Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kalli fuskar Abba da ta yi jaaa Shima idanun sa kamar sun tara ruwa. " Ƙarfin gwiwar da kike bani itace nake kai Bary,da Badan yadda kike ƙarfafa mini ba da bana tunanin zan kai wannan lokaci bary me ya sa ƙaddara ta mana haka,wace irin jarabawa ce yaya na suke kai ".Shiru yayi,Ɗumin da ya ji a gefen idon sa ya shafo hawaye dai ne masu ɗumi ɗan murmushi ya yi yana haɗiye sauran kafin ya shafe ma Ummah na ta da suke cigaba da kwaranya. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi wadda har shi kan sa sai da ya ji ta dan haka ya zuba mata idanu. Sanin ma'anar ajiyar zuciyar ta ta da tayi ne,dan haka a hankali ya furta " ina ƙara baki haƙuri Bary ki cigaba da haƙuri komai zai wuce jarabawar mu ce hakan ina iyakar ƙoƙari na gurin nema mana sauƙi wajen Ubangiji abinda yake damuna ya yaye muna baki ɗaya ". " Kuma in sha ALLAH Allah zai yaye muna zai dubi zukatan mu masu kyau ". " Komai zai zama tarihi ki cigaba da haƙuri Sannan ba zan gaji da neman gafarar ki ba." Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi bayan jin ta akan ƙirjin Abba wanda yake sauke numfashi a jejjere kamar wanda yayi tsere dan a duk lokacin da ya samu kusanci da Ummah haka ya kan ji sauyin yanayi a jikin sa sai dai yana iya ƙoƙarin sa na dannewa. Sun jima a haka kafin ya sake ta yana rintse idanun sa. Miƙewa yayi ya shige toilet ruwa ya sakar ma jikin sa kafin ya zare kayan jikin sa ya ɗauro wanka. Ummah kuwa idanun ta ta rufe tana jin gina da gadon tare da sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ta buɗe idanun ta ta zuba ma ƙofar toilet ɗin idanu. Ɗan murmushi ta saki a hankali kafin ta share wani hawayen da ya silalo mata. Sannan ta fice daga ɗakin tana shigewa nata. Kayan jikin ta ta cire itama kafin ta shige toilet wanka. *Tsut haka ta bayyana gaban sa kamar yadda ta saba zuwa wajen sa a koda yaushe cikin shigar ta da ta saba. Hahahhahhha Dariyar shi ta karaɗe ilahirin dajin. Wadda take fita iri daban daban. " Ta Baiwa yar Baiwa Uwar Mugaye yau da wace aka zo,ki faɗa da bakin ki aiki ya fi ci haka ". Gyaran zaman ta tayi kafin ta gyaran zaman mayafin abayar ta cikin wata murya dake nuna damuwa ta fara magana " Hankali na ya kasa kwantawa ne Dan Baiwa,Har yanzu gani nake kamar babu abun da zai ci da kyau game da aikin mu duk da akwai wasu alamomi da suke bayyane,Sannan Duhun nan da ka yi magana akan sa ya kamata na san me ne ainahin abunda ke cikin sa,haka kawai nake jin kamar akwai matsala ". Dariya ya fara gaggaɓa yana kallon ta idanun sa na wani irin fitar da hucin zafi na kalmomin ta da take fitarwa kamar bata yi imani da shi ba kamar yadda ta faɗa baya.Dan haka cike da wani irin haushi ya ce " Ta Baiwa kin halaka,kin halaka ". "Mun halaka Ɗan Baiwa,ka wuce gado,ba gaba da gaba ko ta baya sai an shirya,Sarkin mugaye uban su ɗan duhu da duna ". Ta yi Zancen itama hankalin ta kwance dan ta san zai sauko saboda ɓacin ran da ya shiga yanzu. Laƙwass Haka Ƙaton bokan nan yayi kafin ya kece da Dariya har sai dai ya kai ƙasa yana mulmulawa jikin nan na sa kamar tsohuwar ƙwarangwal.Abun dariya abun haushi. Sai da ya gama sannan ya miƙe ya ce " kwantar da hankalin ki Lallai sai na bincike wannan abun da ke cikin duhun nan,Bana son ki koma damuwa akan sa,maganar hankalin ki tashe yake ki ƙara imani zai kwanta Ta Baiwa,aikin mu yana nan yana tafiya dai dai kedai ki cigaba da zuba ido ki gani zaki ga kammaluwar sa dai dai lokacin da ya kama ta " . Kai ta gyaɗa masa kafin ta kece da dariya kamar zararrriya ta furta "Lallai nayi imani da kai Ɗan Baiwa na san zaka cika mini buri na,Ka ƙara mini maganin masu mini kutse na fara hango cigaba ". " Hhhhh Ta Baiwa ta Ɗan Baiwa Mai ja dake sai ya shirya,Son zuciyar ki na burge Ni,Rashin imanin ki shine ya ƙara wa su ɗan duhu ƙarfin Miki aiki lallai kin ci lambar yabo nan gaba kaɗan za,a Miki naɗin Uwa ta su ɗan duhu aiki ɓagass,ki saka ki hana ". Wal iyazubillah😭😭 Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un 😭 Masu halin ta baiwa fa suna da yawa wallahi suna nan atsakankanin wannan duniya suna aikata ɓarna son ran su.Ba tare da tunanin yau da goben su yadda zata kasance ba,ba tare da tunanin hukuncin da Ubangiji ya tanadar ma masu aikata shirka ba,Lallai Allah mai jin ƙaine ga bayin sa.Haƙurin da ubangijin mu yake yi damu wani bawan sa ba zai iya yin sa ba.Mukan yi laifi mai muni,mu yi mu maimaita mu nemi gafarar sa ya yafe muna,Lallai ubangiji Mai Rahama ne,Dan haka masu zuwa wajen bokaye ko malaman tsibbo ku ji tsoron Allah ku tuba ku nemi gafarar Ubangiji. Allah mai yafiya ne da jinƙai ga bayin sa. Allah ka yi mana shiriya ka hana muna zuwa wajen da zamu haɗa Allah da wanin sa.Da duk wani wajen saɓon Allah,Allah ka bamu ikon tsarkake zukatan mu.Amin. Dariya ta kece da ita tana gyara mayafin ta kafin kuma ta ce " Na tafi ɗan Baiwa sai wata haɗuwar ". Ta ɓace ɓatt anan wajen. Shima kamin ƙayfatawar ido babu alamar zaman sa wajen dan itace ta fito da shi dama. Allah ka yafe mana zunubban mu.😭🙏 A yau ne ake ta shirye shiryen zuwa da MA'ISHA waje kamar yadda suka gama shirye shiryen su dan Daga Suhail za,a je sai Suhaila da kuma Nurse Mira Duk wani shirye shiryen su an gama sa.Su Dady da Amoh sun Bisu da Addu'ar samun nasara cike da kewar ya'yan na su musamman MA'ISHA da tausayin ta ya gama mamaye zukatan su.Abba Saboda ayyukan office da suka masa yawa Suhail yace ba sai ya je ba shi kaɗai ma ya isa ita Amoh ba,a maganar ta saboda ciwon ƙafafu da take fama dashi. Jirgin su ya tashi daga babban filin tashi da saukar jirage na Abuja. In da bai yi tsinke a ko ina ba sai a Canada. Sun sauka a wata asibiti mai suna British Family Hospital Canada Kasancewar asibitin sun san da zuwan su an riga anyi follow up aka tarbe su cikin karrama wa. Da zuwan su aka karɓi Ishaa dake ta bacci na Allurar Baccin da aka yi mata kafin barowar su Nigeria dan har aka shirya ta bata san ana yi ba. An mata gwaje gwaje aranar sai dai kamar koda yaushe bayanin irin ɗaya ne da sauran asibiton ke nuna wa dan basu ga komai ba duk da sun yi mamaki saboda ƙwararru ne ke kula da ita asibitin ma gaba ɗaya dan shi kan sa Suhail ba baya ba amma yana son wasu su ƙara bincika masa,ko za,a dace su san inda matsalar take.Dan haka suka bawa Suhail haƙuri tare da masa alfarmar zasu mata wannan checkup ɗin na wata ɗaya a gani ko za,a dace. Cikin Tausayin ta ya amince ganin lokaci ne mai tsawo ya sa yace Nurse Mira ta koma gida aka bar Suhaila kasancewar akwai ƙwararrun likitotan Jinya dan haka Mira ta koma gida ta cigaba da aikin ta kafin dawowar su da suke fatan kafin lokacin an gano matsalar. Amoh da ke zaune lokacin da Suhail yake yiwa Dady bayani a waya saboda handsfree take, wani irin hawaye ne suka silalo mata ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta isa wajen yarinyar ta amma ina. Kuka ne ya ci ƙarfin ta haka Dady ƙarfin hali yayi dan lamarin Ishaa ya fara bashi mamaki matuƙa mamakin ma na ra sa abun yi amma duk da haka addu,a yake cigaba da bin ta da ita cikin zuciyar sa yana share ma Amoh hawaye da girgiza mata kai wadda kuka ya ɓalle mata. Wanda da ƙyar ya samu ta natsu bayan ya bata baki wanda shima kan sa ƙarfin halin ne kawai yake yi. A haka suka share wata ɗaya A Canada sai dai tsit kake ji babu wani bayani ƙarshe ma Dr Barack da yake abokin sa shi ya kira Suhail gefe ya bashi haƙuri dan sauran sun kasa tun kararr sa. Cikin lafiyayyen turancin ya sanar masa " I'm sorry gaskiya ba zan ɓoye maka ba Dr.Suhail yarinyar nan ƙwaƙwalwar ta lafiya lau yake bata da matsalar komai,Ku cigaba da yi mata addu'a kuna kainta church,or mosques ana mata addu'a dan bamu ga komai ba ". Shiru yayi yana sauke numfashi da ajiyar zuciya bayan gama sauraren sa.Dan haka godiya kawai yayi masa tare da amsa addu'ar samun lafiya da yake ta yi mata acikin harshen turanci tare da ambatar Jesus kamar yadda bakin su ya saba. Koda ya isa ɗakin ta da take jin ya wanda itada Suhaila kawai ke cikin sa komai akwai shine kawai yake cikin otel ɗin da ke cikin Asibitin mai Shegen tsada da kyau dan saboda mafi yawan mutane suna zuwa hospital ɗin neman lafiya saboda ƙwarewar su. Kwance ya tarar da ita kamar koda yaushe dan bai fi sau Biyar ba ne yake samun ta ido biyu saboda yanayin ta da yake son hutu hakan ya sa likitotan suke bata Alluran barci wadda bata cutarwa dan haka ta ƙara samun Hutu tayi wani irin kyau fatar ta sai sheƙi take yi dan ko abinci suna bata shi a cikin drip abun da zai hana ta saurin jin yunwa da ciko mata cikin ta kafin ta farka ta saka wani abu a cikin ta,kuma gwargwado idan ta farka tana shan madara da fruit ɗin suma da ƙyar kafin a gama ta ɓata jikin ta gaba ɗaya dan zuwan su Canada ma ta rage duk wani haukar irin ɓatattar nan so ɗaya ta yi ta wan sahaken da suka zo ta farka cikin na'urar da ke Binciken ƙwaƙwalwa gashi ko ina tar take ta hargitse musu kasancewa su ƙwararru cikin yan daƙiƙu suka mayar da ita yanayin natsuwa dan haka ta koma sai yadda suka yi da ita idanun ta ƙwar akan su ga hasken da take ji har tsakiyar kwanyar ta,ga abubuwan da take gani a cikin hasken kamar an ƙara musu yawa dan haka hawaye suka yi ta silalar mata a gefen ido koda aka dawo wa Suhaila da ita kuka ta zauna ta darza tana kallon Ishaa a wannan yanayi gashi da haske amma ta kasa ko motsi sai hawaye da take yi ta kafe Suhaila da ido. A bu ɗaya ne matsalar hasken nan da bata so likitota suka matsa da kullum Abar hasken ɗakin kunne.A hakan har ta fara rashin damuwa da shi sannan duk wata rigima ta rage ta, zata yi shiru dai ta zuba ma waje ɗaya ido kafin kaga kuma ta ɗauke kallon ta wajen,Sai kuma hawaye,chan sai kaga tayi dariya ko surutai mara sa kan gado kamar wani yare daban wanda Suhaila bata taɓa sanin akwai shi duniya ba.Kuma yanayin ta hakan yana sanya su Farin ciki ganin kamar wata nasara ce ko wannan maganar tata da take yi cikin Muryan ta ƙarama.Wannan kenan. Idanun sa ya rintse da ƙarfi yana buɗewa kafin ya ja ajiyar zuciya yana barin ɗakin bayan ya sanar da Suhaila su shirya yau zasu bar ƙasar da dare. Kai kawai Suhaila ta gyaɗa masa tana haɗiye wani sabon kukan da ya ta so mata bayan wanda ta gama yanzu,dan ta san tun da bai ce mata komai ba babu wata nasara. Sai da ta darji kuka sannan ta haɗa musu komai na su dama a haɗe komai yake. Da taimakon Nurse suka chanza mata kayan jikin ta daga rigar asibitin... Ƙarfe takwas dai dai na dare suka hawo jirgi sai Nigeria kafin suka sauka ƙarfe bakwai na safe.Driver ne yaje kwaso su tare Amoh har da Dady da Rayyan a mota ɗaya. Su ne suka fara fitowa fitowa tare da ma'aikatan jirgin guda biyu da suka tuƙo gadon da Ishaa take kai. Hawaye ne suka Silalo ma Dady na tausayin Ishaaa, A hankali ya shafe kar amoh ta gani,ita kan Amoh ba,a ma maganar ta.Dan kuka ne ya ƙwace mata ji take kamar ta dawo da yanayin Ishaa akan ta. Driver motar da Rayyan yake ciki ya buɗe wa Suhail ya sanya Ishaa ciki a baya sannan shi ya shige gaban motar. Ita kuwa Suhaila Gaban motar su Dady ta shiga da driver ya tuƙo su. Duk yadda Amoh ke son cigaba da daurewa kamar yadda Suhail ya rarrrashe ta, ta kasa haƙuri dan ko yanzu suhaila baki take ta bata kamar ta yi kuka, ita ganin ta yi kamar ma Ishaa ɗin ta bata numfashi, Badan Suhail ya sanar mata da ran ta bazata yarda ba,ga kuma suhaila da take ta bata ƙwarin guiwa, baiwar Allah hankalin ta duk ya tashi lokaci ɗaya. Dukkanin su sai suka matsu su isa gida dan bai sanar musu da komai ba kuma ya gargaɗi Suhaila ɗin dan haka take ta kame kame ta ƙi yin magana. Dan haka yana cewa zasu dawo gobe hankalin su ya koma ga jin yadda lafiyar ta ta take sai dai ya datse kiran tare da kashe wayar sa hakan shi ya hana musu sanin komai har Rayyan dan Ya san halin sa da zuciya kamar ta mata zai iya tsorata ya furta wata magana kusa da Amoh ya tayar mata da ciwo duk da ko yanzu fama take yi da kan ta. Hankalin Amoh ya kwanta sosai jin cewa an gano matsalar har an bada maganin ta tare da zuwa duba ta duk bayan wasu yan lokutta.Kasancewar Dady ya gargaɗe sa kar ya sanar mata bayan saukar su gama breakfast ɗin su sai ya keɓe da Dady ya fara sanar masa dan haka ya gargaɗe sa dan dama shima ko kwonton faɗa mata yake yi. Dukkanin su kallon Amoh kawai suke yi dake ta farin ciki tana ta faman lailayar Isha dake ta baccin ta har yanzu.Wani sanyi ta ji labarin da Suhail ya kawo mata,itadai Suhaila murmushi kawai take yi tun da ta ji ya'yan ta ya ɓoye ta san cewa saboda Amoh ɗin ne dan haka ta ja ta ƙara tsuke bakin ta,kamar farko. MA'ISHA kwanan ta ɗaya kafin ta farfaɗo,Yanayin ta na shiru shiru ya dawo ta yi sati haka,kafin suka tashi da wani sabon tashin hankalin da suka shiga domin kuwa yanayin da take ciki ya dawo sabo na haukar ta da har yafi na da domin kuwa kayan jikin ta yanzu babu wanda yake kalluwa duk ta musu fata fata ta yaga kamar yankan reza kuma duk wanda ya matsa wajen ta sai ta masa illa.Amoh harda kwanciya asibiti duk da yadda aka kwantar mata da hankali da cewar likitotan ta sunce dole zata yi hakan kafin komai ya fara yin ƙasa.Dan haka suka samu ta ɗan kwantar da hankalin ta. Yanzu har ta kai Ishaa Ɗaure ta ake yi saboda yadda take azabtar da kan ta.Cikin ɗan wannan lokaci wannan a hali sun shiga tashin hankali matuƙa,sai dai sun duƙufa wajen faɗawa Ubangiji ba dare ba rana,sun san shi ya ɗaura mata wannan lalurar shi ya jarabce ta da ita kuma shi zai yaye mata.. Zaune yake gaban wani haɗaɗɗen Glass mai kama da bango guda,wanda ke ta walƙiya yana haska yanayin da garin yake ciki.Sama ya zubawa ido yana kallon yadda Rana take ƙara haska garin Beijing,mutanen garin kowa sai harkar gaban sa yake yi wasu kan mota,mashin,Keke,wasu ƙafa.Komai cikin tsari gwanin burgewa. Idanun sa ya ɗan lumshe a hankali kafin ya buɗe su yana sauke ajiyar zuciya a hankali da numfashi a lokaci ɗaya. Wuyan vest ɗin sa da ke ta shinning fara ƙar da ita da ta haɗe da fatar sa ya gyara.Dan ita kaɗai ce jikin sa sai Short daga bakin guiwar sa bai ma kai chan ba dan haka Santala Santalan ƙafafun sa da suke ɗauke da gashi suke bayyane sai walƙiya fatar ke yi tana kashe ido. kasancewar yau yana Hutu ne zuwa gobe zasu gudanar da Presentation ɗin su dan haka yake zaune wajen yana hutawar sa. Yar sofa ɗin da yake kai mai zagaye wadda ke ɗauke da Haɗaɗɗen center table shima a kusa da ita inda take ɗauke da ruwa da glass cup mai kyau da tsada. Ƙoƙarin tsiyaya ruwan yake yi a hankali cike da natsuwar sa jin maƙoshin sa ya bushe,Sai dai katawa tayi jin basu da maraba da ruwan zafi hakan ya sa shi jan ƙaramin tsaki yana Hararar ƙofa kamar yanzu Mubarak ɗin ya ajiye masa ruwan dan ya san zai buƙace su.Duk da ya san fushi yake yi dashi amma bai hana tun da safe ya zo duba yanayin da yake ciki ba,ganin sa nan zaune ya sa hankalin sa ya ɗan kwanta dan haka bayan gaisuwa bai ce masa komai ba,ya ɗauko masa ruwa ajiye yayi gaba. Wanda har ya fita da gefen ido yake kallon sa,yana mamakin wannan fushi sai kace rayuwar sa zai ra sa.Rufe goran ruwan yayi da kyau.Miƙewa yayi ya matsa wajen wata na'ura kamar dai hot and cool sai dai ita wannan magana take yi abun ka da technologia sannan ga ta dai kamar na'urar Haɗa cupy amma ba ita bace. Ƙaramin tsaki ya ja jin yadda na'urar ta cika masa kunne shi ya sa bai cika damuwa da taɓa ta ba ya fi gane wa ya ɗauko na fridge,ciwon sa ya san bai son sanyi dan haka yake takatsantsan yake kamantawa yana shan masu ɗan ɗumin sanyi,amma shi Mubarak muddin zai ajiye masa ruwa basu da ɗigon ko na sanyi kamar wani mai zunubi, shi gani yake ma kamar mubeey ɗin na ɗunama ruwan. Dawowa yayi ya zauna bayan ta tsiyayo masa ruwan da ta saka shi magana,inda ya sanar mata masu sanyi. Dan haka ya sirka da wayen da Mubarak ya ajiye masa kurɓa biyu yayi ya ajiye. Wayar sa ce tayi ƙara kobai bincika ba ya san cikin biyu ko Abbu,ko Samrah,ko abokan kasuwan cin sa irin masu naci da suke matsa dole dashi suke son yin tsare tsare ba Mubarak ba.Dan haka kullum yake sauya layi saboda ya tsani takura. Abbu ne ya bayyana akan screen ɗin sa dake ɗauke da wani hoto na mace Black beauty da kamala hoton da yayi kyau har ya gaji wanda bai daɗe da samun hoton ba a cikin takardun Abbu,Tare da sunan Mahaifiyar sa a bayan sa dan haka ya adana shi sai kwanan nan ya sa aka wanko masa hoton ya ƙara yin kyau kamar yau aka ɗauke shi.. Cike da girmamawa ya yi sallama kafin Abbu ya fara jan sa da fira yana amsa masa sama sama. " Abbu bari na mayar video call "Ya faɗa a hankali kamar mai tsoron maganar. Abbu cike da farin ciki duk da ya san ba wata maganar kirki amma ganin fuskar sanyin idaniyar shi na saka shi farin ciki dan fuskar mahaifiyar shi yake gani a tattare da shi kuma ita take ɗebe masa kewa. Zuba masa idanu Abbu yayi cike da so da ƙauna kafin ya ce " Wai Ni ko kana cikin abinci kuwa MAHAJ?,Dubi yadda idanun ka suka Zurma ,me yake damun ka ".? Gaban shi ne ya faɗi jin tambayar da Abbu yayi masa dan shi kan sa yan kwana biyun nan ya san ya faɗa ko Mubeey bai samu dama bane da ya sha tambaya jiya. Ɗan murmushin gefen baki yayi kafin ya ce " Abbu Stress ne ". Ɗan shiru yayi tare da shanye idanun sa da suke ta walƙiya da maiƙon nan na su. A hankali ya ƙara furta " kuma bana samun isasshen bacci ne saboda presentation ɗin nan ". Ganin yadda Abbu ya zuba masa ido cike da damuwa. Numfashi Abbu ya sauke cikin yarda da maganar sa ya ce '' Allah ya taimaka ya bada nasara,a riƙa cin abinci yan samari har da shi na ramar mini da kai,nafi son ka yi ƙiba ka tara damtse ". Murmushi ya saki mai sanyi yana shafa ɗan wadataccen Gashin kan sa da na gaba yafi ya wa kamar dai irin na india haka ko turawa. Samrah ce ya hango ta shigo da sallama sai dai ganin MAHAJ wanze akan screen ɗin wayar Abbu mai tsada hakan ya sa ta rugo da gudu bata ma ƙarasa Sallamar ba kasancewar Abbu na sai ti ƙofar ne ya bada baya daga zaunen da yake yana karatun jarida a haɗaɗɗen falon na sa. Kai MAHAJ yake ta gyaɗa mata sai uhmm tun bayan yar tambayar ya ya take da yayi mata cike da sakewa da ƙaunar yarinyar. Fira suke ta masa ita da Abbu cike da ƙauna shi dai iyakar sa uhmm uhmm a haka suka yi Sallama ganin da Abbu yayi kamar ya gaji da Surutun Samrah sai dai shi a nasa ɓangaren bai gaji da kallon wayen nan fuskokin ba Surutun ne kawai da zasu zauna haka da ya ji daɗi yayi ta kallon su,dan haka wasu lokuttan yake a jiye wayar ko system yana jin firar tasu sama sama wata rana kuma yayi muting yayi ta Murmushi daga ƙarshe Abbu ne mai datsewa saboda ya san halin kayan sa. Miƙewa yayi gaba ɗaya ya bar wajen cike da tafiyar nan ta sa ta ƙasaita. Babban falon sa ya koma yayi zaman sa yana chan za tashar labarai.Cartoon yake kallo kamar wani ƙaramin yaro ya mai da hankalin sa kacokan kan su yadda ya mayar da hankalin su kan su ka san yana son kallon toon ɗin. A haka har lokacin Sallah yayi alwallah yayi ya fice, a masallaci suka haɗu da mubeey sai dai bai ce masa ƙala ba haka shima sannan ana gama sallah yayi gaba ya ma riga mubeey ficewa. Mubarak kuwa da yake son yi masa magana ne ganin ya fice kamar ya ɗau fushin da ya fi na sa hakan ya sa ya saki murmushi yana shafa sumar kan sa da take shan gyara itama yanayin ta sa dai irin ta matasan mu ta cikakkun Hausawa. " Ɗan Abbu rigima " Ya faɗa a fili kafin ya kalli gefen sa kamar akwai wanda zai ji ko MAHAJ ɗin na kusa.Yar dariya yayi kafin yayi gaba. Abin cin da ake kawo musu kullum wanda sun riga sun yi ordern sa irin abincin nan ne na Chinese da kuka sani dai kayan Ruwan nan,na halittun ruwa (Sea food )sai snacks sune abincin su idan ba su ra,ayin cin na China ɗin,duk da akwai Restaurant mai kyau dake kusa da su da ake kala.kalan abincin Nigeria sai ka zaɓa.Amma saboda sun saba da na China ɗin suke cin abun su.Idan sun je Nigeria su ci na gida. Ganin shi da yayi har an ajiye hakan ya sa ya ɗauki na MAHAJ wanda ya san zai iya ci yanzu ya shiga falon bayan ƙofar ta masa Surutun ta na koda yaushe na maraba musamman shi da ta san shi harda ɗan chat take gwada yi da shi saboda gulma😂,kamar dai yanzu. Haka ya ji tana furta Sir MAHAJ is watching TV toon channel. Na'urar ƙofa mai GULMA sai a KURMAN ƘADDARA 🚴🚴😂Kai fa'eeh shariii🚴 Murmushi yayi kawai ya shige ba tare da ya bata amsa ba. Shi ko MAHAJ da ke zaune bai ma ji shigowar Mubeey ɗin ba dan hankalin sa yayi nisa sosai,Baki sake Mubeey ke kallon sa kenan dai Dagaske na'urar chan ke yi shi yayi tunanin ko tsohon labari ne waton har yanzu yana kallon toon ɗin lallai da aiki gaban sa garjejen ƙato da kallon Cartoon ina lafiya,shi bai ɗauke sa normal ba kana namiji kana kallon cartoon kamar wani Baby. Ɗan gyaran murya yayi hakan ne ya farkar da MAHAJ da ya saki jiki yana enjoying kallon sa. Chanza tashar yayi zuwa ta wrestling da sauri saboda tun chan baya ya taɓa ganin sa sau ɗaya yace masa kayan yara ne fa wannan yallaɓai har ya rika masa tsokana dan haka ya dena kallon su kusa da mubeey ɗin. Mubarak kuwa shanye dariyar sa yayi kafin ya ajiye kayan kan haɗaɗɗen Centre table dake ƙawace da falon kamar dai kujerun.✍️ Jama'a Allah ya shirya muna TA BAIWA.🥺🤲 Shatou i miss You🥺Ta gida na.😍😁 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza

Chapter 26 of 39