Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 _*KURMAN ƘADDARA*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P________3️⃣4️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* Muryan sa mai sanyi ce ta da katar da Mubarak ɗin daga ƙoƙarin yin serving ɗin sa,bayan ajiye kayan,yana furta " I'm full may be later " Ɗan kallon sa ya yi kafin ya sauke kan sa ƙasa abun ma dariya ya bashi ganin yadda ya ƙara tsuke fuskar sa. Kai Mubarak ya jinjina kafin ya ɗauke komai daga wajen ya kai shi inda ya dace. Sannan ya fice yana girgiza kan sa da mamakin ƙiyayyar Mahaj ɗin da abinci. Shi ko yana tabbatar da Mubey ya fice ya harari bayan sa kafin ya sauya tashar yana maida ita zuwa asalin inda yake inda yafi enjoying.( Kowa da kiyon da ya karɓe sa "🤗 Anan wajen bacci ya kwashe sa kamar wani Baby. Mubarak kuwa ya zama ya ci,ya ƙoshi yana kallon wani series Chinese films da ake haskawa a iQiyi mai suna Hidden Love,Duk da yadda film ɗin ya ɗauke masa hankali saboda yadda yayi kyau amma da ya tuna da mai kallon Cartoon sai yayi murmushi da girgiza kan sa a hakan aka kira Sallahn la,asar Kafin ya fice wajen Sallah kasancewar ya san MAHAJ baya wasa da Sallah dan haka kai tsaye ya wuce masallaci ya san zai gan shi a chan. A ɓangaren Mahaj kuwa bai farka ba sai da lokacin Sallahn La,sar yayi sannan ya farka Alwallah kawai ya yi sannan ya wuce masallaci. A sahu ɗaya suka tsaya ana gama Sallah bayan gama addu,oin sa ya fito cike da natsuwa. Mubarak ma fitowa yayi chan ya hango sa dan haka ya taka da ɗan sauri dan yan zu yana son yama sa bayanin Yadda komai ya wakana a zuwan su ƙauyen su Shatou har da son kawo masa Gulmar shatou,Dan Abbu ya ce ya riƙa sanar masa da duk abinda yake wakana koda bai tambaya ba. A jere suka isa Babban falon. Zama yayi yana kallon dinning alamar sai yanzu yayi ra,ayin cin abincin dan haka Mubarak fahimtar abinda yake nufi hakan ya sa ya haɗo masa komai na buƙata ya kawo masa. Sai da ya gama shan ƙamshin sa alamar har yanzu fushin ne sannan ya fara cin abincin mai tsada wanda ko China sai masu kuɗi ne ke cin irin sa, halittun ruwa ne masu tsafta da wasu irin sinadarai yadda dai kuka san abincin su yake. Ya taɓa snacks kaɗan sannan ya ci asalin abincin na China dan ya ma fi cin sa Sosai,dan ko da safe cuppy kawai ya sha. Yunwa ta tarar masa dan haka ya ɗan tsakura babu laifi. Yana gamawa Mubarak ya kwashe komai ya mayar dashi inda yake kasancewar gidan na'urori ne ta ko ina take kayan da yayi amfani da su take ya wanke komai tare da tsaftace sa ya mayar dashi mazaunin sa sauran abincin ya saka fridge . Zama yayi kaɗan nesa da MAHAJ ɗin ya ɗan mayar da hankalin sa kan Hidden love ɗin da ya mayar yanzu dan cigaba da kallon sa. Mahaj da ya san cewa magana ce bakin Mubarak ɗin yayi dan ya karance sa take taken sa gyaran murya yayi a hankali,irin na ina jin ka. Kallon sa Mubeey yayi kafin ya saki guntun murmushi. Mahaj ya ga murmushin dan haka ya share sa. " Eh dama ina son maka magana ne akan aikin ƙauyen su yarinyar chan Shatou mutuniyar ka ". Wani irin kallon ban fahimce ka ba Mahaj yayi masa. Kan sa ya shafa ganin kamar bai gane ba saboda sunan da ya ji ya ambata,duk da kuma sarai ya san wadda yake magana yana ji a jikin sa ya fahimce sa.Rainin hankali ne kawai. Idanun sa ya ƙara zuba masa alamar ƙarin bayani. Dan haka ya furta " Yarinyar da kuka yi faɗa da ita a zuwan mu ƙauyen a wala ". Idanu Mahaj ya lumshe irin dai yadda kuka san yanayi kafin ya buɗe su tar akan Mubeey ɗan kallon sa yayi na daƙiƙa kafin ya ɗauke kallon sa kan sa yana sauke ajiyar zuciya tare da ƙara shigewa cikin kujerar kamar wani Basarake. Mubarak kuwa fahimtar cewa ya fahimce sa ne ya sa ya cigaba da magana yana sakin guntun murmushi yadda yake tuno badaƙalar su. " Aiki ya fara,komai Abbu ya saka hannu an gabatar ranar ma mutuniyar ka wani ya jogano ta ta kai shi ƙara gurin mai gari tana ta kuka ". Kalaman Mubarak yake saurare da farko ya mayar da hankalin sa kan sa sai dai jin sunan mutuniyar ka da ya maimaita masa ya kuma tabbatar da wadda yake cigaba da alaƙantawa dashi hakan ya sa ya miƙe yana Jefawa Muby wani irin kallo kafin ya ja mugun tsaki yana furta " ka daina alaƙanta ni da wanchan stubborn girl ɗin ".Yayi zancen iya kan laɓɓan sa kamar baya son Mubeey ɗin ya ji shi ko Mubarak sarai ya ji shi dan haka yayi kamar bai ji ba ya ƙara ɗaga murya yana furta " Tayi ta neman ka ". Chak ya dakata daga tafiyar da ya fara domin lamarin Mubarak ya fara shige masa hanci ya fahimci kamar ya fara wuce masa gona da iri duk da wasu lokutan haka suke saboda sabon da ke tsakanin su. " Tayi ta auna mini harara,tana ɗaga kai ganin inda zata gan ka ". Ɗan lumshe idanun sa yayi kafin ya janye daga kan mubeey da ya ɗan waiwayo yana kallo. Shi ko mubeey ganin kamar kallon na sa na neman ƙarin bayani ne hakan ya sa ya cigaba da maganar sa. Ƙaramin tsaki ya ƙara jaa kafin ya bar wajen cikin ɗan sassarfa. Mubeey kuwa ƙaramar dariya yayi yana cigaba da kallon sa hankali kwance haka kawai yake son ƙara ganin haɗuwar MAHAJ ɗin da shatou. Kayan jikin sa ya tuɓe duka kafin ya shige haɗaɗɗen toilet ɗin,tun da ga sama har ƙasa ruwan yake dukan sa bayan tsayuwar sa wajen sabod Shower ɗin irin na'urar nan ce mai amfani da tsayuwar mutun ne kana jayewa kuma zata ɗauke ta kashe kan ta. Sai da ya ɗauki lokaci a cikin toilet ɗin kafin ya fito mayukan sa masu tsada ya murza ma jikin sa kafin ya sanya wasu kayan mara sa nauyi riga da wando yan Companyn apple rigar armless jacket ya ɗaura kai bayan ya ƙara gyara haɗaɗɗen gashin kan sa da be san adadin abun da yake kashe masa ba. Turarukan sa masu tsada ya feshe jikin sa da su kafin ya fice daga bedroom ɗin yana ɗaura p_cap a bisa lallausan gashin sa. Ƙamshin sa ne ya fara bayyana kafin isowar sa wajen dan haka Mubarak ya zuba ma wajen da zai ɓullo ido shi ɗin ne dai ɗauke da system a hannun sa sai tsadaddiyar wayar sa. Kunnuwan sa duka biyun maƙale da Bluetooth fari ƙarr kamar kayan da ke jikin sa dan har Wandon irin buɗaɗɗen nan ne kamar pallazo sai dai shi guntu ne yayi kyau matuƙa kyau iya kyau. Ɗauke idanun sa yayi da ga kan sa. Kafin ya miƙe ya zari keys ya bi bayan sa. Kasancewar ya san bai wuce fita zai yi ba gashi Abbu bai son yana driving a cewar sa bai isa fara driving ba duk da ya san ya iya amma yana tsoron yadda dokokin ƙasashen ƙetare suke su,gashi ko kuskure basu sani ba kar wata rana ƙaddara ta hau kan ɗan gaban goshin sa dan haka ya ce Mubarak ya daina barin shi yana tuƙi duk da kuwa gwanewar da yayi. Gaba ya shige bayan Mubarak ya buɗe motar wanda ya ke ƙara jinjina hali irin na MAHAJ yana haka i na ga nan gaba ya san maganar kurame zasu komawa yi gaba ɗaya. " School Auditorium zamu je "Ya furta cikin muryan sa mai nuna yanayin sanyin sa. Kai tsaye Mubarak ya fahimci inda yake nufi dan haka ya ja motar suna ficewa bayan wangale musu katon gate da aka yi. Sunyi yar tafiya mai ɗan nisa kafin suka isa haɗaɗɗiyar makarantar ta su.SHINHWA University Babbar makaranta ce da take da manya manyan sassa kama daga primary secondary har zuwa tertiary,sannan makarantar biyu ce akwai ɗaya a Korea komai ɗaya da wannan bayan haka suna da sassan su a cikin zagayen Beijing da sauran garuruwan Ƙasar. Makaranta ce ta masu kuɗi da mulki domin duk wani mai maiƙo yana cikin wannan makaranta. Bakin Wani ƙaton Hall yayi parking. Shi ya buɗe da kan sa kasancewar shi kaɗai suke jira dan bai so zuwa ba ma amma saboda jin wani yanayi a jikin sa kamar kasala ya sa ya yanke shawarar zuwa wajen ko dan ya wartsake. Shigar su wajen ne ya ƙara bayyanar mini da girman da wajen yake da shi waje ne mai Shegen kyau ya Tsaru iya tsaruwa komai na sa red kama da kujeru har zuwa curtein komai ya yi kyau ga wasu irin haɗaɗdun kujeru masu kyau,kai daga nin yadda komai yake tsare kasan makaranta ce ta manya board ɗin su ma abun kallo ne. Tun da suka shiga ka fara jin shin shin na tashi a tsakanin su musamman Mubarak da ya fi sakewa.Abun ka da Chinese.Shi ko iya ka ya gyaɗa kan sa da ɗaga hannu ga wayen da ke ta faman furta masa nî háo?.(how are you) A chan ƙasan maƙoshi kawai yake amsa wa da fine yana zama fuskar nan dai sai sa sai sa. Haka suka fara gudanar da Rehersal Presentation ɗin su saboda sun gayyace shi ne ko zai taimaka musu da wani abun duk da gobe ne za,a yi. Mutun uku yayi yan China kafin ya miƙe kamar an masa dole yayi ya yi musu yan gyare gyare sannan ya rufe da xié xíe (Thanks you) Dukkanin su tafa masa suka yi. Godiya suka masa kafin suka watse taron cike da jin daɗi dan yana cikin ɗalibai masu ƙwazo sun san zai tallafa musu sosai duk da suma ba baya ba. Wajen wani gidan shaƙatawa suka nufa bayan ya sanar ma Mubarak ɗin dake ta murmushin jin daɗi dan baiwa irin ta Mahaj na burge sa. Ya san dole gobe ya burge manyan professors. Sun jima wajen kafin ya gama hutawar sa sannan ya fito ya samu Mubarak da yayi zaman sa cikin mota ya ɗan kwantar da seat ya kunna ƙira,a yana saurare tare da bin babbar hanyar titin da kallo mai cike da tsari mai kyau kowa sai harkar gaban sa yake yi. Yana shiga ya rufe motar hakan ya sa Mubarak sanin shigowar sa. Babu wata magana yaja motar dan ba yau ya saba da halin sa ba. Gida suka wuce direct koda suka isa ana kiran Salloli kasancewar dukkanin su da alwallan su ya sa kai tsaye suka shige masallaci ana gamawa kuma kowanne su ya fito dan mahaj ya riga fita ma kafin Mubarak.. Yau ko zaman falon bai yi ba ya zarce war sa sama. Wayar sa ya zuba ma ido yana kallon ñumban Ayya da yayi kewar ta sai dai ya san ko ya kira magana ce mara daɗi zai samu kamar koda yaushe. Numfashi ya sauke mai ɗan fita da hayaƙi na yanayin weather ɗin garin kafin ya danna mata kira. Saboda Allah ya saka masa ƙalahucin Ayya Saboda ita ya buɗe ido ya gani uwa duk da rashin mutuncin da take masa yakan ji kewar ta,kuma bai cika ganin baƙin ta ba kan hakan dan ya san tana da dalilin ta wanda ya rasa gane dalilin da ya sa har yanzu da ya girma fentin bata goge masa shi ba,yana jin tana yawan saka mahaifiyar sa cikin zancen kuma ya san wata rana dole zai san inda Ayya ta dosa. Laifin me kuma mahaifiyar sa ta yi da ta chanchanci yaɓin magana a gurin Ayya duk da cewa ta na ƙasa kwance.Idanun sa ne suka sauya sako wannan tunanin da yayi.Iska ya ɗan furzar kafin ya maƙala Bluetooth ɗin sa a kunnen sa. Ringing daya ba,a ɗaya ba sai ana biyu aka ɗaga. Shiru aka yi ta ɓangaren Ayyah kafin a hankali cikin Muryan sa mai sanyi ya furta " Ayyah Barka da dare ". " Barka " Ayyah ta amsa kamar an mata dole. " Kin wuni lafiya " ? " Da ban wuni ba ne zaka ganni,ja'irin yaro mai mugun hali,halin ne na uwar ka zaka nuna mini hi'illanci,ka ji murya ta garas nake,ina ruwan ka ma da yini na ne, kake tambaya na akan wuni lafiya,to nace ban wuni ba ka haɗa taro kayi party mtsww mugun iri kawai,Ragin dashin ɓarayi,an dai cuce ni wallahi " ƙyatt ta kashe wayar tana ƙara jan mugun tsaki. Tun da Ayyah ta fara magana ya rintse idanun sa da ƙarfi mafi munin kalaman da ya ji na ƙarshe su suka ƙara ta fasa jinin jikin sa wani irin rawa jikin sa ya fara kamar mazari zuciyar yan maza ta motsa. Yafi ƙarfin mintuna biyu a haka kafin a hankali ya sauke a jiyar zuciya wani irin rauni na bayyanar masa idanun sa ya ware da suka chanja launi kafin ya zuba ma wayar idanu. Kalaman na Ayyah na yau sun fi na koyaushe yin nauyi a gare sa.. me take nufi da ragin dashin ɓarayi,me take nufi da mugun iri wace irin cuta ce take cewa an musu ... Haka ya jero wa kan sa wayen nan tambayoyin sai dai babu mai bashi amsar su.Duk iya dogon tunanin sa ya kasa gane inda aka dosa. Kan shi ne ya fara sara masa hakan ya ƙara sanya jikin shi yin sanyi idanun sa ya rufe cike da tunani iri iri.Kiran Sallahn Isha ne ya tayar da shi daga wajen. A ɓangaren Ayyah kuwa sai da ta gama wayar ta gama yaɓa maganganun ta sannan ta lura da wanzuwar Abbu a wajen da ya shigo tun kafin ta ɗaga kiran ta fara mita. Da farko har ta nuna alamar ɗan razana sai kuma ta taɓe bakin ta tana kallon ƙwayar idanun sa da suka sauya daga fari zuwa jaa ɓacin rai da baƙin ciki da damuwa sun mamaye su jijiyoyin kan sa sun miƙe kamar yadda na MAHAJ suka ɗaga saboda yadda zuciyar Shi ta motsa. Yafi mintuna shida wajen tsaye a gefen ta yana kallon ta kafin ya ji saukar furucin ta. " Ka ɗaga mini akai kar ka jagula ni,haka kawai ka saka wa kan ka damuwa har ta kai ka da hawan jini ina dalili,ka san kai kaɗai nake gani ita wacchan gantalalliyar daɗi miji ta bar ni nan dan haka ka natsu ka samu lafiya,shi wanda kake ji ma tausayi bai ji ma kan sa duk wata magana tawa bana ganin tasirin ta gare shi,ɗan neman mai zuciya irin ta uwar shi ". Ajiyar zuciya Abbu ya sauke domin wani irin Tausayin ɗan sa da ya saukar masa dan a gaban sa ya fara maganar, maganar ma na da ko shi da yake mahaifin sa ba kullum yake samun irin haka ba ya rasa wace irin ƙauna MAHAJ yake yiwa Ayya da ya kasa share lamurran ta duk da musgunawar da take masa. Yadda ya ji Muryan ɗan na sa cike da ɗan farin ciki yake gayar da Ayya ɗin hakan ya ƙara karya masa jiki domin a handsfree Ayyah ta saka wayar abun ka da tsufa sai tace bata ji sosai. " Ayyah ba ya da laifi na sha faɗa Miki,daga shi har margayiya Zainab Basu da laifi,nine ɗan ki mai laifi,Ayya me ya sa ba zaki haƙura ba naga dai ta tafiyar ta fa,sannan ko Allah muna yiwa laifi ya yafe muna,bare Ayya ba laifi Margayiya zainab ta Miki ba,me ye lafin ta ƙaddarar ta ce haka,ko ince tamu,shin wani laifi ta yi ne, babu fa,na roƙe ki Ayya ki saurarawa MAHAJ haka ". Baki da hanci Ayya ta saki tana kallon sa kamar irin tana sauraren sa maganar na shigar ta aiko yana kai aya ta aza masa kuka wiwi bai son ta ya fi fi ta ta da ɗan sa da matacciyar matar sa,wai har ita zai dinga wa faɗa saboda ɗan sa lallai zainab tayi nasara dama ai dangin tsafi ta fito,dole a rina,shi yanzu ko Tausayin ta bai ji bata da kowa sai shi. Wayen nan kalamai su suka ruɗar da Abbu har bai san ya kai kusa da ita ba ya rungumo hannayen ta. Hawayen ya fara share mata kafin ya rarrrashe ta da ƙyar yana taushe wani irin dutse mai ɗaci a maƙoshin sa na damuwa da ɓacin rai da ɓakin ciki. Sai dai bai da abun yi akan wannan ƙiyayyar da Ayya ta ɗaura wa MAHAJ babu wani ƙwaƙƙwaran dalili. Da ƙyar ya yi shiru hakan ya sa bai ƙara furta komai ba bayan kalmar haƙuri ya fice daga bedroom ɗin na ta sashen ma gaba ɗaya.. Zarya ya ke ta yi bayan ya koma bedroom ɗin sa yana son kiran MAHAJ ɗin sai dai ya san shi ba zai iya taushe yanayin da yake ciki ba,ya san MAHAJ zai taushe amma shi ba zai iya ba take raunin sa da Damuwar sa zasu iya bayyana.Haka yayi ta tunanin abun da ya dace yayi inda Daga ƙarshe dai ya haƙura da kiran na sa har zuwa da safe. Haka Ammah ta same shi zaune cikin damuwa da ƙyar ya iya ce mata babu komai sai dai duk yadda ya ke ƙokarin ɓoyewa ta gane komai dan haka bata ce komai ba ta ja bakin ta tayi shiru cike da tunani a cikin zuciyar ta,dan ko abincin da tace aka wo masa saboda bai ci abincin dare ba cewa yayi aa dan haka ta zuba masa ido daga ƙarshe ma wanka ya faɗa bai daɗe ba ya fito a gurguje ya kimtsa ya yayi addu'a ya haye kafcecen gadon sa yayi kwanciyar sa cike da damuwa yana rufe idanun sa. Am mah inda saboda ta saba da wannan ɗabi'a ta Abbu a lokuttan da yake cikin damuwa hakan ya sa cikin rashin nuna damuwa itama tabi sahun mijin na ta kasancewar a shirye ta shigo dama tayo Sallama da ya'yan ta dan kayan bacci ne jikin sa. Tun da suka haɗu bayan anfito Sallah ya san cewa akwai matsala ganin yanayin fuskar ta sa, ta ƙara chanzawa ta haɗe irin na mugun izzar nan da iko da kuma yar damuwa da take bayyane. Cike da tausayin sa haka ya bishi da kallon har ya ɓace wa ganin sa kafin ya bi bayan sa. Bai same shi ƙasa ba dan haka shima ya wuce sama. A chan ya same shi sai dai ya saka lock a ƙofar bedroom ɗin sa duk yadda Mubarak ya so na'urar nan ta cire masa makullin ta ƙi haka ya juya yana fatan komai ya zo da sauƙi dan ya san duk ya sha shishar nan da yawa yadda yake hasale haka zai iya yiwa kan sa illa ta kai shi kwance saboda Illar hakan a jikin sa. Shishar kuwa ya ke sha dan gani yake ita ce maganin kawar da Damuwar sa,haka yake ta zuƙar ta kamar yadda ya saba sai da ya ji ya fara tari sannan ya ajiye. Wani locker ya buɗe ya janyo sweet mai ƙamshi ya jefa bakin sa yana sauke Numfashin ajejjere. Sai da ya ja yan mintuna kafin ya miƙe ya saɓule kayan jikin sa ya faɗa da ɗan toilet ɗaure da ɗan ƙaramin towel da yayi masa ɗaurin a zaz zarge kamar ya faɗi. Bai jima ba ya fito ɗaure da wani sabon towel ɗin a jikin sa,ga danshin ruwa a jikin sa,da alama wanka ya ɗauro,sai kam sa na ɗauke da ƙaramin towel white kamar na ɗaure a ƙugun sa.Kayan barci ya saka masu taushi da santsi maroon color da suka ƙara bayyanar da hasken fatar sa irin na turawa.. Turaruka ya fesa masu ƙamshi sannan ya haye gadon sa yana jingina bayan sa da kan gadon yana sauke numfashi. Ya daɗe zaune haka kamar mai wani tunani kafin ya yi addu'a ya rage haske da ƙara gudun A.c. Lallausan duvet ya rufa jikin sa da shi yana lumshe idanun sa.. Mubarak da ke ta faman zagaye sai da ya tabbatar da yayi bacci babu motsin sa sannan shima ya shige. A hankali a hankali bacci ya kwashe sa mai nauyi. Asuba ta gari ɗan Abbu jikan Ayya... Sanye yake cikin Suit blue and white ya sha kyau har ya gaji farin madaran fatar sa sai ƙara kashewa masu manyan guntayen mutanen nan ido yake yi,da jajayen fata,Ga kan shi ya sha gyara Masha Allah sai ƙamshi yake zubaawa.Miƙa masa hannun da ake ta yi ne inji manyan mutanen da aka gayyata a wajen presentation ɗin suna jinjina masa na da nuna irin ƙwazon da yayi,Musamman kasancewar sa ɗan Nigeria dan ba su cika samun yan Nigeria a irin wannan presentations ɗin ba wannan ne karo na biyu dan haka ya samu jinjina wa matuƙa dan tunda ya fara har ya gama tafi ne ke tashi na nuna jinjina da yabawa. Duk yadda yake daurewa da hayaniyar wajen abun ya gagare sa, dan haka ya zubawa Mubarak ido da ke ta washe baki kamar shi yayi presentation ɗin nan ya ji daɗi matuƙa dan yadda ake yabon ɗan Abbu abun farin ciki ne a gare sa ya san Abbu zai ji daɗi matuƙa idan ya san cewa Ɗan sa ya yanke kowa shi ya zo na farko. A ward ɗin sa ma Mubarak ya karɓo sa tare da na makarantar ta su inda su suka yo na farko a cikin gaba ɗaya presenter ɗin kuma shi ya zo na farko. Kallon sa Mubarak yayi dan shi ba yanzu ya so su wuce ba har sai jama'a sun fara ragewa masu taya sa murna. Amma ya san halin uban gidan na sa hakan ya sa ya miƙe shima yana gyara Suit ɗin sa baƙi kamar na sauran mutanen da ke wajen dan suma mafi yawa duk baƙi suka saka Abin kamar haɗin baki mahaj ne kawai mai sanye da blue and white. Taro yayi kyau matuƙa. Ficewa suka yi daga Ƙaton Hall ɗin na gwamnatin China da aka gudanar da taron.. A gajiye ya zauna bayan motar da mubey ya buɗe masa yana jin kan sa na sara masa ga kasala ta gajiya da ta saukar sa,da doguwar maganar da yayi,duk da taƙaitaccen bayani ne yayi,Sannan Gashi Surutun wajen yayi yawa musamman na Chinese ɗin da ke tana faman yawo da shin shin😂✍️✍️ Idanun sa ya lumshe tare da sauke ajiyar zuciya ta gajiya.Ya na ƙara shigewa cikin seat.Tare da yin balance yana untighting necktie ɗin sa. Har suka isa haka yake hakimce bayan mota kamar wani Babba ɗan shekara talatin.Ya sha kyau matuƙa yau kamar ka sace shi ka gudu komai na sa a kallo ɗaya zaka san mai tsada ne. Nima dai nace Nimên hoa ma (How are you All )👋🚴🚴🚴 Wân ãn..(Sai da safen ku) Allah ya bamu alkhairi. Wai me yake damun Ayya ne ? Me take nufi da kalaman ta hmmm 🤭 Ya kamata wani ya samo muna inda ta dosa haba.Ace jikan ki guda kike tsangwama gaskiya ayyah akwai zama 🥺😔 Inda ku ka ga kuskure ku yi haƙuri wallahi cikin bacci na yi editing ɗin sa.🥺 Kumin Addu'a Allah ya bani ikon kammala book one kafin mu fara exams nan da 15 sept dan na kusa tafiya Hutu,na ma yi jinkiri saboda ku a wannan karon,amma in sha ALLAH ina hanya🤗🚴🚴za,a ɗan yi jira na.✍️ Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P________3️⃣5️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* Cikin farin ciki Abbu ya kira shi bayan sanar da shi da Mubarak ya yi. Fitowar shi wanka kenan yana tsane jikin shi.Ya ji ƙarar wayar sa tana fitar da sauti mai daɗi kuma a hankali cikin sauti mara tashi.A hankali ya sauke numfashi mai haɗe da ɗan murmushin gefen baki yana furtawa a kan Leɓen sa Abbu. Wayar ya saka a speaker sannan ya cigaba da goge jikin sa da tsaftaccen towels na sa. Gashin sa ya fara drying da na'urar busar da gashi. Kafin a hankali ya danna wa Abbu wani kira bayan kiran na sa ya katse. Cike da farin ciki yaji Muryan Abbu ta ratsa kunnen sa yana masa sallama. Amsawa yayi shima muryan sa ɗan sake alamar babu wata damuwa a tattare dashi a wannan lokaci. " Congratulations,an kawo mini albishirin yaro na ya goge

Chapter 27 of 39