Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dake jingine kamar baya numfashi buɗe kyawawan idanun sa masu haske yana sauke su akan Muby ɗin. " Sorry ina gudun rigimar yarinyar chan ne kar mu tada mata da ƙura ya sa na rage gudun motar sai kuma ta nemi kubce mini dole na taka burki da sauri ". Muby ya faɗa yana danne Dariyar sa tuno farkon haɗuwar su da ita.Da mamakin ta gata yar mitsitsiya tana fira shi gaulan sai sakin baki yake yana kallon ta. MAHAJ da bai wani fahimci wace yarinya yake zance ba ya ɗauke idanun sa daga kan sa yana lumshe su kamar yadda suke sai dai kuma jin Muby ya tsayar da motar ya ƙi cigaba da tafiya ne ya sa ya zare space ɗin sa a hankali yana bin Muby da kallo na zargi. Sai dai bai iya yin kallo mai tsawo ba hakan ya sa ya ɗauke idanun sa daga kan sa. Ya ƙara lumshe idanun sa tare da mayar da glass ɗin na sa. Tafiya Muby ya cigaba da yi a hankali yana fatan Allah ya sa idon Mahaj ya kai inda yake buƙata yaga Abokiyar faɗan sa.koda suka gota su ya ji haushi na rashin ganin ta da Mahaj ɗin bai yi ba. Sai dai abun da bai sani ba dai dai sun iso wajen MAHAJ da ya ke ƙara mamakin abinda Muby yayi ya ware idanun na sa da ƙyar ta cikin rado ɗin na sa ta yanda mai zato ba zai taɓa zato ba ya ɗan saci gefe da gefen motar sai dai kamar an ce ya ɗaga idon sa ta gaban su sai gashi ya sauke ganin sa kan ta a hankali kafin Iro,tana ta washe bakin ta abunda bata saba yi ba da kowa idan ba Bibu ba da su Amina. Dan dai dai lokacin ne Iro yake gaya mata Yadda ya yaga bakin Shamsu ya san harda jini yayi. Yana bata labarin yana dariya itama haka dan ta ji daɗi ta ji ƙeta.Aiko Iro sai kallon ta yake yi har ya shagala ganin yadda dimples ɗin ta yau suka wani bayyana haɗe da yar ƙaramar wushiryar ta suka ƙara mata kyau na musamman. Idanun sa ya ɗauke da sauri kamar wanda ya ga kashi dan dukkanin su ya gane su tsaf,kuma idan ba mistake yayi ba abinda Muby yayi,yayi hakan ne dan ya ja hankalin sa.Ƙaramin tsaki ya ja a ƙasan laɓɓan sa wanda shi kaɗai ya ji fitar abun sa. Har suka gota su bai ƙara ko tada kan kan sa ba hasalima idanun sa a lumshe suke. Ita kuwa Shatou haka kawai ta dakatar da dariyar ta tana bin danƙara danƙaran motocin da kallo a hankali kasancewar haka kawai ta ji alamar kamar ana kallon ta ganin bata ganin komai har suka wuce ya sa ta janye idanun ta kan su. Shi ko Iro da ya shagala da kallon ta sai da suka matsa nesa da su kaɗan sannan ya lura da motocin...✍️ Yau dai da alama mutanen zasu ƙara haɗuwa fa 🚴🚴🚴😅 Ohni yar babanta Shatoun ku rigima gare ta.Arado Allah ya sa ta bar mana Mahaj ɗin mu kar ta saka mana ciwon kai.🚴🚴🚴💃💃😂 Page biyu ba haɗe muku na jiya da na yau.🙏🙏🙏🚴🚴🚴 Typing 🥺🥺🥺A samu wata hiliss ta muna typing 🚴🚴 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two and three paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________3️⃣8️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ Not edited😴 _____________ " Lallai fa kamar baƙin nan ne suka zo masu aiki zasu duba aikin ina ga kamar motocin su ne ". Iro yayi zancen yana ƙara ƙure motocin da kallo da suka ɗan yi nesa da su kaɗan kamar zai hango wanda ke cikin motar. Shatou kuwa bakin ta,ta mere bayan ta ɗauke idanun ta daga kallon motocin. Iro kuwa da gama furucin ya cigaba da bata labarin faɗan nasu kafin ya koma bata wani labarin daban.Shatou tayi zaton zai wuce sai dai ta ji ya cigaba da tsiyaya surutu kamar fanfo dan haka tun tana ƙaƙalo murmushi har ta kai ta haɗe fuskar ta dan dole fahimtar hakan ne da Iro yayi alamar ta gaji hakan ya sa ya fara ɗan kame kame yana ƙyafce ƙyafcen ido. Haka ta cigaba da tafiya kafin ta fara zabga sauri tun Iro na cimmata har ya kai tafiyar ta su ta rabu dan ta yi gaba. Kafin kuma ta runtuma a Guje sai kuma ita da kan ta abun ya bata dariya ta cigaba da ƙyalƙyala dariyar ta ita kaɗai tana gudu tana waigen Iro da shima ya biyo bayan ta yana dariyar sa kamar wani wawa yana kiran sunan ta da alamar ta tsaya,sai kayi zaton wasu masoya ne na asali yadda suke yi.Har ta zo ta gota mutanen da ke tsaye gurin bata lura ba duk da ta ji yadda wajen ya gauraye da ƙamshin daddɗan turare. Bata tsaya ba sai da ta tsinci kan ta cikin makarantar sannan ta dakata tana nishi. Malam Bello dake nan yana duba wasu takardu daga tsayen da yake ya ɗago idanun sa ya kalle ta,ganin Shatou ce ya sa ya galla mata harara.Ita kuwa shatou sanda ƙirjin ta ya buga ganin malam Bello dan ta san halin sa duk da haka kuwa ta shanye tsoron ta.Baka taɓa ganewa sai dai idanun ta da take ta ƙyaftawa,alamar rashin gaskiya,dan ta san bata da gaskiya ta yi latti ta san dole zata iya samun hukuncin sa tunda mugu ne. Malam Bello kuwa cike da faɗa bayan gama sakar mata harara,Ya furta " Zo nan " .Babu musu Shatou kuwa ta zo ta tsaya kusa da shi kaɗan tana tura bakin ta gaba ga ƙirjin ta dake bugawa kaɗan na ɗan tsoron bulalar sa. " Uban me ya hana ki dawo wa da wuri har aka shige aji " ? Shiru ta masa taƙi ko ɗaga ido ta kalle sa. Ran malam Bello ne ya ɓaci dan haka ya ce " Sun kuya nan ". Bakin ta, ta ƙara turawa gaba kafin ta kai guiwowin ta ƙasa tana yin kneeldown. Malam Bello yayi zaton ta bashi haƙuri sai dai shiru har bayan ɗan lokaci hakan ya ƙara tunzura shi dan haka ya ƙara sanya ta ɗaga hannuwan ta sama tare da rufe idanun ta. A ɓangaren shatou ƙafafun ta sun fara ciwo matuƙa amma saboda taurin zuciyar ta kasa ce masa yayi haƙuri. Ga wata zuciya da take jin tana ta so mata kamar ta miƙe ta yi gida,taana ji duk wanda ya tara ya samu. Kuma ta sha alwashin ba zata taɓa bada haƙuri indai har malam Bello ne. A ɓangaren su MAHAJ kuwa suna zuwa bakin inda aka gina ruwa tare da sanya manyan tankuna na ruwa da ake akan aikin su, nan suka dakatar da motocin na su.Da ƙyar uban gayyar ya fito daga mota. Ko shi sai da ya gama shan ƙamshin sa sannann ya fito yana gyara zaman p cap ɗin sa da ya juyar da ita. Bakin motar da ya fito ya jingina bayan sa yana ƙare wa wajen kallo da sauran filayen ƙauyen dake zagaye da wajen. Bai ɗaga daga nan ba har su Muby suka fara zagaya wajen. Tare da jama'ar garin da suka ɗan taru a gurin,suna satar kallon MAHAJ ɗin da gaida shi wanda sai dai ya ɗaga musu hannu kawai fuskar sa sanye da glass ɗin sa da yake ta ƙara yiwa kyakkyawar fuskar sa armashi. Mafi yawan jama'a sun bi bayan Muby da yake duba ayyukan dan ogan ya gincire anan ya ce su je kawai. Yana ɗan ganin komai daga nesa. Sai ya zamo daga shi sai masu tsaron sa aka bari sai yan tsirarun mutane da ke bin sa da kallon ƙurilla. Da kallon ya ishe sa sai ya juyar da jikin sa yana facing motan tare da ɗaura hannuwan sa jikin kan motar yana jan ƙaramin tsaki.Na kallon da yake jin ya dame sa dan shi mutun ne wanda ya tsani a yi masa kallon da ya wuce ɗaya ya tsani kallo yana daga cikin abinda ke takura masa. Ya ɗan daɗe tsayen inda a hankali a hankali yake jan tsakin da bai san dalilin jan sa ba yanzu ga idanun sa da suke a lumshe ta cikin space ɗin. Gajiya da tsayin da yayi ne abun ka ga ɗan Hutu ga yar ranar da ta fara yin zafi da haske tana kasar masa fata hakan ya sa ya juyo a hankali da niyyar komawa cikin motar da bawa masu tsaron na sa umurni. Ɗan kallon gefen sa na dama yayi a hankali sai dai kamar haske hakan ya hango ta tana falfala gudu kamar wata balbela,Bakin ta sake tana dariya,Sai ga Iro bayan ta shima yana dariya kamar wani wawa. Kallo ɗaya dukkanin su yayi musu ya ɗauke idanun sa yana yatsine fuskar sa kamar wanda ya ga kashi da jan ƙaramin tsaki da ya tsaya iya laɓɓan sa. Hakan ta wuce a Guje kuwa ta gaban su ba tare da ta kalli ko ɗayan su ba kasancewar hankalin ta ba nan yake ba kawai ta tsinci kan ta makaranta take buƙata dan ta san ta yi lattin dawowa sannan bata son wanchan nataccen ya ƙara tsayar da ita,dan ita kaɗai ta san yadda ta ji tsayuwar dashi mugun Haushin hakan take ji bata da yadda zata yi ne dan hakan kawai take ganin mafita wa kan ta. Ta ƙasan ido ya bi ta da kallo bayan shuɗawar ta gaban sa. A jiyar zuciya ya sauke da numfashi na gajiya da tsayuwar sa kafin ya buɗe seat ɗin baya da kan sa ya shige motar ya rufo murfin yana sauke numfashi tare da jingina bayan sa da seat ɗin sa, p cap ɗin da ta yi wa lallausan gashin kansa mai taushi rumfa ya cire ya ajiye gefe ya zamo kyakkyawar fuskar sa ta bayyana gaba ɗaya.Wadda take ɗaure kamar wanda bai taɓa koda murmushi ba bare dariya. A hankali ya duba wristwatch ɗin sa mai tsada da kyau ya ɗan kalla a hankali wanda ke ɗaure akan tsintsiyar hannun sa,Kallo ɗaya yayi ya ɗauke idon sa yana jan guntun tsaki,ganin lokaci ya ɗan ja. Bai jima da shiga Motan ba sai ga Muby da Sauran jama'ar. Shisshiga motar su kayi babu ɓata lokaci dan ya san ogan na sa a cike yake dan bai son jira ko kaɗan duk da aikin sa ne ya bar masa. Sannan haka kawai zuciyar sa ke ayyana masa MAHAJ ya ga wucewar Shatou da jelar ta da ya dakata daga nan. Motsin sa ne ya sanya MAHAJ dake zaune shiru kamar kurma ya ɗan buɗe manyan idanun sa dake cikin glass ɗin kafin ya ƙara rufe su. Shiru ne ya ratsa domin kuwa Mubarak ya san cewa ya na jin sa yan ikon ne ke kai dan haka yayi shiru shima yana ɗan satar kallon sa ta madubi tare da nazartar yanayin sa sai dai bai gane komai ba daga abinda yake son gani saboda Glass ɗin da yayi wa kyakkyawar fuskar sa kawanya. " Idan ba zaka iya driving ɗin ba let me take over " Maganar sa ce da Mubarak ya tsinkayo cikin natsuwa hakan ya sa ya ɗan juya ya kalle sa kafin ya furta " Zamu shiga waccan Makarantar ".Kafin ya tada motar dama already sauran na gaba sun tada na su. Har suka ɗaga daga wajen bai cewa muby komai ba. Shi ma kuma muby bai ƙara cewa komai sai dai nanata Muryan da ta fitar da sautin maganar sa ta ƙarshe yake yi da amon ta saboda son gano ƙwaƙƙwafi da wani hange na sa da yayi da bai san ma yadda hakan zai iya faruwa ba. A ɓangaren shatou kuwa haka ta kasance a wajen saboda taurin zuciya duka malamai sun taru kan ta ta bada hakuri ta ƙi dan shi ya ce da ta bada hakuri ta amsa tayi kuskure zai sake ta. Baiwar Allah fuskar ta tayi jaaa na wahala ga ƙafafun ta da hannuwan ta sun yi mugun sanyi da ciwo na gajiya. Suna hakan kuwa sai ga motoci sun fara kutso kai ta cikin makarantar sai dai daga Gefen sabon ginin da ake musu domin kuwa kwangilar ta koma ta sababbin building bata renovation ba wannan kuma duka aikin MAHAJ ne shi ya bada umurnin hakan sai dai Abbu ya hana ya shiga aljihun sa dole sai nasa dan haka dole ya amince aka shiga ƙarƙashin aljihun Abbun badan ya so ba. A wannan karon bai wani jima ba ya fito da kan sa bayan buɗe masa motar da muby yayi domin kuwa yana son ganin yadda aikin ke tafiya. Da p cap ɗin sa ya fito a hannu kafin ya ɗaura ta akan sa muby kuwa ganin yadda yake ta yatsinar fuska saboda ranar da ta buɗe ne ya koma cikin motar ya ciro lafiyayyen umbrella ta kare rana ya buɗe masa. Jin yadda ranar ta sauka daga kusa dashi ne ya sa ya ɗaga kan sa ganin lema ruƙe hannun muby ya sa shi ɗan ƙare masa kallo kaɗan ta cikin glass ɗin da muby ke ta Allah Allah ya cire sa ƙwayar idon sa yake son gani fili. Idanun sa ya lumshe a hankali yana ware su wanda shine ke nuna alamar yaji daɗin abun da muby din yayi kuma hakan godiyar sa ce ya nuna masa duk da kula da shi aikin sa ne alƙawarine da yayi Abbu har gaban abadan. A hankali suka fara zaga wajen ma'aikatan wajen na na gayar da shi yana gyaɗa musu kai kamar ƙadangare,wasu kuwa ɗaga hannu,wasu ma idanu kawai yake lumshe musu sai kayi zaton wulaƙanci ne ma. Wata dai ta ce haushi kake bata my crush 🙄😏🚴 Kar ku man ta kuna karanta littafin KURMAN ƘADDARA ne tare da Marubuciyar ku ta amana fa'i.💕✨ Kar ku yi sanya wajen BIBIYAR wannan labari dan samun warwaran zare da abawa,wannan tafiya, tafiya ce mai cike da abun burgewa, Soyayya, ƙauna,darasin rayuwa. ______Kafin su gama zagayen kuwa mai gari ya iso wajen bayan samun labarin zuwan su daga Iro da wasu daga cikin mutan gari dan haka ya saɓo babban riga daga Majalisa suka yo nan. Haka ma malaman makarantar su shatou suma rabi da kwata duk sun yi gefen,ayi komai gaban su musamman da kowa ya san MAHAJ ɗin na raba kudi dan ko wancan zuwan ya kashe kuɗaɗe haka ya damƙa su ga muby yabawa malamman su Shatou suka raba da wasu daga cikin jama'ar da suka dabaibaiye sa.duk da basu san asalin wanda ya zo ba amma suna fatan ya kasance shi ɗin ne.Dan haka wajen yake ta cika dan sai yanzu wasu da suka samu labarin abinda yayi wancan zuwan suke samun labarin zuwan sa. Sun zagaya ko ina a gajiye ganin ko ina yayi masa yadda ya ke so ne ya sa yayi ce su tafi yanayin sallama da mai gari dake ta washe baki kamar gonar aufiga Sai Iro biye dashi kamar jela, shima na sa bakin washe. Suna gama Sallamar da mai gari da yake ɗan bawa amsa da ido sai ya juya ya shige motar sa. Muby ma shigewa yayi wanda yayi ɗan jimm yana kallon tsakiyar makarantar ta su Shatou hango yarinya tayi kneeldown Haka kawai zuciyar sa ke ayyana masa itace dan ya sa halin ta da rigimar ta. Sanin halin uban gidan sa ne ya sa ya faɗa mota yana girgiza kan sa.Sai dai Har ya shiga ya kasa share zancen dan haka bai cewa MAHAJ komai ba dake pressing phone ɗin sa a yanzu karo na farko tun fitowar su wanda koda ya ji fitar muby sarai amma ko ɗaga kan sa bai yi ba. Cikin yar Sassarfa ya matsa bakin inda malam Bello yake. Ban san abinda ya yi wa malam Bello ba chan na hango sa yana wasar baki kasancewar gefe ya ja sa suka yi magana tare jin bahasin abinda tayi domin kuwa bayan zuwan sa wajen ya ƙara tabbatar da ita ɗin ce dai kamar yadda ya zarga duk Tausayin ta ya kama sa gashi basa shiri a uban gidan sa bare ya ce ta zo a kai ta gida sabida ƙafafun ta da suka yi sanyi ga gajiya.✍️ Babu ƙorafi😂😏😂Yau har sai an gaji da karatu page ya cika.🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________3️⃣9️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ ✿⁠☉☉✿⁠☉☉✿⁠☉☉ Godiya malam Bello yake masa kamar zai duƙa masa bayan jin hannun sa da ya damƙa masa kuɗaɗe a cike. Wajen ya bari cikin Sassarfa yana komawa cikin motar. Shi ko MAHAJ tun bayan shirun da ya ji bayan fitar Mubarak yake ta mamakin inda ya je tunanin abinda ya fita yi ne bayan ya san sun gama abinda zasu yi hakan ya sa ya a jiye wayar sa a hankali ya zuba ma mirror ido kasancewar yana facing ɗin su Mubarak ɗin dan haka ya hango sa dai dai lokacin da ya damƙa ma malam Bello kuɗaɗe. Idanun sa ne suka ƙara sauka a kan yarinyar dake duƙe ta ɗaga hannayen ta sama ɗan luuu yayi da idanun sa bayan ya ɗan zuba mata idanun sa. Kan sa ya mayar yana jingina da bayan sa tare da jan guntun tsaki na mamakin Gulmar da ta fitar da muby ɗin. Mubarak kuwa yana shiga motar ya rufe ba tare da ya kallo mahaj ba ya tada motar suma sauran motocin na su suka tayar. Tafiya suka fara yi a hankali ɗan satar kallon sa Mubarak yayi ta madubi ganin ya buɗe idanun sa dan ya zare space ɗin yanzu.Waje ɗaya ya ga ya zuba ma ido kafin a hankali ya lumshe idanun sa yana jan ajiyar zuciya a bayyane. Buɗe idanun sa yayi a hankali kafin su sauka akan na muby da sauri kuwa ya janye na sa yana furta " Tuba nake yallaɓai "Wani Shegen kallo yayi masa ya ɗauke idanun sa yana shigewa cikin seat tare da rufe idanun sa. A jere motocin suka cigaba da tafiya sai dai sun ɗan yi tafiya kaɗan mai gari ya dakatar da su ta hanyar ɗaga musu hannu. Glass Mubarak ya sauke a hankali yana sakin murmushi cike da murmushi mai gari ya roƙi alfarmar da su je fadar sa su karɓi saƙon Abbu.Babu musu kuwa suka juya aka lar motocin na su kasancewar ya san fadar.Shidai gogan bai ce komai ba yana hakimce a bayan motar bai ce ƙala ba duk da ya ji komai.Har suka iso fadar mai gari idanun sa a lumshe suke kamar mai bacci sai dai ba baccin yake yi ba. A ɓangaren Shatou kuwa malan Bello na barin wajen Muby ya koma wajen ta bakin sa washe ya ce " Shatou tashi kin ji ai ban san kina da ƙashin arziki haka ba ". " Kuma ba zan kasa faɗa Miki ba ki rage wannan taurin kan ba dan da ban samu masu gidan rana ba sai kin kai maraice haka ". Yana gama furucin sa ya kama hanyar ɗan office ɗin su. Shatou kuwa da take jin sa da sauraren ta wadda ke sauke numfashi a hankali cike da wahala ta sauke hannayen ta jagab tana shanye wasu hawaye da suke son Silalo mata na azabar da hannuwan ta suke yi da ƙafafuwan ta da jikin ta ma baki ɗaya. Zaune ta kai kasancewar ta kasa miƙewa dan har juwa juwa take gani bayan buɗe idanun ta da suka ɗan sauya kasancewar har da su yace ta rufe daga baya. Hawayen da take ƙokarin riƙewa ne suka Silalo mata wanda ta kasa haɗiye su share su tayi bayan ganin gari ya washe mata dan buji buji take gani a idonta. Ta ɗauki kusan mintuna huɗu babu wanda ya ce mata ƙala domin kuwa Dukkanin su suna chan wajen rabon kuɗin da Mahaj ya sanya wani daga cikin masu kula dashi ya basu a matsayin wata yar sadaka nan da ya saba ba su. Ta jima zaune ta haɗe rai tare da miƙe ƙafafun ta sai da ta ji sun sake mata sannan ta miƙe tana ƙara haɗe duk wani annnurin fuskar ta saboda yadda ta ji Haushin abunda take ji da wahalar da ta sha. Sai dai tunanin zantukan malam Bello da yayi bai bar kan ta ba saboda mamakin abinda ya sauya shi. Ajin su ta faɗa babu ko sallama ana tsaka da musu karatu. Ganin yadda ta galabaita ne malamin da ke karatu baice mata komai ba. Dan haka kai tsaye kujerar su ta nufa su Amina dake Binta da ido cike da tausayi suka matsa mata ta zauna. Har aka tada su bata cewa komai ba dan yau ma da wuri aka tashe su saboda masu aiki da zasu duba makarantar da tsarin ta zasu yi aune aune. Dan haka sha biyu na bugawa dot aka ta she su. Koda aka tashe su kuwa shatou fuskar nan a haɗe take sai dai ba irin yanayin jiya ba daka kalle ta dai kasan a galabaice take sannan kuma masife take saboda jira kawai take yi wani ya taɓa ta cikin yara ta sauke masa. Su Amina kuwa zagaye ta suka yi suna bata haƙuri sai dai babu wanda ta tace wa ƙala sai ma idanun ta da suke ɗan walƙiya alamar ruwan hawaye. Hanya suka kama suna tafiya a tare kamar an musu mutuwa.Bibu ma shiru yayi cike da tausayin yar uwar sa. A ɓangaren Su MAHAJ kuwa fadar mai gari sun isa lafiya inda suka tsaya jiran isowar dafaffiyar madara da zuma da bata iso ba.Domin kuwa sha tara na arziki mai gari yayi musu da nufin saƙon Abbu.Sun jima bakin fadar mai gari domin Mahaj yaƙi fita daga motar muby ne kawai ke ta godiya ana sakawa mota da taimakon sa. Koda Baffa na ya kawo zuma sanya wa aka yi kasancewar ita kawai ake jira dafaffiyar madarar an kawo ta daga gidan mai gari. Isowar Baffa na wajen ne ya sanya MAHAJ ɗan sauke space ɗin sa kasancewar Muby ya shiga Mota zasu tada motar bayan saka komai.Lafiyayyen shanu ne Baffa na ya miƙa wa Muby a cikin wata tsaftatacciyar jarka, ta glass ya miƙa masa fuskar sa cike da murmushi bayan ya ɗan ƙare ma bayan motar kallo dai dai kuma lokacin da Mahaj ya cire glass ɗin sa ɗan satar kallon sa ya yi kafin ya janye idanun sa daga kan sa yana rufe idanun sa ruff. Yana ji koda Baffa na suka yi sallama da Muby cike da girmamawa. Sallama suka yi musu kafin suka bar fadar har zuwa lokacin kuma MAHAJ bai ƙara ko dogon motsi ba hasalima baccin gajiya ne ke ɗan fizagar sa. Su Shatou kuwa rabuwa suka yi da su Amina bayan sun kawo hanyar da kowaccen su zata je gida.Sai ya zama na daga Bibu sai Shatou kuma shine yake ta rarrashin ta yana bata baki dan sai cika take tana batsewa,ga kyakkyawar fuskar ta tayi jaaa na azaba da hasalar da take ciki. Tun daga nesa ya hango ta tare da yaro mai kamar sa,ar ta dan haka suna kusa isa inda suke kasancewar yar guntuwar hanya ce dole sai ta inda suke zasu bi. Horn muby ya fara buga musu a hankali yana murmushi. Sai dai Ko waige bata juyo ba Bibu ne ma kawai ya matsa yana cewa itama ta matsa su wuce kar a taka ta tunda sun san mutanen birni. Tafiyar ta ta cigaba da yi kamar bata ji ba duk da kuwa sai nanata wa yake yi kuma ya san tabbas tana jin sa sarai sanin halin ta ya sa bai damu ba. A ɓangaren Shatou kuwa zuciyar ta ta kawo wuya a hasale take matuƙa dan haka take jiran taga Wane isasshe ne zai nuna musu mota yake tuƙi ya cika mata kunne kamar wadda ta cika masa hanya. Mahaj kuwa tun da sautin ƙarar horn ɗin ya fara damun sa yake ta faman ya mutsar fuska sai dai bai ce komai ba. Jin Muby ya ƙara yin wani horn ɗin ne ya sa shi buɗe idanun sa yana sauke kallon sa akan glass ɗin motar da suke ganin komai tarr zuba mata lumsassun idanun sa yayi wayen da suke narke kullum kamar mai jin bacci.Kallon yan daƙiƙu yayi mata yana ɗauke kallon sa daga kan ta yana jan guntun tsaki kamar yadda ya saba. Sai dai tsakin na sa ya fita

Chapter 31 of 39