Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
DOMIN KO BAKA SAYA BA ZAKA GAMSU DAGA KALLON SU.💃💃💃 TANA DA DUK WANI NAU' I NA KAYAN ƘAWA NA KWALLIYAR MATA DA MAZA,MASU KYAU KAMA DAGA TOTE BAGS,COMFY BAGS,DUBAI MATERIALS,LUXURY BAGS,LUXURY ABAYAS.FLAT SHOES.Da sauran su. WANI ABU SAI A KHADSEEN'S COLLECTION💃💃💃💃💃💃WO HOHO HAJIYA TA, KE DAI GARZAYA KI CIKA KAPACITYN 💃 KI A KHADSEEN'S COLLECTION Wa.me//. 8149484562 ZA,A IYA TUN TUƁAR TA TA WANNAN LAMBA DAKE SAMA👆 SAI KUMA LINK NA GROUP NA TA A SAMA 👆A CHAN ZAKU GA KAYAN KECE RAINI,KUDAI💃💃 KU GAR ZAYA KU CIKA KAPACITYN KU MANYAN MATA MASU ADO👜👛👠KHADSEEN'S COLLECTION NA AIKAWA DA KAYAN TA A KOWACE NAHIYAR DUNIYA CIKIN GAMSAR DA ABOKAN KASUWAN CI TA.🛍️🛍️🛍️ https://chat.whatsapp.com/H5xKfOMK5QE2YtMirvcsat?mode=r_t _________________ A haka su Baffa na suka same su suna karanta azkar bayan gama addu'oin kasancewar su Baffa na sun tsaya masallacin sauraren wa,azi. Kamar kullum a tare suka ci abincin daren su su uku.Suna gamawa suka fara taɓa yar fira kafin suka yi Sallama kasancewar gobe Akwai makaranta gashi yanzu shatou na zuwa latti kuma ansha mata faɗa bata denawa saboda kullum da faɗa take zuwa dan bata son karatun yanzu ko kaɗan tilasta mata kawai take jin ana yi dan haka kullum yanzu sai tayi faɗa da Inna ni Baffa na yayi ta Rarrashin kayar sa,Bibu na Dariya a haka da lallaɓawa ake samun tana tafiya,kuma ko taje a banza. A ɓangaren Baffa na tambayoyi ne bakin sa game da amsar da mai gari ya bawa shatou sai dai kuma ya share zancen kan wani dalili na sa. A haka Kowa yayi alwallah ya shige suka yi wa juna sai da safe. Dukkanin su sai da Inna ni ta tabbatar da sunyi addu'oin su kafin ta ƙara shafa musu Sannan ta shige tare da abincin ta da bata ci ba. Zaune ta kai kan wata yar tabarmar kabar ta dake shimfiɗe a ɗan tsakiyar ɗakin da yake da ɗan siminti da ya fara ciccirewa saboda rashin isasshen suminti a cikin sa. Abincin ta zubawa ido kafin ta haɗiye wani irin ɗaci A maƙoshin ta.Zuciyar ta ta mata wani irin zafi.Hawayen da take ta dannewa ne suka silalo mata kafin ta ji saukar su akan wuyan ta,hawaye ne masu ɗumi dake nuna tsantsar damuwa da baƙin cikin abin da yake tabbas a gare ta wanda ya bar ta cikin kokwanto. Kuka ne ya ƙwace mata tuno da wani lokaci da ya shuɗe na rayuwar ta,da ta yi cikin gata da soyayya.Sai da tayi mai isar ta sannan ta Share hawayen na ta.Abincin ta fara turawa A hankali tana jin shi kamar tana haɗiyer magani mai ɗaci saboda ƙunci da kewar da ke dabaibaiye da zuciyar ta mai cike da rauni da bege da kewar da bata san adadin ta ba. Sai da taci rabi sannan ta sha ruwa kafin ta yi addu'a ta nemi waje ta kwanta kan ɗan gadon ta. Wani sabon tunani ne ya ƙara kutso mata dan haka ta kai shi gefe ta rufe idanun ta tana ambaton sunayen Allah.Cikin yardan Ubangiji Kuwa Bacci mai nauyi ya kwashe ta. Baffa na ya daɗe yana Zarya a Cikin Dakin sa ya kasa bacci,dan ya so ya ji ya ta kaya tsakanin mai gari da shatou ɗin duk da ya san abu ne mai sauƙi amma lamarin na Bashi tsoro shi bai shirya kai yar shi gidan kowa ba yanzu,Sannan yana da dalilin sa mai ƙarfi akan wannan maganan,dan haka duk yadda ya so ya share ya kasa duk da abun ya san mai sauƙi ne. Numfashi ya sauke kafin shima ya koma kan gadon sa yayi addu,o I ya kwan ta cike da yar damuwa. Shatou ma babu kwane kwane bacci ya kwashe ta saboda an sha ƙiriniya sosai,haka ma ta ɓangaren Bibu dan shi dama baya wasa da bacci ko ƙanƙani ne. " Oummm !Oummm! Oummm " Wannan sauti shine ke shiga cikin Kunnuwan ta yana karya duk wasu gaɓɓan jikin ta wani irin zubawa yaran tayi idanu daga bakin bishiyar da take zaune ta jingina bayan ta da alama iska take sha,tana bin su da kallo kamar ta ga sabuwar halitta. Sai dai murmushi ta samu kan ta da sakar musu cikin mamakin kiran ta da sunan da suka yi. Tana ƙokarin riƙo hannayen su ne ta ji an fisge su da ƙarfi ana ƙoƙarin jefa su a wani rami mai zurfi cike da tashin hankali ta ke ƙoƙarin ganin mai shirin yin wannan aika aikar da hana afkuwar hakan cike da tashin hankali...A zabure ta tashi tana mai nana ta Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un fuskar ta jage jage da hawaye na tausayi ga wata irin rawa da zuciyar ta keyi kamar ana kaɗa ganga mai taushi. Mafarkin take ta, tariyo wa sai dai mamaki ne fal a ranta na wannan suna da suka kira ta da shi. Fuskokin su take ƙoƙarin hasasowa sai dai ta kasa amma duka muryoyin sun zauna a cikin ƙwaƙwalwarta wanda har yanzu sautin yake ƙara hargitsa tunanin ta tare da girgiza naman jikin ta. A jiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana shafe zufan da yake tsiyayar mata na tashin hankalin abinda ta gani yake shirin faruwa kafin ta miƙe Tayo Alwallah Nafila tayi gwargwadon iyawar ta sanann tayi Addu'oin ta ta koma bacci sai dai abun ya gagara dan bacci ya ƙi kwasar ta wanda bata samu, ya kwashe ta ba sai gangar asuba. Yau kusan wata guda kenan Iro bai ƙara tuntuɓar Shatou da wata magana ba Shatou bata san abinda mai gari ya ce masa ba amma ko mene ne taji daɗi sosai dan haka ta cigaba da rayuwar ta hankali kwance cikin rashin damuwa, haka ma Baffa na.Yayi matuƙar farin ciki.Yanzu hankalin Shatoun sa ya kwanta. Bawan Allah in suka haɗu kan hanya yayi ta kallon ta cike da mamakin abun da zai sa mahaifin sa yi masa kashedi da dakatar dashi da soyayyar sa ga shatou duk iya tunanin ya rasa madafa. Sai dai ya ƙwallafawa ran sa sai da ya samu shatou ko ta ƙarfi ne kuma zai nemi soyayyar ta ko mai gari bai so ba dan shi Dagaske yanzu,son ta yake yi har cikin ran sa,kuma idan har bai samu Shatou ba sai dai abin da ake gudu ya faru a ƙauyen,dan ba zai bar kowa ya same ta ba ya sha wannan alwashin ya fi a ƙirga. A ɓangaren shatou ƙiriniya yanzu sai abinda yayi gaba ga karatun yan zu idan an tura ta sai ta yi daji wajen farauta tun Inna ni da Baffa na na faɗa har sun zuba ma sarautar Allah ido dan ƙiriri take nuna rashin son karatun na ta yanzu Addu,a kawai suke bin ta da ita. A ɓangaren Aikin da ake yiwa ƙauyen an samu cigaba sosai aiki na ta kan kama babu kama hannun yaro abun ka ga an zube kuɗi ƙasa. " Ummahhh " ! REENA ce ta zo da kuka tana sanye cikin wando da t-shirt masu kyau gashin ta ya sha gyara kai da ka gan ta kasan suna cikin gata.Kuka take tana nunawa Ummah ɗin hanunn ta wadda ta sha ado itama cikin wata dakakkiyar shadda ta yi kyau har ta gaji. Dan yanzu ta fito da ga kitchen ta ɗan duba abubuwan da aka jera kan dinning. Hannun Ummah take kallo, ganin ta sangaye shi kamar ya samu rauni da yawa. " Me ya samu hannun ta furta a natse cike da yar damuwar kukan na REENA " " Hannu na LEENA ta karya daga kawai na taɓa nata chocolates na tsarabar Yaya Samir ita bata shanye nata ba shine na ɗauka zan sha ko fasawa ban yi ba ta murɗe mini hannu tana kira mini ɓarauniya ".Ta kai ƙarshen maganar tana fashewa da wani sabon kuka. Ɗan jimm Ummah tayi kafin ta sakin iska mai zafi cike da wata sabuwar damuwa yanayin alamar ɓacin rai na bayyana akan fuskar ta. Hannun ta riƙa wata ƙara LEENA ta saka tana batun sumewa Ummah wajen saboda ta taɓa dai dai wajen da yake mata ciwo. Cike da damuwa da tashin hankali Umma tayi kan ta tana rungume ta kafin ta riƙo hannun ta ɗaya mai lafiya, zauna wa da ita tayi kan kujera har lokacin tana rusar kuka. Rarrashin ta Ummah ta fara yi wadda take tunanin REENA ta samu Bone dislocation Wayar ta,ta fara ƙoƙarin dannawa domin kiran Abba sai ga REENA ta fito tana faman cin chocolate hankalin ta kwance. Fuskar nan Tata ɗaure kamar an mata mutuwa musamman yau da take jin Haushin kowa saboda dawowar ta Bilal dan har yanzu basu shiri tun maganar da suka yi akan wayar Samir ba su ƙara magana ba,bata nemi shi ba shi ma haka ya fita iskan ta,Ummah da Abba duk suna lura sai dai babu wanda ya shiga cikin faɗan sun san daya dawo gidan zata sauko dan shi sun san ayyukan gaban sa,yanzu haka ya ma manta da suna faɗa dan duk yayi waya da ɗayan su yana yawan tambayar ina LEENA da REENA Sai dai duk Suka yi waya da REENA itama takan ce ga LEENA ita kuwa da ta fahimci dashi Reena ke waya sai ta bar wajen dan dashi har Reena ɗin haushi suke bata dan cewa take yafi son Reena. Sai dai cikin Wannan ɗan lokaci abun ya ɗan yi sanyi sai dai sukan yi sati basu yi magana ba sannan kowaccen su ta na Bedroom ɗin ta sai kwanan nan ne ma aka samu dai dai to bayan Ummah ta shiga lamarin ita da Abba. Kuma hakan bai da na saba da ƙoƙarin Samir dan kafin ya wuce daga hutun na sa da ya ɗauko ganin yawan faɗan na su ya tayar masa da hankali hakan ya sa ya sanya aka yi musu sauka dan samun saukin wannan lamari wajen Ubangiji da ya jarabce su dan yanayin da suke ciki ɗin jarabawa ce Babba Yadda suke hantarrar junan su ko kashe juna suna iya yi ga dambe take hakan shi ya ɗaga hankalin Samir ba tare da ya sanar wa kowa abun da yayi ba ya aiwatar cikin yardan Ubangiji kuwa aka samu sassauci sai dai gabar haka kawai da suke yin ta babu dalili LEENA zata ɗaurewa Reena, yar uwar ta tayi ta bibiyar ta jin meta mata,ita kuwa bata faɗi sai ta share ta dan babu dalili,sai wata rana da Reena ta matsa kai tsaye LEENA ta ce mata ta tsane ta duk da ƙarancin shekaru irin na REENA ta ji zafin kalamin sai dai bata faɗawa kowa ba amma ya zauna ranta duk da ta san cewa yar uwar ta ta faɗa ne kawai bada wata manufa ba,kuma ba tana nufin abun da ta ce bane a gare ta.Kuma tun daga lokacin itama Reena sai ta fita iskan ta dan haka kawai ta ji ita kan ta bata buƙatar magana ko da Leena ɗin ne bare zama inuwa ɗaya dan haka kowaccen su ta koma ɗakin ta dake sama. "Ina tunanin SARINA ta samu Gocewar ƙashi Abban su,gashi sai kuka take yi" REENA da jin haka kuwa ta ƙara fashewa da kuka dan sun taɓa Rakiyar Hamrah da ta goce aka yi mata gyara sai da ta yi fitsari a wando saboda a zabar da taji su kan su sai da suka koka duk rashin jituwar Leena da Hamrah ɗin sai da tayi mata kuka bare ma ita Reena uwayen kuka. Yanke wayar ta yi cike da damuwa kafin ta ƙwalawa Rabi kira wadda ke kitchen suna aiki. Da sauri rabi ta zo. Sai da ta gama sauraren Maganar Ummah kafin ta ce " Subhanallah Alinatu baki kyauta ba samm ji bi yadda yar uwar ki ke kuka ". Tana jin abinda Rabi ke faɗa amma bata ko kalli sashen da take ba sai ma cigaba da cin chocolate ɗin ta,tayi tana turo baki gaba wanda ke nuna tana jin ta sarai. Ummah ce ta katsa mata tsawa hakan ya sa ta ɗan zabura dan ta fahimci iskancin LEENA gaba yake yi. Sai kuma ko me ta tuna sai ta sassauta murya cike da Rarrashi ganin yadda LEENA tayi Narai Narai da idanu alamar kuka zata yi. " Haba ALINA dubi yadda kika ji ma yar uwar ki,yanzu kenan nasihar da na ke muku a ban za,ace akan chocolate da gashi nan a ko ina an saka muku shine kika karya mini hannu Yarinya, Alina kin kyauta kuwa,Dubi yadda take kuka ita kaɗai ta san zafin da take ji dubi yadda hannu ke walƙiya har ya fara Kumburewa ". " Ummah ai Chocolate ɗin ya Samir ne kuma itama ai ya bata nata shine ta shanye nata,kuma zata shanye nawa mayyar ". Bakin ta Ummah ke ƙoƙarin kaiwa bugu Rabi ta hana dan ta ji Haushin kalmar mayyar da ta kira wa Reena ɗin. " Wato ke Bakin ki bai da saiti ALINA,kin cewa Ya ta Ɓarauniya gashi ko biro ba bata taɓa ɗaukar min ba,yanzu Idan Bilal ya dawo sai ki masa bayani ,dan a wannan karon ba zan raba ki dashi ba tun da na gane har yanzu kin kasa yin hankali ko Tausayin ta ba kya ji kin ƙara daɓa mata wannan muguwar kalmar,kuma kar naji,ko na ƙara gani kin kira wa SARINA wayen nan sunayen ko makaman tan su,ko Abban ku wannan karon bana fatan ya ɗaga Miki ƙafa sakarya " " Rabi riƙa ta ku tafi Driver ya kai ku bari na ɗauko kuɗin gyaran ". Miƙewa Ummah tayi ta haye upstairs da ɗan sauri ko kallon Sashen da Leena take tsaye bata yi ba wadda ko gizau bata yi ba hawayen ma yaƙi sauka idanun ta sun bushe babu ko alamar hawaye a idon ta ko ɗigon Tausayin Abin da ta yiwa Reena dan a cewar ita ta nema tun da ta taɓa mata abun ta. Rabi kuwa riƙa Hannun REENA tayi bayan ta karɓi kuɗin hijabin ta da ɗauko ta sanya tare da ɗaurawa LEENA gungun mayafi da Ummah ta ɗauko mata daga bedroom ɗin ta. " Baba Rabi Zanje ". LEENA Ta furta cike da ƙuruciya da rashin damuwa. Rabi saƙaƙe tayi tana kallon ta ganin ƙarfin halin ta kafin kuma ta ce " fito muje ". A zuciyar ta kuwa tana mata addu'ar shiriya daga ita har Reena da samun haɗin kan yan biyun. " Wallahi babu inda zata bi ku,ta zauna gida,gashi ma BILAL ya min saƙo ya iso lafiya,ina son ya karya da ita dan uban ta,bari ma na masa saƙon abun da tayi yana isowa yayi mini maganin ta sha sha shaar yarinya ". Rabi kuwa jin Ummah ta rantse ga ɓacin rai da ta gani kwance akan fuskar ta hakan ya sa babu musu ta fice tare da REENA ɗin. Wadda ke cigaba da rera kukan azaba. Junaid ne suka ci karo dashi zai shiga Sashen su kuma sun fito ganin yanayin da REENA ke ciki hakan ya sa ya bi su tare a gaban sa aka yi komai dan kuɗin ma shi ya biya duk da rabi ta nuna masa Ummah ta bada kuɗin. REENA ta sha kuka ƙiris ya rage ta yi fitsari a wandon ta saboda azaba. Dukkanin su sun tausaya mata matuƙa fuskar ta, take tayi jaa idanu suka yi sutu sutu gwanin ban tausayi. Junaid yayi ta tambayar Rabi matsalar ta auku.Sai dai ta yi ta masa kame kame. Hakan ya sa ya share bai ƙara tambaya ya fahimci bata son sanar masa. A ɓangaren LEENA kuwa Haushin maganar Ummah ta ji dan haka ta kwasa da gudu tana fashewa da kuka ta shige Bedroom ɗin ta ta saka lock.Sai da ta rushi kukan ta na rashin dalili kafin Bacci yayi a won gaba da ita.Dan haka koda BILAL ya dawo bata sani ba. Ita kuwa Ummah cigaba da ayyukan su suka yi tare da sauran masu aikin da ke ta kai kawo suna haɗa duk wani abu na buƙata kasancewar BILAL da Ummah ta sanar musu ya iso ya kafin ya shigo tana son komai ya zama ready. Koda Su Rabi suka dawo sun tarar da motocin su B ɗin ga kuma yawan sojojin da aka samu a estate ɗin. A kafaɗa Junaid ya ɗaura REENA dan tayi baccin a zaba sauƙin ta ma sun bi ya wani Babban Pharmacy an siya mata pain relieve anan kuma ya saka ta dole ta sha sannan suka yo gida tare da yar siyayyar chocolate da yayo mata. Da sallama ya shiga a Babban Falon Na Umma. Sauke ta yayi akan doguwar kujerar da Bilal yake zaune a gefe ya gyara mata kwanciya tare da ɗaura hannun inda ya dace da ya sha ɗauri sai walƙiya yake yi an shafa masa magani. Sannan ya ajiye magungunan a kusa da ita,tare da ledar chocolates ɗin. Cikin ɗan kamewa B da ya kasa haƙuri ya kalli Junaid dake gayar dashi cike da girmamawa da yi masa sannu da zuwa ya furta. "Me ya same ta ne naga an ƙudundune hannun haka,kamar wanda ya samu dislocation"?. Cike da girmama Junaid yace masa eh shine sai dai shima bai san inda ta samu raunin ba dan Baba Rabi ta kasa faɗa masa. Tunda ya ji cewa Rabi ta ƙi faɗa ya san inda matsalar ta afku sai dai cikin mamaki yake ƙara kallon REENA da fuskar ta tayi jaa idanun ta sun kumbura wnada da gani na azabar da ta sha ne. Ya ce " OHk " Sai a Sannan ya karɓa gaisuwar Junaid da ya ƙara maimaita masa dan ya san ya'yan nasu baya ɗaukar wasa. Cike da kulawa yake amsa masa da masa tambayoyi yana bashi amsa cikin basa girman sa. Dai dai nan Ummah ta fito Gaisawa suka yi da Junaid ɗin kafin ya fice dan ya samu kiran Abba ƙarami da alama aikar sa zai yi ko abinci za,a kai masa office,dan haka suke yi dukkanin su daga shi Har Abba idan aiki yayi musu yawa sai a dafa akai musu ba sai sun ci na cafteria"n ma'aikatar ta su ba ko na restaurant.Duka wannan sabon Matayen su ne,Ummah da Hajiya dan sun fi sauran kulawa duka a gurin mazajen su duk da suma sauran nayi amma na su na dabanne.. Ficewa yayi yana musu Sallama tare da ƙara yiwa Reena Addu'ar samun lafiya. Ummah da ta ga Bilal dan bata san har ya dawo ba ta zata idan yayi fresh up ɗin tunda ya cika tun bin sa ya ɗan kwanta ya ɗan huta sai ta gan shi zaune fuskar nan cike da masifa da ko bata tsaya bincike ba ta san ya gane inda matsalar take,dama tun wajen cin abinci yake ta tambayar Inda suke Ummah tace Leena bacci take yi Sarina kuwa sun fita da rabi sai bata faɗa masa ba,dan haka ya kasa yin Bacci ya zo ya ga ƙannnen na sa da yake jin ya shekara bai saka su a idanun sa ba yayi kewar su. Dan haka yanzu bata ce komai ba sai ɗaukar Reena ta yi ta haye sama da ita ta kwantar akan bed ɗin ta.kan ta,ta sha fa kafin ta tofa mata Addua sannan ta rufa mata blanket mai taushi ta fito tana sayo mata bedroom ɗin. Rabi ce tsaye tana masa sannu da dawowa cikin girmamawa haka ya amsa mata shima yana sauke kan sa kafin ya ce '' Me ye silar gocewar SARINA ". Rabi ta fahimci bada wasa ba jin yadda ya kira Sarina ɗin dan bata cika jin ya kira su da cikakken sunan su ba. Cikin ɗan damuwa ta ce '' Ba wani abu bane ba fa Alhaji ƙarami dama chan wajen wasar sune da yar uwa .." .. Shiru Rabi tayi ganin kallon da ya sauke mata. Hakan ya sa ta yi shiru ta kasa ƙarasa zancen. Shima komawa ya jingina da kujerar yana sauke numfashi da ajiyar zuciya wani irin damuwa na dabaibaye shi ya rasa wace irin Masifa ce wannan ke bibiyar rayuwar ƙannen sa shi har ya fara zargin lamarin na su. Rabi kuwa kuɗin da ta zo kawo ma Ummah ne na aikin da Junaid ɗin ya biya ta koma kitchen da sauri dan ta ga zuciyar sa ta motsa idanun sa har sun garwaya sun rikiɗa. Yadda jijiyoyin kan sa suke harbawa hakan ya ƙara tabbatar wa Ummah da ta ke ƙare masa kallo tun saukowar ta. Ta san cewa ya tabbatar da aikin na Leena ne Ita ma ajiyar zuciya ta sauke cike da damuwa. Kafin ta zauna kusa da shi cike da so ta kamo hannun sa ɗaya da ya dafe goshin sa dashi da yake ɗan sara masa. " Soja " Ta kira a hankali Muryan ta ƙasa ƙasa. " Kai kake ƙarfafa mini kai da Abban ku,kune na farko wajen ƙarfafa mini akan yara na,me ya sa yanzu zaka bayyanar da taka Damuwar da zata iya linka mini ɗimbin Damuwar da nake ciki,ya ra na suna cikin wata irin jarabawa mai tsani, ban taɓa sanin yan biyu na tsanar junan su ba sai akan na wa,ban taɓa sanin suna cutar da Junan su irin haka ba sai akan nawa shin me ya sa,me ya sa BILAL, Wannan wace irin jarabawa ce ".?? Kuka ne ya ci ƙarfin ta cike da wani irin ɗaci ya rungume ta ya fara rarrashin ta. " Me kake tunanin mutane zasu faɗa akaina akan tarbiyyan su,ina jin tsoro Mai girma akan rayuwar da suke yi mai ban al'aja.." Kuka ne ya ci ƙarfin ta a karo na biyu Shi kan sa BILAL hawayen ya share masu ɗan ɗumi. Ya cigaba da rarrashin Mahaifiyar sa Abar son sa yana haɗiye wani irin dutse mai ƙarfi na baƙin ciki mai girma da ya tsaya masa a maƙoshi.. Shiru falon yayi sai Shesshekar kukan Ummah gwanin ban tausayi. Abba ne da ya shigo tun ɗazu yayi gyaran murya.Shima idanun sa sun kaɗa sun yi jazir wani irin yanayi yake jin zuciyar sa ciki wanda ya daɗe da shuɗe masa wanda yake haɗe da damuwar ya yan sa da yanayin da suke ciki da har yanzu ya kasa natsuwa da zantukan malam Hambali sannan yana tsoron kuskure masa kasancewar ya san Malam babban Malami ne masanin Addini ya san ba zai mishi ƙarya ba duk inda zai je dai maganar ɗaya ce ko kuma ya samu aka sin ta makaman ciyar ta amma har yanzu abunda malam yayi yana ransa na rarraba shafa ruwan addu'ar a tsakanin su Leena,yana jin tabbas akwai abinda malam yake ɓoye masa.✍️ Nifa kaina cigaba da yake da ƙullewa🚶🥺 Amma dai muje zuwa zamu🚴🚴 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P________3️⃣2️⃣➖3️⃣3️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* Ba tare da ya ce komai ba ya haye upstairs jiki a saɓule daga ganin yadda yake tafiya sun san yanayin da zuciyar sa ke ciki kai Ummah ta ɗauke daga kallon sa tana sauke a jiyar zuciya kafin ta miƙe ta bi bayan sa. Guntun murmushi ta sakar wa Bilal kafin ta bar wajen bayan ta ɗan bubbuga kafaɗar sa. Numfashi ya sauke mai zafi tare da ajiyar zuciya kafin ya miƙe ya bar Sashen gaba ɗaya domin wani irin sarawa kan sa ke masa. Sashen sa ya shige dake iri ɗaya da sauran ginukan. Zaune ya kai kan Corner seater da ke kusa da ƙofa yana sauke numfashi. Ganin damuwa na neman dabaibaiye shi hakan ya sa ya miƙe ya shige Bedroom ɗin sa da babu wata hayaniya a cikin sa so simple sai ƙyalli yake Saboda ana gyaran sa duk bayan ɗan lokaci. Hayewa yayi kan gadon na sa bayan ya zare rigar sa Gudun Ac ya ƙara ta hanyar remote ɗin sa kafin ya rufa tafkeken blanket mai taushi dake ƙawace da bed ɗin. Addu'a yayi ya tofa kafin a hankali bacci ya fara fisgar shi,sai ya fara bacccin ya farka kuma a firgice kamar mai jin tsoro da alama akwai shuɗaɗɗen lokacin da yake tunowa ko yake gani a idon sa a wannan ɗan baccin dake fisgar sa.Addu,oi ya cigaba da yi,Har kuma a hankali bacccin ya ɗauke sa mai nauyi dan tafiyar safe ce yayo. " Na daina damuwa fa Abban su Alina,Kawai dai ina cikin wata irin damuwa ce akan yanayin su Twins,Zuciya ta na shiga ƙunci a duk lokacin da na gan su haka,Abubuwa da dama nake tunawa, abu mafi muni ace naka sa tarbiyyantar da ya ya na " Hawaye ne suka silalo mata masu zafi kafin ta

Chapter 25 of 39