kan yi musu haka a wasu lokuttan.A ɓangaren SHATOU kuwa ɗan wannan lokacin ta ji ta tsinci kan ta cikin nishaɗi kamar ba ita ta gama kuka ba ɗazu.Da gangan ta bi gefen da ta san abokan Iro suna zama duk da ba hanyar ta bace aiko aguje ta biyo hanyar tana kururuwa " Kura! Kura ! kura! " da farko basu tsorata ba sai dai ganin yadda take waigen bayan ta sai suka yi zaton wajen farauta ta kuskure ta biyo ta,duk da sun gan ta da uniform,A guje suka miƙe dukkanin su ganin Dagske take yi dan har da hawayen ƙarya irin na tashin hankali, A guje suka miƙe har wasu na faɗawa kan wasu ba su kaɗai ba har majalisar dattawa dake chan wata rumfa zaune a guje ko wannen su ya fara neman hanyar gudu dan tsira da rayuwar sa,tun da har ita yar mafarauci ta iya gudu su mai zai su tsaya a guje, aiko akayi ta kururuwa ana faɗawa gidaje.Iro da ya kamo hanyar zuwa majalisar ta su bayan isar da saƙon ga mahaifin sa ya an kara da abun sa ke faruwa ganin mutane na ta gudu ana kura ta gudo daga daji ta biyo SHATOU da farko tsaye yayi bai yarda ba sai dai bayan hango ta a guje itama kan ta hakan ya sa ya auna a masifar gudu yana waigen bayan sa cike da wani mugun tsoro da ya dirar sa tare da tsine ma shatou da ta jaji ɓo musu bala'i.Shatou kuwa da ta hango sa ƙara ƙarfin gudun ta tayi tana sakin ƙarar neman taimako tana haɗiye dariyar ta wadda take saki idan ta faki idon jama,a masu gudu.Mai gari da jama'ar sa dake ƙofar gida cike da farin cikin saƙon da ya same sa ya ga Iro a guje yana faɗin kura ta yi ɓatan hanya daga daji ta biyo SHATOUn Jibril farauta yadda zasu gane kai tsaye aiko ko rufe baki bai yi gaba ɗaya suka runtuma a guje suna neman gurin ɓoyo.
Daga mai gari har yan fadar sa wani ɗaki suka rufe suka shige duk uban zafin da ake tsulawa a gari.Tsit haka garin ya koma kamar anyi mutuwa.
Cike da natsuwa ta shiga gida cike da murmushi a kan fuskar ta kamar an biya mata aikin hajji dan wani daɗi take ji musamman ganin yadda ta rama abun da Iro yayi mata cikin ruwan sanyi duk da har yanzu nata huce ba amma kina komai ta saka shi tiƙar gudu..
Ummah ce ta ke ta kallon baki sake kafin ta iya furta wani abu sai ga su Bibu sun faɗo a guje su huɗu.
Amina ce ta baya saboda ta gaji sosai.
Shessheka suka dinga yi a gajiye.Inni da ɗai ɗai take bin su da kallo ganin yadda kowannen su yake a hargitse cike da tsoro gashi da alama gudu ne Suka yi bana wasa ba.
Kallon SHATOU suka dinga yi harda leƙen ta suna cigaba da sauke numfashi.
" Me yake faruwa ne,ku ka shigo gidan wani hargitse kuma daban daban " .?
Inna ni tayi tambayar kafin su bata amsa sai ga Baffa na ya shigo fuskar sa cike da tashin hankali mai girma.Dan ko sallama bai samu ya yi ba sai ganin sa suka yi.
Idanu ya zuba ma SHATOU ganin ta hankali kwance sai murmushi take saki, kafin ya mayar da idanun sa kan su Bibu suma sai dai su tasu a tashe take sai nishi suke saukewa.
"Allah yasa lafiya,Baffan su "?Cewar Inna ni
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce " Babu komai dama na zo duba wani abu ne ".
Yayi zancen yana shigewa ɗakin sa da sauri cike da jiran ta kwana dan yasan magana ce Babba shatou ta janyo dan yana kasuwa yaga ana guje guje.ya tambaya lafiya aka sanar masa da yar sa ce kura ta biyo yanzu haka kowa neman wurin ɓuya yake yi dan haka babu ɓata lokaci ya rufe yayo gida cike da tashin hankalin da ya kasa barin ƙwaƙwalwar sa da mamaki dan ya san dai Shatou na makaranta ya za,ayi ta je gurin farauta duk da ya san halin ta tana iya zamewa ta tafi tun da wani lokacin ta kan yi hakan,wannan tunanin yasa ya zo gida cike da sauri.
Sai dai bayan shigowar sa gidan ya gan ta zaune kan yar guntuwar kujera hankalin ta kwance ta cire hijab ɗin,tana wasa da jelar gashin ta da ya sauko har kan kafaɗun ta.
Su ko su Bibu kowanensu su shima hankali tashe kamar yadda yake.Numfashi ya sauke yana neman mafitar wannan case ɗin domin kuwa ya sa akwai matsala Babba saboda SHATOU garin ta taɓa gaba ɗaya yau.
A tsakar gida kuwa kallon tuhuma dukkanin su Inna ni take bin su dashi tana son karantar wani abu kafin a hankali jikin ta mace ta ce " Amina me ta aikata " ?
Shiru Amina tayi fuskar ta cike da damuwa ganin yadda SHATOU ta marairaice mata ta san faɗin zai iya zame mata illa.
Kan Ramata Inna ni ta koma dan ta ji ko zata samu amsar tambayar ta sai dai itama ɗin shiru ce sai kai da ta sunkuyar ƙasa ita fuskar ta na son bayyanar da dariya saboda tuno yadda ta ga mutane nata guje guje harda manya masu ƙaton tumbi na ƙauyen su,koda suka iso hanyar da shatou ta bi basu ga ƙurar ta ba sai dai sun samu labarin kura ta biyo ta daga wajen farauta,dan haka tun chan suka fara sheƙa dariya dan duk sun san ƙarya ne,tun da tare suke da ita.Sai dai saboda sanin da suka yi akwai matsala ya sa suka yo gida cikin sauri dan sun san akwai rigima Babba zasu yiwa SHATOU abun da zai saka ta farin ciki dan haka suka yanke shawarar abun da zasu ce,ba zasu taɓa ƙarya ta ta ba,ba kurar bace zasu ma bada shedu.
Ƙatuwar murya ce take rangaɗa sallama a ƙofar gidan hakan ya sa da sauri Inna ni ta kalli gefen SHATOU dake zaune hankalin ta tashe fuskar ta na cigaba da bayyanar da kyakkyawan murmushin ta dan dariya ce ke cin ta matuƙa amma tana ɓoye ta saboda Inna ni sai take mazewa tayi murmushi babu wanda take tunowa face Iro yadda ta hango sa yana gudun ceton rai yana kururuwa shima a tsorace ta san ko haka ta tsaya wallahi ta gama da case ɗin shi dan haka take ta sakin murmushi kafin ta samu damar zubar da kwandon dariyar itada su Amina dan duk ta san akwai dariya a cikin ta.
Wata Sallamar ce aka ƙara rangaɗawa kafin aka sanar da saƙon mai gari " mai gari na son ganin Jibril Farauta da yar sa a gaban fadar sa yanzu yanzu ,idan kuma ba,a zo tare da ita ba,akwai hukunci mai tsanani bayan wanda aka tanadar mata " Shine abun da mai kawo saƙon ya furta yana gamawa ya juyawar sa fada sanin cewa saƙon ya isa dan har maƙota ma wasu sun leƙo yan gulma a ji abun da ta sake yi yanzu kuma.
Baffa na cike da sauri ya fito dama a shirye yake ita kuwa SHATOU da komai ya shiga kunnen ta bata motsa ba illa ma satar kallon Inna ni da take yi wadda fuskar ta ta sauya lokaci ɗaya tashin hankali ya bayyanar mata wanda ta rasa gane dalilin da ya sa duk case ya haɗa da ita sai ta zamo abun tausayi.
Hannun ta Baffa na ya riƙo ya miƙar da ita tsaye ya saka mata hijab ɗin ta kafin bai cewa Inna ni komai ba ya fice daga gidan suma su Amina bayan su suka bi dan tabbatar da alƙwarin da suka yi na fitar da ita.
***
Koda su rabi suka gama jera komai na breakfast ɗin a gaban idon ta,sannan ta fice ta tayar da su LINA da kowaccen su jikin ta yayi tsami babu ma kamar LINA.
Wanka ta taimaka musu suka sake yi kafin suka shirya suka fito.Falon sai dai cikin su babu wanda ya kula wani ita REENA lamarin LINA tsoro ya bata dan haka ta sha jinin jikin ta cike da tsoron sake shan wani dukan,ita kuwa LINA tana son yi mata magana sai dai ganin kamar fushi take yi da ita sai ta kasa.
Wayar sa take ta faman kira bata shiga dan haka ta aika REENA ta kira sa daga sashen sa azaton ta yana chan,duk da tayi mamakin abun da zai hana sa samun Chaji su da suke da wuta koda yaushe dan ta su ce ta kan su bata gwamnati ba,Babban injin na su babu inda baya bayar da isasshen wuta mai kyau koda yaushe.
Miƙewar REENA da yar kumburarriyar fuskar ta zata je kiran na sa sai ga Rabi tana furta " ai ina ga Ƙaramin mai gida ya koma gurin aikin sa dan zan shigo nan na gan sa an da ƙatuwar jakar da yake zuwa da ita nan,suka shiga Mota shida wayen nan sojojin nasa,an buɗe musu gate sun fita,tafiyar ma kamar ta sauri ce dan motocin a guje suka fice ".
Idanu Ummah ta sakar mata kafin ta furta " kin tabbatar da abun da kika faɗa kuwa rabi".
" Allah na gani da ido na,ki ma tambayi Baba Tsoho na Uwani kiji "Kai ta jinjina cike da mamaki kafin cikin sanyin da jikin ta yayi ta bawa REENA Umurnin dawo wa ta zauna.Ita kan ta REENA Jikin ta yayi wani mugun sanyi taji kamar ta saka kuka lokacin.
LINA kuwa ji tayi zaman dinning ɗin ya gagare ta dan dama bata so fitowa ba amma saboda tsoron hukuncin sa ya sa ta fito,yanzu kuma gashi saboda ita ya bar gida ba tare da ya gama hutun sa ba,ko tsararabar su basu karɓa da yake basu bayan kwana biyu da Dawowar sa ba.
Hawaye ne suka cika mata ido dan itama tasan wannan karon a bun yayi yawa dole yayi fushi da ita.
Serving nasu rabi tayi ƙamar yadda ta san kowa na buƙata kafin ta bar gurin tana komawa kitchen cigaba da ayyukan dake gaban su.
Kowanne su babu mai jin test na komai dan LINA har ta miƙe ummah ta mayar da ita dan haka baki ture tayi ta cusa bread da ƙwai a baki suka ɗai ta ci duk tarin abun da ke kan dinning dan bata cikin mood ji take ya'yan na su ya ƙara tsanar ta fiye da koyaushe akan wannan case dan zuciyar ta take mata wani irin ƙunci da zafi.✍️
WANNAN LABARI NA KUƊI NE A MANHAJAR WAHTSAPP
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Commente,and like pls 🙏
*_Typing_*
*💋KURMAN ƘADDARA💋*
*©®Faiza Almustapha Murai*
*FA'EEH BG*✍️
P..1️⃣5️⃣
*BOOK ONE*
~PAID~
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eeh Bg*
Tun da suka kama hanyar zuwa fadar mai gari take ta waswasin yadda zata tsara mai gari a yarda a zancen ta dan ta san wasu munafukai sun je sun ƙarya ta maganar kurar.
Har suka isa bata tantance ba saboda tunani da ta take ta faman yi yadda zata fita ba tare da an gane ba.
Zama suka yi gurin da yake cike da jama'a dan mutanen gari sun cika wajen saboda har da su suka kawo ƙarar ta dan sun samu labarin ƙarya ce tsantsarta SHATOU ta ke yi hasalima daga makaranta take bada ga wurin farauta ba.
Kan ta ta sauke ƙasa bayan ƙarewa duk jama'ar dake wajen kallo kafin ta saki wani Shegen Murmushi tuno da yadda ta sako su gaba manya da ƙanana ana ta Guje guje kamar yan gudun hijira.Kafin kuma wata irin dariya ta kubce mata mai ƙarfi irin wadda ta yi wa Iro aɗazu.
Ba Baffa na ba har mai gari zuba mata idanu suka yi suna kallon ikon Allah kafin kuma,wani ɗan kazagin mai gari ya furta " ke yar talakawa Yar mafarauci,ki guji ɓacin ran mai gari,shirmen ki ya isa haka,da ace ba yarinya kike ba da tuni na sheƙa Miki bulaliya ta "Ya kai ƙarshen zancen yana Hararar ta tare da nuna mata ƙatuwar bulalar sa da ya Fiddo yanzu.
Ƙasa da sama SHATOU ta ƙare masa kallo kafin ta zunɓure baki tana tsayar da dariyar ta badan kuma maganar sa ba sai dai kallon da Baffa na yayi mata tare da girgiza mata kan sa alamar dai yana roƙon ta daina ta natsu.
Natsuwa kuwa tayi kamar ba ita ke dariya yanzu ba.
Su Amina kuwa suma dariyar ke cin su sai dai ganin bulalar ya sa duk suka natsu kowa zuciyar sa cike da tsoro,dan har ɗan ƙwarin guiwar da suka zo dashi suna jin yana neman guje musu yanzu.
Shiru wajen ya ɗauka tsitt ganin mai gari ya ci mur fuskar sa babu annuri kafin ya fara magana cike da ɓacin rai yau ko sallama bai yi ba da jama'a.
" Malam Jibril farauta yar ka ta sanya mutanen gari na shiga duniyar tsoro mafi muni,shin ya abun yake ne,gaskiya ne ko ƙarya domin na samu labarin ba daga gurin farauta take ba daga makaranta take ,Kuma ba kowa ya sanar mini ba face Iro domin shine ya tarbi minister Kuma ya gan ta chan,babu yadda za,a ce har ta fito daga makarantar ta shiga daji "...
Ya kai ƙarshen zancen yana jiran amsar da yake son samu dan wannan karon sai ya hukunta SHATOU dan shi kan sa ya ji jiki har da zawo yayi cikin wando yanzu haka yana gudawa kowane irin lokaci zai iya miƙewa gurin ya rage zafi.
Da sauri Shatou ta kalli gefen da Iro yake yaci mur dan sai da ya samu gurin ɓuya sannan ya tuna da cewa makaranta ya bar SHATOU ba zai yiyu ace har ta wuce gurin farauta ba,gashi baƙi a kayi yau.Dan haka take zuciyar sa ta ayyana masa ƙarya take yi,Sai gashi ma yana cikin sanar da mai g
Mai gari su buɗe ɗakin ƙarya ne wanda Alokacin mai gari ya buɗe ɗakin da wari ya cika sa fadawan sa sai shaƙar hanci suke yi sai dai babu damar nuna alamar sun ji wani abu.Sai ga mutanen gari suna cewa ƙarya ne a hukunta SHATOU da ta sanya su guje Guje domin ya yan su sun ce daga makaranta take bada ga wajen farauta ba,kuma itace ta ƙarshen fitowa makaranta,saboda ana hukun Tata.Gashi kuma har yanzu babu wanda yayi ido biyu da kurar.
Numfashi Baffa na ya sauke kafin ya ce " Allah ya taimaki mai gari Shatou ba zata iya yin ƙarya ba,a dai bincika lamarin na fi tunanin daga makarantar ta wuce chan dan ta saba haka,sai ta ci karo da ita ta tsorata ne sosai dan haka ta shigo gari a hargitse saboda a kwai yarin ta kan ta ka sani,ina rokon a sassauta ma Shatou ko dan asalin yadda rayuwar ta take,ƙuruciya ce Kowane yaro da kalar ta sa ".
Yana gama furucin yayi shiru zuciyar sa jagule,yana fatan ɗan mashin da ya soka ma mai gari a kai kace ya sauka dai dai inda ya ke buƙata.
Mai gari shiru yayi yana kallon SHATOU kafin ya nisa yace " Kin tabbatar da kin shiga Dajin Dagske " ?
Kai ta gyaɗa masa tana marairaice wa kamar irin da gaskiyar ta.A ƙasan zuciyar ta kuwa dariya ce mai ƙarfi.
" Kina da shedu "?
Mai gari ya ƙara furtawa yana kallon ta.
Kai ta ƙara gyaɗa wa kafin ta juya ta kalli su Amina dake tsaye cirko cirko.
Kallon su mai gari yayi kafin ya furta " Kun tabbatar da cewa bada ga makaranta take ba '' ?
" dan idan na samu ƙarya cikin zancen ku zan sa a hukunta ku da laifin ƙarya a bulale ku,kamar yadda za,a yi mata ".
Kallon kallo aka fara tsakanin Amina da su jawairiyya kowa zuciyar sa na rawa har ta Bibu sai dai yafi su ƙarfin hali dan haka ya gyaɗa kai alamarsun amince.
Numfashi SHATOU dake jin kamar ta hau su da duka tayi dan yanzu su kaɗai ne zasu kashe mata case ɗin,ya kasu saboda tare take da su dole za,a yarda.
" Eh ta tafi Daji dan duk da mun riga ta fita, sai da muka jira ta,kuma tana fitowa ta kama hanya,zuwa daji kuma dama tace yau zata je wajen farauta,sai nace mata kar ta je saboda za,ayi baƙi kamar yadda na samu labari a makarantar,shine da aka tashi ta wuce,mu ma muka biyo bayan ta,zuwa gida,Sai dai hankali na bai kwanta ba,dan haka na yi niyyar bin ta dajin nace su Amina su wuce gida,nabi bayan ta sai dai kafin ma na ƙara wani tako muka hango ta a Guje,kuma na san duk abunda ya saka Adda SHATOU a tsoro babba ne,dan ta yuyu mafaɗaciyar kura ta haɗu da ita ta tsorata shine ta yo gari ".Yana kai ƙarshen zancen yayi shiru.
Kowa dake wajen ya ji ya gamsu sai yan kaɗan daga cikin su irin su Iro da su Zaidu .
Amina ce ta ƙara da cewa" ai ni na riƙa mata jakar ta gata nan wajen har da kayan farautar ta na ciki ma da ta manta da su ".
Ta Fiddo da kibiyar tana nunawa mai gari.
Su jawairiyya Nana ta zancen suka yi irin na Bibu.Kafin wajen yayi tsit bayan ɗan cecekucen da aka fara.Wasu na furta Baffa na ya daina barin ta ai bai dace ba tana mace ma tana shiga daji farauta ,yanzu da kurar ta mata illa fa masu tausayi ke wannan zancen musamman ganin yadda SHATOU ke hawaye irin na tana cikin tsoro har yanzu.
Kafin ta kware ɗan ƙaramin bakin ta ta fashe da kuka tana furta " Baffa nidai mu bar garin nan,kar kurar nan ta zo har gida ta chanye ni,dan ta ga fuska na " .
Wata sabuwa Baffa na ya furta a ransa duk da ya san shirme ne irin na ta da rashin jin da yake hawa kan ta yanzu.
" Yi shiru ba zata dawo ba kinji zan je na farauto ta hankalin ki ya kwanta shikenan ".
Kai SHATOU ta gyaɗa tana share hawayen ta.Su ko su Amina da su Bibu dariya ce ke cin su sai dai babu halin yi dan sun san tayi duk wannan dan kawai mutane su ƙara yarda da ita.Shiru tayi ta makure kamar yar Marainiya.Sai kuma ta bawa mai gari tausayi musamman tuno da zancen Baffa na.Jikin sa ne yayi sanyi dan haka ya yi shiru shima kafin wurin ya ƙara samun natsuwa sannan ya furta " Daga shaidun da muka samu na tabbatar da SHATOU a kan gaskiyar ta take dan haka daga yau Jibril kar ka ƙara barin ta shiga daji,haƙƙin ka ne kare wannan yarinya kamar yadda ka ɗaukar wa Allah ya yan mu amana ne a gare mu,Dan haka ka kula da kyau,Na san ko ban bincika ba A'i na cikin tashin hankali a yau dan haka a kula da kyau,Shatou a daina shiga daji kinji Allah ya tsare gaba ".
Zancen mai gari.
Tun da ya fara zancen Baffa na yake murmushi cike da jin daɗi dan haka ya ɗago yayi masa godiya cike da girmamawa.
Ita kuwa SHATOU dariya ke cinta marar control dan haka ta cije bakin ta gamm ta ƙi cewa komai sai kai da take langaɓewa irin na tausayi ɗin da wanda yake cikin tsoro.Sai kuma Haushin mai gari da ya kira sunan Inna nin ta a gaban jama'a.
Miƙewa suka yi bayan furucin mai gari da ya furta " Na sallami kowa ".
Sake da baki Iro ke kallon SHATOU da ta sakar masa muguwar harara da Gwalo dan cike take dashi jin shine munafikin da ya ƙarya ta ta ashe.Dan haka yanzu ƙyat take jira ta masa rashin mutunci cikin ruwan sanyi duk da har yanzu bata haƙura da sunan da yayi mata ba ya tozar ta ta,dan ma tsaye take da sunan ya bita dan kowa na shakkar ta ne da tuni ba shatou take amsa wa ba.
A ɓangare ɗaya kuwa zuciyar sa kwata kwata bata yarda da zantukkan su Amina ba.Dan haka yake bin su da kallon tuhuma yana son su Kalle sa cikin ido sai dai kowaccen su tayi ƙasa da kan ta ta ƙi bashi dama.
Ƙyafci yayi wanda ya sauka a cikin Kunnuwan SHATOUn kuma ta san da ita yake dan haka ta ƙara sakar masa muguwar harara kamar idanun ta zasu zube gaba ɗaya sannan tayi gaba a bin ta su Baffa na a bayan ta.
Haka taron ya watse wanda kafin ma ya watse mai gari ya miƙe dan zagawa.
Dariya take ta wangala tana tsallen murna in ta rungumi Amina ta rungumi Bibu Takoma ta rungumi Jawairiyayya,Ramata,sai yanzu dukkanin su suke sauke kwandon dariyar dake cikin su.Baffa na da suka baro Baya kallon ikon Allah kawai yake yi tare da sakin murmushi dan shi kan shi ya san babu gaskiya ko ɗaya a zancen su bai ma san sadda aka saka kibiya a jakar ta ba,mamakin ma.wayon su yake yi yana musu kallon haka haka yara masu cike da ƙuruciya dukkanin su dan har bibun bai yi tunanin zai iya tsaro zance haka ba wanda ba,a yi ba.
Har suka kawo gida suna dariya tare da gwada irin yadda wani ɗai daga cikin masu kuɗin garin su ya ke gudu ciki ture sai su ƙara tintsirewa da dariya suna cigaba da kwaikwayon sa,Tafiyar Iro ce ta ƙwanbo ta faɗo ma SHATOUn arai hakan ya sa ta ƙara sakin wata mahaukaciyar dariya dai dai ta shiga gidan babu ko sallama sai gata ƙasa tana dariyar ƙeta tana ambaton Iro tare da yin tafiyar ta sa wadda ba SHATOU ba har su Amina da Inna ni da ke kallon ikon Allah sai da ta dara haka ma Baffa na dariya yayi kaɗan kafin ya samu kujerar roba da suke da ita gidan ƙwaya ɗaya ya zauna yana sauke numfashi.
Inna ni da ta tsinci kan ta cikin nishaɗi ganin farin cikin yar ta hakan ya sa ta cigaba da sakin murmushi fuskar ta na washe wa da ga Damuwar da ta ke ciki wadda suka bar ta ciki tun fitar su.
Ruwa ta ɗebo ma Baffa na masu sanyi a randa ta ajiye masa.Ɗauka yayi ya sha yayi hamdala.
" Ke wai uban me kuke yi wa dariya haka kamar wayen da suka kode eh,babu sallama haka kuka faɗo mana cikin gida "
Cewar Inna ni.Tana son tambayar Baffa na amma ta san ko ta tambaya idan bai ga damar faɗa ba ba faɗa zai yi ba.Haka ma su Amina ta san idan har SHATOU bata basu dama ba,ba faɗa zasu yi ba sai dai ayi ta yar kallon kallon tsakanin su.
Shiru SHATOU tayi tana dakatar da dariyar ta har su Bibu ma kafin cike da murmushi tace '' Babu komai Inni ni dama Iro ne ".
Sai ta kwashe labarin yadda yayi ta ƙwanbo a ɗazu.Inni da ta gama jin komai dariya tayi mai isar ta sannan ta ce " Allah ya shirye ki Shatou ".
" Amin,Inna ni ta "
SHATOU ta amsa.
Baffa na dai murmushi yayi kawai yana ƙara mamakin wayan Shatou yanzu ƙiri ƙiri ta ɓoye wanchan laifin dan ta san halin Inna ni yanzu sai dariyar ta koma kuka.
" Yanzu dai kuzo na zuba muku abinci kuci sai kowa yaje yayi wanka a fara shirin makarantar islamiyya ".
Cewar Inna ni wadda take mamakin wayon SHATOU dan ba wannan zancen ta so ji ba dalilin kiran mai gari take son sani,amma ƙiri ƙiri Shatou ta kawo mata maganar da ba ita ba.Kuma ta san cewa dagan gan tayi dan ta ɓoye wancan zancen kuma tun da aka yi haka zai yi wahala ta san abinda ya faru waje.Amma zata bincika ko mene ne dan mai gari baya kira banza musamman kiran Shatou.✍️
Ayi haƙuri ba yawa.
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Commente,and like pls 🙏
_*💋KURMAN ƘADDARA💋*_
_©®Faiza Almustapha Murai_
_FA'EEH BG✍️_
P..1️⃣6️⃣
*BOOK ONE*
PAID
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eeh Bg*
🕳️🕳️🕳️
Tun da suka isa bai fito ba ko nan da falo ne.Babu abun da ya taɓa tunda ga abincin rana har dare da ke jere a kan dinning da aka shirya masa saboda sun san da zuwan sa AB ya sanar da Dawowar su.Ganin hakan ya sa suka kasa haƙura ganin shirun yayi yawa gashi ya kashe duka wayoyin sa dan haka suka kira Ummah kai tsaye tsakanin wadda itama hankalin n ta tashe dan ma su Sir sun kwantar mata da hankali zai neme
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 39