccen su tayi fess da ita hasken su ya ƙara fitowa haka ma manyan idanun su.
Yau ta kama laraba Abba da kan shi ya shirya ya kai ya yan sa makaranta domin kuwa nan ne yake samun damar basu ruwan da malam yace dan haka yace ya hutar da Drivern su sai dai duk da haka cikin dabara yake yin komai tunda har da su Hamra da Nina yadda ba zasu taɓa ganewa ba dan har su ya haɗa tun da Addu,o,I ne na kariya.kwana biyu yana kai su sai da ya tabbatar da ya cika maganar malam gaba ɗaya sannan ya bawa driver damar cigaba da kai su makaranta.
Ummah ma da B sun ɗan shiga mamaki saboda kowa ya san hidimomin dake gaban Abba ta harkar business ɗin sa sai dai sun ji dadi sosai musamman ganin yadda su Leena da ta fara ɗan samun ƙarfin jiki ta na ta murna Abba da kan sa yake driving na su.
Drivern sa tare da security na sa a bayan su.
Kowaccen su murna take yi sosai dan haka basu taɓa kawo wa kan su komai ba daga ruwan da Abba yake ba su idan sun fita kuma koda wasa babu wacce ta taɓa yin maganar koda da Ummah ne ko wani na cikin gidan dan basu ɗauke shi a komai ba.
Cikin ikon Ubangiji kuwa jikin kowaccen su ya samu ƙarfi sun koma asalin su sai rigima ta dawo sabuwa har kamar ma ta yanzu ta fi ta da dan basu ko shaƙar inuwar ɗayar su ɗan abu kaɗan sai ƙokarin illa ta juna.
Sabo da hakan ya sa yanzu Ummah take sassauta murya wajen yi musu faɗa tun da ta san faɗa da ɗaga murya ba zai taɓa shirya mata ya yan ta ba,sai Addua,a.
Dama B ne kuma ya koma Lagos.
Abba ma yayi tafiya satin da ya gabata dan haka take lallaɓa abun ta,tana jan su jiki sai faɗan ya ɗan fara raguwa dan tana zaunar da su ta musu nasiha mai ratsa jiki,wadda wani lokaci ta shiga wani lokaci tafita.
A haka rayuwa ta cigaba da tafiya ta kowanne ɓangare yau da daɗi gobe babu daɗi.A kwana a tashi ba wuya wajen Ubangiji yau ake cika sati Uku daga lissafin zuwan Ramadana da ake yi kuma cikin ikon Ubangiji yau ne ake dibon wata idan an gan sa za,a tashi da azumi idan ba,a gan shi ba za,a duba zuwa gobe.
Cikin ikon Ubangiji kuma an samu ganin wata mai alfarma a saudia wanda har an gabatar da sanarwar anan Nigeria.
Baffa ne ya shigo bakin sa cike da farin ciki yana furta " Anga wata fa gobe sai tashi da azumi ".
Shatou dake zaune fuskar ta kamar zata yi kuka dan tun da aka ce yau ake dibon wata ta koma marainiya ta ce " yanzu da gaske Inna ni duk azumin da kuke yi shi zanyi Ni fa sai in ga kamar ban isa ba wallahi dube Ni fa kalli ɗan ƙirji na shamfal " ta kai ƙarshen zancen tana jin kamar ta saki kuka kasancewar wannan shine lokaci na farko da zata yi azumi goma ma a jere a chan baya iyakar ta biyar ko shida a rarrabe har Ramadan ya ƙare Inna ni ta yi faɗa Baffa na ya tare wa shatou ya ce ta huta har lokaci ya zo.Wanda sai yanzu ta fahimci lokacin gashi yanzu tana jin kamar bata iya yin su duka gashi Kuma idan ta ajiye babu laifin komai, tana da babban laifi gurin Ubangiji Allah zai hukunta ta,Sannan ƙofar da aljanna da ake buɗewa masu azumi bada ita ba gashi kullum Baffa na da malam Abu suna faɗa musu ni'imar Aljannar fiddausi har da Inna ni idan yan maganar ta na kai.
*Allah ya saka mu aljanna baki dayan mu,Ni da ku masoya wannan labari na nesa da na kusa.Allah ubangiji kuma ya nuna muna zuwan Ramadana na 2026 lafiya,Allah ya yafe mana kurakuran mu,wayen da muka aikata a cikin sanin mu da wayen da muka ba,a cikin sanin mu ba.🤲🤲🤲*
" A,a ni zan Miki " Cike da Haushin surutun na shatou da take shaƙa da babu sayi bakin ta inna ni tayi furucin,Ita kuwa shatou muryan Inna ni ce katse mata tunanin ta.
Bakin ta tura gaba
Kafin ta kalli Bibu da ko a jikin sa dan shi ko waccan shekaran azumi ishirin yayi duk da da ƙyar ya kai shi wanda ko shi Baffa na da Inna ni sun yi sun yi ya bar shi a goman da suka ce yayi ya ƙi.
Yace na sa goma sauran ladar goma na su ne.
Sun ji daɗi sosai ita ko Giwa girman banza da rigima ake kai shi da sanya idon Inna ni dan ta san halin ta tsaf zata iya shan ruwan ta ta lankahe mata ala dole ƙisa take ji duk da haka kuwa Inna ni ta san Allah dai ya kyauta.A zumin manya.
" Yanzu Bibu kai ba zaka taya ni a zumin ba ".
Yar dariya yayi yace zan Miki kema ai wannan karon.
Dariya tayi kafin ta ce " kai kammm ka huta "
Baffa na dake kallon ta yar dariya yayi yana girgiza kan sa kafin ya ce " Ke ma kin huta ai ".
" Baffa na wai Yanzu Dagaske dai Nima tare daku zanyi a zumi kuma duk saboda wannan jin..."
" Ke ban son shirmen banza dan uban ki,azumi ne sai kin yi shi wallahi kona sassɓa Miki,idan kuma kina wasa na ji ko naga koda wasa kin saka wani abu a bakin ki bayan wucewar lokacin sahur,Sakarar yarinya kawai ".
" Ke kar ma na ƙara jin maganar a zumin nan bakin ki ibada ce ta zama dole gare ki,dan haka ki rufe mini shi ko na haɗa dake da shi na zane ".
Inna ni ta kai ƙarshen zancen tana haɗe fuska.
Shatou kuwa ganin tana neman tono rigima hakan ya sa ta yin shiru tana ƙyafƙyafta idanun ta tana ƙara cunna bakin ta gaba.
Baffa na dai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 39