Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta girgiza kawai zuciyar ta cike da rauni kafin a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana furtawa a fili Allah ya baku lafiya ya ya na. Amin Reena ta furta tana gyara zaman ta kan doguwar kujeran da take kai wadda take kallon ta Ummah. Dai dai nan LEENA ta fito tana ya mutsar fuskar ta da ke nuna har yanzu tana jin jiki sai dai akwai alamar sauƙi ya fara samuwa itama. Zama tayi kusa da Ummah tana shagwaɓe fuska. " Ya jikin na ki " ? Ummah ta faɗa tana taɓa wuyan ta. Jin da zafi sai dai ba sosai ba hakan ya sa ta jan ajiyar zuciya tana ƙara rungume ta jikin ta bayan ta gyaɗa mata kai. " Aleena ya jikin ki " Yar hararan Reena tayi jin ta kira ta da complete name na ta kafin ta rufe idanun ta tana ƙara ya mutsar fuskar ta. " Ummah Leena itama ta fara samun sauƙi ko " ? Kai Ummah ta gyaɗawa Reena wadda ta ƙara yin tambayar ta kulawa da yar uwar ta. Dai dai nan Abba ya shigo wanda ya dawo yanzu daga office. Dan yanzu ya fara samun damar leƙawa kwana biyu ciwon ya yan na sa ya tayar masa da hankali matuƙa. Ɗauke da murmushi akan fuskar sa ya zauna kusa da Reena yana ƙara ƙawata fuskar sa bayan amsa masa Sallamar sa. " My babies sun samu lafiya ". Cike da murmushi Reena ta ce " Eh Abba mun samu lafiya, Leena ce kawai yanzu take ɗan jin ciwon kan ta ,Amma itama Ummah ta taɓa jikin ta temperature na ta ya sauka." Murmushin Abba ne ya ƙara faɗaɗa cike da jin daɗi ya shafa kan Leena yana furta " Allah ya ƙara muku lafiya ya kare ku daga sharrin maƙiyi da sharrin Aljan da duk wani abun cutarwa da muke gani da wanda bama gani ". " Amin " Reena da Leena suka haɗa baki wajen faɗa dan suna matuƙar ƙaunar Addu,an Abba haka ma Bilal da ya shigo yanzu ya amsa a hankali yana sakin ɗan murmushi. A ɓangaren Ummah kuwa ido ta zubawa Abba kafin ta sauke kallon ta daga kan sa tana Amsawa da Amin ganin yadda ya ɗan faɗa wanda sai yanzu ramar ta ƙara fita. Ajiyar zuciya ta sauke yar ƙarama tana shafa kan Leena. " Barkan ku da yini,Ummah da Abba " Cikin sakin fuska Ummah ta amsa masa kafin ta ƙara sakin murmushi na jin yar kunya.Jin Abba na kiran " Momyn Yara yau babu sannu da zuwa ga masoyi sai ta ya yan ki kike yi ".? '' Ya jikin Leena ɗin ".? Ya ƙara faɗa yana ta sowa daga kujerar da yake kusa da Reena yana komawa zuwa kusa da ita. " Sannu da dawowa,Abban su,Leena ta samu lafiya itama ". " Murmushi yayi ganin yadda Ummah ke soke kai kafin ya shafa kan Leena yana dawo da ita jikin sa fuskar ta ya shafa a hankali yana ƙara jin Tausayin ta na ƙara mamaye sa musamman da ya ji ɗan zafi a jikin ta sai dai bai kamar na ɗazu ba da safe. Idanu Leena ta ɗan Lumshe kamar mage tana ƙara shigewa jikin Abba kafin ta ce a hankali " Abba sannu da zuwa ". " Yawwa ya jikin,?kin samu lafiya ko "? Kai ta gyaɗa masa tana sakin gun tun sanyayyen murmushi. Kan ta Abba ya ƙara shafawa kafin ya sakar mata kiss a goshi. Yana cewa." Allah ya baku lafiya ". Amin suka haɗa baki wajen faɗa. Miƙewa yayi ya haye Sama bayan ya gaisa da Bilal ɗin da sai yanzu suka haɗu shima dan da wuri ya fita shima ya fita wajen motsa jiki. " Babu komai a tattare da su kamar yadda na faɗa maka,amma dai abun da kawai zan ce maka shine ku ƙara da gewa da Addu,a akan su nima a ta gefe na zan dage sosai dare da rana zan taya ku nema musu kariya wajen Ubangiji,yanzu ƙuruciya kawai ke damun su ". " Ungo wannan ka ba su,su sha sannan kuma ka tabbatar ka shafa wa kowaccen su a kai da ƙafafu ". " Kar ka yarda da kowa yayi wannan aikin ka tabbatar kayi shi da kan ka " Sallamar Ummah ce ɗauke da jakar sa a hannu ya sa shi dawowa daga duniyar tunanin da ya shiga na zantukan malam Hambali dan yanzu daga wajen su yake daga office ya wuce chan har yanzu kalaman malam suna masa shawagi "Babu komai a tattare da su ....." Shin me hakan ke nufi kenan akwai wani abu a ƙasa sannan me zai saka malam yin wayen nan zantukan " Ka tabbatar kayi shi da kan ka ....." Numfashi ya sauke da ajiyar zuciya bayan zaman Ummah ɗan kusa da shi kaɗan. Zuba masa ido Ummah tayi ganin yadda ya yi shiru kamar ya ƙara komawa duniyar tunanin da ta same sa. Numfashi ta sauke kafin a Hankali cike da yar damuwa ta ce " me yake damun ka Abban yara ". Murmushi Abba ya ƙaƙalo kafin ya ce " Babu komai Barry kawai dai ciwon yaran chan ne yake damu na,ina tsoron wani abu ya same su ". Hawaye ne ya wanke fuskar Ummah cike da wani irin raunin ta dake bayyane ta ce " Abban su,ka cire damuwa komai zai wuce,zasu samu lafiya,sannan duk wasu rigimar su zasu daina ". " Kune ƙwarin gwuwaita Abban su dan Allah ku daina sage mini gwiwa ". Ajiyar zuciya Abba ya sauke yana ɗan samun sanyi a ran sa,ko ba komai ya samu ƙwarin gwiwar da ya ke jin yana neman rasawa. " Kar ki damu Barry,amma akwai wani hanzari wai Ni kaɗai nake hasashen yaran nan kamar akwai sihiri a jikin su ". " Tunani ne ke faɗa mini hakan Barry na kan ka sa yardar wa kai na babu wanda ya ke bi mini ya ya da bita da ƙulli ". Wata irin faɗuwar gaba ce ta saukar wa Ummah cike da tsoro ta ce " Abban su Sihiri me za,a tsinta a jikin ya yana,me suka yi wa wani babu abun da suka sani fa,bamu da wani maƙiyi Abban su,kai gaskiya Abban su Wannan hasashe ne kawai Dan Allah Abban su ka daina irin wannan maganar wallahi ka tayar mini da hankali innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un " Ta kai ƙarshen zancen tana fashe masa da kuka. Jikin Abba ne ya ƙara yin sanyi ya ji dama bai yi maganar ba a hankali ya ɗan rungumo Ummah jikin sa ya fara rarrashin ta. "Ba cewa nayi Dagaske ba hasashe na ne kawai,kuma sai yanzu na tabbatar da hasashe na ba gaskiya bane domin kuwa bamu da wani maƙiyi bare su na fili da na ɓoye duk abinda kika faɗa ba gaskiya ne". " Allah ya basu lafiya,ya sa komai ya zamo muna tarihi mu da su,ya dawwamar da mu cikin farin ciki ". Amin Ummah ta faɗa a hankali bayan tsaida kukan na ta. Tana share hawayen ta tare da sauke ajiyar zuciya mai nauyi. " Zamu kai kukan mu ga ubangiji a koda yaushe mu masu miƙa wuya ne,dan haka Abban su ka ɗauka jarabawar mu ce wannan mu da su,Amma bana son ka raunata imanin ka ta hanyar yin wannan hasashen Abban su,Shekaran jiya ma na saka anyi musu saukan Alqur'ani,yanzu ma zan bada kuɗi a ƙara musu wata ". Murmushin Abba ne ya fito da wani irin farin ciki ya washe fuskar sa daga damuwa. Hannun ta ya riƙo a hankali yana fuskan tar ta kafin ya ce " Allah yayi Miki albarka Barry,Allah ya saka Miki da Alkhairi ya ƙara Miki ƙarfin renon ya yan mu da basu tarbiyya ". " Amin " Ummah ta amsa tana sakin murmushi. Jakar ta sa ya amsa bayan ya miƙe daga zaunen ya saka ta inda yake ajiye jakar sa. Tuno da abun da malam yace masa dan haka ya tura jakar cikin lockern sa kamar yadda Ummah ta saba yi masa. Kallon sa ta dinga yi ganin yau da kan sa yake ƙokarin ajiye jakar ta sa. Kafin ya ta ce " Abban su Yau ko kayi mantuwa wannan ba aikin ka ba ne ". Murmushi Abba yayi yana juyowa kafin ya ce " kar ki damu na ga kina gajiye ne ga kula da marasa lafiya shi ya sa na ke ƙokarin yin komai da kaina ina son ki huta ne ". Murmushi ta ƙara saki na jin daɗi. Wanka ya faɗa yana furta" bari na shiga na sake jikin nan nawa". Kai Umma ta gyaɗa kafin ta miƙe ta fice kasa wajen haɗa masa abincin sa,ta san Abba baya wa sa da cikin sa. A ɓangaren Abba kuwa bai daɗe ba ya fito daga cikin toilet ɗin tsaf ya kimtsa cikin kaya mara sa nauyi na zaman gida. Jakar sa ya janyo kafin ya Fiddo da yan gorunan ruwan addu,an da malam Hambali ya ba shi. Zuba masu idanu yayi gora biyu ce ciff yanda malam yace a ba su na kwana biyu. Har ya ɗauki ɗaya ya fita da ita sai ya tuna maganar malam hakan ya sa ya mayar da ita cikin jakar yana ficewa daga ɗakin. A ɓangaren Bilal kuwa bayan wucewar su Ummah cike da yar kulawa ya dubi Leena. Yace " Y jikin na ki ".Naji sauƙi. Ta bashi amsa. Daga haka bata ƙara cewa komai ba sai shigewa cikin kujera ta ƙara lafewa lafe. Ita kuwa Reena jikin shi ta shige tana cewa " Ni ya ya B baka mun ya jiki ba ". Ɗan guntun murmushi ya saki yana kallon fuskar ta da tayi fayau kafin ya ce '' Na ga ba kya buƙatar tambaya ne Reena,gashi kina da ƙarfin jikin ki har kin samu damar surutu ". Ya kai ƙarshen zancen yana shafa kan ta. Yar dariya tayi tana cewa " eh na ji sauƙi y B " A wannan karon murmushin ya ƙara saki kafin ya ce " Ta ci abinci ". Fahimtar wadda yake magana hakan ya sa ta ce " Eh ta ci chocolate,kuma tace ta ƙoshi haka ta cewa Ummah ". Kai ya gyaɗa kafin ya ce " Je ki Kice wa Inna Rabi ta haɗo mini tea mai kauri ". Miƙewa Reena tayi jikin ta sanyaye dan har yanzu da Sauran rashin ƙarfi a jikin ta itama. Dai dai fitowar ta dai dai lokacin da Ummah ta ke saukowa daga step steps fuskar ta babu yabo babu fallasa..... Sai dai fuskar ta kamar da danshin ruwa da alama sai da ta shiga bedroom ɗin ta,ta wanko fuskar ta. Kallon B tayi dake zaune ya zuba wa Leena idanu yana kallon ta wadda idanun ta ke rufe da alama bacci ya fara kwasar ta. Ɗan jimm tayi kafin ta karasa saukowa tana giftawa ta gaban sa hakan ya sa ya ɗauke idanun sa kan ta yana jin wani mugun tausayin Ƙannen na sa na sukar zuciyar sa. Zama Ummah tayi kafin ta shafa kan Leena ta ce " Baiwar Allah ta fara samun barci ". Kai B ya gyaɗa kafin ya ce " Ashe bata ci abinci ba ". " Eh wai ta ci chocolate ta ƙoshi ". Ummah ta bashi amsa. " Ummah Chocolate ai ba zai yi ba shi ya sa jikin na ta ya ƙi yin ƙarfi ". " To ya za,ayi Soja basa jin dadin komai ne itama Reena da ƙyar ta yarda ta ci coslow ko shi kaɗan ". Reena dake zaune ce ta ce " Ummah ai na ƙoshi ". Kai Ummah ta gyaɗa mata tana Murmushi kafin ta ce wani abu sai ga Inna Rabi ɗauke da cup a kan ɗan ƙaramin ti re mai kyau. To subscribe yours contact this number 08069059746 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣ 3️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ 💕💕💕💕💕💕💕 💕💕💕💕💕💕 💕💕💕💕💕 💕💕💕💕 💕💕💕 💕💕 💕 Wani table ne dake kusa da Bilal ta ɗaura tiren Saboda Reena ta faɗa mata saƙon sa ne. Gaisawa suka yi kaɗan sannan ta ƙara yiwa yan biyu ya gajiya sannan ta bar falon tana amsa umurnin Ummah dake tabbatar musu da a ƙara kimtsa dinning tunda sun gama aikin Su da wuri ita da masu aikin. Miƙewa Ummah tayi tana cewa " Kuma fa ina ga har da yunwa ke ƙara nuƙurƙusar ta fa,da zata iya ai da an haɗa mata abu mai sauƙi ta sha". Cike da yar natsuwar sa da kulawa ya ce " Ummah ai wannan ita aka haɗawa ko kaɗan ne sai ta sha ". Kai Ummah ta jinjina kafin ta ce "Eh yayi hakan bari na tashe ta ". " Alina,! Alina ! Alina ! " Haka Ummah ta jera mata sunan na ta inda kafin a hankali ta fara buɗe idanun ta da suka fara mata nauyi.Ya Mutsa fuskar ta tayi kafin ta ce " Ummah na fi son kwanciya ".tana batun sakar mata kuka. Ummah cike da kulawa tace " yi hakuri ki tashi zaune,kin ji ki saka wa cikin ki wani abu ". Ɓata fuskar ta tayi kafin ta ce " Ummah ai na faɗa Miki na ci chocolate fa,kuma na ƙoshi,Dubi fa ciki na " Ta kai ƙarshen zancen tana buɗe shaffafen cikin ta. Bilal dake kallon su ne ya janye idanun sa da sauri yana kallon shayin dake ta tururi. Ɗan fara feta shi yayi da spoon yadda zata ji saukin shan sa. Ummah kuwa rarrashin ta ta fara kafin tace " Ni dai yanzu ke da ya yan ku bari na je na ɗauko waya na,kafin Abban ku ya fito ". Miƙewa tayi ta haye steps tana jin yadda Leena ke ta ƙoƙarin sakin kuka. Ita kuwa Reena kallon ta kawai take yi. " Ya B ka rarrrashe ta,ko Ni na sha shayin makon ta ". Ɗan murmushi yayi yana jan table ya zauna ya miƙa wa Leena ɗin tea ɗin yana haɗe kyakkyawar fuskar sa. Ɓata fuskar ta tayi kafin ta karɓi cup ɗin da ya dungura mata. A hankali ta fara sha ganin tana sha da wasa hakan ne ya sa ya karɓa ya fara bata da kan sa haka take karɓan tea ɗin kamar ɗaci duk da ta ji daɗin saukar sa a cikin hanzayen ta. Motsin Abba ne ya sa shi ɗan kallon steps din. Abba ne kuwa ke saukowa fuskar shi cike da murmushi yana kallon su wani irin farin ciki na mamaye sa kulawar da Bilal yake bawa yan uwan sa na sanyaya masa zuciya ya san cewa ko ba sa duniya Indai har yana raye zasu samu kulawa bayan ta kakannin su. " Ai dole sai da hakan dan tun da na shigo na ga alamar bata ci wani abun kirki ba ". " Ka kyau ta Allah yayi muku albarka ". " Amin Abba ". " Yawwa Ina Umman ku ". Dai dai nan kuma ummah ta fito riƙe da wayar ta a hannun ta fuskar ta ƙawace da murmushi. Yau Abba Dinning Abba ya wuce bayan hango an jera komai a chan. Bayan sa Ummah ta bi bayan ta yiwa BILAL kallo ɗaya da Leena. Reena kuwa hankalin ta ta mayar kan Tv tana cigaba da kallon ta shar toon. *** " Ba zai yuyu ba gaskiya Boka gangaro ya kamata dai ka ƙara duba mini lamarin nan babu yadda za,a ce komai yana faruwa haka ba tare da kasan wayen da ke wannan aikin ba ". " Hmmm ba zaki gane bane ai shi rame da ƙarami yake farawa kafin ya yi girma na sha faɗa Miki ki fitar da hannun ki cikin wannan rigimar wannan abun daɗaɗɗen aiki ne yanzu ya fara ci,bana son Ni dake mu shiga Masifar da zata yi muna wahalar fita,Masu wannan aikin ba ƙananan Azzalumai bane suna aiwatar da shi ne cikin kuzari domin kuwa su ɗan duhu kowa ya Sani ba su san inda imani ya shiga ba,ba wani sanin su ne ban yi ba,a wancan karon na ji tsoron su ne hakan ya sa na ɓoye mikisaboda yadda na tsorata da abun da na gani,na dai shaida Miki ki fita wannan sabgar aikin ki ɗaya kuma yana kan ci,muna aiwatar da shi,duk da an riga ki aiwatar da shi amma zamu iya loda na mu koda ace wanchan ya sauka ". " Hakan shine zai kawo mana salama Ni dake ". Ƙaramin tsaki matar dake zaune itama cikin shigar ta ta alfarma sai dai fuskar ta rufe ruff da wani irin liƙab irin na zamani wanda sai kayi da kyau zaka iya hango idanun ta domin rufe yake ruff. " Naji yanzu ga wannan Ni dai a yi mai yuyuwa kuma zan yi ƙokarin kwantar da hankali na,tun da haka kake so,amma muddin na ga cigaban da na gani ya tsaya zan dawo kayi aikin nan ko na chan za waje ". " Ba sai an kai chan ba shegiya yanzu dai zube muna kuɗin mu kiyi gaba ". Itama tsaki ta ja dan ta tsani zafin ga da yake mata wasu lokuttan duk da kasancewar sa boka ji take kamar ta kai masa bugu sai dai tana da tsoro dan tana mugun tsoron aljanu dan haka take raga masa kar ta kai kan ta ta baro. Kuɗaɗe ne ta Fiddo da su masu yawa ta a ajiye masa aiko ya kwashi abun sa yana gaɓɓatan dariya kamar wani zararre. Miƙewa tayi ta fice da baya baya tana zagin sa yana Amsawa,sannan ya na ramawa. Haka tayi ta ta fiya da baya baya har sai da tayi masa Nisa kamar kullum sannan ta juya tana cigaba da tafiyar ta hankali kwance. Fitowar ta bakin titi ne inda ta parker motar ta ta shige tana tada ita sai dai tunda ta shiga motar take jan tsaki ita kaɗai.... " Shiru haka take zaune ta kafe waje ɗaya da kallo ga idanun ta cike da ƙwalla ta sha igiyoyi a jikin ta na ɗauri saboda kwanakkin nan da suka shuɗe tun bayan dawowarsu Canada abun ya ƙara hauhawa sai ta ƙara ƙaimin ji wa kan ta ciwo akwai lokacin da ta yanke gefen cikin ta glass wanda har yanzu ba,a san inda ta same shi ba, wanda da ƙyar aka ceto ranta kasancewar ba sosai ta samu yan kan ba amma duk da haka ta zubar da jini sosai. Komai na jikin ta ya sauya saboda yanayin jikin na ta. Wani irin kuka ta fashe dashi tana rufe idanun ta,tana sake buɗe su. Tana ƙokarin nuna inda ta kafe da idanun ta sai dai hannuwan nata a ɗaure suke baiwar Allah daga ɗauren ta fara buga kan ta da bango haka kake jin sautin ƙuu ƙuu tana gwara kan ta a bangon fillern da aka ɗaure ta akai,dai dai lokacin ne kuma ya zo kawo mata abinci domin kuwa yanzu shine kawai yake iya shigowa batare da tayi har gowa ba,domin tsoron kowa take yi dan ko su Amoh da Dady sai ta samu bacci da su Nurse mirra suke zuwa duba ta da tsaftace mata jikin ta,cikin wani irin sauri ya buɗe ɗakin da key da ya zo da shi kafin ya shige da sauri cike da tausayin ta da tsoro gudun kar ta yiwa kan ta illa duk ya san ba lallai ta iya ko dogon motsi bane saboda yadda Uncle Yaqub ya ɗaure ta dan shi kasawa yayi haka ma Dady dan Tausayin ta suke ji sosai kowannen su ji yake kamar ya da wo da lalurar ta jikin sa,Amoh kuwa tun da jikin Isha ya ƙara rikichaɓewa itama jikin ta ya tashi,yanzu haka tana fama da Bp. Wasu irin hawaye ne yake jin suna neman sauko masa sai dai kasancewar sa namiji mai ƙarfin hali da zuciya hakan ya sa ya shanye ya matsa kusa da ita yana ajiye wayar sa akan gadon dake ɗan nesa da ita kasancewar an chan za mata ɗaki yanzu tana kusa da Suhaila ga ƙofar ta gata ta. " MA'ISHA " ! Ya ambata yana haɗiye wani irin abu mai ɗaci a cikin zuciyar sa kafin ya fara ƙoƙarin kunce ta dan bayan ɗago fuskar ta da tayi kacha kacah da hawaye tayi jawur ya ji ya kasa jurewa ganin ta hakan,sai dai yana fara kunce ta, ta fara kai masa bugu da ƙarfi tana cigaba da kuka mai tsuma zuciya.Idanun sa ne suka yi jazir kuma ya kasa hana ta dukan na sa ganin yake yi kamar shin e abun da zai rage mata raɗadi. Uncle Yaqub da ya shigo gidan yanzu ne ya zo direct nan dan ya gan ta kasancewar suhaila tace masa Suhail na nan aiko cikin sauri ya matsa ya riƙe ta yana katsawa Suhail tsawa mai girma ganin abun dake faruwa domin ya san tsaf zata iya ji masa domin ba acikin hankalin ta take ba,maimakon ya hana ta bugun sa shine ya saki jiki tana ta jibgar sa gata da ƙarfi kamar na maza goma. Da ƙyar Uncle Yaqub ya ɗaure ta yana furta " Are you in your right sense Suhail , What's this " .? Ɗagowa Suhail yayi ya kalle sa da idanun sa da suka ƙara rikiɗewa na damuwa da tausayi dan shi kwata kwata bai ji zafin dukan da ta masa ba. Rufe idanun sa yayi da yake jin sun masa wani irin nauyi. Babu abun da ke ƙara hargitsa tunanin sa irin jin kukan ƙanwar ta sa dake ratsa dodon kunnen sa. " Gaskiya baka cikin hankalin ka Suhail so kake kai da ita ku zama ɗaya ne,me ye wannan,ita fa ba,a cikin hankalin ta take ba,Amma kai fa ".?karamin tsaki yaja kafin ya ƙara furta " Gaskiya kaima kana buƙatar Ganin likita Suhail because what you did,person that's has normal sense can not do it Wallahi,yanzu kai ne kadai take sakewa da kai idan ka bari wani abu ya same ka ita kan ta da take a wannan yanayi ba zata taɓa yafe maka ba Suhail haba ". Kara ɗago jajayen idanun sa yayi ya zubawa Uncle Yaqub. " Yes kalle ni da kyau na ce ba zata taɓa yafe maka ba,Suhail dan Allah ka kula da lafiyar ka taka ita zata taimaka mana mu samu ta Ishaaa,domin ka san abinci ma kai ne ka wai ke iya saka ta cin sa ,to idan ka samu rashin lafiya duk wazai yi wannan zata zauna cikin damuwa da rauni na jiki da na zuciya." Miƙewa Suhail yayi yana cigaba da jin faɗan da Uncle Yaqub ke masa na kwance ta. Allura ya haɗa wanda tunda ta hango yana haɗa ruwan ta fara sakin wani Marayan kuka mai tsumaa zuciya tana girgiza kan ta,alamar bata so.Duk yadda yake jin Tausayin ta haka ya cije ya zube mata ruwan nan tare da taimakon Uncle Yaqub ko minti ɗaya bata yi ba kuwa bacci ya kwashe ta wuyan ta yayi gefe. Tare wa yayi ya jinginar da ita ga ban gon yana ƙ ara zuba mata idanu.Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi kafin ya miƙe ya fita tare da abincin da yazo mata dashi dan ya san yau ba za ta iya saka komai ba a cikin ta saboda baccin da zata yi ta yi har wayewar gari,ko kuma tsakar dare.✍️✍️ Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 Book one zai kare a page 50 Dan haka wadda ta shirya sai ta saka kuɗin ta dan babu wanda zamu jira zamu cigaba da wannan tafiya in sha ALLAH.🙏🙏🙏 # _FA'EEH BG CE✍️_ *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣ 4️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ 💕💕💕💕💕 Amoh ce zaune idanun ta sun sauya na Zallar Damuwar da take ciki. "Amoh ki yi Haƙuri kin ga ko ɗazu sai da Yaya Suhail ya ce ki rage ya wan damuwa Bpn ki yana hawa yana sauka ". Ɗan kallon Suhaila Amoh tayi dake maganar kafin ta sauke numfashi ta ce " Suhaila yaushe Ya ta zata samu lafiya,yaushe Auta zata zamo kamar kowa,a koda yaushe ina yin mararin wannan mafarkin sai dai kamar abu ne mai matuƙar wahala,Ya Allah ka yaye wa baiwar ka, ka sa iya kar wahalar kenan,Allah ka bata lafiya ''. Amin Suhaila ta amsa jikin ta sanyaye. " Amoh zata samu lafiya in sha ALLAH,jarabawa ce,Ke kike faɗa mana Allah yana jarabtar bayin sa ta hanyoyi da ban daban lallai mu tamu jarabawar kenan,Allah ya bawa Ishaa Lafiya,ka nuna mana ranar da zamu zauna muyi fira da ita ". Kai Amoh ta girgiza cikin karyewar zuciya ta ce " Amin ". " Allah ya sa " Shigowar Suhail ce ta sanya Amoh zuba masa idanu. Kawar da kan sa yayi daga kallon ta shima yana zama kusa da ita,jikin sa sanyaye. " Ta samu bacci ai " Ajiyar zuciya Amoh ta sauke tana cewa " Allah ya bata ikon farkawa cikin aminci " Amin dukkanin su suka amsa. Uncle Yaqub ne da ya gama

Chapter 34 of 39