nan ba saboda idan ya ce A'isha ta rage shi da wani abu yayi ƙarya.A haka har aka yi Auren kuma gwargwado sun haɗa kan su suna mutunci sosai a tsakanin A'isha da amaryar ta sa Ruƙayya.Ya haɗu da Ruƙayya ne a kasuwa tana kai masa tallan Nono mai kyau.Cikin aminci suka cigaba zaman su babu hayaniya har amarya ta samu rabo ta samu yar ta mace.Aka saka mata sunan Yar uwar Saleh mace ƙwaya ɗaya tal da suka fito ɗaki ɗaya da ita mai suna Sakina wadda yayi kukan rabuwa da ita saboda ya neme ta bai gan ta ba bai san inda ta faɗa ba dan da alama ɓacewa tayi,basu lura bata cikin ayarin ba sai da suka samu kan su a cikin jama'a,kuma har yanzu bai cire rai da sake ganin fuskar yar uwar shi ba.Sakina ta ɓata ne a lokacin da suka yi gudun hijira daga asalin mahaifar su a chan wani ƙauyen Adamawa.
Sakina ta samu kulawa ta ko ina ga yayyen na ta ga kuma mahaifin ta da A'isha da suke kira Mama.
A haka yarinya ta fara girma da wayo har ta gane dukkanin yan uwan ta itama ta tashi cike da gata.
Ana nan kwatsam sai Allah ya ɗauki ran Ruƙayya da tayi fama da masassara ta kwana biyu.
Mutuwar Rukayya ta taɓa kowa a cikin gidan babu ma kamar Sakina tayi kuka matuƙa saboda ta fara yin wayau sosai.Su kan su su Sada da Usman sun ji mutuwar haka ma A'isha da ta saba da Ruƙayya sosai kamar ya'ya da ƙanwa haka zaka ga suna mu,amalar su.Bayan rasuwar Ruƙayya Ciwo ya sako Sakina itama da ƙyar ta sha cikin yardar Ubangiji ta samu lafiya.A hankali ta fara sakewa cikin yan uwan ta tana samun kulawa fiye da wadda mahaifiyar ta take bata haka suka taso cikin so da ƙauna Sakina yarinya mai shiga rai da tarbiyya.
Akwana a ta shi rayuwa ba wuya yau kusan shekara biyar da rasuwar ruƙayya kuma a yau ne Alhaji Saleh ya kwanta dama,sunyi kuka sun ƙoshi cike da kewar bangon su,ana haka kuma Babban shagon sa dake kasuwa ya kama da wuta,babu abinda aka tsira da shi,a kuma dai dai lokacin da iftila'in ambaliya ya afkawa gidan su,cikin ikon Allah sun tsira da rayuwakan su,amma babu maganar kayan inganta rayuwa.Rayuwa tayi wa su A'isha da su Sada zafi babu duk tarin dukiyar su ta bi ruwa sun koma basu da komai sai kayan jikin su da rayuwar da Allah mai rahama ya bar musu.lokaci ɗaya suka fara fita hayyacin su saboda rashin bangon na su ga yunwa da take son sako su gaba.Gashi suna zaune cikin gidan kamar dole saboda yadda yake dawo musu da moment tare da mahaifin su.
Karatun su,na boko na Arabia komai na su ya tsaya chak domin ko taimakon su babu wanda ya iyayi sai wani bawan Allah da yake maƙwabcin Saleh a kasuwa shine mai basu hatsi.A haka rayuwa ta fara tafiyar wa da Su sada babu daɗi koda yaushe cikin ƙunci.ƙara fahimtar rayuwa da suka yi ganin babu mai taimaka musu hakan ya sa suka koma neman na kan su suka shige kasuwa suka bazama nema dama ance zafin nema baya kawo samu to haka dai suke kalato wanda zasu saka a abaki ko bai ishe su ba koda mahaifiyar su ce kawai da Sakina za su yi farin ciki dan sun san sune mafi buƙatar kulawa yanzu..
A haka suka jin gine karatun su suka cigaba da shiga kasuwa suna yin dako da dai duk wani aikin ƙarfi,tun basu iya jurewa har takai ta kawo suna iya yin aikin su babu tsoro zuciyoyin su sun riga sun bushe da neman na kai da abun da zasu rufawa kan su asiri da mahaifiyar su da yar uwar su Abar son su.
Sada da yake babba shine mai ƙoƙarin sauke nauyin gidan duk da shima Usman yana yi amma saboda ba hankalin su ɗaya ba a lokacin.Cikin ikon ubangiji Allah ya fara buɗawa Sada yana samu gwargwado har ya buɗe yar ƙaramar kwntena ta kayan wasan yara cikin hakan ya samu ya saya musu kayan amfani masu yawa tare da yan kayan abincin da zasu iya kai su yan kwanakki.
Sannan ya saka Sakina makaranta tare da mayar da Usman makaranta,sai dai dukkanin su ta gwamnati ya mayar da su.Shi ya jingine ta sa a haka rayuwa ta cigaba da tafiya cike da gwagwarmaya Har Allah ya sa suka fara tsallake wani mataki na cigaba ya ƙara gyara musu gidan su kafin ma gaba ɗaya suka bar unguwar saboda shima Usman yana samu a wajen yan buge bugen sa shima take Allah ya fara buɗe ma sa.A tare suka wuce makarantar gaba da jami'a.Ita kuma Sakina Alokacin tana aji shidda cikin ikon ubangiji suka gama,suka karɓi kwalin su da suka ci gwagwarmaya a fannin business Administration dukkanin su shi suka yi.Ga kasuwan cin su komai dai dai yadda suke so.A haka rayuwa tayi ta tafiya Har Allah ya ƙara sakawa Kasuwancin na su Albarka ya faɗaɗa sosai nan ne suka yanke shawarar sayen ƙaton fili suka yi ginin da bai wuce sashe biyu ba na su wanda kowannen su zai zauna da iyalan sa sai kuma na mahaifiyar su da take tare da Sakina.Ba,a shanye shekara ba dukkanin su suka yi Aure dan babu tserewa a tsakanin su saboda yadda Mama ta sha musu kai.Sada ya auro wata bafillatana yar Borno shi ko Usman ya Auro yar garin Adamawa a lokacin dukkanin su sun haɗu ne da su a wajen yawon kasuwan cin su.Anan ƙasar mu.
Shekara na zagayowa Allah ya albarka ci matar Sada ta samu namiji inda aka saka masa suna Sadam.Yaro ya taso cikin Gata da kulawa ta ko wane gefe musamman ta gefen Sakina da matar Usman yana shan kulawa sosai.Matar babu ruwan ta tana da kulawa sosai sai dai har Sadam ya girma ita bata da komai.Mama mace ce mai saurin fahimta hakan ya sa bata taɓa nuna wa sarakuwar ta ta komai ba ta san Allah ne mai bada wa Alokacin da ya so.Ana haka sai ga wani cikin a gun Matar Sada mai Suna Hajara suna kiran ta hajo haka suka yi ta renon cikin gaba ɗayan su cikin yardar Ubangiji ciki ya taso har ya kai lokacin haihuwar sa.Cikin ikon Allah tana haihuwa sai ga wani santatelelen Namiji Wanda ya kwaso kamar sakina sak yaro ya zo cikin gata ranar suna yaro ya ci sunan sa Saleh.
Haka suka cigaba rainon yaron cikin kulawa.Har zuwa lokacin da yaron yayi wayau Allah bai kawo wa matar Usman mai suna Ramlat ba suna kiran ta Uwani saboda haka dangin ta ke kiran ta dan ta ci sunan mahaifiyar mahaifin ta.
Ana haka sai ga wani ciki ya bayyana ga Hajo kasancewar Saleh yayi shekara ɗaya sai bata damu ba ta cire shi ta cigaba da rainon cikin ta.Lokacin haihuwar sa na yi ta haifi ɗan ta santatelele namiji mai suna Ibrahim tunda ta haifi Ibrahim kuma sai komai ya tsaya chak dama kuma a lokacin tana neman hanyar da zata dakatar.Sunyi farin ciki sosai da samun ƙaruwar haka yaro ya tashi cikin gata kamar sauran yan uwan sa.Hajo dake cike da tausayin Uwani tayi magana da Sada dan ya amince mata ta basu sadam tun da ta ga yadda suka shaƙu da Uwanin shima kasancewar yana Tausayin matar ɗan uwan na sa da ɗan uwan na sa ya amince Sadam ya koma sashen su baki ɗaya.Farin cikin Usman a wannan rana bai da adadi shida Uwani har kukan farin ciki sai da suka yi haka suka rungumi Sadam da ya fara tasawa suka fara mishi gata.A lokacin itama Sakina anyi nata bikin tana gidan ta.Inda ta Auri wani Babban ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa mai suna Aliyu Bukar mai Billions haka ne laƙanin familyn sa yake.Ya ga Sakina daɗewa ne tun a wani taro da suka zo na ganawa tsakanin manyan yan kasuwa anan gidan tare da su Sada ta zo kawo musu abun sha ne tare da Ma,aikata tun da ya ƙyalla ido ya sa a ransa har yayi yadda yayi ya samu shigowa tun da abun ba mai wahala bane sun san juna.tunda ya zo da zancen aka sanar da sakina take ta murmushi,wanda koda bata ce komai ba sun san abun da murmushin na ta yake nufi dan sun san ta da kunya hamdala suka yi cike da farin ciki sannan aka fara shirye shiryen biki ba a ɗau lokaci ba aka yi bikin aka kai Amarya cikin katafaren gidan ta dake cikin Ƙaton gidan na su dan A Bukar mai Billions babban family ne mai ji da kuɗaɗe suma ya samo asali tun da ga ka kan su ne har zuwa mahaifin su Bukar mai Billions,dan Alokacin ma sun fi su SS family yan chanji duk da suma sun tara sosai dan har sai da ya kai ko ina an gine a ƙaton filin na su anyi gini na alfarma da koda yaushe ake cikin sake gyara sa.
Amarya ta shiga cikin dangin ango babu tsangwama ko ƙyara.Sai da ta share shekara biyar zuwa shidda sannan ta samu ciki inda haihuwar farko ta haifi yar ta mace ta ci suna Barirah sunan mahaifiiyar Aliyu.Kafin samuwar cikin kuwa ta fara ganin sauye sauye acikin dangin na mijin ta dan maganganu sunyi ta dawowa kunnen ta akan rashin haihuwar ta,bata ta ɓa faɗawa Aliyu ba sai dai ta sha kukan ta ita kaɗai,sannan ta kan sanar da Uwani saboda itace ta san raɗaɗin da take ji,Uwani sai dai ta rarrashe ta,dan har zuwa lokacin bata samu komai ba duk da sun yi yawo asibiti amma an nuna musu babu komai kawai Allah ne bai kawo ba sai maganukkan da ake bata da zasu iya taimakawa.
Kowa yayi farin ciki da samuwar Barirah yarinya ta samu gata ta ko kowane ɓangare,cike da kulawa.Yarinya bata ko haura shekara da watanni ba sai ga wani sabon cikin wanda ya ƙara sanya zuri'ar Bukar mai Billions farin ciki dan kamar tare ma suka cigaba da rainon cikin Sakina ta samu farin ciki matuƙa ita kan ta kuma ta gode Allah da Ni,imar da yayi mata dan cikin yardar Ubangiji duk wani da ya fara mata magana mara daɗi da barin gefen ta sun dawo Gata da son mutane.Aliyu yayi farin ciki sosai haka ma Mama tayi farin ciki ita da Su Sada.Lokacin haihuwa nayi Aka kwashe ta aka yi asibiti da ita saboda jaririn da yaƙi fitowa, dan wancan haihuwar gida ce,da kan ta ta haihu kuma bata wahala ba kamar wannan.
Ana zuwa a asibiti cikin yardar Ubangiji ta haifi yar ta mace kyakkyawa mai kama da ita sak yarinya mai shiga rai kowa ya gan ta sai yayi Masha ALLAH.Gaba ɗayan familyn biyu sun tsincin kan su cikin farin ciki.Yarinya an mata zanen suna da A'isha taci sunan mama mahaifiyar su sada.Sai dai wani irin tashin hankali ne ya same su suna shirin barin asibiti sai ga ɓallewar jini ta samu Sakina.Cike da tashin hankali kowannen su yake su kan su likitotan ma dan sun kasa tsayar dashi gashi basu samo silar shi ba.Da ƙyar suka gama binciken suka tsayar da jinin ta da rasa sosai dan idan har ba,a yi gaggawar saka mata wani ba zata iya rasa ran ta.Cikin ikon ubangiji aka sanar da su an samu tsaida jinin da doguwar naƙuda ta jawo mata zubar shi.
A Bukar dake zaune ya haɗa zufa farin ciki ne ya mamaye sa shida su Sada da suke zaune a wajen jugum mama ma da ƙyar suka samu ta yarda aka mayar da ita gida.Haka ma Hajiya Barirah mahaifiyar su A bukar.Jini aka saka mata da aka ɗiba ga mijin ta da ɗan uwan ta Usman dan na su ne iri ɗaya.Sai dai duk da haka abin da aka gujewa shine ya auku idan lokaci yayi babu makawa babu maɓoya sai an tafi dan ba,a fi mintuna goma da saka mata jinin ba sai ta fara fisge fisge.
A bukar da ke waje dafe da kai ne hawaye suka silalo masa saboda kalmar da ta faɗa masa yanzu kafin fitowar sa wajen na ta da ta kasa barin tunanin sa.
" Kamin alƙawari idan na bar duniya zaka bawa Yaya Usman riƙon Barirah da A'isha,yanzu ko wata rana zuwa lokacin girman su " idanu ya zuba mata cike da faɗuwar gaba yana niyyar yin magana kawai ya lura tayi bacci kuma da alama ya mata daɗi.Hakan ya sa ya baro ɗakin bisa umurnin likita.
Sai dai kwatsam yanzu Kunnuwan sa suka jiye masa abun da Likitan da ya baro wanda yake shine Babba a team da suke kula da ita yana furta " Allah yayi wa Sakina Saleh Rasuwa " inda ya sanar musu da samun tsinkau tsinkau ɗin da yayi ajalin ta tare da basu haƙuri.
Riff haka suka ji faɗuwar a bu a ƙasa bakowa bane face A bukar.Kan shi suka yi cike da koke koke kowanne su zuciya a ruɗe wasun su ma basu yadda da rashin na Sakina ba...✍️
ALLAH YA JIƘAN WAYEN DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA.😭😭
Wanda bai gane bayanin ba ya samu rufaida yogurt ya sha mai sanyi zai fahimci bayanin🚶🚶🤭😅Ni kaina wani wajen ba fahimtar sa nake yi 😬😁
Dan Allah,kuyi,sharing da comment shine ƙarfin rubutun mu. 🙏
A Wasu lokutan shike sagewa marubuci gwiwa ya kasa iya baku page a kullum.
Wannan littafi na kuɗi ne.
Amma in sha Allah Zan baku page goma sha biyu free kamar yadda nayi niyya..
Masu son fara yin payment zaku iya farawa ga details a ƙasa👇
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh 💞
*_Typing_*
*💋KURMAN ƘADDARA💋*
*©®Faiza Almustapha Murai*
*FA'EEH BG*✍️
*BOOK ONE*
free pages👌
P..0️⃣9️⃣
>>>>>>>>>>>>>> > >>>>>>>>>>>>>>>
*CONTACT DIS LINE👉08069059746 FOR ADVERT.*
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
Channel link
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
Posting room link
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn
*LITAFFAN MARUBUCIYA*
*A MAFARKI NA SANTA*
*RAYUWAR MU A YAU!*
🍃🍃🍃
Haka aka kwashi A bukar sai gadon asibiti.
Har aka yi komai aka rufe margayiya Sakina bai farka ba sai dai Yan uwan ta ne suka yi jagora aka rufe yar uwar su.
A wannan rana wannan ahali biyu sun shiga tashin hankali matuƙa dan har zuwa lokacin A bukar bai farfaɗo ba.Haka ma jikin Mama ya tashi ita ma sai da ta ga likita dan Bpn ta ya tashi wanda ya same ta tun rasuwar mijin ta Saleh.
Su Sada sunyi kuka matuƙa haka ma A Bukar da ya farfaɗo a kwana na biyu yayi kuka kamar zai rasa ransa na rashin mata mace mai haƙuri da alkunya,da Biyayya wadda yake ganin ba zai taɓa samun maye gurbin ta ba a gare sa.
Bayan anyi zaman makoki Bukar ya sanar da Wasiyyar da Sakina ta bar masa duk da bai ce zai cika mata ba amma ya ji a zuciyar sa idan wannan zai saka ta farin ciki dole sai ya aiwatar ya cika mata burin ta.Dan ya san wannan shine burin ta tun farko ta bawa ɗan uwan na ta ya guda idan su samu rabo mai yawa sai gashi yanzu ta roƙi a ba su duka.
Bai nuna komai ba haka duk dangin suka amince mahaifiyar sa ma ce ta so ta hana wanda aka shirya da ƙyar idan sun yi wata ɗaya zuwa biyu za,a mayar da su wajen su ɗin.
Farin ciki kuwa Familyn Saleh sunyi shi kuka Uwani da Usman Saleh suka zauna suka ɓarza cike da kewa da Tausayin yar uwar su da zafin rabuwa da ita dan mace ce mai ƙima da daraja alkunya haƙuri.Haka Sadam da su Saleh, Ibrahim sun yi kuka matuƙa saboda shaƙuwar da ke tsakanin su da ƙanwar mahaifan ta su.
A haka yara suka taso cikin Gata da kulawa ta kowane ɓangare suna cika wata ɗaya kamar yadda aka tsara aka damƙa su hannun Uwani kamar yadda mahaifiyar su ta nema Uwani itace ta cigaba da shayar da Aisha da suke kira Maamaaa dama chan madara a ke bata.Barirah kuwa take ta sake dan bata fahimci komai ba ko chan baya koken ne da ta ga kowa nayi sai neman mahaifiyar ta ya sa ta kuka amma ba dan ta fahimci akwai wani abu ba,sai dai duk dare sai tayi kukan mahaifiyar ta.A haka har suka share watanni ta ƙarasa sakewa.Aka cigaba da rainon su a gidan Usman Saleh wanda tare da Sadam ake yiwa Maaamah komai saboda ƙaunar da yake yiwa jinjirar.Haka Barirah tana matuƙar son yar uwanta.A haka rayuwa ta cigaba da tafiya yara suna ta girma musamman ma Maammaa da take ta sowa itama gwanin burge wa kowa na ƙaunar su ita da Barirah sai dai tafi Barirah samun kulawa sosai saboda tafi ta saurin shiga rai.Da kuma sabo da sakewa ga mutane da faranfaran.Sunyi karatu na Arabia da boko a ƙarƙashin mahaifin Su da suke mugun so da ƙauna tun bayan fahimtar shine asalin mahaifin na su kasancewar ba,a bar shi baya ba gurin kula da ya'yan na sa abun son sa haka ma duka dangin na sa.Dan haka Suka ta so cikin gata basu san wani abu shi maraici ba.Kuma Basu taɓa nunawa Uwani da Usman Saleh basu ne suka haife su ba suna musu kara matuƙa musamman maama bata taɓa zancen mahaifiyar ta gaban Uwani saboda tana da fahimta da wayau,tana fahimtar yanayin da Uwani take shiga suka nuna damuwar rashin mahaifiyar su,suna kiran Uwani da Ummu,kamar yadda su Sadam ke kiran ta.Haka suka cigaba da rayuwa cikin yan uwan su har girman su.
Shekaru sun shuɗe dan lokacin Sadam ya gama karatun sa da ya yo akan kasuwan ci.Ita ma kuma Barirah ta kammala Tata makarantar a secondry.
Mama da Sada suka yanke hukuncin haɗa Auren zumunci a tsakanin Sadam da Barirah tare da shawarar mahaifin su dan dama su matan su basa karatu mai zurfi dan ko sakina da ƙyar suka barta tayi diploma a economics....
Lokaci mai jaaa idan akwai rayuwa a yanzu Saleh Sada ne mai tarin dukiyar da ko shi kan sa bai san kan ta ba,A yanzu yana da mata uku ta farko itace Hajiya Asma'u suna kiran ta da (momy)tana da yaaa ƙwaya ɗaya itace Hamrah,mai shekara goma sha ɗaya da rabi tana a ji ɗaya a junior sec,Dan su Reena suna gaban ta dama kaɗan dan dama sun girme mata kaɗan. Sai mai bi mata Hajiya Sa,ada ita bata samu rabo ba har yanzu.Suna kiran ta Mamy Sai kuma Hajiya Barirah ita tana da ya'ya uku na farko shine Bilal ma,aikacin soji ne yana matsayin Captain shekarar sa Ishirin da biyar sai yan biyu Alina da Sarina,suna da shekara goma sha uku suna aji uku a junior sec sch,Ibrahim Sada kuwa yana da Mata biyu ta farko Sunan ta Maryam Suna kiran ta (Hajiya)tana da ya'ya uku Maza,na farko shine Samir,yana aiki a Custom service,yana da shekara ashirin da huɗu,Sai na biyu Abdul jabbar,yana da shakara sha tara yana Ug II I a Wata Babbar University dake nan jahar su wadda ake zube ma Naira,sai Ayman mai shekara goma sha biyar yana aji Biyu ne a University wadda Abdul jabbar yake yi.Sai matar sa ta biyu sunan ta Ramlat suna kiran ta Momcy tana da ya'ya biyu Junaid,mai shekara sha tara yana aji biyu a University tare da su Abduljabbar suna mataki ɗaya sai dai kowa field ɗin sa daban.Sai Amina (Ninah) mai shekara sha uku suna matakin karatu ɗaya da su Reena.
🍃🍃🍃
*MU KOMA LABARI.*
Suna gama gaisawa da Junaid ya matsa kusa da tsohon yana rusunar da kan sa ƙasa yana cewa " kaina a ƙasa Sir S S ".Saboda haka suke kiran sa da Sir gaba ɗaya jikokin na sa.
Murmushi Yayi yana jan kunnen BILAL yana furta " wane SS ɗin ne uban ka ko ni "
"Ouuch Sir pls " Ya furta yana ɓata fuskar shi.
Murmushi yayi yana cewa " Laifi muka yi ne da za,a shigo aka sa zuwa wajen mu ka san yanzu ƙarfe nawa ne,ohh kana sane ma".
Ya furta jin yana bashi amsa da 4:30pm.
Sakin shi yayi yana riƙe hannun sa na dama yana furta " Ya aikin " ?
" Alhamdulillah Sir ya tsufa ".?
"Tsufa ai sai ku BILAL mu yanzu muke Tashe na bai fi naka ƙwari ba ne " Dariya Bilal yayi yana furta " Haka ne Sir ai yanzu kake tashe ma " Ya kai ƙarshen zancen yana sakin guntuwar dariya.
Dai dai isowar su Abdul Jabbar da Ayman a wajen suma fuska cike da farin ciki suka rungume Bilal ɗin suna haɗa baki wajen gaishe sa.Shima cike da murmushi ya amsa musu yana musu yan tambayoyi game da karatu suna amsa masa gaba suka yi bayan sun ɗan yi barkwanci tare da gaida Sir.
Har Sashen sa ya kai shi anan ya tarar da Hajo zaune tare da mama da tsufa ya mayar da ita kamar yarinya komai sai anyi mata Uwani da ita suna ƙoƙari akan su duk da yadda su kan su tsufan ya taso musu amma suna ƙokarin faran ta ran surukar ta su.
"Ja'iri sai yanzu ka ga damar shigowa ko,ai ko Badan mu ba kana shigowa ka ga Uwar ka " Tayi zancen tana Murmushi tana nuna Mama da ke tauna goron da Hajo take daka mata a wani ƙaramin dutse mai kyau guda biyu wanda aka sawo mata shi tun da ga saudia kuma idan ka ji kuɗin sa zaka jima kana mamaki,shi an yi shine kawai saboda tsofaffi irin su da ba komai suke iya taunawa ba saboda yadda haƙoran su suka yi taushi,suka koma kamar dasashi irin dai na yaro ƙarami.
Ƙasa yakai yana murmushi tare da riƙo hannun Mama yana furta " Tsohuwa mai ran ƙarfe,Allah ya ja da rai da nisan kwana,ya ƙarfin jikin ".
Fuskar shi ta shaafa tana furta " Ɗan ga ne,ka dawo me ka yo mini tsara ba,ya aikin ka ".
Ta jero zantukan da sai ka kwantar da hankali zaka ji fitar su a bakin ta.
"Ina nan Mama".Yayi zancen yana riƙo hannun ta.
" Me ke kika so dan ban siyo komai ba,irin na ki keda Hajo ma,da Sir "
Da ƙuwa Hajo ta sakar masa tana furta " Ai mu bamu yi wannan tsufan ba,baka gan mu garass ba ko goro Bama ci ".
Ta kai ƙarshen zancen tana tauna goron da ke hannun ta wanda bata daɗe da fara cin sa ba.
Dariya yayi yana kallon Sir da ke zaune yana kallon su yana murmushi musamman mahaifiyar sa da ke ta mamular bakin ta tana tauna goron da Hajo ta ke daka mata tana Murmushi tana sauraron abun da BILAL yake faɗa.
Itama Hajo murmushin ta saki.
" Ina son kilishi Samiru baya nan dama shi yake sayo mini shi "." Bani son na nan gidan bai min daɗi "
Ta kai ƙarshen zancen tana ƙara damƙe hannun sa.
" Kilishi kike so Mama,gashi ance likita ya hana ki cin jan nama Ba zaki haƙura ba ".
" A'ah nidai ka sawo mini Likita bai isa ya kashe ni ba,sai lokaci na yayi,Koh Sada ".
Kai Sir ya girgiza kawai saboda sun yi sunyi su hana ta abun ya gagara saboda tana fama da sugar likitota suka yi suggesting tabar cin nama jaa.
Ga su da naman kowane iri a gida har kilishin da sabo da tsoho kullum sai masu kula da Sashen nama sun yi shi dan haka akwai sabo akwai tsoho.Amma bata son shi saboda rigima sai na waje.
" Sir me ya sa kuke barin ta,lafiyar ta fa na iya ragwanta ".
BILAL ya yi zancen yana kallon Sir .
Numfashi Sir ya sauke shima cike da Muryan tsufa ya furta " Ya zamuyi har kuka take sakawa sauƙin ta ma shi kaɗai take nema,dan ta san Samir na sayo mata shi ya sa da ya zo sai ta Masa zancen ".Sai ya sayo mata a sace tun bamu gane ba har muka gane aka masa faɗa amma da ta buƙata sai kowa ranshi ya jagule sai ta yi ta kuka,gashi bata cin na gida ko bata aka yi ta san ba wanda take ci bane ".
Numfashi BILAL ya sauke kafin ya furta " Mama zan nemo Miki shi kin ji ki kwantar da hankalin ki,dan saboda tana jin abun da yake faɗa har ta fara hawaye saboda bata da wuyar kuka.
" Yawwa yawwa nagode Bulal Allah ya jiƙan magabata ".
Ta kai ƙarshen zancen kuka na sake mata.
Jikin su ne yayi sanyi suma babu ma kamar BILAL saboda wani giɓi ne ta soso masa da yake zagaye da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 39