Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wa sinawa da turawa Hadda ". Murmushin da bai yi niyyar yi ba ne ya suɓuce masa.Jin furucin Abbun. Jin saukar murmushin sa da Abbun yayi ya ƙara tsintar kan sa cikin farin ciki domin abinda ya faru jiya ya saka masa waswasi da tsoron kar ya hana MAHAJ ɗin gudanar da abun da ya dawo da shi school ɗin yi.Dan haka koda ya kira Mubarak ya ji ya su ke ya sanar masa da lafiya lau,gashi har MAHAJ ɗin ya shirya zasu tafi.Addu'a kawai yayi masa kawai dan yanzu idan ya kira sa ya ji yanayin Muryan sa zai ji babu daɗi dan ya kasa cire damuwar a ran sa. " Kayi ƙoƙari,Allah ya taimaka,I'm so proud of you ''. " Thanks you best father ". Ya furta a hankali kamar bai son wani ya ji. Murmushi Abbu yayi kafin ya ya ɗanyi jin sannan ya furta. " I hope baka saka Damuwar wani a bu a ranka ba game da Ayyah " ? Shiru MAHAJ yayi duk da ya ji zancen Abbu ɗin. A jiyar zuciya Abbu ya sauke sai ya ji dama bai masa maganar ba ganin Damuwar ya ɓoye ta amma yana son ya rage taushe ta ne ya na rage zafin zuciyar sa idan ya na sanar wa wani. Shiru ne ya ƙara ratsa tsakanin su. Abbu ne ya katse shirun na su ta hanyar chanza magana,yana furta. " Yanzu yaushe zaka dawo ? ya kamata kaje ka duba yanayin aikin nan ka ga gashi Ramadan na gabatowa ba lallai ka iya zuwa lokacin ba,Gara ka je yanzu kaga yadda komai yake tafiya ". Ajiyar zuciya MAHAJ ya sauke kamar wanda ya sharɓi kuka. Dan Maganar Ayya da Abbun yayi sai da ya dakatar da duk abinda yake yi dama mai ne yake ta faman shafawa jikin sa dole ya dakata yana kallon wayar da idanun sa da suka sauya,jikinsa na yin sanyi domin ya san cewa Abbun yaji abun da ya faru tsakanin sa da Ayyah wannan zancen na sa shine tabbacin hakan,kuma shi ba haka yake so ba dan duk abinda zai saka mahaifin sa damuwa baya so kamar Yadda baya son komai ya shafi Ayyah ɗin sa.Ya san tabbas jiya Abbu ba lallai ya iya bacci ba,sai yanzu ya gano dalilin ƙin kiran sa da bai yi ba da safe. Abbu da ya ji saukar ajiyar zuciyar ta sa ne ya ji wasu irin hawaye suna neman zubo masa. Haɗiye su yayi jin MAHAJ ɗin na furta " Zan huta Abbun na ɗan lokaci zuwa kafin a zumin zan shigo na ƙarasa Hutu na Nigeria ". Murmushi Abbun yayi jin ya sauke numfashi na doguwar maganar da yayi. " TOH Allah ya bada iko,ka kula mini da kan ka Kaji ɗan Albarka ". Kai ya gyaɗaa kamar yana gaban Abbun tare da ɗan sakin fuskar sa. Kasancewar Abbu ya san yana buƙatar hutawa hakan ya sa babu wata fira yayi masa Sallama. " Komai ya kusa zuwa ƙarshe MAHAJ zaka samu farin ciki in sha ALLAH ". Abbu ne yayi Furucin yana ƙawata fuskar sa da murmushi wanda yake fitowa daga ƙasan zuciyar sa, Murmushi ne mai cike da ma'anoni da ban daban da shi kaɗai ya bar wa kan sa sani. A ɓangaren MAHAJ kuwa Jerarrun Ajiyar zuciya yayi ta sauke wa bayan yanke War da Abbu ya yi,tun ɗazu yake son sauke ajiyar zuciyar na abun da abinda yayi masa tsaye a maƙoshin sa. Dai dai ya gama murje jikin shi ko ina tare da saka manyan turarukkan sa masu tsada da suka riƙa bedroom ɗin na sa da duk wani abun amfanin sa da yake taɓawa yau da kullum idan yana ƙasar. Wani wando ya saka mara nauyi kamar na jersey sannan ya haye gadon sa bayan ƙara gudun Ac da yayi tun daga kan sa har ƙafafun sa ya rufe da tattausan duvet kafin yayi addu'a bacci yayi a won gaba da shi. Kamar yadda MAHAJ ya sanar da Abbu haka kuwa aka yi domin kuwa sai da suka sha hutun wata ɗaya sannan ya haɗo kayan sa tare da Mubarak suka dawo Nigeria. * " Wallahi ni dai Ban yafe ba,duba ki ga yadda ya tulɓe mini fata,Wallahi Allah ya isa na ". Ta kai ƙarshen zancen tana jan majina fuskar ta tayi Jawur ba kowa bace kuwa face Shatou da ta yi fashin islamiyya malam Abu ya zane ta,wanda su su Inna ni ba su ma san cewa ta yi ba dan tana fita da zummar zuwa makaranta,wanda su sai yanzu suke jin ashe laɓewa take yi bakin makarantar bata shiga dan haka yau da dubun ta ta cika malam Abu ya kama ta ya zane. Inna ni dai zuba mata idanu tayi fuskar nan Tata cike da damuwa ganin yadda take kuka kamar za,a zare ran ta ga Allah ya isa da take ta jifan malam Abu. Numfashi ta sauke kafin ta ce " Ai shine dai dai dake dan uban ki tun da baki jin magana ta,bare ta mahaifin na ki da yake ɗaure Miki yake bi dake ta Rarrashi,ai Ni ya ci Ni goro,ungo Habibullah kai wa malam sadaka,Allah ya biya shi ". Ta miƙawa Bibu Naira dari biyar ɗin tana jan ƙaramin tsaki tare da haɗe fuskar ta. Baffa na dan guntun murmushi kawai yayi jin furucin Inna ni kafin ya kamo hannun shatou dake cigaba da kuka tana ƙara masa giya Saboda kalaman Inna ni da suka bata haushi. Rarrashin ta ya dinga yi tare da Bibu da ya faki idon Inna ni da ta shige ɗaki ya ƙi fita daga hanyar da ya nufa. " Baffa na kalli hannun ta fa Wallahi Adda shatou kin daku,Kuma bamu yafe wa Malam Abu ba.". Cewar Bibu. Kallon hannun ta,ta yi inda shatin bulala ya kwanta kan lafiyayyar fatar ta. Cike da sangarta ta ƙara ɓare ƙaramin bakin ta. Tana yi tana kallon gurin tana sake fashewa da kuka. Baffa na hankalin sa duk ya tashi dan haka ya cigaba da rarrashin ta. Sai da suka tabbatar ta yi shiru sannan Baffa na ya furta a hankali " Karki ƙara yiwa malamin ki Allah ya isa kinji shatou malamai sune magada annabawa kinji,haka kaima Bibu kar na ƙara jin haka ". Kai suka ɗaga masa ganin babu alamar wasa kan fuskar sa. Miƙar da Shatoun zaune yayi kafin ya ce " Ki riƙa zuwa makaranta kinji ko,bana son ana dukan ki,gashi ma Makarantar boko sai karar ki ake kawo wa dan Allah ki daina kin ji , Mahaifiyar ki bata jin daɗin haka bare ni,Ki mayar da hankalin ki kamar yadda Bibu ke son zama ba kin ce Yar sanda kike son zama ba " ? Kai ta gyaɗa masa.Cikin tabbatar wa. Murmushi yayi kafin ya ce " Yawwa sai kin dage dan karatu shine gaba su ma ba haka Kawai suka saka kayan Yan sanda ba ". Dan Shatou tunda Abbu ya zo tare da masu kayan yan sanda taga harda mace cikin to tunda ta ƙyalla ido ta sha wa Baffa na kai irin wacchan matar da ta gani ga wannan mutumin mai kyau take son ta zama nan ya ce mata yan sanda ne ta ce ta ji har da aikin su ya faɗa mata ta ce ta ji ta gani.Da farko dariya abun ya bashi sai da yaga dagiyar tayi yawa da nacin tambaya hakan ya sa ya gane da gaske take yi.Shi ya sa yake biye mata a je hakan kawai shi ya san babu wani yar sanda da zata zama suna sake ko suna ɗaure,ai Bama nan gizo ke saƙa ba.Hmm Numfashi ya sauke yana ƙara ƙawata fuskar sa da murmushi kafin ya ce " dan haka ki dage kin ji,Allah ya baku sa,a gaba ɗaya,shi Bibu ya ce mai Shari'a yake son zama kamar yadda mai gari yake yi ". Dariya ta saki kaɗan jin wai bibu mai Shari'a yake son zama kamar Mai gari yana nufin irin yadda idan an kai wa mai gari ƙara yayi sulhu ya bawa mai gaskiya gaskiyar sa.Chab lallai ita kam yar sanda take son zama sai ta saka wayen nan uniform ɗin ko dan ta kama irin su MAHAJ masu rainawa talakawa suna musu yadda suka so. Sunan MAHAJ da ya shigo cikin zancen zucin ta ne ya sa ta jan guntun tsaki. Har sai da Baffa na ya Kalle ta ganin ta haɗe rai tare da sakin tsakin. " Lafiya dai ko ".? Ya tambaye ta yana kallon ta. Ƙara taɓe fuska tayi tana turo baki gaba ta gyaɗawa Baffa na kai kawai. Murmushi yayi kawai tare da girgiza kan sa.Yana mamakin halin shatou wasu lokuttan tayi ta abu kamar mai tashin iska. A ɓangaren Iro kuwa abun duniya ya sha masa kai dan gargaɗin mahaifin sa yake tunowa sai dai har yanzu bai jin ya bar zancen dan haka yau ɗin nan ya shirya tare shatou idan Allah ya Fiddo da ita dandali dan yanzu ba kullum take fita ba sai tayi sati bata fita ba.Kuma hakan mugun yiwa Inna ni daɗi yake yi dan haka yanzu bata wani mata faɗan fitar saboda ko ta fitan tana dawowa da wuri kuma tare da Bibu suke tafiya dan gaba take saka shi.Sai dai Kullum Inna ni cikin Bin ta da Addu,a take ta kariya daga shaiɗan da aljan,da mutun. Kamar kuwa ya sani yau Allah ya fitar da Shatou tun daga nesa ya hango ta tana yankar gudu dan haka bakin shi washe ya tare ta yana zuba mata idanun sa. Turus ta ja ta tsaya ganin sa. Ɗan zuba masa idanu tayi na ɗan lokaci kafin ta ɗauke idanun ta daga kallon sa tana taɓe bakin ta ganin duk yayi duhu ya faɗa kamar wani mai aikin wahala,bayan kuma A iya sanin ta mai gari bai barin sa ko noma ne saboda gata. " Haba Shatou idan babu yaƙi me ya kawo gaba " ? Harara ta sakar masa kafin ta ja ƙaramin tsaki sannan ta ce " Yaƙi kuwa tsakani na da kai ai baya ƙarewa tunda haka kake so yanzu me ye na tare mini hanya ta idan ba neman faɗa ba ". Ta faɗa tana hura hanci irin an dame ta ga cikakkiyar budurwa dan hannuwan nan zaune suke dam a gefen ƙugu. Shidai Iro kamar Gaula haka ya zuba mata ido dan shi duk wani abu da shatou zata yi yanzu burge sa yake yi Kamar kar mahaifin sa yayi masa kashedi da ita ya ji duk duniya babu wanda ya isa ya raba shi da Shatou sai Allah. Ya sha shan alwashi iri iri akan ta tun bayan da ya fara son ta har izuwa yanzu haka yake dan ya sawa ran sa idan har ba shine mijin shatou ba kuwa sai dai yayi mai hisshe sa wadda zata saka dole a duba masa ko ba,a so.Dole na so ki yar Abar nan ga Shegen kyau kamar hindiya. Numfashi ya sauke yana ajiye maganar zucin sa,yana murmushi da yake bayyana haƙoranta sa da suka fara yin jaa saboda rashin wanke bakin. " So ne fa ba komai ba ya kamata Babies ki gane ". Wata uwar Harara ta ƙara sauke masa tana ƙara hura hancin ta musamman jin sunan Babies da ya kira ta dashi dan ya mata daɗi amma bata yarda ta nuna masa ba kar ya ga damar ta ko ya zaci wani abun. Shiko Iro cike da iyayi yake ta ƙara Nana ta haba Babies. Wai tsaya 🤔🤭ko dai yan matan da yawa suke gaban iro bamu sani ba.Koda yake degree ce ga Manya🤣 Gaba tayi aiko Sarkin nacin ya ƙara cin gaban ta. Cike da tsiwa ta fara sauke masa Masifa sai dai abun haushi har ta gama murmushi ne yake saki. Abun da ya fara sage mata gwuiwa kenan domin babu rashin mutuncin da bata juye masa ba a wannan lokacin mai gari ne kawai bata zaga ba har sunan dabba ta kira sa dashi amma sai dai fuskar sa babu alamar damuwa. Tsaye tayi tana kumbure fuska cike da haushin masifar da ta gama.Ji take kamar ta tsinka masa mari ko ta yanke kan sa yadda ba zai ƙara ganin ta ba. Ganin dai bazata taɓa rabuwa da shi ba ta hakan ba ya sa a hankali wata dabara ta faɗo mata ta sauke kan ta ƙasa tana ɗan sakin fuskar ta kafin ta ce. " Yanzu dai muje dandalin ". Tayi gaba tana haɗe rai tare da hararar shi ta gefen ido. Shi ko kamar Gaula haka ya bi bayan ta yana jin kan sa sama musamman da suka jera a tare sai yake jin kamar an biya masa kujeran makka,ko an masa kyautar manyan kuɗaɗe. A haka suka isa dandalin a tsawalle take domin yana yi yana Kallon ta gashi bata wani saba ma hakan da kowa ba sai Bibu ko Baffa na amma yau ɗan anace ya saka ta jerawa da shi dan dole,dan haka take ta cika tana batsewa ba tare da sanin sa ba. Oho shikan ina ruwan sa ai gaba tayi da shi.. Kallo ne ya koma kan su, su Ramata har gwara kai suke yi da Amina wajen ƙara kutsa idon su wajen da suke dosowa da ɗan farin wata ya haske su. Take guri ya amsa kuwwa samari na ta dariya ta irin burge su da Iro da shatou suka yi, dan sai suka ga muguwar dacewar su tare gashi sai ka zata wasu masoyan na ƙwarai ne dan ta sake fuskar ta tana yi tana kallon Iro da yake ta yaƙar baki sai dai ta ciki na ciki ji take kamar ta kai masa mari ga Shi sai tsine masa take yi ƙasan zuciyar ta. Abokan Iro da ke wajen kuwa sama suka ɗaga sa suna cillawa saboda murna shi ko sai kwasar dariya yake yi yana ƙara jin kan sa sama. Ita kuwa Shatou tana samun sun janye sa ta fara jan mugun tsaki wanda ya sa su Ramata Kallon juna. Amina da ta fahimci komai murmushi kawai tayi dama ta san babu komai sharrin shatou ne. Aiko bata gama tunani ba ta ji ta tana furta " Allah ya raba ni da Auren mummuna ƙazami ".Ta tofar da miyau tuno da haƙoran Iro. Sannan ta cigaba da furta " Ni sai ɗan birni mai kyau,amma ba mai kyaun Aljannu ba,wanda idanun sa suke da mugun tsoro " Dukkanin su idanun su suka zuba mata sanin inda zancen ta ya dosa. Ganin yadda suke kallon ta ne ya sa ta furta a hankali " Kai lafiya kar ku cinye wa Inna ni da Baffa ba kyau na ". Amina ce kawai ta yi murmushi suko su jawairiyya shiru suka yi mata musamman Ramata fuskar ta dake haɗe tun dosowar su wajen bata saki ba su kan babu wanda ya lura cikin su sai shatoun ce ma ta lura sai ta basar da ita,dan ta san dai bata mata komai ba. A hakan suka fara wasannin su sai dai ba,a je ko ina ba dambe ya kaure tsakanin Shatou da wata ana tsaka da wasan wai saboda bata mata riƙon dai dai ba ta faɗi dan haka ya sa ta ci ƙasa shine tana tashi ta kama yarinyar da kokawa abun da ta ɗan jima bata yi ba. Aiko da ƙyar aka ƙwaci yarinyar nan. Yarinya ta ji azaba sosai, dan haye ta Shatou tayi yarinyar gata Barakallah kamar ni 🤭😂amma haka ta haye kayan ta dan a girme ma zata bawa shatou shekara biyu. Kukan ta ne ya ankarar da jama'ar wajen musamman maza da suke chan gefe wayen da basu lura da abun da ke faruwa ba. Shi ko saurayin yarinyar dan har an musu baikon su irin na ƙauye jin Muryar ta hankalin sa ya tashi gashi babu mutucin aiko ya zo da azama zai kama shatou ya kakkarya sai yayi rashin sa,a dan Iro ya ce bai san wannan zancen ba zai yi maganin sa musamman jin irin zagin da yake jifan Shatou da shi bayan zagi harda kiran ta da Sunan yar tsintuwa,mara asali yar karuwa.Wayen nan kalamai sun yi tasiri ga zuciyar Shatou duk da ƙarancin shekarun ta,dan take taji kamar a bar ta ta yi maganin sa sai dai su Amina sun san bazata iya faɗa da shi ba gashi ma ba faɗa take yi da maza ba baki ne kawai.Shi ya sa yau suka ji daɗin kasancewar Iri iro wajen dan yau da sai buzun shatou. Dambe ne ya kacha me mai rai da lafiya kowa na tashen balaga.Aiko da ƙyar aka raba , dan Iro sai da ya zubarwa yaron nan da jini.Anan taron wasa ya ƙare,domin kuwa faɗa ne ya ƙara kachamewa tsakanin abokan Iro da na yarinyar duk da dai dama abokai ne wasu ƙungiya daban bayan na iro dan yaron ɗan wani mai kuɗin ƙauyen ne shima jin kan sa yake yi sosai. Da ƙyar aka raba faɗan bayan wasu sun je sun gaya wa mai gari da bai tashi daga fadar sa ba. Koda aka isa da su wajen mai gari da ya turo daga fadar sa,cike da mamaki yake kallon su kafin ya iya yin magana jin bahasin rigimar koda ya bincika ya ji cewar Shatou ce sai ya shiga mamaki dan ya san dai ya raba Shatou da Iro,gashi kuma zagin da iro yace yaron ya mata ya girgiza sa sai dai bai nuna ba ya dai tsawatar musu,a hakan ya samu ya raba case ɗin aka watse sai dai shi kamm Saurayin nan mai suna Shamsu bai bar zancen ba,ya sha alwashin sai ya rama ma Nazihwa budurwar sa bugun da shatou ta mata. A ɓangaren shatou kuwa dukkaninn su hanyar gida suka nufa a tare,gudun kar wani abu ya faru su Amina basu bar Shatou ba sai bakin ƙofar gidan Baffa na suka ajiye ta saboda yau dai babu Bibu a tare da ita ya ce kan sa ke ciwo. Duk da ta ce su tafi amma haka suka ƙi sai da suka ajiye ta sannan suka juya kowa zuciyar sa maƙare da tsoro na damben da aka yi sai dai ita giwar babu ko ɗar a jikin ta.Hasalima ta watsar da komai kofar gidan. Koda Inna ni taga shigowar ta bata ce mata ƙala ba bayan amsa mata sallama Sululu kamar wadda tayi ƙarya haka ta shige ɗakin ta. Inna ni ajiyar zuciya ta sauke kawai ta shige ɗakin ta bayan ta tabbatar mata da ta tabbatar sai tayi addu'a kafin ta kwanta daga chan ta amsa da toh. Tana cire kayan jikin ta ta ɗaura zani saboda zafin da ta ji ya taso mata. Baffa na dai da dake biye da shatoun tun fitar ta har Dawowar ta,yana biye bayan su iya da su Amina faɗan ma ya ji komai da ya faru,duk da yana nesa kaɗan aka yi shi,a hankali ya sauke ajiyar zuciya da numfashi yana shigewa gidan tare da sakaya shi bayan yayi basmalah. Yau sati ɗaya da dawowar su MAHAJ wanda ya kama kuma saura Sati uku a zumi dan haka ya zama ko ina sai shirye shiryen tarbon baƙo ake yi ta ko ina sai gyare gyare ake yi.✍️ A GAFARCE Ni na so yafi haka jiya ban yi da yawa ba sai na tsaya na ƙara muku,yayi tsawo to abun ya gagara exams on next Monday gara nayi focusing kan karatu kar na kwaso carryovobibi🤣Father yace a ajiye rubutu. Zan tafi Hutun wata ɗaya zuwa october zan dawo in Sha ALLAH.Idan muna cikin masu gani idan Rabbi ya lamunce mini. Zan dawo mu cigaba da wannan tafiyar mai ban mamaki da al'ajabi da rikitarwa. Na san zaku ji rani ko nan da shekara ne.Dan haka nake alfahari da ku.🥰💯✨🙏 Allah ya bar kauna.🤲🤲 Dan Allah ku saka Ni a cikin Addu'oin ku.Allah ya bani sa,a da duk wani mai rubuta jarabawa. Shin Iro zai samu Shatou kuwa ? Shatou zata zama yar sanda kuwa kamar yadda take buri? Ina labarin Alina,Sarina ????? Yan biyu masu abun mamaki da tsoro. Ina labarin ta baiwa ? Ina labarin Mai zuwa wajen boka gangaro? Me ye abun da Ayyah ta tsana akan mahaj game da mahaifiyar sa ? Shin wane irin abu ne yake damun rayuwar Bilal Me malam Hambali yake ɓoyewa ? Ya tushen wannan labari ya ke,ina asalin sa,hmmmm mu haɗe a nan da October in Sha ALLAH ✍️✍️ Akwai abubuwa da yawa bayan wayen nan da ya kamata na warware muku kafin zuwa na Hutu sai dai Allah bai nufa ba.Dan haka ku sha kurumin ku zan dawo da zafi zafi 💃💃💃ba tare da tsaiko ba In Sha ALLAH.Ngd.yan amana ta.✨✨🥰 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________3️⃣6️⃣ *BOOK ONE* *_FREE._* _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* _________________________ Alhamdulillah, all praise be to Allah, the Most Glorified and Exalted, who granted me the opportunity to return from the short journey I undertook.I appreciate the support you all showed me by waiting patiently throughout these past days. I’m proud of you, my beloved ones both near and far, those I know and those I don’t.May Allah preserve our love and strengthen our bonds of kinship. I also pray to Allah to not let me face disgrace and to grant me the ability to complete this book successfully without any obstacles. My sincere gratitude goes to my readers,📚 because this name Fa’iee🥰😍✨wouldn't have had meaning without you lovelies 💕. Thank you so jazakallahu khairan.🙏Kurman ƙaddara na godiya ƙwarai Dagaske kun nuna masa ƙauna matuƙa kuma na ji daɗi kamar in taka 🤭😍💃💃💃 Endless thanks to my family,may Allah bless us, increase us in unity and strengthen our ties of kinship. Ameen.🤲 🕊️🕊️🕊️ Yau kwana biyar da samun gocewar ƙashin REENA Kuma har yanzu B bai yiwa LEENA maganar ba kuma ya zuba mata ido da mamaki musamman ganin ta cigaba da harkokin gaban ta,bata nuna wata muguwar damuwa ba akan yanayin yar uwar ta da take fama dan kwanaa biyu Bata ma samun bacci isasshe, sai Ummah ta yi mata addu'oi ta shafa mata akan ƙafar da ke mata zugi haka Sir shima da Dada sai da suka dage da shafa mata addu'a Sannan a hankali ta fara samun sauƙin ƙafar kuma duk wannan yanayi na azaba da Reena take ciki bai taɓa tadawa leena Hankali ba hasalima koda sau ɗaya bata taɓa nuna nadama akan fuskar ta ba,ko damuwa dan haka Ummah da B suka zuba wa sarautar Allah ido. Yau ta kasance Laraba sun shirya tsaf zuwa gaida kakan su dukkannin su tsohon arziki,su uku suka shirya suka tafi dan BILAL ɗin ne ya saka su gaba zuwa wajen Baba Mai Billions ɗin da yake ɗan fama da jiki. Har suka isa babu wata sakewa a tsakanin su.Tsitt suke zaune a cikin tangamemen falon na sa Badan komai ba sai dan Yadda Fuskar Bilal take haɗe kamar wani kumurcin maciji dan tun abinda Leena tayi wa Reena ya kasa sakewa da su fuskar sa ta zamo kullum a ɗaure Ummah kullum cikin masa faɗa take Badan komai ba sai dan samun sakewar Reena da take ɗan raɓewa gefe na jinyar da take yi ta ƙafar kafin ta warke gudun abu biyu yayi mata yawa.Sai dai yana bata kulawa Sosai,kamar yadda kowa yake iya ƙokarin sa. " Ni nayi fushi ace ace sai yau kuke zuwa gaida mai gidan na ku kamar baku son shi " Farin dattijo ne yake yin zancen yana saukowa daga matattakalar benen fuskar sa ƙawace da murmushi kallo ɗaya zaka masa kasan shine mahaifin Ummah dan babu inda ta baro shi. Da sauri Reena ta miƙe tana tura ƙafar ta da ta ke ɗan mata ciwo kaɗan ta isa gaban sa tana dariyar farin ciki. Ba tare da ta tuna gargaɗin Bilal ba na natsuwa da yace kowaccen su tayi wanda kuwa ya yi furucin ne ba dan kowa ba sai dan Leena kuma maganar ta shiga kunnen ta dan ta natsu tayi shiru sai satar kallon sa take yi daga gefe har fitowar dattijon da matar sa wadda suke kira Kaka tayi kiran sa dan sun tarar da ita asashen na sa. Murmushi ƙawace akan fuskar sa yake kallon Reena yana shafa kan ta cike da tausayin ta da wani irin yanayi na kewar abun da yayi masa nisan kiyo. " So ake na huce da wuri haka ne,ake rungume ni " ? Yayi maganar cikin dattako yana shafa farin gemun sa da ya ƙawata fuskar sa. Kai Reena ta gyaɗa masa tana kallon fuskar sa. " Ya jikin B B

Chapter 28 of 39