ta.
Kalaman ta ne suka sanya jikin sa yin mugun sanyi sannan da kalmar haƙuri da ta bawa Iron da babu wanda yayi tsammani acikin su sun zata sai sun kwana wajen ko shi mahaifin ta bai yi zaton haka ba saboda yasan kafuwar ta akan gaskiyar ta,ya so ya ƙara cewa wani abu amma saboda ganin yadda ta nuna tana son barin wajen ya sa ya amince idan shine farin cikin ta.
A ɓangaren SHATOU kuwa bata nuna komai akan fuskar ta ba sai dai akwai ɓacin ran da take ɓoyewa wanda shi mahaifin ta ya hango sa.
Haƙuri ya yi ta bata da rarrashin ta har suka iso gida.
A ƙofar gidan suka tarar da Bibu wanda aka yi komai gaban sa yana ganin sun ta so ya bi hanya mafi sauri ya ya riga su zuwa gida ranshi jagule amma ya san tunda tayi Allah ya isa lallai Allah zai isar mata haka ma kuma ba lallai haƙurin da ta bada ya tabbata ba har zucin ta ba akwai dalilin ta.
" Adda SHATOU kundawo,Baffa na adda ta aka bawa gaskiyar ta koh "?
Yayi furucin yana riƙo hannun ta.
Hararar wasa Baffa na ya sakar masa yana cewa " Bayan ka gama laɓen ka ai na ganka Malam Habibu,hanyar ma daka biyo na san ta ".
Yakai ƙarshen zancen yana murmushi tare da shafa kan sa.
Shiko Bibu yar dariya yayi irin ta yara cikin yar kunyar ganin sa da Baffa na yayi ya ce " Allah Baffa na ka ganni " Yayi zancen cikin yar dariya.
Dariya Baffa na yayi yana gyaɗa masa kai.
Ita kan ta SHATOU sai da ta ɗan murmusa dama ta san sai ya je gurin koda Inni ni ta hana sa.
" Dama na san dole zaka je Sarkin wayau "
Baffa na ya ƙara faɗa yana dariya.
Dariya Bibu yayi sannan yace " Wallahi Allah Baffa na sai Allah ya isar wa Adda SHATOU an cuce ta ga gaskiya ƙarara amma sun danne haka ranar aka yi wanchan case ɗin,Wallahi bamu yafe ba tunda suka saka Adda ta zubar da hawaye gaban su,mugaye ".Ya kai ƙarshen zancen yana sharar hawaye masu zafi na jin Haushin abinda aka yiwa yar uwar sa.
" Kuyi Haƙuri kunji kuma SHATOU A riƙa tausasa harshe kinji gaban manya wata rana mai gari zai iya saka a zane ki ba zai dubi ƙarancin ki ba ".Cewar Baffa na.
Baki ta turo gaba tana cewa " Allah ni ba ƙarama bace Baffa na Sai dai Bibu dan yafi Ni tsawo ne ma yake jin shi kamar Babba " .
SHATOU tayi zancen tana tura bakin ta gaba irin na sakuwa.Dan in tana cikin su ji take kamar yau ta zo duniya.
Dariya Bibu yayi yace " Baffa na ai in tsawon Banza ne wani yayi mugani Adda SHATOU guntuwa yar ƙarama,kuma ma ai Baffa na tace ma Inna ni bata son ta girma haka take son zama yar ƙarama kamar yar gidan mai gari saratu" Ya na kai ƙarshen zancen yayi cikin gida da gudu yana dariya cikin farin cikin yadda SHATOU ta saki fuskar ta.
Yadda ta zaro ido waje ne ya san ya tsokano rigima hakan ya sa ya gudu ciki yana dariya.Saboda bata son ya na ko kaman ta ta da saratu yar tsohon mai gari wadda take Wada domin haka halittar ta take.
Baffa ma dariya yayi ganin yadda ta bishi a guje tana cewa " Wallahi Allah ya raba Ni da zama saratu Wada miyan ka ya tsallaka rafin maliya ya wanke tass "..
Ciki Baffa ya shige shima yana sayo gidan na su bakin shi washe kamar ba yanzu dukkanin su suke cikin zafi ba amma gashi har Bibu ya sa sun manta musamman Shatou koda yaushe yana ƙara ƙaunar soyayyar dake tsakanin junan su,yana Roƙon Allah ya shirya masa su ya daɗa haɗa masa kan su.
Tun shigar Bibu Inna ni ta fito wadda ke zaune kamar a ƙaya cikin ɗakin na ta tana jiran Dawowar su,sai leƙe take ko zata hango su,ta sako hijabi kuwa yafi sau biyar ganin sun daɗe tana son ta isko su sai ta kasa zuwa ta ji nauyin zuwa wajen.
Numfashi ta sauke a hankali ganin Shatou ta shigo a guje tana dariya Wanda ya kwantar mata da hankali a tunanin ta an bawa shatoun Gaskiya ne.
Cirko cirko Baffa na ya isko su tsaye.
Cikin kwantar da hankali Baffa na ya kalli Inna ni yace " Komai ya wuce ki kwantar da hankalin ki yar ki ce mai gaskiya kuma anyi sulhu ba zai ƙara shiga gonar ta ba,ko ta shiga ta sa ".Baffa ya faɗa mata bayan ya kora su Shatou ɗakunan su tare da basu umurnin kowa ya kwanta yayi Addu,a.
A jiyar zuciya ta ƙara saukewa Jikin ta sanyaye kafin ta masa sai da safe ta shige ɗakin ta tana sayo shi.
Tana zama akan ɗan madaidaicin gadon na ta wasu irin hawaye masu zafi suka silalo mata kafin kuma ta fashe da wani irin matsanancin kuka mai tsuma zuciya kuka irin na bege da tausayi,sai da tayi mai isar ta sannan ta miƙe ta ɗauro Alwallah ta yi raka'a biyu ganin tunani zai addabe ta sannan ta kwanta bacci wanda ya kwashe ta da ƙyar.Baffa na da ke laɓe bakin ƙofar ne ya shige ɗakin sa cike da tausayi dama ya san sai ta koka ya rasa yaushe zai raba ta da wannan kukan yana son cika mata burin ta amma babu dama.Haka ya kwanta shima cikin Tausayin ta da na Shatoun.da su kan su gaba ɗaya.
A ɓangaren mai gari kuwa haka taron ya watse kowa zuciyar sa babu daɗi sai suka ji kamar sun aikata babban Zunubi.Amina da su Ramata kuka suka yi tayi har suka isa gidajen su tare da iyayen su da su kansu basu san abinda ke faruwa ba sai yanzu kuma sai gashi ya yan su sun ƙarya ta zancen Shatoun.Gashi sai koke koke suke yi ba ma kamar Amina da zantukan na shatoun suka mata wani irin zafi sai taji kamar ta rabu da ita har abada Dagasken.
🌷🌸🌸🌷
*KADUNA*
Ya rane mata sa da ba za su haura sha ba suka zagaye wata yarinya dake zaune Dirshan a ƙasa tana kuka kamar ranta zai fita sun kasa Rarrashin ta sai kallon ta suke yi kowa na tsoron abun da kan iya zuwa ya dawo idan ya taɓa ta ko hana ta kukan.
" Kutumar uban nan uban wa ya taɓa ki REENA "??
Wata yar mitsitsiyar yarinya ce kamar dai wadda ke zaune ƙasa tayi zancen tana doso gurin bayan jin kukan yarinyar da nake zaton yar uwar ta ce.
Matsawa baya dukkanin su suka yi suna kallon ta dama tsoron su ɗaya su taɓa ta ace sune yanzu suji ajikin su dan dukkanin su sun halin ta.Yanzu sai su ci na jaki kan yar uwar Tata.Cikin ɗan tsoro suka fara mata bayanin nan suka ganta zaune tana kukan haka.
Hannun yarinyar ta riƙo tana kakkaɓe mata uniform ɗin jikin ta da suka yi duhu saboda ƙasar da ta kwanta tayi murje murje kamar yar goye.
Hanya ta kama tare da ita hannun su ruƙe da na juna.Dama Driver suke jira bai zo ba shine ta nemi yar uwar Tata bata gan ta ba tayi zaton ta tafi ta bar ta kamar yadda ta saba ko sai ta wahalar da ita da driver neman ta,tafiya suka yi sai da suka ɗan ja kaɗan kusa da yaran ta sake ta tana Hararar ta tana cewa " Amma wallahi REENA ke wawuya ce wai har yanzu kin kasa yin hankali ji yanzu dan ubanki yadda kika yiwa uniform ɗin ya kike son a kalle mu idan mun koma ne so kike Ummah ta ji Babu daɗi ne a ce kullum ya yan ta ne marasa jin magana ƙazamai ".
" Wallahi LINA kar ki ƙara ce mini Wawuya nikammm yanzu da Banyi haka ba ai ba zan gan ki ba me Shegen yawon tsiya kawai ".REENA tayi furucin.
" ohh wai dama saboda ni kika kwanta ƙasa kika kashe jiki haka kamar kura saboda baki da wayau ".
Wadda aka kira LINA tayi zancen tana Dariya irin ta yarinta tana kallon jikin yar uwar ta ta,kafin ta fara dariyar da ta san tana ƙular da yar uwar ta ta.
Aiko kafin kace me REENA ta far mata da duka tana kuka na sangar ta dan LINA tafi ta wayau,dambe suka kaure dashi LINA ta haye abarta tana jibga kamar kullum da suke dambe duk da tsananin soyayyar dake tsakanin su amma in ɗaya ya taɓa ɗaya sai an yi rigima,babu ma kamar LINA da take cikin tsokanar ta koda yaushe,Duk yadda REENA take da sanyi haka take biye ta suyi tayi gata ba wani ƙarfi ba.Ga LINA da Shegen jan magana ko ka tsokane ta ko baka tsokane ta ba ita sai ta yi domin yar rigima ce ta ƙwarai dan REENA haƙuri take matuƙa da ƙarfin hali ita kawai ka bar ta da rigimar ta ga LINA wanda ba kullum take kula ta ba sai rashin son maganar ta da yake nature nata da yar shagwaɓar ta.Da sauri Mutumen dake cikin danƙareriyar motar da yayi parking kusa da su ya fito yana furta " Subhanallah LINA me ta Miki ".
Da sauri ta ɗaga ta tana nishin Masifa.
Ita kuwa REENA kuka ta fashe dashi cikin azaba dan ta jibgu.Kafin ta furta " Allah ya isa na Wallahi kuma sai na faɗa ma Abban mu,kuma sai na faɗa ma Ya Bilal muguwa kawai ".
Jin sunan ƙarshe da REENA ta kira ya sanya hankalin LINA mugun tashi har tsigar jikin ta na tashi.Kafin ta fara zarar idanu kamar kazar da ta sha ruwa.
Riƙo hannun ta Drivern na su yayi yana furta " Baki kyauta ba LINATU babu wani dalili kika ma yar uwar ki wannan mugun duka Yanzu ya kike son fuskantar Yallaɓai Bilal idan har ta faɗa masa ".
Ɗan Dattijon Drivern na su da ya isa haihuwar su ya furta yana Rarrashin REENA dake cigaba da rera kuka harda na shagwaɓa....
" Bafa haka kawai na dake ta ba Baba Adamu itace ta kawai daga na yi mata dariya ta hau ni da duka ni kuma naji bazan iya ƙyaleta ba shine na hau ruwan cikin ta na rama ".
LINA tayi zancen tana turo bakin ta gaba ga wata irin Fargaba da ta mamaye ta jin sunan wanda aka ambata yanzu duk da kuwa baya kusa amma ta san kowane irin lokaci zai iya zuwa Dan ganin shi kawai suke yi tsulum a cikin gidan ba tare da sun shirya ma zuwan sa ba.
" To yanzu dai ke REENATU ki yafe wa yar uwar ki,kar ku shiga gida kuna faɗan nan kun ji ko "..yayi zancen yana ɗan kallon motar ta sa.
Kai REENA ta gyaɗa tana furta shi kenan na yafe mata.
" Ni dai ta bani haƙuri sannan na yafe mata ai itace ta fara kai min duka Wawuyar yarinya ".
Zaro ido malam Adamu yayi jin abinda LINA ta furta kai tsaye cikin haɗe rai bare yayi zaton wasa take yi tunda an kashe case ɗin.
Cikin sauri da rarrashi ya furta " haba " Ya ta LINATU ,na ce fa ku daina ba kya son Mahaifiyar ku ta samu salama ne kullum kuna cikin rigima tana fama daku ".
Shiru LINA tayi kafin ta furta " Ni ba LINATU nake ba fa,Baba Adamu LINA nake ".Tayi zancen tana tura baki gaba.
Kafin kuma kamar mai tashin iska ta wuce fuu ta take ta shigewar ta bayan motar ta su.
Hararar bayan ta REENA tayi ta yi ƙyafci sannan ta bi bayan ta.
Malam Adamu kan sa kawai ya girgiza yana musu Addu,ar shiriya.Yana bin bayan su da sauri dan ya san wanda ke cikin motar yanzu haka ya gaji da jira.
LINA da bata lura da shi bane ta waiga da sauri jin ƙamshin turaren da ke razanar da ita.Shi ɗin ne dai cikin sauri ta fara ƙoƙarin ficewa daga motar jikin ta na wani irin rawa....
Su waye LINA,REENA BILAL???
Daga Alƙalamin Fa'eehbg ✍️
Gimbiyar taskira 👑
(FirstLady 🙌)
Ba zamu daɗe muna free pages ba gaskiya zaku iya fara payment...
1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
*08069059746*
Daga wannan sati bazan ƙara posting a weekend ba gaskiya saboda ranar Hutu ce.🙏
Ƙarin bayani.
08069059746
Like share and comment pls 🙏
Rashin yin REACT zai sa na daina yin Update kullum.✍️
Idan kuna son cigaba LABARIN KURMAN ƘADDARA Ku riƙa comment da react.
*UPDATE*
https://chat.whatsapp.com/BzXaAD3pB6yJ1wBBrkE4V0
*Masu son ganin ƙarshen labarin sai suyi following channel ɗita.👇*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*💋KURMAN ƘADDARA💋*
©®Fa'iza Almustapha Murai
Daga Alkalamin✏
👄FA'EEH BG👄
💎Sadaukarwa ne ga class mate ɗina ɗalibban GGC T/MAFARA,ZAMFARA STATE SET 2K18.A duk inda kuke Alkhairin Allah ya kai muku.🤲💎
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
_Daga marubuciyar littafin_
*A MAFARKI NASANTA 1&2(paid)#500*
*RAYUWAR MU A YAU complete (free)*
____________________________________
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
___________________
_Wannan page kacokam Sadaukar wane gare ki Hafsat Bature(BOSS BATURE)💔💋 Nagde ƙwarai da kulawar ki akan wannan Book Allah ya bar zumunci,🤲dan kin yi mun abun da wasu suka kasa yi,Ina Alfahari dake🌹🥰KK story na godiya_
*BOOK ONE*
free pages👌
P..0️⃣4️⃣
🌬️🌿🌲
Sai dai me kakkausar Muryar sa ce ta shiga Kunnuwan ta yana cewa " Don't dare try to move "
Numfashin ta ne take jin yana shirin yin sama bayan tabbatar da shi ɗin ne.Tsinewa Malam Adamu ta fara yi a cikin zuciyar ta tun kafin ta iya dawowa cikin natsuwarta,dan mugun tsoron yayan na su take yi matuƙa saboda yadda ya saka mata ƙahon zuƙa saboda rashin jin ta.Zama tayi kamar kace ƙyar ta gudu musamman da ta san bata da gaskiya.Da ta san yana cikin motar Nan da tuni ta bar faɗan nan har haƙurin ma zata iya bawa REENA har ƙasa ma ta duƙa mata idan ta kama.
REENA da ta shiga gaba itama da sauri ta juya tana kallon bayan motar bayan jin ƙamshin na sa cikin farin ciki take kallon sa tana " Wel come back Ya B. " Shima da Murmushi ya Kalle ta yana furta ya " How are you girl ". "I'm fine ".
Ya studies ya mata ta amsa masa cikin sakin fuska kamar ba yanzu ta gama kuka ba.Shima haka ya saki ta sa fuskar.
Shiru ne ya ratsa motar bayan gama gaishe gaishen na su.
" LINA wai baki ga Ya B. Ba kika yi shiru ".
REENA tayi zancen kai tsaye ita har ta manta da faɗan da suka yi ma murnan ganin ya'yan na su ya gusar mata da zafin jibgar da tasha.
LINA murmushi ta ƙaƙalo kafin ta ce " na gansa ai har na gai da shi,amma bari na ƙara masa sannun da zuwa ".Ta yi zancen a ɗar ɗar.REENA bata ƙara tankama ta maba sai ma sautin ƙira'ar Alqur'ani da ta fara bi da ya ke tashi daga cikin motar kaɗan kaɗan.
Ganin kamar hankalin sa bai kan ta hakan ya sa a hankali ta furta " Ya .B Barka da dawowa Ina wuni ".
Yi yayi kamar bai ji abun da take faɗa ba ya share ta har sai da ta ƙara maimai ta sunan na sa kamar zata yi kuka cike da Haushin da ta ƙunsa na share ta da yayi.
" Kunnuwa suke ji ba " Kuma kika saka mini kuka na ci uban ki yanzu wajen nan ƙatuwar banza mara hankali ".Shiru tayi kamar ruwa ya cita jin yadda ya jefo mata magana kamar jiran ta yake yi dama kuma ta san za,a rina tun da ya gan ta da idanun sa kan ruwan cikin REENA yar gaban goshin sa tama jibgar ta kamar ta samu aikin yi.
Ɗiff tayi kamar ruwa ya cita tana turo baki gaba haɗe da gunguni tana kallon glass ɗin mota da suka ɗai suke iya hango na waje tinted ne glass ɗin motar shi yasa basu lura da Bilal ɗin a cikin motar ba.
Har suka isa gida babu wanda ya ƙara furta komai sai dai hankalin LINA ya ƙi kwanta wa ko kaɗan burin ta ta samu ta gan ta kusa da Ummah lokacin ne zata san ta tsira.Wata ƙatuwar mension ce mai tsari da burge wa wadda take cike da gidaje na alfarma masu kyau motar ta kutsa Hancin ta bayan wangale mata gate.
Tsarin gurin gwanin burge wa irin yadda kuka san estate take ko ina ƙalƙal sai sojojin da ke wulgawa kaɗan kaɗan saboda a ciki saboda mai gidan su da yake gari.Ganin sojojin da yawa ya ƙara tabbatar mata da ya dawo kenan,kuma da alama zai daɗe gida,dan ƙwarori ne suke tsaron estate ɗin amma daka gansu da yawa to yana gari.
Dai dai mazaunin motar ya yi parking motar wanda ko ida dai dai ta parking bai yi ba ta fara kiciniyar fita motar da iya ƙarfin ta.Baba Adamu da ya fahimci saurin na ta sai ya cire lock ɗin yana sakin guntun murmushi.Aiko kamar jira LINA take yi ta banka aguje cikin wani gidan da yake ɗan kusa da parking lots ɗin.Yana dai dai ta Parking ɗin REENA da ke ta sakin murmushi tana jiran ya'yan nasu su fita tare yana fitowa itama ta fito tana tsalle tsallen ta tana jin kamar yanzu ta ga ya yan nasu da ya kan ɗan kwana biyu bai garin saboda yana yin aikin sa Kasancewar sa Land army na ƙasa bai cika zama ƙasar ba ma.
Guntun Murmushi ya saki yana kallon REENA kafin ya riƙo hannun ta ganin yadda take ta tsalle tsalle sannan ya furta " Ki Nutsu kinji " Natsuwa kuwa tayi kuwa tana cigaba da sakin murmushi.A tare suka shiga cikin ƙaton falon jakar ta sargafe a bayan ta ga datti jikin ta duk ya bayyana.
Da gudu ta faɗa jikin Matar da ta fito daga kitchen tana kitchen tana amsa waya Fara ce tass kamar Bilal da REENA sai dai kama Bilal ya fi kama da ita sosai bisa ga su LINA da suke kama sosai da mahaifin su.
" Ummah I miss You "REENA tayi furucin tana dariyar farin ciki.
" Oh ni Barirah bint Usman Wai yaushe SAREENA ta zata yi hankali ne ALINA ta shigo a hargitse,REENA kuma ta dawo da datti me ya ɓata jikin ki haka ne,Ke da kika fita tsafff ".Ta kai ƙarshen zancen tana sakin murmushi mai cike da natsuwa
Tana zare ma REENA school bag ɗin tana kallon Bilal dake murmushi shima jin mahaifiyar su ta kira cikakken sunan ta.
" Ummah Faɗuwa nayi " REENA ta furta itama cikin murmushi.
Hararar wasa Ummah ta sakar mata kafin ta furta " naƙi wayon Wannan akwai alamar rashin faɗuwa jibi yadda kika yi busu su fa gashi idanun ki sunyi rau rau kamar sun yi kuka,anya kuwa ba halin kuka yi awaje ba keda wacchan shiryayyar ".
Kallon Bilal tayi tana tsoron ta faɗa wa Ummah ya kama LINA ya daka duk da ta san may be ya riga ya gansu.
Bilal kuwa yi yayi kamar bai san maganar da ake yi ba ya mayar da hankalin sa kan wayar sa.
" Ummah faɗuwa fa nayi,shine LINA ta mun dariya na yi kuka ".Ta kai ƙarshen zancen tana yar shagwaɓarta.
Murmushi kawai Ummah ta saki tana furta " to jeki ki watsa ruwa idan kuka yi sallah sai ku fito yin lunch ga ya yan ku nan bai ci komai ba ya dawo ya matsa sai ya fara ganin ku jeki, kuma LINA ta tabbatar ta fito yin lunch ".Ta san tsafff zata ƙin fitowa tunda basa ba maciji da ya yan na su.Duk yadda ake firar sa kullum baya nan da ya dawo sai ta fara ɓoye ɓoye na rashin gaskiya.
Dariyar farin ciki ce ta kama REENA jin ya yan su bai ma iya yin lunch ba sai ya fara ganin su hakan ya sa da gudu ta bar falon tana tsallen murna ya nason su sosai.
Idanun sa ya bita da su yana sakin murmushi a hankali kafin ya maida kallon sa ga Umma ya ce " Ummah Barka da hidima "
" Barka da dawowa Soja,na san kaga komai da ya faru faɗan suka yi ko ".?
Tayi mishi zancen cikin sanyin da jikin ta yayi ta sigar tambaya tana zuba masa idanun ta.
Idanun sa ya ɗauke daga na mahaifiyar sa yana sakin ajiyar zuciya saboda ya san sune Raunin ta matuƙa waɗannan yan biyun ya yan na ta ya rasa abinda yake damun su musamman LINA kamar mai ƙwanƙwammai haka take wasu abubuwan wata rana ma kamar mai taɓin hankali dan so da yawa ya sha kama ta tana wasa ita kaɗai tun bata fara kai haka ba,ita kuwa REENA sangar ta gashi saboda mugun faɗan su abun ya zamar ma mahaifiyar su faɗe a cikin familyn da kishin samrin ta da kuma kishiyoyin ta ta rasa yadda zata yi maganin matsalar amma abu ya faskara sai gaba yake yi.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya furta a hankali cikin natsuwa " UMMAH dambe suka yi " nan ya labarta mata abun da ya gani da idanun sa.
Kai UMMAH ta jinjina kafin ta sauke ajiyar zuciya " tana furta kwana biyu naga an samu zaman lafiya amma ashe abun gaba yake yi ,Allah ya shirya mini su,Dan ALLAH Karka dakar mini "Yaa Kaji Soja,Addu,a kawai zamu cigaba da saka ta,gaba ɗayan su ma ".
Kai ya jinjina yana furta " Amin " Amma tabbas da badan Mahaifiyar su ta hore sa ba da sai ya hora LINA sai tayi kamun kunne wanda zata daɗe bata yi rigima ba,tuna cewa ya sha hora ta amma bai yi aiki ba sai Shegen tsoron ta ya sa shi girgiza kan sa kawai yana tuno wani lokaci da ta yi wa REENA wani irin duka kamar zata raba ta da duniyar ta kan kawai ta sanya hular ta tace ta cire bata cire ba.Ai ko ya wahalar da ita kamar yadda suke yi a wurin training na sojoji ta wahala sosai harda jinya amma bai hana ta koma ba.A.lokacin kaɗan ya rage ya sha mari ga UMMAH dan Abba faɗa kawai yayi masa na ya riƙa haƙuri,ƙucuciyar ta ce haka, LINA taci baƙar wuya da ƙyar take iya tafiya a lokacin har sai da tayi kusan sati bata iya tafiya lokacin suna da shekara takwas ciff a duniya.
miƙewa yayi bayan Sun gama maganar shima ya wuce na sa sashe dake part ɗin duk da yana da ɓangaren sa kuma achan yake sauka idan ya zo ko sashen Abba Babba duk da gidan ba kowa a cikin sa.
Zama tayi jagwab akan gadon tana sauke ajiyar zuciya kafin ta saki guntun murmushi tana kallon wayar ta da ta gama amfani da ita yanzu bayan shigowar ta ɗaki.
Wani kiran ne ya sake shigowa akan wayar hakan ya sa ta ɗaga da sauri tana furta " Abban su Barka " Bayan amsa Sallamar sa.
"Sun dawo school ko,Injin ba,a yi halin ba " .Kai ta girgiza kamar yana gaban ta kafin tace ''Basu yi ba yanzu haka ma sun fito yin lunch "Murmushi yayi mai sanyi yana jin wani irin farin ciki na mamaye sa.Itama murmushin ta saki kafin suka ƙara yin maganar dawowarsa dan yaje yayi attending wani business class a Morocco wanda yana yawan tafiye tafiye kasancewar sa ɗan kasuwa Babba,A halin ma gaba ɗaya tunda ga kakan su Yan kasuwa ne familyn basa wani aikin gwamnati face kasuwancin su in ka cire Bilal da yake da muradin aikin soja wanda shima yana taɓa Business ɗin sosai bai saki gadon gidan na su ba.
SHATOU
Yau ta tashi da wani matsanancin ciwon kai wanda ya hana mata zuwa makarantar allo ta safe a safiyar lahadin,tare da ayyukan da ta saba ɗan jagwalgwalawa mahaifiyar ta,tunda ba wani iya wa tayi ba ita dai barta da aikin gidan ta horu da iya share share da yan goge amma ta fannin girki ba,a cewa komai.
Baffa yau ya ma kasa iya fita farauta ko kaɗan,Bibu ma da ƙyar ya iya tafiya makarantar.Kula take samu ta ko ina Baga Baffa ba Baga Inna ni ba ita kuwa an samu abun yi sai ƙara lanƙwashe wa take yi,dan ko abin karin daƙyar ta tsakura ta sha magani ko shi sai da INNA Ni tayi daƙyar.
Sai zuwa maraice ya ciwon ya lafa mata dan ba kasa fai take kwanciya ciwo ba tun dai wanda ta sha yi lokacin tana ƙarama saboda rashin samun kulawa ta uwa dan Inna ni
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 39