Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
batun barasar ƙauna? Aiki kake ba wasa yau kana can gobe kana can, yanzu kuma ka ce aure, wa zai yi aikin? Wa kuma zai soshale ya tatile da barasar ƙauna?" Umar ya ƙarishe faɗa yana dariya, idanuwanshi a kan system nashi. "Umar daga kai sai ɗan iska wallahi, in ba iskanci ba me na wannar magana? Kana abu kana tsare gida kamar boss a gaske, amma ka ƙware a maganar banza." Umar na ƴar dariya, ya ce, "Na ƙware a maganar banza kamar yadda ka aje kunya a gefe za ka auri wacce ka kusa haifa ba, Allah ya sa ma dai kar ka ɓalle wa Umma autarta, domin wanna shirmenta ba zai barta ta yi gwaɓi ba, kai kuma a direnka kake wane doki." "Ɗan rainin hankali." "Ƴan rainin hankali dai ni da kai duka, ai ko ƙafarka a nan ma ban kamo ba, kai fa a komai kana gaba da ni bro, wai ba ma za ka tambaya ya muka yi da su Abba ba?" "Dama na aike ka ne?" Sadeeq ya faɗa a taƙaice. "Ni na aiki kaina, kuma komai daidai, Mama ta baka Abba ya lamunce, sai ka shirya amgwancewa ka baza hajarka son ranka." "Ka yi abinda ke gabanka ka bar wa ƴan iska maganar banzarsu." "Ah! ina sam-sam ba zan bari ba, akan barasar ƙauna da ni da kai da kowa ma ƴan iskan ne, dan haka kabarni nayi lokaci ne, kuna fara aje mana yara ai dole na kame bakina na sanya masa code kamar yadda ka saka wa box ɗin ka", faɗin Umar yana dariyar neman magana. Ƙwafa kawai Sadeeq yayi tare da yin shiru, daga haka kuma Umar ke maganar Sadeeq na amsa mishi jefi-jefi, a haka suke hirar har Umar ya kammala ya kwanta, Sadeeq ma ba jimawa bacci yayi gaba da shi, wajajen ƙarfe biyu ya farka, nafila yayi tare da addu'oi, sannan ya koma ya kwanta, ko da asuba ta yi, Umar ne ya fara tashuwa dan har sun kusa makara, sai da ya ɗauro alwala sannan ya tashi Sadeeq, shi ma yayi alwalar, suka bi jam'i a nan ɗaki, bayan sun idar sun shafa addu'a, Sadeeq ya koma ya kwanta ba jimawa bacci yayi gaba da shi, Umar lokaci ya duba, ganin ƙarfe biyar da mintuna arba'in ne, sai ya koma ya kwanta zuwa ko bakwai ne kamun nan ya taɓa bacci. Ƙarfe bakwai da rabi Sadeeq ya farka, sai da ya wanko bakinshi ya fito sannan ya tashi Umar, wanda lokaci ɗaya da tashin da shigowan ƙira wayar Umar, hakan ya sa Umar ya tashi, ya ɗau ƙiran, a gajarce ya amsa wa wanda ya ƙira bayanin da yake mishi sannan ya kashe ƙiran ya wuce toilet. Zuwa takwas likita ya shigo, duba Sadeeq yayi, Sadeeq na ƙoƙarin yin magana a kan sallama, sai likitan ya ce Umar ya bi shi office, yana ficewa Umar ya rufa mishi baya, ko da suka je office ɗin, bayani likitan ya yiwa Umar tare da kafa mishi abubuwan da za a kiyaye game da Sadeeq, da kuma shi ma Sadeeq ɗin ya kiyaye, sai da suka gama tattaunawa sannan ya ba su sallaman. Umar na komawa ɗaki wajan Sadeeq ya samu Khalid ya zo da abun karyawa, amsa gaisuwar Khalid ɗin ya yi sanna ya ce, "An bamu sallama ma, mu tattara mu koma gida, idan kuma zai karya a nan tukunna sai ya karya mu wuce." "Mu je gidan, ma karya a can", faɗin Sadeeq yana tashuwa zaune daga kwancen da yake. Umar da Khalid ne suka haɗa ƴan tarkacen su da babu yawa, Khalid ya tattare ya kai mota, sannan suka fice a ɗakin suka wuce wajan mota, Khalid na mazaunin direba, Umar na seat da ke gefenshi, Sadeeq kuma yana baya ya jingija da jikin kujera, suna ficewa a cikin asibitin, Sadeeq ya sa Khalid ya sauƙe mishi glass na ƙofar gefenshi, fresh air yake shaƙa yana jin nitsuwa na sauƙar mishi, da ƙwarin guiwar tinkarar abinda Umar ya ɓallo mishi, domin har ga Allah masifar binckken Umar ne ya ɓallo mishi wannan ruwa, kuma dole ya tare ruwan. Khalid ya ce, "Amma dai likitocin nan sun kyauta da sallamar safe." Umar ya ce, "Ya matsa musu ya takura musu ya suka iya, sallamarshi ya zame musu dole." Ƴar dariya Khalid yayi, shi dai Sadeeq bai tanka su ba, Khalid ya koma batun company, suka cigaba da tattaunawa da Umar, har suka isa gida. ⭐️ RAYFIELD      SADIYA POV         *** Da sassafe Mama ta sa Sadiya a gaba suka kama aikace-aikace, kamun bakwai sun gama komai, ta haɗa wanda za a kai asibiti, da kanta ta ɗauka ta fice a gidan bata bi ta kan Sadiya, da ke cewa ta bari za ta ɗauka mata ba.   Knocking na ƙaramin ƙofar gidan Mama ta yi, mai gadi ya buɗe mata suka gaisa cikin girmamawa, ya buƙaci ta ba shi basket ɗin ya shigar mata, amma ta ce ta yafe ta wuce ciki. Da sallama Mama ta shigo palourn, Umma ta amsa tana murmushi tare da cewa, "wai ke ce da sassafen nan Maman Sadeeq, da kin huta abinki ai Khalid ɗin zai bi ya amsa ka mun ya wuce." Zama Mama tayi tare da aje basket na hannunta tana cewa, "Umman yara ai fitowa da sassafe ya zama dole, mu da muke nema dole mu buga sammako, fatan dai Abbansu yana nan?" "Yana nan Maman Sadeeq", Umma ta faɗa tana ƴar dariya. "Yauwa maza a taimaka a mini magana da shi, na zaune bai ga gari ba, ai kuwa nima banga ta zama haka ba, babana na son autar Abba." "Sadeeq ne ko rigima, hmmn, wannan baba naki da nemar magana yake." "haka kuma za a yi haƙuri da shi a yi maganar ba, a taimake ni a mini magana da uban amarya." Umma na dariya ta miƙe ta haura sama, ba jimawa sai ga su sun sauƙo tare da Abba, ya ƙaraso ya zauna, cikin girma da mutunta juna Abba da Mama suka gaisa, sannan Abba ya ce, "Ya shirye-shirye kuma?" "Alhamdulillah Abban yara,shirye-shirye fa sai godiya, balle yanzu da abin ke shirin sauya sheƙa, ai yanzu za mu yi shirin gaske." Abba cikin rashin fahimtar maganar Mama da yake bai san ta san da maganar ba, ya ɗauka su kawai Umar ya sanarwa, shiyasa ma ya ce da Umma kar ya ji kada ya gani, yana murmusawa ya ce, "Allah ya shige mana gaba." "Amin Abban yara." Ɗan jima kaɗan palourn yayi shiru, sai can Mama ta ce, "Abban yara na zo ne a kan batun Babana da Sadiya." Abba da sauri ya juya suka haɗa ido da Umma, alamar yaushe ta sanar da maganar, Umma kuma tayi saurin girgiza kai, hakan ya sanya Abba ya nuna kamar bai gano nufin Mama ba, ya ce, "Me kuma ya faru Maman Sadeeq?" Murmusawa Mama ta yi, sannan ta ce, "Maganar dai da Umar ya same ka da ita, a kan mai babban suna yana son autarka, Umar ya faɗa mini yadda kuka yi, kuma haka ne Abban yara, gaskiya ne ba su kyauta ba, domin ba a nema cikin nema, amma kuma dan Allah a duba lamarin da idon fahimta, gida bai ƙoshi ba ai ba za a kai wa dawa ba, babana yayi laifi amma a yafe shi ya tuba mun tuba duka, a taimaka a yi wa mutanen nan bayani ta fahimta, kuma indai ta ni ce wallahi na bai wa mai babban suna Sadiya duniya da lahira, halak malak Allah ya tabbatar musu da alkairi da zuri'a masu albarka." Umma murmushi ta yi, domin ta san tunda Mama ta zo magana ya ƙare, ko Abba bai saurareta ba to zai saurari Mama. Abba numfasawa yayi tare da gyara zama ya ce, "To..... *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD @UwarBatoorl96 ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 💔NAUYIN BAKI....👄💔        Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠     اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 33 _ 34 ⭐️ Abba numfasawa yayi tare da gyara zama ya ce, "To Maman Abubakar, ban ƙi ta bakinki ba, amma dai duk a zantukan naku ke da Umar, ban fahimci dalili guda ɗaya da zai sa Abubakar ya ta da wannar magana a yanzu ba, hankalinshi ne ya ba da ajiya? Ko kuwa iliminshi ya bayar aro? Ko dai tunaninshi ya haɗa da magani ya kurɓe?" Mama murmushi ta yi, don ta san dole sai ta sha fama da Abba dama, cikin kamalalliyar muryarta ta ce, "Abban yara a dai yi mana afuwa, amma ko guda ɗaya mai babban suna bai yi ba, a cikin ukun da ka lissafa, ƙauna ce da soyayya ta autarka suka ƙure shi, kuma a wannan fasali inma akwai mai laifi to ni ce, ina gaba a laifin, domin matsayina na uwa ga babana da autarka, ya kamata a ce na hango wannar soyayya, amma kuma ban mai da hankali ba har dai aka kawo yanzu, dan Allah a dubi ƙoƙon baranmu." "Wannan lamari yana ɗaure mini kai yana bani mamaki wallahi, Abubakar na son auta, yaushe ma ya fara son nata? Tun kamun a tsayar da maganarta da Aliyu ne ko bayan an tsayar? Idan kamun a tsayar ne meyasa bai yi magana ba sai yanzu? Har kuma ya shige wa shi Aliyu gaba a maganar, sannan idan bayan an tsayar da maganarta da Aliyu ne, meyasa zai fara son ta bayan ya san akwai sadakin wani a kanta?", Abba ya ƙarishe maganar a kausashe, saboda ran shi ya fara ɓaci. "A yi haƙuri Abban yara, amma tun Sadiya bata san kanta ba mai babban suna yake son ta, kawai ya jinkirta ne da niyar ta kammala karatu kamun ya mata magana, sai kuma aka samu akasi maganar Aliyu ta shigo, shi ne har aka samu akasi haka, amma amana afuwa mu daidaita komai mu gyara." "Jin cewa Abubakar ya so auta ne tun ba yanzu ba, ya fi komai ɓata mini rai, domin ya fi muni a kan a ce ya so ta ne daga baya, duk da son ta bayan ya san akwai sadakin wani a kanta hakan ma laifi ne, amma gwanda haka, dan zan iya mishi uzuri tunda soyayya bata shawara take shigewa mutum zuciya, amma kuma wai yana dakon soyayyarta tun ba yau ba, dan sakarci da sokanci har ya shige wa wani gaba a kan batun aurenta, to ya fi komai ɓacin rai da muni, kuma wannan ba uzuri ne da zan karɓe shi ba balle na duba, ai Aliyu da ya shigo rayuwartata ya burgeni matuƙa, domin dama masu iya magana sun ce, idan ba ka yi ka bani waje, tunda shi bai da hankali da lissafi to wanda ya fi shi lissafi ya yi gaba, idan ba rashin lissafin ba to me amfaninmu na manya? Idan bai sanar mata ba saboda baya son karatunta ya katse, ai sai ya sanar mana mu iyayensu dan mu san da maganar, domin da ya sanar mana da lokacin da wasu suka zo da maganarta to za mu ce an mata miji, amma sai daga baya bayan banza, da shi aka yi komai, yana ji yana gani har shawara da shi an yi kamun aka yanke komai, aka tsayar da ranar biki, kuma sannan yanzu yau biki saura kwana biyar kuma a ce ga wannar magana, mahaukata ya ɗaukemu ko yara ƙanana? Me ya hana shi ci gaba da riƙe soyayyar a cikinshi yadda yayi niya? Ba duk dan yana so ya sa mutuncinmu ya zube a idon mutane ba? To ba mai ba wa Abubakar auren auta, ya ci gaba da riƙe soyayyar a cikinshi, ya mai da maganar ya haɗiye abarshi, mu ma za mu yi kamar bamu ji ba, a je a haka, Allah ya ba su zaman lafiya ita da Aliyu, ai shi ya zaɓi haka tun da ya shige gaba aka yi komai, wallahi wannan abin ya fi komai ƙona mini rai, Abubakar kam me ya ɗauke ni ne? Ƙaramin mutum yake son mai da ni?", a matuƙar hasale Abba ya ƙarishe maganar, dan zuwa sannan ran shi ya ɓaci sosai, domin ji yake wannan raini ne Sadeeq ya mishi, ya raina shi, idan ba raini ba me zai sa sai yanzu zai ta da maganar? Mama a tausashe da muryar magiya ta ce, "Shiyasa tun farko muka nemi tuba kamun muka yi magana, domin tabbas mai babban suna bai kyauta ba, amma yana da dalili, kuma dalilinshi mai matuƙar muhimmanci ne, daliline wanda zai sa a amince mishi da auren Sadiya, domin ya cancanta, dalilinshi zai nuna gwargwadon yadda zai riƙe ta da amana idan ya aureta." "Dalilin Abubakar na banza da wofi, raini ne kawai yake damun Abubakar ba komai ba, amma ba komai za mu haɗu ne, sai na saɓawa Abubakar fiye da tunani, domin bai isa ya mayar da ni ƙaramin mutum mai magana biyu ba." "Abban yara dalilin mai babban suna yana kan daidai, duk ya yi wannan kuskuren ne saboda kiyaye farincikin auta, saboda yana son farincikinta fiye da nashi, saboda yana ƙaunarta sosai, ya zaɓi ta kasance a farinciki ko da kuwa zai rasa rayuwarsa ce..." Abba katse zancen Mama ya yi ta hanyar cewa, "Indai da gaske haka yake nufi to ya rasa rayuwarsa mana ya barta da Aliyun, ta nuna Aliyu take so har kuma shi ya shige mata gaba, yanzu kuma me zai sa ya ta da wannar magana muddin yana son farincikin nata da gaske?" "Ba mai babban suna bane ya ta da maganar, Umar ne ya bincika har ya gano haka, domin kasancewar babana a wannan hali yana damunshi matuƙa, shiyasa har ya bincika kuma Allah ya amince ya gano sanadin damuwar, muma kuma sai mu bai wa zuciyarmu haƙuri, kar mu duba komai kawai mu bai wa yaranmu abinda suke so, saboda Allah, domin sosai babana ya cancanci auren Sadiya fiye da Haidar, don cancantar Umar ya gano har ya sanar da mu maganar." "A ba su abinda suke so? Kuna tunanin auta tana son Abubakar ne? Ko za ta haƙura da Aliyu ta ɗau Abubakar ne? Ina da yaƙini a kan cewa auta Aliyu take so." "Ko shi mai babban suna sai da suka kai ruwa rana da Umar, sannan ya amince da batun auren har ya faɗawa Umar ɗin gaskiyar komai, dan haka Sadiya za ta iya cewa bata so da farko, amma ina da tabbacin aka mata bayani shikkenan za ta amince, domin duk wanda a rayuwa zai tauye kan shi domin kai ka wadata, to wannan babban masoyinka ne, da in ka rasa shi, kai da kanka za ka yi kuka da kanka, ba na yiwa Sadiya fatan yin da-na-sani a ɓangaren zaɓar miji, tunda aure rayuwa ce ta har mutuwa ake fata, ba zan ce Haidar baya son ta ba domin shi ma yana iya ƙoƙarinshi, amma kuma na fi hango mata alkairi a zama da mai babban suna, duk ma bayan haka Sadiyar ma tana son mai babban suna kawai duk sun kasa furta wa juna ne." "Shikkenan, duk da ba ina nufin na yarda zan bai wa Abubakar auren auta bane, amma dai bari mu ji ta bakinta tunda kuna tunanin tana son shi ita ma, idan har ta yarda da aurenshi da kanta, to zan yi tunani akan mai ya kamata na yi, domin duk da haka ba yana nufin zan amince bane na aurawa Abubakar ita, amma kuma idan ta ce bata yarda da aurenshi ba, wallahi ko me zai samu Abubakar ba zan aura mishi auta ba." Da sauri Umma da kanta ke gefe tana sauraransu, ta juyo jin Abba ya rantse, kallon Mama ta yi suka haɗa ido, sannan ta mai da kallonta ga Abba, shi ma haɗa idon suka yi, kuma ta ga alamar tabbaci a ƙwayar idanuwanshi, wanda ya ɗaura mata da tabbacin furci, ya ce, "Hakan nake nufi, kuma ba zan yi kaffara ba in sha Allah, don haka idan Maman Abubakar kin koma gida sai ki turo mini auta, kuma ban lamunta ba ki tilsta mata, dan na fahimci lamarin naku da son kai ya zo, domin ni ban ga wata cancanta da aka fi Aliyu ba, in sha Allah aka yi auren to shi ma da amana zai riƙe ta, kuma za ta fi samun farinciki ma a wajanshi saboda yana sonta tana son shi." Murmushi Mama ta yiwa Umma da Abba, sannan ta ce, "Ka gama magana Abban yara, tunda ka ce na turo auta ai dama ce ka bamu, kuma mun gode, in sha Allahu kuma auta za ta amince da babana, domin ni sai yanzu ma nake hasaso irin soyyyar da suke gwadawa juna ba tare da saninsu ba." "Koma dai menene, muddin ta nuna bata yarda ba, to kar wanda ya kuma mini wannar magana, indai bata amince ba to binne maganar nan za a yi kamar ba a yi ta ba, don baƙi za muyi, bai kamata su zo biki kuma ƙananun maganganu na tashi ba, in batu ya kai ga gidan surakunanta kuma wani damuwar aka saya mata tun kamun ta je", Abba ya faɗa yana miƙewa tare da nufar upstairs, yana mai jaddadawa Mama ta turo mishi Sadiya. Abba na wucewa Umma ta sauƙe gauron numfashi, tare da cewa, "Allah ya kyauta." "Amin Umman yara, kum Allah ya tabbatar da alkairi, domin muddin autarku ta auri babana to ba ku da wani kokonto, da amana zai riƙe muku ita da soyayya." "Hmn! Magana ta gaskiya Sadeeq bai kyauta ba Maman Sadeeq, duk da ina son batun aurensu da auta, amma nima ina jin haushin abinda ya yi kamaar dai yadda abin ke ƙona ran Abbansu, duk me amfaninmu da idan bai sanar mata ba mu ba zai sanar mana ba? Sannan yanzu ma sai Umar ke bincikowa, da Umar bai binciko ba kenan idan abu ya zo da ƙarar kwana sai ya mutu haka? Kuma ko da Umar ya binciko har yana da ƙwarin idon da zai musa har sai an kai ruwa rana da shi kamun ya amince? Wannan wane irin hali ne? Me ke damun Sadeeq?" Numfasawa Mama tayi tare da cewa, "Tabbas mai babban suna bai kyauta ba, kuma musamman wa ni, sam-sam bai kyauta mini ba ban zaci haka daga gare shi ba, domin wallahi ni mai ba shi auren Sadiya tun tana tsumman goyo ne, amma kuma ba komi na mishi uzuri, son da yake mata da son farincikinta da tunanin makomar karatunta shi ya ja komai, Allah ya shige mana gaba kawai ya tabbatar da alkairi nan dan wasu watanni mu fara ganin jikoki." Murmusawa Umma ta yi tare da cewa, "To Amin Ya Rabbi, Allah ya musu albarka, ƴan baya ma Allah ya kawo musu abokanan zama na gari." "Amin Ya Hayyu Ya Qayyum Umman yara, bari na wuce na samu na aiko autar taki, a samu a yi komai da zafi-zafi a wuce wajan", faɗin Mama da ta miƙe tsaye. "To Maman Sadeeq, a isa lafiya, sannu da ƙoƙari, ki ja mini kunnen jikokinki fitinannun nan." "Ƙawayena nitsatstsu dai ko", Mama ta faɗa tana dariya. "Tunda dai kin ce musu nitsatstsu shikkenan, amma ba wai dan a nitsen suke ba, yanzu dai ƙyale ta maganar yara masu kama da masu jajayen kunnuwan nan, ki ƙaraso mu karya, sai ki wucen." "A a Umman yara, ai ban ci ta saka komai a cikina ba, sai na je na turo Sadiya, ta zo an yi magana an wuce wajan, sai na tabbatar ta dawo ta shaida mini sun gama magana da Abbansu sannan zan karya yau." Ƴar murmushi Umma tayi tare da cewa, "Abin na yi ne kenan." "Saka wando ta ka ba", Mama ta faɗa tana dariya. "To Allah shige mana gaba ya tabbatar da alkairi." Da, "Amin Ya Allahu", Mama ta amsa tana murmushi. A haka Umma da Mama suka yi sallama suna raha, Mama ta fice ta wuce gida.   Umma komawata yi kan kujera ta zauna bayan fitar Mama, a sanyaye ta ce, "Ya Rabbi ka tabbatar mana da alkairin da ke cikin wannan lamari, idan Sadeeq alkairi ne ga auta ka amince wa aurensu, idan kuma ba alkairi tsakaninsu ka bai wa zuƙata haƙuri Ya Rabbi, ka tausashi zuciyar Sadeeq ka ba shi lafiya mai ɗaurewa, ka ara mishi juriya da jarumta, Ya Rabbi kada haka ya zame sanadin da zan rasa ɗa na, Allah ka sa muna da rabon ganin jinin Sadeeq, kar ya koma gare ka bamu ga jininshi ba, Ya Allahu", Umma ta ƙarishe addu'an, cikin matuƙar rauni da kuma tausayi irin na uwa, idanuwanta fal ƙwalla wanda suka gangaro tana shafa addu'ar, ta sani mutuwa dole ce kuma ko wani bawa lokacinshi yake jira, amm ba ta fatan ganin gawar ko da mutum ɗaya ne a cikin yaranta, tana addu'a dukkansu su sanyata a makwancinta na gaskiya, domin jin Sadeeq na ƙoƙarin rasa ran shi a kan auta ya fi komai ɗaga mata hankali, ba dan wannan ba da tana goyon bayan Abba na a hana Sadeeq auta, amma kuma batun rasa rai ya sa tana tausayin Sadeeq tare da yi mishi fatan samun Sadiya.   Jiki a mace Umma ta miƙe da niyar haurawa sama, sai Khalid da da Sa'ad suka fito, sannu da aiki suka yiwa Umma, domin sun gaisa tun da sassafe bayan dawowarsu masallaci.   Amsa sannun Umma ta yi, sannan ta ce, "Khalid ga abin karyawan mutanen asibiti Mamanku ta kawo ka haɗa ka wuce musu da shi duka, kai kuma Sa'ad zo ka karya kamun ka fita wajan aikin." Khalid ya san nufin Umma shi ya je su karya a can asibitin, shiyasa bai wani ja magana ba ya ɗauka duka ya fice tare da yiwa Sa'ad ya dawo lafiya. Umma da Sa'ad suka wuce dinning, Sa'ad yana zama ba tare da ya taɓa komai ba a wajan, idanuwanshi a kan fiskar Umma ya ce, "Umma me ya faru? Me ya same ki naga idanuwanki wani iri? Ko ciwo suke miki? Ko abu ne ya faɗa?" Umma ƙaƙalo murmushi ta yi dan kawar da yanayin fiskarta, ta ce, "Ba komai Sa'ad, ka yi maza ka tafi ka ga takwas ta yi." Sa'ad bai ja maganar ba, tunda dama ba musu suke da iyayensu ba, kuma wataƙila tunda ta ce ba komai duk da ya ga alamar akwai, to ba zai shige ita da Abba bane, wanda ba ruwansu da haka, na su kawai addu'a da fatan alkairi ga iyayen nasu ne. Umma tana zaune har Sa'ad ya zuba abin karyawarshi ya soma ci, har ta miƙe tsaye sai kuma ta koma ta zauna, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kallon Sa'ad, cikin yanayi da ke nuna tausayin uwa da kuma soyayyarta ta ce, "Sa'ad, damuwar Sadeeq ke damuna." Ɗagowa Sa'ad yayi, cikin kulawa ga mahaifiyarshi ya ce, "Me ke damun Yaya Sadeeq kuma Umma? Ina ce jikinshi da sauƙi? Jiya da muka wuni wajanshi fa har fita harabar asibitin ya yi, menene kuma ya faru?" "Maƙasudin ciwon nashi nake magana a kai Sa'ad, abinda ya sa shi ciwon nake nufi ba wai matakin samun sauƙinshi ba." "Menene Umma? Kun gano abinda ke damun Yaya Sadeeq ɗin kenan? Ni ai na jima da fahimtar abu na damunshi wallahi, duk miskilancinshi ya ƙaru a kwanakin, kai murmushi ma ta yaƙe yake yi, menene ke damunshi dan Allah Umma?", Sa'ad ya faɗa cikin zaƙuwa. "Sadeeq son auta yake yi, tun ba yau ba tun tana yarinya, ɓoyewa kawai ya yi, kuma yanzu batun aurenta ne nake tunanin ya haddasa mishi wannar ciwo." "What?, Umma da gaske ko da wasa? Yaya Sadeeq na son auta, autarku Sadiya? Tun ba yau ba, amma to meyasa ya ɓoye?", murya a ɗan sama kuma cike da mamaki Sa'ad yayi duk wannar magana. Umma ta ce, "Son da yake mata ne kawai ya sa ya ɓoye, yanzu ma Umar ne ya gano in ba haka ba da ba wanda zai sani." "No wonder, haba mana, shiyasa ashe duk ya zama so silent tun da aka tsayar da ranar bikin, domin ina kule da Yaya Sadeeq tun daga lokacin ne ya fara sauyawa, ashe soyayyar auta ce, kuma har yake ƙoƙarin mutuwa saboda haka, Allah mun gode maka da ka taƙaita mana wannar jarabawa, Allah ya yiwa Yaya Umar albarka da ya gano wannar matsala." "Amin Sa'ad", Umma ta amsa cike da alfahari da Umar. "Amma yanzu Umma ya ake ciki? Fatan dai an mayar da auren kan Yaya

Chapter 21 of 32