Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuciyar sa. Miƙewa yayi ya musu sallama bayan ya rarrashe ta tare da ƙara tabbatar mata da tabbacin kawo mata kilishin na ta. Sashen Uwani ya fara shiga bayan fitowar sa daga part ɗin Hajo cike da farin ciki ta tarbi Jikan ta tana tsokanar sa bayan sun gaisa. " Ango na na kaina,Allah ya sa babu ƙari da gani,idan kuma ka ƙara mini na kashe baka damu ". Murmushi yayi yana cewa " Nifa kin mini tsufa Uwani yawwa,ina Ni ina tsohuwa ai Ni na yarinya ne ". Daƙuwa farin Dattijon da ya fito yana murmushi ya sakar masa yana cewa " Ja'iri ai kar ka ƙara kira mini Mata da Tsohuwa dan yarinya ce shakaf haka nake nake kallon ta ".Ya kai ƙarshen zancen yana zama kusa da BILAL ɗin. Dariya BILAL yayi kafin ya ce " naga alama ai,Ya tsufa " ? Dariya yayi kafin ya furta " Tsufa gashi nan muna jaa yau ma ban samu na fita sallah ba ƙafafun suka tasar mini da ƙyar na samu yanzu na motsa yanzu ma da zan fito ". " Ayyah Sannu Dada " Dan haka suke ce masa. " Allah ya ƙara afuwa ya sa kaffaran jiki ne,ashe shi ya sa bangan ka ba a masallaci ina ta duban ka ". " Amin " " Eh Ai sai yanzu shima Yaya muka yi magana dashi ya kira ni bai ganni gurin Sallah ba ". Fira suka taɓa irin ta ƙauna tsakanin Kaka da kika kafin ya musu Sallama ya fice. Sashen Hajiya ya nufa kai tsaye bayan fitowar sa,Da sallama ɗauke a bakin sa ya shige haɗaɗɗen falon da yake ta tashin ƙamshi. Masu aiki ne kawai suke ta kai kawo a falon ko ina tsit. Har ƙasa mai aikin ta da ke kula da tarbon baƙi tayi,kuma wadda bata ma shamaki da komai na ta kasancewar bata da mace sai ta sake mata.Ruwa aka aje masa masu sanyi da lemu sannan ta gayar da shi. Sama tayi ta kira uwar ɗakin ta ta. Bayan fitowar ta da yan mintuna sai gata ta fito.Babbar mace ce mai ji da wanka ta fito. Tun daga chan take sakin murmushi Ganin wanda ke zaune a wajen kasancewar ta samu labarin Dawowar sa ga su Abdul Jabbar kafin su wuce makarantar islamiyya. Ƙasa ya rusuna shima cike da murmushi ya gaida ita. " Ya aiki ya kuka baro legos ɗin ". " Lafiya lau Hajiya,na same ku lafiya ". " Muna lafiya BILAL ai shekaran jiya ma da muka yi magana da ɗan uwan ka yace kana hanya zaka zo ashe ko ka samu shigowa ". Murmushi ya saki a hankali kafin ya ce " eh mun ɗan yi maganar kwana biyu,shima aikin na sa yana ɗaukar zafi yace sai a hankali ". Murmushi ta saki kafin ta furta " Allah ya taimake ku ya bada nasara ". " Amin " ya amsa cike da jin daɗin Addu,ar ta ta. Dan Hajiya mecece mai karamci ga kula ga na ta da wanda ba na ta ba ma. Sallama ya yi mata ya fice.Bayan sun ɗan taɓa fira kaɗan da ta shafi ta aikin su. Yana fita wani sashen ya shiga kamar dai wanchan sai dai funitures ne suka bambanta da kuma yanayin kalar ƙamshin da kowacce take da shi. Zaune ya same ta cikin falon tana kallon wani series da murmushi ta tarbe sa inda take ta saka aka cika masa gaban sa duk da ya ƙoshi da yake sanar mata. Cike da girmamawa suka gaisa. Suna fira cike da kulawa " Ai ɗazu ninah take faɗa mini sun koma yin halin a hanya ,ashe ma kana kusa,nidai nace Allah ya shirya muna su tace Reena haka ta dawo kacha kacha da ita,gaskiya Barirah na haƙuri Allah ya ƙara shirya muna ". Gyaran murya yayi yana son katse zancen sai gashi ta katse abun ta ta hanyar furta " Ai Junaid ya sanar da ni ka dawo ". Kai ya jinjina mata yana Murmushi tare da miƙewa yayi mata sallama. Ajiyar zuciya kawai ya sauke yana jin Tausayin mahaifiyar sa dama wannan shine abun da take gudu yadda kowa yake buɗe baki yayi zancen yanayin su Reena ɗin. Sashen momy ya fara shiga suka gaisa cike da kulawa yayi mata sallama. Itama take sanar mishi ashe Su Reena faɗa suka cigaba da yi a titi abun har yayi girma dambe a titi dan Hamrah ta faɗa mata lallai dole ya ƙara tayar musu tsaye kar abun ya kai inda ba,a so.Shi dai bai ce mata komai ba sai ma in sha ALLAH da yake faɗa na zai ƙara saka musu ido. Sannan ya shiga sashen Momcy itama dai sai da ya zauna zaman jiran ta dama ya saba da hakan kuma bai taɓa damuwa ba saboda halin ta ne idan ka zo wajen ta sai ka jira ko kai waye. Ya daɗe yana duba a gogon hannunsa saboda yana da abin yi kafin ya ji takon ta cike da ƙasaita ta fito tana bin shi da kallo. Zama tayi tana ɗaura ƙada ɗaya kan ɗaya cike da izza irin ta manyan mata ta furta " Ashe an dawo ". Ƙasa ya durƙusa ya gayar da ita cike da kulawa.Amsa wa tayi tana tambayar sa ya aiki shiru falon yayi babu wanda ya ƙara cewa komai tun Gaisawar da suka gama suna gamawa ya miƙe ya yi mata sallama. Bin shi tayi da kallo kafin ta galla ma bayan sa Harara tana jan mugun tsaki tana furta " Dangin jaraba " . Mai aikin ta ta ƙwalawa kira ta kawo mata abun taɓawa hakan ya sa da sauri saboda ta san halin ta ta kawo mata su ta ajiye mata.Dama fruit ɗin sun zama ready tun ɗazu ta yi cutting na su yadda take so. 🍃🍃🍃 A ɓangaren shatou kuwa nan bacci ya kwashe ta bayan ta gama cin abin ci,sai dai a cikin bacccin harda mafarkin wanda ya rubuta sunan na ta a allo ta yi sai dai bata ga fuskar sa ba ta dai gansa yana rubutun.Dan haka tana farkawa babu abun da ta fara sai tunanin yana yin shigar sa da ta gani sai dai ta kasa tunawa hakan ya sa ta miƙe ta fito wajen anan ta isko baffa na ya dawo shi ko Bibu yayi makarantar Allon.Buta ta fara suntuma fahimtar ba,a tada ita tayi Sallah ba.Dan Baffa na ya hana saboda ta samu sauƙin ciwon kan da tace saboda Inna ni ta faɗa masa duk abun da ke faruwa.Sai dai duk da ya taɓa jin sunan bakin Zaidu bai nuna ya taɓa jin sunan ba a bakin wani saboda ya san halin yar ta sa. Tana gama Sallah la,asar ta miƙe ta yo waje tana furta " Inna ni,Ni me ya sa yau baki tashe ni ba,gashi na rasa makaranta,kuma nayi lattin Sallah " Saboda duk rashin jin ta tana son karatu gwargwado. " Ga Baffa na nan shi zaki tuhuma bani ba " Inna ni tayi Furucin tana kallon ta. Baki ta cunno tana furta " ai Baffa na zaka min ƙari ko ". Kai ya jinjina mata cike da murmushi. " Baffa na gobe ina zuwa Farauta ". Ta ƙara furtawa. " Keda wa "? Cewar Baffa na saboda ya san gobe akwai makaranta. " Da kai " Ta bashi amsa tana Murmushi. Kai ya girgiza cikin alamar rashin wasa ya furta " A'a makaranta zaki je Shatoun Baffa na " Shiri tayi bata ƙara cewa komai ba. Murmushi Inna ni tayi kawai tana girgiza kai bata shiga cikin zancen ba ganin yadda yayi Furucin in serious wanda dole ta natsu ta ƙi tada maganar.Yayi hakan ne dan ya san cewa idan ba haka yayi mata ba sai ta addabe su ƙila ma ta tafi ba,a sani ba.Ko ta same shi chan daga makaranta. Ficewa Baffa na yayi ya musu sallama yayi majalisar su. Azkar ɗin ta Inna ni ta sanya ta ɗaukowa saboda tana son ta ƙara dagewa da addu,in kariya. Ɗaukowa tayi fuskar nan a cushe ta ji Haushin hana ta da Baffa na yayi kuma bata ga alamar wasa ba bare ta fice dan kan ta.Ga shi yanzu abinda aka mata Makarantar boko ya dawo mata cikin ikon Allah mafarkin da tayi na kalar kayan wanda yayi rubutun ya dawo mata a ido.Dan haka yau taci alwashin sai ta fita ko Allah zai sa ta samu mai irin shigar da kalar kayan mugun da ya disga ta cikin makaranta. Hmmmmm Allah ya baki nasara ta hannun damar Baffa na 🤭🤭😂😂Lallai akwai case yau muddin ta gano mai kayan nan yau sai mun yi kallo. Ina masoyan SHATOU ku kawo a gaji kar ta janyo wata rigimar 🚶🚶💃🤣 Wannan littafi na kuɗi ne. Amma in sha Allah Zan baku page goma sha biyu free kamar yadda nayi niyya.. Masu son fara yin payment zaku iya farawa ga details a ƙasa👇 *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh 💞 *_Typing_* *💋KURMAN ƘADDARA💋* *©®Faiza Almustapha Murai* *FA'EEH BG*✍️ *BOOK ONE* free pages👌 P..1️⃣0️⃣ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting room link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn *LITAFFAN MARUBUCIYA* *A MAFARKI NA SANTA* *RAYUWAR MU A YAU!* 👅👀👂Ka tsarkake wayen nan ɗan uwa. Na farko_harshen ka.(Magana mara daɗi,mai iya jefa ka haɗari ) Na biyu _Ganin ka.(Daga haramun) Kunnuwan ka _ Jin ka.(Daga Haramun ) Idan ka kiyaye waɗan nan kaga ma samun natsuwa ta duniya ɗan uwa. 🌻🌱🌻🌱🌻🌱🌻 A ɓangaren su LINA kuwa tun da Ya'u ya hau titi babu wanda ya cewa ɗan uwan sa ci kan ka tsakanin ta da su Ninah ɗin.Har suka sauka gaban ƙatuwar gate ta makarantar kai da ganin ta kasan Naira ce ke aikin ta dan haka malammai ma suke iya yin su saboda yadda iyayen yara suke zube kuɗade makudai dan samun ingantaccen ilmin Arabia na ya'yan su kamar na boko kamar dai Familyn SS da suke da wannan babu gefen da suka saki dan akwai wayen da duniyar kaɗai suka saka gaba. Firfitowa suka yi suka shige cikin makarantar kasancewar basu yi latti ba kai tsaye kowaccen su tayi na ta aji dan an rabasu gaba ɗayan su waccan an kai ta Faslul A'isha R.A wacchan Usman R.A kowacce da nata sai dai duk a bu ɗaya ake koya musu. Zaman ta ke da wuya wata ƙawar ta da halin su ya zo kamar ɗaya mai suna Anisa ce ta zo da sauri kasancewar ta ga shigowar su tana wani ajin tana faɗa da wani yaro da ya buge ƙanwar ta.Anisa da Lina kawancen su ya fara ne lokacin da kowaccen su ta gano kanwar kasa ce ita,dan farkon zuwan su LINA itace kaɗai take nuna rashin tsoron ta har dai suka saba,kuma itace ta fi kowa sake mata saboda yadda kowa yake shayin ta saboda agaban su ranar da aka kawo su tayi dambe da REENA ta daddaki kayan ta.Shine silar haɗa kan su amma duk da haka ko yanzu ta haɗa su sai an raba su kare jini biri jini suke yi. " Ke lafiya nagan ki kamar a tsorace " LINA tayi zancen tana kallon ta. " Isah na dako,da ya daki Rahima ". Ta bata amsa kai tsaye tana cigaba da zare ido. " To shi ko zare idon na me ye " ?Ta ƙara yin zancen tana Hararar ta tana ciro qur'anin ta a jaka. " Wallahi ina kai shi ƙasa na fara nusa naji tsitt ashe Ustaz Babba na tsaye yana kallon na " Shine duk ajin suka natsu bayan ganin tsayuwar sa. " To sai me dan ustaz Babba ya ganki,ba bulala ce ba kawai sai ki tsaya a Miki ki tashi ki kakkaɓe hannun ki da hijab ". LINA tayi zancen tana buɗe shafin da zata bada yau. " Hmmm ba zaki gane ba bane ustaz Babba ya fi kowa iya Bulala a makarantar nan,kin zata irin dukan su Uztaz ne da kike kakkaɓe ma hijab ". " Shi kuma Isah sai yayi bayani bari a tashi,haka kawai zai kama ta ya daka saboda yana shugaba ". LINA tayi Furucin ba tare da ta tan ka ma Anisa ba. Shiru suka yi tana cigaba da karatun ta cikin sauti mara ƙara dan duk abunta ta wannan fannin akwai natsuwa da mai da hankali,dan ta tsani ta je karatu tayi ta kure a na mata gyara.Dan duk littafin ta na karɓan hadda jaidan ne ke tashi a rubuce. Kasancewar Ustaz na ajin na su ya zo ya sa suka natsu karɓan hadda ya fara a hankali ta kowane ɗalibi kuma gwargwado ajin kowannen su yana ƙokari. Su LINA ne seat na baya a sashen mata kuma itace ta ƙarshen seat itace ta ƙarshe a karɓa.Cikin ƙwarewa da iyawar da Allah ya bata ta yi ta tayi ta rera karatun ta a cikin suratul kahfi ustaz na su sai gyaɗa kai yake yi yana jinjina kai saboda yadda take tafiya babu wani kuskure. Haka har ta gama ta miƙe bayan an mata kabbara kamar yadda aka yiwa kowannen su. Ƙari aka musu gaba ɗaya saboda tare suke tafiya gaba ɗaya ajin. Sallamar Ustaz Babba ce ta sanya ƙirjin Anisa bugawa da ƙarfi kafin ta lafe a kan kujerar su tana sauke niƙab ɗin ta. Gaisawa suka yi da Ustaz.Kasancewar Duka malamman na su Suna kiransu da ustaz Babban da suka ƙara na shugaban makaranta ne shine banbancin.Suna banbanta wa ne kuma a lokacin da magana ta shigo sai su faɗi ustaz wane da da sunan sa. Da Larabci yayi wa Ustaz na su bayanin komai harda sunan Anisa kasancewar kowannen su yana jin Yaren sai suka fara waigen Anisa da take zaune cikin ta ya ɗuri ruwa kamar kace ƙyat ta yi gaba saboda a kunnen ta Ustaz Babba ya faɗi komai. Kallon ta Ustaz na su yayi kafin ya ce " ta'al ta'al Anisa " Jikin ta ne ya fara rawa dan ta san yau sai ta ci na jakuna ganin yadda ran ustaz na su ran shi ya ɓaci ganin sa duk irin ƙoƙarin da yake kan su ace wai ɗalibar sa ce dambe da maza,inda ma Isah ƙarami ne amma da kallon ta kasan ya girme mata koda shekara biyu ne. Ta sowa tayi tana jin kamar tafiyar gaban Allo ta ƙara tsawo. Niƙab ɗin ta Ustaz ya sa ta ɗage wanda idanun ta sun cika da hawaye har sun fara zuba,kafin ya fara mata faɗa dai dai lokacin da bulalar da Ustaz Babba ya aika a ɗauko masa ta iso.Saboda Har Isah yayi wa hukunci itace ya bari ta samu damar karɓan hadda. Sai da ya gama faɗan sa Sannan Ustaz Babba ya yi mata bulala Goma a ƙafafun ta.Kowa sai da ya tausaya mata kuka ta ke tayi amma hakan bai sa Ustaz Babba ya ƙyale ta ba. LINA ta tausaya mata matuƙa dan haka ta sha alwashin sai ta yiwa Isah bugun wahala dan zasu yi same age dashi,Wanda ko nan gaba aka ce ya taɓa wani ba zai ƙara ba. Da ƙyar ta rarrashe ta tana jin zafin abun da aka yiwa ƙawar Tata.Duk da bugun da aka yiwa Anisa bai sa LINA jin tsoron aiwatar da wani a bu dan Anisa da ƙyar ta iya taka ƙafafun ta sunyi jaaa sosai dan sai ka cire socks. Ana tashi Ya'u ya zo ɗaukar su,tare da Anisa da ƙanwar ta suka wuce ganin ba,a zo ɗaukar su da wuri ba gashi sai kuka take yi,hakan ya sa LINA shigar da ita tasu su sauke su gidan su sannan su wuce na su. Har gida suka ajiye Anisa tare da yiwa Maman su bayani sai dai mahaifiyar su Anisa faɗa tayi ta mata na dambe da maza da ta fara.Su dai su LINA dama ita da REENA suka shiga da ita,Sallama suka yi mata. Koda suka fito suka shiga Mota Ninah sai faɗan an bar su zaune a mota take yi su sun gaji har da cewa Ya'u ya tafiyar sa. Sai dai ya ƙi saboda ya san inda rigimar zata ƙare kan sa. Babu wanda ya tanka mata cikin su sai dai LINA da ta yi kamar bata ji ta ba ta ce " Ke bafa shirun kura ya zamo tsoro bane,wallahi yanzu sai na lallasaki gurin nan,Uban wa zaki ɗagawa murya mtsww ". "Ke ɗin ko kema kin zata tsoron ki ake ji da da yan zu ba ɗaya bace wallahi sai dai muci uban juna ".Cewar Ninah. " Uban wa kike zagi " ? LINA ta yi Furucin tana ƙoƙarin baro gaban motar da take. Ya'u ne yayi parking motar yana cewa " Dan Allah Hajiya ALINA Kiyi haƙuri kinji ku bari nidai na kai ku gida lafiya,ku tausaya wa abinci na yanzu idan wani ya taɓa wani ya ji mashi ciwo cewa za,ayi laifi na ne da ban raba ku ba,dan Allah kiyi haƙuri,REENA ki bata baki ". Hararar sa tayi tana jan ƙyafci REENA da ta buɗa bakin ta tana furta " Kefa LINA saurin ɗaukar zafi gare ki ". " Rana ce " LINA ta bata amsa tana Hararar ta " kuma wallahi kika matsa mini sai na haɗe ku duka na ci ƙaniyar ku ".Ta ƙara furta wa REENA Hararar ta kawai tayi tana jan mugun tsaki kafin ta ce baki iyawa wallahi. LINA saboda kawai ya'u da ya roƙe ta ya sa ta share ta da sai ta yiwa bakin nan aiki ta cika sa da jini. Shiru motar ta ɗauka babu wanda ya ƙara furta komai itadai Hamrah shiru take saboda tsoro gare ta ta san halin LINA ƙwarai bata manta yadda ta sha wahalar ta chan da bata san halin ta ba. Yana dai dai ta parking ta fito tare da wartar jakar ta.Koda ta shiga ta tarar da su Ummah da BILAL zaune a falon sai kuma Hamida yar wajen Ƙanen su Ummah.Wadda ta girme ma su LINA sosai dan ita budurwa ce duk da bata cika irin cikar nan ba.Amma a shekaru zata yi shekara sha Shida. Duka da ido suka bita Hamida dake kiran sunan ta shiru tayi dan ko juyowa bata yi ba duk da ta gane Muryan ta duk da bata lura da ita ba kan ta sama yake. Kai Kawai BILAL ya girgiza kafin ya ce " Ummah kin gani ko ". Numfashi ummah ta sauke kafin ta kalli Hamida da tayi shiru sannan ta furta " Hamida kin san halin mutuniyar taki sai ahankali ƙila wani ya taɓa ta awaje tun da kina nan har an jima zata sauko ". Kai Hamida ta gyaɗa tana sakin murmushi kafin suka cigaba da taɓa fira rabi duk ta jikin kakan su A bukar ce da yake ɗan fama da jiki kwana biyu dan ita Ummah bata ma sani ba sai yanzu a bakin Hamida dan yace kar a faɗa ma kowa ba wani ciwo bane tsufa ne kawai.Dan dama baya da Isasshiyar lafiya abubuwa biyu sun ƙara Raunata sa ga tsufa. Shigowar REENA ce ta sanya su kallon ta cike da murmushi kamar yadda fuskar ta take washe. " Oyoyo yaya Hamida,shekaran jiya ma sai da nayi wa LINA maganar muje muga Baban Billions amma tace mu bari sai week end muje mu yi shi chan ". Murmushi Hamida tayi fuskar ta washe itama kafin ta furta " ai nayi fushi gashi ni na zo da kai na duk da haka ". Cike da shagwaɓa REENA tace" Uhmm karki yi fushi Yaya Hamida ni yanzu ma idan Ummah ta bar ni sai muje tare na ga su Ammah ". '' To naji yanzu dai je ki cire uniforms ɗin ,kizo muyi fira " . Ummah murmushi tayi haka ma BILAL "Ummah Barka da wuni,yaya Barka da wuni"Ta furta tana sakin murmushi. Jin " BILAL na furta " Mu ba,a gan mu bane ". Da sauri ta wuce bayan duk sun amsa har ta kusa take wa upstairs zuwa bedroom ɗin ta saboda ta ga yanayin yar uwar ta. Ta san tsafff zata jan ta rigima su yi ta faɗa ta jiyo Muryan UMMAH na tambayar ta me ya sa LINA ta shigo kamar ran ta ɓace dawowa tayi da baya tana tsayuwa dai dai ta zayyane duk abinda ya faru. Kai kawai su Ummah suka girgiza kafin Ummah tace " tafiyar ki bedroom naki barta kinji na san yadda take jin zafin chan tsafff zata lallasa mini ke,ohh na man ta ya yan ku na kusa ". Ta kai ƙarshen zancen tana sakin guntun murmushi.BILAL dai bai ce komai ba kuma babu wata alamar ko damuwa akan fuskar sa ta sa ko ya ji abun da ake faɗa amma yaji komai duk da wayar sa yake taɓawa. " Wai Ummah har yanzu LINA bata daina rigimar nan ba,naga kwana biyu an samu sauƙi dan ko chan suka je ba sa yi ashe halin na nan ".Hamida tayi zancen cike da damuwa. Cike da damuwa Ummah ta ce " Lamarin LINA sai Addu'a Hamida haka take kwanan nan abun ya dawo,addu'a kaɗai zamu cigaba da yi musu ita kaɗai ce abun da ke shiryar wa,duka ko zagi ba ya kawo sauƙin rashin ji face hinjirar wa da yake yi, Shi ya sa nake cewa Soja ya daina dakar mini yaaa". Kiraye kirayen Sallah ne ya dakatar da ita daga abun da take son furtawa tana furta "Alhamdulillah" BILAL miƙewa yayi cike da natsuwa yayi wa Ummah Sallama yayi ficewar sa masallaci dan gabatar da Sallah magriba akan lokacin ta. Bayan gama Sallolin kuwa Falon dukkanin su suka dawo har LINA da Hamida ta fito da ita da ƙyar da rarrashi dan suna ɗan sawa da ita wadda basu shiri itace yayar ta Samira. Shiru tayi suna ta fira amma ta ƙi yin magana ta haɗe fuska waje ɗaya har aka yi Sallah isha'i suka ɗaga bata saka bakin ta ga firar ta su ba. Bilal bai dawo ba sai da ya siyo ma Mama kilishin ta sannan yayi sallar Isha ya shigo cikin part ɗin. A chan ya yi Dinner ɗin sa yaci Tuwon dawa da Hajo tayi wa Sir dan yafi son na ta,idan yayi ra,ayin sa ita ke shiga da kan ta ta girka masa. Koda ya shigo suma sun gama Dinner ɗin su,da zummar idan ya zo sai ya ci na sa dan ya faɗa ma mahaifiyar ta sa inda zaije sashen Hajiya.koda ya zo suna ta aikin Rarrashin LINA da ta ƙi cin abincin ta kafe da ta ƙoshi. Sallamar sa ce ta sanya ta miƙewa da sauri tana nufar dininng bai ce komai ba shima sai bin bayan ta da yayi saboda ya ji komai ya san tsafff zata iya ƙin cin abincin ta miƙe haka dan haka ya zo da kan sa yayi serving ɗin ta yace Rabi ta wuce. Tura mata yayi gaban ta.Da sauri tayi ta turawa saboda so take ta tashi ta shige ɗaki bata buƙatar ganin kowa haka kawai yanzu take jin jikin ta wani iri kamar an sassara naman ta,ga zuciyar ta da take mata rawa kamar tana cikin damuwa ko matsala. Bai hana ta cusa abincin ba sai da ya tabbatar da ta ƙoshi sannan ya miƙe yana bin bayan ta kasancewar ta riga shi miƙewa. Direct ɗaki ta nufa bai hana ta ba sai ma zama da yayi yana kallon agogon hannun sa cike da kulawa ya furta " Hamida Dare ya soma ya kamata ki koma gida ". Kai Hamida ta gyaɗa tana furtawa cike da shagwaɓa " Allah da Badan school ba da zan zauna anan sai na yi sati ɗaya ". Ummah murmushi tayi tana furta " Lallai kam ki tsaya kiyi Rarrashin mutuniyar ki naga yau fushin da ban ne ban san dalili ba,gashi dai ba ma faɗan aka yi ba mai muni ". Miƙewa tayi tana furta " bari na kira driver." " No bari na kai ki ba sai kin kira shi ba ". BILAL yayi Furucin. " Nagde yaya ". Hamida ta furta tana shigewa ɗakin na su LINA tayi mata sallama tare da ƙara Rarrashin ta.bata iya furta komai ba sai ma a hankali ta furta " Allah ya tsare Anty Hamida,ki gayar da Ammah da Baba B " tayi Furucin Ganin bata kyauta mata ba na share ta,dan bata saba mata haka ba. Cike da murmushi Hamida ta fita tana furta "Amin, Zasu ji in sha ALLAH ". Sallama tayi da su Ummah sannan ta fice daga dan har BILAL ya zari keys daga inda suke ajiye. Kasancewar dare yayi Ummah ta ce REENA ta je ta kwanta saboda schl gobe kar ta makara. " Ummah sai da safe ". REENA ta furta." Allah ya bamu Alkhairi,kar a manta da addu,ar kwanciya bacci ". " Amin,in Sha ALLAH ".ta furta ta wuce sama zuwa bedroom ɗin ta. Itama Ummah miƙewa tayi ta tayi sallama da Rabi da wasu daga ma'aikatan masu kula da tsaftar part ɗin. Ɗakin Su LINA ta faɗa kwance ta isko ta idanun ta rufe bacci ya fara ɗibar kwasar ta. Murmushi tayi kafin ta matsa ta tofa mata Addua sannan ta rufo mata bedroom ɗin. Bedroom ɗin ta ta

Chapter 8 of 39