Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
LINA tayi kafin ta zo da sauri tana marairaice wa kamar ta duƙa ma REENA tana furta " Ki rufa mini asiri ba zan ƙara ce Miki Wawuya ba REENA " Murmushi REENA tayi abun ka ga zuciya mai sauƙi take ta ce " ai ba zan faɗa masa ba na rufa Miki,da zan gaya masa tun ɗazu ai da na faɗa masa ma ". Numfashi LINA ta sauke har da dafe ƙirji Dan wasu maza tayi dambe dasu su uku bayan school kawai dan sun yi Gulmar ta maganar ta dawo kunnen ta shine ta aika musu da saƙon su haɗu lungun kaci uwa ka idan basu tsoron ta wanda da ƙyar wani security na su ya raba faɗan har suka bashi cin hanci ganin Dagske zai kai report wa school a hukunta su sannan a kira iyayen su. Gaba tayi zuciyar ta na yin sanyi tana fatan kar wata rana Surutun REENA ya tashi ta faɗa ta san ranar sai ya kakkarya ta tayi faɗa da maza ko matan ya ta ƙare in zancen ya zo kunnen sa. " Ummah ta ce mu fito da wuri muyi lunch tace har ke ki fito kuma ". Tana gama sauraren zancen na REENA ta fice daga toilet ɗin tana yatsinar fuska ganin kamar an takura mata dan bata so fita ba, ta so akawo mata abun ta nan hankalin ta kwance amma yanzu da ta haɗa ido da Ya B. Ta san Harara ce zata ƙosar da ita. Ta shirya da wuri amma itace last fitowa dan zaman ta tayi sai da tayi ta tunanin zaman dinning saboda ta san haushe yake da ita tunda gaban shi ta daki yar gaban goshin sa, gashi bata da gaskiya ganin take ko wane irin lokaci asirin ta zai iya tonuwa dan ta san REENA gaɓa ce wata rana tsafff zata iya kawo zancen idan fira tayi daɗi. Zama tayi tana ƙaƙƙyafta idanun ta kamar wadda tayi ƙarya.Rabi mai aikin Ummah a asashen dafa abinci dake tsaye gefe, da sauri kuwa tayi serving nata bayan ta zaɓi abinda take buƙata.Sauƙin ta ma babu wanda ya kula kan ta dan sun saba da rashin fitowar ta ta da wuri sai taga dama Dan haka suke fara cin abincin su ba tare da sun jira ta ba idan ka gan ta ta fito da wuri to Abba ya dawo ne kafin shima a cire marmarin sa. Tun da suka fara cin abincin babu wanda ya cewa kowa ƙala dan sun saba da rashin yin magana idan ana cin abinci sai dai koda magana kaji to bakin LINA ne kuma Abba na kusa.Shirun ne ya ishe ta gashi har yanzu babu wanda ya tashi tsakanin Ummah da BILAL hakan ya sa ta yin ɗan tari na farko babu wanda ya Kalle ta na biyu ma haka ana uku ne UMMAH ta miƙa mata ruwa cikin kulawa shiko BILAL spooon ɗin hannun sa ya ajiye yana zuba mata idanun sa da suke saurin kaɗa hantar cikin ta,Tana kafa bakin ta a ruwan kuwa jikin ta ya fara tsuma ganin kallon da yake mata wanda ya sa ta sarƙewa Dagaske idanun tane suka firfito take suka yi jaaa na azaba. Hawaye REENA ta fara tana miƙa mata ruwa cikin Tausayin yar uwar Tata. Itama umma da rarrashi take ɗan bubbuga bayan ta tana furta mata kalmar sannu.Shiko BILAL Allah ya ƙara kawai ya iya furta wa A hankali yana Hararar ta wanda dama da gangan yayi saboda ya fahimci tarin munafunci ne,miƙewa daga gurin yyi yana yin falo ba tare da ya bi ta kan su ba.. Rashin Chaji ya sa baku samu page jiha ba saboda biyu ya kamata a samu.✍️ Wannan labari na kuɗi ne akan N#1000. Yanzu muna kan free pages, kuma baza,a same su da yawa ba gaskiya dan haka kuna iya fara yin payment. 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt *08069059746* Daga Alƙalamin ✍️ GIMBIYAR TASKIRA 👑 FA'EEH BG ✍️ FIRSTLADY 🙌 LIKE,REACT, COMMENT sune kawai nake buƙata,shine zai nuna mini yadda kuka karɓi book ɗin..✍️ _Typing_ *💋KURMAN ƘADDARA💋* ©®*FA'EEH BG* *BOOK ONE* free pages👌 P..0️⃣6️⃣ ''''"""$""""$""""" *Contact dis line👉08069059746 for advert.* *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn 💋💋💋 Hawaye ne suka silalo mata masu zafi na azaba cike da Haushi da baƙin cikin sa na furucin da yayi mata cikin rashin tausayi ta matsa gefe tana sakin kuka Itama REENA zama tayi gefen ta kafin kuma ta rungume ta suka haɗe kai waje ɗaya. Ummah murmushi kawai tayi cike da ƙaunar ya yan nata ta furta " wai duk saboda kin samu chocking ne zaku mayar muna da gida gidan kuka,Allah idan baku daina ba zan bar ku dashi kun san sauran ". Shiru suka yi kamar ruwa ya cisu dan kamar sun manta waye yake zaune cikin falon. REENA ce ta riƙo hannun yar uwar ta da idanun ta suka yi jazir na azaba. Fisgewa LINA tayi tana barin dinning ɗin tana gunguni wanda ba kowa zai iya cewa ga abun da ta ke faɗa ba. Har ta kusa shigewa lungun da zai sada ta da bedroom ɗin su dake ƙasan ta taji saukar Muryan sa " Wallahi kika shiga ɗakin nan sai kin yi tuman kwaɗɗo ɗari " Cikin sauri ta juyo tana share hawaye kan ta ƙasa saboda fushi take yi dashi ta zo ta zauna kusa da REENA da ke zaune kusa dashi ta yi shiru tana kallon Cartoon da ya kunna mata bayan dawowar su Falon ita da Ummah.Ummah da ta gama bawa masu aikin na ta umurni ne ta zo ta zauna cike da kulawa ta furta " Soja ya hanya ya kuma aiki,tunda ka ƙi bari mu ko gaisa sai ka fara ganin ƙannen ka ". Sunan Soja itace kawai ke kiran sa dashi.Murmushi yayi yana kallon mahaifiyar ta sa Abar son sa sanyin idaniyar sa sannan ya furta " Ummah Alhamdulillah komai lafiya lau". " Amma baka cin isasshen abinci ko Soja,dan wannan karon ban ga kayi wata ƙiba ta arziki ba ". Murmushi yayi kafin ya ce " Ummah ai idan nayi ƙiba aikin zai min wahala,Gudu ma sai ya gagare ni " Idanu ta zuba masa tana ƙara ƙare masa kallo kafin cikin cire Muryan wasa ta furta " Dagaske fa nake yi Soja ka yi rama a wannan karon,me yake damun ka ". Shiru yayi zuciyar sa na wani irin chanza sauti kafin ya samu damar bata amsa yana furta " Ummah aiki ne kawai,kin san munje wani mission na sati biyu to Bama samun isasshen abinci achan ko daga ni har ya ra na kowa kika gani zaki ga ya chanza saboda yanayin wurin da muka samu kan mu " . Kai ta girgiza masa kamar ta yarda kafin ta sauke ajiyar zuciya da ita kaɗai ta san ma,anar ta. A ɓangaren sa ajiyar zuciya ya sauke a ɓoye yana rufe idanun sa bayan ƙare ma LINA kallo da ke zaune kamar wadda an ka yiwa mutuwa fuskar nan Tata ta sauya ta wani karkace kai irin bata son magana da kowa ma. Ammah ce ta ƙyafato ta bayan sun haɗa ido yanzu ganin har yanzu ranta a ɓace yake ta furta " Zo nan ". Zama LINA tayi a kusa da ita wanda ya ƙara tabbatar mata da fushi take yi da kowa dagasken.Dan da ba haka ba kan ƙafafun ta zata haye. Murmushi tayi tana ɗago face ɗin tace " ALINA my baby girl waya taɓa min ke,waya taɓa sanyin idaniyar SS family ne ''Tayi zancen tana janyo ta jikin ta duk da ta san kan wa ake fushin. Kuka LINA ta fashe da shi mai cike da shagwaɓa tana furta " Ba Yaya Bilal bane ya min Allah ya ƙara ai dama na san baya sona,ya fi son REENA ai ban manta ba yace ni ba ƙanwar sa ba ce bai haɗa komai dani ba ". Buɗe idanun sa da suka masa nauyi yayi saboda bacccin da ke cin su yayi yana sauke su kan ɗan ƙaramin bakin da ke zuba kalaman da baka taɓa tunanin ta iya zaro su saboda yarintar ta. Murmushi kawai ya saki yana kallon REENA da ta zuba masa idanu tun ajiyar zuciyar da ya sauke wanda kaɗan ya rage tace masa Yaya Ba ka lafiya ne naji ka yi ajiyar zuciya.Sai kuma ta dakata saboda Ummah ta katse mata zancen na zucin ta da take son fito dashi ta hanyar yiwa LINA magana. Jinjina kai yayi yana furtawa azuciyar sa Lallai LINA bata da mantuwa shi da yayi zancen ya daɗe da mantawa kuma lokacin tun tana yar shekara bakwai ne a duniya lokacin tana cikin ganiyar rashin jin magana babu wanda bata addaba ba cikin estate ɗin ita faɗa da wanchan yau gobe da wani wanda shi kuma ya sako ta gaba dan ya tsani rashin jin magana dan duka yaran familyn suna tsoron sa sosai itace kawai mai kunnen ƙashi ya rasa dalilin rashin jin na ta gashi kullum abun nata gaba yake yi,shi ya sa ya ke matsa mata kamar yadda take cikin rashin ji kullum yake hukuntata sai dai banza dan Tsoron nasa ma bai wuce shekara uku da ta fara yin sa ba.May be ko saboda suna gida ɗaya ne bata jin maganar sa Oho. Hararar sa Ummah tayi bayan sun haɗa ido. Kafin ta furta " Soja kar ka ƙara ta kura ma sanyin idaniyar gidan SS kaji ka iya bakin kaji abun da aka yi tun shekara huɗu Bata manta ba abun na ran ta,yanzu dai kar ka ƙara dakar min Yaa kuma ka bata haƙuri ,ko muci ga da fushi da kai ". Idanu ya zaro yana furta " Ummah Haƙuri fa,ai ita ya kamata ta bani haƙuri,a gaban ido na nagan ta tana dakar REENA kamar Allah ya aiko ta,sai kace ba yar uwar ta ba,kamar ba ciki ɗaya suka fito ba,wannan wane rashin ji ne idan har tayi wa wasu dake waje ai bai kama ta ta yiwa REENA ba,bana son yawan faɗan nan na su abu kullum kamar gaba yake yi,kuma a duk lokacin da za,ayi rigimar itace fa mara gaskiya fa Ummah ". Shiru yayi dan har ransa ya ɓaci tuni bayan tunano irin rashin jin da tayi tayi a baya dan bata ragawa kowa a cikin yaran gidan ga rashin kunya ga manya sai in bata ga damar ka ba,ko bata ga dama tana yi sai dai a dake ta tayi kukan ta ta share hawayen ta.Ta sha yin dambe iri iri da yan matan har haƙora ta taɓa cirewa Ninah ɗiyar ƙanen mahaifin su.Shi yasa har yanzu ba wani shiri take yi da ita ba. Kan sa ya sauke ƙasa cike da haushi yana ƙara furta " Allah Ummah ke kike ƙara wa aya zaƙi kamar kina goyon bayan yarinyar nan akan abun da take yi,ace mutun bai son zaman lafiya,kowa ya buɗa baki sai ya faɗi mara daɗi kan sa,ni bazan lamun ta ba gaskiya Ummah,ba zan iya jure shirmen ta ba ".Ya kai ƙarshen maganar matuƙar ransa ɓace.Jikin sa har ya fara ciccira LINA dake hango sa ƙara shan jinin jikin ta tayi tana rufe idanun ta saboda tsoron da ya ƙara kama ta ganin yadda ya'yan na su ya juye lokaci ɗaya da alama zuciyar sa ta ke son motsawa dan Allah ya zuba masa zuciya dan haka baya son a kawo masa wargi sannan bai cika shiga harkar yaran gidan ba,bare ma kuma duk tsoron sa suke yi. Ganin yadda ko ƙanwar sa da suke ɗaki ɗaya bai raga ma ba. Murmushi Ummah ta sauke kafin ta kalli fuskar LINA da idanun ta suke a rufe.Kan ta ta ɗauke kan ta ,tana mayar wa kan REENA da take cikin tsoro ji take kamar a ce ƙyat ta ruga ganin yadda ran yan maza ya ke son motsawa LINA zata janyo musu Masifa da rana tsaka.Dan idan yana irin wannan yanayin ko Ummah da ƙyar take tanƙwasa sa bare ma Abba da yake ba zama yake yi sosai ba saboda harkar business ɗin sa. Kai ta girgiza kafin ta furta "SSB" dan wata rana haka take kiran sa. " Ni nake ƙarawa aya zaƙi Soja " ta furta tana jin jina maganar. Shiru yayi jikin sa sanyaye jin furucin ta kafin ya ɗago ya Kalle ta,fahimtar kalaman na sa kamar sun mata tsauri tun da ya san itama fama ta ke da su yace cikin Muryan nadama da ladabi " Kiyi haƙuri " bata tan ka masa ba sai ma cigaba da magana da tayi. " Ka cigaba da shan ragin ruwan Alwallah wannan zuciyar taka na zata ta tafi a she tana kusa,yanzu lallashi SAREENA dake gefen ka, kasaki fuska Karka sabauta mini Yaa ".ta kai ƙarshen furucin tana kallon REENA da idanun ta suka yi rau rau alamar kuka a kowanne irin lokaci zai iya zo mata.Samun kan sa yayi da sakin guntun murmushi kafin ya janyo ta jikin shi yana tsokanar ta.Kasa sakewa tayi sai da ya kunna wayar sa ya kamo Pics nasu lokacin suna yan dagwai yake nuna mata wanda take ta fara dariya,tana furta " LINA nafi ta kyau,Ji bi bakin ta a tsakiyar haƙoran ta kamar ta ga " tayi zancen tana kallon ƙaton giɓin su da yake bayyane saboda sun washe baki ne a dariyar. LINA da tayi likimo ne kamar bata san akwai wasu a falon ba ta ɗago tana furta " Wallahi baki fi ni kyau ba,mu ma ga pics ɗin " Tana zancen ta sauko jikin Ummah da sauri ta na komawa bayan kujera kusa da Bilal da REENA ɗin.Ammah kai kawai ta girgiza ganin har ta sauko lokaci ɗaya,gata bayan wanda ake faɗan ma dashi ana neman yin sabuwar fitinar domin idan ba Allah ya tsayar ba sai an yi rigima,dan LINA ta tsani REENA ta kira mata mara kyau duk da da wasa take mata dan kamar su ɗaya a jiki da fuska da komai ba za ma ki iya banbance su ba idan ba sanin su kika yi ba,ko shi ta gefen natsuwa da REENA ta fi LINA ɗin. miƙewa Ummah ta yi bayan ta sauke numfashi kamar wadda aka tsakura ta miƙe ta shige bedroom ɗin ta da yake sama.Ba tare da ta bi ta kan su ba. Gidan kamar sauran gidajen yake dan dukkanin su tsarin su ɗaya in ka cire na BILAL dan shima yana da na sa PART anan amma dukkanin su haka suke babu banbanci a tsakanin su,gida ne fankacece mai ɗauke da ƙaton falo mai ɗauke duk wata duniya acikin sa daga ƙasa su REENA suna da bedroom ɗaya daga sama kuwa kusa da bedroom ɗin abban su suna da ɗai ɗaya kowacce nada nata shaƙe da kayan ɗaki na alfarma irin samfurin na yara da komai da ya shafi yara,dan har da sashen karatu kowace an ɗebe mata an ɗaura komai na buƙata.Ɗakin Ammah biyu ne tana da ɗaya ƙasa kamar su LINA tana da ɗaya sama kusa da na su LINA ta gefen dama.Abba yana da bedroom ɗin sa ta ɗaya a ƙasa shima mai ɗauke da babban ɗakin tarbon baƙi dan bayan guest house da suke dashi a gidan suna da ɗakin tarbon baƙi a kowanne sashe,ɗakin masu aiki akwai shi chan sashen kusa da kitchen nan nasu yake,duk da suna da part na su a chan maza da mata kowa nashi daban amma bai hana aka ware musu ɗakuna a falon ba dan idan suna da aiki mai yawa suna iya yin komai a nan kafin su koma gefen su.A sama ma ɗakin ABBA yana kusa da ɗakin su LINA ta hagu BILAL kuma nasa bedroom ɗin a ƙasa yake gaba ɗaya ta wani gefe chan dan sai kin yi yar tafiya kafin ki isa part ɗin sa daga cikin gidan,sai ba,a ware masa na sa ba saboda yadda ya nuna ƙin hakan duk da manyan bedroom da falos da ke a achan upstairs ɗin dan ƙoƙofi ne birjik ta wanchan ɓangaren.Gidan dai ya tsaru iya tsaruwa,komai Masha ALLAH ba sai an faɗa muku irin dukiyar dake cikin sa ba. Hoton ta kalla bayan REENA ta miƙo wayar daga sama dariya ta ƙyaƙyace da ita tana furta " Yy Dan Allah giɓin waye yafi kyau,wallahi nawa yafi naki kyau Allah duba fa,wannan ƙofar ta me ce,ƙofar mata ce ko ta ɗan agundi ". " Allah bari na cewa "Ummah a mayar dake Kano Ƙofofin haƙoran ki duk na su ne," ta kai ƙarshen zancen tana ƙyalƙyata dariya tana kallon ƙaton giɓin na su kowaccen su ta sha doguwar riga yar guntuwa ƙafafun su sake sai walƙiya suke yi.Sun yi kyau sosai dan kayan su iri ɗaya ne a duk hoton da za,a wuce. REENA shiru tayi kamar ta ƙwage tana ɓata fuskar ta. Jin bai bata amsa ba ya sa ta ɗagowa tana ƙara maimai ta tambayar " Dan Allah yaya a faɗi tsakani da Allah na wa yafi a lokacin " ? Ɗan buɗe idanun sa da ya rufe yayi yana sauke su akan ta kafin ya mayar da su ya rufe sannan ya furta " na REENA man ".ai tafi ki kyau nesa ba kusa ba duk da kamar ku ɗaya ai abun bayya ne " Ya yi zancen bayan ƙare ma REENA da tayi sagado cike da Haushin zancen LINA.Tsalle ta fara bayan jin furucin sa kafin ta faɗa jikin sa ta rungume sa tana cewa " Ai yaya dama na san na fi ta kyau,ai duk da fuskar mu ɗaya dole za,a ga wanda yafi wani kyau,nafi yar wata kyau yelun"Ta kai ƙarshen zancen tana Hararar LINA da ta ɓata fuska idanun ta har sun sauya alamar kowane irin lokaci tana iya zubar da ƙwalla. Ta gefen ido ya Kalle ta ya karanci yanayin ta dan ba zai iya ba ma da rigimar Tata ya miƙe yana karɓan wayar sa hannun ta yana barin falon gaba ɗaya bayan kashe din banda faɗa da ya musu. " LINA an fara saka sabon tomm and Jerry zo mu kalla kin ga yanzu na gan sa ". REENA bata lura da yanayin LINA ba tayi furucin sai dai kafin ta ankara ta kai ma fuskar ta bugu cike da Haushin ta ita da ya yan su. Baƙin cikin ta ɗaya wai REENA tafi ta kyau. Fitowar Ummah daga ɗaki kenan ta ga faruwar abun kafin rigima ta kaure tsakaninsu da ƙyar ta raba su REENA sai kuka take yi ita kuwa kamar wata samna. Ammah kan ta ji tayi kamar ta ƙarawa REENA abu kaɗan sai kuka shi yasa LINA ta raina ta,ta mugun Tausayin REENA saboda yadda rayuwar ta take mai sauƙi gashi irin wannan kana cin wahala a mutane Bama REENA ba kowa na gidan ganin bata son fitina suna ƙoƙarin shige mata ga hanci sai da LINA tayi maganin kowa sannan suka shafa mata lafiya,dan ita in zata chasa ta sau goma bata damuwa amma idan wani yayi ko sau ɗaya tana jin baƙin ciki,inda take shigewa faɗan.Ko kuka taga yar uwar ta nayi idan dai ba ita ta san ta saka ta ba akwai matsala.Haka suke gudanar da rayuwar su mai cike da abun sha'awa cike da soyayyar junan su. Rarrashin ta Ummah tayi kafin ta yi shiru. Neman ba,a sin faɗan tayi inda cike da haushi LINA ta faɗa mata. Zuba mata idanu Ummah tayi kafin ta furta " oh ni bint Usman,SOJA ka haɗa mini faɗa a gida, yanzu wannan shine abun faɗa kuma LINA da zaki saka mini yaa a gaba haka,yanzu duk faɗan da Soja ya Miki,a banza, a gaban ki nan kika ji yadda yake hawa ya ke sauka idan na barki dashi a lokacin ƙalla mun ke kawai zai yi,amma shine bayan ɓacewar sawun sa kika koma,nide Allah ya shirya mini ke ALINA ban san yaushe zaki yi hankali ba may be sai kirji ya cika an zama yan mata,Allah dai ya shirya mini ku "Ta kai ƙarshen zancen tana girgiza kan ta tare da sakin murmushi. Ganin yadda LINA ta turo baki hakan ya sa ta ƙara furta " In ban da abun ki ALINA kamar ku ɗaya fa ni kaina da nake mahaifiyar ku da ban yi da ƙyar ba ko bazan iya gane ku ba ko lokacin da kuna ƙanana haka nayi ta fama bana gane ku sosai amma da yake ni na haifa a buna take nake gane ku,tun ran da kuka fito ciki haka kuka fito kala ɗaya babu mai banbanci atsakanin ku kyawun ku iri ɗaya ne,kun kwaso kyakkyawar fuskar iyayen ku,Kyawawan Idanun ku duka nawa ne yanayin shape na fuska na mahaifin ku ne ,yara masu kyau ai duka familyn SSS babu kamar ya'ya na a fagen kyau " haka tayi ta koɗa su kafin ka ankara fuskokin su suna cike da murmushi har da mai kuka. Samun kan ta tayi da sakin yar ƙaramar dariya kafin ta janyo hannayen su waje ɗaya ta zauna tare da su. Tana ƙara furta " Kune hasken idaniyar mu,ya yan Gata,LINA soyayyar da ya yan ku yake Miki dai dai take da ta REENA kawai rashin jin maganar ki ne ke haɗa ku,da zaki daina zaki gani,gashi harda yarin ta ya sako mini ke gaba babu abinda zaki iya fahimta " " Allah ya shirya mini ku ya sa naga yan matan cin ku naga Auren ku Allah ya muku Barka ". " Amin " Suka haɗa baki suka faɗa suna murmushi.Kan su ta shafa itama cikin murmushi kafin tayi musu peck a goshin kowacce.Fira suka fara yi suna bata labarin school suna cigaba da kallon Cartoon ɗin su tana biye musu cike da so da ƙauna,har waya suka kira Abba suka yi dashi cike da farin ciki da kewar sa mai haɗe da ƙaunar mahaifin na su. *** Hajiya ɗazu naga fitinannun yaran chan sun dawo daga makaranta ɗayar baki ga jikin ta ba kamar tayi faɗa da kura,Da alama dai halin suka ƙara yi a waje,tun da sun zama yan dambe. Murmushi Babbar matar dake zaune a kan kujerar alfarma tayi irin murmushin nan na masu aji da wata manufa. Kafin ta ɗan muskuta sannan ta ce " Ina son zan tura ki wani waje ma dan akwai aikin da nake son yi dan na fara hango matsala babba dole na sake sabon shiri,Ba zan lamunci ina kallo ba kasuwa ta watse dani babu riba" " LINA rigimammar kan ta ce da kika sani luba,shi ya sa nake son yarinyar " Sai ta ƙara sa zancen tana sakin murmushin da ita kaɗai ta san ma,anar sa. Dariya itama yar dattijuwar matar da aka kira luba tayi tana yiwa uwar ɗakin na ta kirari ganin ta miƙo mata bandir na yan dubu dubu guda uku. Fitowar yar tace ƙwaya ɗaya tal mai suna Hamrah ya sa juya wa tana kallon ta fuskar ta cike da murmushi tana furta " Yar gwal an fito " Baki yarinyar ta cunno gaba irin na sakuwa kafin ta faɗa jikin mahaifiyar ta tana rungume ta... " Momy na gaji da ya wallahi tun da na dawo school ƙafafu na suke ciwo gashi bakya nan bare ki rarrashe ni,Yawwa Momy kin sa wai su REENA yau dambe suka ƙara yi a schl kwana biyun chan ba su yi ba,har naji daɗi amma yanzu kin gan yadda suke dambe,ni dana ga ba,a zo ɗaukar su ba na san halin LINA nace wa yusuf driver kawai ya wuce ba sai na rage musu hanya ba,dan malam Adamu bai je ɗaukar su da wuri ba ". Murmushi matar tayi kafin ta furta " Ya yan ku ne ya dawo shine ya tsayar da shi,suka je ɗauko su tare,nima duk yanzu Luba take faɗa mini " Ai bata bari ta rufe baki ba ta dire ƙasa cike da wani irin tsalle tana furta " Momy nayi part ɗin Ummah na ga Yaya ". " A'ah karki je a haɗa dake gashi da baki kin ce dambe suka yi na san shi ma BILAL ɗin ba zai rasa ji ba ko gani,ba zan lamunci ya haɗa dake ya sakar muku ƙarfin sojoji ba,ki bar su chan da yawar su ". Tabbatar da zancen mahaifiyar ta gaskiya ne hakan ya sa ta dawo jiki mace ta zauna kusa da Mahaifiyar ta tana ɗaura kan ta a bisa kafaɗar ta tana rungume ta,dan tayi kewar ya'yan na su. Dariya Momy tayi haka Luba dan sun san Hamrah da Shegen tsoro. Miƙewa luba tayi ta mata sallama tana ficewa daga part ɗin gaba ɗaya,cikin son isar da saƙon uwar gijiyar ta ta da ta san ko saƙon me ne ne.✍️ INA ƊAN FAMA DA ZAZZAƁI NE SHI

Chapter 5 of 39