Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya saka mini Baby gaba,Ni na san baki taɓa Leena ba ai,ke da babu ruwan ki ko yatsa aka saka Miki a baki na san ba zaki ciza ba " " Gaskiya bai kyauta ba,kuma zan masa magama kar ya ƙara shiga sabgar Baby na ". Duk da akwai tazaran shekara ɗaya a tsakanin su hakan bai hana su mu'amala da juna yadda ya dace ba duk da shi Bilal bai da irin muguwar sakewar nan kamar shi Samir ɗin. kai ta lanƙwashe tana Murmushi tana jin. wani daɗi a ranta jin zai masa magana duk da ta san Bilal ne Babba amma ta san zai saurare sa saboda kamar ƙawaye haka suke tare suka tashi su biyu. Ita kuwa Reena ka sa haƙuri tayi dan haka ta ce " Yaya fa bugu na tayi har ta sumar da ni,shine fa yaya ya dake ta kuma har yayi fushi da ita,yanzu ma duka faɗa take yi dashi,shima yaya B babu ruwan sa da ita ".Ta kai ayar maganar Tata cike da damuwa kamar zata yi kuka. Uwar Harara Leena ta makawa Reena taana ji kamar ta jawo ta ta ƙara jajjagawa,sai kawai ta buga ƙyafci dan taji Haushin Reena ta ƙarya ta ta tunda ta san bai son tana faɗa ce faɗacen nan kamar dai Bilal shi bugun ta kawai bai yi sai dai ya yi fushi da ita. Shi ko Samir murmushi kawai yake yi saboda ya san Gaskiya ya san komai dake faruwa ya ji a bakin Bilal ɗin,kuma ya roƙe sa ya daina dukan ta ƙuruciya ce,dan haka bai nuna musu ba kawai ya share zancen Reena ta hanyar furta " Ku jira na zo,ku bani labaruka " " Hajiya ta bari naje na watsa ruwa na dawo yunwa ma nake ji " Ya na zancen yana shafar ɗan tumbin sa.Kai Hajiya ta gyada masa wadda ta fito daga kitchen yanzu tana Murmushi cike da jin daɗin ganin su Leena a arha dan ba su cika shigowa sashen na ta ba sai ko gaisuwa idan ta kawo su dan ita bata da mace ko ɗaya duk maza ne. Su Leena kuwa kowaccen su waje ta nema ta zauna bakunan su ɗauke da murmushi sai kuma aka koma fira da Hajiya da take tambayar su ya Ummah take dan kwana biyu ba su haɗu ba koda wajen gaida sarakkan su ne dan itace kawai Ummah bata cika sakewa da ita ba. Yau kwanan ta ɗaya biyu a asibitin dan riƙe ta Suhail ya sa aka yi ta ƙara samun sauƙin raunukan ta,sai ka sallami rabi kawai sannan suka Bata hutun kwana biyu.Dan haka suke bata allura mai ƙarfi bayan lokaci zuwa lokaci dan brain ɗin ta ta samu hutu mai kyau.Tunda ta buɗe idanun ta ta ga haske tar ko ina ta fara kiciniyar ƙwace kan ta idanun ta na rikiɗewa suko ma jajir da su kamar an baɗa mata barkono.Babu kowa ɗakin dan haka ta samu ta ɓalle duk jone jone dake a jikin ta Wanda Likitawa suka yi.Su Suhaila dake waje basu san abunda ke faruwa ba sai dai ganin mutun kawai suka yi ya fito a guje,cikin kiɗima da razana suka bi bayan ta cike da tashin hankali ita kuwa gudu take ta rusa akan babban coridor ɗin da zai fitar da kai daga sashen su.Ta ke hular kan ta,ta zare gashin kan ta ya barbaje har akan fuskar ta saboda kafin su zo nan an walwale kan ba,a samu aka kitse ba aka bar shi haka dan ba ta ma bari aka taje shi ba. Dabb haka kan ta ya bugi ƙirjin sa,ɗan rufe idanun sa yayi kafin ya buɗe su,ita kuma a lokacin ta samu ta zare jikin ta ƙara fallawa a Guje sai lokacin ya an kara da su Suhaila dake kuka sun zo sun gifta ta sa ita da Nurse Mira sai nurses guda biyu mace da namiji su ma a bayan su ɗan yanayin gefen fuskar ta da ya ɗan gani yake son hasasowa tare da tunanin wace ce cike da tausayin ta yanayin ta dan yanayin da take ciki ya nuna Zallar Hauka ce,yanayin da ya samu kan sa ne a lokacin da jikin su ya haɗu ya san ya shi sauke a jiyar zuciya da numfashi yana mamakin abun da ke tattare da wannan mara lafiya da tausayin ta ya dabaibaiye shi kiran wayan shi da aka yi ne ya sa ya cigaba da tafiya ba tare da ƙara kawo tunanin komai ba sai dai zuciyar sa cike take da tausayin take,haka kawai ya ji ina ma yaga fuskar ta. Gaba yayi yana amsa waya hankalin sa kwance. A ɓangaren su Suhaila kuwa da suke cikin tashin hankali da gigicewa dan yaune rana ta farko da ta samu damar yin irin wannan gudun wanda take nuna alamar ɓacewa daga gida dan tana nuna son guduwa sai dai yau ne kawai ta samu dama dan chan iyakar ta compound saboda tsaro. Da wani irin karfi ya fisgota bayan ta ɗan gota shi kaɗan daga tsayen da yake,dan ya daɗe tsaye wajen yana kallon tafowar tata a inda yake saboda bai daɗe da shigo wa ba sai dai a ƙafa yake dan taxi ta sauke shi a bakin gate dan ƙa'idar su ce ba,a shiga da ita,dan dawowar ta sa bai sanar ma da kowa ba bare a je ɗaukar sa ko driver ban sa bai sanar ma ba. Ƙammmm haka ya rungume ta a jikin sa yana sauke a jiyar zuciya cike da tausayin ta ga wasu hawaye masu zafi da ciwo da yake jin suna neman sauka akan fuskar sa.Su ko su Suhaila chak suka tsaya zukatan su na musu wani irin raɗaɗi da ƙuna ga su kowaccen su fuskar ta tayi haja haja saboda kuka da fita hayyaci dan sun san muddin ta hau hanya su kan su ba su san yadda za,a iya kama ta ba. Numfashi suka sauke ganin wanda ba su zaci gani ba a lokacin,Nurse Mira Murmushi ta saki haka ma Suhaila Rayyan ma da ya shigo yanzu murmushi yayi cike da farin ciki dan ya na shigowa ya hango su a Guje itace gaba kafin ya san abun yi sai aka yi sa,a shima Ya na kusa. Kiciniyar ƙwace kan ta take yi sai dai ya ƙi bata damar hakan dan riƙo yayi mata bana wasa ba. Daga ƙamshin turaren sa ta fahimci shine sai dai a idanun ta a wannan yanayin babu abun da suke da buƙatar gani face ta tsince ta a inda take ganin kan ta a cikin idanun na ta.Addu,oi yayi ta tofa mata dan ƙara take ta saki ta na gaɓɓatan dariya kafin kuma a hankali hawaye masu zafi suka silalo mata suka sauka aƙirjin sa idanun sa ya rintse da ƙarfi da suka yi jaaa abun ka da farar fata fuskar sa tayi jaa na damuwa da baƙin ciki na yanayin da ƙanwar ta sa take ciki. Jin da yayi jikin ta ya saki hakan ya tabbatar masa da cewa tayi bacci dan haka ya durƙusa ya ɗauke ta dai dai nan aka kawo kujerar marasa lafiya daura ta yayi ya gyara mata zaman kafin ya bi bayan Nurses dake kula da ita. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya amsa sannu da zuwa da Rayyan yake masa. Su Suhaila ma sannu da zuwa suka masa bayan sun isa inda Sashen na masu ciwon ƙwaƙwalwa yake. " Captain manya yau nake ganin idon ka ". Murmushi matashin da aka kira captain yayi kafin ya shafa kan sa.Hannu suka haɗe waje ɗaya cike da murmushi. " Wallahi ko ayyuka sun yi yawa yanzu ma dole ce ta kawo ni nan Yaqub ". " Kuna da patient ne anan halan " ? "Eh wallahi wani ma'aikacin mu aka kawo sun samu accident to abun kamar ya taɓa brain ɗin sa shine na shigo,idan ka lura tafiyar ma ta wa ce ni kaɗai " Kai yaqub ya jinjina kafin yace " Allah ya bashi lafiya,Nima na zo ganin Patient ɗin mu ne ta kwana biyu nan Ni sai yau Allah ya kawo Ni dan bana ƙasar na yi tafiya kwana biyu,Yar wajen Yaya na ce itama tana fama da matsalar ƙwakwalwa abun ba,a cewa komai gashi na ta tun tana yarinya har yanzu babu wani cigaba " Ya karasa zancen cikin alhini. Cike da tausayi saurayin da aka kira Captain ya ce " Allah ya basu lafiya ya sa kaffara ne ya kawo karshen wahala ". " Amin '' Yaqub ya amsa " Bari kawai muje na gan ta sai na wuce tunda har mun haɗu sai ayi zumunci ". Kiran wayar sa ne ya katse maganar da Yaqub zai yi. Cike da ladabi ya gama wayar kafin ya sara yana kashe wayar.ya kalli yaqub da ke jiran sa su wuce yaga patient ɗin ta sa ya ce " Sorry Yaqub Wallahi na samu kiran gaggawa sai wata haɗuwar idan kuma na samu time zan zo na ga mara lafiyan ,Allah ya bata lafiya " " Amin bakomai Captain sai mun yi waya " .Hannaye suka tafa kafin suka yi Sallama kamar kar su rabu,dan an kwana biyu ba,a haɗu ba. Matashin da aka kira yaqub Shima gaba yayi yana caɓa car keys sama yana ɗan waigen Motar Captain da ta bar asibitin yana murmushi cike da kewar abotar ta su da suka yada kwana biyu kasancewar su class mate suna ɗan chat sai dai yanzu sun jaa baya. Tsaye ya isko su cirko cirko Ganin Rayyan a kusa ya sa shi cewa " Lafiya Rayyan ko Jikin Isha ne ya tashi kuma ? Na gan ku cirko cirko ". "Sannu da dawowa Uncle,Wallahi Uncle shine yanzu abun ya motsa mata ta fita ba tare da sanin kowa ba Allah ya taimaka Ya ya Suhail ashe ya dawo yau shi ya tare ta da bamu san inda zata je ba inda Allah ya takaita sai ya zamo a kwai mutane a kusa ". Rayyan yayi zancen cike da damuwa da raɗaɗin da ke maƙare da zukatan su. Cike da damuwa ya dafa kafaɗan sa yana cewa in sha ALLAH zata samu lafiya komai zai zama tarihi ganin hawaye sun kwaranyo a idanun Rayyan. " Ina Suhail ɗin " ? Ya tambaya ba tare da amsa sannu da zuwan da yayi masa ba. " Yanzu ya wuce office ɗin sa " . Kai Ya gyaɗa kafin ya matsa ya gaisa da su Suhaila da Nurse Mira ya musu ya mai jiki tare da ƙara musu ƙwarin guiwa dan kowa chan gida haka ya baro Amoh sai a hankali damuwa ta mata yawa dan ma sun hana ta zuwa ne da tana wajen. Da Sallama ya shiga office ɗin yana samun wajen zama dai dai shima Suhail ɗin ya fito daga toilet yana gyara hannayen rigar sa da ya tattare hannayen da danshin ruwa da alama alwalla yayo. Cikin ɗan sakin fuska ya ce " Uncle Yaqub yaushe garin,? Ina wuni " ya faɗa cike da girmamawa duk da Uncle ɗin ba zai wuce ya bashi shekara ɗaya ba. Murmushi yaqub yayi kafin ya ce "lafiya lau,ai Jiya na shigo tafiyar dare nayi dan haka ban faɗa ma kowa ba ". " Naje gida ganin ku aka ce baka nan,suma su Rayyan suna hospital tare da Suhaila Saboda jikin Ishaa da ya tashi ". Zama Suhail Yayi Yana Sauke Numfashi " Ai da sauƙi ma dan yanzu tana samun isasshen bacci yanzu ma bacccin aka mayar da ita amma zuwa anjima zan mayar da ita gida kawai dan ma akwai wani likita da zai taimaka mini mu haɗa hannu mu cigaba da lura da yanayin nata sai dai ba nan ƙasar bane Canada yake dan haka nake son muje da ita idan mun gama shirye shiryen,ban ma yi magana da su Daddy ba ". " Allah ya bata lafiya,jarabawa ce kowanne bawa da kalar ta sa ita wannan ce ta ta damu baki ɗaya,Allah ya bamu ikon cinye wa ya kuma bada ladar ɗawainiyya Allah kuma ya saka muku da Alkhairii ". " Amin Uncle Yaqub ya hanya,kuma " ? Suhaila ya faɗa bayan ya sauke ajiyar zuciya mai cike da wani irin rauni wadda Uncle ya ji ta sai dai bai wani damu ba dan ya san akwai damuwa sosai a yanayin sa zuciya dole sai ta hakan take rage nauyi musamman ga re su maza tun da basu cika zama su yi kuka ba............. Koda ta shige ɗaki ƙaramin tsaki ta ja tana Hararar bango kamar Iro ɗin ne gaban ta Cike da Haushin sa yau ita da take ce ma su Amina da Bibu ga kalar saurayin ta da zai fara zuwa fira amma sai a ka rasa wanda zai zo sai Iro,to amma ai faɗa ma suke yi dashi kodai ba fira ya zo yi ba. Wata zuciyar ta yi maganar da alamar tambaya ?wata zuciyar ta bata amsa da ba fira ya zo yi ba, tsaki ta ja a bayyane kafin a fili ta ce " To uban me zai sa ya ce a kira ni wallahi idan ma soyayya ce ta kawo shi sai na masa mugun wulaƙanci,ni kamata zai ce yana yiwa sallama ". Tsaki ta ƙara jaaa sai kuma ta yi ƙyafci ta kwanta kan katifar ta, mai ta tuna sai kuma ta miƙe daga kwancen,tana miƙewa kuma ta fito waje tare da yafo ɗan mayafin ta,ta suri ta kalmi, su Baffana da ke tsaitsaye su ka gan ta kawai ta bi gaban su ta wuce. Baffa na idanu ya waro yana ji kamar ya janyo ta ta dawo dan wani irin tashin hankali ne ya ji ya mamaye masa ilahirin jiki gabas ya kalla da kudu kamar mai tsoron yanayin da yake ciki ya bi bayan Shatou shiko Bibu dariya yake yi kafin ya fara rera waƙar masoya ya shige ɗakin sa. Dai dai Iro na juyawa bayan ya tsaya jira ya tabbatar da zargin saƙon yaron da ya aika shin ita tace Dagske bata zuwa,ko,ko wanda dama ya san hakan zai iya faruwa saboda yar tsamar dake tsakanin su. Gaban shi ta sha,ta tsaya tana riƙe ƙugu.Shi ko kamar Gaula ya sakar mata idanu yana murmushi Harara ta ƙara maka masa ganin yadda ya ƙara washe baki.✍️ # 2025 # Hausa novel # Love,and romance story # Labari mai tafiyar saƙar gizo gizo # Soyayya mai tsayawa a zuciya # Kaddara mai cike da ƙalubalen rayuwa # zamba ma yar aike ce. # Cuta mai mai ban tsoro. # Mummunan Zuciya kai bawa mahalaka # All in one story ~*KURMAN ƘADDARA*✍️~ # Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣6️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 " me ya kawo ka waje na " ? Ta furta masa tana haɗiye fuska ta re da girgiza ƙirji kamar wata cikakkiyar budurwa. Shi ko Har zuwa lokacin murmushi yake yi dan haka kawai ya ke jin kamar an ƙara masa wani mashin son ta da yake sukar sa ya ƙara ƙarfi a ɗan lokacin nan dan haka ya kasa haƙuri sai da ya same ta kozai cire abun da yake ji. Sai da ta ƙara maimaita masa cike da tsiwa shiko kamar Gaula kamar ba Iro ba ya ɗan yi ƙasa da kan sa kamar Ba fade a gaban Sarkin sa ya ce " Dama zuwa nayi kawai na ganki ". Baki ta taɓe tana hararar sa kamar idanun ta zasu zube ƙass.Shiko murmushi ya ƙara saki kafin ya ce " Wallahi Dagske ganin ki kaɗai nazo yi Shatou" Ƙaramin tsaki ta ja kafin ta sauke idanun ta ƙasa da ga mugun kallon da take masa ta ce " da ka ganni kuma sai me ye " " Ajiya ka bani ne,ko na tsokane ka,ba ma an yi muna kashe di da juna ba " Shiru Iro yayi kafin ya sauke ɗan ajiyar zuciya sannan ya ce " Babu ko ɗaya " " To kama hanya ka wuce gidan ku,ko na haɗa ka da Baffa na ". Ta yi maganar tana nuna masa hanya Murmushi yayi ya ce " Toh an gama sai da safe " Ya wuce yana waigen ta kamar sakarai yana sakin murmushi.Ita kuwa muguwar harara ta bishi da ita kafin ta miƙi hanyar shiga gida fuuu kamar iska zai kwashe ta cike da Haushin Iro da mamakin wannan lamari na sa sai kace ajiya ya bata da zai ce ganin ta ya zo yi. Ƙaramin tsaki ta ƙara ja tana juyawa ta harari hanyar da ya wuce wanda har ya shanye kwana.Daf haka goshin ta ya bugi kafaɗar Baffa na dake tsaye yana jin duk abunda ke faruwa da kallo murmushi ya sakar mata bayan ya sauke a jiyar zuciya mai haɗe da numfashi.Bata ce masa ƙala ba ta yi yar dariya dan haka kaiwa ta ji kunya sannan ta shige gida tana ɗan mirza goshin ta shima Baffa na murmushi kawai yayi kafin ya bi bayan ta yana sakaya gidan. Ya ɗan daɗe tsaye tsakar gidan kamar mai tunani komai ya tuna kawai ya shige ɗakin sa zuciyar sa cike da wani irin tsoro da shakku da halin ƙaƙanikai. A ɓangaren Shatou tana shige wa ta haye gadon ta sai tayi ta tuno yadda ta ke gatsa masa magana amma bai mata komai ba hakan ya tabbatar mata da babban dalili ne zai saka Iro yin sanyi haka.Dan haka sai jikin ta yayi sanyi wai ita Iro zai ce ya zo gani akan me ?.Ta tambayi kan ta. Akan yana son ki wata zuciya ta bata amsa.Kai ina ba zai yuyu ba wallahi ta bawa kan ta amsa tana jan ƙaramin tsaki. Adduar kwanciya Bacci tayi bayan ta rage kayan jikin ta sannan ta juya kwanci kafin kace me sai bacci. A ɓangaren Inna ni kuwa zaune take,tayi ta gumi tuninika iri iri ke addabar zuciyar ta ta rasa yadda zata kwatanta ma Baffa na abinda ke cin ranta shekara da shekaru,dan haka Damuwar tayi mata wani irin riƙo a zuciya wanda dama cikin ta take damuwa ta san bata rabo da ita sai lokacin da Allah ya iyakance. (" Suna cikin matsala rayuwar su na cikin hatsari,Kuyi wani abu zasu hallaka su,zata samu sauƙi zata samu waraka zata sami lafiya ".) Wayen nan kalamai na Shatou dama wasun su sune ke ta amsa kuwwa a cikin Kunnuwan ta.Ta ina zata fara shin zata yarda da abun da iska suke faɗa mata ne zata gasgata su bayan kuma su ɗin sun kasance masu ƙarya mafi yawan zancen su ƙarya ne,idan har abun da Shatou ta faɗa gaskiya ne tabbas zancen alaƙar sa da wannan tabbatatta ce me zata yi me ya kama ta tayi ta tambayi kan ta.Addu,a shine abinda zuciyar ta ta faɗa mata hakan ya sa ta sauke numfashi mai zafi kafin hawaye masu mugun zafi da raɗaɗi suka silalo mata duk yadda take son dannewa ta ka sa hakan ya sa ta sake wani irin kuka mai fitowa daga ƙasan zuciyar ta sai da ta yi mai isar ta sannan ta kwanta saboda ta na fashin Sallah ta yi addu,a ta kwanta.Cikin ikon Allah sai kuwa bacci mai nauyi ya kwashe ta sai dai daga nin yadda take kwancen ka san a cikin damuwa take.Baffa na ma a ɓangaren sa ya kasa barci dan haka ya ke kai kawo shima ɗin kamar akwai abunda ke damun zuciyar sa sai dai shi kaɗai ya sani sai mahaliccin sa.Ya daɗe haka kafin ya koma ya buɗe wata yar jaka ta shi ta ajiyar abubuwan sa masu amfani sannan ya jefa wata leda baƙa a ciki yana zuba mata ido kamar mai tsoron abun da ke ciki.Haka ya rufe ta yana sauke ajiyar zuciya.Sannan ya je yayi Alwallah yayi Addu'a ya kwanta shima kuma cikin yardan Ubangiji bacci ya kwashe sa dama an kwashi gajiya.Bibu ma tun da ya shige babu labarin sa da alama yayi bacci dan shi baya wasa da duk wani abinda ya shafi Hutu na sa. Asuba ta gari shatoun Baffa na. Cikin ikon Allah Bata farfaɗo ba har sai da yayi discharge na su dan haka tare suka koma gida da ita. Har dare yayi yana kan ta shi ya zauna zaman kula da ita dan haka ma ya ce Mira ta wuce gida kawai Nana tunda ta samu sauƙi sai ta dawo haka kuwa aka yi. Cikin ikon Allah kuwa Ishaa bata farka ba sai da safe kuma cikin yardan Allah ta tashi babu hayaniya sai dai kamar a tsorace take da kowa dake gidan dan ta ki sakin jikin ta sai tayi ta kakkamewa kamar yadda take yi ta makure waje ɗaya babu ci babu sha sauƙin ta ma Suhail tana karɓan na sa shima ganin ko na shi kwana biyun nan sai ta ga dama take karɓa rabi duk ta zubar hakan ya sa suke ƙara jin Tausayin ta dan tana azabtuwa matuƙa sosai. Dan haka suke kara bata kulawa fiye da wadda suke bata saboda yanayin da take ciki dole ka tausaya mata,a ɓangaren fitar da itama suna nan suna shiri dan Suhail ya tun kari iyayen su da maganar kuma sun aminta tare da nuna jin dadin su da sanya masa albarka. Koda ya fito duk suna nan zaune suna kallo wanda an kwata faɗa yayi kusan sau biyar Hajiya na tare wa ta raba.Haka Samir koda ya fito cikin shirin sa na kaya marasa nauyi ya same su Leena sai aikawa Reena harara take yi kamar idanun ta zasu zube murmushi kawai yayi ya ƙaraso wajen yana furta "Take it easy My Baby ".Kunya ta ji dan haka ta sauke kan ta ƙasa tana Murmushi shi shiko Dariya yayi kafin ya miƙar da ita tsaye haka ma reeena da Ninah suna dariya.Yadda ya tallabo kamar wasu yan teddies.Tare suka isa bakin dinning da dama An riga an shirya sa shi kaɗai ake jira dukkanin su ka zazzauna har su Ayman da ake firar da su dan sun riga shi ma fitowa.Cike da sakewa su Leena da aka zubawa ko wacce nata suka fara cin abincin hankali kwance.Sai dai Leena ko rabi ba tayi ba ta koma kusa da Samir wai na shi take son ci babu musu kuwa yana murmushi yace ta wanke hannun ta da gudu kuwa ta wanke hannun a nan cikin robar da aka ajiye ta wanke hannun saboda Samir da yake cin abinci da hannu a mafi yawan lokuttaa yanzu hakan ma shine kawai ke cin abincin sa da hannu hankali kwance. Cike da murna ta zauna suna cin abincin tana kallon sa tana Murmushi shima murmushin yake yi Reena dai bata tanka mata ba sai cin abincin ta take yi a haka suka yi ta shirita wajen cin abincin kafin suka koma Falo su Abduljabbar da Ayman Sai tsokanar ta suke yi ta yiwa Hajiya ya ji yau tunda Samir ya dawo ta zo harda zama, idan ba ya nan kuwa gaisuwa kawai ke kawo ta,ko ita ba kullum ba Haka suka zauna suna ta fira suna bashi labari yana kwasar dariya dan harda labarin islamiyya aka taɓo masa harda dukan da Ustaz Babba ya yi mata ta bashi labari tana dariya tana nuna yadda wai cikin ustaz Babba yake motsawa idan ya ɗaga bulala.sai da ya gama cin dariya sannan ya ce " Yanzu Leena Uztaz Babba mai makaranta gaba ɗaya shine kike kwaikwayo "? Dariya tayi itama kafin ta ce " To Ai shi ya dake ni yaya ai da faɗa kawai yayi mini kamar yadda kai da su Ummah kuke mini ". Ta kai ƙarshen maganar tana turo ɗan ƙaramin bakin ta gaba. Dariya yayi kafin yace " Gaskiya ba,a.kyauta mini ba an sako mini Baby gaba ". " Ai wallahi yaya wannan da kake gani sai dai Allah ya shirya shekaranjiya fa wani ta gani yana jan wata mota mai kuka kamar mataccen injin kawai ta saka mishi dariya tun bai gane da shi take ba har ya gane,haka fa ta tura kan ta a glass tana kwasar masa dariya,shi ko fahimtar da shi take ya hau zagi harda kira ma Su Abba ɓarayin gwamnati ". Ayman ne yayi zancen. Dariya Ce ta kama Samir kafin ya ce " ohh ina kuka je hala ?" " Mun je aikar Sir Ni da

Chapter 20 of 39