Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da magananshi, Sadeeq haɗe fiska yayi tare da cewa, "Zan iya", a taƙaice yayi maganar. Umar sarai ya gane dalilin haɗe fiskan Sadeeq , hakan ya sanya ya ɗage kafaɗanshi irin ohk ba matsala, sannan ya matsa gefe yana faɗin, "Bismillah." Sadeeq maida idanuwanshi yayi ya lumshe, sai da ya busar da iska mai zafi a bakinshi, sannan ya yunƙura cike da jarumta, da bismilla ya samu ya tashi zaune, ƙirjinshi yake jin nauyi sosai, hakan ya sanya ya ɗan dakata, kamunnan ya ƙarisa miƙewa tsaye, cikin takun da ke nuna yana cikin ciwo, ya ƙarisa toilet ɗin. Umar da ke binshi da ido, yana ganin shigewanshi ya zauna a gefen gadon da Sadeeq ɗin ya tashi, yana faɗi a ranshi ba zai bar lamarin shiriritar Sadiya ta ƙarisa Sadeeq ba. Alwala Sadeeq ya ɗauro ya fito, ya samu Mama ta ida sallahn har ta tashi a kan darduman, sai ya ƙarasa a nitse ya tsaya ya kabbara sallah. "Assalamu alaikum", sallaman Abba da Sa'ad ya karaɗe ɗakin, su Umma du suka amsa cikin haɗin baki, sannan Abba da Sa'ad suka shigo, kallonsu suka kai ga gadon da Sadeeq ke kwance, Abba na ƙoƙarin yin magana ganin gadon empty ba kowa sai Umar da ke zaune a gefe, Sa'ad ya riga shi ta hanyar cewa, "Kai amma alhamdulillah ma sha, Yaya Sadeeq ya tashi har yana sallah a tsaye." Abba kallonshi ya kai ga Sadeeq da ke raka'a ta biyu a sallahnshi, "Alhamdulillah, Allah ƙaro ƙarfin jiki Abubakar." "Amin ya Rabbi, sannunku da dawowa Abba", Umar ya faɗi yana murmushi. Amsawa Abba yayi shi ma da murmushin, sannan ya amsa sannun da Umma da Mama suka mishi, ya ƙarisa wajan ɗaya gadon da yake empty wanda nan mai jinyan mara lafiya ke kwana, ya zauna yana amsa gaisuwan Mama, ya kuma ɗaura da cewa, "Ya jikin ita auta? Fatan dai da sauƙi? Ita da wa aka baro a gidan?" "Jikinta da sauƙi Abban yara, na baro ta ita kaɗai, ban ma jima da zuwa ba." Abba cikin rashin jin daɗin cewa an baro Sadiya ita kaɗai ya ce, "Ma sha Allah! In dai har kun gaisa da Abubakar ɗin, to ku yunƙura direba ya maida ku gida, bai kamata a barta ita kaɗai ba." Umma da Mama amsawa suka yi, Umma murmushi tayi dan tasan za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, daman ɗazu ma sai da ya gama faɗanshi ya tafi. Sadeeq cikin nitsuwa ya ida sallahnshi ya sallame da addu'oinshi, sannan ya juyo a nitse cikin girmamawa ya ce, "Sannunku da shigowa Abba." Washe baki Abba yayi cike da godiya ga Allah da jin daɗin tashuwan yaron nashi ya ce, "Yauwa Abubakar, sannunka kai ma, fatan jikin da sauƙi?" "Alhamdulillah", Sadeeq ya faɗi yana jinjjna kai. Mama ce ta miƙe ta jawo basket da suka zo da shi, ta saka wa Sadeeq Kunun wanda yake na markaɗaɗɗen shinkafa da gyaɗa har da kwakwa, ya ji kwakwa da gyaɗa yayi wani fari yayi fresh kaman kindirmo ko youghourt. * Za ku iya samun littafin a wannan manhajoji. BAKANDAMIYA HIKAYA. AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: 💔NAUYIN BAKI....👄💔 Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠 اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 36 _ 40 ⭐️ Ganin kunun kaɗai a ido sai ranka ya biya, ba tare da Mama ta saka sugar ba sanin Sadeeq ba ya shiri da sugar, madara kawai ta saka ta gauraya mishi sannan ta miƙa mishi tana murmushi ta ce, "A lallaɓa a sha ko mai babban suna." Sadeeq da hannu biyu ya amsa cikin girmamawa ya ce, "Allah ya saka da alkairi Mama." "Amin Babana, Allahu ya ƙaro lafiya da ƙarfin jiki." Abba cewa yayi, "To maza ku je direba ya maida ku, a kula da auta sosai." Umma miƙewa tayi Mama ma haka, ƴan kimtse-kimtse da abinda za su tafi da su suka haɗa, sannan suka nufi ƙofa suna yiwa Sadeeq fatan Allah ya ƙara sauƙi. "Kai ma Umar ka bi su ka samu ka watsa ruwa, sannan sai ka dawo", faɗin Abba. Umar ya ce, "Abba na ɗauka ko zan jira ku je kuyi sallah tukunna." "Mun yi Sallah a nan masallaci kamun muka shigo, kai kam kaje ka samu kai ma ka huta, yau kam dai tunda Abubakar ɗin ya tashi kuma da alama jikin da ƙwari ma sha Allah, ya ma kamata ka kwana gida, Khalid ya zo ya kwana da shi." Taƙaitaccen murmushi kawai Umar yayi, bai ce wa Abba komai ba ya miƙe ya fice ya bi bayan su Umma, ya samu duk sun shige mota direba na ƙoƙarin yi mata key, ganin Umar sai ya dakata, sai da Umar ya shiga sannan direba ya yiwa motar key suka fice a asibitin suka nufi gida. Suna tafe Umma ke cewa, "Amma dai yau kam ya kamata ka kwana a gida ka huta ko Umar." Murmushi Umar yayi ya ce, "Umma me abun wahala a jinyan? Ba fa abinda nake yi na wahala, Abba ya ce na huta kuma kun ce na huta, ba wani aiki nake ba a jinyan, kuna gani dai ɗazu ma da kanshi ya tashi ya wuce toilet, ai ba wani gajiyan da zan buƙaci hutu", ya ƙarishe magana yana feeling he can't stay at home while Aminin shi Sadeeq na asibiti. Mama ta ce, "Allah ba wa mai babban suna lafiya da ƙarfin jiki cikin gaggawa, duk ku dawo gidan ku huta tare." Duk da, "Amin", suka amsa har direban, sannan Umar ya ce, "Yauwa Umma, fatan dai ba ku sanar da Sister Khausar maganan jikin Sadeeq ba? Dan mun yi da Abba kar a sanar mata, duk da dai ta matsa da ƙira na wai bata samun Sadeeq kusan week kenan, dan ko ɗazu kamun magrib ta ƙira ni." "Ba wanda ya sanar mata, Abbanku ya hana ai, ni jiya da yau ma duk bamu yi magana da ita ba, ko ya take da yaran nata da mijin nata", faɗin Umma. Umar ya ce, "Duk suna lafiya ta ce ma suna hanya in sha Allah mu zuba ido." Mama murmushi tayi ta ce, "Nima dai haka ta ce mini a satinnan suna tafe mu zuba ido, na ce to mun kuwa zuba, Allah ya kawo mana su lafiya cikin aminci." "Amin Ya Rabbi", duk suka faɗi. A ƙofan gidan su Umar direba ya fara parking, Mama da Umar suka sauƙa, Mama na yiwa Umma a huta gajiya, Umma ta amsa tana faɗin za ta shigo duba jikin autarta ai, sannan direba ya wuce nasu gidan, sai da suka shiga ciki yayi parking sannan Umma ta fito, direban yana mata a huta gajiya ta shige ciki. Umma na shigowa palourn ta hangi Khalid zaune a dinning yana cin abinci yana danna wayarshi, kasancewan ya ji sallaman Umma har ya amsa, yana murmushi ya ce, "Sannu da dawowa Umma, ya jikin Yaya Sadeeq ɗin?" "Yauwa Autan maza kai ma sannu da dawowa daga aiki, jikin Yayanku da sauƙi suna can mun baro su da Abbanku wataƙila ma suna hira." "Lahh! Ya tashi ne Umma?" "Eh ya tashi tun da jimawa, sai ka bi Umar ka gano shi." "In sha Allah kuwa Umma, daman na ce sai da safe zan je dan yau na gaji sosai wallahi, ba Yaya Sadeeq ba Yaya Umar ayyuka kaman za su hallaka miki autan maza, amma tunda Yaya Sadeeq ya farka, zan je na kwana can tare da Yaya Umar." "To Allah ya kai ku lafiya, Rabbi ya muku albarka." "Amin Ummanmu, bari na ƙira Yaya Umar ya jirani mu koma tare, a huta gajiya Umma" Da "Yauwa", Umma ta amsa tana murmushi ta haura sama ta wuce ɗakinta. Khalid a gaggauce ya kammala cin abincinshi ya mayar da plate ɗin kitchen, don wannan tarbiyan Umma ne, duk da kuwa suna da masu aiki, to Umma ta horar da su muddin suka ci abinci to su ɗaga kwano, in ba dai in general aka ci abincin kowa da kowa ba, amma indai kai kaɗai ka ci abinci to za ka ɗaga kwano ka maida kitchen. Khalid na fitowa a kitchen ya koma ɗaki ya ɗau abinda zai ɗauka ya fice, motar Yaya Umar da dashi ya je wajan aiki ya yiwa key aka buɗe mishi gate ya fice a gidan, a ƙofan gidan su Umar ɗin yayi parking sannan ya fito ya shiga cikin gidan da sallama. *** Sadiya tana jin Mama ta gama magana har ta fice, bata ko motsa ba balle batun ta amsa wa Mama, and she's still crying, feeling like ta kulle idonta ta ganta a gaban Yaya Sadeeq nata, saboda kwata-kwata bata ji a jikinta like Yaya Sadeeq ya tashi, she just saw him unconsciousness in the morning, some hours ago, and now a ce ya tashi, Yaya Sadeeq ya tashi kuma a ce ta yi kuka bai lallasheta ba, how on earth would this be possible?, Yaya Sadeeq dai ta yi magana bai amsata ba, "Noo! It's not him", ta faɗa a fili with a crying sound, a jikinta take ji daman ba shi bane kawai ana son yi mata wayo ne, saboda haka cigaba tayi da kukanta. Sadiya har aka ƙira magrib tana nan inda take kwance tana kan kuka, wanda har muryanta ya dishe and she's having a very strong headache, worse than before, saboda ji take like her head will fall off, idanuwanta kuwa har rufewa suke, a haka ta lallaɓa ta shige toilet da ke a ɗakinta, alwala ta ɗauro sannan ta fito, walking slowly har ta sanya hijabi ta haye darduma ta tada sallah, ko da ta idar addu'a ta ɗaga hannunta tana yi tana kuka. Mama ko da suka shigo gidan tare da Umar, ce mishi tayi, "Za ka fara sanya wa cikinka wani abu ne ko sai ka shirya?" "Bari na watsa ruwa tukunna Mama", faɗin Umar yana ƙoƙarin fara cire agogon da ke maƙale a hannunshi. "To kamun ka fito bari na dubo rigimammiyar yarinyar nan, na tafi na barta tana ta shan kuka." Umar ƙwafa yayi tare da wucewa ɗakinshi, shi shirirtar Sadiya da duk wani sakalci da take ai samun waje tayi, yarinya ta girma har ana hada-hadan aurar da ita amma tana abu kaman ƴar goye, watarana ji yake kaman ya sauya ƙanwa saboda tsabar yanda abubuwan Sadiya suke hawa kanshi, da ace shi da Mama sun ɗaure mata wajan zama to da wataƙila abun nata ba zai ganu ba balle ya faɗu. Mama da kofin da ta sako wa Sadiya kunu tun kamun ta tafi ta fara karo, sai yanzu ma ta tuna Sadiya bai wuce kurɓi uku ta yiwa kunun ba ta ajiye kuma bata ci komai ga, ɗazun tana saurin zuwa asibiti dubo mai babban suna bata tuna ba sai yanzu, girgiza kai kawai Mama tayi ta nufi ɗakin Sadiya, tana addu'an Allah ya sa ta bar kukan ta ɗibo tuwo ta ci. "Assalamu alaikum", Mama ta yi sallama sannan ta tura ƙofan ɗakin ta shiga, idanuwanta suka sauƙa a kan Sadiya da ke zaune kan praying mat ta tsura wa waje guda ido tana kuka mara sauti saboda muryanta da ya dishe, don ciki-ciki ma ta amsa sallaman, Mama ko jiyo sautin bata yi ba kawai dai ta san Sadiya ta amsa sallaman. Ƙarasawa ciki Mama tayi tana faɗin, "In ce dai kin bar kukan kin bai wa cikinki haƙƙinshi?" Sadiya tura baki tayi, idanuwanta na sake cikowa da ƙwalla. Mama tunda ta ji shiru to ta san sarai Sadiya bata ci komai ba, aikin kukan kawai take yi, tunda dama ita ba mai wuyar kuka bace, cikin sigar faɗa ta ce, "Sadiya wai kam ke ƴar goye ce? Iya idanuwanki da hawayenki ke da haƙƙi a kanki da za ki wuni kuka? Cikinki bai da haƙƙi a kanki ne? Ko kuwa lafiyanki bai da haƙƙi? Ba ki ci tuwo ba balle a yi maganan magani, idan har baki bar kukan nan ba Yayanki Umar zan turo miki ki mishi kukan da kyau, ƴar buhun albarka kawai", Mama ta ƙarishe faɗan tare da juyawa ta fice a ɗakin, kai tsaye kitchen ta wuce, tuwon shinkafa da miyar busashshen kuɓewa da nama zuƙu-zuƙu, shi ta ɗiba wa Sadiya a ƴar kwano, sannan ta saka wa Umar nashi, baro na Umar ɗin tayi a kitchen, sannan ta ɗau na Sadiya da ruwan leda ta fito a kitchen ɗin, tana kan mitan Allah ya shirya mata Sadiya. Sallaman Khalid shi ya katse mitan Mama, ta amsa tare da sake fiskanta tana faɗin, "Yaron Abba ne da yammacinnan." Khalid murmushi yayi tare da ƙarasowa ciki yana faɗin, "Eh Mama, na zo ne na bi Yaya Umar mu koma asibiti wai Yaya Sadeeq ya tashi." "Ai kam mai babban suna ya tashi jiki sai godiya alhamdulillah, Umar ɗin yana ɗakinshi sai ka ƙarasa ciki bari na kai wa rigimammiyar ƙanwarku tuwo." "Lah! Wallahi na sha'afa Mama, yau aiki kaman zai hallaka ni, na mance da autar Umma, a bani tuwon na kai mata sai na mata ya jiki, kamun Yaya Umar ya fito", faɗin Khalid da ya ƙaraso gaban Mama ya miƙa hannu zai amshi kwanon tuwon Sadiya. Mama miƙa mishi tayi har ruwan tana faɗin, "Yau da rigima take ji autar Umman, wuni tayi kuka, ka mata da gaske ta ci tuwon bari na ɗauko magungunanta." Khalid amsa yayi ya wuce ɗakin Sadiya, da sallama ta shiga ɗakin, a kan darduman ya same ta har yanzu tana zaune, ƙarasawa yayi gabanta yana faɗin, "Ran Amaryan Haidar ya daɗe, Allah ya huci zuciyan ƙanwar Yaya Sadeeq, wa ya taɓa mana ke autar Umma?" Sadiya jin muryan Khalid sai wasu hawayen suka kuka gangaro mata, ta juyo tana fuskantanshi, murya a dishe ta ce, "Yaya Khalid it's true wai Yaya Sadeeqna ya tashi?" "Yes! Absolutely true ma kuwa, Umma ta faɗa mini and Mama ma ta faɗa mini, i purposely come to follow Yaya Umar hospital, in ba dan ya tashi ba ai da ba inda zan je, yau aiki nayi kaman zan sheƙa, but what's wrong with you? Me ya saka kika wuni kuka?", Khalid ya ƙarishe maganan in a compassionate way. Sadiya numfashi ta sauƙe tare da jero ajiyan zuciya sannan ta ce, "But why I feel like he's not awake? Yaya Khalid ji nake kaman kawai wayo kuke mini, amma something is going wrong, I'll only feel okay when i heard from Yaya Sadeeq ko da kuwa ban ganshi ba, tunda nasan nobody will let me see him again." Murmushi Khalid ya mata tare da cewa, "Let's make a deal." Manyan kyawawan fararen idanuwanta da kuka suka maida ƙanana kuma rinannu ta ɗago su ta zubawa Khalid, alaman tana sauraranshi. "Ki ci tuwo kuma ki sha magani, and ni kuma ko da ban kaiki wajan Yaya Sadeeq ba, to zan haɗa ku kuyi magana ta video call in ya amince." "You promise?" "Yes i promise", Khalid ya amsa mata cikin tabbatarwa. Sadiya ɗan nitsuwa ta ɗan ji dai-dai, ba musu ta miƙe da hijabinta ta wuce toilet, wanko hannunta da bakinta tayi sannan ta dawo ta zauna, da bismilla ta fara cin tuwon, Khalid na mata hira wanda yake na zolaya ne, so yake ta ware dan bayajin daɗin ganinta haka, duk ɗin su suna son Sadiya, jinta suke kaman Ummansu ce ta haife ta, musamman shi da Sadiya ta maye masa gurbin ƙanwa, a maimakon ya kasance auta sai Umma ta maida Sadiya autarta, indai Umma ta ƙira shi autan maza to zolayanshi take ko tana cikin farinciki. Mama tana miƙa wa Khalid ta juya ta koma kitchen, tuwon Umar ta ɗauko, shi ma ta sako mishi sauran kunun da ya rage, ta ɗauko da ruwan leda, tana fitowa kitchen ɗin sai ga shi ya fito a ɗakinshi, da sauri ya ƙarisa ya amshi trayn da ke hannun Mama yana faɗin, "Mama kece fa kika haife mu ba mu muka haife ki ba, dan Allah ki daina mana irin wannan hidiman, in na fito ai zanje kitchen ɗin na ɗauko tuwon da kaina, ki raba mu da wutan Allah." Murmushi Mama tayi tare da cewa, "Allahu ya muku albarka, in sha Allah ba ku ba wuta albarkan uwa na tare da ku, kuma yardan iyaye na a tare da yardan Allah." "Duk da haka dai Mama ki daina", Umar ya faɗa yana zama a kujera tare da aje trayn a kan centre table. "In so kuke in daina daga kai har mai babban suna, to sai kuyi maza ku kawo mana surakunai, duk kun bai wa talatin baya amma ba mai maganan aure kun sa aiki kawai a gaba, ba ku aje mata ba balle batun yara to su wa za su ci kuɗin naku?" "Mama mun kusa ai in sha Allah." "Allah ya haɗa ku da shiryayyu nagari, ya kuma ba da zuri'a masu albarka." Da, "Amin", Umar ya amsa sannan yayi bismilla ya fara cin tuwon shi. Mama juyawa tayi ta wuce ɗakinta, ledan magungunan Sadiya ta ɗauko, sannan ta fito, ɗakin Sadiya ta wuce tana faɗin, "Bari na miƙa wa Sadiya magani, in ta ƙi sha za ka jiyo ƙira na, dan nasan yanzu haka kasa wa Khalid halinta take yi." Umar bai ce komai ba har Mama ta shige ɗakin, cigaba yayi da cin tuwon shi yana jujjuya wasu abubuwa a zuciyarshi, lamari ne a kan Sadeeq, abubuwa ne da suka shafi Sadeeq, sam ya gaza gane ta ina zai ɓulle a tunane-tunenshi, hakan yana daga cikin dalilin da ya sa dole ya kwana a asibiti tare da Sadeeq, kuma in son samu ne shi kaɗai, domin so yake ya titsiye Aminin nashi ya mishi bayani dalla-dalla, so yake ya faɗa mishi me ke damunshi ko me yake ɓoye mishi domin ya taya shi nemo mafita, lafiyan Sadeeq na nufin komai a gare shi. Mama da sallama ta shigo ɗakin, ta tarar da su Sadiya ta ɗan sake tana cin tuwo, Khalid kuma na mata hira, ƴar murmushi Mama tayi da hamdala ganin Sadiya na cin tuwo, sai da suka gaisa da Khalid gaisuwan da basu samu sun yi ɗazu ba, ta tambayeshi ya aiki, ya amsa sai godiya, ta sanya musu albarka tare da addu'an Allah ya taimaka, sannan ta ɗaura da cewa, "Tun da rowa take maka ba za ta ce ku ci tare ba, ƙyale mata hiran ka je ku ci da Umar ya fito yana palour." Khalid miƙewa yayi yana guntun dariya ya ce, "Ta mini tayi fa Mama, kawai na ce ta ci ta ƙoshi ne saboda amarya bai kamata a ganta da ƙashi ba, ta ci ta ƙoshi tayi ɓul-ɓul haka ya kamata." "Aikam dai faɗa mata autan maza, amarya dai da kumarinta ta fi kyan gani, in ta sake ta zama ƙashi da rai to kwa ba za ta ganu ba." Dariya Khalid ya kuma yi sannan ya dubi Sadiya ya ce, "don't forget our deal, so take ur pills", yana gama faɗin haka ya juya ya fice a ɗakin, kai tsaye wajan Umar ya nufa yana faɗin, "Yaya Umar congratulations ashe amininka ya farka." Umar murmushi yayi, ba tare da ya amsa tsokanar Khalid ɗin ba ya ce, "Zo mu ci tuwo." "Yanzu na gama cika ciki a gidan Umma, wallahi ba dan cewa su Umma suka yi Yaya Sadeeq ya farka ba, da yau ba inda zan je, Yaya Umar ka taimaka ka bar mini kula da Yaya Sadeeq kai ka koma aiki, wallahi ayyukan companynku za su hallaka wa su Umma ni." "Allah ya maka rahama." Marairaicewa Khalid yayi tare da cewa, "Please Yaya Umar a dubeni, yaro ne fa ni ayyukan sun yi mini yawa, am just 24." Umar bai ce mishi komai ba ya miƙa mishi kofin kunu, da sauri Khalid ya amsa dan duk ƙaunar kunun Mama suke, ita kuwa in ta yi to sai dai musamman wa Sadeeq, ko Sadiya idan bata da lafiya. Khalid na gama kwankwaɗe kunu, Umar ma ya aje cokalin da ya ci tuwo da shi, kamun ya motsa da niyan tattara kwanukan ya maida trayn kitchen, Khalid ya riga shi ya haɗa har da kofin da ya sha kunu ya ɗauki trayn ya kai kitchen, ya dawo ya samu Umar na danna wayarshi, cewa yayi, "Yaya Umar muna nan ai ba ku ɗaukan kwanuka." "Amma kuma aiki kam bar mana za ku yi ko?" "Eh to, wai saboda ku manya ne Yaya Umar, ai aiki na manya ne." "Yanzu dai menene? Ina son na wuce asibiti Abba su samu su dawo gida su huta, akwai wani matsala ne a companyn?" "Ba batun company ya kawo ni ba Yaya Umar, na zo mu je asibitin ne tare na dubi jikin Yaya Sadeeq." "Okay, then mu yi sallah kamun mu wuce", faɗin Umar yana miƙewa, ɗakin Sadiya ya nufa, Khalid kuma ya shige ɗakin Yaya Umar da sauri-sauri dan ya ɗauro alwala. Mama zama tayi a bakin gadon Sadiya tana faɗin, "Ga magungunanki nan, kuma kika tsaya mini shirme, na ƙira miki Yayanki Umar yana nan ba inda ya je, ina sane sarai da cewa ɗazu baki sha kunun kirki ba balle ki sha magani." Sadiya daman ta ƙoshi, cire hannunta tayi a cikin kwanon ta ɗauki ruwan ledan ta ɓula, sannan ta miƙa wa Mama hannu ta amshi maganin, cikin dauriya ta watsa magungunan a bakinta sannan ta bi da ruwa, ta haɗiye da ƙyar tana jin kaman za ta amar da tuwon da ta ci. Sai da ta ja mintuna sannan ta miƙe ta wuce toilet, hannunta tana wanke ta kuskure baki sannan ta kuma ɗauro alwala ta fito, kan darduman ta koma ta zauna, ajiyan zuciya take sauƙewa na kukan da ta sha, sai sannan Haidar ya faɗo mata a rai, rabonta da shi tun jiya, yau kwata-kwata ba su yi magana ba, wayan nata ma ta baro shi gidan Umma, sallaman Umar ne ya katse wa Sadiya tunanin da take yi, a take ta sha jinin jikinta ta ɗauka ko ya zo mata wani abun ne. Da sallama Umar ya shigo ɗakin, sannan cikin girmamawa ya ce, "Mama bari mu wuce, sai da safe." "To Umar, Allah ya kai ku lafiya ya kuma ƙara sauƙi, a gaida mini shi mu kwana lafiya." "Amin Mama." Har zai juya bayan ya amsa wa Mama, sai kuma ya kai kallonsa ga Sadiya ta yi ƙasa da kai bata ko yi tari ba balle gaisuwa, haɗe fiska yayi tare da cewa, "Ni kike so na gaishe ki?" Da sauri Sadiya ta girgiza kai, idanuwanta na ciko wa da ƙwalla ta ce, "Aa Yaya ka yi haƙuri, ina wuni, Ya mai jiki? Allah ƙara sauƙi." "Amin, Ya naki jikin?" "Alhamdulillah." "Allah sauwaƙa, kuma ki cigaba da kukan banza kada ki daina, za mu haɗu ne kin san sauran, rubbish girl kawai", yana faɗin haka ya juya ya fice dai-dai Khalid ya fito da alwalansa, a tare suka fice a palourn, Yaya Umar ne ya shiga mazaunin direba, Khalid ya zauna a mazaunin gefen direba, sannan Yaya Umar ya ja motan, sai da suka isa asibitin, sannan suka tsaya a masallacin asibitin suka yi salla, kamun suka wuce ciki. Sadiya tana jin fitan Umar, hawayen da ta maƙale suka gangaro, bata ce da Mama komai ba ta miƙe, ta tada sallah, Mama kuma ta fice a ɗakin, ɗakinta ta wuce ita ma ta yo alwalan ta tada sallah. Sadiya ko da ta idar da sallah, hannayenta ta ɗaga sama tare da koro addu'a ga mahaifinta da ƴar uwanta, sannan mahaifiyarta da su Umma da sauran al'umman Annabi SAW, ta yiwa Yaya Sadeeq addu'a sosai, sannan ta yiwa Al-Sad nata da ita kanta ta shafa, a sanyaye ta miƙe tare da naɗe darduman ta aje shi ma'ajinshi, tattara kwanukan da taci tuwo ta yi ta gyara wajan, sannan ta ɗau kwanukan ta fice da su ta kai kitchen, sai da ta ɗaurayewa Mama kwanukan sannan ta tsane hannunta da towel ta fito a kitchen ɗin, ɗakin Mama ta wuce, sallama ta yi bata shiga ciki ba, daga bakin ƙofan ta ce, "Na tafi wajan Umma." Mama da shafa addu'anta kenan bayan ta ida salla, juyowa tayi tana kallon yanayin Sadiyan ta ce, "To ki kula, Allah ƙara sauƙi, mu kwana lafiya, kin hutar da ita dan daman ta ce za ta shigo." "Amin, In

Chapter 9 of 32