daga cikin jirgin bai yi gigin kiran sa ba sai ma ƙokari tare taxi da yake yi.
Sai dai kamar an ce ya juya ya hango sa jingine da wata irin lafiyayyar mota mai ƙirar Naira ya harɗe hannayen sa cikin ƙirjin sa haka ƙafar sa ɗaya ya ɗan karkata ta da take sanye da kafiyayun baot masu kyau,yana sanye cikin kaya mara sa nauyi kamar shigar ɗazu guntun wando mai kyau da wata yar riga armless sai uban rado dake kan fuskar ta da wanda har yanzu bai cire shi ba daga nesa gashin sa sai sheki yake yi wanda yake shan gyara.
Murmushi Mubarak ya ɗan saki kafin ya taka izuwa inda yake.
Yana kaiwa wajen da yake ya shafa kan sa yana furtawa a hankali " thank you sir "
Ko kallon sa MAHAJ bai yi ba sai koma wa da yayi bayan motar yayi zaman sa kamar yadda ya zo dan yana da driver da ke kula da shi idan Muby baya nan dan ba kullum yake tare da shi ba saboda shine yake taimaka masa a wajen kasuwancin sa nan da yake gudanarwa.
Buɗe masa drivern yayi ya shige yana masa godiya kafin suka bar filin jirgin.
Koda suka isa masaukin su dan wani Babban apartment ne mai dauke da gidaje masu kyau irin tsarin ginukan Chinese masu kuɗi komai ya ji tabarkallah.A wani irin Babban fili na ajiyar motoci suka yi parking cike da ƙasaita ya fito bayan driver ɗin ya buɗe masa.
Ficewa yayi ba tare da ya magana da kowa cikin su ba.
Shima Mubarak da ya bude da kan sa murmushi kawai yayi yana ayyana wa a ransa miskillancin na asali ya motsa dan haka ya karɓi jakarsa hannun Drivern da ya Fiddo masa a boot godiya yayi ma ba chinen mutumin kafin ya shige ƙofar da na ga ya shiga mai ɗauke da wadattacen glass,sai da akayi scanning na sa sannan ya shige bayan ta wangale.
Ƙaton Falo ne na alfarma da yake ɗauke da komai hanyar upstairs ya kalla kafin ya saki murmushi kawai sannan ya Miki hanyar.Tafiya yayi kaɗan ya iso wata ƙofa mai ɗan kyau itama ta glass sai da ta gama scanning ɗin sa sannan ya shige kayan sa kawai ya ajiye ya faɗa toilet domin samun damar sauke gajiyar da ya kwaso.
Duk da tafiyar jirgi ce amma yana jin jikin sa yama da tsami dan sun ɗauki a wanni da dama a saman iska.
A ɓangaren Mahaj kuwa ƙudundune yake cikin ƙaton duvet sai dai bai rufe jikin sa ba gaba ɗaya dan kana iya hango fresh skin ta sa da take ta sheki kasancewar babu riga a jikin sa yana shigowa ya zare ta.
Wani irin kwalba ne kamar na gold mai cycle sai ƙyalli yake yi ajiye yake a gefen sa kan bed side drower ta makeken gadon na sa dake ɗauke da bedside lamp a kowanne gefe gefe da gefe.
A hankali ya lumshe idanun sa da yake jin sun masa nauyi saboda rashin samun isasshen bacci tun dawowar sa ya maida hankali akan presentation ɗin domin zai wakilci school ɗin su ne su uku aka zaba shi daya daga Nigeria sai wani dan China da wani dan america guda dan haka ganin Makarantar ta nuna bukatar kulawar su yake iya ƙoƙarin sa wajen yin research mai ma,ana da gamsar wa.
Zuƙar hayaƙin flavour shi shi yayi yana jin wani iri a kan sa da yadda yake jin hayaƙin nan na kawar masa da komai da yake damun zuciyar sa.
Zuƙa yake yi a hankali sai dai irin zuƙar nan mai ja da yawa dan da ganin yadda yake shan ta kasan ya saba da ita,zuƙa yake yi sosai wanda take hayaƙi turneƙe ɗakin, tari ya fara a hankali yana jan numfashi lokaci ɗaya idanun sa suka yi jaa.
Mubarak da yayi wankan sa ne ya fito ya faɗa wa MAHAJ ɗin saƙon Samrah ya faɗa Bedroom ɗin da sauri cike da tashin hankali bayan ƙofar ta wangale.Aiko da wani irin mugun sauri ya kunna na'urar da ke korar hayaƙin abun ka da kasar da ke da technologia take ya fara ɓacewa da sauri ya matsa ya fisge shi shi ɗin dan har yanzu tarin yake yi kuma ya ƙi daina zuƙar ta.
Kashe ta yayi gaba ɗaya cike da damuwa ya ke kallon mahaj da ya zuba masa idanun sa da suka rikiɗe yana kallon sa irin na ban son shisshigi.
Mubarak yi yayi kamar bai fahimce sa ba dan haka ya sauke kan sa ƙasa dama ba kasa fai yake haɗa ido dashi ba duk da yana masa maganar bai son munafunci ya daina masa hakan amma saboda girmamawa yake kasa wa sai irin wayen nan lokuttan.
Bai ce masa komai ba sai ficewa da yayi da kwalbar yana jin babu daɗi a zuciyar sa dan ya san muddin ciwon sa ya tashi a kwai matsala kafin a samu farfaɗowar sa sai ya ci wahala gashi har yanzu babu wanda ya san yana da wannan ciwon sai shi Mubarak ɗin da Ayyah Abbu bai san komai ba saboda ciwon bai taɓa ta shi a gaban sa ba,a mafi yawan lokutta zuciyar sa ma idan ta motsa tana tayar dashi dan haka Mubarak yake kaffa kaffa da shi dan daga baya ciwon ya bayyanar masa sai chan baya ayyah ta san yana tasar masa dan ta taɓa kai shi asibiti aka faɗa mata matsalar harda maganin sa tunda kuma ya tashi ya san abinda ke damun sa yake saurin danne fushin sa,sai gashi ta silar wannan hayaƙin yake shirin tado ma kan sa da lalurar da yayi kwana biyu babu ita dan ya manta ma da yana da ita ta daina ta shi sosai chan baya harda damuwa take ƙara mata ƙaimi kuma duka Mubarak ne yayi kula dashi a lokacin yana school tare dashi kuma suka ɓoyewa Abbu itama Ayya abun bai wani dame ta bata taɓa faɗawa Abbu ba a cewar ta ba zata kashe ɗan ta ta raya na wata ba saboda ta san yadda Abbu ya tsani ciwon ko kan ƙani ne a jikin MAHAJ ɗin sa take yake sauyawa saboda damuwa Bpn sai ya tashi.
Ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe idanun sa da suka garwaya daga asalin farin madarar su.
Ƙofar da Mubarak ya banko ce ta sanya shi ya mutsa kyakkyawar fuskar sa kafin ya ɗan harari ƙofar yana sakin murmushi a zuciyar sa dan haka yake ƙara jin ƙaunar Mubarak saboda kyawawan ɗabi'un sa yana bashi kulawa kamar ta mahaifin sa da mahaifiyar sa yana iya ƙoƙarin sa wajen ganin ya riƙe amanar da Abbu ya basa dan koda ya fahimci MAHAJ na shan shi shi bai matsa masa da dole sai ya daina ba yayi dai koƙarin ganin ya yi yadda zai yi ya rage har Allah ya sa a samu ya daina tunda itama shan ta baida fa'ida dan hayaƙi ce itama yadda taba zata cutar haka itama zata taɓa huhu.Sannan bugu da ƙari cutar da yake fama da ita.
Jan jikin sa yayi ya kwanta yana yana sauke numfashi ya san Mubarak yayi fushi daga jin yadda ya banko masa ƙofa.
Kasancewar dare ya riga yayi dan a gogon ƙasar har ya nuna sha biyu na dare wanda gari yake kamar rana hakan ya sa ya tofa addu'oin kwanciya bacci kafin ya miƙe ya kashe haske ya bar bedside lamp wanda itama ta gefe ɗaya kawai ya kashe ya bar ɗayar tare da rage ta..
A haka barci mai daɗi ya kwashi ɗan Abbu.
Mubarak da ya dawo yanzu ne ya tura ƙofar a hankali ganin ya kashe haske ne ya san cewa yayi barci hakan ya sa ƙatuwar TV dake aiki a hankali wadda take dai dai da saiti gadon ya kashe ta kafin ya matsa ya kashe masa Hasken bedside lamp tare da rage masa gudun Ac saboda ita kan ta illa ce a gare sa amma haka ya ke ƙure ta.Dan haka yake fama dashi a kullum idan suna kasar nan.
Baya shigo masa Bedroom sai yayi barci ko ya same sa a irin haka amma iyakar sa Falo.
Ficewa yayi bayan ya gyara masa kwanciyar ta sa dan filon mai taushi ya bar kan sa sai ya zama na ya aza kan sa a kan hannayen sa da suke ta shinning da alama zasu yi taushi dan Jawur haka suke sai alamar taushi da suke da shi a bayyane kamar na sabon jariri.
Kyakkyawar fuskar sa da take Baby face wanda zaka tabbatar jikin ne kawai amma yaro ne shakaf MAHAJ matashi mai tasowa cike da burikan rayuwa da wani irin raunin zuciya da ya rayu dashi,wanda yake fatan wata rana ya sauke wannan nauyin ya samu farin ciki.
Murmushi yayi cike da tausayin sa sannan ya fice daga ɗakin take kuwa ƙofar ta rufe ruf wadda take kamar ta Karfe kamar kuma glass dan itama sai ta bincike ka tsaf amma idan ta saba da ɗaukar baya nan ka kana zuwa take buɗe maka ka shiga.
Shima kasancewar ya kwaso gajiya hakan ya sa yana dawowa ya nemi waje ya kwanta shima cikin haɗaɗɗen bedroom ɗin sa mai kyau sai dai duk da haka na MAHAJ ya fi sa nema ba kusa ba.
Asuba ta gari.
" Ta baiwa ki cigaba da aiwatar da komai cikin natsuwa muna samun nasara an kusa Haska duhun da ke bai baiye dake yanzu kawai jini za'a ƙara ba wa su ɗan duhu zasu bazama kuma suna son na sabon jariri da na mai ciki dan haka aiki ne Babba "
" Sirrin ki naki ne yana nan ɓoye bana son ki ƙara mini magana akan sa,Babu wanda zai taɓa zargin ki koda kuwa ya ga wata alama mun toshe kowace ƙofa,ki yarda da mu, ba zamu taɓa bari aikin shekaru da dama ya tafi a banza ba,kin mance sharaɗin mu da Sarkin Aljannu muddin muka kuskure su ɗan duna da ɗan duhu suka halaka akan wannan aiki Ni dake duk mun halake dan haka ba zan taɓa wasa da wannan aikin ba na toshe kowace ƙofa "
" Na yarda da ku Dan Baiwa,Kawai dai wata rana sai nake jin kamar akwai wanda yake da wani sani akai kuma yake cikin kokwanto akan abun wanda wata rana kaɗan zan fallasa,Yanzu dai shi kenan bari na tafi dan dama wata yar dama na samu na fito sai na sake dawowa ".
Kudade ta ajiye masa masu yawan gaske kafin ta miƙe tana zagin sa yana zagin ta sannan tana juyawa ta ɓace ɓatt kamar yadda ta saba yi kullum idan ta zo shima ɓacewa yayi kamar bai taɓa zama wajen ba.✍️
Ta Baiwa 🥵
Ta baiwa 🥵
Ta baiwa 🥵
Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800
# _FA'EEH BG CE✍️_
Book one free
Book two paid N#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin✍️
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔
_*KURMAN ƘADDARA*_
_©®Faiza Almustapha Murai_
_FA'EEH BG✍️_
P________2️⃣8️⃣
*BOOK ONE*
_FREE._
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*
_____________" Umma Ya Samir ya dawo "
Reena ce tayi zancen tana washe bakin ta kamar gonar audiga.
Ita kuwa Leena zama tayi tana haɗe rai kamar wacce aka yiwa mutuwa.
Murmushi Ummah ta saki kafin ta ce " Masha ALLAH,yau ya samu zuwa kenan,shi kam kamar ana korarar sa da gida shida Soja ko hutun basa son zuwa ".
Ta yi zancen tana kallon Leena da ta ke shiru.Hannun ta ta riƙo tana furta " Wa ya taɓa wannan kayan ita kuma ta shigo min haka ".?
Dariya reena ta ɗan yi wadda ke ƙara wasar da idanun ta da suka fara ɗan sauyawa dan tun shigowar su Ummah ta lura sai dai ba ta tambaya ba kawai tana jiran su faɗa da bakin su,amma ta lura ba faɗar za,ayi ba dan giwar a cike take.
" Yaya B ne ya ɓata mata rai "
Kyaɓe baki Umma tayi a hankali kafin ta ce kunfi kusa cikin zuciyar ta tana Murmushi amma a fili sai ta ce " Kai BILAL bai kyauta mini me ya sa ya taɓa mini yaaa yaushe ma aka shirya bamu sani ba ".?Takai ayar zancen tana jiran amsar su fuskar ta sake.
Baki Leena ta tura gaba ita kuwa Reena dariya ta saka ganin yadda Ummah tayi da fuska tana kallon Leena. Cike da ɗan irin mamaki.
" A ina kuka samu yin magana da shi ne " ?
" A Wayan Yaa Samir ne "
Reena ta bawa Ummah amsa.
" Ku bar ni da shi zamu garwaya ba faɗa masa bana son yana takura wa ya ya na amma naga alamar bai jin magana sai na fara zane shi da bulal.. ".
Ai ko kafin Ummah ta kai ƙarshen zancen Leena ta fashe da dariya haka Reena dan sosai suka dinga dariya wai sai Ummah ta zane shi garsheshen ƙato dashi har ta hango Ummah na dukan shi yana kuka.
" Ummah kina iya zane sa,yafi ki ƙarfi fa " ?
Leena da ta saki fuskar ta tayi zancen tana kallon Ummah da fuskar ta ke cike da murmushi na farin ciki ganin yadda suka saki fuska lokaci ɗaya musamman Leena da ta haɗe ta gabas da yamma wanda ko bata tambaya ba ƙara ce ta kawo mata shi ya sa aka shigo aka yi mata zugumm kamar kurma yayi faɗa,dan ta san dole zata tambaya in ita bata faɗa ba Reena zata faɗa.
" Sosai ko har yayi kuka harda karya sa ma zan iya a ƙafa ".
Dariya Leena da Reena suka ƙara fashewa da ita kafin Leena ta miƙe kamar wadda aka tsikara ta fara tafiyar gurmunta ta irin in ƙafar ka na ciwo haka tana nuna yadda ya B ɗin zai yi idan Ummah ta karya sa.
A wannan karon Ummah sai da ta dara kaɗan tana girgiza kan ta dan shashancin su Leena abun dariya ne har yanzu basu yi wani mugun wayau ba kullum yan jiya suke koma mata,kamar lokacin da suke cikin zane.
Shiru tayi bayan wani tunani da ke shirin kutsowa a cikin ƙwalƙwalwarta na abinda ya faru shuɗaɗɗen lokaci hakan ya sa ta miƙe daga zaunen da take tana cewa " ku tashi ku je kuyi Sallah kafin Abban ku ya dawo naji yana neman ku kafin ya wuce masallaci "
Cike da dariya kuwa suka miƙe suna cigaba da yin tafiyar sai dai itafa Reena dariyar ce kawai take amma tasha alwashin sai ta fadawa ya B kar ya zo gida Ummah zata karya shi.
Ita kuwa Leena wani irin nishaɗi take ji jin Ummah zata rama mata kuma ta san tana iyayin hakan dan haka ta saki fuskar ta take ta manta da abunda akayi mata.
Ummah sama ta haye da sauri tana ɗaukar kiran da ya shigo wayar ta tana Murmushi da dariyar su Leena.
" Haba B tin yaushe nake kiran ka baka ɗagawa bana jin daɗin abinda kake mini samm wallahi,sai ka riƙa ware Ni kamar ba yar uwar ka ba nifa ina kiran ka ne mu gaisa amatsayi na na yar uwar ka,zuwan da kayi kwanan baya har na shirya na zo gidan aka ce ka koma,Wallahi banji dadi ba,na so mu gana ".
Shiru yayi bayan jin ta aje aya tana Sauke numfashi dan tun da ya ɗaga wayar take ta uban surutu ko gaida shi bata yi ba ta fara zuba masa zance.Dama haka take bata ko gajiya da kiran na sa.
" How is Hamida and Momma " ?
Shiru tayi kafin a hankali jikin ta mace jin bai ma bata amsa akan maganar da tayi ta zuba wa ba kamar an buɗe famfo sai ma tambayar Hamida da Momma.
Wani takaici ne ya turneƙe ta sai dai ta san halin sa hakan ya sa cike da wani irin haushi ta ce Tace " They are fine,Amma B baka ji abinda nace ba,duk maganar da nayi "?
Uhhm ya ce kawai dan har yanzu bai jin dadin jikin sa tun ruwan da suka dake sa a toilet yanzu haka koda ya fito sai da ya sha pain relieve Dan wani irin ciwon kai ya taso masa da sanyi da ya saukar masa yana son ya huta ita kuma uwar nacin son zumunci tana son addabar sa dan shi duk da ya fahimci inda ta dosa duk da bata taɓa faɗa masa ba yake ƙokarin kawar da faruwar wata magana a tsakanin su yafi son ta bar shi a matsayin Zumuncin take bi.
" Samira ina jin headache pls I want to hang up the call,want to sleep and rest "
" Ki gayar da su Bb Mai Billions duk da minyi magana dashi jiya da su Ammah,ki gaida Abba da kowa da kowa,Bye ".
Ya yanke kiran yana ajiye wayar tare da jan guntun tsaki.
Sage da baki Samira ke kallon wayar kafin ta Saci kallon gefen da Hamida take kwance hankalin ta kwance tana danna wayar ta kamar hankalin ta bai kan ta.
Wulaƙancin yau yafi na koyaushe take gani dan haka wasu hawaye ne suka silalo mata masu ciwo kasa jurewa tayi dan haka ta miƙe da sauri ta fice daga ɗakin tana ɓare baki kamar ƙaramar yarinya.
Ita kuwa Hamida duk da dariya na son ka mata amma ta ji Tausayin yar uwar ta matuƙa dan haka duk da haka dai sai da ta dara ta girgiza kan ta dan ta daɗe tana cewa yayar ta ta raba kan ta amma taƙi ji dan ita duk da yarinya ce ta fahimci Ya B baida bukatar yayar ta Samira yanzu ga irin ta nan tace wa Momma ta daina goya mata baya amma dukan su sun nace kamar Auren zumunci dole ne kowa ta tsiya ake ci a cikin sa gashi Samiran ta ƙwallafa rai ga ya yan na su.
Samira na fita da kuka ta faɗa jikin wata Babbar mace da ta fito daga wata ƙofa da alama bedroom ne.
Kallon ta tayi ganin hawaye jagaga bayan ta ɗago fuskar ta kafin ta ce " Samiran Momma lafiya kuwa " ?
" Waya taɓa mini ke " ?
" Momma ba B bane ya ya yi mini wulaƙanci ".
Ta bawa mahaifiyar ta su amsa tana jan wani sabon kukan.
Murmushi matar tayi kafin ta riƙo hannun ta suka zauna anan kan ɗai daga cikin hadaɗdun sofas dake ƙawace da falon.
Hawayen ta fara share mata kafin ta sauke numfashi ta ce " Nifa ban ce ki matsa mishi da yawa ba, ba sai na riƙa Nana ta Miki halin Mazan nan ba Samira wata rana sai naga kamar Hamida tafi hankali ma,a hankali a hankali ake tafiyar da komai Hamida na min zancen na ce ki daina ta kura masa,sai dai ina yi mata ne kamar bana jin ta amma Ni na san Indai kika matsa zai gundura dake,Ki bi komai a hankali na miki alkawarin sai kin samu Bilal zumunci kawai muke son mu karfafa dan koshi Baba Mai B na ra'ayin hakan dan na taɓa masa zancen ya ce a bari har gaba to yanzu dai ga gaban ta fara zuwan ki kwantar da hankalin ki,Ni Rashida sai na ƙwato Miki Soyayyar BILAL ba dai mahaifiyar shi na so ba kar ki damu Abban su kuma na san bazai taɓa musawa ba haka ma duka a halin dan ba zasu taɓa manta da halaccin da Baba Mai Billions Yayi musu ba dan ance ko kafin Shima Baba Bukar ya rasu ya nuna yana son haɗin zumunci a wannan a ahali dan haka na san Baba Mai B ba zai hana faruwar hakan ba ki saka a ranki kin Auri BILAL SSS kinji kin zamo surukar Ummah surukar Abba ".karshe sai ta fara rera mata waƙar nan " ƙanwata kiyi Haƙuri .....
Dariya suke yi bayan ta kai aya cike da farin ciki a haka Momma ta sharewa Samira hawayen suka koma dariya kamar ba ya da mahaifiya ba gwanin burge wa suna ta barkwancin su har Hamida anan ta same su ta zauna aka cigaba da fira da ita kafin lokacin ya ƙara shigewa kowa ya watse saboda dare ne ba,a dade da ga ma Sallahn Isha ba.Su na nan zaune sai ga mahaifin su ya shigo Alhaji Ahmed Aliyu Mai Billions Sannu da dawowa suka yi masa dan sun san inda ya fito yana sashen Mahaifin na sa.Ammah da kuma A Bukar.
Fira suka cigaba da yi cike da kaunar juna kafin su kayi Sallama da juna.
A ɓangaren su Leena ma koda Abba ya dawo duk sunyi sallolin su anan suka zauna gaba ɗayan su har su Samir da suka shigo suka yi ta fira kafin lokacin islamiyya yayi suka shirya suka wuce ya'u ya kai su kasancewar weekend ne sai bai zauna ba ya dawo gida time nayi ya dauko su ya dawo da su,sai dai fa ko a mota sai da aka tashi kwata wata rigimar domin Ninah da Leena ta kama tana Hararar ta dan ita ta so shiga gaban mota shine tayi karaff ta shige shine dalilin faɗan na su,da ƙyar ya'u ya raba faɗan.
Koda suka dawo gida ma suna cire uniforms ɗin su suka yi sashen Sir da duk yau ba su shiga ba wajen Maaama Da Hajjow har da su Uwani ma da Dada.
A chan suka yada zango sashen kakannin na su dan wajen Ummu aka fara zuwa da Dada kafin suka yi sashen Hajjow suka ta sa ta gaba tana biye musu itada Sir cike da ƙaunar Jikokin na su da suke musu wata irin ƙauna da su kan su Bazasu iya bayyana ta ba.
Shigowar Abba ce a ƙaton falon na Hajjow ya san ya Reena miƙewa da sauri tana masa oyoyo tare da amsa Sallamar sa kamar ba ɗazu suka rabu ba.
Shi ko Murmushi yake ta saki yana kallon su tare da iyayen na sa kafin ya kara sa wajen su har ƙasa ya kai yana gayar da Hajjow tare da Sir sai kuma Maama da ke ɗan jingine da wani tintimi kamar filo sai dai mai mugun taushi saboda jikin tsufan ta shi ya sa suke samar mata da duk abu mai taushi da zata ji daɗin jikin ta.
Zama yayi kusa da Mamaa yana cewa " Wai ke tsohuwar nan yaushe zamu ci dafa dukan ki " ?
Kuka ta fashe da shi tana furta " ka jiya ko Sada,Kana jin shi ko ".
Daƙuwa Sir yayi masa yana furta " Babana Karɓi nan,nace gyatumar ka Uwani,Nace ka daina saka mana uwa a gaba baka bari sai ka karasa muna ita muna lallaɓa a bar mu,Ai ga na kan nan sun tsufa su ya kamata ka fara cin dafadukar su ".
Dariya Abba yayi dan haka yake Indai ya shigo Sashen sai ya Tsokano Kakar ta sa su yi ta rigima ta yi ta kuka tana cewa bai son ta.Sir ne yake shige mata ko Hajjow amma Abba ya riga ya saba sai ko su BILAL da su Samir da take mahaifiyar su tunda tattaɓa kunnen ta ne, sai su yi ta ɓata fuska idan Abba na yi ma Mamaa haka a gaban su,duk in sun tashi suna tsokanar ta.
Ita dai Hajow dariya kawai take yi saboda kawaicin ɗan farin da take yiwa Abba a yanzu.Kamar yadda Mamaa take yiwa Sir wanda sai yanzu da tsufa ya kamata take kiran Sada da sunan sa.
" Wallahi Sada wannan ba Saleh na bane wai jairin Ni yake yiwa fatan mutuwa "
Kuka ta ƙara fashewa da shi wiwi.wiwii
Dariya kuwa su Leena kamar sun samu abun yi.Kukan na ta cike da tsufa da abun dariya dan harda yar majina ake fyacewa da ɗan tisssue dake gefen ta da ake ajiye mata a kusa da ita.Idan ta tara sai Hajow ta kwashe tun da ita take kulawa da ita basu saka kowa ba da ita da Sir da sauran ahalin suke kula da ita cike da tausayi ta da ƙaunar ta.
Hannun ta, ya janyo cike da sakin murmushi yana cewa " Haba Maama ta ai ni mijin ki ne fa ba sunan kawai na ci ba,ai Sir shaida ne ,shi na biyo dan dai tsufa ya cinye muna ke ai kema kin san da haka ".
A wannan karon Hajow kasa hakuri tayi ta masa daƙuwa.Dariya yayi cike da farin ciki.Kafin ya ce " Ai ina son Mamaa Gashi harda kilishi na tana do Miki mai daɗi ".
Baki washe kuwa kukan ya tsaya nan hawaye
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 39