ita ma duk abinda ta saka to incorrect, ya ƙi buɗuwa, hakan ya sanya Khausar ta ce, "Uncle U, mu je mu huta, zuwa anjima sai mu buɗe, may be kamun anjima mun tuna correct code ɗin.
Ba musu Umar ya miƙe, ita ma ta aje box ɗin suka fice tare da ja mishi ƙofan palourn, sun samu palourn ba kowa, hakan ya sanya Umar ya mata sai anjima ya fice, ita kuma ta haura sama.
⭐️
PLATEU SPECIALIST HOSPITAL.
ABUBAKAR SADEEQ POV
***
Khalid da Sa'ad su ke tare da Sadeeq, ko da likita ya zo sake duba yanayin jikinshi, cikin gajiya da zaman asibitin Sadeeq ya ce da likitan yana buƙatar sallamanshi, likitan ya bashi haƙuri akan ya bari aai gobe Monday a duba idan komai lafiya sai a sallameshi, Sadeeq shiru yayi bai kuma cewa komai ba har likitan ya gama ya fice.
Sa'ad ne ya ce, "Yaya Sadeeq ai ma ka yi ƙoƙari wallahi, ba dan ciwo ba yanda aka iya mishi ba, ai bana tunanin za ka yi sati guda a asibiti balle fiye da haka."
"Ciwon kenan ai, ko ya mutum yake idan ta zo ba ruwanta sai ta kwantar da shi, haka ma mutuwa da ta zame dole", faɗin Khalid.
Sadeeq dai bai ce musu komai ba, su kuma basu fasa hirarsu suna jefo shi a ciki ba, daga ƙarshe ya fara amsa musu sama-sama.
Da rana direba ne ya kawo abinci, Khalid ya ɗiba wa kanshi, ya ɗiba wa Sa'ad, shi Sadeeq kunu ya ce Khalid ya zuba mishi, dan baya jin cin abinci lokacin.
Kunun Khalid ya zuba mishi ya miƙa mishi, yana ƙoƙarin kai cup ɗin bakinshi sai ga ƙira wanda daga sautin ya san wacce ke ƙira, aje kunun yayi a drawern gefen gado na asibiti, sannan ya ɗau ƙiran, sallama ta mishi a ɗaya ɓangaren, ya amsa tare da cewa, "Ina lafiya Sa'adiyahh, jiki alhamdulillah."
Shiru yayi alamar yana sauraren abinda take faɗa a ɓangarenta, sannan ya bata amsa, a haka har suka kammala wayar, basu wani ɗau lokaci suna wayar ba suka yi sallama, ba haka ta so ba amma ba yanda ta iya, suna gama wayar ya sanya ta a flight mode ya ajiye ya fara shan kunun shi.
⭐️
RAYFIELD
SADIYA POV
***
Khausar ko da ta duba ɗakin Umma ba Sadiya, komawa ɗakin da suke gyaran jiki a can ta yi, nan ta same su, sannu da aiki ta yiwa Umma, wacce ke cewa, "Wai tun ɗazu kuna tare da Umar ɗin?"
"Eh Umma", Khausar ta amsa.
"Na rasa me kuke tattaunawa da Umar wallahi, kar dai ku yi gulmar mutane har ta wuce ƙa'ida, fatan dai ya tafi dan ya samu shi ma ya huta yau Lahadi kam."
"Ya tafi Umma, ina su Najla?"
"Suna tare da Abbanku, ina jin suna a wajan shan iska ta baya, kinsan Abbanku idan yaga fararen yaranki masu kama da turawan nan ba iya ƙyalesu su kaɗai zai yi ba, da cewa yayi yau zai yi bacci ya ɗan huta, amma yanzu fitinannun nan sun hana shi, ni ana sallahn azahar ma ki tattarasu ku koma wajan Maman Sadeeq, ya samu yayi bacci kamun la'asar."
"To Umma", faɗin Khausar tana ƴar guntun dariya.
Miƙo mata cup uku da abubuwa a ciki Umma tayi tare da cewa, "Ungo amsa ki sha, auta ta tsammaki."
"Ina godiya kuwa, sannu da juriya small Mum."
Tura baki Sadiya tayi tare da cewa, "Wallahi duk na gaji aunty."
"Haka kuma za kiyi haƙuri ba, domin mace sai da gyara musamman aure za kiyi, kuma kada kiyi irin ta wasu yammatan zamani masu rawar kan tsiya, ba iya gyaran jikin za ki saka a ranki ba, har da nasihohin da ake miki ki adana, kindai ji abinda Abba ya ce mana, rayuwa sai da haƙuri, kuma halinki da biyayyarki da haƙurinki shi ke saya miki komai wajan miji da danginsa, inji masu iya magana suka ce ba a ƙin mutum sai dai a ƙi halinshi."
Daga haka Umma ma ta ɗaura da nata nasihar wa su duka, da ƴan shawarwari da dabaru na zaman aure da sauransu, ba iya Sadiya ba har da Khausar ta ƙaru da wasu shawarwarin, duk da daman kullum kusan maganar Umma kenan, ba za su yi waya su sallame ba sai ta mata faɗa da nasiha.
Ana hada-hadan sallahn azahar Khausar ta ja hannun Sadiya zuwa sashin Sadeeq, wannan box ɗin ta ɗauko tare da cewa, "Small Mum plss kiyi tunani mai kyau, wannan box nake so ki buɗe mini, code da kike tunani Yaya Sadeeq zai iya sakawa, may be sunanki yadda yake ƙiranki ko wani abun da kike tunani haka dai."
Sadiya kallon box ɗin tayi sai ta kalli Khausar, sai kuma ta fidda wayarta ta kira Sadeeq, sai da suka gaisa ya kashe wayar, sannan tana tura baki ta ce, "Aunty ki saka Sa'adiyah mu gani ko haka ne."
Khausar ƴar murmushi tayi na tura bakin da Sadiya tayi, wato da gaske hasashen uncle U, Yaya Sadeeq da small Mum suna ƙaunar junansu, wataƙila kamar yadda ya ce ne shi Yaya Sadeeq ya sani, amma ita small Mum bata sani ba, to ya ma za a yi ta haɗa soyayyan mutum biyu a zuciyarta? Ah lallai kam akwai kallon ikon Allah, dan wannan ba mai yankewa ko lissafo me zai iya faruwa sai dai abinda Allah yayi kawai, "Allah ya sa mu ga alkairi", ta faɗa a fili bayan ta gama zancen zucinta.
"Amin Ya Rabbi, alkairin menene aunty?" Faɗin Sadiya tana kallon Khausar.
"Ba komai", Khausar ta faɗa yayinda take sanya sunan kamar yadda Sadiya ta faɗa, bayan ta gama saka wa, ganin abinda ya nuna ta sa ta ɗago tana kallon Sadiya.....
***
Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji.
●BAKANDAMIYA HIKAYA.
●WATTPAD
@Uwarbatoorl96
●AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
●WHATSAPP
09161720046
a kan Naira #500.
Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah.
# Hareeyh
# 09161720046
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
[07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
💔NAUYIN BAKI....👄💔
Na
Uwar Batoorl.
𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍
🅿️ 27 _ 28
⭐️
Khausar ta ɗago tana kallon Sadiya tare da cewa, "Small Mum anya kin tuna daidai kuwa, ko ɓata miki rai Yaya Sadeeq ɗin yayi? Haka ya sa kika mance."
Sake cunna baki Sadiya tayi tare da fara magana idanuwanta na cikowa da ƙwalla, don ta taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi a zuciya, cewa tayi, "Aunty yanzu Yaya Sadeeq yana kyauta mini?"
Da mamaki Khausar ke kallon Sadiya, lokaci guda kuma tana ƙara zuba mata ido, dan ta fahimci abinda suke tunani a kai da kyau, cewa tayi, "Me ya miki small Mum?", cikin sigar tausasawa tayi maganar da kuma lallashi.
Cike da ƙuncin da ke nuna yadda take ji a zuciyarta ta ce, "Yaya Sadeeq ya daina so na Aunty, ko magana a waya ma ya daina yi da ni sosai balle ƙira yadda muka saba, an hana ni zuwa asibiti shi kuma ya ƙi na kalleshi ko ta video call, phone call ɗin ma da ƙyar yake yi, ni da Yaya Sadeeq na saba hira kowa ya sani, shi ma ya sani, amma yanzu Yaya Sadeeq ya daina hira da ni balle ya ji damuwata, gaba ɗaya ya canja mini , ya sauya daga yadda na sanshi kuma muke, abun na damuna sosai a zuciya, kawai ina dannewa ne saboda Umma, Aunty wallahi Yaya Sadeeq shi ne duniyata, na fi son shi fiye da Yaya Umar, matsayinshi ya wuce na Yaya Umar a wajena, jin shi nake tamkar mahai...."
Saurin katse ta Khausar tayi ta hanyar girgiza kai tare da cewa, "A a, small Mum kada ki kai shi wannan matsayin, don kada ki haramta abinda Allah ya halarta a tsakaninku."
Sadiya cikin rashin gane me maganar Khausar ke nufi, ta cigaba da cewa, "Yanzu dan Allah tun ban yi aure ba haka, idan nayi aure kuma ya Yaya Sadeeq zai ke treating na? Bayan kuma a addinance ma yana da kyau Yaya ko Uba su dinga ziyartar ƴar su ko tuntuɓatarta, dan jin halin da take bayan ta yi aure, da kuma su mata nasiha su bata shawara, Yaya Sadeeq shi ne duk matsayin haka a wajena, idan yana irin haka ya zan yi a gidan aurena? Don Yaya Umar daman ba ƙaunata yake yi ba balle ya tuntuɓi ya nake."
"Uncle U yana ƙaunarki, kuma dole shi zai miki duk wannan, sai kuma Abba."
Ɓata fiska Sadiya tayi tare da cewa, "Ni ko ma dai menene ba na son nashi, na Yaya Sadeeq nake so dan da shi na saba."
"Dole Yaya Sadeeq za ki haƙure da shi a wannan mataki, nomatter how you feel about him, it won't change the fact that you're not having the same father or mother with him, Allah ne ya ƙaddara shi ba muharraminki ba, to a dalilin haka, ya zama dole a wani mataki Yaya Sadeeq ya kiyaye biye miki ko da kuwa Haidar ya lamunce mishi, idan a wajanmu mun ɗauki uncle U da Yaya Sadeeq abu ɗaya a gare ki, to fa a wajan Allah ba haka bane, Yaya Umar shaƙiƙinki ne muharraminki ne, shi kuma Yaya Sadeeq zai zama muharraminki ne kawai idan ya aure ki, kin sani dan haka kada ki take saninki small Mum, am very sure saboda kiyayewa ya sanya Yaya Sadeeq ke janye jikinshi daga gare ki, and he's quite right, haka ya kamata ya yi, mai zurfin ido ai da wuri yake fara kuka, so ki fahimta kuma ki bar ganin laifinshi, halaccin auren da ke tsakaninku ne ya sa yake haka dan kiyaye dokar ubangiji, ki mishi uzuri."
Hawaye ne masu ɗumi suka zubo wa Sadiya jin bayanin Khausar, tabbas ta san haka ne gaskiya ta faɗa, amma ba ta son irin wannan gaskiyar, murya a karye ta ce, "Aunty stop saying this please, kuma in akwai yadda zan yi nayi settling wannan dalilin nashi, da nayi na goge, Yaya Sadeeq nake so ya zama guardian na akan komai ba Yaya Umar ba, please aunty ki bar ambatar aure tsakanina da Yaya Sadeeq ko a wasa, domin cikin Umma ɗaya na ɗauke shi, Yaya Sadeeq nake so ya zama waliyyi na ko a ɗaura aure ma."
Khausar ta ce, "Ko me za ki ce ko za ki yi, ba zai sauya cewa Yaya Sadeeq ba muharraminki bane, dan haka Allah ya tsara, zai kasance ne kawai idan ya aure ki."
"Shikkenan Aunty mu bar maganar, Allah tashi kafaɗun Yaya Sadeeq ya dawo gida lafiya."
Khausar ta ce, "Amin Ya Rabbi, amman kuma da kike cewa Yaya Sadeeq ne waliyyinki a ɗaura aure, su ƴan uwan Baba za su amince ne? ko kuwa Abba zai yarda?."
Ɓata fiska Sadiya, tayi tare da cewa, "Ni dai Yaya Sadeeq nake so ya zama waliyyi na, dan ta su mutanen Minna ba na jin su, Abba ne nake so dai yayi haƙuri ya fahimce ni, ya mini uzuri, kuma ya amince, Aunty wallahi bakina ba zai iya furta matsayin Yaya Sadeeq a wajena ba, duk wanda ke son Yaya Sadeeq ina son shi, haka duk wanda ke girmama shi, kuma ina ƙin mai ƙin shi ko waye, fatana dai Allah ya sa Abba ya amice wa wannan muradin nawa, na samu ya cika."
"Uhmn Amin to", Khausar ta amsa tana mai kuma tabbatar da maganar Umar a zuciyarta, lallai-lallai Sadeeq ke ƙidarshi da rawarshi, Sadiya bata fahimci ƙaunar Sadeeq da ke a zuciyarta ba ta masoya, kuma dole a mata uzuri, domin yarinya ce, Haidar ne first love nata bata wani san soyayya sosai ba, shiyasa ba lallai ta gane feeling's da Sadeeq yake da shi a kanta ba, ko ita take ji game da shi a zuciyarta, sai dai duk da haka tana mamakin yadda muradin auren Haidar ke danne komai a zuciyar Sadiya, da har take jin sanya Sadeeq a gaba a kan komai, lallai Sadiya na son Haidar matuƙa, Allah ne kawai ya san abinda zai iya faruwa a gaba, muna fatan khairan Ya fa'alun lima yuridu.
Sadiya jin Khausar tayi shiru sai ta ce, "Aunty, bani box ɗin na gwada buɗe miki da kai na."
Ba musu Khausar ta damƙa wa Sadiya box ɗin, ita kuma ta amsa tana ƙare mishi kallo, sai da ta yi bismilla tare da fatan, Allah ya sa ta iya buɗewa, sannan ta kai hannunta ta fara gwada sa'arta, ta gwada ya kai sau biyar duk ba daidai ba, hakan ya sanya Khausar ta sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya tare da cewa, "small Mum bari kawai, tashi mu je."
Sadiya ajiye box ɗin tayi, har ta miƙe tsaye sai kuma ta koma ta zauna tare da ɗaukan box ɗin, ƙanƙance idanuwanta tayi tare da taune lip nata na ƙasa da ƙarfi, «Sa'adiyah18», haka ta sanya tare da saurin kulle idanuwanta gudun kar har yanzu bata canka daidai ba.
"Wow! awesome small Mum, sai da ke ƙanwar Yaya Sadeeq", faɗin khausar da ke murmushi tare da kai hannunta ta ɗauki box ɗin a saman ƙafar Sadiya, dan ya riga da ya buɗu.
Sadiya buɗe kyawawan idanuwanta tayi ita ma tana murmushin, wushiryanta ya ƙawata murmushin, yayinda dimple nata gefe guda ya lotsa.
"Menene a ciki aunty?" Sadiya ta tambaya tana ƙoƙarin komawa gefen Khausar dan ta leƙa cikin box ɗin.
Khausar ta ce, "Kar ki damu za ki san menene a ciki, bari komai ya daidaita."
Kasancewar Sadiya ba ma'abociyar bin ƙoƙƙofi ko jin ƙwaƙwaf ba, ya sa bata ja maganar ba ta miƙe tare da cewa, "Bari na ja su Najla mu tafi gidan Mama, Abba ya samu yayi bacci."
"Ai kam ya kamata, ku gaishe da Mama, zan shigo idan na kammala abinda zan yi."
"To aunty, a kammala lafiya."
"Amin small Mum", faɗin Khausar tana sakar mata murmushi.
Sadiya ficewa tayi a sashin, ta samu daidai Abba da su Najla sun shigo, hakan ya sanya ta yiwa Abba sannu, sannan ta ɗauki Nayla ta kama hannun Najla suka fice dan daman da hijabinta a jikinta.
Khausar tana ganin ficewan Sadiya ta ƙarisa buɗe box ɗin, tare da sanya hannu ta ɗauko envelope da ke a ciki, ajiye envelope ɗin tayi a gefe, sannan ta kuma sa hannu a cikin box ɗin, yanzun waya ta ciro ƙirar Samsung, amma wayar a kashe da alama bata da chaji dan ko da ta yi ƙoƙarin kunnawa ya ƙi kunnuwa, ko da ta mayar da hannu ciki sai key ta ciro, sai sauran tarkacen ciki, lims, ring mai alphabet na S, sai wristwatch, duk a kan centre table da ke a gabanta ta baza su, ta kuma bar box ɗin a buɗe ta miƙe ta shige bedroom na Sadeeq, alwala ta ɗauro, bayan ta fito a bedroom ɗin sai ta ƙira Umar, yana ɗauka ta sanar mishi box ɗin ya buɗu ya zo, Umar ya amsa a gaggauce a hanzarce, dan lokacin yana hanyar zuwa masallaci ne ma, sauri yake kada yayi missing raka'a saboda an riga da an fara sallar.
Khausar ma tana gama wayar ta ajiye, tare da sanya wayar da ta ciro a box ɗin a chaji, sannan ta tayar da sallah a nan palourn.
Umar ana idar da sallah ya samu ya shafa addu'a, a hanzarce ya miƙe ya fice tare da sahun masu fitan farko a masallacin, kai tsaye gidan Abba ya nufa, kuma ko da yayi sallama ba kowa a palourn, bai damu ba ya wuce sashin Sadeeq, da sallama ya shiga nan ma, inda ya samu khausar ta ida sallar har ta koma ta zauna, hakan ya sanya ta amsa mishi sallaman, shi kuma ya samu waje ya zauna, nuni ta mishi da kan centre table ɗin, in da tarkacen abubuwan da ta ciro suke zube, ta ce, "Ga su nan a ciki na ciro su kaf, har wancan wayar", ta ƙairshe faɗa tana mishi nuni da wayar da ta maƙala a chaji.
Murmushi mai kyau ne ya yalwata a kyakkyawar jarumar fiskar Umar, hannu ya tafa tare da ɗaga mata yatsa guda alamar jinjina ya ce, "Na san tabbas za ki taimaka mini sosai sis, shiyasa na ce za ki tayani binciko gaskiya."
Murmushi kawai Khausar ta yi, duk da a gefen zuciyarta tana kissima wani abu, rashin gano bakin zaren matsala ce gare su, barazana ce ga lafiya da ma rayuwar Sadeeq gaba ɗaya, amma kuma abinda take hasasowa a gano bakin zaren, bata addu'an abinda take hasasowan ya tabbata, domin a nan ma wata matsalar ce ƙasurguma, "Khairan Ya Rabbi, ka kawo mafita ta alkairi, duk abinda ya faru bisa ikonka, to Ya Rabbi ka bai wa zuciyoyi haƙuri, juriya da jarumtar amsar ko ma menene, domin tabbas akwai tirka-tirka, daga mutane da dama."
"Amin sis", Umar ya faɗa, domin ya san gaskiyarta, amma kuma a wajanshi komai mai sauƙi ne da yardar Allah, ba ya hasaso wani damuwa, komai ne zai tafi cikin fahimta da salama da aminci, muddin dai aka yi wa juna bayani da kuma uzuri.
Envelope ɗin ya fara ɗauka, sai da ya sauƙe ajiyar zuciya sannan ya buɗe ya ciro photo's da ke a ciki da kuma letter da ke naɗe, wani irin murmushi ne ya suɓuce mishi da yayi arba da hotunan, domin a iya hotunan nan, ko mahaukaci ya gani ya san dalilin ajiye su, duk da Sadeeq ya ƙware a coner da kuma rainin hankali, to lallai ko ɗaya ba zai yi aiki ba a wannan karon.
Umar yana gama kallon hotunan ya miƙa wa Khausar, a maimakon ta fara kallonsu kai tsaye, sai ya ga ta juya bayan hotunan, ɗaya bayan ɗaya ta bi ta karance writeups da ke a bayan hotunan, wani irin mamaki ne ya rufe ta gami da matuƙar tausayin yayanta, lallai Yaya Sadeeq yana fama da abu a zuciya, idanuwanta ne suka ciko da ƙwalla, ta miƙa wa Umar hotunan, shi kuma tambayarta yake, "Meyasa kika miƙo mini su baki kalla ba? Na ga duk bayansu kika duba."
"Abinda ke a bayansu ya jima da shaida mini da asalin photon da ke gaban, domin abinda ke a bayan ya fi tsuma ni fiye da hotunan, bayani ne a kan irin halin da Yaya Sadeeq ke a ciki a ko wani mataki na hoto guda ɗaya, lallai ina tausayin Yaya Sadeeq domin abun tausayi ne shi, Yaya Sadeeq na da jarumar zuciya ƙwarai da gaske, Yaya Sadeeq jarumi ne, domin ba lallai wata zuciya ta iya riƙe abinda ta shi zuciyar ta riƙe a tsawon lokaci ba, sannan kuma zuciyarshi ta iya sadaukar da komai da komai ga waninta, ta hanyar shige mishi gaba wajan mallakar abinda ta fi muradi da ƙauna, abincin ruhi kuma cikon ruhi, ina tausayin Yaya Sadeeq", Khausar ta ƙarishe faɗa tana share ƙwallan da ya zubo mata a ido guda.
Umar da sauri ya amshi hotunan tare da ajiye lettern da ya ɗauka, da sauri-sauri ya dinga karance write-ups ɗin tare da sake juya hotunan kaman bai kalla ba dama, dan duk wanda ya karanta bayanshi to sai ya juyo gabanshi, yana kammalawa da su ya aje, tare da buɗe takardan da ke naɗe(letter), a hanzarce ya fara karantawa, yana yi yana kallon zoben da kuma maɓallin hannun riga(lins), da kuma agogo(wristwatch), a haka har ya kammala karancewa, sannan ya miƙe ya isa ga wayar ya ciro a chaji, kaman zai kunna sai kuma bai kunna ba, duka a cikin box ɗin ya tura tare da kullewa, idanuwanshi sun kaɗa sun yi ja, har jijiyoyin kan shi sun tattashi, ɓacin rai tsantsa a kwance a fiskars shi, ba tare da ya dubi Khausar ba ya nufi ƙofar fita.
Da sauri Khausar ta miƙe, murya a sanyaye ta ce, "Uncle U ina za ka je a haka?"
Umar yana taune leɓenshi ya ce, "Sister Khausar asibitin zan je na same shi, zan gani ne ko har yanzu yana da idanuwar da zai dube ni da su ya musa mini."
"Zan bi ka", Khausar ta faɗa a sanyaye har sannan, domin ita Allah ya gani mugun tausayin Yaya Sadeeq ne ya rufe ta, domin ita tana iya hango kaɗan daga cikin abubuwan da za su iya faruwa.
"Zuwa dare ko safiya zan zo mu je tare, but yanzu ki yi haƙuri ni da shi kawai nake so mu yi magana", Umar na gama faɗin haka ya fice, a haka ya fita a gidan, a fusace ya shige motarshi ya mata key tare da ficewa a gidan da mugun gudu, wadda har mai gadi ke mamaki domin ya san Umar bai cika irin tuƙin nan ba, a nitse yake komai, a fili mai gadin ya ce, "Allah ya sa lafiya, Allah kuma ya kare ka", shi yayi addu'an kuma shi ya amsa da amin ɗin, sannan ya koma kan abinda yake yi.
Khausar a sanyaye ta fito a sashin ita ma, tana isowa palourn ta samu Umma da ke tsaye tana bin ƙofar fita da kallo, domin a kan idonta Umar ya fice, kuma ta ga alamar kamar ba lafiya ba ran shi a ɓace, ga shi a fusace ya fice kamar gilmawar walƙiya balle ta samu ta mishi magana.
"Ke Khausar menene ya faru? Lafiya na ga Umar ya fita haka?", Mama ta faɗa tana mai da dubanta ga Khausar, dan tun fitowarta kwanar sashin Sadeeq ta ji motsinta.
Khausar cikin ƙoƙarin ɓoye abinda ke faruwa ta ce, "Shi da wani abokin cinikayyarsu ne", ta ƙarishe faɗa tana istigfarin ƙaryar da ta yiwa mahaifiyarta, amma hakan shi ne mafita, domin ya kamata komai ya daidaita kamun iyayensu su ji, musamman Umma da Abba.
Numfashi Umma ta sauƙe tare da cewa, "To Allah ya kyauta, Allah kuma ya tsare ya kai shi ko ma ina ne lafiya, domin irin wannar fusata ta Umar ba ma za ta barshi yayi tuƙi a nitse yadda ya saba ba, ko ma menene dai Allah ya saisaita ya kawo musu da sauƙi, dama mu'amala da mutane sai a hankali sai haƙuri kuma, ko da ta rayuwace kawai balle kuma har da kasuwanci a tsakani, Allah ya taimaka ya muku albarka duk."
"Amin Ya Hayyu Ya Qayyum", Khausar ta faɗa tare da wucewa ta haura sama, Umma kuma ta wuce kitchen dan dama can za ta tafi, ganin yanayin Umar ya sa ta tsaya jin ba'asi.
⭐️
PLATEU SPECIALIST HOSPITAL.
ABUBAKAR SADEEQ POV
***
Sadeeq suna gama waya da Sadiya ya soma shan kununshi a nitse, kunu mai yawa ya sha sannan ya kora da magungunanshi, wayar ta shi da ke a flight mode ya danna tare da duba lokaci, ganin azahar ya kusa sai bai kwanta ba saboda kar bacci ya ɗauke shi, dan a maganinshi akwai mai ɗan saka shi bacci, duk saboda a samu yanayin zuciyarshi ta dawo daidai.
Ɗan jingina da kan gadon Sadeeq yayi tare da lumshe idanuwanshi, can kuma sai ya jawo wayarshi tare da shiga gallery, hotonta ya zuba wa idanuwa yana mai jin wani iri a zuciyarshi, amma ya dinga ƙoƙarin kaudawa da daurewa, dan tabbas yana buƙatar sallama zuwa gobe duk rintsi, kamun Umar ya je ya mishi binciken ƙure maleji har ya tono abinda yake binnewa, gwanda ya koma gida ya taka wa komai birki.
A jinginen ba tare da Sadeeq ya ankara ba, baccin da ya guda yayi awun gaba da shi mai daɗin gaske, domin mafarkin Sadiya ne fal ciki mai armashi.
Ƙiiii!, ƙaran buɗe ƙofan da su Khalid suka yi ya katse mishi daddaɗar mafarkinshi, domin guntun baccin watsewa yayi, fiskarshi a haɗe yake bin su da kallo, wanda sun san na menene.
Khalid da sauri ya ce, "Afuwan Yaya Sadeeq daga masallaci muke, mun je salla ne."
"Ya Allah!", Sadeeq ya faɗa yana dafe goshin shi, tare da cewa, "Amma kuna gani ina bacci ba za ku tashe ni ba na samu na bi jam'i."
"Afuwan Yaya Sadeeq, wallahi Sa'ad ne ya ce mu barka, idan muka tashe ka kanka zai yi ciwo tunda ba lafiya ne da kai ba", yanzun ma Khalid ne ya bai wa Sadeeq amsa yana nuna Sa'ad.
Kallon da Sadeeq ya yiwa Sa'ad ɗin ya sanya shi cewa, "Afuwan Yaya, lafiyarka nake tunani."
"Ni kam na warke alhamdulillah, next time ku tashe ni na samu bin jam'i ko da ba zan samu zuwa masallaci ba", ya ƙarishe faɗa yana miƙewa, cikin takunsa na jaruman maza majiya lafiya da ƙarfi ya taka ya nufi banɗakin, domin tabbas a zahiri jikinshi da sauƙi, har ɗan faɗawan da yayi ya ragu.
Sadeeq toilet ya shige ya ɗauro alwala ya fito ya ta da kabbaran salla, su Khalid kuma suka samu waje suka zauna suna magana ƙasa-ƙasa.
Sadeeq a nitse yayi sallarshi,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 32