An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Update👇
https://chat.whatsapp.com/BzXaAD3pB6yJ1wBBrkE4V0
Masu son ganin ƙarshen labarin suyi following ɗina.👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*💋KURMAN ƘADDARA💋*
©®Fa'iza Almustapha Murai
Daga Alkalamin✏
👄FA'EEH BG👄
💎Sadaukarwa ne ga class mate ɗina ɗalibban GGC T/MAFARA,ZAMFARA STATE SET 2K18💎A duk inda kuke Alkhairin Allah ya kai muku.🤲💎
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai
ya Allah ina tawassali da sunayenka tsalkaka Allahu,Arrahmani,Alwadudu Yaa ubangiji kabani ikon kammala kk story lafiya kamar yadda kabani ikon wallafa shi cikin kuzarin jikina da ƙwaƙwalwalta.
_______________________________________
💋KK💋Story ƙirƙiraren labari ne,duk wani abun da ke cikin labarin ƙirƙira ne, Idan kuma yayi shige da rayuwar ki kiyi haƙuri a kasine ,banyi rubutuna dan cutar da kowa ba,sai dai nayi ne dan kawo Sauyi ga alumma da cigaba......
*WARNING!!!*
Ban yarda wani yayi amfani da wani sashe na kk story ba ko ajuya minshi ta wata sigar ,ko akaranta mini shi ta youtube,ko ɗaura mini a wasu shafuka sai da izini na idan kuma kika yi mini ganganci na barki da rabbil izzati....
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
👄FA'EEH BG👄
*(FirstLady🙌)*
--------------------------------------------------------------------
Littafan marubuciya
A MAFARKI NASANTA
RAYUWAR MU A YAU
------------------
*BOOK ONE*
Free pages👌
P.0️⃣1️⃣
The story is all about ........
*# Destined*
*# Jeoleus*
*# Arrogant*
*# Love and romance*
*# Hatred*
*# Politics*
*# Sympathy*
*_THE BEGINNING_*
*SULEJA*
Daji ne dake cikin garin suleja wanda ake kira ƙare kukan ka.
Babu abun da ke tashi sai kukan tsuntsaye kala kala sai kuma yana yin yadda itatuwa ke kaɗawa suna bada iskan hunturu mai daɗi kasancewar lokacin sanyin da ake ciki.
Matashiyar budurwa ce ke tafiya cikin dajin a hankali da wani irin tulelen ciki a jikin ta da alama cikin zai kai kamar wata shida haka ko bakwai.Hawaye ne jage jage a kan fuskar ta ga idanun ta sunyi wani irin jaaa tafiya ce ta ke yi wadda bata san inda take jefa ƙafafun ta ba.Yadda take tafiyar kai kan ka zaka shaida a gajiye take kuma a galabaice.Kukan karnuka da taji a bayan ta ne hakan ya sa ta fara sauri tana ƙarawa tafiyar ta sauri kafin ta haɗa da gudu domin kuwa ko ba,a faɗa mata ba ta san ko suwaye kuma suka cimma ta rayuwar ta na cikin galalari domin kuwa kisa ne mai zafi zasu aiwatar akan ta domin yadda suka yi neman ta a chan nan ma hakan ne zai kasance.Cikin wani irin gudu haka take kutsa ƙafafun ta cikin ramukkan dake gaban ta da tulelen cikin na ta ga wata irin Hajijiya da ke kama ta wadda ba ta san mafitar ta ba.Sai dai tana fatan da irin wannan yanayi gwara mutuwar ta domin kuwa wata irin azaba ce ke ta so mata na gudun da take yi dan gudu ne bana wasa ba.Tana kawowa dai dai bakin wani ƙaton rame mai kama da kogo ta faɗa nan domin tsira da rayuwar ta da abinda ke cikin na ta tana sauke haki kafin kuma kan ta ya buge da wani irin ice da bata lura dashi ba A cikin kogon wanda hakan ya sanya ta fara ganin dishi dishi kafin kuma Numfashin ta ya ɗauke ɗiif.
***
*A WALA*
Sararin samaniya ne da ya ke bada wani irin kala mai kyau da ke ƙara Haska gari tare da ranar da take Kutsowa a lokacin wanda a lokacin ne kowannenn mai fita nema yake fita dan samar wa kan sa abun saka wa a bakin salati,fita irin ta yau da kullum.
Ƙauye ne mai tarin hikima kowane irin yare ya haɗa Fulani,Fulani Hausa, wuri,sai dai Fulani sun fi yawa.ƙauye ne wanda ke ɗauke da manyan mutane masu al'adu da ban daban masu hikima,Sannan ƙauye ne da mutanen cikin sa suke yin ta ka tsan tsan da tarbiyyar yan matan su kuma suke ƙoƙarin bawa ya yan su ilmi na Addini da na boko gwargwado...
***
Gudu take a hankali kamar wata zakanya a cikin dajin har da wani irin tsalle kamar wadda ke gurin yaƙi yanayin yadda take tsallakar itatuwan da suka yi mata kawanya da abun harin ta.Ba,a iya ganin fuskar ta sai dai bayan ta da yake ɗauke da dogon gashin ta.Dai dai ta isa inda zata ɗana kibiyar ta kenan taji ana furta..
" Adda shatu,Kiyi Sauri ki kama kar ki bari Baffa na ya riga ki " .
Saboda yadda suka hango abin farauta yana ta ƙara falla gudu.
Da jin wannan furuci na wannan yaro aiko ta ƙara ƙaimi wurin saita abun harin ta wanda ke gudu daga nesa domin tsira da ransa.
Ganin kamar tayi gaba da yawa hakan ya sa ta dawo baya da sauri inda ta ja da baya kamar yadda kuka san Actors na yi a film irin na farau ta haka ta ja daaga ta ƙara saita abun harin ta inda ta juya a hankali ta kalli gefen ta tana kallon mutumin da nake tunanin shine Baffa na ganin da tayi yana shirin sakin ta sa kibiyar hakan ya sa ta sakin murmushi kafin a hankali ta saki nata a tare kibiyoyin nasu suka kama hanya suna bin abun harin na sua jere.Wani irin tsalle ta buga tana ɗaga hannayen ta sama tana furta.
" Baffa na ka riga ni zuwa kuma ina ga na cinye ka ta wa ta fara isa ".
Juyowa tayi tana tare yaron da ya kawo kusa da ita wanda kamar ba zasu wuce sa,anni ba sai dai da ka gani zaka iya tantance wanda ke babba a cikin su.inda ya rungume ta cikin farin ciki, ita ma Rungume shi tayi kamar yadda ya rungume ta sannan suka saki juna suka fara gudu a tare cikin nishaɗi sai dai basu wuce mintuna biyar ba suka isa inda dabbar take domin kuwa ƙatuwar dabba ce suka samo yau kamar yadda suka saba fita farautar su itadah mahaifin ta da ɗan uwan ta wani lokacin ma ita ke fita ita kaɗai duk da yadda take shan magana akan fitar ta ita kaɗai,ko kuma da wannan yaron wanda da alama shi ne ƙane sai dai duk da hakan da gani ka san babu wata tazara tsakanin su dan sai ka yi zaton Yan biyu ne ma.
Suna zuwa bakin ƙatuwar Dabbar da ke kwance yashe,Tsalle suka fara wanda yayi dai dai da zuwan wani dattijon mutun kamar bafulani domin fari ne tass wanda kamar su ke sak da yaron.Wata uwar zabira ya Fiddo daga cikin wata yar jaka tashi Sannan ya sai ta wuƙar sa mai kaifi a Wuyan kurar ya yi Bismillah ya yanka inda take jini ya ƙara ɓalle wa a wuyan ta, 'yan murje murjen da take yi take ya tsaya Chak.Bata ƙara shurawa ba.
Yana gamawa ya ɗago ya kalli Yar Matashiyar yarinyar da aka kira Adda Shatu wadda a ƙiyasi shekarar ta bata wuce goma sha biyu ba ko sha uku ba sai kuma shi yaron bazai wuce goma ba ko sha ɗaya ba kamar dai saanni suke.
" Shatu na ta kashe kura,gaskiya ya kamata a baki kambun girma,maza da yawa ba su iya samun abun harin su kai tsaye amma shatu na take ta ke bin shi da kibiya na jinjinawa Yar Inna Adda ta,Kuma Adda Shatou bace wa Baffa ya yi ki zauna gida ki huta ba shine kika fito,ya ma akayi Inna ni tabar ki kika fito ne?? "....Matashin yaron ya kai ƙarshen furucin yana kallon ta yana ƙara tsalle cikin murna Haka ma Baffa na murmushi yake yi kawai yana kallon ta bayan zare kibiyar ta da ta ture ta sa.........
* A gajiye take saboda ta aikatu yau matuƙa duk sai da suka cika komai na gidan gashi daga gurin jidar ruwan akwai nisa,Sannan tare da mahaifiyar ta suka yi ayyukan gidan har aikin gyaran gefen dabbobin su Baffa na da Bibu ke yi.Kafin kuma ta bi bayan mahaifin ta da suka fice tun ɗazu bayan yin karin kumallon su,duk yadda ta so hana ta haka ta barta saboda kukan da ta sanya mata har da murje murje.Tunda ta fito take gudu kamar bazata daina ba saboda nisan wajen da zata isa a cikin ƙungurmin dajin da suka saba farauta ita da mahaifin na ta.
Duk wani mai kiran sunan ta bata ko sauraren sa babu abinda ta ke son gani face ta isa inda ta san zata same su.Wasu kai tsaye suke kiran ta da mara kamun kai saboda yadda take tsalle tsallen ta dan ta ɗebo gadon mahaifinta takan saci hanya ta fice ita kaɗai basu ko duba ƙarancin shekarun ta,sai dai a sanar da mahaifin ta an ganta ita kaɗai ta fice farauta,wanda hakan mutanen ƙauyen sai suke faɗe faɗe akan ta wasu har mahaifin ta suna yiwa magana kan yadda ya ke barin ta shiga daji farauta duk iya ƙoƙarin sa shida mahaifiyar ta ga ƙarancin shekarun ta kuma da alama bata tsoron kowa duk da bata shiga harkar kowa,sai an Jata. Bata samu jin ta dai dai ba sai da ta isa dai dai inda zata same su sannan ta dakata.Dukkanin su da suka gan ta Murmushi kawai suka yi dama sun san za,a rina,Saboda yau weekend ce babu makaranta,ta allon ma ta su yau ba,a zuwa.Shiru tayi bayan tuno yadda ta fito kafin ta ƙara sakin murmushi ba tare da ta bashi amsar tambayar sa ba ganin yadda yake ta murna kafin ta ƙara ɗana wani mashin ta jefi tsuntsuwa da tayi fira daga kan iccen Mangwaro a yanzu aiko cikin sa,a sai gata ƙasa tana bille bille da sauri Baffa ya yanke wuyan yar kurciyar yana murmushi ganin yadda ta ƙara cilla ta ya san shatu da namiji ce anan gaba da tafi shi ƙwarewa akan harbi duk da ko yanzu tana nuna masa iyawar ta duk da tana da ƙananan shekarun ta.
Tsalle ta daka " Na ƙara samun sa,a Bibu " tayi furucin tana kallon yaron. murmushin farin ciki yaron ya saki yana tsallen murna shima a karo na biyu.
Murmushi mutumin da suke kira Baffa na yayi wanda yake matsayin mahaifin su.
A haka suka haɗa komai na su na farauta sannan suka doshi wani ƙaton rafi aka gyaran naman tsafff sannan suka kama hanyar gida kai tsaye kasancewar sun yi sa,ar fita yau lokaci ɗaya sun yo farautar Babban Kamu.
Sai da suka yi tafiya mai tsawo daga cikin jejin sannan suka iso dai dai wani ɗan madaidaicin gida na ƙasa da ya ji fenti fari sai kuma wasu yan bukkoki dake cikin sa tare da wasu ginukan ƙasa da ake iya hangowa ta ciki saboda rashin girman katangar.
Da sallama ɗauke a bakunan su suka shiga cikin gidan.
Yar matashiyar matar dake zaune a kan tabarmar kaba ce wadda kamar ta take kamar an tsaga kara da Shatou saboda ita ta biyo bata wani kama da Baffana ta amsa Sallama fuskar ta cike da murmushi tana kallon su musamman Shatu dake ta tsallen murna na irin ƙwazon da tayi a yau ɗin duk da dama tana yawan samun abun harin ta awurin farauta amma na yau ya banbanta saboda Babban kamu tayi ba irin ƙananan dabbobi bane.
" Maraba lale maraba ".
Ta yi furucin bayan amsa Sallamar su miƙewa tayi da ɗan sauri ta riƙa ma Baffa kayan dake riƙe a hannun sa cikin sakin fuska.
Murmushin ya saki shima tare da sauke ƙwaryar naman da suka feɗe a bakin wani rafi.
"Sannu da dawowa Baffan su."
"Yawwa Sannu A'i "
"Kin san yau Mutuniya ta tayi muna babban kamu".Ya ƙara yin furucin yana murmushi.
Murmushi ta yi tana mamaki mai girma da wannan lamari nan Shatou gashi bata san yadda zata raba ta da Farautar nan ba.
A hankali ta kalli kuma ta kalli Shatu dake ta murmushi ta furta " Su Hajiya rigima an yi sa,a,Kuka fa ta zauna ta na mini harda murje murje,Allah da na same ta da sai ta ci na jaki yan nema shekara sha biyu cikin ta uku babu wayau sai rigimar tsiya,ko Bibu na yafi ta hankali ".
Murmushi Baffa na yayi yana furta " Sai gata kuwa,na so ace ta zauna ta huta,bana son yadda mutanen ƙauyen nan ke magana akan guje gujen ta ".
" Allah dai ya shirye ta indai Shatu ce sai Addu,a,Allah ya shirya maka ita ".
Inna ni tayi furucin
" Amin A'iie ". Baffa na yayi furucin yana sakin murmushi yana kallon Shatu da ta turo bakin ta gaba ganin Bibu na dariya ƙasa ƙasa ance yafi ta hankali.
Sallar la,asar kawai kowa yayi yi suka huta suka ci abinci sannan suka zauna a tare suka yi aikin yanke naman tsaff ita da su Bibu da shatu yana yi yana bata labarin yadda komai ya wakana a chan dajin.Ita ko tana mitar guje gujen da zuwa farautan na ta da yawan fita ma da take yi a sace da take ƙokarin hana ta.Amma abu ya gagara.
A haka har suka gama zuwa lokacin ta hura wuta da yangan ice da shatu tayo jiya
Har aka kusa Sallar magriba suna nan zaune suna taɓa fira tare da ƙara rura wuta akan tukunyar dahuwar naman su,wanda suke dafa wa a matsayin abincin daren su.
Wanka kowannen su yayi Sannan mazan suka wuce Masallaci dan gabatar da sallahn magriba.Suna dawowa dai dai naman yayi rugu rugu,Inna ni ta gama shirya komai da taimakon Shatu suka zauna suka ci suka ƙoshi kowannen su yayi nak.
Sannann Aka yiwa su Shatu bitar karatun su.Sallar Isha'i ce ta tashe su gaba ɗaya Sannan kowannen su ya wuce wajen sauƙe Haƙƙin Allah dan har yaran iyayen su sun sabar musu da yin Sallah a lokacin ta.
Tun da aka gama Sallolin Isha bayan dawowar su Baffa da Bibu Inna ni kamar yadda suke kiran ta,take jiran fitowar Shatu daga ɗan madaidaicin ɗakin na ta da yake kamar yar bukka saboda ba wani mai girma bane, sai dai wayam shiru babu labarin fitowar ta.A zaton ta ma sallar ce bata gama ba amma sai gashi har aka gama sallolin mazan suka shigo gidan babu labarin ta,sai dai dan tabbatar da zargin ta bayan shigowar ta su ya sa ta faɗa dakin na ta yadda taji shiru haka ɗakin yake babu mai kama da shatu sai yan kayan ta da yar tabarmar ta dake da ɗauke da zanen shimfiɗar ta ko ina tsaf sai dai ga kayan da ta cire nan yanzu a watse ta chanza wani.
Shiru tayi bayan fitowar ta daga ɗakin kafin ta nisa ta girgiza kan ta.Yawon shatu tsoro yake bata data samu dama sai ta fice daga gidan duk irin faɗan da take mata a banza gashi wata rana harda bugu take haɗa mata mata dashi dan ma Baffa na, na hana ta da kullum sai ta jibge ta.
" Ta fice ko "???
Baffa ya yi furucin yana girgiza kan sa shima fuskar wanze da Murmushi dan ko ɗazu kafin su fice sallah sai da ya ce mata " banda fita Shatu a zauna gida a huta a haka yau anyi farauta Babba."
Ashe bata shiga kunnen ta ba maganar.
Kai kawai Inna ta iya ɗaga masa tana zama akan sallayar da ta sha jiki wadda ta shimfiɗa akan Tabarmar kaba da take kai.
Charbin ta da take jaa ta cigaba da jaaa sai dai hankalin ta na kan yar ta tsoron ta ɗaya kar ta jawo musu abun magana saboda Mafaɗaciya ce ta ƙwarai shatu koda yaushe cikin kawo ƙarar ta ake gidan ta yiwa wani, wani abun daga cikin warin ta ko wayen da basu kai ta ba har manya ma in suka shiga gonar ta sai ta rufe ido ta yi rashin mutum ci shi yasa bata shiga sabgar da bata shafe ta ba saboda bata da haƙuri idan ka taɓa sai ta rama a kullum Addu,ar iyayen ta kenan samun hankalin ta na wannan yawan faɗaɗace faɗacen, idan ka mata kallo ɗaya zaka hango natsuwa a tattare da ita amma ana taɓa ta zaka san akwai ruwan rigima da suke ɓoye a cikin ta,wanda Tsokanar ta ke iya tsokalo su.
"Baffan su,wai ni Shatu ba igiya zan fara saka mata ba,tsoro nake ji ta jawo muna wata rigimar domin ban manta karon ta da ɗan gidan mai gari ba da yan zu ya illata ta ga tsoro ga ban tsoro kura,bana son fita wasar nan ta Dare".
Murmushin Baffa yayi jin Furucin Inna ni kafin ya sauke Kan sa ƙasa Yana kallon Bibu dake jin kamar ya saka kuka jin mahaifiyar su ta fara zancen ɗaure Adda shatu.
" Baza,ayi haka ba ai ".
" Na san abun da zanyi A'ie."
Bata iya furta komai ba ta miƙe daman bata yi shafa'i da wutiri ba ta kabbarta Sallar ta,.Sai dai Ranta a jagule yake matuƙa.Kusan kullum sai ta mata faɗa Dan shi Baffa bai son ana mata faɗan ma ko kaɗan idan tayi sai yayi ta Rarrashin ta yana mata faɗan cikin hikima a cewar sa yarinya ta ce,kuma ya san duk wanda ta taɓa shine ya fara tsokanar ta.Bibu kuwa da Baffa cigaba da bita karatun Alqur'anin suka yi a tare hankali kwance duk da rabin hankalin su na kan Shatoun su.
A ɓangaren Shatu kuwa tunda ta samu ta fice ta ke fanfala gudu kamar wadda take harin abu farautar ta a daji bata tsaya ba sai inda suka saba tsaya wa suyi wasannin su ita da sauran ƙawayen na ta.
Sai dai yau anyi rashin sa,a duka basu taru gurin ba sai ita sai mazan dake wajen yan na iya masu zuwa kallon su.
Wuri ta samu ta zauna zaman jiran su saboda zasu kai su goma amma manyan ƙawayen ta su uku ne kuma kan su komai tana iya yi mafi yawan rigimar ta akan su ne su aka taɓa saboda kowa na tsoron shiga sabgar ta.
" Yan mata ".!!
Duk yadda take jin sautin na shiga kunnen ta bata jin zata ko kalli mai maganar Dan bata da lokacin sa,saboda ta raina sa tun asali,kuma ta san kowane ne.Ibro ne ɗan gidan mai gari da yake ta Bibiyar ta..
Like and share.
Ku ta yani Sharing saboda Allah.🙏
Daga Alƙalamin✍️
Firstlady🙌 (Fa'eeh BG)
GIMBIYAR TASKIRA 👑
08069059746
For more information👆
UPDATE👇
https://chat.whatsapp.com/BzXaAD3pB6yJ1wBBrkE4V0
Masu son ganin ƙarshen labarin sai suyi following channel ɗita.👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*💋KURMAN ƘADDARA💋*
©®Fa'iza Almustapha Murai
Daga Alkalamin✏
👄FA'EEH BG👄
💎Sadaukarwa ne ga class mate ɗina ɗalibban GGC T/MAFARA,ZAMFARA STATE SET 2K18.A duk inda kuke Alkhairin Allah ya kai muku.🤲💎
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
______________💔
_Wannan Shafi naki ne baki ɗaya masoyiya ta AMMYN LAYLAH 😘💞 Ina godiya da kulawar ki a kaina da wannan labari,Ina roƙon Alkhairin Allah ya kai Miki A duk inda kike,kuma ya raya muna Love(Layla).🥰🤲🏾_
______________💔
_Daga marubuciyar littafin_
*A MAFARKI NASANTA*
*RAYUWAR MU A YAU*
'''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''’'''
*BOOK ONE*
Free pages👌
P..0️⃣2️⃣
Shiru ta masa tana fatan kar ya ƙule ta ta masa rashin mutunci kamar na ranar Da ya tashi kaɗe ta, ta fahimci bai da zuciya bai ji kashe din da aka musu ba a tsakanin su.Tunda har zai iya Binta a karo na biyu.Ganin ya dawo ta gaban ta yasa ta ƙara ɗauke kanta tare da rufe Hancin ta irin na wari yake yi dan ta ɓata masa rai da siffar wulaƙanci duk da ba warin yake yi ba.
Shiko Iro murmushi kawai ya saki na yaƙe sannan jiki mace ya ja baya yana komawa cikin yan uwan sa da suke masa dariyar abun da ta yi masa duk da ya san laifin sa ne,amma zai yi maganin ta zai cire mata girman kan dake kan ta.
" Ya kamata fa ake ce raini dake tsakanin ka da Yar shilar chan yarinya ba komai a ƙirji sai ƙwailanci amma kana ta Bibiyar ta tana dizga ka,yaro mai ilmi duk ƙauyen nan kana Buz guy,gaskiya Iro ka yi tunanin abin yi dan ni waccan yarinyar tsafff zan iya karya ta karass na watsa ƙasusuwan ta a rafi "
Wani daga cikin Abokan na sa ya faɗa kai tsaye bayan tsaida dariyar sa ta ƙeta ganin iro na masa kallon bana son haka.
Iro dai sauraren sa kawai yake yi sai wani cije baki da yake yi yana jan yaji irin na ɓacin rai wanda ya taso masa yanzu.Musammman da ya tuno rashin mutuncin da tayi masa a ranar da ya so buge ta da mashin ɗin sa mara shalan sa da ya addabi ƙauyen da shi wanda ya zo dashi bayan gama JLC ɗin sa da yake faɗin degree ce da ya kwashe yan shekaru a A birni.Anan ƙauyen ma ana secondry school bayan primary wanda kuma nan iya bokon na su yake ƙarewa bakin SS3 wasu ma basu kaiwa ake musu Aure wasu kuwa sukan fitar da ya yan su birane masu kuɗi kenan sai su cigaba da karatun su.Kamar dai Iro ɗai daga cikin ya yan mai gari wanda bai ma fara karatun a nan ba ya fara karatun sa a birni tun Daga jss1 zuwa jss3 bayan gama primary ɗin sa wanda rabi da kwata yawon banza ne da kashe ma matan hanya kuɗaɗe da tangaririya a cikin gari sai ya dawo ƙauyen yana fafa da sunan Jami'a yake yi har ya ci wasu shekaru a chan bai haɗa ko Takardar gama secondry ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 39