Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Sadeeq." "To yanzu dai ba zan ce ga shi ba, domin Abbanku ya ce bai amince ba, sai dai da Mamanku ta mishi magana to ya ce sai ya ji ta bakin auta, muna fatan jin alkairi." "Ahh! In dai ta auta ce kar mu wani damu, auta ai ba za ta ƙi auren Yaya Sadeeq ba, yadda take son sa shi ma yake sonta, ai dama auren junansu shi ne daidai, Allah dai ya tabbatar da alkairi, Allah kuma ya bai wa Haidar haƙuri da danga." "Amin Sa'ad, wallahi ina tausayin Sadeeq sosai, amma shi ma Haidar ɗin tausayinshi nake, yanzu ba dan mutuwa ba ai da duk wannan mai sauƙi ne, sai a bai wa Sadeeq auta, shi kuma Haidar a ba shi Husna." "Allah sarki rayuwa, Allah dai ya jaddada rahama ga mamatanmu, Allah kuma ya tabbatar da alkairi." "Amin Ya Rabbi, ka yi ka gama ka wuce ko, bari na shiga ciki", Umma ta faɗa tana miƙewa, dan ta ɗan ji sanyi a ranta da magana da Sa'ad, saboda ko ba komai a maganganunshi akwai ƙarfafa guiwa da tabbacin in sha Allah Sadeeq zai samu auta, kuma hakan na nufin ba za ta rasa Sadeeq nata ba. "To Umma, a fito lafiya." Amsawa Umma ta yi ta wuce, har ta fara taka stairs ta tsaya tare da cewa, "Kar na ji wannar magana a bakin kowa daga ni sai kai sai kuma Allah, idan kuma ka labartawa wani Abbanku ya ji kai da shi ba ruwana", tana gama faɗa ta wuce abinta. Sa'ad murmushi yayi tare da tabbatar wa Umma ba wanda zai ji, amma a zuciyarshi mamaki ne da kuma farin ciki, domin Sadeeq da Sadiya sun dace matuƙa, "Perfect match couples kenan", ya faɗi yana murmushi, yana mai tuno wani anko da Yaya Sadeeq ya yi shi da Sadiya ranar bikin kammala makarantarta, kyau suka yi wane amarya da ango. ⭐️      SADIYA POV         *** Bayan ficewar Mama, Sadiya ta kammala sauran abubuwan, sannan ta wuce ta yiwa su Najla wanka ita ma ta yi wanka, Khausar ma wankar ta yi duk suka shirya, sannan suka fito suka zauna karyawa, Sadiya kasa haƙuri ta yi, domin da maganar a rai ta kwana kuma da shi ta tashi, tana sauƙe kofin kunu da ta kurɓa ta ce, "Aunty jiya muna magana bamu ƙarasa ba kuka fita, kamun ki dawo kuma na yi bacci." Khausar murmushi tayi tare da cewa, "Eh small Mum haka aka yi." "Aunty ina jin ki, wani irin soyayya kike nufi? Wani irin soyayya Yaya Sadeeq yake mini? Bayan irin son da muke yiwa juna." "Table manners small Mum, let's finish eating first", faɗin Khausar tana kai spoon bakinta. Sadiya bata kuma cewa komai ba ta yi shiru, har suka kammala karyawa, ta tattare kwanuka, ta gogewa su Najla jikinsu, ta wuce kitchen ta wanke abubuwan da suka ɓata sannan ta fito, su Najla suna wasa suna kallo a madaidaicin plasma da ke palourn, Khausar kuma na danna wayarta, a gefen Khausar ta zauna, sannan ta ce, "Aunty ina ji." Murmushi Khausar ta yi tare da cewa, "kin matsu ki ji ne small Mum?" Tura baki Sadiya tayi tare da jinjina kai cikin shagwaɓa. Ƴar dariya Khausar ta yi tare da cewa, "Rigimammiyar Yaya Sadeeq, zai je ya cigaba da fama ai, dama shi ya ɓata ki, shi ya fara sai ya ƙarisa." Murmushi Sadiya tayi kawai bata ce komai ba, tana dai sauraran Khausar ɗin. Khausar idanuwanta na a kan wayarta ta ce, "Small Mum, ba soyayyar da kike nufi ta Yaya da ƙanwa bane, soyayyar da Yaya Sadeeq yake miki, halattaciyar ƙauna yake miki, wadda Allah ya halitta kuma ya halarta tsakaninku, Yaya Sadeeq na matuƙar ƙaunarki tun baki san kanki ba, Yaya Sadeeq na ƙaunarki da gasken gaske, Yaya Sadeeq ya haƙura ne har ya shige miki gaba a kan batun Haidar, saboda ke kika so hakan kuma kin nuna mishi hakan ne farincikinki, wanda nake da tabbacin indai Allah ya nufa, to ko muradinki na ya zame waliyyinki ne, zai zame ya ba da aurenki muddin hakan ne zai faranta miki, saboda shi Yaya Sadeeq he took your happiness as his priority, he don't match everything related to you da komai, duk abinda ya shafe ki so daban ne a wajanshi, but believe me small Mum, Yaya Sadeeq love's you soo much, he loved you since the first day he saw you, i meant the day you were born, and he keeps on loving you till date, soyayya ce Yaya Sadeeq ke miki wacce ke da wuyar samu, whoever sacrifice his life for your happiness, he means world to you, na sani kina cewa Yaya Sadeeq shi ne duniyarki, but you have to take it this way, ki faɗi kalmar da shauƙin soyayyar da take nufin ta mallakar juna ne ta hanyar aure." "Pardon, Aunty ban fahimceki da kyau ba, am very sure kunnena abu daban suke jiye mini da wanda kike faɗa, and I don't know why", Sadiya ta faɗa cikin rashin fahimta. Murmushi Khausar ta yi tare da aje wayarta a gefe, cikin tabbatarwa da cire kokonta ta ce, "Son soyayya ta saurayi da budurwa, that turns the lovers to husband and wife, wannar soyayyar Yaya Sadeeq yake miki, aurenki yake son yi." Da wani irin expression Sadiya ke kallon Khausar, she's just staring at her without blinking her eyes, and without saying a word, kallon Khausar take deeply like she sees someone new not Khausar da ta sani. Wannan kallon da Sadiya ke yiwa Khausar, ya yi matuƙar kaɗa Khausar, domin tana iya hango shock ɗin da Sadiya ta shiga, tana hango wani abu daban bayan shock ɗin, but she don't believe it and she wish ba gaskiya bane abinda take hangowar. "Small Mum say something, kin yi shiru kina kallona", Khausar ta fara in a calm voice. Sadiya saurin lumshe idanuwanta ta yi, zuciyarta na wani irin bugawa da sauri-sauri, idan ta ce za ta buɗe baki ta yi magana, she can faint saboda yadda take ji, she can't believe what Khausar just said, neither she can't understand too, she know this most be joking, but why she looks so serious while talking? Kuma meyasa sai yanzu za ta mata wannar wasa? Wasa irin wadda bata taɓa mata ba, kai babu ma wanda ya taɓa mata irin wannan wasa sai friend's nata da Khalid, and she stopped them as soon as possible, meyasa yau kuma Khausar? Kuma a irin wannan lokaci da take daf da kasancewa mallakin nitsuwar ruhinta Aliyu Haidar Al-Sad. Khausar magana ta dinga yi tana ƙiran sunan Sadiya, amma ta yi nisa a duniyar tunani idanuwanta a kulle, hakan ya sa Khausar ta kai hannu ta girgiza ta tare da cewa, "Hey small Mum what's wrong? Are you okay? Ko maganar da nayi ne?" Sadiya har ra buɗe baki za ta yi magana,  sai kuma ta fasa ta girgiza wa Khausar kai kawai, ta miƙe ta wuce ɗakinta without turning back, hakan ya sanya Khausar ta bi ta da kallo tana jan numfashi tare da cewa,  "Ya Allah ka sa ba abinda zuciyata ke zargi bane tun farko, Ya Rabbi khairan." Khausar na zaune tana nata zancen zucin sai ga sallaman Mama ta shigo, amsawa tayi tana faɗin, "Sannunku da dawowa Mama." "Yauwa Khausar, fatan kun karya? Dan na ce da Sadiya kada ku tsaya jirana." "Eh Mama mun karya, ya su Umma da Abba?" "Yauwa, suna lafiya, ina ita Sadiyar?" "Yanzu ta shige ɗaki." "Lafiya dai ko? Waya ta je yi ko kuwa ƙullen ne ya tashi?" Murmushi Khausar tayi tare da cewa, "ko ɗaya, magana dai muka yi da ita sai ta tafi, ko amsa ma bata bani ba." "Maganar mai babban suna? Daman baku gama maganar jiya ba?" "Eh Mama, na dawo asibiti na samu ta yi bacci, sai yanzu muka yi maganar, amma dai bata ce mini komai ba ta tashi ta shige ɗaki." "Ai kuwa shiga ɗaki bai same ta ba, dan bata ci ta ƙulle ba, ta bari sai ta zama amaryar sannan ta kama ƙullen ɗaki." Murmushi Khausar tayi tare da cewa, "Da dai an barta ta huta, ina tunanin ta ji shock ne a kan maganar, ta shiga mamaki kamar yadda duk muka shiga." "Ba hutu Khausar, yanzu daga wajan Abbanku nake, ya dage a kan batunshi na ba zai bai wa mai babban suna aurenta ba, to dai daga ƙarshe da na saka naci na samu ya ce zai duba lamarin muddin Sadiya ta yarda da auren, kuma kinsan idan ya ce zai duba kamar dai ya amince ne, kuma bana jin ba za ta amince ba, amma fa ya rantse idan bata amince ba, ba zai ba wa mai babban suna aurenta ba." "Kamar dai yadda Yaya Sadeeq ma ya rantse ba zai aureta ba sai ta yarda, idan babu yardarta ba zai aureta ba." "Shi ai mai babban suna dan sonta da yake ne ya faɗa haka, kuma dan farincikinta, amma Abbanku so kawai yake ya hana mu ita, amma in sha Allah yanzu zan shiga na mata magana na tura ta, sai ta sanar da shi da bakinta ta yarda, shikkenan an wuce wajan sai batun mu sake zage dantse wajan shirye-shirye." "Haka ne Mama, Allah shige gaba ya tabbatar da alkairi." "Amin Ya Allahu", Mama ta amsa tare da miƙewa ta nufi ɗakin Sadiya, da sallama ta shiga ɗakin, can ƙuryar gado ta hango Sadiya a kwance cikin bargo ta yi rub da ciki, amma daga yadda ta tallafe kanta da hannayenta da kuma yadda take motsa ƙafafuwanta za ka tabbatar idanuwanta biyu, hakan ya sanya Mama ta ƙarasa bakin gadon tana faɗin, "Kin daina amsa sallama ne inna uwasu?" Sam-sam Sadiya bata ma ji motsin shigowar Mama ba, balle ta ji sallamarta, domin ta yi nisa a duniyar tunani, har yanzu zantukan Khausar ke amsakuwwa tare da maimaita kansu a kunnuwanta, ƙwaƙwalwarta da zuciyarta, tana kuma ƙoƙarin tariyo wani abu da Yaya Sadeeq ya mata mai kama da zancen Khausar, amma ta kasa gano wa. Mama zama ta yi a gefen Sadiya, tare da kai hannu ta taɓa ta tana faɗin, "Me kike tunawa haka har baki ji motsina ba balle sallama na?" Firgigit! Sadiya ta dawo hayyacinta tare da saurin janye hannayenta ta kife kanta tana sauƙe numfashi, dan ta ɗan razana. Mama gyaran murya tayi tare da cewa, "Menene ya faru?" Cikin rawar murya, Sadiya ta haɗe kalmomin bakinta tare da cewa, "Nothing, ba komai", murya a ciki-ciki Sadiya ta furta haka. Mama jinjina kai tayi tare da cewa, tashi ki zauna to za muyi magana. Ba musu Sadiya ta tashi ta zauna tare da sunkuyar da kanta ƙasa. Mama sai da ta ƙare wa Sadiya kallo sannan ta numfasa ta ce, "Sadiya na tabbata kun yi magana da Khausar, kin kuma ji abinda ta faɗa sannan na san kin fahimta kuma..." Da sauri Sadiya ta katse Mama ta hanyar girgiza kai tana faɗin, "Ban fahimta ba Mama, domin kunnuwana sun kasa jiye mini asalin abinda take faɗa, abu daban ta faɗan su kuma abu daban suka jiya mini." "Me kunnuwan naki suka jiye miki?" "Mama wai ni aunty Khausar ke cewa Yaya Sadeeq yake so, soyayya irin ta yin aure, irin dai soyayyar da Haidar yake mini", Sadiya ta ƙarishe maganar tare da ɗago kanta ta zuba wa Mama ido, cike da fatan ta ji saɓanin wannan daga bakin Mama. Murmushi Mama tayi tare da jinjina kai ta ce, "Kin yi mamaki ko? Tabbas muma mun yi mamaki fiye da wanda kika yi, amma kuma gaskiya Khausar ta faɗa miki, daidai kunnuwanki suka jiye miki, kuma yanzu nima zan jaddada miki hakan dan ki fahimta, Sadiya daga mu har ke mun kasa harbo jirgin mai babban suna, yana sonki ne tun ranar da ya ɗaura idanuwanshi a kanki, ya ɓoye ne saboda ki kammala karatu tukunna, sai kuma ga maganar Haidar, sai ya cigaba da ɓoyewa saboda farincikinki ya fi mishi komai, ciki har da rayuwarshi, wadda hakan har yayi sanadin ya kwanta wannan ciwo, da ikon Allah kuma ya farka sanadinki, hakan ya sa Yayanki Umar ya binciko har ya gano soyayyar da mai babban suna ke miki, da irin sadaukarwar da yake shirin miki, na haƙura ya rasa rayuwarsa saboda farincikinki, kuma...." Yanzunma Sadiya a kiɗima ta katse Mama da sauri, domin bata gane dogon bayanin Mama, tun tabbaci da ta samu na farko a kan abinda Khausar ta faɗa, shikkenan ta daina gane komai da Mama ke faɗa, murya a karye ta ce, "Amma Mama..... *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD @Uwarbatoorl96 ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/12/2025, 20:50] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 💔NAUYIN BAKI....👄💔        Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠     اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 35 _ 36 ⭐️ Murya a karye yana rawa, Sadiya ta ce, "Amma Mama ina yiwa Yaya Sadeeq kallon Yayana na uwa ɗaya uba ɗaya ne, Mama ba zan iya mishi wani kallo ba kuma bayan haka, Yaya Sadeeq ya haramta a gareni..." Mama saurin dakatar da Sadiya tayi ta hanyar cewa, "Sadiya dan kina mishi kallon Yayan da kuke kaman ciki ɗaya, ba yana nufin a zahiri haka bane ko kuwa har a wajan Allah haka bane, sannan ɗan adam ba zai haramta abinda Allah ya halatta ba, dan haka ki iya bakinki, mai babban suna yana son ki, kuma kema kina son shi kawai sai dai idan baki fahimta bane.." "Mama wallahi ni Haidar nake so, indai irin wannan soyayyar ne to bana son Yaya Sadeeq, ban taɓa mishi irin soyayyar ba kuma bazan taɓa ba da yardar Allah, soyayyar da nake mishi na kasancewarshi Yaya ne kawai a gareni cikin Umma ɗaya", Sadiya ta ƙarishe maganar idanuwanta na zub da ƙwallan da suka jima da taruwa a ciki. Mama kwantar da murya ta yi, tare da cewa, "Sadiya bana son ki kuma faɗar irin wannar magana a gaban kowa, ciki kuma har da ni da Yayanki Umar, Sadiya kina son mai babban suna kawai kin yi yarinya ne ba za ki iya fahimta ba." "Amma na fahimci ina son Haidar Mama, meyasa yaranta bata hana ni fahimtar haka ba? Mama bana son kowa sai Haidar, har abada ba zan yi wa Yaya Sadeeq irin wannan soyayyar ba." "Bana son damuwa Sadiya, bana son jan magana, kin san waye mai babban suna, kin san yadda ya zame miki a rayuwa, mutuwarshi za ki zaɓa saboda son zuciyarki? Ba ki ganin ƙoƙarinshi na yunƙurin sallama rayuwarshi saboda farincikinki ba? Ke ba za ki iya sadaukar mishi da taki zuciyar ba? Kin fi kowa sanin jarumta da dauriya irin ta mai babban suna, tunda har ya kwanta ciwo kuma irin haka, abinda bai taɓa yi ba a rayuwarshi tun sani na da shi, to lallai wannan ba ƙaramar soyayya yake miki ba." Cikin muryan kukan da ke son ƙwacewa Sadiya ta ce, "Mama, Yaya Sadeeq shi ne duniyata, abinda ya zame mini a rayuwa ya sa nake bashi matsayi fiye da Yaya Umar, nake jin shi tamkar uba a gare ni, kuma hakan ya sa ba zan taɓa yi mishi kallon wani soyayya bayan ta son Yaya da ƙanwa ciki guda ba, Mama ina son Yaya Sadeeq fiye da kai na, zan iya ba shi rayuwata idan aka ce sai na mutu zai rayu, amma ba zan iya bai wa irin wannar soyayya ƙofa a tsakaninmu ba, Haidar nake so Mama, shi kaɗai zan iya kallo a matsayin miji, da shi kawai zan iya zaman aure, Mama wallahi ba na jin komai makamancin wanda nake ji a kan Haidar game da Yaya Sadeeq, Mama dan Allah a bar wannar magana." Mama sake baki tayi tana kallon Sadiya zuciyarta na suya, ranta ke ƙoƙarin ɓacuwa amma ta yi ƙoƙarin dannewa matsayinta na uwa, dole ta yi rarrashi, domin tabbas Sadiya na son Haidar, amma yadda Sadeeq zai iya sadaukar mata da rayuwarshi, ya kamata ta iya sadaukar masa da zuciyarta da soyayyarta muddin ita ɗin ƴar halak ce. Miƙewa tsaye Mama tayi, murya a saisaice ba amo ta ce, "Ki tashi maza yanzu ki je wajan Abbanku yana jiranki zai fice, idan kin je zai tambayeki ne a kan mai babban suna, kamar yadda tun farko ban hango ko tsammaci matsala daga gare ki ba, ina fatan tabbatar haka har yanzu, domin na fahimceki kuma na miki uzurin duk abinda ke faruwa, saboda na taɓa kasancewa a irin halin da kike ciki, amma da nayi abinda ya kamata makamancin wanda nake so ki yi, ga shi ina hamdala da godiya ga Allah da ya bani ikon yin haka tun lokaci bai ƙure mini ba, kuma ina alfahari da hakan, dan haka kema ina miki fatan ki yi abinda ya kamata domin za ki yi alfahari zuwa gaba, ina tsammanin jin labari mai daɗi daga wajan Abbanku a kan kin ce masa kin yarda", iya haka Mama ta faɗa ta fice, duk da a sigar lallashi ta ƙarishe maganar,  sam-sam bata yi wa Sadiya tsawa ba, balle faɗa ko wani abun. Wani irin kuka ne ya kufcewa Sadiya tana jin Mama ta kulle ƙofa, cikin kuka ta ce, "Why? Meyasa? Meyasa haka Yaya Sadeeq? Meyasa za ka bijiro da abinda bazan taɓa iya aikata maka shi ba? Kullum fatana na yi abinda zan saka maka, na faranta maka ka yi alfahari da ni, amma meyasa da irin wannar magana za ka ɓullo? Ka fi kowa sanin wa zuciyar Sadiya ke so da ƙauna, ka fi kowa sanin Haidar shi ne farincikinki na, meyasa Yaya Sadeeq? Meyasa har za ka zaɓi ka cutu ka kusa mutuwa saboda ni? Bayan ina faɗa maka kai ne duniyata kamar wanda muka fito ciki ɗaya haka na ɗaukeka, idan ka mutu ya kakeso na yi da rayuwata? Wa zai dube ni ya rarrasheni ya bi mini kadu na? Wa zai tsaya mini a komai? Yaya Sadeeq kallon uba nake maka, ba zan iya sauya hakan ba kuma, irin wannar magana ya haramta tsakaninmu, ka yafe mini Yaya Sadeeq, ki yafe mini Mama, Umma ku yafe mini, yanzu Abba zan tunkara na sanar da shi bana son ɗan shi? Ya zan yi da rayuwata? Wayyo Allah na ni Halimatu Sadiya, Allah ga ni gare ka, ka fidda ni, Allah kada ka jarabceni da auren Yaya Sadeeq domin ba zan taɓa iya mishi kallon miji ba, zan cutu zai cutu kuma zan kwashi haƙƙinshi na kwashi zunubi. Mama na ficewa a ɗakin ta samu waje a palourn ta zauna, tare da faɗin, "Da yardar Allah dai mu ma za muyi surka, daga mai babban suna kuma sai Umar shi ma ya kawo mana ta shi matar." Khausar dariya tayi tare da cewa, "Amman kuwa aka bai wa small Mum matsayin surka to tabbas an yi da ita, an mata ƴan ubanci." "Ba wani ƴan ubanci fa, ni matar mai babban suna ai ko wace ce to surka take a wajena, kuma ɗiyata." "Gwanda-gwanda dai har da matsayin ɗiyar, idan ba haka ba ai har na fara tausayin small Mum, dan ma dai tana da Abba da Umma ga su Khalid, kuma nima dai partynta nake, Allah dai ya tabbatar mana da alkairi, Allah ya kuma kawo wa su uncle U ma mataye na gari." "Amin Ya Allahu", Mama ta amsa tana murmushi cike da fatan ganin sauran surakunan nasu. Khausar miƙewa tayi tare da cewa, "Bari na kawo muku abin karyawanku Mama." Amsawa Mama ta yi, Khausar ta wuce kitchen, it kuma ta miƙe ta nufi ɗakin Sadiya ganin har yanzu Sadiyar bata fito ba, da sallama ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, Sadiya da ke rungume da pillow tana shan kukanta da sauri ta haɗiye kukan tana jin sallaman Mama. Mama tana tsaye daga bakin ƙofar ta ce, "Amma dai kamar cewa nayi ki tashi ki je Abbanku na jiranki zai fita ko Sadiya?" Miƙewa tsaye Sadiya tayi ba tare da ta amsa wa Mama ba, toilet ta wuce ta wanko fiskarta, sannan ta fito kanta a ƙasa ta rarumi hijabinta ta nufo ƙofa. Mama tana tsaye tana kallon Sadiya har ta sanya hijabi, daga idanuwanta kuma ta gane kukan da ta sha, hakan ya sa ta ce, "koma ki kuma sanya wa idanuwanki tozali, kar ki kuskura Abbanku ya tsammaci tilasta miki na yi, domin ni ban tilasta miki ba, kawai dai Sadiya ina hango miki alkairi a auren mai babban suna ne, Sadiya ni na haifeki, duk wani mai sonki bayana zai biyo, ba zan so miki abinda zai cutar da ke ba." Wasu ƙwallan ne suka cikowa Sadiya a idanuwa, amma ta yi ƙoƙarin shanyesu, ta juya ta sanya kwalli kamar yadda Mama ta ce, ai kuwa ta sake yin kyau rass da ita abinta, a nitse ta ƙaraso bakin ƙofar har inda Mama ke tsaye kanta a ƙasa. Mama jawo Sadiya jikinta ta yi ta rungumeta, ta dinga bubbuga bayanta alamar rarrashi da ƙarfafa guiwa, ta ce, "Halimatu Sadiya yarinyar kirki ƴar albarka, in sha Allahu za ki ji daɗin wannan aure, za kuma ki yi alfahari da hakan, watarana ko da kuwa bama raye za ki bi mu da addu'a tare da gode mana, Allahu ya miki albarka autata, Allah ya dubi rayuwarki da ta zuri'arki, duk wani mugun abun na ji ko na gani Allahu ya kareku da shi." Sadiya lafewa ta yi a jikin Mama, amma ta kasa amsa wa, saboda zuciyarta da ta ɗanyace kuma ta raunata, ji take idan ta buɗe baki to kukan ne za ta kuma yi, hakan ya sa sai ajiyar zuciya kawai take jerawa. Mama shafa kanta tayi tare da janyeta a jikinta, tana murmushi ta ce, "Allahumma ya miki albarka Sadiya, ki je ko, kuma ki tabbata kin sanar da Abbanku kin yarda, kada ki bani kunya Sadiya", Mama ta ƙarishe faɗa tare da matsawa a ƙofar ta bai wa Sadiya hanya ta wuce, ita dai jinjina kai kawai ta yi ta fice kai a ƙasa, bata ko kalli cikin palourn ba balle ta yi wa Khausar ko sauran yaran magana. Mama sai da ta tabbatar Sadiya ta fice a palourn, sannan ta sauƙe gauron numfashi tare da ficewa ta ja ƙofar ɗakin, palourn ta ƙarasa ta zauna, wanke hannu ta yi da ruwan wanke hannu sannan ta soma cin ɗumamen tare da cewa, "Allah yayi albarka Khausar." "Amin Mama", Khausar ta amsa tana murmushi, cike da ƙaunar Mama, sai ta rasa tsakanin su Umma da Mama wa ya fi wani kara, sosai Mama take da kara da kuma kirki, kamar yadda Sadiya ke faɗin ta fi ƙaunar Sadeeq a kan Umar, to haka idan Mama na tare da Sadeeq da Umar, za ka ga tsantsar ƙaunar Mama ga Sadeeq, za ka ɗauka ma shi ne asalin ɗan ta. Daga haka Mama ta cigaba da karyawanta, suna hira sama-sama da Khausar, su Najla  da Nayla kuma an nitsu an mayar da hankali ga cartoons. Sadiya a sanyaye take tafiya kanta a ƙasa, idanuwanta na kawo ƙwalla amma tana mayar da su dan dole, a haka har ta ƙarisa ƙofar gidan Abba, wadda take jin yau nauyin shigarsa take, sosai take kunyar Abba da Umma, yanzu sai ta dubi idon Abba ta ce mishi bata son ɗan shi? Ko kuwa Umma za ta kalla kuma bayan ta nuna bata son ɗan su? Sun yi halarci gare su musamman wa ita da Yaya Umar, idan ta yi haka bata kyauta ba, amma kuma Haidar fa? Shi ta kyauta mishi? Yana sonta yana ƙaunarta ita shaida ce, idan ya rasa ta shi kuma bata san wanne hali zai shiga ba, domin ba ta ta kanta ta shi take yi, dan ta sani a rubuce yake, wannan wajibi ne za ta yi matuƙar cutuwa, kuma ba za ta iya damƙa kanta da soyayyarta ga wanin Haidar ba, ko da kuwa shi Yaya Sadeeq ɗin ne, tukunna ma idan ta aikata haka me Haidar zai ɗauketa? Mayaudariya? Maƙaryaciya? Macuciya? Ko kuma maciyiyar amana? Ya za a yi ta jure irin waɗannan kalamai ko sunaye daga Haidar, idan Haidar ya mata wannan kallon ba za ta taɓa yafe wa wanda ya zama sila ba, a ko da yaushe Haidar na jaddada mata irin soyayyar da yake mata da irin kishinta da yake yi, amma yake faɗa mata ya yarda da ita, daga gare ta baya taɓa tunanin samun wani damuwa ko abinda bai kamata ba, a yanzu kuma yarda da maganar Yaya Sadeeq, tamkar ta sa almakashi ne ta kekketa yardar da ke

Chapter 22 of 32