Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Sai ta watse firar ta sanya su shirin makaranta dole haka suka shirya suka wuce gashi yanzu lokacin zuwan bai ƙara sa cika ba ma amma saboda sun ishe ta ta ce su tafi kar suyi lattti.Haka ko suka fito suka wucewar su kowa fuskar sa turneƙe babu ma kamar Bibu dan bai gama gyaran da yake yi ba aka ce su tashi su wuce dan sallah kawai sai abinci da suka ci ya sa ya tashi daga aikin ita kuwa sana,a guda domin kuwa ɗiyan toton rake ɗin sun kusa goma kuma duka nata ne,haka take bin su layi layi kamar an zo gidan kitso tana kitse musu gashin wasu ayi musu hannu biyu,wasu zane. Yau tun asuba haka ta tashi da a hargitse Saboda ciwon ya motsa gashi ta rufe ɗakin,Babu wanda ya ankara da halin da take ciki sai Nana da take kwana da ita a ɗayan wani ɗaki dake cikin bedroom ɗin dan ƙofar shi Anan take.Kamar ta dai irin hanyar da Suhail yake biyowa daga part ɗin. Duk yadda Nana take kururuwa babu wanda ya ji ta saboda ɗakin a rufe yake,ta kasa buɗe nata ta kawo mata ɗauki saboda tsoro duk da ta na jin yadda take faffasa komai da ya ke na fasawa da wanda bana fasawa ba a ɗakin.Gashi sai wani irin Dariya take ban kawa tana cigaba da aikin hargitsa ɗakin dan abun da bai wuce mintuna goma ba ta lalata komai da ke cikin ɗakin.Ta daɗe hakan kafin Nana ta ji shiru dan haka koda Nana ta ji haka cike da tausayin ta ta buɗe bedroom ɗin na ta tana leƙowa sai dai a matuƙar razane ta saki wata irin Mahaukaciyar ƙara domin kuwa Ba kowa ta gani gaban ta ba face Ishaa Tsaye fuskar ta jina jina sai soshe soshe take yi tana ganɓalan dariya,ga kayan jikin ta duk sun lalace nan kwalba ta shige nan ta fasa ko ina ta ji ma kan ta rauni. Ai kamar jira take yi dama shine tsayin da tayi ta faɗa cikin bedroom ɗin kamar an jefa ta sai ga Nana ƙasa tana neman agaji domin haye ruwan cikin ta tayi tana nusar ta,bugu na fitar hankali cikin abun da bai wuce mintina uku ba ta mayar da Nana kamar ta dan har kayan jikin ta ta yayyaga. Rayyan da ya shigo ta ƙofar bayan ne ya ji kamar sautin kuka na ta shi sanin cewa suna da mara lafiya a gidan hakan ya sa babu tsoro ya fara ƙoƙarin tura ƙofar sai dai kamar an buɗe Kunnuwan sa tarr ya ji kukan Nana,dai dai lokacin da Nana take sakin wata irin ƙara kuma a lokacin ne Allah ya bashi ikon sanya spare key dake maƙale a chan kan wata yar fulawa mai kyau ta yan gayu da ya zaro. Da Inna lillahi ya matsa wajen yana cigaba da Nana ta sunan Allah domin kuwa wuƙa ce Ishaa ta ke riƙe da ita wadda bai san inda ta samo ta ba.Cike da tashin hankali ya ambaci sunan ta " Ishaa "Ganin ko juyowa bata yi ba ta kalle sa hakan ya sa ya ƙara furta " MA'ISHA " shiru ta masa sai dai tana nan tana yaƙen nan da wasu marasa hankali suke yi.bata juyo ba sai da yayi mata kira biyu sannan ta juyo tana saita mishi wuƙar da take ta sheƙi dan da ganin ta sabuwa ce dall. Dariya ta ɓalle da ita kafin ta ce " Sai na kashe su,sai na kashe su dukkanin ku,bana son su ". Kafin gurin ƙara riƙe wuƙar da kyau ta yanke hannun ta.Jini yana ɗai daga cikin abinda yake bugar da ita a duk lokacin da ta gan shi yana zuba haka da sauri idan an samu ozzz sai kan ta yayi ta sarawa ko a cikin haukar take ta asali ko sama sama.Dan haka cikin abun da bai fi secconi ba sai gata ƙasa luuuu.Da sauri Rayyan ya taro ta yana ƙwala kiran sunan ta cike da tausayi ƙanwar ta su.Hawaye ne suka wanke masa fuska ganin yadda jinin yake zuba wani ƙaton ɗan kwalin Nana da yake yashe gefe ya yajawo ya ɗaure mata hannun sai dai babu sauƙi dan haka babu wani kuzuri jikin sa jin kamar bata numfashi.Sun kasa saboda ciwon MA'ISHA sun kasa aminta bata taɓa samun lafiya, kasancewar ba,a san dalilin ciwon ba har yanzu bare a yi maganin sa. Da ita ya faɗo Babban falon Amoh yana share zufan da take keto masa. Da Suhaila ya fara cin karo wadda ta fito ɗaukar wani abu ta saka ma cikin ta dan bata da jimirin yunwa tun fil azal. Ƙara ta saki mai tada hankalin mai hankali kafin ta sulale wannan ƙarar kuwa itace ta ankarar da Amoh da Alhaji Sardauna.Wanda suke kira Dady. ALHAJI IDRIS SARDAUNA. Shine cikakken sunan Dady,ana kiran sa Hon Sardauna daga abokan aikin s,da kuma wajen gari,Saboda kasancewar sa Minister mai kula da har kar Noma,a gida ya'yan sa suna kiran sa Dady,Amoh Cikakken sunan ta Amina yara da dangin ta suna kiran ta da Amoh. Amoh nada yaya Biyar Babba shine Suhail sai mai bi masa Suhaila,sai kuma Rayyan sai Kuma ƙaramar su MA'ISHA Wadda suke yiwa wani irin mugun so sai dai lalura ta musu shamaki sai dai duk da hakan suna iya kar ƙoƙarin su na bata kulawa yadda ya dace yadda bazata cutu ba bare ta cutar da wani,Amoh ko da yaushe cikin kukan zuci take na damuwa da ɗimuwa yanayin da yar ta ke ciki.Haka Dady kowa dake gidan yana ji da MA'ISHA sosai.Dukkanin Wannan a hali suna zaune ne A buja a cikin Ministers estate inda su MAHAJ suke.Suhail yana da ya kammala degree ɗin sa a fannin likitanci tun shekarar da ta gaba ta wanda Bama aƙasar nan yayi karatun ba,Yanzu yana aiki a wata Babbar private hospital dake nan Abuja, Suhaila kuwa yanzu take kusan kammala degree ɗin na farko,Sai Rayyan shi yana ug 2 ne a jami'a tare yake da Suhaila a school ɗaya,MA'ISHA ba,a ma zancen ta dan bata samu ilmi ba saboda yanayin ciwon ta ko school ba,a saka ta ba,saboda yadda abun ya taɓa ta dan tun tana ƙarama take da abun kamar yadda muka sani tun farko.Dan haka kowannen su yake jin mugun tausayin ta.Duk da haka kuma Suhail yana iya ƙoƙarin sa dan shi ya koyar da ita sign kamar na kurame kafin ta samu damar iya yin magana dan wasu lokuttan har bakin na ta bai iya yin magana,Kuma yayi ƙoƙarin sanya mata Abcd sai dai ba lallai yanzu ta iya kawo su ba.Su Suhail sun taso cikin Gata kamar yadda iyayen na su ke ƙokarin faranta musu,da basu tarbiyya gwargwadon ta Addinin Musulunci... Da wani mugun sauri suka sauko daga benen kowannen su fuskar sa cike da tashin hankali babu ma kamar Amoh da duk guiwowin ta sun Sage saboda tashin hankalin abun da ta hango dan kuwa Kuka Rayyan yake yi kamar ƙaramin yaro ya kasa yin komai ga Suhaila kwance ƙasa a sume ga kuma hannun MA'ISHA na reto alamar babu rayuwa a jikin ta.Daddy Ma koda ya iso wajen hankalin sa yayi matuƙar ɗagawa da abinda idanun sa suke gane masa dan ga alama ta bayyana babu lafiya dan ko ina na jikin ta jini ne wani wajen shatin kwalba sai inda yafi tada musu da hankali inda ta yanke dan ɗan kwalin da ya ɗaure ne yake ta tsiyayar da jini saboda yadda ya tsuma. Daddy bai tsaya wata wasa ba ya zari car keys dama a shirye yake da Jallabiya jikin sa saboda basu jima da dawowa daga masallaci ba. Hannun Rayyan ya karɓe ta da sauri dan shi kamar ya zama hoto haka ya koma sai dai ya kalli MA'ISHA ya kalli Suhaila ya ƙara ɓarkewa da kuka. Bayan Daddy ya bi da kallo yana ɗan dawo wa hayyacin sa ganin Suhaila da Amoh ta watsawa ruwa ta dawo dai dai tana sauke numfashi kafin ta ɓarke da wani irin kuka mai ban tausayi da katse zuciya. Riƙota Amoh tayi kafin ta taimaka mata ta zauna sannan ta juya da sauri ta koma sama ta ɗauke hijab Babba ta ɗaura akan kayan Kwanan dake jikin ta. Shafa bayan Suhaila tayi da ta rafka ta gumi kafin ta fice sai dai bata karasa ficewa ba sai ga Rayyan ya dawo yana furta " Amoh Nana,aje duba halin da take ciki ".Cikin sauri Amoh ta juya ta koma zuwa ɗakin a sume ta isko Nana da ta yi zaton kwanan ta sun ƙare.Ruwa ta Yayyafa mata bayan ta kunna hasken ɗakin kan ta ta dafe da wani irin sauri da ya sara mata saboda ganin yadda komai ya koma upside down.Hawaye ne ta ji sun silalo mata.Ta sanya Nana ta kwashe Kayan kwalaben nan, amma bata san yadda ake dawo da su ba dan toilet ko cikin lockers nan aka ce a mayar da su saboda yadda zasu iya zama illa a gare ta.Saboda sun lura idan so ɗari za,a cika madubin sai ta hargitsa komai kuma hakan bai taɓa damun su ba sai ma ƙara son ganin sun gyara rayuwar yar su. Tuno yadda ta ga kwalabe duk sun soke ta hakan ya sa ta runtse idanun ta da ƙarfi tana share wani hawayen da ya zubo mata mai zafi.Wani rauni ne ya ƙara bayyanar mata ta san muddin da ace Suhail yana nan sai ya fi kowa shiga tashin hankali dan haka ba zata bari ya san da zancen ba,saboda duk yafi shaƙuwa da Ishaan ta. Dan haka ta sauke ajiyar zuciya bayan dawowar Nana cikin hankalin ta tana ta sauke numfashi tana jan Ajiyar zuciya. Nana kuwa a tsorace ta miƙe tana neman guduwa tana cewa " Dan Allah MA'ISHA ki min rai bani bace wadda kike nema,bani ce ba kar ki kashe ni "...Ta kai ƙarshen zancen tana ɓarkewa da kuka bayan Amoh ta janyo ta tana bubbuga bayan ta. Kafin tace. " me kike nufi da bake bace wadda take nema "? " Ta ambaci sunan wani ne hala " " Ehh kamar haka " Nana ta bawa Amoh amsa jikin ta na rawa saboda tsoro tana mugun tsoron yanayin MA'ISHA sai dai tana kaunar ta matuƙa Allah ya ɗaura mata son ta,dan haka ko ta so ta ajiye aikin sai ta kasa dan haka take kula da MA'ISHA da zuciya ɗaya cike da so da ƙauna kuma ba yaune ta fara yi mata irin hak baa,sai dai na yau ya bata tsoro ganin ta da yuƙa sabuwa. " Tou Ikon Allah Sunan wa kika ji ta kira Nana " ???✍️✍️ # Wannan labari na kuɗi ne #800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣2️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* ____________________"Banji ba sosai Saboda na suma a lokacin amma kafin na ƙarasa fita hayyaci na,naji tana ƙara nanata sai ta kashe su,sai ta kashe ta,sai kuma bakin ta da na ga yana motsi a hankali tana faɗan wani suna nidai na kasa kawo shi Amma kamar yana tashi da Ta...,daga nan ban ƙara sanin abun da yake faruwa ba." Nana tayi furucin cike da kalamai masu nuna tausayi dan Dagske tana jin Tausayin Ishaa Matuƙa. Amoh ɗan numfashi ta sauke bata jin daɗin rashin jin ƙarashen sunan ba dan ta so ta ji sunan wa ta kama dan su har yanzu basu yarda da ciwon Ishaa ba saka hannun wani bane saboda yadda suke fafutika kan neman maganin ta amma abun babu gaba babu baya.Sai dai basu matsa ba sun dage da yin addu'a da miƙa lamurran su ga Allah shi ya jarabce su kuma shi ne zai yi maganin matsalar a lokacin da ya so. Taimaka ma ta Amoh tayi suka fice a tare dan itama tana buƙatar ganin likita saboda yadda ta ji raunuka. Suhaila ta yi driving na su dan su Rayyan da Daddy sun wuce. A Chan a sibiti kuwa saboda sanin mahimmancin su Dady da matsayin da yake dashi da irin shares da yake da ita kaso biyu,na asibtin,aka karɓi Ishaa cikin sauri da karrama wa,da kulawa aka fara bata taimakon gaggawa domin dama duk sun san ƙaunar Dr.Suhail ce wanda sun san da ace yana nan shi zai kula da ita a gida ma ba sai anzo nan ba sai in abun ya ɓace.Cikin ikon Allah an samu ƙwararrin likitota suka hau kan ta sun ɗauki kusan awa ɗaya suna duba ta kafin suka samu Dawowar Numfashin ta da dai dai tar bugun zuciyar ta.Alluran bacci suka yi mata mai ɗan karfi saboda yadda jinin ta yake dan zata iya farkawa yanzu ba tare da tayi mata wani aiki ba. Haka Ita ma Nana an karɓe ta anyi mata treating raunukan ta kamar yadda aka yiwa Ishaa nata aaka tsaftace mata jikin ta. Tunda aka sanar da su halin da take ciki yanzu suke sauke nunfarfarshi kowa fuskar sa babu yabo babu fallasa sai dai tana cike da damuwa mai tarin yawa wadda suke jin babu ranar gushewar ta sai ranar da suka samu lafiyar yar su. Rayyan ne ya sauke waya akan kunnen sa bayan ya gama waya da ɗan uwan sa da ya kira shi hankalin sa tashe saboda samun labarin halin da take ciki da Wani daga cikin friends ɗin sa Doctors ya sanar masa an kawo ƙaunar sa ciwon ta ya tashi,ta ji ma kan ta ciwo .Bawan Allah take hankalin sa ya tashi seminar da yaje yi yaji zai iya barin ta duk da kasancewar ta mai matukar Amfani dan International seminar ce sai dai a nan Nigeria za,a yita,Lagos.Kwantar masa da hankali Rayyan yayi kafin suka yanke kiran sai dai ya san cewa bai lallai ya saurare sa cewar da yayi masa da sauƙi ba. Dan haka kai tsaye ya sanar da Daddy halin da ake ciki. Shiru Daddy yayi kafin ya ce " kira mini shi ". Babu musu kuwa Rayyan ya danna ma ñumban ta sa da yayi saving Yaya Suhail. Ringing biyu ya ɗaga dan baya wasa da lamarin ahalin sa musamman abun da ya shafi Ishaaa saboda yadda suke mugun Tausayin ta. Miƙa wa Daddy wayar yayi ba tare da yayi Magana ba.Shiru yayi jin Dady na kiran sunan sa yana furta " Na san halin ka,kar ka baro abun da ka je yi zamu bata kulawar da ta dace,kaji ko,ta samu lafiya sai abun da ba,a rasa ba,Allah ya taimaka " . Ɗiff ya kashe wayar,Dan bai son ya masa wata magana,duk da ya san bazai Musa ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana ajiye wayar bayan ya gama ƙare mata kallo kamar zai ga komai a cikin ta.. Numfashi ya sauke yana komawa ya zauna daga tsayen da yake bakin window yana shaƙar iskan da yake kaɗawa mai daɗi yana ji kamar yayi tsuntsuwa ya samu kan sa a cikin asibitin.. Dady Saboda yana da wani meeting da zai yi hakan ya sa ya bar su Amoh nan sai dai yana fitowa yayi murmushi ganin securites nasa da suke tsaye cogai cogai. Bata re da yace komai ba ya shiga motar da ya tuƙo da kan sa sai dai a wannan karon wani daga cikin su ya tuƙa ta. Amoh ma gida suhaila ta matsa mata ta koma saboda yana yin jikin ta ga ciwon ƙafafu da take fama dashi dan haka kai tsaye aka mayar da ita gida inji ɗai daga cikin securites da aka bar musu. Nurse Mira da bata san abun da ke faruwa ba ta zo gidan sai dai tun abakin gate ta samu labari ga securites cewa an fita Ida Ishaa amma Hajiya da Alhaji sun dawo dan haka cike da tashin hankali ta faɗa gidan.A kitchen ta tarar da Amoh tana bawa masu kula da girki umurnin abun da zasu yi wadda bata daɗe da shigowa ba. Amoh fuska cike da damuwa ta faɗa mata duk abun da ke faruwa,kamar yadda Nana ta mata bayani yadda ta fara,Hawaye ne suka wanke mata fuska cike da tausayin Ishaaa. " Bari na je na gyara komai kafin su dawo da ita,kuma fa na cire duka kwalaben turaren nan na mayar da su toilet ban san wanda ya dawo mata da su ba anan kan mirror ". Tayi zancen tana mamaki gashi Itama Nana ta ce wa Amoh ba ita ta jera su ba.Dan haka sai suka yi ta mamaki da tsoro domin sune abinda suke ji mata ciwo a tashin farko idan ciwon ya tasar mata. " Nikaina abun yaɗaure mini kai ". Amoh tayi furucin fuskar ta cike da damuwa. Nurse Mira da ta rasa abun cewa ne ta ce " Allah ya bata lafiya,Amoh bari na yi sauri,ina son naje a asibitin " . Kai Amoh ta gyaɗa mata tana wucewa itama tana wuce wa bedroom ɗin ta. Wani irin hawaye ne ya ƙara wanke mata fuska ganin yadda ɗakin ya ƙara hargitsewa komai ya farfashe ya koma kamar ba,a taɓa zama a cikin sa ba har ta mirror ta fasa shi ga kwalabe nan zube an farfashe wanda ita kanta idan bata yi ta ka tsantsan ba zata jima kan ta rauni.Dan haka babu jira ta cire hijab ɗin ta ta lankafe sannan ta koma ta ajiye jakar ta a ɗakin Nana da shima farkon shi a hargitse sai da ta shiga ciki ma ne shima ta ga ga kaya nan a watse. Cike da rashin kuzari na Tausayin Ishaa ta fara gyara komai bayan ta kwashe kwalaban turaren da suke masu kuɗi saboda manya ne dukannin su babu karami sai Shegen ƙamshi da ɗakin yake ta yi saboda yadda turarukkan suka watse akan carpet da ta mahe ɗakin. Tsaf ta gyara ɗakin ta sanya sabon bedsheet dan wanda aka cire ko kwana biyu bai yi ba.Dan jiya Nana ta saka mata shi.. Dai dai ta gama Amoh da masu girki sun kimtsa komai dan ba wani abu mai wahala aka yi ba irin wanda zata iya ci ne ruwan zafi sai masan ƙwai da irish da suka soya mata irin mai haɗe da kayan miya da kuma ƙwai a cikin sa. Nurse Mira kuwa kwasar kayan tayi ta fice da su inda dama bata saka motar ta a garage ba dan haka ta jata ta fice. Koda ta isa Nana ta ɗan wartsake saboda ruwan da aka ƙara mata ta samu ɗan ƙarfin jiki.Sannu ta yi mata cike da tausayin ta tare da furta Allah ya tsayar nan da tsare gaba ya bawa Ishaa lafiya. Da Amin duk suka amsa mata har Suhaila da ke zaune jugum dan yanzu ta baro sashen da Ishaa take har yanzu ta lura ko motsi bata yi,babu abun ke raba ta da gawa face ɗan ƙirjin ta dake ɗagawa tayi fayau da ita gashi dama ba wani auki ne da ita ba. Haɗa ma Nana shayi tayi ta haɗa mata duk abun da ta san zata buƙata,Babu musu dama yunwar take ji dan haka ta fara cin abin ta hankali kwance dan ta saba mafi yawan lokuttan da ta kwana gidan a tare da mutan gidan take breakfast sai dai in ya kasance Suhail na kusa ita kan ta gizagon sa take gani dan haka take ka sa iya motsi duk yadda za,a ce ta zauna bazata zauna ba sai dai a saka akai mata ɗaki,har ya kai ta saba mafi yawan lokutta a tare da Ishaa suke yin breakfast ko lunch wanda ake kare shi alalala ce dan ita Ishaa babu hankali ita kuwa sai ta yi ta biye mata,suyi ta haukar a tare. Cike da kulawa Nurse Mira ta isa ɗakin na ta cikin tausayi ta ƙare mata kallo tare da share ƙwalla sannan ta mata Addua ta rufo ɗakin. " Ta Baiwa kin halaka,arniya,Ta Baiwa baki da imani,ta Baiwa magajiyar baƙin aljani,baƙin duhu ba naki bane " ..Ya kai ƙarashen zancen yana gaggaɓan dariya mai tsoratar wa dan duk wani cikakken mai lafiya dariyar tsafff zata iya mayar da shi mara hankali dan abun tsoro ce. Kamar ko yaushe zaune take gaban shi ta tanƙwashe ƙafafun ta cikin baƙar a baya da uban niƙab wanda yake fallasar da manyan idanun ta dake ciki,sai dai ba su bayyana sosai ba dan wanda ya santa ma sai yayi da ƙyar ya gane ta. Dariyar take gaggaɓa itama wanda ya Kaita har ƙasa kwance kafin a cikin yar bukkar ta sa da kullum take upside down sai dai inuwa ta ko ina duk da ranar da ake watsawa a cikin ƙungurmin dajin. Sai da tayi mai isar ta tana taya shi sannan ta yi shiru ganin ya sha fuska,ban sani ba ko dama dariyar limit gare ta Amma haka wajan yayi tsit har kukan tsuntsaye ma babu a wannan karon. " Ta bai wa faɗi damuwar ki da bakin ki,ke nake son jin yadda abun ya dame ki,duk da ɗan duna,da baƙi sun faɗa mini komai,faɗi Damuwar ki a yaye miki,ina son ki ta Baiwa ke ta amana ce, imani da aiki na shine ke ƙara mini ƙaunar ki ta Baiwa tare zamu halaka "... Ya saki kukan jarirai mai ban tsoro wanda sai kayi zaton ba shi ke yi ba dan kukan bana jariri ɗaya ba ne. Cike da ƙwarin gwiwa da rashin tsoro da rashin damuwa ta ce " Ɗan Baiwa maganar gizo ce bata wuce ta ƙoƙi kuma na san kasan da haka,abun na ƙara ƙuntata ni,Yau naga haske gobe na ga duhu,ya kamata ayi wani abu dan bana buƙatar mai mai ta magana ɗaya Ɗan Baiwa,a wancan karon har su duna na bawa a shayar da su jini amma ban ga wani Haske ba sai duhu da yake ƙara da baibaye ni " . " Ni yanzu Babbar Damuwa ta ma,kan wannan munfukar matar ne a yi mini maganin ta ta cika shige mini hanci da yawa ". Ta kai ƙarshen zancen tana jan dogon tsaki. " Hhhhhhh ta Baiwa ke makakka ce,ai irin su ba da wuri ake kame su ba,ita kan ta ba tsaye take ba haka nan,Rame mara zurfi ba wurin ɓoyon ɓera bane,ki riƙa nazartar wasu abubuwan,zan Miki maganin ta,zamu saka yan jajaye su karya ta,idan har tana taƙama da wani abu ". Ya kai ƙarashen maganar yana ganɓalan Dariya. Ita ma dariyar take yi tana " ho na Baiwa Ho Na Baiwa " tana yi kamar tayi masa Sujjada. Muryan sa ce ta katse ta yana cewa " Ta Baiwa ban riƙe ba kar ki mini Sujjada " . Dariya tayi kafin tace " Ɗan Baiwa ko ita kake so zan maka,nidai burina ya cika,ya kasance daga Ni sai shi zamu mallaki komai muyi rayuwar mu mai cike da jin daɗi da soyayya,dan ba zan yarda aiki na na shekaru ya tafi a banza ba " " Duhun da yake bi na Ɗan Baiwa a cigaba da neman hanyar Haska shi,ya kama ta muga abun da ke ɓoye ". " Idan har wata matsalar ce sai mu rufe ta da wuri ". " Kar ki damu ta Baiwa,aiki an gama duhun nan bana matsala ɗaya bane ,kuma ina ga dunƙulallun Abubuwa ne a cikin sa,amma zamu cigaba da bincike,waccan matsalar kuma an kusa kai ƙarshen ta,komai zai zamo tarihi,Haihuwa da shi kamar anyi an gama duk wanda yayi wannan kutsen ya ci nasara amma zamu warware aikin dole zaki samu Magaji,ko ajiyar aljanu ce sai kin haifa " Yana kai ƙarshen zancen ya ƙara sakin wata mahaukaciyar dariya kafin ya jawo ƙwarya ya ƙara nuna mata abun da ya nuna mata ranar wanda ya ƙara sanya ta farin ciki mai girma. Cikin farin ciki bayan ta gama kece Wa da dariyar ne ta bude wata yar jakar ta ta ciro masa bandir na manyan kuɗade yan dubu rafa biyar kamar dai zasu kai dubu ɗari biyar. Wani ruwan ya ƙara bata a gora tare da wani irin turare mai ƙarfi dan da ta shaƙe shi sai da ta lumshe idanun ta kan ta ya ɗan sara saboda kaifin ƙamshin sa. Haka ta cusa komai acikin jakarta tare da wasu irin ƙulle ƙulle da ya bata ta fara sakin dariya tana zagin shi tana yabon shi. Tana cewa " Shege,Shege ne,ɗan iska, ɗan iska ne,Ɗan gado ka wuce gado,Baiwa ta Allah ce,Amma kai mai nasara ne,nayi imani da kai kaine

Chapter 17 of 39