ya jita kamar yadda itama bata zaci jin bulalar ba.Iro dai da ya ga Kamalu ya riga ya gama aikin da bai bashi dama ba hakan ya sa ya kakkaɓe ƙasar da ta gama musu wanka da ita wadda ya cire ta idanun sa da ƙyar sannan ya ce " muje kamar baƙin nan sun shigo fa " Yana yi yana kallon suturar jikin sa da tayi buɗuɗu.Yana ma tunanin yadda zai je wajen haka yaron nan ya masa kallon banza.Basu kula Shatou dake Masifa ba tana Allah ya isa kuma yanzu yanzun nan sai ta je ta samu mai gari da cin fuskar da suka mata bata musu komai ba dan ta riƙe shatin bulalar da ya ɗan kwanta mata.
Basu kula ta ba suka miƙe hanyar da suka ga baƙin motocin nan sun wuce saboda inda za,a fara aikin ne yau ne ranar ƙaddamar da shi.
Ita ko shatou cike da masifa ta miƙi hanya bata zame ko ina ba sai fadar mai gari sai dai ta tarar da ya tafi chan gurin dan haka ta nemi ƙofar gidan na sa ta zauna tayi zaman nan na duk wanda ya tara ya samu dan jira take wani ya mata ko kallon banza ne ta masa rashin mutunci.Kamar ko sauran ya yan mai gari sun sani duk wanda ya zo da yayi mata kallo ɗaya ya shigewar sa gida Mutun ɗaya ne Abu shine ya tsaya tambayar ta me take yi zaune cikin wannan rana.Sai dai kamar yadda bangon da take jingine da shi ba zai iya magana ba haka itama bata tanka masa ba.Yar ƙaramar dariya yayi kawai ya shige cikin gida dan ya san ɗayan biyu baza a rasa da wani a gidan take rigima ba ko Zaidu ko Iro da ya rasa dalilin da ya sa yake biyewa yarinya yar firit da ita amma ya biye mata shi idan shine da tuni ya fita iskan ta.Dan shi Mutun ne mai daraja mutane ba halin su ɗaya da Iro ba da Zaidu dan ko Iro rashin jin na sa sai ta kama yake yin sa ko ta Shero masa.
A dai dai lokacin da SHATOU take ƙara cika tana batsewa kuma alokacin ne aka ƙaddamar da fara aikin Gina manyan bohole da kuma fanfuna tare da aikin makarantar su Shatou.
Cike da farin ciki mai gari ya kamo hanyar gida tare da jama'ar sa tare da manyan motocin nan a bayan su saboda yadda mai gari ya Matsa da akwai babbar kyautar da zai basu dan haka babu musu Abbu da ya samu zuwa yau ɗin saboda MAHAJ ya koma schl akan wani uzuri na gaggawa shi ya sa bai samu dawowa ba dole Abbu ne ya gabatar da aikin cike da farin ciki da alfahari.
Isowar su gurin ya bawa jama'ar dake tare da mai gari gyara wajen shimfiɗar cike da farin ciki dan abu ne da basu taɓa tsammani ba domin sun ji farin ciki sosai ba,a taɓa samun wani mai muƙami da ya kula da su ba kamar sa,koda suka kai koken na su ba suyi tunanin zai karɓu ba dan suna ɗan fama da matsalar ruwa kaɗan saboda a rafi ake ɗebo su kuma bohole ɗaya da suke da ita da wata ƙungiya mai zaman kan ta ta gina da daɗewa itama bohole ɗin sai a hankali Saboda ya tsufa kun san halin ƙarfe da ta tsufa sai dai a yi ta haƙuri.
Sai da duk suka Zazzauna masu zaman gurin yan fadar sa sannann aka fara jawabin godiya tare da fito musu da ƙwaryan Nono mai kyau,da zuma da duk wani kalar abu da ake samu a ƙauye,Zuma ta fito daga wajen Baffa na ne saboda ya san inda ake samun zuma dan haka ana samun mai kyau a wajensa saboda haka mai gari ya masa magana da wuri dan haka aka tana de ta mai kyau da ita da uwar saƙar ta babu haɗi.Haka aka jere Musu su cikin boat ɗin motar da Abbu yake ciki.
Ganin irin kayan da aka fito da su ne ya sa Abbu fitowa daga cikin danƙararriyar motar ta sa da ya ke hakimce a bayan ta.Cikin wata dakakkiyar shaddar sa fara da ta ƙara fallasa asalin kalar fatar sa,Shaddar sa sai maiƙo take yi, ya fito yana zuba ƙamshi fuskar sa cike da murmushin da ke nuna farin cikin sa da kuma kasancewar sa mutun mai sanin darajar ɗan Adam da girmama sa bai ji Dar ba ya nemi waje tare da gyaran babbar rigar sa ya zauna hakan sai ya ƙara masa ƙima a idon al ummar garin.
Godiya ya fara yi musu da karamci su cike da farin ciki.
Sai dai me kamar Shatou jira take yi ya sauke zancen sa,dan bata tsaya tantance mai maganar ba ma ta ce " Baba Mai gari ina da magana ".Tsit wajen yayi jin yar ƙaramar Muryan ta dan babu wanda ya lura da ita a wajen dan har Baffa na na wajen saboda suna cikin manyan ƙauyen.
Zuba mata idanu yayi kasancewar bai san da ita wajen ba dan mutane sun rufe ta saboda taron harda ƙananan yara da suka biyo motocin cike da burge wa.
Kallon ta mai gari yayi jin yau har da Baba mai gari ake kiran sa dan haka yayi murmushi yana fatan ba rigima ta kawo ta ba.
" Ina jin ki SHATOU "
Magana ta fara " wallahi su iro ne suka ci zarafi na shida abokan sa kuma ban musu komai ba,kuma wallahi sai an rama mun idan ba haka ba kuma wallahi ban yafe musu ba wuta balbal" Kuka ne ya ci ƙarfin ta hawaye suka wanke mata fuska kowa dake wajen kallon ta yake yi kowa na son tofa albarkacin bakin sa sai dai mai gari bai bada damar hakan ba.
Babu wanda ya dakatar da ita daga kukan har sai da ta dakatar da abun ta sannan ta yi shiru.
" Ikon Allah ke ko Shatou bugu dai,dame suka buge ki,sannan dawa dawa aka yi aikin,faɗa mini su yan zu su ji hukunci,dan lalle tabbas basu kyauta ba "
Mai gari yayi zancen cike da nuna alhini sai dai a kasan zuciyar sa dariya abun yake bashi shi har ya gaji da case ɗin ta.
" Kamalu ne sauran kuwa dariya suka dinga yi mini kuma bai bani haƙuri ba dan haka bulalar zasu nemo Nima na rama,dan da bulala ya dake ni,kama ga inda suka buge ni nan har an fasa mini naman jiki na,harda jini gashi jini na litre kusan biyar ya ƙare kwanan baya,duk ya tafi saura kaɗan gashi kuma sun ƙara zubar mini da abu na ".Ta kai ƙarshen zancen tana sakin kukan sangarta.Dariya wasu daga wajen suka fara dan abun ma na dariya ne,wai sun ƙarar.mata da jini.Mai gari murmushi ya saki cike da basar da dariyar da yake son yi ya ce " Subhanah har da jini suka zubar miki muga inda ya zuba ".
Hannu ta miƙa masa inda shatin bulalar ya zauna kaɗan shima sai ka matsa ne sosai zaka iya gane shatin dan ma tana fara ne shi ya sa wajen yayi jaa kaɗan.
Kai mai gari ya jinjina cike da alhini harda ɗan rufe ido kamar irin ya ga inda jinin ya zuba alhalin babu alamar gurin ya zubar da jini.
" Ka gani ko,Wallahi sun zalince ni matuƙa dan haka nake son ka bi mini haƙƙi na ".
Ta kai ƙarshen maganar tana share ƙwalla .
Baffa na da ke zaune a nan kaɗan da ita ya sauke numfashi yana ɗauke idanun sa akan ta cike da wani irin Tausayin ta dan ya san tunda tace an dake ta yi anyi ɗin.
A yanzu mai gari Baffa na ya ɗan kalla kafin ya ce " Kamalu me ta yi maka " Bayan ya kallo gefen da suke cirko cirko.
Tsaf suka kwashe komai suka faɗa masa,har kasar da ta musu wanka da ita wanda ga alama nan kowannen su bususu babu ma kamar Iro da kamalu da idanun sa suka yi jajizir saboda ƙasar da ta shiga cikin su dan har yanzu yana jin ta sai zuji suke masa yana jin ƙasa na ɗawafi a cikin idanun.Ƙare musu kallo yayi ga dariya babu halin yi.
Kanta ya dawo tambayar Dalilin da ya sa tayi musu hakan cike da wani irin mugun Haushin su har mai gari ta zayyane masa komai ƙarshe ta kasa faɗin sunan da ya saka mata aka yi aka yi ta faɗa ta kasa faɗa.
Sai Amina ce aka tambaya da suka zo wajen ba da daɗe wa ba ta sanar da mai gari.Nan take da wasu suka dinga dariya shi kan shi mai gari yayi dariyar sunan babu halin fitar da dariyar sa,dama kowa yana son darawa su Iro da ita kan ta uwar kawo ƙaran.
" Yanzu kin san abun da za,ayi zan hukunta su da hannu na,tun da har kin rama Kinga ko hakan nan ai kin rama abun da suka Miki,duba yadda kika mai da su kamar kuran daji, ".Ya kai zancen ƙarshe fuskar shi da ɗan murmushin " kar ki damu,na fahimci gaba ɗaya laifin Iro ne dan haka da kaina zan rama Miki bugun da suka miki,ba sai kin wahala ba har ki ƙara zubar da jinin ki,ayi haƙuri Hajiya Shatou,ƙasar nan ma hukuncin ta yayi "
Ya kai ƙarshen zancen yana sakin ɗan murmushi.
Ita kuwa SHATOU wani gingiririm kan ta yayi mata cike da jin daɗin har da Hajiya yau ta samu sunan da ake kiran yan birni da shi dan haka ta ce " A ƙara masa kashe di da zugar abokan hi dan Wallahi suka ƙara shiga gona ta sun san sauran sai na musu abun da basu zata ba " Dai dai ta gama furucin idanun ta suka faɗa a cikin na Baffa na.Baki ta tura gaba tana ƙyafƙyafta idanun ta.Alamar rashin gaskiya da kuma mamaki.A hankali ta fara bin sauran jama'ar dake wajen.Dai dai ta tsaida kallon ta kan Abbu da yake ta sakin murmushi tun lokacin da ta fara magana ya zuba mata idanu kamar ya samu tv wani irin lamari mai girma na ɗarsuwa a cikin zuciyar sa akan SHATOU.
Murmushi ya sakar mata mai sanyi ganin yadda ta zuba masa idanu kafin ta sauke kallon ta kan Mubarak da ke ta sakin murmushi shima dama ya hango ta ɗazu da suka shigo sai dai bai yi zaton faɗa ake yi wajen ba yayi zaton ma taɗi ne suke yi irin na ƙauye tunda ya san da wuri suke yi wa ya yan su Aure daga Mazan har mata.Samun kan ta tayi da mayar masa da murmushin,tana mayar da idanun ta kan Mubarak karo na biyu kafin ta galla masa harara dan tsaf ta gane sa, idanu ta ɗan ƙara warewa ko zata hango uban gidan na sa da ta tara kalolin masifar da zata masa sai dai babu alamar sa a gurin fahimtar hakan ya sa Mubarak Shafa kan sa cike da murmushi ya girgiza mata kai.Harara ta ƙara jefa masa duk da cewa ta fahimci abinda yake nufi ɗin.Ita koda ta ga manyan motocin bata san sune suka dawo ba.A zaton ta wasu baƙin aka yi daban dan bata ji zancen ba ko ga su Baffa na ne saboda kwana biyu tana samun yawan bacci tun fara yin al'adar ta dan ko fita rage yi tayi.Koda taji Iro na maganar baƙi sun zo ta yi zaton sababbi ne ashe sune dan sai yanzu ma da ta ga Mubarak ta ƙara tuna cin kashin da take faɗa ya mata,dan kwana biyu ta watsar da shi da lamarin sa,sai dai ta daɗe tana tsara irin abun da zata masa na ramuwa a,a chan farko har bacci ranar da aka yi abun bata yi ba,kusan kwana uku,a cewar ta ai ko Dagaske shi ɗan gidan elibabeth ne sai ta rama sai dai ya tarkato dangin sa turawa ayi faɗa dan ita da Bibu da Baffa na sun ishe su.
___________Hoo uwayen rigima🤭🤣
_FA'EEH BG✍️_
~👑GTW👑~
________Kallon ta yake ƙarayi ganin ta yar cukur da ita kamar ka hura iska ya kwashe ta,gata ba wani tsawo ba.
Hannun rigar ta sai faɗuwa yake tana mayar da abun ta dan mayafi ne hannun a jikin ta,dan haka aka dawo dashi a hannu kun san dai irin shigar mu ta ƙauye duk da haka dai ita taɗan banban ta dasu dan babu ruwan ta da wannan damɓare damɓaren powder da su Ramata suke yi da Sauran ƙawayen su dan itama Amina tana shafawa sai dai ba kullum ba.
" Daga yau Iro,Kamalu,Rabilu,Saminu,Dauda .... Babu ruwan ku da shiga sabgar Shatou kun ji na na faɗa muku ko,dan na fahimci cewa kune baku da gaskiya,kun ji ko,maganar wankan ƙasa da tayi muku kuyi haƙuri kun Kaita ƙul kar wanda ya ƙara saka mata hannu da sunan bugu ko ba ita ma ba kar ku ƙara bugun wata a ƙauyen nan."
Maganar mai gari ta dawo da hankalin ta kan sa tana cire idanun ta daga Mubarak da take ta aikawa da harara kamar taga uban gidan na sa shiko sai murmushi yake saki abun sa.
Haka ma Abbu sai kallon ta yake yi ya kasa miƙewa su wuce har yanzu mamakin ta bai bar sa ba na yadda take ta zance haka kamar wata babba kuma.dudu shi gani yake Bama zata wuce shekara goma ba,idan ma ta kai su.
Allah Abbu idan ta jika kana kiran ta Yar goma zaku yi rigima,da ka san rigimar da ke tsakanin ta da ɗan ka hm🚶🤣
Kai su Iro suke gyaɗa masa kamar ƙadangaru,sun kasa iya furta komai kamar an musu dabaibayi, ga mamakin munafurcin yarinyar da suke yi dan haka suka ƙara kullatar ta azukatan su sai dai shi Iro wani lamarin ne yanzu da ban a cikin zuciyar sa wanda ya fi na baya kamar yadda dama chan yake ƙoƙarin ganin ya cusa kan sa gare ta,sai abun ya ƙara zama mai girma gare sa dan haka ya amsawa mahaifin na sa anatse babu wata damuwa akan fuskar sa,kamar bashi ba.
Suko cike da hasala suke kallon ta suna jin ina ma da wuta su kaɗa ta su huta ta zamar musu ala ƙaƙai yanzu ko an zo wajen mai gari ita ake bawa gaskiya.Musamman ma Kamalu.
" Kema Shatou ki daina shiga sabgar su kinji ko,mace kike bai kama ta kina biye Musu ba,idan sun ja ki kawo mini ƙara ko bama su bane,ki bar ɗaukar hukunci da kan ki kinji ko "
Kai ta gyaɗa masa cike da sanyin da jikin ta yayi saboda tana jin idanun Abbu akan ta,idanun da ta ke hango su sak na mutumin da ko sunan sa bata sani ba,Dan haka take jin cewa da alama suna da zumunci tunda ta gan shi shima tare da Mubarak ɗin.Ƙila ya'yan shine ta ayyana aranta.
Kafin ta kalli mai gari ta ce " Ai dama Ni babu ruwan na da su dama Inna ni tace na daina kula kowane namiji idan ba Baffa na ba ko Bibu,A yanzu ma nan sauri nake na fita gurin nan ".
Murmushi Mai gari yayi yace " To Allah ya sa mudace kinji A kula sosai,Banda faɗa kinji nida kaina zan yi Miki maganin su "
Kai ta gyaɗa masa kafin ta fice daga wajen.
Chan ta ɓulla inda zata iya ganin Baffa na da kyau ta Kalle shi cike da murmushi kamar ba ita ta gama kuka ba ta ce " Baffa na, na jira ka,ko na wuce wa ta,?."
Zuba mata ido Baffa na yayi ganin Dagske amsar tambayar take nema dan haka ya samu kan sa da sakin Murmushi yana girgiza kan sa.
Sannan a hankali cikin sake fuska ya ce " Shatouwa Ai ba tare muka zo ba,ki tafi kawai ".
Baki ta tura gaba kafin ta ɗan saci kallon gefen da Su Abbu da Mubarak suke tare da masu tsaron sa da suke zagaye da gefen na su kamar jira suke yi,suma securites din kowannen sa fuskar sa babu annuri kamar dai yanayin masu kula da MAHAJ ɗin.
Murmushi ta mayar ma da Abbu cike da wani irin yanayi da kallon na sa ke sakata dan sai taji guiwoyin ta sun riƙe.Shi ko Mubarak Wata Hararar ya ƙara samu.Juya wa tayi ta kalli Gefen da su Amina,ramata,Jawairiyya,Ta banka musu harara kamar idanun ta zasu zube sannan ta yi gaba abunta tana tsalle tsalle.
Idanun sa ya sauke yana girgiza kan sa kaunar yarinyar na ƙara samun waje a cikin zuciyar sa natsuwar da ya hango ta ɓoye ya ke ƙara jinjina da kuma baiwar hankali da take dashi a yan shekarun ta na ƙuruciya.
Hmmm Abbu ina hankali anan🤭
Mai gari ma murmushi ya saki kafin ya maida kallon sa kan Abbu yana bashi haƙuri tare da ƙara yi masa godiya.
Abbu kuwa cike da murmushi yayi musu sallama bayan ya miƙe yana ƙara gyara zaman Babbar rigar sa.Ƙarewa Baffa na kallo yayi kafin ya miƙa masa hannu kasancewar duk haka yayi musbaha da yan majalisar..
" Baffa na,Ina ji kamar kabar mini yar nan taka,na tafi da ita, tana da abun dariya da bada nishaɗi"
Murmushi Baffa na yayi kafin yace
" SHATOU haka take Ranka yadaɗe ƙuruciya kowa da irin ta sa,ita haka Tata take,ai kalar mu ce ba zaka iya da rigimar ta ba "
" Haka ne lallai ita Tata mai kyau ce kamm dan tana da hankali,da tarbiyya,ina son yaro haka mai sake wa da ƙarfin guiwa "
Murmushi Baffa na ya ƙara saki karo na biyu kafin cike da jin daɗin yabon irin sa yayi masa godiya.
Jinjina hannun sa Abbu yayi da hannun sa ɗaya kafin ya sake sa suka shige mota.
Hannun Baffa na ya kalla da ya darmaƙa masa manyan kuɗaɗe masu yawa,yan Bandir na Naira dubu.
Yana ƙara nanata abinda ya furta masa sama sama kafin barin sa wajen " Abawa Hajiya Shatou "
Baffa na kuwa dubawa yayi idan babu mai ganin su dan haka ya sauke numfashi,dan kowa hankalin sa yanzu yana ga motocin da suka fara reverse, yana mamakin dalilin da zai sa ya bawa Shatou kuɗi dan bai da ikon mayar wa saboda sun riga sun shige mota hakan ya sa dole ya cusa su a cikin aljihun sa saboda kar abun ya zama ƙananun magana a cikin ƙauyen..✍️
_FA'EEH BG CE✍️_
Book one free
Book two paid#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Like,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔
_*💋KURMAN ƘADDARA💋*_
_©®Faiza Almustapha Murai_
_FA'EEH BG✍️_
P_____2️⃣1️⃣
*BOOK ONE*
_FREE._
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eeh Bg*
___________Tunda suka kama hanyar barin ƙauyen yake ta sakin murmushi yana ƙara jin wani lamari na ginuwa a zuciyar shi game da Shatou.Shi kan shi Mubarak Murmushin yake saki a gaban mota yana driving hankali kwance yana ji ina ma ace tare da MAHAJ suka zo ya ƙara ganin Abokiyar rigimar sa dan ya san har yanzu abun na ranta daga Hararar da ta ta sakar masa.
Ƙasa haƙuri yayi ya ce " Mubarak Ka san wannan yarinyar ne,hala,naga yadda take ta jefa maka Harara a ɗazu ɗan shafa kai Mubarak yayi kafin ya furta " eh wanchan zuwan da muka yi sai da aka yi rigima da ita da MAHAJ ".Ya kai ƙarshen zancen yana sakin ƙaramar dariya.Abbu kuwa idanu ya ɗan waro cikin mamaki yana furta " shi Mahaj ɗin ".Kai Mubarak ya gyaɗa masa kafin ya fara bashi labarin yadda komai ya faru.Kai Abbu yake girgizawa fuskar shi cike da murmushi babu ma abun da yafi bashi dariya furucin ta na ko shi ɗan gidan waye ne,ko ɗan gidan elibabeth da donath trup.Dariya ya ƙara saki mara sauti yana ƙara mamakin yadda Mahaj ya biye mata har da mayar mata da amsa ya kira ta mai bilicin.Ji yayi ya so ace a gaban shi komai ya faru dan haka next time ya ƙudurta wani abu a ransa.
" Baku kyauta ba ai da ya bada haƙurin amma na san ba lallai ma ta samu kalmar ba lallai MAHAJ ya haɗu da dai dai shi waton duk rashin son maganar ɗana sai da ta saka shi magana " Ya kai ƙarshen maganar ya na ƙara ƙawata fuskar sa da murmushi.
Shi ma Mubarak Murmushin ya saki kafin ya ce " abun da ba zai taɓa yuyuwa ba kenan Dady ".
Kai Abbu ya girgiza yana jingina kan sa da sit ɗin kafin ya sauke numfashi da ajiyar zuciya a hankali ya cigaba da karatun jaridar sa sai dai duk bayan ɗan lokaci zai saki murmushi wani irin nishaɗi yake ji a ran sa.
Baffa na kuwa gida ya wuce shima cike da jimamin lamarin da ya ke gani kamar alamara haka kawai abawa yar sa kuɗi irin wannan bai taɓa riƙa irin wayen nan kudaɗen ba kuma a hakan ma basu burge sa ba dan sai yake ganin kamar ba dan Allah Abbu yayi ba,ya san halin yan siyasa ance suna bada kuɗin tsafi,kuma suna bada kudaden su Badan Allah ba sai dan wata rana su nemi wani abu a wajenka,shi bai hango hakan gun Abbu ba dan a ɗan zaman da suka yi ya hango nagartarsa da kuma mutuncin sa da addinin sa da suka kai shi matsayin da yake kai yanzu domin a kallo ɗaya zaka shaida Abbu mutumin kirki ne mai nagarta.
Har yaje gida yana juya kuɗaɗen cikin aljihun sa.
Tun da ya shiga ya kafe Shatou da idanu yana kallon ta ita kuwa tunda ta ma sa sannu da dawowa ta cigaba da yan wasannin ta na kitson ɗiyar a guro ta toton rake tana kitson tana labta ma kan mai kamar na mutun,tunda ta fara Inna ni tayi mata faɗan ta daina saka mai,kar ta ƙarar musu dashi,ta amsa da, to ta tashi ta mayar da kwalbar,sai dai ashe ta ɗibi wani ta saka a saman ƙafar ta.
Dan haka Inna ni bata lura ba,tayi zaton ta mayar da shi dan haka take yin abun ta hankali kwance,hankalin ta ya ɗauku dan haka bata kula da kallon da Baffa na yake Binta da shi ba.
Inna ni ce ta lura bayan fitowar ta daga ɗakin ta yanzu kai tsaye ta ce " lafiya Baffan su kuwa ? "
Kai ya jinjina mata yana ƙawata fuskar shi da murmushi kafin ya ce " Babu komai A'ee kawai Shatou nake kallo naga sai girma take ta ƙarawa da hankali " .
Ba shatou ba har Inna ni murmushi tayi ita kuwa SHATOU wani daɗi ne ya mamaye ta dan haka ta ɗaga idon ta ta kallo Baffa na Sannan ta ce "Allah Baffa na Dagske " ?
Kai ya gyaɗa mata kafin ta miƙe cike da wani irin tsalle tana furta " Yee na kusa yin Aure Nima "
Ido Inna ni ta waro kafin ta rarumi mabur kaki ta bi Shatou da shi aiko a Guje Shatou ta shige ɗakin Baffa tana Dariya dan ta san nanne kawa zata shiga ta tsira.Ai ko Inna ni bata matsa ba sai murmushi ta saki tana hararar ta saboda Baffa na ba zai barta ta taɓa ta ba saboda a ƙofar ɗakin ya zauna kan yar kujerar sa.
Murmushi ya saki yana furta " A'e kar ki karye mini ƙashin ya da wannan abun "
Yayi zancen yana nuna maburkakin.
Kai Inna ni ta girgiza kafin ta sauke a jiyar zuciya idan ta tuno da furucin Shatou.
Shi ko Baffa miƙewa yayi yana furta " fito yar albarka ".
Fitowa tayi tana Dariya.Bibu ma dake gyaran wasu tsofaffin fitilu da ya fara koyon aikin ya ƙara sakin dariya yana cewa kedai Adda SHATOU Allah ya kai damo ga harawa,Allah Ranar Auren ki akwai bidiri a ƙauyen nan ".
Dariya ta saki tana wani farfar da idanu inna ni da ta gani kai kawai ta girgiza tana yiwa SHATOU Allah ya shirya a cikin zuciyar ta.
Ita kuwa zama suka yi suka fara tsara yadda za,ayi bikin na ta ita Bibu suna dariya kamar yadda kuka san wadda take da tsayayyen saurayi.
Inna ni da take jin su bata kula su ba sai ma wani abun in an faɗa tayi dariya ta ji hawaye sun wanke mata fuska wanda take kaikaitar idanun su ta goge.
Har Baffa na ya ƙara fita bayan kiran da aka yi masa zancen da suke yi kenan.
Daga karshe da suka ishi Inna ni
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 39