Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai ƙaryace ƙaryace duk da kuwa yana da ƙananan shekaru shima dan bai wuce sha shidda ba amma Allah ya zuba masa ƙarya ga ɗan ruwan da ya iya ɗan watsawa na mutumen ƙauye da ya je birni shi ya sa mutanen ƙauye suke ji dashi haka ma mai gari da aka rufe da wasu takardun bugi shima ya zauna akan ɗan sa ya haɗa degree yayi karatu mai zurfi a yanzu haka ya na nema masa aikin yi ne da takardun sa,kuma idan aka yi baƙo a ƙauyen shine mutun na farko da ake kira gudun kar a haɗu da Bature wanda bai jin Hausa su kasa iya communication.Ga kuma Case na biyu daga bata Shawara bai daddara ba dan ya san guje gujen ne nata suka sa yayi niyyar kaɗe ta sai komai ya juye.Wannan kenan. 'Zuwan yara ne su biyar da basu wuce shekarun ta ba yan sha uku sha biyu ya sa ta miƙe tana washe baki hankalin ta kwance ta tare su itama da gudun nan na ta kamar yadda suka zo a guje gurin dan dama sun san ta iso tun da har gidan su sun leƙa basu gan ta ba.Sannan suka fito a guje kafin Inna ni ta gan su ta riƙe su gidan kamar yadda take musu idan sun biyo mata haka wanda daga ƙarshe dole Shatu ta baro wajen dan ta san muddin bata gan su ba har lokaci ya cika suna gurin Innar ta tana musu fira Dan bata son fitar kwata kwata ta Shatu wanda kuma da shatu ta ga haka take komawa gida baki kunbure na rashin yin wasar daren da basu yi ba.Abu kamar jaraba. 🤭 Yo Shatu wasan Dole ne.Bari dai nayi shiru kar amini rashin mutunci😂 " Shatu ! Shatu ! Shatu " ! Shine abun da suka haɗa baki gurin faɗi dai dai isowar su kusa da juna cikin washe baki itama bakin ta washe ta riƙo hannun Babbar ƙawar ta Amina daga cikin su ƙawayen nata tana furta " Nidai na zaɓi Abokiya ta ".Kallon ta kawai suka yi babu mai bakin magana a cikin su dan sun san kullum aka zo haka take musu wayau kuma har Amina ta saba duk da tana da ɗan tsoro shi ya sa kafin su iso sai sun gargaɗe ta ko da an zo tace bata son Shatu matsayin Abokiyar haɗin ta.Amina dai bata iya cewa komai ba sai ɗan murmushi da ta ƙaƙalo kafin ta koma gefen Shatun tana ƙara washe bakin ta. Su kuwa sauran ƙawayen na su kowacce kama Abokiyar ta tayi cikin jin haushi kafin su fara gabatar da wasan na su duk da sauran ƙawayen na ta na amana biyu suna cike da jin haushin abun fifikon da Shatu ke Nuna wa a tsakanin su.Wasannin su suka fara kamar yadda suka saba irin dai wasannin nan na dare da yara ke yi na tsalle tsalle da yar goye goyen nan,wanda yar goye goyen ce ma ke saka Shatu zaɓar Amina saboda sune basa da jiki amma duka sauran sun fi su girma ita cewa take bazata iya ɗaukar ƙatuwa ba.Dan shi take zaɓen Amina kai tsaye bata ma bari ayi wasan a fitar da wanda zai goya wani.Sun yi wasannin su cikin nishaɗi sai dai me suna gab da kammalawa kowa ya watse mazan da ke gurin su Iro kenan suka yo cikin su suna hudi irin abun nan na iskanci suna shigewa cikin su duk wadda ka samu ka rungume.Cikin rashin sa,a Iro ya faɗa hannun Shatu bada sanin sa ba Aiko tana jin yadda ya ke ƙoƙarin rungumar ta ta yi masa mugun cizo a hannun sa da iya ƙarfin ta har sai da ta ja sosai fahimtar shine dama da Haushin shi take matuƙa na ƙazafin da yayi mata kwanan baya wai ta zage shi ta zagi mai gari da ga kawai ya ma ta faɗan ta daina guje guje,bayan rashin mutuncin da ta masa ranar da ya tashi kaɗe ta,bata kula sa ba,dan bata son shigar shigula,ko ranar ma rayuwar ta yayi niyyar illatawa da mashin ɗin sa shi ya sa ta masa tass,Alhalin kuma ƙarya yake mata bata zage sa ko ranar dan daga ƙarshe ma da ya ishe ta sai ta masa tsawa,shine da ya ji Haushi ya je ya faɗa ma Mahaifin ta shine aka mata faɗa ta ji haushi ta gan shi kan hanya ta ƙara gaggaya masa magana cikin rashin tsoron sa.Haka magana tun tana ƙarama har ta zama Babba ta kai ga mai gari an taɓa ɗan gaban goshin sa hasken ƙauyen su,ya tara zaman ba,a si,sai dai mutane sai faɗar suke itace bata da gaskiya saboda a gaban jama'a ta yi masa rashin mutunci kamar sakon ta,kuma sun lura da lalama ya mata maganar guje gujen na ta,haka aka yi zaman babu daɗi daga ƙarshe aka yi sulhu aka tsayar da kowa matsayin sa.Tun daga wannan rana kuma duk da kashe din dake tsakanin su yake bibiyar ta dan shi burge shi take yi musamman ma faɗan na ta ɗan ƙaramin bakin ta ya ke son ganin yana motsi saboda yana burge sa,shi ya sa yake ƙara shisshige mata musamman da ya ke ji da kan sa shima sai yake ganin yafi ƙarfin ta ma dan haka yake da ya gan ta yake mata magana kamar wanda ya bata ajiya ita kuma tana share sa dan mugun tsanar sa take ji dan kan shi Baffa yayi mata faɗa sosai Inna ni ma ta so ta dake ta,da ƙyar ta sha kuma itace mai gaskiya... Ƙarar da Iro ya sanya ce ta ankarar da mutane halin da yake ciki,kan su aka yo kafin su an kara Shatu ta falfale a guje wasu daga cikin ƙawayen Iron ne Musa da isaka suka bi bayan ta sai dai kafin su an kara ta ɓace ma ganin su saboda mugun gudun da take yi gashi ɗan jikin ba wani ba kamar balbela.Haka suka dawo suna cizon baki da wassafa yadda zasu ci uban Shatu in suka riƙe ta Iro bai so matsawa ga re su ba amma suka matsa masa gashi sun ja masa wahala dan ya cizu.Haka suke kallon sa cikin tausayi sun zagaye sa,suna masa fifita tare da mayar da bakin yadda aka yi. Su kuwa Su Amina kowaccen su gida ta nufa bayan samun kuɓuta daga hannun Mazan hankalin su a tashe dan sun tsorata basu taɓa musu haka ba sai yau.Kuma sun ji daɗin abun da Shatu tayi ma ɗai daga cikin su duk da basu san kowaye ba dan ta cece su matuƙa. Hannun sa da ya fara tartsar da jini wani ya yanki gefen hannun rigar sa da ta ji jiki yana furta " Yarinya kamar mayya duba yadda ta fasa maka hannu wallahi sai taci uban ta yarinya mai Shegen tsiwar tsiya wallahi Iro kabar ni da ita Sai na koya masu hankali shegiya dangin Mayu masu farautar naman mushe ". Ya kai ƙarshen zancen yana ɗaure masa hannun da ke masa zuji shiko Iro Wata irin kunya ce ta dabaibaye shi da baƙin ciki lokaci ɗaya yadda zai wulaƙan ta rayuwar Shatu kawai yake hangowa.Shi da ya san ita ce ai ba zai faɗa mata ba,Amma wallahi zata gane kuren ta sai zaman ƙauyen ya gagare ta haka yake ta tunani kala cike da baƙin ciki dan a cikin a bokan na su akwai masu masa dariya ƙasa ƙasa musamman da suka ga yana jin jiki sosai ya wahala matuƙa. Suna barin wajen direct gidan mai gari suka wuce maimakon su wuce ɗan ƙaramin chemist na ƙauyen a bashi maganin rage raɗaɗi. " Keh Adda lafiya kika faɗo muna gida a hargitse keda kike shigowa a sace yau sai gaki a guje da alama wayen nan idanun naki basu da gaskiya Adda Shatu". Bibu yayi furucin yana kallon ta bayan kiciɓus da suka yi saboda ganin bata dawo da wuri ba shine zai saci hanya yaje neman ta.Sai gata a guje tana neman kai shi ƙasa tana zarar ido kamar karen da yayi ƙarya. Hararar wasa ta sakar masa kafin ta sauke ajiyar zuciya ta yi masa raɗa a kunne tana sakin ƙaramar dariya. Idanu Bibu ya zaro cike da tsoron abun da ta faɗa masa kafin ya riƙo hannun ta da sauri ya shige ɗakin sa da ita yana kallon ƙofa. Ba,a fi mintina biyar da shigar su ɗakin na sa ba sun yi jugum sai ga Ƙatuwar Muryan Wani Babban yaron mai gari ya'yan Iro mara kunya yana rabka sallama cikin hargowa.Ƙirjin ta ne ya buga da sauri kafin ta shanye tsoron da ya shige ta domin ita yanzu mahaifiyar ta take tsoron ta ji abun da ta yi duk da ta san da gaskiyar ta duk inda za,aje amma ta san da wanchan mugun ba zai faɗi shine mara gaskiya ba ko a yanzun. Da sauri Baffa na dake ɗakin sa ya fito haka ma Inna ni da sauri ta fito nata ɗakin dama a tsame take hankalin ta na kan Shatun ta. Jikin ta na bata sai ta zo musu da wata rigimar. " Na rantse da Allah sai na kakkarya Shatu kosongo shegiya mara tarbiyya " Laƙanin da wasu daga cikin mutanen ƙauyen suka mata kenan,kuma daga bakin Iro ya fito saboda guje gujen ta da Shegen gudun da Allah ya bata,sai suma mutanen gari suka ɗauka,A ɓoye Dan ya taɓa ganin wata dabba mai Shegen gudu mai suna kosongo shine ya kira sunan gaban abokan sa yana kaman ta Shatu dashi sai suka ɗauka suna kiran ta dashi.Amma saboda fitinar ta ba kowa ke iya kiran ta hakan ba saboda bata shiga sabgar kowa Shatu yarinya ce mai halin manya dan Shegen wayau ne da ita duk faɗan da ake mata tana takatsan tsan amma da zaran an Jata sai tace katt,musamman irin su Iro yan na iya. " Iro ta ciza har sai da ta fasa shi yanzu haka yana chan hannun na sa yana zuza yana kuka, saboda ta saka masa mugayen haƙoran ta masu kama da na kura sun zabci naman daji har sun gaji wallahi sai na lallasa ta kafin ma mai gari ya yi maganin ta ko shi iro Ni zan yi " Ya kai ƙarshen zancen ganin Baffa na ya zuba masa idanun sa yana kallon sa cikin mamakin yadda yake zagin yar sa gaban sa babu kunya harda wani Shegen suna da suka mata wanda shi bai taɓa jin sa ba sai yau. A jiyar zuciya Baffa na ya sauke kafin ya ja numfashi Yace " Zaidu a riƙa tausasa harshe koba komai Ni mahaifin Shatu ne ba komai ya kamata ka faɗa a gaba na ba,kuma na san Shatu na bazata iya aikata abin da ka faɗa ba ba tare da an tsokane ta ba wannan halin ta ne na sani,Dan haka ba zan gaji da bada haƙuri ba kamar ranar ayi mata haƙuri yarinta ce ke damun ta duka duka Shatu shekarar ta Sha biyu cikin ta sha Uku Zamu je yanzu na kai shi a duba hannun "..Baffa na ya kai ƙarshen zancen yana sauke numfashi.Dai dai kuma lokacin ne saƙon mai gari ya iso masa na neman Shatu da iyayen ta. Mai bada saƙon Yana gama sanar da Baffa ya wuce cikin mamakin abun da Zaidu yake yi anan amma ya san bai wuce takakka ce ya kawo gidan ba saboda ɗan uwan sa. " Wallahi aja mata kunne ko na lafira ya fi ta jin daɗi wallahi yau ta leƙo barzahu ta gane mana asarori ".Zaidu yayi zancen yana barin wajen shima. Inda ya bar Baffa na cike da takaici na rashin mutun cin sa da kuma neman da mai gari yake masu.Tunanin yadda case ɗin zai ƙare ne ya fara a tsaye ganin tsayin bazai amfana masa komai ba ga dare na yi hakan ya sa ya juya ya koma cikin gidan inda ya isko Inna ni tsaye ƙofar ɗakin Bibu ga Shatu daga ciki tana ta kuka kamar wadda aka yanka kafin ma ta taɓa ta dan duk ta ji komai da ya faru kuma tana da tabbacin Shatun ta dawo gida dan haka ta leƙa ɗakin ta sai dai babu ta ciki hakan yasa ta koma ɗakin Bibu Tun kafin ma ta shiga taji ƙusƙus ɗin su Bibu na ce mata kar ta ji tsoro ai itace mai gaskiya waya sa ya taɓa ta ai ya taɓa jin akwai lokacin da Inna ni tace mata kar ta riƙa bari maza su taɓa jikin ta koda hannun ta ne kar ta bari Indai ba Bibu ba sai Baffa na.Hakan da Inna ni taji ta tabbatar da yar ta ce mai gaskiya hakan ya sa ta dakata da ga shiga ɗakin sai dai ta ɗaga murya cikin kaushin murya tana kiran Sunan Shatun,ita kuwa Shatu cike da tsoro ta fara kuka dan ta san yau sai kashin ta ya bushe A hannun Inna ni. Baffa na bai cewa Inna ni komai ba ya shiga ɗakin ya riƙo hannun Shatu yana share mata hawaye cikin Tausayin ta kafin ya tambaye ta ta faɗa masa gaskiyar abun da ya haɗa ta da Iro a karo na biyu idan har itace da gaskiya zasu tsaya mata a bata gaskiya komai wahalar samun gaskiyar. Cikin kuka ta sanar masa da komai dake faruwa.Ɓacin rai ne ya bayyanar masa hakan ya sa rai ɓace ya ja hannun ta suka fice daga gidan ba tare da ya cewa Inna ni komai ba da ma shi ya san akwai dalilin da yasa Shatu ta masa haka. Inna ni ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Bibu da yaji Tausayin yar uwar ta sa shima ya fara hawayen dan bai yi tunanin zata sha ba ko yanzu ma bai jin Inna ni zata ƙyale Shatun sa..... Ba zamu daɗe muna free pages ba gaskiya zaku iya fara payment... 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga wannan sati bazan ƙara posting a weekend ba gaskiya saboda ranar Hutu ce.🙏 Ƙarin bayani. 08069059746 Daga Alƙalamin ✍️ Gimbiyar taskira👑 FirstLady 🙌 React and Share, Comment PLS 🙏 *UPDATE* https://chat.whatsapp.com/BzXaAD3pB6yJ1wBBrkE4V0 *Masu son ganin ƙarshen labarin sai suyi following channel ɗita.👇* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *💋KURMAN ƘADDARA💋* ©®Fa'iza Almustapha Murai Daga Alkalamin✏ 👄FA'EEH BG👄 💎Sadaukarwa ne ga class mate ɗina ɗalibban GGC T/MAFARA,ZAMFARA STATE SET 2K18.A duk inda kuke Alkhairin Allah ya kai muku.🤲💎 *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* _Daga marubuciyar littafin_ *A MAFARKI NASANTA* *RAYUWAR MU A YAU* '''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''’'''"""""""" *_𝐌𝐚𝐫𝐲𝐚𝐦_𝐝𝐞𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭_* Best kayan kwalam 09025859622 or 09163353050 *END OF DISCUSSION PACKAGE* Now available in- candies package stop in and stock up on a sweet piece of summer! 🍬🍔🧆 𝐌𝐚𝐫𝐲𝐚𝐦_𝐝𝐞𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭: ce ta shirya tsafff domin kawo muku. Samosa Spring rolls Filled doughnut Glazed doughnut Puff puff Shawarma Cupcake Birthday cake Bento cake Egg roll Milk cake Candy's Alewar madara Gullisuwa Tsami gaye Coconut laddo Milky gireba Albishir Mandula Sayen daya ko sari muna aikawa ko ina cikin aminci muna karɓar order bikin suna ko aure Location zamfara state ,gusau What's no :-09025859622 or 09163353050 Hajiya karki bari wannan garaɓasa ta wuceki domin taken mu shi ne 𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝘿𝙀𝙇𝙄𝙂𝙃𝙏 Koda kuɗinka seda Rabonka... Se kun zo _______________&&&& *BOOK ONE* Free pages👌 P..0️⃣3️⃣ 💦💦💦 Ɗaki ta juya ta shige zuciyar ta cunkushe.Shi ko Bibu a sace yabi bayan su. A ɓangaren su Baffa na da Shatou kuwa har suka isa Fadar mai gari yana Rarrashin ta dan ta kasa tsaida kukan ta Muryan da mahaifiyar ta tayi amfani da ita wajen kiran sunan ta ne abun da ke ƙara tayar mata da hankali. Dai dai sun kusa isa Fadar ta mai gari ne ta tsayar da hawayen ta chak tare da haɗiye fuska dan kar ma a ga ruwan ta a samu damar yi mata rainin wayau ko ta muzan ta tana kuka gaban shi yayi zaton tsoro ne. Zama suka yi a gafe kamar yadda Iro da abokan sa suke zaune.Gayar Da Mai Gari Baffa na yayi,sannan yayi shiru bayan ƙare ma su Iro da kowannen su yake cike da batsewa jira kawai suke yi a basu dama su illata shatou sai abun ya bashi dariya da ya kalli girman Shatun sa da kuma yan matasan da ke ta cika suna batsewa kan ta ,wani ko cikin Hancin sa zai iya tura ta amma nan dama suke jira su ci zarafin ta,ƙila har su karya masa yaaaa. Ba su ɗauki mintina uku da zuwa ba sai ga duka abokan nan wasan na su Shatou an tattataro suma tare da iyayen su. Gaggaisawa suka yi da mai gari kafin kowa ya samu guri ya tsaya masu zama kuma suna zaunawa. Gyaran murya mai gari yayi tare sallama ga kowa dake wajen har da wayen da ba,a gayyata ba a wajen yan ganin ƙwamm. Sannan ya cigaba da magana... " Shatou Iro ya kawo ƙarar ki,kumaa na samu shaidu da dama anan dan ga abokan sa sun tabbatar da ke kika aikata masa wannan ɗanyen aiki,ki duba ki ga yadda hannun ya kumbura lokaci ɗaya,sun ce bai Miki komai ba kika aza masa haƙora haka ". Ai da sauri Shatou ta ɗaga idanun ta tana zuba ma mai gari da ya sauke ayar zan cen da ya ɗauko.Ido cikin ido ta ke kallon sa kafin kuma ta ɗauke idanun ta tana mayar da su kan Zaidu da yake furta " Uban kike kallo haka ". Samun kan ta tayi da sakar masa murmushi irin na baka da hankali kafin ta furta ƙasa ƙasa ta yadda shi kaɗai zai iya gane abun da ta furta masa " Ubanka dai " Idanu zai du ya zaro da sauri yana ƙoƙarin yin kan ta aka riƙe sa inji wani daga cikin ya yan mai garin mai suna Ali wanda duk yafi su hankali kuma yaga lokacin da Shatou ta furta masa amsar da ta bashi,wanda sai da ya saka sa murmusawa da mamakin ƙarfin halin shatou.Ciccika Zaidu yake yi yana cije bakin sa ran sa ɓace ji yake ina ma akwai wuta ya jefa Shatou ya futa dan wata irin tsanar ta yaji jin yadda ko tsoron sa babu a idanun ta ta basa amsa. Ita kuwa Shatou Hararar sa tayi tare da kallon Baffa na da yake kallon ta ganin tana Hararar Zaidu gashi yaga ana riƙon sa wanda kuma yana jin sa yanzu ya gama zagin ta a gaban sa,gashi kamar kan ta yake son ya zo.Kan sa kawa ya girgiza yana mamakin abinda ya ƙara harzuƙa sa haka.(Niko nace yar ka ce Baffa na 😂) Kafin ya bata damar magana da idanun sa sannan ya furta " ki faɗi gaskiya kinji Shatou na ".kai ta gyaɗa masa tana sakin ajiyar zuciya. Kamar ba zata yi magana ba ta buɗe bakin ta cikin rashin tsoro ta ce " Dukkanin abokan sa munafukai ne wallahi mai gari shine bai da gaskiya,Sun dai rufe zancen da ƙaryar su,maƙaryatan banza ko kunya baku ji gashi malam Habu yace wuta ake saka mai ƙarya da badan bawa bai isa ya yanke wa bawa hukunci ba da dan an muna karatun da tuni nace yan wuta kuke dukkanin ku Tarin dolaye kawai,Bari kaji mai Gari wallahi a tambayi su Amina a ji Haka kawai suka yi cikin mu muna wasa suka kama faɗawa jikin mu,Ni kuma gashi Inna ni ta ce kar na bar kowa ya taɓa ni,sannan malam Habu ma ya muna karatun shine na cije sa kuma ni ban ma san cewa Iron ka bane da sai dai na gudu ba zan taɓa maka shi ba ".Tana kai ayar zancen tayi shiru.Inda Fadar mai gari tayi wata irin hargitsewa lokaci ɗaya Abokan Iro kamar zasu cire bakunan su wasu na zagin Shatou wasu na tsinema ta,wasu na ƙarya ta abun da ta faɗa duk sun cika wajen da Surutun su,inda da ƙyar aka samu suka lafa dan har wasu suna son kai hannu kan Shatou sai da Baffa na yayi da ƙyar da sun taɓa yar gaban goshi.Maganganun Shatou sun yi tsauri gare su take wani Haushin ta ya da muguwar tsanar ta suka fara kutsa su ji suke kamar su kashe ta take gurin. Baffa na da hankali ya kwanta ya ce " Allah ya ƙara ma lafiya mai gari ni na san cewa SHATOU ba zata taɓa yin ƙarya ba a bincika a tabbatar". Ɗan jim mai gari yayi badan komai ba sai dan yadda zantukan SHATU suka shige sa dan yayi mamakin yadda ta iya zaro irin wannan kalamai kamar ana tsara mata. Sai da ya gama ƙare ma Iro da sauran abokan sa kallo sannan ya dawo da kallon sa ga su Amina da suke tsaye cirko cirko. " Gaskiya ne abun da Shatou ta faɗa "? Mai gari yayi furucin yana kallon su Amina, Ramatu,Jawariyya Manyan ƙawayen na Shatou.Kame kame suka fara gaba ɗaya kowaccen su na son faɗin gaskiya sai dai tsoro ya cika musu zukata ganin yadda iro yake bin su da wani irin kallo da Zaidu ga kuma sauran abokan na sa da suke jifar su da mugun kallon nan na idan kuka faɗi gaskiya zaku gane kuren ku. Amina ce da tafi su Tsoro ta buɗe bakin ta da ƙyar bayan kashe din da Iro yayi mata yanzu ido cikin ido ta furta " A'a ba haka bane,Suma sun shiga ayi wasan da su ne wai ".takai ƙarshen zancen jikin ta na rawa Muryan ta ma na rawa kamar mazari. Wani irin mugun kallo SHATOU ta jefa mata kafin cikin ta kaici ta ce " Wallahi ƙarya ya faɗa,Wallahi tsoron su take ji,ki rantse idan ba jikin ki suka je taɓawa ba " Ta kai ƙarshen zancen cikin takaici wasu irin hawaye suna zubo mata na raɗaɗi da baƙin cikin amsar da Amina ta bada dan ta ji zafin amsar tata fiye da abun da su Iro suka mata dan ita kam ta rage zafin abun da iro ya mata dan ta bar masa dafin da bazai ƙara gigin kai hannun sa kan ta ba. Kuka take yi wiwi Saboda yadda ranta ya ɓa ci musamman dasu Ramatu suka ƙara tabbatar da zancen na Amina haka ma sauran abokan wasan na su. Baffa na ne yake Rarrashin ta da bata baki inda da ƙyar ya samu ta yi shiru. " To ka dai ji kai da kake nuna ka yarda da yar ka ɗari bisa yaran yanzu ai ba abun yarda bane,suna da wayon da kai kan ka zasu iya sayar da kai inba kayi hankali ba,yanzu dai SHATOU ƙarya kika yiwa Iro ni dama na san ba za su iya aikata wannan aiki ba ƙazafi ne kawai ". Shiru Baffa na yayi ran shi yayi matuƙar ɓaci amma da yake mutun ne mai haƙuri matuƙa sai yayi ƙoƙarin shanye ɓacin ran sa. SHATOU kuwa samun hawayen ta tayi sun ƙafe ƙaff kafin cikin wani irin kakkausar murya ta furta " Mai gari nice mai ƙarya ko,wallahi bana ƙarya,a tambayi Baffa na amma tunda kace shi ne mai gaskiya naji na yarda, amma ku sani wallahi kune maƙarya ta gaba ɗaya wannan shari'ar ta ƙarya ce,kuma wallahi sai Allah ya saka mini badai kunce ƙazafi na masa ba,wallahi sai haƙƙi na ya fita nan kusa,Ku kuma su Amina daga yau babu ni babu ku kowa ya tsaya kan sa ni ba mutuniyar banza bace maƙarya ciya.Zan bashi haƙuri kamar yadda aka ce ".Sannan ta kalli Iro tace Kayi haƙuri Muryan ta a sanyaye cikin wani irin baƙin cikin da ya mamaye mata zuciyar ta. " Baffa tashi muje ".Tayi furucin bayan ta miƙe tana jan hannun rigar ta da ya saɓule kaɗan saboda rashin jikin ta gashi kwana biyu tayi yar rashin lafiya ta faɗa. Ƙaramin kallabin ta, da ta cire yanzu ta sanya a kan fuskar ta goge hawayen baƙin cikin da ya silalo mata a ɓoye. Baffa na bai iya cewa komai ba ya miƙe ya riƙe hannun yar sa suka bar fadar bata re da jiran jin wata magana daga bakin mai gari ba. Mai gari haka kawai ya samu kan sa da zuba ma yarinyar ido wadda yake mugun jin Tausayin ta saboda yanayin da rayuwar ta take ,sai dai ya san bata jin magana kuma shi akan iro zai iya ɓatawa da kowa ma dan haka Tausayin ta yake yin ƙasa ya kasa aiwatar da ƙwaƙƙwaran bincike,ya rasa mai yasa suke yawan samun matsala da Iro duk da shima ya ja masa kunne akan

Chapter 2 of 39