Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣1️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ 💕💕💕💕💕💕💕 💕💕💕💕💕💕 💕💕💕💕💕 💕💕💕💕 💕💕💕 💕💕 💕 Ganin Inna ni na tun karo ta ne hakan ya sa ta koma bayan Baffa na da yake tsaye yana kallon su bayan shigowar sa yanzu,domin kuwa koda bai tambaya ba ya tabbatar da ta ji komai. Ɗan murmushi yayi yana kama hannun Shatou ya riƙe gamm ganin Inna ni ta tayi tsaye waje ɗaya idanun ta sun sauya na damuwa lokaci ɗaya. " Ayi haƙuri mun san munyi laifi " Ya faɗa yana ɗan kallon Bibu dake hawaye domin ya san duka laifin shi ne da yayi subutar baki. Ajiyar zuciya Inna ni ta sauke domin kuwa wani sabon tunani ne ya shigo kan ta tun bayan jin zancen. Wanda shima Baffa na ya tsinci kan sa a wannan tunanin da ganin yanayin Inna nin ɗin. Ɗaki ta shige ba tare da ta furta komai ba. Ɗan numfashi Baffa na ya sauke yana dawo da Shatou gaban sa wadda take ta zarar ido tana ƙyaf ƙyafta su. " Ki daina irin haka kin ji Shatouwa Wayen nan mutanen,mutanen kirki ne,Wannan mutumin da kika taɓa gani mai kama dashi a fadar mai gari mahaifin sa ne ba hamman sa bane,Kinga ko dan shi bai kama ta ki masu hakan ba su ci darajar shi,bana son hakan ki daina kin ji gashi na ga kinyi hankali kuma sai ki ƙara komawa gidan jiya " Ya kai ƙarshen zancen yana sakin guntun murmushi irin na manya mai ma'anoni da dama da shi kaɗai ya bar wa kan sa sani. Shatou kuwa idanu ta ƙwalalo tana kallon Baffa na jin zantukan sa wai ba Hamman sa bane chab ita kam ta zata wa da ƙane ne ashe mahaifin sa ne,lallai kuwa Baban sa (Abbu) bai tsufa. Niko nace Yo to mutumin da Hutu da Naira suka ratsa ya za,ayi a hango tsufan sa take.🤭 Wannan sai talaka bawan Allah. Allah ka azurta mu da arziki mai albarka.🤲 Kai ta jinjina tana Murmushi bayan Baffa na yace mayar da idanun to,kar su zube. Bibu kuwa kallon Baffa na yayi da shatou yana share hawaye, Shatou ɗan hararar shi tayi bayan haɗa idon da sukayi,dariya ta ɗan saki kaɗan ganin yana matsar hawaye.Baffa na neh yace " haba kai ko Habibullah maza ba a san su da saurin kuka ba duk ka komawa Inna nin ku kamar Shatou ". Baki shatou ta turo gaba tana furta " Ai ni na girma dan na san na girmi Bature nesa ma shi da yake da girman biredi dan haka na bar wa Bibu kuka ba zan ƙara yin kuka Bama ". Zuba mata ido Baffa na yayi yana kallon ɗan ƙaramin bakin ta dake magana chau chau.Murmushi ne mai faɗi ya samu kan sa da yi yana girgiza kan sa domin kuwa ya san wa take magana kai. " Allah ya sa " Shine abun da Baffa na ya furta kawai yana cigaba da murmushi kan wani al'amari dake shiga zuciyar sa akan lamarin shatoun na yau. '' Ki daina yiwa mutane rashin kunya yanzu Kinga Innar ki ta Hasala dake ". Ganin yadda ta ɓata fuska ne ya sa ya furta. " Zamu cigaba da bata hakuri karki damu shatoun Baffa nan ta ". Ya kai ƙarshen zancen yana shafa kan ta tare da ƙara ƙawata fuskar sa da murmushi. Itama sakin fuskar ta ta tayi tana sakin guntun murmushi. Bibu kuwa zuwa lokacin ya share hawayen sa yana shesshekar kuka. "Adda shatou kiyi haƙuri wallahi ba ƙarar ki na je kawo wa ba,baki na ne ya yayi maganar ban sani ba ". Yar guntuwar harara ta ƙara sakar masa ta wasa tana riƙo hannun sa tace " Ai ban ce ban yafe maka ba da zaka yi irin wannan kuka,kuma baka ga Inna ni bata dake ni ba " Ta kai ƙarshen zancen tana ɗan kallon ƙofar ɗakin Inna ni. Baffa na ne ya ce " kowa ya wuce yayi Sallah kafin ta wuce dan tana hanya " Dan haka suka rabu kowa ya shige ɗakin sa bayan yayi alwallah. Cire kayan jikin ta tayi ta sanya wata yar rigar ta, ta a tampa ta,ta da Sallah. Shiko Baffa na ficewa yayi daga gidan gaba ɗaya. A ɓangaren Inna ni kuwa ta jima zaune bakin ɗan gadon ta tana dafe ƙirji da ƙoƙarin hana tashin hankalin ta bayyana fili.Sai da ta samu natsuwa bayan nanata sunayen Allah sannan ta fito daga ɗakin tana cigaba da ayyukan gaban ta sai dai ta sha al washin ko ranƙwashi ne sai ta yiwa Shatou da ta tayar mata da hankali ko ta rage zafi da raɗaɗin abun da ta ji. Shatou na gama sallah bayan ta yi addu'a ta cire rigar jikin ta ta ɗauro zanen ta na wanka sannan ta fito tana sakin yar doguwar Hamma ta yunwar dake naniƙar cikin ta. Tsaye tayi ganin Inna ni zaune sai kuma ta fara susar kai tana furta " Inna ta ina Yini " Ɗan ɗagowa Inna ni tayi ta Kalle ta ta ɗauke kai. Ɓata fuska shatou tayi kafin ta matsa kusa da ita cikin ɗar ɗar cikin yin ƙasa da kai ta ce " Na fa daina wannan ma saboda sun taɓa yi muna wulaƙanci ne, saboda ina da Haushin su shi ya sa na musu rashin kunya,kuma kar ta san kar ni da su babu abinda zasu iya mini dan ogan na su ma girman biredi ne " . Ta kai ƙarshen zancen tana dariya harda ƙyalƙyatawa.Inna Ni dake sauraren ta sai yanzu ta ɗaga kai ta kalle ta kafin ta saki guntun murmushi tana girgiza kan ta a cikin zuciyar ta kuwa faɗi take mai hali baya fasa halin sa yanzu a wannan yanayin har ta samu damar dariya irin haka. Ganin murmushin Inna ni ya sa shatou ƙara gyara zama tana cewa " Kuma fa Inna ni baki san abinda suka mini ba kwata fa suka watsa wa su Amina " Ɗan shiru tayi ganin Inna ni ta kalle ta sai ta ƙara furta " Ai har da ni,Ni kuma shine yanzu na rama ". Kai Inna ni ta girgiza bayan gama zancen Shatou wadda ta yi shiru tana ɗan leƙen fuskar Inna ni da ta juyar da kan ta dan ganin ko ta saki fuskar gaba ɗaya. Dai dai nan kuma Bibu da ya gama ta sa Sallah ya fito yana furta " Inna ni yun wa nake ji,Ina abincin mu ". Kallon sa Inna ni tayi da murmushi kafin ta ce " Habibullah kamar dai yau ka sauka gidan nan ". Shima dariya yayi dan sun san inda take ajiye musu abincin su. Amma yau shine da tambaya duk da wata rana ita ke zuba musu ta kawo musu. " To ai Inna ni kin fi saba mana da ki kawo mana da kan ki ". Shatou tayi zancen. A wannan karon Inna ni Murmushi ta yi wa shatou kafin ta ce " To yanzu sai ku je ɗaya ya zuba muku sai kuci tare ,dan tuwo ne ma na dawa yau muka yi gidan ". Ai ko rufe baki bata yi ba shatou ta fashe da kuka tana furta " Allah Ni ba zan ci tuwo ba haba,jiya ma fa shi muka ci,yau ko yar murjin nan Ace ba,a dafa mana ba " Ta ƙara ɓarkewa da kuka " Shikenan sai mutun ya dafe shima,ai in mutun na cin tuwon dawa kullum baƙi yake yi dan haka Ni dai ba zan ci ba Allah kuwa sai dai na zauna da yunwa na idan Baffa na y zo ya siyo mini tsiren Sharehu " Ta kai ƙarshen zancen tana shesshekar kuka tare da ƙara taɓe baki na sangar ta. Ƙala Inna ni bata ce mata ba sai da ta gama har ta fara share hawayen ƙaharun sannan ta ce " Habibullah shiga ka ɗauko mini Bulalar nan da nake ta ajiya ƙasan gado na,dama ta tsuma sosai jini kawai take jira ta ɗiba,sauri zaro mini ita". Aiko shima Bibu baki ture ya kama hanyar ɗakin yana kallon Shatou da ta ke ƙoƙarin maƙalkale Inna ni aiko yana shigewa ta shige jikin Inna ni kamar zata koma ciki tana furta " Ai na ce na daina kuka fa yanzu ma baki ga dariya nake yi ba " Ta fara ɓallan dariya ga hawaye na Silalo mata dake nuna dariyar ƙarfin hali ce kawai da Shegen tsoron ta tunda ta san Baffa na baya kusa dan haka ta yiwa kan ta wannan dubaran dan fidda kai. Inna ni kuwa ikon Allah take kallo tana son tayi dariya amma ta haɗe ran ta. Sai dai cikin zuciyar ta sai da ta dara musamman da ta kalli fuskar shatoun ta da hawaye keta silalowa tana gogewa tana ƙara cewa " Dube ni fa na daina kukan nan ai haka na cewa Baffa na ko Bibu " Ta kai ƙarshen zancen tana kallon Bibu dake tsaye bakin ƙofar ɗakin Inna ni Hannayen sa ɓoye a bayan sa. " Kawon bulalan ". Inna ni ta furta wa Bibu bayan ta ƙare masa kallo daga tsayen da yake. Kuka shatou ta ƙara fashewa da shi kafin ta ce "Na fa daina wallahi Na tuba Inna ni ki mini afuwa ina son shiga aljanna zan dinga jin maganar ki ". Jin Inna ni na furta kin shigo hannu mai kunnen ƙashi bayan gama furucin ta na farko.Kuka kasharɓan shatou take yi wanda ya sanyaya jikin Inna ni da ta haɗe mata hannaye waje ɗaya,alamar Dagaske dakan ta zata yi kamar yadda shatou take zato da Bibu da idanun sa suka cika da hawaye. " Bani bulalan,ko sai na zo gurin " Inna ni ta ƙara furtawa zuciyar ta ƙuntace domin kuwa wata irin damuwa take tsintar kan ta a duk lokacin da shatou take cikin yanayi mara daɗi tunanikan baya ke dawo mata marasa daɗi da masu daɗi da wayen da ya kamata su zauna mata akai da wayen da basu kama ta ba. " Dan Allah ki yafe mini Inna ni ina son shiga Aljanna zan dinga jin maganar ki,kuma idan nayi kuɗi zan kai ki Umrah da hajji ke da Baffa na ".inda ta kai ƙarshen zancen tana ƙokarin ƙara fashewa da kuka. Wani irin rauni ne ya bayyana gare ta ƙarara sai da idanun ta suka cika da hawaye sai ta shanye abun ta gudun kar yaran su gani duk da ba lallai su fahimta ba. " Nace ka bani bulalan fa " Inna ni ta ƙara furtawa tana ɓoye murmushin ta da ya fi kuka ciwo.Duk da ta san cewa Bibu bai ɗauko komai ba hasalima bata da wata bulala dan ta samu ta rage fitinar Shatou ne da ita kan ta ba son bugun ta take yi ba. " Inna ni idan ba kya sona zan bar gidan nan kawai ni nama yarda a mini Aure kawai ". Cike da sakin fuska Inna tace " Dagaske ". Kai shatou ta gyaɗa mata tana sharar hawaye. Yar ƙaramar dariya Inna ni tayi kafin ta ce " kai Masha ALLAH,to waye mijin dan mu kai ƙarshe kafin zuwan Baffan ku ". " Ni kawai Zan Auri iro tun da yana sona idan na zama yar sanda zan je da shi birni ya riƙa wanke bakin sa,Idan na zama Babba kuma sai na sake shi ya dawo ƙauye yayi sabon Aure " Wannan karon dariya Inna ni tayi da ta bayyanar da wushiryar ta irin ta Shatou mai kyau kafin tace " Kai masha Allah wannam abun alkhairi ne Bari Baffa nan ku ya zo sai aje neman Aure da wuri da kan mu ma zamu je na dangin mijin zasu zo ba sai a fara daga yar mafarauci ". Shiru Inna ni tayi bayan fitowar wannan furuci da ta ji ya mata wani iri a baki kafin ta ɓatar da yanayin da zuciyar ta ke hauhawa tana ƙara sakin dariya. Ita kuwa Shatou baki ta tura gaba tana sauke ajiyar zuciya. " Ai na yafe Miki shatoun Baffan ta ". Hawayen ta,ta ida sharewa tana sauka daga jikin Inna ni. Bibu kuwa yar ƙaramar dariya ya fara yi tun bayan fara maganar ta Aure. Ɗauko muku abincin ku yau faten dankali ne muka yi,abincin mutuniyar ka ". Ai ko shatou take ta wartsake ta miƙe jin abinda Inna ni ta furta nan ta fahimci Inna ni tsokanar ta take yi shi ya ƙara sakar mata da jiki tabbatar da cewa ta haƙura. " Yeeehhh Dankali dankali " Shatou ta furta cike da farin ciki miyan ta har katsewa suke yi.Saboda yadda take son sa. Lokaci guda ta manta abun da ya faru yanzu.Murmushi Inna ni tayi cike da farin cikin sakewar shatou tana cigaba da saƙar ta tana yiwa ya yan nata addu'ar shiriya.Bibu da sauri kuwa ya ɗauko musu abincin tare suka zauna suka ci suka ƙoshi kowanensu na ta zuba santi.A ɓangaren Baffa na kuwa fadar Mai gari ya wuce a chan ya tarar da mai gari ana ta fadanci da jama'ar sa ana ta yaba irin ƙokarin Abbu da Mahaj.Ganin sa da mai gari yayi kuwa dai dai wannan lokaci ya ce " Malam Jibril Sai yanzu ". Murmushi Baffa na yayi kafin ya ce " Eeh wallahi na samu kira tun ɗazu sai dai rikicin Shatou ne kasan ba ƙarewa yake yi ba shine ya tsayar da ni,nan ya labarta ma mai gari komai " ai ko mai gari ya yi dariya Sosai wanda har ya bawa jama'ar fadar mamaki shi kan sa Baffa na Murmushi yake yi. Sai da duk jama'ar suka watse kasancewar mai gari ya ce kowa ya zai iya tafiya. Sannan ya kalli Baffa na ya sake yin murmushi. " Tabbas Farauta Haske zai samu a cikin duhu a cigaba da addu'a Allah ya tabbatar mana da Alkhairiin sa a ko da yaushe ". Amin Baffa na ya amsa yana ƙaƙalo ɗan murmushi da bai kai ciki ba. Sai kuma suka miƙe suka shige wani ɗan ɗaki na mai gari ban san abinda suka tattauna ba amma sun jima sannan Baffa na ya fito zuwa lokacin an fara kiraye kirayen Sallah la,asar. A ɓangaren su Mahaj kuwa suna fita Babban titi suka koma yadda suke kafin suka fara sharara gudu kamar zasu tashi kasancewar Umurnin Ubangidan na su ne. Basu daka ta ba sai da suka samu waje suka yi Sallahn azahar da ke neman wucewa,Sannan suka kama hanyar asalin Abujar.Koda suka isa anyi Sallan La,asar dan haka kai tsaye masallaci Suka sauka suka fara sauke farali. Babu kowa cikin Babban falon dama bai tsammana ba dan haka kai tsaye ya shige Sashen sa.Kai tsaye wanka ya faɗa bayan tuɓe kayan jikin sa.Ya daɗe ruwa na sauka jikin sa masu ɗumi kafin ya ɗauro wanka. Ɗaure da guntun towel ya fito fari ƙar wanda yayi wa ɗaurin saɓu saɓu ga kan sa na ɗigar da ruwa kaɗan kaɗan kasancewar ya ɗan goge sa da towel a cikin toilet ɗin.Bakin fankacecen mirrorn sa da ya kusa ma he rabin bango wanda yake shaƙe da kayan gyara masu tsada da kyau da inganci ga lafiyar fata da kuma turarukkan sa masu Shegen ƙamshi da ƙamsasawa wayen da suka kama bedroom ɗin sa sai kace wani Company na turare. Hand dryer ɗin sa mai kyau ya kunna wadda take a jiye a waje mai kyau ya busar da gashin kan sa tass kafin ya kashe ya koma murza mayukkan sa sai da ya bi ko ina na jikin sa da man sa mai kamshi sannan ya koma gyara gashin sa da ke ta shinning kamar an masa ruwan mai aiko take ya ƙara yin wani irin haske da shinning har wani kashe ido yake yi. Sai da ya gyara sa tass sannan ya taje ya koma ya bi jikin sa da Haɗaɗɗen body spray na sa.Haka kan sa ma sai da ya ji na sa turaren sannan a ɗan gaggauce saboda baccin da ke idanun sa ya bar bakin madubin yana komawa gaban sip ɗin sa kasancewar sip ɗin ta sa mai taya ce kafa kawai ya saka ta buɗe da kan ta ƙananan kaya ya zaɓa mara sa nauyi daga cikin dubannin kayan dake tsare cikin ta cikin tsari mai kyau gwanin burgewa komai dai irin na luxury life babu ƙaramin abun a ciki. Saka kayan yayi wanda suka kasance guntun wando ne na mai santsi mai haɗe da vest fara ƙal kamar yanayin wandon. Yana gama kimtsawa ya saka turarukan sa masu ƙamshi.Masha Allah, yayi kyau kamar wanda zai je wani taro ɗan tsaye yayi bakin mirrorn ya ɗan zuba ma kan sa ido kafin wani tunani ya shigo ƙwaƙwalwar sa hakan ya sa shi jan guntun tsaki mara sauti kafin ya ɗaga ƙafa a hankali ya kwanta kan gadon sa bayan ƙure gudun A C,da rage haske. Yana kwantawa kuwa bacci mai daɗi ya kwashe sa duk da ya ɗan yi ta juye juye Kafin ya kwashe sa. Muby kuwa Bai zame ko ina ba sai part ɗin Abbu cike da zumuɗi. Koda yayi sallama tare da knocking a ƙofar falon Abbu,Abbu na zaune yana duba wata tsohuwar jarida ya zuba mata idanu bazaka taɓa iya tantance yanayin da yake ciki ba sai dai daga yanayin fuskar sa zaka shaida ba mai kyau bane,domin kuwa jikin sa a sanyaye yake dan tun bayan dawowar sa meeting da Mr president ya ke aikin karatu ko muce na zarin wannan jarida dan yau ko Amma bata gane wa kan sa ba abinci ma bai saka a bakin sa ba wanda kuma bata damu ba domin inda sabo ta saba da wannan yanayin na sa dan haka ta share sa kafin ya dawo dai dai. Koda Abbu ya ji knocking kuwa ɗan zuba ma ƙofar idanu yayi dan hankalin sa na kan su Mahaj ɗin sa dan haka yayi zaton shi ne ya dawo,miƙewa yayi ya mayar da wannan jarida cikin wata locker mai kyau sannan ya saka makulli ya rufe ta yana saka keys ɗin a cikin bedside drower. Sai da ya ɗan sanya wa kan sa jarumtar ɓoye yanayin da yake ciki kafin ya bada izinin shigowa.Cike da Sallama Muby ya buɗe ƙofar yana kutsa kan sa ciki bakin sa dauke da murmushi,cike da girmamawa ya duƙar da kan sa ƙasa ya gayar da Abbu da yi masa Barka da gida wanda ke zaune a kan kujerarar sa ya ɗan miƙe kafafun sa akan Centre table. Cike da farin ciki Abbu da yayi zaton Mahaj ɗin ne wanda sai yanzu ya tuna da sai ya huta yake zuwar masa idan ma har yanzu suka dawo. " Kun dawo kenan ya hanya ". " Lafiya lau Abbu " " Masha ALLAH Allah ya sanya albarka " " Amin " " Y komai yake tafiya ta ɓangaren ayyukan " ? " Lafiya lau Abbu suna ƙokari sosai " " Masha ALLAH Allah yayi mana jagora ya sa amizani " " Amin " Muby ya furta yana ƙara sakin murmushi. Murmushi Abbu yayi kafin ya ce " An sake wata draman kenan ". Baki washe Muby yace " Sosai Abbu". Cikin sakin yar ƙaramar dariya Abbu ya ce " Sha fa mini na ji,ai na manta da recording na nace ka mini " Ya kai ƙarshen zancen yana ƙara ƙawata fuskar sa da murmushi jin wani yanki na damuwar sa na raguwa tun kafin ya ji abinda ya faru. Muby kuwa gyara zama yayi daga ƙasan da yake zaune ya labartawa Abbu komai da ya faru bai ɓoye masa komai ba.✍️ To jama'a Abbu zai kwashi romon drama 🤣🤣🤣🤣🤣Kai Allah ya shirya mana Amarya Shatou uwar gida a gidan Iron mai gari.🤭🤭🤭An bar muku kayan ku mutanen Shatou saura shan buki💃💃💃🚴🚴🚴🚴🚴🚴😂😂😂 Zanje ganawar sirri da (INAYATH KHALIL) Sir ZAFIN KAI.😏my next Novel,idan na dawo sai a bani labarin yadda ɗaurin auren ya kasance da malam Iro🚴🚴🤭🤣 Amma fa Muby akwai ɗan munafunci 😏 Ya zai mana haka.🙄 Kar ku ji komai Ni ɗin ce dai ta ku muna tare har ƙarshen wannan tafiya.In sha ALLAH.🤗🤗💃💃 Ku kasance tare da yar mutan Zamfarawa dan gane wa idon ku ƙarshen wannan labari mai abin mamaki da al'ajabi,sarƙaƙiya,ruɗani,cin amana yaudara.All in one story📚Kurman ƙaddara. Na gaishe ku na amana ta.🔥✨💕 Labari yanzu yake ku dai cigaba da Bibiya ta.🔥🔥🔥🔥🔥🔥 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 Book one zai kare a page 50 Dan haka wadda ta shirya sai ta saka kuɗin ta dan babu wanda zamu jira zamu cigaba da wannan tafiya in sha ALLAH.🙏🙏🙏 # _FA'EEH BG CE✍️_ *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣ 2️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ 💕💕💕💕💕💕💕 💕💕💕💕💕💕 💕💕💕💕💕 💕💕💕💕 💕💕💕 💕💕 💕 Tunda Muby ya fara bashi labarin yake ta sakin murmushi yana ƙara jin wani irin farin ciki a ran sa shi haka kaiwa yake samun kan sa a farin ciki idan suka haɗu waje ɗaya. A kallo ɗaya zaka san cewa Abbu yana cikin farin marar misaltawa. Domin kuwa fuskar shi ta da ɗaɗa sosai murmushi kawai yake saki yana gyaɗa kan sa tare da girgiza sa cike da jin wani irin farin ciki. " Lallai kuwa na yi missing ya zama dole na saya maka Camera ko dan ɗaukar rahoto ". Cewar Abbu bayan Mubarak ya gama zayyane masa komai. Yar ƙaramar dariya Muby yayi yana shafa kan sa. Yana gamawa yayi wa Abbu sallama bayan sun ƙara tattaunawa akan yadda komai yake tafiya. Koda Muby ya fita Abbu kasa zama yayi ya miƙe ya fito Bai zame ko ina ba sai bedroom ɗin Mahaj koda yayi knocking ya ji shiru sai ya fara tunanin abun da zai ce masa dan haka yayi tsaye kafin kuma ya juya fuskar sa cike da farin ciki. Sai dai koda ya koma falon sa kasa zama yayi ji yake ina ma ace a gaban sa aka yi komai ya samu abun tsokanar mahaj ɗin sa tun da ya samu dai dai shi wadda duk miskillancin sa sai da ta saka shi magana mai ɗan tsawo.A haka wannan yini ya zo wa Abbu cikin farin ciki dan koda Amma ta same shi gab da Magriba sake ta samu fuskar sa wanda ya sanya ta ɗan mamaki duk da ba abun mamaki bane hakan a gare sa.... ***A ɓangaren su Alina kuwa yau sun tashi da wani irin mahaukacin ciwon kai gaba ɗayan su wanda ba abun mamaki bane irin haka a gare su domin kuwa sukan yi rashin lafiya wani sa'in tare. Dan haka aka kira family doctor na su ya duba su ya basu ɗan taimakon gaggawa saboda Leena da jikin ta ya fara ciccira. Cikin ikon ubangiji yana basu taimakon gaggawa da ya dace bacci ya kwashe su mai nauyi.Hankalin Ummah da B ya tashi sosai babu ma kamar Abba domin shima yar ƙaramar ciwo yayi saboda damuwa dan kwanan su uku haka. Sai yau ne suka fara samun sauƙi,sai dai Reena ce kawai jikin ta ya fara sauƙi dan dai Leena ba,a cewa komai amma dai itama ya rage mata ba kamar kwanakkin da suka wuce ba... * " Hahaha Lallai ta baiwa ke Masifa ce,da sannu zaki ga yadda aikin mu ke ci ke shaida ce Ɗan Baiwa baya aiki kawai dan haka ki ƙara kwantar da hankalin ki wayen nan alamomi ne na cikar aikin mu ".Ya kai ƙarshen zancen yana gaggaɓan dariya. Inda itama ta fara dariyar kamar wata zararrriya. " Hankali na ya fara kwanciya Ɗan Baiwa buri na ya kusa cika komai ya kusa dawowa hannu na daga ni sai shi dole mu ƙara zage damtse a ƙara bawa su ɗan duhu jini su ji ƙarfi a jikin su su aiwatar da aiki cikin kuzari,nayi imani da kai ɗan Baiwa na san ba zaka taɓa bani kunya ba ". Ta ƙara sakin dariya ta na kai ƙarshen maganar. Cike da rashin imanin ta. " Hhhhhh ta Baiwa kenan,kibar wuƙa da nama a hannun mu zamu ɗaukar Miki fan sa har da riba dole komai ya koma hannun ki ". Miƙewa tayi kamar yadda suka saba tana zagin sa yana zagin ta kafin ta yi layar zana ta ɓace ɓatt. Ɓacewar ta shima ya ɓace ɓatt kamar bukkar sa bata taɓa zama wajen ba. " Ummah jiya fa mafarki nayi mara kyau akan LEENA amma na manta wallahi Ummah ina dai tuna kukan ta ne da na ji " Reena ce ke zancen idanun ta na cika da hawaye. Idanu Ummah da ke kallon ta zuba mata wadda ke kallon ta bayan fara maganar. Numfashi Ummah ta sauke cike da ƙaryewar zuciya ta " Ta ce ki yi mata addu'a Allah ya bata lafiya da ke baki ɗaya,amma wane irin mafarki ne kika yi haka " ? " Na faɗa Miki Ummah na manta fa ". Kai umma

Chapter 33 of 39