tayi wata rashin lafiya sosai Alokacin Baffa na bai ma taɓa tunanin zata iya samun lafiya ta koma dai dai ba.
Da ƙyar Baffa na da Bibu suka iya fita shi ya wuce farauta shi ko ya wuce makaranta,wadda sai da aka rarrashi shi sannan ya wuce harda yan hawayen sa.
Cikin abinda bai wuce daƙiƙa ba jikin Shatu ya ƙara rikicewa Hankalin Inna ni ya tashi matuƙa musamman ganin yadda jikin ta yake jijjiga tsoro abun ya bata wanda ya sa ta zuba ma yar Tata idanun ta kawai tana kallon ta,tana fatan abun ya tsaya nan, kafin wasu hawaye masu zafi su zubo mata dan ko rantsuwa tayi bazata yi kaffa ra ba tsohon ciwon ta ne ya tashi na matsalar jinnu da tayi fama dasu shekaru uku da suka wuce dama shine abinda take gudu tun safiyar yau da ta tashi da matsanancin ciwon kan cikin ɗarr take na abinda kan iya zuwa ya dawo.Riƙo hannun ta tayi.tana tofa mata Addua,a kafin cikin wani irin kuka Shatou ta fara magana ƙasa ƙasa ganin bata jin abun da take faɗa hakan ya sa ta kara kunnen ta a bakin ta " Suna cikin matsala rayuwar su na cikin hatsari,Kuyi wani abu zasu hallaka su,zata samu sauƙi zata samu waraka zata sami lafiya ".
Tana gama furucin kuma sai wani irin bacci ya kwashe ta,mai Nauyi.
Wani irin kuka ne ya ƙwacewa Inni ni wanda ya sa ta durƙushe wa nan tana rungume yar ta cikin wani irin baƙin ciki mara misaltuwa itama take jikin ta ya ɗau zafi saboda kukan da ta yi gashi babu mai rarrashi.........
Meye matsalar Inna ni wai ???
Haba na san a rina shatou ku ba ita kaɗai take ba ahe 😂😂Mai gari ya mata uzuri🚶🚶
Wasa farin girki✍️✍️
Wannan labari na kuɗi ne akan N#1000. Yanzu muna kan free pages, kuma baza,a same su da yawa ba gaskiya dan haka kuna iya fara yin payment.
1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
*08069059746*
Daga
Alƙalamin ✍️
GIMBIYAR TASKIRA 👑
FA'EEH BG ✍️
FIRSTLADY 🙌
LIKE,REACT, COMMENT sune kawai nake buƙata,shine zai nuna mini yadda kuka karɓi book ɗin..✍️
_*Typing*_
Update 👇
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn
*Masu son ganin ƙarshen labarin sai suyi following channel ɗita.👇*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*💋KURMAN ƘADDARA💋*
©®Fa'iza Almustapha Murai
Daga Alkalamin✏
*FA'EEH BG*
💎Sadaukarwa ne ga class mate ɗina ɗalibban GGC T/MAFARA,ZAMFARA STATE SET 2K18.A duk inda kuke Alkhairin Allah ya kai muku.🤲💎
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
_Daga marubuciyar littafin_
*A MAFARKI NASANTA 1&2(paid)#500*
*RAYUWAR MU A YAU complete (free)*
____________________________________
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
___________________
*MUNA TALLATA HAJA KOWACE IRI CE A FARA SHI MAI SAUƘI...*
*BOOK ONE*
free pages👌
P...0️⃣5️⃣
Sai da tayi mai isar ta Sannan ta share hawaye ta tare da gyara ma Shatou kwanciyar ta dan baccin take mai nauyi kuma da alama yayi mata daɗi.Dan rage ma kan ta tunani ne da yake son kutso mata ya sa ta janyo wata tsohuwar saƙar da ta fara ta cigaba da yi tare da ƙara sautin redion da yake fitar da sautin Qira'a mai daɗi ta Sheikh sadiqu Sadiq Gusau.
Tana nan zaune har aka kira sallar la,asar sannan ta miƙe ta gabatar da sallah tare da jerawa Ubangiji damuwowin ta da suka cike zuciyar ta.Tana gamawa ta tsakuri abinci kaɗan Dan bata jin ɗanɗanon sa ko kaɗan saboda yadda zuciyar ta take harbawa tun bayan kalaman da suka fito daga bakin Shatou suka shiga kunnen ta.Duk ta tuno da zantukan sai jikin ta yayi wani irin mugun sanyi sai ta ƙara jin wani irin rauni ya ta so mata.Bata da mafitar da zata iya yin komai akan zancen da Kunnuwan ta suka jiye mata face ta miƙa lamurran ta ga Ubangiji shine wanda ya san damuwowin ta.Zama tayi a kusa da SHATOU tana zuba mata idanun ta wasu irin hawaye masu zafi suka silalo mata wayen da bata ma shirya wa fitowar su ba.A hankali ta ware idanun na ta da suka bayyanar da yanayin rashin lafiyar ta ta sunyi wani irin garai garai ta zuba su kan fuskar Mahaifiyar ta ta da ɗigon hawayen ta ya ɗigar mata a kan fuskan ta, da ta ƙara yin fayau tsantsan yarinyar ta ta ƙara fitowa ƙarara dan Shatou da ace irin gidajen masu kuɗi ne masu sangarta yara da har yanzu babu aikin da ta iya saboda shekarun na ta da kuma girman ta bata da wani girma haka take yar firit da ita.
" Inna ni " Cikin sanyi Sautin ya shiga Kunnuwan Inna ni da ke duƙushe gaban shatoun.Idanun ta ta share da sauri tana goge hawayen da ke ƙoƙarin sake fito mata.Da murmushi ta zuba ma Shatou idanun ta kamar yadda ta zuba mata nata tana ƙaƙalo dariyar farin ciki ganin shatou ta tashi garass babu wani ciwo à jikin ta da alama zazzaɓin ya sauka ma gaba ɗaya." Sannu kin tashi ya jikin,ina yake Miki ciwo yanzu " Inna ni ta jera wayen nan tambayoyin tana shafa fuskar Shatou cikin Tausayin ta.
Kai SHATOU ta gyaɗa mata tana kallon ta cikin ido ganin yadda idanun ta suka yi jaa kaɗan na kukan da tayi a ɗazu.
"Inna ni kawai dan ban da lafiya kika yi kuka haka,?Ashe haka kike so na ban sani ba ".Shatou tayi zancen kafin kuma ta ƙara sa zancen Baffa na dake tsaye a gefe ya sauke Numfashi tare da girgiza kan sa cikin tausayin su.Sannan ya ƙara so ciki yana maimaita wata sabuwar Sallamar dan tun ɗazu ya shigo tun lokacin da Inna ni ta durƙushe ƙasan idanun ta na tsiyayar da hawayen da bai san dalilin zubar su ba a wannan karon duk da ya saba da irin wannan yanayin nata.
Amsa masa sallamar sa suka yi a tare cikin washe baki Shatou tayi masa Barka da dawowa tana miƙewa daga kwance cikin ɗan ƙarfin da ya rage mata.Washe bakin sa yayi yana kallon ta yana furta " Shatou na ta murmuje sosai ko dan da alama Kwana kika yi mai daɗi ".
Murmushi tayi tana gyaɗa masa kai dan ita kam iya sanin ta tunda su Baffa suka fita bacci ya kwashe ta sai yanzu.Kuma gashi baccin ya tafi da ko wane ciwo na ta.
" Masha ALLAH,Allah ya ƙara sauƙi Shatouwa ta ".
Ya furta yana cigaba da murmushi mai cike da natsuwa.Baki ta Turo gaba jin ya kira ta da Shatouwa sunan da bata so,kuma shine ƙaɗai ya ke kiran ta da wannan Sunan.
Kayan farautar ta sa ya ajiye a ma,ajiyar su sannan ya zo ya zauna yana ƙara yi ma Shatou ya jiki tana Amsawa fuskar ta a washe.Inni ni kuwa abun farautar ta sa da ya ajiye ta miƙe ta ɗauka ta ajiye shi a inda ya dace zuciyar ta cunkushe da tunani kala kala.
Baffa na dai idanu kawai ya bita da su yana jin wani Tausayin ta na mamaye shi kafin ya sauke idanun sa ƙasa yana tasbihi Sannan ya mayar da kallon sa kan SHATOU " Baffa Banyi Sallah ba fa,Inna ni bata ta da ni nayi Sallah ba ta bar ni ina ta barci ".Kan ta ya sha fa a hankali sannan ya furta " Inna ni bata kyauta ba gaskiya tashi kiyi Alwallah ai lokacin ta bai wuce ba ''.
Cikin ɗan kuzarin ta kuwa ta miƙe tana washe baki Ruwan da ya ajiye mata yanzu a buta ta ɗauka ta zaga makewayi sannan tana fitowa ta ɗaura Alwallah ɗakin ta ta shige ta ɗaura zani mai girma ta kabbara Sallah.
A tsakiyar gida kuwa Bayàn Tabbatar Da Shatou ta shige ɗakin ta ne Baffa na ya kira sunan Inna ni a hankali. Sannan ya ce " Kiyi Haƙuri A'ie ban matsa Miki ba ki faɗa mini abinda yake damun ki yake yawan saka ki kuka ba,Duk da na san raba ki da kuka yana da wahala a wannan lokaci amma ina son ki sani Komai yana da lokacin sa ki cigaba da Addu,a Allah zaiyi mafita a duk abunda ya tsananta a gare mu,Kuka ba shine maganin matsalar mu ba,Sannan ba zan gaji da faɗa Miki ki faɗi wata alama da zata iya bamu mafita ba,ina son sanin komai da yake faruwa kin ƙi bani dama bare a samu mafita,Àmma duk da haka bazan matsa Miki ba zan bar ki sai ranar da kika buƙaci hakan,Sannan na roƙe ki kar ki taɓa bari Shatou ta san wani abu shekarun ta basu kai na lokacin da zata iya sanin abin da ba zata ji daɗin sa ba,".
Yana gama furucin sa ya shige ɗakin sa ya bar Inna ni dake zaune jikin ta ya mutu mutus domin ta san ba tun yau ba,yake son tace wani abu amma ta kasa sannan duk wasu zantukan da shatou ke yi a lokacin da iskan ta suke tashi bata taɓa faɗa masa ba,tun tana farkon samun ciwon dan sun fi tashi a lokacin da suke daga ita sai ita a gidan.Shin ta ina zata fara ita kan ta ba ta san ta ina zata fara ba bata san komai ba duk yana yin da take ciki tsintar kan ta kawai tayi,wasu lokuttan ta kan rasa tunanin da zata yi amma ta san tabbas duk abinda Mutantanin Shatou suke yawan faɗa mata basu yi mata ƙarya ba,duk wani lokaci sukan faɗi ƙarya,zancen su shine kawai abinda ke natsar da zuciyar ta yake kwantar mata da hankali kuma yake tayar mata da hankali.Numfashi ta sauke mai Nauyi cike da nauyin da ya maƙare zuciyar ta wanda bata san ranar da zai gushe ba.
Shatou Kuwa bayan ta gama sallah sai tayi ajiyar zuciya tuno yadda ta ga fuskar mahaifiyar ta amma kan ta bai iya kawo komai ba sai ma murmushi da ta ƙara saukewa tana jin daɗin wai Inna ni na son ta sosai ashe faɗan ne kawai take mata tana son ta.Sai ta ji zata rage ɓata mata rai ta daina abinda bata so amma fa muddin wani ya taɓa ta sai ta nuna masa ya taɓa ta.dan bata yarda a raina ta kamar yadda aka raina Amina ba.
Miƙewa tayi tana sakin murmushi jin muryoyin su Amina da su Ramata suna sallama duk sun cika gidan ai ko burumm sai gata tsakar gida tana washe baki har ta manta abun da ya faru jiya sai dai tana haɗa idanun ta da su sai ta wani irin shan kunu kamar taga kashi tana bin su da kallo ɗai ɗai sai ta kama Hanyar ɗakin ta tana neman komawa ɗakin ta tino yadda suka kunya ta ta jiyan ƙiri ƙiri suka goyi bayan ƙarya wanda ko da asuba sai da tayi hawaye na baƙin cikin abun.
" Yau na ga shegan taka Shatou ba gurin ki suka zo ba kika kare musu kallo kuma kika shige ɗaki,Kamar ba su Aishan ki ba,wata sabuwar tsirfa ce haka ko me?"
Inna ni tayi furucin bayan tagama ansa gaisuwan da suke mata suma bakunan su washe kafin kowaccen su ta sauke idanun ta ƙasa na rashin gaskiya dama da ƙyar suka zo saboda cike suke da tsoro ko yanzu dan ta kama dole ne rashin lafiya ne da Bazasu iya tunkarar ta ba saboda yadda kowaccen su ke cike da tsoron ta.
Baki ta turo gaba tana zama Kusa da shinfiɗar tabarmar da Inna ni ta musu.
" SHATOU Ya jikin ki,Bibu yace baki ji daɗi ba ".
Kai ta gyaɗa musu kawai tana shan ƙamshi.
" Allah ya baki lafiya,yasa ki ji sauƙi ƙwarai " suka haɗa baki wajen faɗa suma cikin rashin sakewa ganin yadda duk ta haɗe rai sai bai musu daɗi ba sun zo baki washe amma fuska ta sauya saboda yadda ta sha fuska.
" Amin " Inna ni ta amsa cikin murmushi tana bin su da kallo haka ma Baffa na da ya shiryo har ya chan za kaya shima murmushi yayi yana furta " A yafe musu haka Manya, sun ji gata kin ga suma sun san basu kyauta ba ai ".Yayi furucin yana kallon Amina da ta ƙara yin ƙasa da kan ta cike da nadama ga kuma sanyin da jikin ta yayi dan ta tsani ɓacin ran aminiyar ta ta dukkanin su ma haka suke dan ko rigima suka taro itace mai tare musu ko wanda yafi karfin ta ne tana tare wa,dan shi suke mugun ji da ita a tsakanin su,amma kuma idan faɗan su ya tashi a tsakanin su ba,a mai kyau dan shatou bata raga musu.
Murmushi ta saki tana cunno baki gaba.Hararar su tayi musamman Amina da ta zuba mata idanun ta tana jiran jin amsar ta dan ƙirjin ta har bugawa yake yi dan tana azabtuwa matuƙa jiya ko bacci. Kirki bata yi ba har da kuka ta saka wa mahaifiyar ta yau da safe wai shatou fushi take da ita,mahaifiyar ta ta ce taje gidan su ta ka sa,tace sai dai ita taje, ta ce bazata je ba,haka dai ta shirya tayi makaranta tayi shiri da wuri dan ta samu ta haɗu da shatou sai dai cikin rashin sa,a Bibu kawai ta gani wanda ya sanar mata da rashin lafiyar ta Shatou.
" Na yafe musu badan halin su ba saboda Kai Baffa na " Tayi furucin tana jefe ma Ramata Harara,dake washe bakin ta da duk yayi datti dattin da shatou take addabar ta da bakin ta wari yake yi,sai ta gyara ta fara wanke sa yanzu kuwa saboda kwana biyu bata sako ta gaba ba cikin ƙawayen su sai ta koma yar gidan jiya dan yanzu haka bakun yellow yake.
" A'a Shatou ki ya fe musu Saboda Allah kin ji sai ki samu lada,ki riƙa yin abu saboda Allah shine wanda ake yi dan shi a bari dan sa ".
Baffa na yayi furucin yana murmushi.
Kai ta gyaɗa masa na zancen ya shiga kunnen ta da zuciyar ta.
Haka su ma su Amina kai suka gyaɗa kamar da su yake magana.
" Na yafe muku saboda Allah,amma wallahi kuka koma sai na chan za ƙawaye ,kun yarda".Tayi furucin kamar irin Dagaske.
Inna ni kai kawai ta girgiza tana sakin murmushi ganin yadda duk suka haɗa baki waje furta eh suna gyaɗa kai kamar ƙadangarru.Addu,ar shiriya ta musu baki ɗayan su tana sauke numfashi tana kallon su tana jin wani abu a ranta mai girma da raɗaɗi musamman da su ka rage su huɗu kawai a wajen saboda sauran su sun wuce manyan ƙawayen ne suka zo jinya.Hawayen da ta ji suna neman silalo mata ne ya sa ta shige ɗakin ta da sauri ta bar su kan tabarmar suna bawa Shatou labarin karatun da aka yi musu a yau.Na Al'ada wanda malamin ya sanar musu da duk wacce ta fara ganin jini zata iya ɗaukar ciki su riƙa kama kan su dan daga lokacin sun girma zasu iya haihuwa.Haka dai suke bata labarin tana sauraren su tana dariya kafin ta furta '' Wai Jini to ai mu ba zamu taɓa yin sa ba ma har yanzu yara muke,kuma ma taya ciki zai zauna a wannan shafaffen cikin na wa ".Ta kai ƙarshen zancen tana shafa shafaffen cikin ta.Sannan ta ƙara furta " Ai Babu ruwan mu da maza mun san halin mutanen ƙauyen nan ba zan manta abinda aka yiwa yar gidan malam Shehu ba ".Tayi zancen cikin yarinta.
Kai suka gyaɗa mata suma kafin suka yi shiru Baffa na ne ya fito daga ɗakin sa bayan gama cin abinci yana furta " A'i na fita sai na dawo " adawo lafiya ta masa duk da tafiyar bata wuce majalisar su ce zai je.
Amina ce ta riƙo hannun Shatou jikin ta a sanyaye bayan sun yi ma Baffa na a dawo lafiya, tana furta " Dan Allah shatou karki daina ƙawan ce damu kin ji bazamu ƙara ba ".Ta kai ƙarshen zancen kamar zata yi kuka.
" Ai naji kunya ƙwarai da kuka ƙarya ta ni gashi malam Habu yace ƙarya haramun ce,amma kuka rufe ido kuka tozarta ni da girma na " Ta kai ƙarshen zancen da ya sanya Inna ni dariya dake zaune tana cigaba da yan ka naman da Baffa na yayi farauta.Saboda Bata da R sai yana yin furucin na ta na ƙarshe da ta furta ya ƙara bayyanar da rashin R ɗin ta fili.Ƙara jinjina kalmar Inna ni tayi wai da girma na hakan ya sa ta ƙara sakin murmushi tana kallon yar ta ta yar firit da ita amma ita ke zancen da girman ta kamar wata babba.
Ai kin ta cigaba da yi tana sauraren su suna ƙara ba shatou haƙuri wanda bata san abin da ya faru ba sai yanzu dan har yanzu Baffa na bai sanar da ita yadda komai ya wakana ba.Ajiyar zuciya kawai ta sauke bata shiga zancen su ba har suka gama suka chan za firar ta bikin gidan su maraƙisiya da zasu je mamarta ta haihu kuma bikin jibi ne dan yau jiye ne ta haihu da dare.Murna Shatou tayi ta yi dan dama bata gan ta ba cikin su ashe mamar ta ce ta haihu, farin ciki ne ya kama shatou matuƙa wanda har ya bawa Inna ni mamaki dan sosai ta yi murna musamman da ta ji mace aka samu sai ta ji ina ma Inna ni ce ta haihu.Tana cikin wannan mamaki ne ta tsinkayi SHATOU na furta " Ni Inna ni wai yaushe zaki haifa mini Yar ƙanwa Allah ina son samun yar ƙanwa Nida Bibu,kin ga da kin haifa muna ita Allah na daina fita wasa sai muyi Wasar mu cikin gida anan tare ".
Shiru Inna ni tayi kamar ruwa ya cita kan ta ya rufe ɗiff sai kuma cikin ɗan murmushin da ta ƙaƙalo ta furta " Ai Ni shatou na tsufa baki ga harda furfura ba a kaina,kuma kin san tsofaffi basa haihuwa ".
" Laaaah Dagaske Inna ni ai Ni ban taɓa ganin ta ba,Inna ni kan ki fa baƙi wulik yake ai ina buɗe shi na taɓa wata rana idan kina bacci saboda daɗin taɓa sa nake ji taushin sa kamar kayi ta bacci ".
Waro idanu Inna ni tayi tana sauke ajiyar zuciya da firar ta su ta sauya.
Kafin ta furta " Ohh ni Indo gashin nawa ke saka bacci kuma Shatou,ai ga naki nan da baki son a taɓa sai ki riƙa taɓa shi dan naki yafi nawa taushi nesa ba kusa ba kawai na wa kika zuba ma ido ko,zan ma aske shi saboda ke ".
" Wallahi Inna ni ba zaki aske shi ba ki saka naji kunya har fa labarin shi na ke bawa su Amina ko ".
Kai su Amina suka gyaɗa suna murmushi dan suna shan labarin jin yadda gashin Inna ni yake da silɓi wanda suko suke ganin bai kai na Shatou ba saboda akwai ranar da ɗan kwallin ta ya cire bayan sun yi dambe da wata yar aji biyar ta yaga mata hijabi har ɗan kwalin ta ya cire wajen Masifa daga nan suka san shatou ma nada gashi dan bata son ana ko taɓa kan na ta bare a ga abun da ke cikin sa kitso daƙyar inna ni take ma ta shi kuma bai wuce kalaba itace kawai ta iya.
Dariya Inna ni tayi wadda ta ƙara bayyanar da kamar ta da shatou har yar wushiryar su ma iri ɗaya ce.
Itama shatou murmushi tayi mai haɗe da dariya ganin dariyar Inna ni wadda ba kullum take yin ta ba.
" Inna Dan Allah a bar maganar wasa kar ki aske shi wallahi kika aske shi ba zan ƙara fita ƙauyen nan ba dan gori za,a mini ace Inna ta Tal kwabo gare ta ".
A wannan karon Inna ni daƙuwa ta jefa wa Shatou tana dariya.
Itama shatou dariya tayi tana chafke daƙuwar tana shigewa cikin su Amina da suke ta dariya suma gwanin burgewa ganin yadda shatou ke wasa da mahaifiyar ta.
" Allah ya shirye ki Shatou ya baki hankali "
Inna ni ta furta tana girgiza kan ta Dan ta fahimci idan ta biye wa shatou haka zata lalace wajen.
Shigowar Bibu ce ɗauke da Sallama a bakin sa ya dakatar da su da dariyar da suke yi.Zama yayi cikin su cikin farin ciki yana furta " Adda shatou kin ji sauƙi sosai naga kina farin ciki sosai,Naji daɗi ".
Dariya tayi tana furta " Naji sauƙi sosai Bibu baka ga har ƙiba na ƙara da girma ba " .
Dariya yayi sannan ya ce " Wallahi Adda SHATOU ba wata ƙiba kin ga yadda kika rame,girma kuma ai kince bakya son ki girma,dan Baffa na ya ce kar na miki addu,a da sai na Miki Addu,a ki zama Saratu Wada ".
Ai ko su Amina me zasu yi in ba dariya ba ganin yadda ta bata fuska saboda sun san yadda ta tsani sunan.Bibu kuwa shima dariyar yayi yana tserewa bayan Inna ni yana furta Inna Barka da aiki ".
Amsa masa tayi tana furta" Sarkin jan magana ko Allon an kasa ajiyewa sai tsokana na san da ba kai bane da wani ne yake haɗa wacchan rigimammar da saratu da tuni wani zancen ake yi ba wannan ba" ta kai ƙarshen zancen tana kallon shatou dake Hararar Bibu kamar idanun ta zasu faɗo.
Dariya yayi tare da tsalle yana furta " Sai ni na Adda SHATOU guntuwa ".
Yana gama furucin ya shige ɗakin sa da gudu yana dariya.
Har ta miƙe,kuma ganin cewa in ta biye masa haka zai ta ƙara kiran ta ya sa ta dawo ta zauna tana dariya tana furta " Ai in ba tsoro ba mutun ya zo ya faɗi gaba na ".
Inna ni ce ta karɓe zancen tana furta " Ai maza ba sa tsoro,bare Habibullah na ai jarumi ne ".
Baki Shatou ta turo gaba bata ce komai ba.
Inna ni kuwa murmushi tayi kawai tana cigaba da yin aikin ta.Tana jiyo dariyar Bibu daga ciki.Sai taji sanyi dan hankalin sa tashe ya bar gida sai gashi daga shigowar sa ya samu nishaɗi.
Su shatou kuwa firar su suka cigaba da yi kamar babu abinda ya shiga tsakanin su.
Daga ƙarshe ma Inna ni aka tashi aka ƙara ƙalƙalewa gida.Ita kuwa sai kallon su take yi tana murmushi cike da wasu irin tunani ka iri iri.
***GTR👑👑👑
Kafin fitowar ta su wajen lunch ɗin sai da aka kusa yin dambe saboda LINA bayan gama yin wankan ta ƙin fitowa tayi daga toilet ɗin saboda dama tana shiga chan ta yi tsinke,Jin shiru ya san ya REENA buɗe toilet ɗin kai tsaye dan babu motsin ruwa.
Zaune ta isko LINA gaban madubin toilet ta na ta kallon kan ta tana Murmushi tare da jan dogon gashin ta da ta jabga ma ruwa yanzu.
Cike da haushi ganin jikin ta ya ma bushe tana ɗaure da towel tayi zaman ta gashi Ummah tace su fi to da wuri saboda ya'yan su,amma ita har ta zama ta bata kamar ba ɗazu a school ta gama faɗar yunwa take ji ba bayan ta gamo faɗace faɗacen ta.
" Mutun ba wani kyau ba sai iyayi ".
Tayi furucin tana nufar inda set na towel ɗin su suke jere gwanin burgewa.Ko ina tsafff ba zaka taɓa cewa ƙananan yara ke aiki dashi ba,saboda yadda ake kula da tsaftar su.Komai na su tsaf dashi.
" Damar abun kamar mu ɗaya idan ma rashin kyau ne Kinga har ke baki da shi ".
LINA tayi furucin tana wani juya ido gaban madubi tana mayar da gashin ta baya kamar wata ba indiya.
Sai kuma chan kamar an dawo da sense nata ta ta so da sauri tana yowa kan REENA tana furta " Uban wa ne mai iyayi " .
" Wallahi da ba Abba zan zaga ba da sai nace uban ki ".
" Hehehe " tayi wata irin dariya ta na yaƙunar fuska sannan ta ƙara furta " wallahi kin zagan kuma Abba ya dawo sai na faɗa masa,Wawuya kawai ".
Take idanun REENA suka cika da hawaye baƙin cikin ta ɗaya kalmar Wawuya da LINA ke yawan kira mata bata son ta ko kaɗan Dan bata ga inda take wawanci ba amma abu kaɗan sai LINA ta kira mata wawuya abun na ƙona mata rai dan tun bata san ma, anar kalmar ba har ta gane ba mai daɗi bace.
" Wallahi ma rufa Miki da nayi sai na faɗa ma Yaya Kin tafi yawo bayan an tashi breakfast,har sai da aka kusa tashi kika dawo ".
Zaro idanu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 39