yadda idanun suka sake rufewa dan bai ga alamar taji jiki ba.
Cike da tashin hankali Ummah ta yanka masa marin da sai da ya kusa ɗauke wuta.Amma ko gizau sai ma rufe idanun sa da yayi yana sauke ajiyar zuciya,yana haɗiyar baƙin ciki bibbiyu zuciyar sa ji yake kamar tayi bindiga ta fasa ƙirjin sa asan baƙin cikin dake mamaye da ruhin sa.
Bulalar ta ƙwace da sauri ran ta ɓace tana batun bashi damar fita kawai ya sa kai ya fice cike da mugun sauri kamar zai yi tuntuɓe.Kukan LINA har tsakiyar zuciyar sa sai dai bai da damar hana kan sa hukunta ƙanwar ta sa saboda abun na ta yayi yawa lamarin ya fara bashi tsoro ace yan biyu ciki ɗaya kamar Annabi da kafiri babu wani sassauci ko ragi.
Part ɗin ya bari gaba ɗaya yana tafiya kamar ya tashi sama.
Bai zame ko ina ba sai asalin na sa part ɗin.Cike da zafi da ƙunar rai ya sakarwa kan sa shower yana sauke ajiyar zuciya tare da huci mai zafi da raɗaɗi.Sai da ruwan suka shiga jikin sa sosai har kayan jikin sa sun fara ɗiga sannan ya kashe yana ɗauro wanka tare da fitowa sharp sharp yayi shirin sa cikin uniform na sa da suka ƙara masa kyau bai yi sallama da kowa ba ya haɗa abun buƙatar sa ya fice tare da sauran yaran sa.Dan gaba ɗaya ji yayi baya buƙatar ganin komai daya danganci estate ɗin musamman ya san Ummah sai tayi fushi da shi dan haka ba zai iya jura ba Gara yayi gaba yayi ba zai iya jurar abubuwa da dama ba.
A ɓangaren Ummah yarda bulalar tayi cike da tausayin LINA ta rungume ta dan ta daku kukan ma ta daina sai zubar da hawaye da take yi a galabaice dan ta ma fi REENA da kuwa.Toilet Ummah ta faɗa kamar zata zubar da hawaye ta haɗa mata ruwan wanka masu ɗan ɗimi sannan ta tada ita da taimakon ta suka shige toilet ta bar ta ta yi wanka da kan ta dan taƙi yadda Ummah ta mata wanda sai abun ya ba ummah dariya wanda ka raina da hannun ka gashi har yanzu bai wuce wanka ba shine da ɓoye ɓoye kamar wani girman tayi.fitowa Ummah tayi ta bar ta tayi wankan Sannan sannan ta haɗa mata shayi mai kauri tare da bada umurnin kawo mata bread da sauran kayan karin kumallo masu kyau.
Tana fitowa ta sanya kaya masu ɗan nauyi saboda zazzaɓi da ya fara saukar mata a jiki na azaba.Da dabara Ummah ta shayar da ita shayin saboda sai wani sabon babin kuka ta buɗe mai cike da shagwaɓa.Maganin da Ummah ta bata kuwa ta kanne shi ƙasan harshe ita kuwa Ummah ganin ta kora ruwa bayan ta saka maganin ba tare da wani musu ba duk da tayi mamaki sai ta ji daɗi dan ta san yadda ake rigima da ita kan magani.Rufa mata tattausan duvet Ummah tayi bayan ta hau gadon da ta so ta zille wai ɗakin ta take so da ƙyar Ummah ta rarrashe ta ta zauna kusa da yar uwar ta zata ji daɗi idan ta farka.Fitar Ummah keda wuya ta buɗe idanun ta tare da ciro ƙwayar maganin da ta ɓoye a ƙasan harshen na ta.chan ƙasan katifa ta ɗaga kaɗan ta sanya shi dan har ya fara watsewa.Ya ƙune fuskar ta tayi kafin ta miƙe ta shige toilet ta kuskure bakin ta.
Sai a lokacin ta kallo kan ta gaban madubi yadda jikin ta yayi Jawur abunka ga fata mai haske ko ina shatin bulala ne.Hawaye ta ji sun silalo mata masu zafi da ƙuna,babu ma abun da ya ƙara gudun kukan ta tuno yadda ta mayar da REENA cikin ƙanƙanin lokaci ita kan ta abun ya bata tsoro dan idanun ta a rufe suke bata san ta aikata ba sai dai Allah ya kawo Ummah da ƙila sai dai ta kashe yar uwar ta,da ita ma ko sai dai ta kashe kan ta.Ta bawa kan ta amsa daga tunanin na ta.
Sai da tayi kukan ta na ƙuruciya da tausayin yar uwar ta kafin ta fito ta je ta kwanta take bacci ya kwashe ta mai nauyi.
***" Ɗan Baiwa Wallahi ina cikin farin ciki dan haka na kasa haƙura na same ka,ɗan baiwa aikin nan bai wargaje ba yana nan,babu abun da ya chanza,da kace sun je Hutu, na kasa yarda ashe dagaske ne,lallai na yarda dakai Ɗan baiwa na yi imani da kai,Lallai kai abun ruƙo ne dole na zube maka manyan chanji yau dan nuna murna ta " " ga na ka gana jajayen aljanu da baƙaƙe a yi musu yan ka a zubda jini su sha su ƙoshi yau ranar su ce hhh ta kece da dariya ".
Macen da ke durƙushe gaban wani yaƙususasshen mutun mai zubin bokaye take zancen, dan babu inda yayi kama da mutanen kirki ko daga inda yake zaune zaka fahimci cewa Boka ne mai saɓon Allah mara imani dan bukkar da yake kai ita kan ta Abar kallo ce Dan upside down take kuma duk da haka rana bata kan musu sai ma wata irin inuwa da ke zagaye da rumfar mai cike da wasu irin surƙulle ɗaure ɗaure gwanin ban tsoro,ga wani irin sauti mara daɗi dake fita shi ba kuka ba shi ba dariya ba,amma matar nan babu alamar tsoro atattare da ita dan da alama ta saba da gurin kuma gurin zuwan ta ne.
Dariya ya kece da ita kafin ya natsu amma dariyar ta cigaba da tashi itama kamar sabon kamu ta riƙa dariya,dariya ta ƙeta harda hawaye.
Wata irin ƙwarya ya nuna mata abun da ta gani ne ya sanya ta ƙara sakin wata irin mahaukaciyar dariya harda kwantawa ƙasa.
Miƙewa tayi zaune jin yana furta " Natsu " Cikin wata birkitacciyar murya mai ban tsoro.
Idanun ta ta zuba masa daga cikin baƙar abayar da take saye da ita da baƙin niƙab da idanun ta kawai zaka iya hange a ciki.Cike da rashin tsoro haka take bin shi da kallo cike da azarɓaɓin son jin abun da zai furta.
" Ai na faɗa Miki ta Baiwa,kin ƙi yarda,sai ma kin so ki watsa muna ƙasa,dan har sun hasala sun so a cire Miki aikin zana,amma tun da kin yi imani da mu kin sha haka muke so mu ɓace tare hhhhh ".
" Kinga yadda kika ga haka haka zasu koma a duk inda suke,mai iya cire wannan aikin sai ni hhh aikin mugaye kenan,ki kwantar da hankalin ki,zai kai ga ci ".
" Sai abu naga ba akwai wani duhu da yake bibiyar ki,shima zamu Miki aiki kan sa,zamu cire sa kar ki damu,Zamu bi hanyar da ta dace idan ta kama muyi farfesun ɗan sabon jariri da naman alade dan mu haska wannan duhun muga abun da ke cikin sa "
"Ungo wannan"
Ya furta yana miƙa mata wata irin gora tana ɗauke da fararen ruwa sai dai ga wasu irin halittu nan na yawo a cikin su kamar tsutsotsi.
" Kin san abun da zaki yi da wannan ɗin ba sai an maimaita Miki ba ki tabbata komai ya tafi yadda ya dace ".
" An gama Ɗan Baiwa,ɗan gado kafi gado,ko waya ja da kai sai ya bar duniya aikin ka ya ci dubu,babu abun da ke karya ka sai ikon ka,shine ajalin ka ".
Tana gama zancen ta juya bayan ta ta ɓace ɓatt tana sakin wata irin dariya ta ban tsoro.
。☬☬。☬。☬☬。
Tun da ya dawo daga ɗakin motsa jiki yaga fitar sa tare da yaran na sa cike da mamaki ya ke bin motocin da kallo har suka bar harabar gidan aka wangale musu gate.Kai ya girgiza dan ya san bai saba hakan ba yayi kwana ɗaya ya wuce ba tare da yayi wa kowa sallama ba.Tunanin da ya shigo sa na ƙila kiran gaggawa ne ya samu hakan ya sa ya cigaba da tafiyar sa yana sauke gajiyar da ya kwaso tare da ta tsufa da take tattare da jikin sa.Hankalin sa ne ya kasa kwantawa hakan ya sa yana shiga Sashen na su bayan ya zauna ya ce " Uwani bani waya ta ".
Miƙa masa wayar tayi tare da ruwan sha da ta ajiye ɗauko masa masu ɗan ɗimi saboda an hana sa shan abu mai sanyi haka ma an saka shi yawan motsa jiki saboda sugar dake barazana a jikin sa.
" Ina kwana Yaya ".
"Lafiya lau,An tashi lafiya ya ƙarfin jiki " Sir ya amsa daga chan ɓangaren dan ba su samu haɗuwa masallaci ba ɗazu.
" Alhamdulillah yaya jiki sai na tsufan mu na ji sauƙi ".
Murmushi Sir yayi yana furta " Allah ya sa mu yi kyakkwan ƙarshe ya raya muna zuri'ar mu ".
"Amin" Ya amsa harda Uwani da ke gefen sa dan wayar handsfree take.
" Yawwa Yaya nace ko Lafiya,naga BILALU ya fice yanzun nan bayan na baro wajen ɗan motsa jikin Nan da Turawan chan suka tilas ta mini,kuma kamar tafiyar sauri ce zai yi "
" Shi BILALUn ai bai yi Sallama da kowa ba tun da har kai ma ba ka yi magana dashi ba,to Allah ya sa lafiya,ta yuyu tafiyar gaggawa ce a ka kira sa,amma na san ko ta waya ya na sanar wa ko ɗayan mu ne,bar shi zuwa anjima zan kira sa muji ko lafiya idan bai kira ba. "
Sallama suka yi kowa na fatan Allah ya sa lafiya ce ta fitar da BILAL gidan tun da safe ba tare da yayi sallama da kowa ba...
乁✿༼✿☯‿☯✿༽✿ㄏ
A ɓangaren Ummah wanka ta fito tsaf ta shirya cikin shigar ta mai kyau da ke ƙara fitar da ainihin kyaun ta da kamala.
Falo ta dawo cike da bada umurni take bawa su rabi umurnin abun da take son a girkawa su REENA wanda ta san favorite na su dan in ba haka ba ta san da ƙyar su ci abin ci.
Class teacher ta su ta kira bayan ta zauna akan cusion cike da mutun ta wa suka gaisa sannan tayi mata bayanin rashin zuwan na su LINA school sun tashi babu lafiya gaba ɗayan su.Cike da tausaya wa malamar ta musu Allah ya sauƙaƙa tare da furta dama yan biyu haka suke ai ciwo lokaci ɗaya suke yin sa bare su da suke Identical.Sallama suka yi ta ajiye wayar.
Miƙewa tayi tana barin wayar nan tare da shigewa kitchen dan ganin yadda suke gudanar da komai dan ta san BILAL bai da jimirin yunwar safe.
🕳️🪐🕳️🪐
A ɓangaren SHATOU kuwa da ido tsaitsaye take kallon motocin har suka fice daga makarantar, kallon da ya jefa mata yanzu bayan miƙewar sa na dawo mata,duk da kallo ne na ƙasan ido ta san na rainin wayau ne bai san dama shima cike take dashi ba,Hararar bayan sa tayi wanda shi Mubarak ya gani kai kawai ya girgiza lamarin yarinyar na bashi tsoro bata da tsoro ko kaɗan,sai dai abun da bai sani ba Hararar a kan idanun sa ta sauka saboda ya ɗan juya kaɗan yana kallon yadda take durƙushe babu tsoro akan fuskar ta,kuma ya san cewa dole zasu iya hukun Tata tun da malaman ta ne.
Suna fita ta miƙe tana kakkaɓe hijab ɗin ta cike da ɓacin rai take furta " Wallahi Iro bai isa ya saka ni abu nayi ba ko yanzu biyayya ce nayi ga Malan Bello,amma wallahi Indan iro ne sai dai a yi gunduwa gunduwa da nama na ".
Duka zuba mata idanu suka yi musamman ma iro da malam Bello da bata taɓa haɗa sa da ita ba yana dai jin labarin rashin jin ta idan wasu daga cikin ɗalibbai suka shiga gonar ta koda kuwa wayen da suka wuce ta da aji ne.
Iro da ke cike da Haushin ta ne har yanzu gashi malam Yusi ya ƙi cewa komai ya ce " Dan Allah a hukun Tata,bata jin magana,Ni bari muje na isar da saƙo ga mai gari ".
Yana gama zancen yan gayar sa su huɗu da ya zaɓo ya zo da su suka take masa baya yana ƙara bubbuɗawa yana ƙwambo yadda kuka san marigayi ɗan Ibro na yi in ya fito mai kuɗi.Har wani doro yake yi.
Sai dai ko tako biyar bai yi ba yaji ta kece da wata irin dariyar wadda ta fi ta ɗazu domin har da kwanta wa tayi tare da dafe ciki.Tsaye yayi kafin ya juyo ya Kalle ta ya je fa mata harara tare da ƙyafci sannan ya gyaɗa kai irin na zamu haɗu.
Ita kuwa SHATOU da ta ɗago ta ƙara kallon sa ne ta ƙara sakin wata dariyar tana nuna sa.Dan harda ƙeta take haɗawa saboda abun da yayi mata ko ta hakan ta bar shi ta san ta rage hasahi,dan haka take yi ta ƙure sa.Dan tun bata nuna kai tsaye dashi take ba har ta fito fili harda nunen sa da tayi yanzu.
Malam Yusi shi kan shi ya dara Badan komai ba sai dan ita kan ta dariyar ta Shatou abun a dara ce musamman idan ka kalli wanda take yiwa dariyar sai ka kasa riƙe dariyar ka yadda yake zuba ƙwanbo da kuri da yayi masa yawa harda wani aski aka yi mai kama da ci chan ci chan gefe gefe an chanye aka bar tsaka da yar suma sai dai ba da yawa ba.
Barin makarantar iro yayi ran sa jagule su kuwa yan zugar sa sai zuga sa suke yi na yayi maganin ta,ko ya basu dama in suka gamu da ita hanya su karya ta.Sai dai bai ce musu komai ba shi kaɗai ya san irin abun da yake tsara wa a ransa da zai yi mata.
Ita kuwa SHATOU yana fita ganin tabar hango ƙurar sa ta miƙe tana mayar da sauran dariyar da ta yi mata saura kafin ta fashe da kuka dan ta san tsaf za,a iya hukun ta ta gata da tsoron bulala bata son abun da zai taɓa fatar ta.
Malam yusi da su Malam Bello da duk wanda ke gurin idanu suka zuba mata ganin ta fashe da kuka na ƙwarai lokaci ɗaya kamar ba ita ta gama dariyar ƙeta ba yanzu.Sai abun ya bawa Malam Bello dariya ma dan haka ya cewa malam Yusi a bawa SHATOU aiki kawai gobe tayi shara.Hankalin malam yusi kwantawa yayi dan dama bai san ta yadda zai hana malam Bello zane ta ba dan bai iya duka ba in yaro ya shiga hannun sa gashi shi an bashi saƙo mai kama da amana.
Sauran ya ran kuwa gida aka ce kowa ya koma dan sun aikatu.SHATOU kawai aka bari kafin itama aka sallame ta bayan malam yusi ya rarrashe ta.
Idanun ta ta goge kafin ta sakarwa malam Bello harara ta gefen ido wanda malam yusi ya gani sai dai kawai ya girgiza kan sa.
A chan bakin makaranta ta tarar da su Amina da Bibu da ya kasa tsaye sai zagaye yake yi hankalin sa tashe.
Fitowa tayi tana Murmushi kamar ba ita ta gama kuka ba.Zuba mata idanu suka yi kowannen su na kallon ta baki sake kafin suma su saki murmushi.Haɗe rai tayi ganin dukkanin su suna murmushi basu ma ji Haushin abun da aka yi mata ba kenan.
Gaba tayi bata kula kowa suko cikin sauri dukkanin su,suka bi bayan ta suna kiran sunan ta kafin ta zunduma a guje,suma suka mara mata baya shi Bibu ma sai da yayi dariya kamar kar ya daina sannan ya bi bayan su dan lamarin yayar ta sa na yau dariya yake ba sa mace kamar mai aljanu...✍️
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
*_Typing_*
*💋KURMAN ƘADDARA💋*
*©®Faiza Almustapha Murai*
*FA'EEH BG*✍️
P..1️⃣4️⃣
*BOOK ONE*
~PAID~
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Follow my accounts*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eeh Bg*
Tunda suka kamo hanyar barin ƙauyen yake jan hayaƙin Shisha kamar zai shanye sa duka.
Mubarak ne ya Kalle shi ta cikin madubi cike da ɗan girmamawa kamar yadda shima yake basa na sa girman ya furta " Hayaƙin nan yayi yawa zai iya tada maka da ciwon ka fa ".Idanun sa ya ɗago ya kalli Mubarak kafin ya lumshe idanun sa sannan ya cigaba da zuƙaar abun sa dan kan sa yake jin yana cigaba da sara masa kamar zai rabe gida biyu.
Sai da ya zuƙa iya zuƙa sannan ya cire ta ya tura ta mazaunin ta inda ya Fiddo da ita.
" Yallaɓai MAHAJ "
Mubarak ya ambaci sunan sa dan ganin ko lafiya ganin yadda yake sauke numfashi.
" My name is MAHAJ not yallaɓai MAHAJ ".
Ɗan shiru yayi kamar ba zai yi magana ba sannan ya ƙara cewa cikin shaƙaƙƙiyar Muryar sa mai sanyi dan ta cikin maƙoshi yayi zancen.
" This is the last time da zan gyara maka sunan nan Muby,I really don't like yallaɓai,yallaɓai is for the elders, Right".
Mubarak dai murmushi yayi kawai yana satar kallon sa ta madubi kafin ya furta " noted sir ".
Idanun sa ya ware ya kalli Mubarak da ke tuƙin sa hankali kwance,yana Murmushi.
Rufe idanun sa kawai yayi bai furta komai ba.Dan ya fahimci Mubarak ba zai iya kiran sa da sunan sa ba,duk da kuwa ya girme sa dan zai bashi shekara kusan biyar,amma bai da abokin magana bayan mahaifin sa,sai Mubarak,sai ko ɗan uwan sa idan yana ƙasar,ko in sun haɗu duk da ba magana yake yi ba sosai daga uhmm Yes,sai ok,a'a,sune kalaman da yafi an bata,sai abun da yafi ƙwarewa da shi zancen kurame dan tun Mubarak bai gane wa har ya fara ganewa kuma ya fahimci haka halin sa yake na miskalanci.
Haka suka isa cikin garin Abuja a cikin a katafaren gidan na su dake cikin ministers estate ginukan ne na alfarma sun tsaru iya tsaruwa kamar ba Nigeria ba ko ina Naira ta zaunu.Babu bincike ganin tambarin motocin aka bar su suka shige ana ɗaga masa hannu dan sun san ko waye ne ya shigo,dama dokar estate ɗin ce in ka fita ka dawo sai an bincike ka,ko baƙo aka yi sai ya sha bincike har ya gaji kafin a bar shi ya shiga.Dokar kenan amma saboda shine Babu mai tare sa dan sun san fitinannen yaro ne da baya daukar raini ko kaɗan Dan yanzu sai ya ce fitowa zai yi ya sa a chanja musu gurin zama,dan ɗan gata ne ta ko ina duk wasu ministoci dake zagaye da su suna ji dashi saboda akwai basira da dattako a gare sa duk da baida wasu shekaru kuma a hakan yana da na sa share a cikin estate ɗin dan babban ɗan kasuwa ne bai zauna haka ba,ganin mahaifin sa na dashi,ya tara dukiyar da shi kan sa yanzu ba bi ta kan ta yake yi ba a wannan shekarun na sa.Yanzu haka yana karatu ya kusa haɗa masters ɗin sa na farko,duka a fannin business dan dama burin sa ne yin business dashi ya tashi tun yana ƙarami,har ya samu goyon bayan mahaifin sa,ta fannin karatun sa.Mubarak shine wanda mahaifin sa ya taɓa haɗuwa dashi a wata tafiya da yayi yana cikin halin taimako sai ya taho dashi nan ya taimake sa, sai ya damƙa masa kula da Mahaj da kasancewar su tare tun yana shekara sha biyar a duniya a haka har suka fara sabawa tun bai sake dashi ba har ya sake dashi,kuma kowannen su na girmama wanin sa da bashi matsayin sa,mafi yawan duk tafiyar da zasu tare suke yin ta har ta karatu mubarak dashi a school ɗaya suka yi,sai dai shi Mubarak tun da ya haɗa degree na sa yace ya gama boko duk yadda ko MAHAJ ɗin ya so ya ga yayi ya ce kan sa ba zai iya ɗauka ba.
Dai dai wani ƙaton gate mai kama da wata duniya guda aka wangale musu gate bayan ganin motocin na su ta cikin CCTV dake aiki anan wajen da ciki wanda duk wanda zai shigo ana kallon sa kafin a tantance sa.
Haka motocin suka shige cikin ƙaton compound ɗin na alfarma dake ɗauke da shuke shuke masu kyau wasu ganyayyakin daga nin su Bama na ƙasar nan bane yanayin ginin yayi kama dana turawa komai atsare dai dai motocin sun gama parking ya fito ba tare da ya jira ma an buɗe masa ba.Bai yi magana da kowa ba sai kallon Mubarak da yayi kafin ficewar sa a motar dan haka kai ya sunkuyar kawai alamar ya gane.Cikin ƙaton falon ya shige da yar ƙaramar Sallamar sa yana ya mutsar fuskar sa mai cike da rashin annuri da ta haɗe tun bayan shigowar su cikin estate ɗin.Raɓa su yayi ya wuce cike da izza Ganin hakan ya sa bai iya ce masa komai ba sai ma cigaba da maganar sa da yayi da mutanen da yake tare dasu,ba kowa bane face abokan sa yan siyasa da suke tattaunawa kan wani isssue na harkan siyasar su." Ko zaka je ka duba sa kamar ba lafiya ba Hon gagara " ? Babban mutumin da ke zaune daga cikin mutanen uku ya furta ganin hankalin sa ya rabu gida biyu.Numfashi farin mutumin da aka kira Hon Gagara ya sauke a hankali yana bin bayan sa da murmushi.Kafin ya furta " ƙyale sa gajiya ce kawai kasan yadda abun yake,Nima ina son na ɗan huta shine na tura sa,dan dama ya kama ta ya fara shiga mutane ina tsoron wani abu ya kamu da wani ciwo ne kasan Indai ya zo ƙasar nan Hutu haka nake fama dashi baya iya zuwa ko ina ". Shigowar Mubarak ce ta dakatar dashi daga maganar da yake yi.
Har ƙasa Mubarak ya duƙa ya gaishe su cike da girmamawa.Cikin jin daɗi Hon Gagara yayi masa sannu da zuwa tare da yan tambayoyin ya komai ya wakana nan take kuwa Mubarak ya zayyane masa komai dan ya san dama shi ne zai yi aikin ba dai shi ba.
" Dama kuma shine zai yi aikin a cikin aljihun sa amma yace kar a faɗa maka ".
Mubarak ya kai ƙarshen zancen yana kallon ƙofar inda ya san zai iya ɓullowa kasancewar ɗakin sa yana da ƙofofi daban daban.
" Kai Masha ALLAH "
Hon Marafa ya furta yana cewa " Allah yayi albarka gaskiya koda yaushe ina taya ka farin cikin samun wannan yaro,dama zai iya shiga siyasar mu da munci riba sosai dan daga nin sa zai iya da kowane Shege ".Ya kai ƙarshen zancen yana dariya.
Hon Gagara da fuskar shi ta kasa daina bayyanar da murmushi ne ya girgiza kan sa cike da ƙaunar ɗan na sa ya furta " Baya ra'ayin ta da a ce yana da dama Ni kaina ba zan yi ta ba,sai dai yana girmama abun da nake so kamar yadda nake girmama na sa a matsayi na na mahaifin sa dan haka ma tun farko ban taɓa kwaɗai ta masa ba tunda ya nuna mini nikaina baya son ta da ni ".
Su ma sauran murmushi suka yi suna jinjina kai.
Mubarak kuwa miƙewa yayi cike da Murmushi.
Yayi musu sallama Sannan ya miƙe ya bi bayan Mahaj ɗin da wayoyin sa a hannun sa.Upstairs ne na alfarma mai kyau ya take da ɗan sauri.
Wata haɗaɗdiyar ƙofa ce ta alfarma ya bi inda sai da yayi yar tafiya sannan ya isa dai dai wata ƙofar mai kyau da tsari.Buɗe ta yayi a hankali.Ƙamshin ɗakin ne da ya daki Hancin sa ya san ya sa rufe idanun sa dan jin kamar an yi masa buɗaɗen turare bayan fitar su,wanda bai rasa na saba da yawan gyaran da yake samu daga wani daga cikin masu kula dashi. Sanyi ta ko ina lif lif sai tashin ƙamshi yake yi.Kasancewar babu wani shamaki tsakanin su hakan ya sa ya shige ciki da sallama ɗauke a bakin sa,bayan buɗe ƙofar.
Tsitt haka ɗakin yake dama bai yi zaton zai same sa nan ba hakan ya sa ya a jiye masa su nan ba tare da ya neme sa ba.
Ajiye komai yayi sannan ya fice bayan ya rufo masa ƙofar.
🔏🔏🔏
SHATOU bata da kata ba sai da ta yi gudu mai nisa Sannan ta dakata tana sauke numfashi tare da bin su da kallo daga nesa dan ta musu nisa sosai,kawo War su kusa da ita ya sa ta sakin dariya cike da ƙuruciya ta shammace su ta ƙara falfalawa a guje tana waigen su.Su Amina kuwa a gajiye kowannen su ya dakata suna kallon juna,Kafin suka mara mata baya suna dariya.Dan sun fahimci yan wasar ne suka motsa take son wahalar da su.Dan ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 39