Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kafin ta iya furta " Wallahi da kika sani Alhaji sai da na kauce sannan na samu ya rabu da ita,saboda yarinyar ta haɗu ko ni da nake mace na sara ma baiwar da Allah yayi mata ta sura bayan haka ga kyau kamar wata ɗiyar aljanu wallahi sai dai kin gan ta a fili zaki iya fahim ta ta,kuma duk masifar nan taki wallahi ta na iya shanye ki,dan magana guda zata faɗa Miki ta kashe Miki motsin zuciya saboda zafin ta ". " Yanzu me ye abun yi Anty ruƙy ".? " Abun yi kawai shine kema ki bi hanyar da na bi ki jaye shi wajen ta kafin ki rasa shi ". Numfashi Hajiya makiyya ta sauke kafin ta ce " An jima zan zo gidan ki Anty ruƙy wallahi yau ba zan iya barci ba sai na san abin yi dan ba zan yarda ina ji ina gani wata shegiya ta jaye mini miji ba a bariki ba, ko ta karɓe mini shi ". Sallama suka yi tana a jiye wayar tare da jan tsaki tana haɗiyar wani baƙin ciki bayan tuno da saƙon da ta gani wanda mijin ta ya rubuta shi da kan sa cikin salon roƙo,gashi sai ja masa aji ake yi. Tsinewa Leesha ta dinga yi kamar ta cire bakin ta. Kafin ta miƙe ta haɗiye komai ta fito ta cigaba zaman jiran fitowar Alhaji Mamman ɗin wajen breakfast saboda yana fita da wuri majalisa yau,tare burin aiwatar da maganar Anty ruƙy da tace kar ta yadda ta nuna masa ta ga wani abu a wayar sa. A ɓangaren Mamma kuwa shayi kawai ta haɗawa Asad mai kauri ta bashi ya sha. Sannan ta ƙara masa wani sabon wanka ta shirya sa tsaf cikin shigar sa ta uniform dark blue masu kyau da necktie ɗin su.Kayan sun masa mugun kyau kamar koda yaushe yau ma Mamma sai da ta zuba masa idanu tana kallon sa dan koda yaushe wani kyau yake ƙarawa a idanun su.Turarukan sa dake shaƙe akan madubin sa ta fesa masa tare da gyara masa kan sa dake shan kayan gyara kafin suka fito daga bedroom ɗin na sa dake kusa da na Alishat ɗin sai dai na shi ta ko ina kayan wasan yara ne masu tsada da kyau. Da sallama Mamma ta shiga bedroom ɗin na ta tare da Asad riƙe a hannun ta yana kumbure kumbure. " Ummieey,Mamma wai ba jata bani ice cream ba na sha ". Maganar sa da ta shiga kunnen ta cikin barcin da ya fara fisgar ta ne hakan ya sa ta buɗe manyan idanun ta a hankali a kan sa tana ɗan Lumshe su tare da sakin guntun murmushi wanda daga shi sai Mamma da Abbi ke samun sa. " Asad yau an tashi da sanyi ka bari sai anjima idan ka dawo school ". Jin wannan magana ta sanya shi fashewa da kuka take dukkanin su hankalin su ya mugun tashi idanu Alisha ta zuba masa kamar ta saka kukan itama,saukowa daga kan gadon tayi a hankali ta janyo shi jikin ta,ta rungume ta fara rarrashin sa.ƙin shiru yayi sai da ta ɗaga shi sama ta fara juyawa dashi tana masa chakulkuli take kuwa ya sake ya fara ƙyalƙyata dariya kamar ba shi ba itama kan ta dariyar take yi cike da jin daɗi da farin cikin da take samu a gurin ɗan na ta. Mamma kuwa kallon su kawai take yi cike da tausayin su. Bakin wata locker ta je dashi rungume akan kafaɗun ta wata jaka ta janyo ta saka hannun ta ciki sai gata da chocolate guda uku masu tsada jakar sa dake kan wata yar hanger mai kyau ta buɗe ta zuba masa su a ciki dan ta san halin sa da shan chocolate kamar dan shi aka yi su bakin sa ya san kwaɗayi kwarai da gaske,haƙorin sa ɗaya har zaƙi (cin Zuma)ya fara kama sa sai fira (giɓi)Ya cire sa.Bakin sa washe yana murmushi yake kallon mahaifiyar ta sa cike da ƙauna kafin ya sakar mata kiss gefen kumatun ta ya ce " thanks you Ummmiey " cikin yar Muryar sa ta yara. Murmushi ta saki mai sanyi kafin ta sakar masa kiss a goshi itama sannan ta sauke sa ƙasa.Tare suka fito falo har da ita bayan ta ɗauro wata doguwar hijab akan rigar baccin jikin ta,da ta a za rafa akan sa.Tare da keys a hannun ta,dan ita ke Kai sa ta ɗauko sa. Mamma ce ta Kalle ta kafin ta ce " Lafiya hala baki fita yau ".? " Zan fita amma sai zuwa 10 ko 11 Mamma ". Kai Mamma ta jinjina kafin ta miƙa ma Alishat lunch box na Asad ɗin.Kasancewar baya breakfast mai nauyi tun da safe. Abbi ne ya fito cikin shirin sa na karya wa yana gamawa ya fice daga nan. Har ƙasa Alisha ta gayar da shi. Shiko Asad da sauri ya faɗa jikin sa yana dariya ɗauke sa sama Abbi yayi kafin ya ce " yoo my boy,Yau ka yi missing lada mai yawa,kar ka bari gobe ka rasa ka ji,ina son mu shiga aljanna tare ". " Abbi zamu sha Ice cream ko mai yawa ko ". Kai Abbi ya gyaɗawa Asad cike da murmushi. Dukkanin su murmushi suka yi kaɗan sun san inda ya dosa. Dariya yayi mai kyau da take fitar da haƙoran sa dake a ware wasu duk sun fita ma saboda firan sa da yake kai yanzu. Mamma ce ta ce " Ɗan nema ice cream ɗin nan dai ba zai fita bakin ka ba ". Dariya yayi bai ce mata komai ba sai faman shafa chocolate da Abbi ya basa yake yi yana jin daɗi dan Indai chocolates ne babu wanda ke masa shamaki da su Amma abun da ya shafi su Ice cream sune ake hana masa saboda yanayin ciwon sa. Sai da ya gama firan sa da Asad sannan ya ce " Yau ba da wuri za,a fita ba kenan " ? Ya furta wa Alisha wadda ya karɓa gaisuwar ta kafin ɗaukar Asad. Kai ta ɗaga masa kafin ta ce a hankali " Sai zuwa 10 haka ". " Allah ya taimaka ".Cewar Abbi. " Amin " Suka amsa har Asad. Miƙa mata shi Mamma tayi bayan saukar sa jikin Abbi. Bye bye yake musu har suka fice shi daga gidan Alishat dai sai ɗan murmushi take saki a hankali tana kallon Asad ɗin da ta tashi da mugun tausayin sa da ta kwana da shi,wanda yake maƙale ƙasan zuciyar ta koda yaushe. Suna fita tsakiyar compound ɗin wata lafiyayyar mota suka nufa ta buɗe,ta saka lunch box da school bags da ta fito da ita,bayan ta sanya su ta buɗe ma Asad extra sit sannan ta rufe ta koma mazaunin driver ta shiga. Kunna motar tayi kafin ta bata wuta suka fice gidan bayan wangale musu gate da aka yi na gidan... Gudu take a hankali na zallar kwarewar ta akan kwaltar.karatun Qura'ani ta kunna musu,ƙira'ar Sheikh Afif inda take bita wa a hankali,sai Asad da ke ta tsalle tsalle kan sit yana bitar dan inda ya iya ne ta kunna masa,wanda har ta gaji da furta ya zauna ya ƙi. Suna isowa dai dai makarantar ta su dake ɗauke da tambarin S&A Staff school Abuja. Ta dakata ta juyo tana kallon Asad da ya hargitse gashin kan sa da ya sha gyara. Ɗan zuba masa idanun ta tayi tana jin wata irin kasala na saukar mata domin a duk lokacin da zata yiwa Asad kallo na ƙwas dan ganin ainahin kamannin ta da shi da kuma tantance irin ta sa kamar da zubin da har yanzu take mamakin yadda hakan ya kasance.Sai ƙirjin ta yayi ta bugawa har ta ji Numfashin ta na neman barin gangar jikin ta. Yanzu ma hakan ce ta kasance sa ita dan haka da sauri ta janyo ruwa kusa da ita ta sha sannan ta rufe idanun ta jingina da sit tana sauke numfashi. " ummieey mun iso fa ". Muryan Asad ta sauka cikin kunnen ta yana furucin. Yana kallon gate ɗin na su da ake ta wuce wa da yara cikin sa dan an buɗe sa sosai. " Yes maa boy I know,I just want you to have a good small rest ". Dariya yayi mata yana furta " Yes Ummieeey na "Murmushi tayi tana shafa kan sa. Sai da suka ɗauki mintuna biyu kafin ta ce a hankali cikin Rarrashi " Asad don't fight anyone pls,Ka kula da kan ka,kayi karatu sosai idan ka dawo ka koya mini ". Kai ya jinjina mata cike tabbatar mata da zancen ta ya shiga kunnen sa. Sai dai tana fatan haka dan wata rana shima ɗan rigima ne,na kwarai da ya shiga cikin yara sai ya zama mafaɗaci a gida kuwa ba zaka taɓa cewa shine haka ba. Hannuuwan su suka dunƙule suke ware tare kafin suka tafa gwanin burgewa tana furta " promise,and deal " Shima ya furta " Yes Promised,deal accept d" Kiss ta sakar masa a goshi sannan ta buɗe motar. Fitowa tayi daga cikin motar ta ɗauko lunch box na sa da school bags ɗin sa kafin ta rufe bayan,sannan ta buɗe masa ta fito dashi ta ƙara taje masa kan sa da ƙara gyara masa zaman necktie ɗin sa. School bag ɗin sa ta goya masa kafin suka yi addu'a a tare suka kama hanyar cikin makarantar suna shiga kuwa yara aka zuba musu ido ana kallon su har da wasu daga cikin malammai ma da suka iso. Har a jin su Na nursery two ta kai sa ta damƙa sa hannun malamar su sannan ta fito da ƙyar dan kullum haka suke sai yayi kuka muddin ta zo komawa gida. Kuma haka zai ƙi sakin jiki sai ya ga dama sannan wani lokaci har a tashi baya kula kowa mutun ɗaya ce yake kulawa Chucu sai ya yan ta wanda yake primary one ko su ba sosai yake sakewa da su ba.... Gida ta koma cike da kewar sa dan duk lokacin da zata bar sa wani wajen sai ta ji kamar kar ta bar sa ko wani abu zai iya samun sa dan ita yanzu tsoron duniyar ya shige ta sosai. Koda ta koma gida Abbi har ya fita Mamma ce kawai a gidan sai masu aiki. Ita ma ɗin Mamma na ɗakin ta,da alama ta koma bacci ne. Bedroom ɗin Asad ta shiga da zummar tayi bacccin ta chan sai dai tarar da mai gyara musu ɗakuna na aikin ta duk da ba wani datti ke a cikin ɗakin ba wanda ana masa gyara uku a rana hakan ya sa ta juya nata bedroom ɗin wanda aka gyara shi tsaf sai wani irin ƙamshi da yake yi mai daɗi ko ina ƙal ƙal ƙal dama kuma a tsaftaccen sa yake kamar na Asad ɗin. Toilet ta shiga direct bayan ta zare kayan jikin ta ta ɗauro wanka da haɗaɗɗun bath lotion ɗin ta.Masu ƙamshi da tsada. Tana gama wankan ta ɗaura guntun towel da ya tsaya iya tudun Hips ɗin ta zuwa ƙasan laps kaɗan. Dogon gashin ta da wanke da shampoo masu kyau da tsada ta ke gogewa kafin ta fito daga toilet ɗin tana jan guntun tsaki jin ƙarar wayar ta dake kan gado. Bata kula ta ba sai da ta gama busar da kan ta da hand dryer sannan ta murza mayukkan ta masu kyau da tsada skin care product masu kyau sannan ta,taje kan ta da ya ji mayuka masu kyau,na gyaran gashi da ƙamshi,sannan ta sanya masa band mai kyau ƙwaya ɗaya ta kama shi da ƙyar. Jelar gashin dake kwance a bayan ta buzu iska na ɗan kaɗa shi kasancewar window na baya dake a ɗan buɗe da mai aikin ta buɗe da zata fara gyaran ɗakin,kuma ta manta bata rufe ba. Kame shi tayi da ƙyar kamar farko ta fara masa kalba tana sauke numfashi da tura bakin ta gaba kamar wadda aka yiwa laifi kuma bada kowa take ba sai gashin na ta wanda kusan kullum haka take akwai lokacin da ta ce wa Mamma zata je ama ta aski Mamman ta hana dan haka take ta fama dashi gashi sai ƙara haukar sa yake yi ga tsawo ga yawa.Sauƙin ta ma ya na da taushi irin na Fulani ne,mai santsi da walƙiya. Da ƙyar da numfashi aka ɗaure jelar gashin da ya sauka a tsakiyar bayan ta Dan Allah ya mata albarkar gashin kai mai kyau.Dan ko Asad da mace ne da anyi gashi ko yanzu kan sa a cunkus yake kamar ka kama ka kitse abun ka,ɗan shigar da shi tayi kaɗan ya zama kamar an yi mata donut ya kuwa zauna da kyau a ƙasan kan ta dan parking na ƙasa tayi. Tayi matuƙar kyau kyakkyawar fuskar ta ta ƙara yin sharr da ita kamar wata yar Baby Masha ALLAH jiki duk madara kai daga nin yadda fatar ta ke shinning ka san cewa gyara ne take samu na musamman. Turarukan ta ta murza masu ƙamshi tun da roll on,body spray,oud masu tsada haka ta bi kowane saƙo na jikin ta da kamshin nan take bedroom ɗin ta ya ƙara haɗewa da ƙamshi ta ko ina. Babu abun da tayi wa fuskar ta face shafa Kajol da ɗan lipbalm mai kyau da ƙamshi. Bakin gadon ta nufa bayan ta gama ƙarewa kan ta kallo wanda akoda yaushe lamarin Ubangiji take dubawa bata taɓa saran zata koma haka ba,zata tsinci kan ta a wannan rayuwar ba sai gashi Allah mai iko da buwa,ya mayar da ita haka wanda wasu lokuttan ita kan ta ta kan kasa gane kan ta,shi ya sa a koda yaushe take godewa Ubangiji. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi jin wani irin tunani da ya ke kutso kan ta wanda bata rabo dashi a cikin zuciyar ta sai dai bata da madafa akan komai dan haka ta barwa Allah komai yayi mata zaɓi. Wayar ta ɗauka ta na kallon missed call ɗin.Ɗan ya ƙuna fuskar ta tayi kafin ta " Mayar da kiran ". Ringing ɗaya aka ɗaga kasancewar an san halin na ta,sai ta kashe wayan gaba ɗaya. Shiru tayi bayan ɗaura wayan akan kunnen ta " Leesha ki zo school yanzu an bamu Presentation kuma yanzu ake buƙatar mu kammala sa muyi submitting " " Waye ya bada ".? Ta tambaya cike da sanyin ta da kuma ko in kula. " Prof Maitama ".Aka bata amsa. "Okey I'm on my way ". Daga haka ta katse kiran. Bata re da ta jira ko zai ƙara yin wata magana ba. Shiru tayi tana zubawa ñumban ido wadda tayi saving da Course mate. A chan ɓangaren sa kuwa yana gama wayar ya sauke ajiyar zuciya domin wani irin sanyi ne ya ratsa shi jin tattausan muryan ta da tayi amo a cikin kunnen sa,duk yadda ta ke nuna masa kamar bata san inda ya dosa ba amma kullum soyayyar ta ƙaruwa take a zuciyar sa. Ya ɗan jima zaune a cikin capterian kafin ya fito yana komawa department na su na LAW dan fara gudanar da aikin na su kafin zuwan ta. A natse ta fara shirin ta,tana jan ƙaramin tsaki. Wata Jeans ne ta sanya ƙirar Companyn Dolce and Gabbana sai rigar sa fara mai buɗewa wadda ta ɗan saukar mata baya gaba kuma ta ɗan datse kaɗan. Masha ALLAH domin kuwa kwalar rigar ta zauna mata haka ma dogayen hannuwan rigar sun yi kyau sosai dan kamar yadda rigar take mai botir haka hannuwan suke. Black blue jersey veil ta yana a kan ta tare da sanya takalman ta hill masu mugun kyau da tsada wayen da suka ƙara yiwa kafar wani irin mugun kyau kamar dai yadda kuka san turawa na saka su sun zauna musu. Turarukan ta,ta ƙara saka sannan ta ɗauki wayar ta da duk wani abun bukatar ta ta fito falo bayan ta duba kan ta a cikin madubi da ƙara gyara zaman mayafin ta. Ficewa tayi da yar ƙaramar jakar ta a hannu tana tafiya tana baza ƙamshi.✍️ Idan an ga typing error a yi haƙuri cikin bacci na yi aikin. Kuma ina baku hakuri rashin update jiya,munyi yar hidima ne ta haihuwa🙏✍️ Book one na ta sallama.💃💃💃 Gobe ne last page namu na free in sha ALLAH. Kar ku ji wai daga gobe mun gama samun free book one ya ƙare. Dan haka ku hanzar ta shiga cikin wannan tafiya kar a yi babu ku kar ku bari wannan labari mai cike da abun mamaki nishaɗi,rikitar wa,ruɗani son rai ya wuce ku. Labarin da ban yake kamar yadda salon ma da ban yake.🤗🤗🥰ku dai ku zama cikin shiri kuma ku sanya juriya. Ban ce ki sayi littafi na ba idan baki da juriyar jiran page page kar ki zo ki Adda be ni ba update yau,yaushe za,a gama 😏🤭😅 Komai a hankali yake tafiya dole na san komai dade wa inda rai da lafiya zamu kammala labarin nan in sha ALLAH. Allah ya bamu iko ya ƙara muna juriya da Ni da ku yan ( KK CONVERSATION ROOM PAID & KURMAN ƘADDARA BOOK)Allah ya bar min ku na amana ta. Saƙon gaisuwa ga duk ɗaukacin member na wannan gida ina muku fatan alheri. To subscribe yours contact this numbers 0806 905 9746 0808 750 4734 FA'EEH BG CE ✍️✍️✍️ SHARE FISABILILLAH. LIKE,REACT,VOTE AND COMMENT PLS 🙏 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________5️⃣0️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *LAST FREE PAGE* Wannan shafi Sadaukar wa ne ga ɗaukacin masoya wannan littafi.📚 Jinjina gare ku,da gaisuwa mutanen kirki.. Maman Abba Ayeesha Abdullahi(ta kwaran shatou)😜 Na'eemart Collection H.S Ammiey Layla oumm Amjad Boss Bature Sadiya ka'oje Nainarh KD Zee Dodo Ibnatu Umar Oum Zainab (Diamond lady) Fauziyya yakubu ɗan Bello. Hudatu Umar Zainab Ishaq. Hajara kawu gana Habibah Yusuf Hausa Novel Audio and documents.(Rewa Novel Bilog). Maman Abdullah Mhiz bareemat. Hauwa Musa yeldu. Fatima A Bello Aishatul humaira. Maman Hanifah Pretty Minal Kuna da yawa fa har wayen da ban lissafo ba ina miƙa gaisuwa da jinjina.🙏🙏🙏💕Allah ya bar tare. _______________________________________ *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ # Asad # Aleeshat # Kamal Yarima # Doctor Mahuta # Part one ending # Faiza Almustapha murai# # Fa'eeh BG#✍️ 💦💦💦 Turuss tayi bakin ƙofar barin falon jin muryan Mamma da ta fito bada jimawa ba tana furta. " Breakfast fa ". Ɓata kyakkyawar fuskar ta tayi tana ɗan juyowa tana kallon Mamma. Mamma dai guntun murmushi tayi kafin ta ce. " Haba Hajiya ta dake ɗan naki ban san wanda yafi wani ƙiyayyar abin ci ba,yanzu da haka zaki fita da ciki a kwashe ". " Dawo ki karya,zaki fi samun ƙarfi a jikin ki ". " Mamma ba daɗe wa zanyi ba ai ". " Ahaf ai sai kiyi ". Ɓata kyakkyawar fuskar ta ta ƙara yi kafin ta dawo cike da yar shagwaɓa ta kama hanyar dinning da komai yake kai. Mamma Murmushi tayi kafin ta ce " Wa kunbo wa kayan ta ". Ɗan guntun murmushi Aleeshat tayi kafin ta zauna ta haɗa ma kan ta shayi mai zafi shi kaɗai ta saka ma cikin ta inda tayi ta sipping ɗin sa a hankali tana duba tsadadden a gogon hannun ta.Har ta shanye sa dama kaɗan ta haɗa dai dai cikin ta. Tana gama wa ta miƙe bayan ta ɗan goge bakin ta da tissue sannan ta ce a hankali " Mamma na tafi sai na dawo ". Ta kama hanya tana Amsawa da Amin jin addu'ar da Mamma take yi mata. Mamma da ido ta bita cike da tausayin ta domin kuwa ta san yanzu sai sun gan ta sai kuma idan lokacin tashi school na su Asad yayi idan ta dawo ta kan ƙara fita sauƙin ta ma yanzu saboda ya fara wayau ta rage fitar,da sun yi ƙokarin hana ta fita koda yaushe abu ya gagara har sun zuba ma sarautar Allah ido domin kuwaa duk lokacin da suka so hana ta fita musamman ta dare ita da su wani yanayi suke shiga domin haka take koma musu kamar zata haukace musu da magiya tace ita kaɗai ta san abinda take ji a jikin ta a duk lokacin da suka yi yunƙurin hana ta fita.Sauƙin ta ma yanzu ta rage sosai. Numfashi Mamma ta sauke kafin ta kama hanyar da zata sada ta da ɗakin ta. A ɓangaren Aleeshat kuwa cike da takon ta na rausaya kamar tarwaɗa haka ta isa kusa da motar ta,wata ce daban ta buɗe ta shiga yanzu kamar irin BMW ɗin na Black mai kyau. Wuta ta bawa motar bayan ta kunna ta inda aka wangale mata gate ɗin ta fice. A Guje kamar zata tashi sama dan dama ta saba da gudun ta ba Damuwar ta ba ce duk inda zata shiga cikin Abuja a high speed take gudun ta,sai ko idan Asad na aciki ne ta ke yin gudu kaɗan. Ba ta haura mintuna arba'in ba sai gata a iconic University Abuja branch parking ɗin motar ta dai dai ta, ta fito.Koda ta fito idanu ne kan ta kamar ƙasa dama kuma sun san wacece domin ita kaɗai ce Dalibar da ke yin parking na motar ta a parking space na staff ba tare da an mata komai ba.Ita ce kawai mai wannan capacity ɗin. Kawar da kan ta tayi daga kallon sa dan da shi ta fara haɗa ido kasancewar bakin department na su ne tayi parking. Ba tare da ta ce masa ƙala ba ta rufe motar tare da locking ɗin ta sannan ta cigaba da tafiyar ta inda ta san zasu haɗu zai iya yuyuwa chan ne inda team ɗin suke dan ba ta jin zata masa wata magana daga inda yake ko ta isa wajen sa. Shiko Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗan shafa kan sa dan ya shagala da kallon ta dan koda yaushe kyawun ta ƙaruwa yake a idanun sa ba ma shi kaɗai ba kowa ya san Leesha yar gayu ce ƙwarai ga kyau da zubin halitta da Allah yayi mata,a awasu lokuttan yakan ji kishi mai yawa ya rufe masa idanu sai dai bashi da yadda zai yi ne,domin wata shigar da take yi shikan sa fitina ce a gare sa bare wanin sa. Gashi manyan Alhazzawa ne ke bibiyar ta da sunan soyayya masu dukiya tana wulaƙan ta su bare shi da yake ɗan talakan sa duk da suna da kuɗi gwargwado amma bai kai na wayen da take kulawa ba.Abin na ƙona masa rai matuƙa baya da yadda zai yi ne da tuni ya furta mata kalmar da sauran mazan suke furta mata da suke shan wulaƙanci asalin sa.Bayan ta ya bi yana ƙarewa halittar ta kallo yadda hips ɗin ta ke juyawa cikin rigar.Numfashi ya sauke kafin ya janye idanun sa a kan ta,da suke dauke da wani mugun kishi. Aleeshat kuwa bata damu da duk kallon da ake mata ba daga student har teachers haka take ratsa mutane tana baɗe su da ƙamshin ta. Bakin Audit ɗin su ta dakata dan ya zo ya nuna mata inda suke kai tsaye ba tare da ta wahala ba. Bata daɗe da tsayuwa ba sai gashi ya iso Murmushi ya saki kafin ya ce '' Ran ki ya daɗe Barka da isowa ". Ɗan kallon sa tayi jin wani sabon kilin bibin da ya zo mata dashi na kiran ta da ranki ya daɗe. Ɗan sake fuskar ta tayi kaɗan ba ta nuna komai ba " yawwa Kamal " Daga haka bata sake cewa komai ba. Sai ma janyo wayar ta da tayi tana kokarin yin kira. " Muje " ya furta Fahimtar dama abun da take jira kenan.Bayan yayi wani murmushi na jin daɗin yadda sunan sa ke fita bakin ta cikin wani salo wanda ita ba da wata manufa tayi sa ba.Gaba yayi kafin ta bi bayan sa.Chan ƙarshe suka nufa sai dai tun da ta shigo idanun kowa ya koma kan ta musamman mazan da ke ciki suna karatu.Har da matan ma masu jin haushin ta suka fara zagi da Harare gare ta sai dai a banza babu wanda ta kalli gefen sa cikin su. Suma sauran team ɗin idanun duk suka zuba mata sai dai tun da tayi sallama bata ƙara cewa komai ba. Suma babu wanda ya ƙara yin magana cikin su. Sai ɗan satar kallon ta suke yi mazan, macen dake wajen ita ɗaya,kasancewar suna ɗan gaisawa ta saki fuska suka gaisa, anan suka haɗu da Nafisa sai dai duk yadda Nafisa ta so su jone a bu ya gagara kusan yan zu shekarar su ta uku da fara karatun Law.Nafisa Hamza Indabawa itama yarinya ce yar wanka da gayu mai kirkiri ita kanta bata ɗaukar raini dan haka ya sa ma take sake mata kaɗan.Dan ta fahimci itama ba ƙyalliyar ta bace,kowaccen su nada nata aji gwargwado. Abun da ya tara su,suka fara kafin kowa ya riƙa bada ideas na sa ita ce ƙarshe wadda ta kawo Tata idea. Har ta gama bayanin ta a tsanake cikin ƙwarewa da basira kowannenn su idanu ya zuba mata,kafin ta

Chapter 38 of 39