ɗan fira kaɗan wadda ke nuna shaƙuwar dake tsakanin a halin kafin suka yi sallama a tare Abba ƙarami da su Leena da Samir suka fito daga sashen harda Dada sai dai kowa na sa ɓangaren ya nufa.
Ummah da ke zaune falon ce ta rafka ta gumi kamar wadda ke cikin damuwa ta ga shigowar ta su idanu ta zuba musu cike da so da ƙauna kafin ta yiwa Abba sannu da zuwa yana zama kuwa ta miƙa ta shige kitchen ta haɗo masa shayin sa da yake sha asashen ta kusan kullum dan ta san sun ci abinci chan kamar yadda suka saba yi idan sun tafi Sashen Hajow ko Dada ɗin,sai bata tambaya ba.
Su Leena kuwa kasancewar akwai school gobe Abba ya ce kowa yaje yayi brush yayi alwallah ya yi wanka ya kwanta dan su tashi da wuri haka kuwa ya kasance babu musu suka wuce sama bayan sun yiwa iyayen na su sai da safe.Daki ɗaya suka shiga na Reena dan ita giwar shiga na ta rigima ne da matsala ga Reena ɗin dan duk abun da ta taɓa sai an yi faɗa kan sa amma ita idan shekara za,ayi akan na Reena ko a jikin ta haka ita mai ɗakin bata taɓa damuwa ko kaɗan sai ma ta ka tsaan tsan da take yiwa halin yar uwar ta ta,tun da ta fahimci saurin fushin ta akan ta yake.
Abba na shan shayin suna taɓa fira a hankali cike da so da ƙauna basu ko share awa ba wajen suka miƙe suka wuce sama a tare suka shige bedroom ɗin Abba dake sashen wanka ko wannen su ya yi suma kafin suka bi lafiyar gado shi dai Abba bai daɗe ba bacci ya kwashe sa rungume da matar sa a jikin sa.
Amma Ummah ta daɗe tana juye juye Kafin bacccin ya kwashe ta mai nauyi.
Chan ba,a haura ko awa ba ta miƙe a firgice tana sakin ƙara wadda ke nuna alamar tsoro miƙewa Abba yayi yana Nana ta Inna lillahi wa Inna ilaiihi raji'un yana kunna bedside lamp dake gefen ta ai ko ta haɗa zufa sharkaf.
Addu'a yayi ta tofa mata kafin ta samu natsuwa ta fara sauke numfashi.
" Lafiya kuwa Bary mugun mafarki kika yi ne " ?
Kai ta girgiza masa tana ɗan sakin murmushi sannan ta ce " Wai fa yanzu baccin ya kwashe ni,shine naji kamar kenkeso a cikin jiki na yana mini ya wo shine fa na tashi a firgice ka sanni da tsoron coacroch "
Abba dai zuba mata idanu yayi cike da tausayi dan ya san mafarkan da ta saba yi ne a chan baya wanda har yanzu ta ƙi bayyanar masa da asalin abun da take gani so ɗaya ne zai iya cewa ya ji ta yi wani furuci a cikin mafarkin wanda ya ɗarsa masa mugun tausayin ta,da na sa tausayin dana ya yan sa baki ɗaya, wanda kuma yana tunanin har yanzu bata tuna mafarkin ba,saboda bai taɓa jin ta masa zancen sa ba sai dai yana ganin ta cikin damuwa a wasu lokuttan ya san cewa abun ne ke damun ta matuƙa,dan haka kasancewar shi shirme ya ɗauki abun ya watsar dashi nan inda ya ji shi dan ya san wanda ya mutu baya taɓa dawowa duniyar nan ya tafi kenan dan haka mafarkin nata aikin shaiɗan ne musamman irin wannan.Ko yanzu ya san bai da na saba da irin wancan da ya ji dan haka yake cike da wani irin mugun tausayin ta da na su Leena.
" Kiyi abunda ya dace,Allah ya sauƙaƙa ya yaye muna damuwoyin mu "
A hankali ta furta
" Amin " Kafin ta juya gefen hannun ta na dama dama ta kuskure ne ta kwanta a na hagu.
Ta ƙara shafa addu'oi sannann ta rufe idanun ta.
Abba ma numfashi ya sauke kafin ya fara yin sabuwar Addu'ar ya tofa mata ya shafa mata sannan ya shafe ma jikin sa cike da kulawa.
Bai daɗe ba bacci ya kwashe sa.
Ita kuwa Ummah baccin ne ya gagara sai ma wani dogon tunani da ta lula a hakan bacci mai daɗi ya kwashe ta.
" Wai Ni Samir abokin wasan ka na koma eh "
Abba ƙarami ne riƙe da kunnen ɗan na sa na fari Samir yake zancen bayan fitowar su daga sashen Sir inda suka sosai sashen Hajiya mahaifiyar su Samir ɗin dan Sashen ta ya koma da daren nan kwanan ta ya fara.
Yar ƙara Samir ya saki kafin ya ce " Abba ƙarami na fa kira ka ba ka ɗaga ba kwana biyu da suka wuce niko na zata ka shiga busy shi ya sa ban neme ka ba ".
Dun gure masa kai Abban Yayi kafin ya shafa kan sa yana murmushi ya furta " Na yarda ka barranta ".
Dariya Samir yayi yana shafa kan sa da murza kunnen sa yana ɗan ɓata fuska.
Hajiya da ta fito yanzu jin motsin su ta saki murmushi kafin tace " Sannu da dawowa Abban su,Yawwa mar atussaliha"
Murmushi ta saki haka ma Samir dake shafa kan sa dan ya san halin mahaifin sa babu ruwan sa a gaban su yake yabon matar sa kuma eh ai Hajiya ta chanchanta rayuwar su da Ummah abun burgewa ce a gare sa dan haka yake son koda zai yi aure matar sa sai ta koyi dabarun zama da jama'a a da miji a wajen Ummah da Hajiya dan rayuwar su na burge sa.
" A kawo muku Dinner ɗin nan ne "
" Kwantar da hankalin ki,kin dai ci kin ƙoshi ko keda zarata na ".
Kai Hajiya ta gyaɗa ma sa tana murmushi kamar yar yarinya.
Shima murmushin yayi ganin yadda ta bashi amsa.
Samir kan gaba yayi yana musu sai da safe.
" Mun ci abin ci sashen Sir da su Yaya "
Kai ta jinjina kafin ta mayar da komai inda ya dace sannan ta dawo ta kama hannun mijin na ta suka wuce na su Bedroom ɗin su.
Koda suka isa Lagos lokacin magriba yayi dan dama tafiyar maraice ce suka yi manyan motocin na sojoji ne suka zo suka kwashe su cike da tsari sai a salin ƙaton gidan sa da ke nan.
Shaf shaf suka yi alwallah suka yi masallaci dan gabatar da sallah wadda har an wuce su da raka'a ɗaya.
Bai fito daga masallacin ba sai da ya gabatar da sallahn Isha sannan gaba ɗayan su suka fito kafin suka yi sallama da ogan na su dan sun san da ya shige ya shige bare sun yi tafiya yana bukatar hutawa.
Kayan sa da Ab ya jera masa su a inda ya dace ya kalla kafin ya girgiza kan sa dan sai da ya ce masa kar yayi ya bari ya zo zai yi komai da kan sa.
Wanka kawa yayo ya bi lafiyar gado babu wani tunani bayan yin addu'a bacci yayi gaba da shi.
Tun da Baffa na ya fita ta bi bayan shi da kallo ta kasa ɗauke fuskar ta da idanun ta har ya fita yana jin idanun ta akan sa Wani abu ya tuna hakan ya sa yayi astagfirullah a cikin zuciyar sa ya shige masallaci.
Ita ma Inna alwallah ta yi bayan ta sauke a jiyar zuciya sannan ta shige ɗaki dan gabatar da Tata sallahn akan lokacin ta.
A ɓangaren su Shatou kuwa koda ta isa mai gari ya shige masallaci tare da jama'ar sa dan haka ta samu daga ta ja ta tsaya tana tokare ƙafa shidai Bibu tsoro yake ɗan ji amma babu halin nunawa saboda ya san rigimar Addan ta sa.
Shi ko Iro ya koma gefe sai sakin murmushi yake yi ji yake kamar ace a ɗaura masa Aure da shatou dan dama jibi ne bikin Musa ɗai daga cikin abokan sa to haka yake ji kamar a haɗe bikin yau a Daura a fadar ta mai gari dan wata irin ƙaunar Shatou ce ke ƙara huda jinin sa.
Koda jama'ar mai gari suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya haka suke bin Shatou da kallo kowa na tunanin da wace aka zo yau har suka gama fitowa kuwa babu wanda ta ce wa ƙanzil harda masu ɗan tsokanar ta sai dai ta ture bakin nan gaba.
Bibu ne mai ƙokarin gayar da duk wanda ya fito.
Mai gari da ya fito da ita ya fara sauke idanun sa chak ya tsaya yana zuba mata idanu kamar yau ya saba ganin ta.✍️
Ku gafar ce ni ji na da kuka yi jiya shiru jikin ne babu daɗi ulcer ya sako ni gaba shi ya sa ko Online ban samu na leƙo ba jiyan.Amma a hakan dan na faran ta muku na matse da ƙyar na muku word 400 da wani abu.Ina baran Addu,an ku.
Allah ya bamu lafiya baki ɗaya.
Ngde da kulawar Ku.
Masoyan wannan labari na nesa da na kusa ina godiya ina alfahari da ku.allah ya bar ƙauna mai ɗaurewa.
Fa'i bg Heart ❤️ u o'll💞🙏🙏🙏
Masu ganin Bama sauri kuyi Haƙuri muna kan hanyar inda ya kamata mu isa idan nace nayi rushing ginin labarin zai rushe.
Amma tabbas wasan yanzu aka fara ku ƙara ɗaure ɗamara akwai dubbanin abubuwan da suke ƙulle a kan mu da zamu warware.Wannan kuma tare da ku kawai ne zan samu ƙwarin guiwar hakan ngd.🙏
Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800
# _FA'EEH BG CE✍️_
Book one free
Book two paid N#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin✍️
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔
_*KURMAN ƘADDARA*_
_©®Faiza Almustapha Murai_
_FA'EEH BG✍️_
P________3️⃣0️⃣
*BOOK ONE*
_FREE._
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*
*Wannan shafi na ku ne rankatakaff in ji Bahaushe💃💃🥰💕Maman Abba,Ayeesha Abdullahi,HS,Feenat Ahmad,Hajara kawu gana,Na'eemart Collection,Zainab Ishaq,Habibah Yusuf,Huudatu Umar,Aishatul humaira,Clothing,Zeinabousmaneidi,FB graphics Queen,His Queen,Meryama,Husaina Baby Mohammed,Ummigambonbala, Hauwa'u Musa yeldu,Oumsamha410,Sadiya ka'oje ,Adama Ahmad,teemah beauty,Suhaila,Miss Abdul,Rocky handsome (Lady)😇da sauran su.Ina miƙa saƙon gaisuwa a gare ku.
Allah ya ƙara yiwa rayuwa albarka,ya bar zumunci.I heart😍💕 you all ✨ 🤲*
_________________
___________
_______
____
__
_
Sai da ya gama ƙare mata kallo na kusan seconni goma kafin ya janye kallon sa daga kan ta yana sakin ɗan murmushi.
Ƙarasowa yayi inda take tsaye cike da yar tsokana yace " Yau da me aka zo mana Hajiya shatou "
Baki ta ƙara turawa gaba kafin ta ɗan taka kaɗan ta ce " Wallahi Iro ne ya addabi rayuwa ta shine na kawo sa ƙara"
" Kuma dai me ya haɗa ku ".
Mai gari ya furta yana sakin murmushi.
" Wai so na yake yi yanzu duk inda zanje haka yake bi na kamar tare Inna ni ta haife mu,kuma nace masa ya daina bi na ya ƙi ya daina,Ni kuma shine na ce bari na kawo shi ƙara a masa magana tunda Ni ba ya jin ta wa ".
Ta kai ƙarshen zancen tana ɓata kyakkyawar fuskar ta.
Tun da ta fara zancen fuskar mai gari ta haɗe kamar bai taɓa dariya ba ko Murmushi duk wani annnurin fuskar sa shi ya kau dan haka kallo ɗaya yayi wa Iro dake gefe yana sakin Murmushi sai dai kallon da Mahaifin sa yayi masa ya sa shi shanye Murmushin da duk wani ƙwarin guiwar sa abun da bai tsammana ba a gurin mahaifin sa.
Zama yayi a cikin yar kujerar sa ta zaman fada kafin ya sauke numfashi.Dan murmushi ya saki yana ƙyafato Shatou a hankali kuwa ta ɗan matsa chan kusa da shi ta tsaya tana sauke kan ta ƙasa dake nuna alamar ran ta ɓace yake da abun da Iro yake yi mata.
" Tafi gida zan yi magana dashi kinji daga yau ba zai ƙara Miki magana ba ".
Kai ta gyaɗa masa kafin ta yi gaba ba ta ko kalli Bibu ba dan ta ga yadda yake a tsantance kamar tsoro yake ji dan haka ya bata haushi.
Su ko sauran mutanen fadar murmushi kawai suke yi suna kallon shatou da ta wuce kamar bata son taka ƙasa dan kamar an rufe mata baki haka ta ji bata yi jayayya da mai gari ba ko kaɗan dan haka kowa dake wajen yake murmushi na mamaki da hango alamar hankali ya fara samuwa A tattare da ita.
Shi ko Bibu bayan ta ya bi yana ɗan sauri da haɗawa da gudu yana ƙwala mata kira amma bata ko waiwayo ba ko ta nuna ta jishi.
A ɓangaren Iro kuwa hankalin shi ya ɗan tashi dan bai fahimci ma'anar kallon na mahaifin sa ba mai kama da gargaɗin gaske.
Numfashi mai gari ya sauke yana bin bayan Shatou da kallo ɗauke da murmushi kafin ya koma mayar da kallon sa kan Iro wanda ya sha jinin jikin sa musamman yanzu ganin irin kallon da Mahaifin na sa ya ƙara jefa masa.
Sum sum haka ya bar wajen yana kama hanyar majalisar su ba tare da ya gabatar da Sallahn La,asar ba cike da damuwa akan fuskar sa.
Mai gari kuwa da ido ya bi shi ganin damuwa ta bayyana akan fuskar sa wanda ke nuna masa Dagske yake yi ɗin maganar shatou babu gyara cikin ta.
A ɓangaren SHATOU kuwa da sauri Ya sha gaban ta,zille masa tayi ta na haɗe rai murmushi yayi yace " Ke Adda SHATOU duk akan mene ne wannan haɗe ran "?
Ƙin tanka masa tayi sai yin gefe da ta ƙara yi,fuska ya ɓata kamar zai yi kuka.Kama hanya tayi ta cigaba da tafiyar ta kamar bata ga Bibu na neman yin kuka ba.
Juyawa yayi cike da damuwa ya Kalle ta kafin ya bi bayan ta.
Ta ɗan tattaka kaɗan sannan ta tsaya ta juyo tana fuskan tar sa, yar tsintisyar hannun ta ta ɗaga ta masa alamar ya zo.
Ɓata fuska yayi kafin ya taka da sauri yana murmushi.
Sai da ta tabbatar ya saki jiki ya kusa cimmata dan ya tabbatar zata jira sa ɗin kuma ta sauko Ai ko ta yanka a guje tana dariya.
Kamar yar balbela haka Bibu ya hango shatou aiko cike da dariya shima ya bi bayan ta yana ƙwala mata kira ta jira shi su yi gasa aga wanda zai riga isa gida.
Bata saurare shi ba da alama ita har ta fara gasar shima ƙaimi ya ƙara dan haka sai ya zamo ya riga ta jefa ƙafa a tsakar gidan na su.
Baffa na da ya gansu ne a hanya ya bisu da ido yana murmushi kafin yayi gaba.
" Wallahi ba zan yarda ba ".
Sai kuma ta fashe da kuka tana ƙaƙalo hawaye.
Inna ni da ta fito daga ɗakin ta yanzu ne ta saki baki tana kallon su Ita Shatou na cigaba da ƙaƙalo hawaye da kukan da ke nuna tsantsar sakarci.
Da mamaki ganin alamar yanzu suka shigo hakan.
Inna ni ce " Wai lafiya kuka shigo muna gida haka babu ko sallama ''?
" Wai daga kawai nace muyi gasa shine muka yi na riga ta saka ƙafa anan, shine take kuka wai ba zata yarda ba "
Cewar Bibu yana cigaba da yin dariyar sa.
Salallami Inna ni ta hau kafin ta ce " na shiga uku ni Indo yanzu wannan ne abun kuka Shatou ke da kullum ba kya girma dan uban ki ƙanen ki ma ya fi hankali wani sa'in ".
" Daga yau ma kaine wa na karɓe daga gare ta,idan tayi laifi ka zane ta a matsayin ka na babba ".
Tunda Inna ni ta fara zancen yake wasar baki yana dariya.
Ita ma Inna ni dariyar take yi ƙasa ƙasa ganin yadda hakimar ta haɗe rai kamar an mata mutuwa ga hawaye sun wanke fuskar ta ta a wannan karon Dagaske.
Tsalle Bibu ya daka yana murnar sa ita ko shatou kamar ance mata Inna ni ce ta mutu ko Baffa na ko shi Bibu da su Amina ta cigaba da sakin kukan ta mai ƙara.
" Amma dai anyi ƙatuwar banza SHATOU "
Inna ni ta ƙara furta wa.
Matsawa ta yi kusa da SHATOU ɗin tana dariya sai kuma ta juya ta shiga madafar su sai gata ta fito da maburkaki a hannun ta, fuskar ta haɗe dan ta lura lamarin na Shatou sai a hankali.
Aiko Shatou na hango ta,ta miƙe tana shigewa ɗakin ta tana waigen Inna ni.
Dariya Bibu yayi kamar zai kai ƙasa kafin ya yi alwallah ya fice masallaci yayi Sallah.
Inna ni ma kan ta,ta girgiza tana sakin guntun murmushi tana furtawa a ranta kura ga tsoro ga ban tsoro.
A ɓangaren Baffa na kuwa koda ya isa fadar mai gari gaisawa kawai yayi da mai gari da sauran jama'ar fadar yayi gaba,Mai gari da ya fahimci dalilin zuwan sa ya wuce ɗin bai ce masa komai ba sai sakin murmushi da ya ɗan yi ta gefen baki kulawar Baffa na ga yar sa na burge sa.
A ɓangaren shatou kuwa tunda ta shige ɗakin ta,ta ke sauke ajiyar zuciya kafin ta tura baki gefe ta miƙe tuna bata yi Sallah ba.Koda ta fito tsakar gidan babu kowa dan haka tayi alwallah ta wuce ɗaki tayi sallah anan bacci ya kwashe ta bata farka ba sai gab da magriba.Cike da mafarkaii haka ta tashi tana zarar idanu addu'oi tayi tayi a zuciyar ta kafin ta samu su fito fili har ta buɗe idanun ta tar akan Inna ni dake kan ta wadda itace ta tada ita daga baccin na ta ganin shiru har su Baffa na sun yi masallaci bata fito ba shine ta zo duba lafiya ta same ta tana bacci dan ta yi zaton ma a ɗazu ta fice gidan su Amina ko Jawairiyya sai Bibu yace mata ai tana nan ya dubo ta lokacin da Baffa na yake zancen ina take kafin ya sake ficewa,dan haka ta fita iskan ta dan ta san ƙila wani abun ya ɗauke mata hankali kamar aikin aji da sauran su dan baya ma yi zaton bacci take yi ba.
Inna ni zuba mata idanu tayi ganin tana zare ido alamar har yanzu tsoron abinda ta gani a mafarkin bai sake ta ba dan ta fahimci mafarki tayi dan haka tayi ta tofa mata addu'a, itama da ta fahimci ta farka daga mugun mafarkin ta fara addu'oi Inna ni na taya ta a hankali kuwa ta fara sauke dogon numfashi tana ya mutsar fuska cike da son tuna yanayin mafarkin na ta sai dai duk yadda take son tunawa ta kasa dan haka ta kalli Inna ni da idanun ta da ke cike da hawaye da suka taru lokaci ɗaya dan zata iya tuna mafarkin ba mai kyau bane duk abun da ta gani a cikin sa akwai tashin hankali a cikin sa mai girma.
" Mafarkin me kika yi haka Shatou " ???
Inna ni ta faɗa tana zuba ma yar Tata idanu cike da wani irin rauni da ya dabaibaiye ta ganin hawayen yar ta wanda suke tabbatar da cewa har zuci lamarin babba ne na abunda zai karya mata zuciya haka a game da mafarki wanda kuma kowa ya san kaso goma kashi uku duka ƙarya ne mafarki.
Kuka ta ta fashe ma Inna ni dashi rarrashin ta Inna ni ta dinga yi kafin ta samu ta lafa ta yi shiru.
Cike da wani irin ɗan tsoro tace " Mafarkin na kasa tunawa fa shine nake ta son na tuna amma na kasa Inna ni kuma fa abun da na gani ba mai kyau bane,Harda kuka nayi a mafarkin "
Sai kuma ta fashe da kuka
" Ya isa barshi kawai kinji duk ranar da kika tuna sai ki sanar mini yanzu dai ki dage da addu'a ƙila da zaki kwanta baki yi addu'a bane ba ko ? "
Kai shatou ta gyaɗa mata.
Ɗan murmushi Inna ni ta ƙaƙalo kafin tace " Yawwa yanzu anyi Sallah tashi kinji ".
Miƙe tayi da taimakon Inna ni suka fice daga ɗakin.
Ruwan Alwallah ta zuba mata sannan ta miƙa mata ita kuma ta shige nata ɗaki kafin ta fito da littafin azkar ɗin ta dan kwana biyu ba su zauna zaman karatun azkar ɗin ba.
Tabar mar dake shinfiɗe ta gyara mata abun Sallah kafin ita ma ta kabbara Tata Sallahn akan abun Sallahn da ta shimfiɗa ma kan ta,hijabi shatou ta ɗauko ɗakin ta itama mai ɗan girma ta tada Sallah a natse , abun mamaki yau Inna ni ta riga Shatou gama sallah.
Inna ni dai ikon Allah take ta kallo da wani shakku akan yanayin shatou da mamakin wannan wane irin mafarki ne ya lallasa jikin Shatou haka komai babu kuzari take yin sa.
Tun Inna ni na mamaki ta daina dan shatou bata gama Sallahn ba sai da a ka kusa kiran Sallahn Isha shima tana gama magriba ɗin ta hau yin Ba,adil magrib.Inna ni dai ga mamaki ga kuma wani irin karye wa da zuciyar ta ke yi na yanayin yar ta ɗin.
Ƙarshe sai dai ta girgiza kai tana sakin murmushi tana tuna wani lokaci da ya shuɗe lokacin da tana amarya ta dinga rafka sallah tana amarya bayan ango ya tafi Rakiyar abokai har ya dawo ya same ta haka,sai yanayin ya dawo mata da komai sabo ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi zuciyar ta na fara wani irin rawa kamar ana daka sakwara ga wani irin ɗaci da ya maƙare zuciyar ta da ruhi wani duhu da ta fara gani na damuwa ne da baƙin ciki hakan ya sa ta fara ambaton sunan Allah da neman agaji take kuwa ya kawo mata ɗauki ya hana yanayin da zuciyar ta ke neman shiga yin tasiri a gare ta.
Bayan ta samu natsuwa ne ta juyar da kallon ta kan Shatou da tayi zugum tana kallon ta ganin yadda take ta rintse ido tana dafe ƙirji.
Murmushi ta ƙaƙalo dan bata son ta fahimci komai bare ta dame ta da tambaya har Baffa na ya fahimci wani abu.
Aiko tambayar da ta guda itace ta ratsa dodon kunnen ta.
" Inna ni me kike dafewa ƙirji da rufe ido ko bakya da lafiya "?
Murmushi ta ƙara saki ganin shatou na gama furucin ta ƙara zuba mata manyan idanun ta alamar amsa take jira dan haka ta ce " Babu komai shatou gajiya ce kawai "
" Irin yadda naji ranar ne kika ji ko Inna ni ai nima haka na dafe ƙirji na har kika ce mini sakarci ne kawai "
Murmushin inna ni ta saki kafin ta ce " Eh fa shine ai na fahimce ki fa,ranar gajiya ce ta saka ki jin haka,Nima itace dan haka yau da wuri ma zan kwanta ".
Kai shatou ta jinjina cike da gamsuwa kafin ta cigaba da addu,oin ta ita kuwa Inna ni ɗan murmusa wa tayi kafin ta sauke ajiyar zuciya.
Dan bata san mai zata ce mata ba dan ko ita ta ta faduwar ƙirjin a wancan ranar abun ya tsaya mata a rai ta san tabbas babban abu ne zai kawo wa yarinya ƙarama irin wannan matsalar sai kuma idan an haifi ya ro da hawan jini ko ya samu tsoro mai girma.To bare ita da ta san ainahin ta ta damuwar,da ta kasu kashi kashi wanda ta san hankalin shatou ba zai taɓa iya ɗauka ba,ba yanzu ya kamata ta fuskanci komai ba.Ƙaddarar ta wani babi ne da take ganin shafin sa ɗaya bayan ɗayan akan yar ta kuma Garkuwar ta,da ƙaddarar su take tafiya a tare da rayuwar su.Numfashi ta ƙara sauke wa tare da su jan ajiyar zuciya wanda har sai da Shatou ta waiwayo sai dai bata ce mata komai ba ta cigaba da yin addu'a tana jerawa su Inna ni Addu'oi tun rana yi a zuci har ta fito fili hakan shi ya sanya ya zuciyar Inna ni yin sanyi tare da sakin murmushi tana karɓawa da Amin.✍️
Ku GAFARCE Ni hiliss mutane kirki na san na muku laifi wallahi na shiga.Busy kwana biyu dan haka typing ya gagare ni.🙏 Jama'ar facebook ma da muka wuce sosai gashi a jiye basu samu update ba ayi haƙuri ✍️
Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800
# _FA'EEH BG CE✍️_
Book one free
Book two paid N#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin✍️
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔
https://chat.whatsapp.com/H5xKfOMK5QE2YtMirvcsat?mode=r_t
_*KURMAN ƘADDARA*_
_©®Faiza Almustapha Murai_
_FA'EEH BG✍️_
P________3️⃣1️⃣
*BOOK ONE*
_FREE._
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*
ADVERTISING! ADVERISING!💃💃💃
KHADSEEN'S COLLECTION
GIDAN KAYAN ADO 👜👛👝👡👠⌚👗🛍️
BABBAR YAR KASUWAR NAN TA KU TA MATA MAI SUNA KHADSEEN'S COLLECTION TA ƘARA KAWO MUKU HAJAR TA MAI KYAWON KALLO
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 39