Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
murmushi. Umar ya ce, "Mama kun yi magana da Abban ne?" "Eh Umar, mun yi magana, ai da zafi-zafi ake dukan ƙarfe, sammako na buga na same shi muka magantu, ya dai yi kafiyarshi ya gama, daga ƙarshe muka ci nasara, ya ce na tura mishi Sadiya, muddin ta ce mishi ta amince to shikkenan zai san yadda zai yi, amma idan bata amince ba ya rantse ba zai ɗaura ba, kuma da na dawo na tura ta, dan bata jima da dawowa ba tana ɗaki, da alama dai ta amsa mishi shiyasa ta ƙi kulamu, mu ma mun ƙi bin ta ɗakin ne dan ta yi kukanta ta gama ta bari dan kanta, ai da abin arziƙi aka so ta, ita ya kamata ta gode ba wai a lallasheta ba." "Au shiyasa dawowanmu muka same ta a zaune a can kenan, wajan Abban ta je, shikkenan tunda ta amsa to ta taimakai kanta, domin ko bata amsa ba sai ta auri Sadeeq in sha Allah." Khausar numfashi ta sauƙe dan ita a jikinta ba ta jin kamar haka, shiyasa a taƙaice ta ce, "Allah dai ya tabbatar da abinda ya fi alkairi." "Amin Ya Allahu", Mama ta amsa. Umar yayi ƙwafa tare da cewa, "Ina rasa ko sauyo miki yarinyar nan aka yi a asibiti Mama, Sadiya kallon mutane take har tsakar ka..." "Allah dai ya shirya mini ita ya mata albarka, Allah ya ba su zaman lafiya", faɗin Mama dan maganar ta wuce, dan yanzu ita muddin ta tabbata amsawa Sadiya ta yi da batun Sadeeq,  to lailayarta za ta dinga yi da lallashi kamar jaririya dan ta gama biyanta. Khausar ta amsa da, "Amin." Umar kuma ya miƙe ya wuce ɗakinshi tare da yiwa su Mama sai ya fito, su Najla suka koma kan kallonsu suka ƙyale shi ya tafi, ko da ya shige ɗakinshi shi ma wanka ya yi tare da sanya iya gajeren wando ya bi lafiyar madaidaiciyar gadonshi ya kwanta, shi ne bai tashi ba sai azahar daga haka ya sake watsa ruwa ya shirya ya fito, abinci ya ci wanda Mama ta miƙo mishi da kanta, sannan ya mata sai ya dawo ta amsa da a dawo lafiya ya fice ya wuce company, amma sai da ya tsaya ya yi sallar azahar sannan ya ƙarasa katafaren office ɗin da yake mallakinshi. Khausar ko da ta koma ɗaki samun Sadiya tayi tana bacci da wannan ajiyoyin zuciya, kallonta take cike da tausayi, sannan ta yi musu addu'an alkairi ta shirya ta fito, abinci ta ci ita ma ta yi wa Mama sallama ta fice ta nufi gidan Abba, su Najla a gidan Mama ta bar su saboda suna baccin rana su ma. ⭐️ ALIYU HAIDAR POV    *** Tun daga ranar da Aliyu ya fatattaki Husna da ta kawo mishi coffee, tun daga ranar ya samu sarari, Hajiya ta sakar mishi mara, ya samu salama a lamuranshi gaba ɗaya, domin yanzu ko hanya basa haɗawa da Husna, Hajiya ma bata sake yi mishi maganarta ba, hakan ya ba shi damar mayar da hankalinshi kacokam kan ayyukanshi, da kuma Al-Sad ta shi, suna soyewa tare da mararin bikinsu da ke ƙaratowa, a wannar matakin Haidar har ranshi yake jin ko fa mutuwa ne to dole ya sarara mishi ya mallaki Sadiya kamun ya ɗauke shi in sha Allah, balle kuma wani mutum. Da farko Haidar ya so ya gyara gida ɗaya daga cikin gidajen da Alhaji ya ce ya zaɓa wanda za su zauna a ciki da Sadiya, amma kuma firrr Hajiya ta turje ta ce bata san zancen ba, ba wani gida can nesa da za su je, ai ga nan sashinshi, iyayen Sadiya su kawo furniture's nata a saka a ɗaya ɗakin da yake empty, dama dan haka ta ce a barshi empty, ita bata isa yaronta ya yi nisa da ita ba, Nufawan nan su ma ba abun yarda bane, kar Sadiya ta mallake mata yaro ya ko daina zuwa suna kallonshi yadda suka saba, dan haka a sashinshi za su zauna. Wannar magana ta Hajiya wai kar Sadiya ta mallakeshi ba ƙaramar dariya da kuma taƙaici ta bai wa Haidar ba, shi idan Sadiya ta mallakeshi ai shi ne da godiya, sai dai abinda ya ba shi taƙaici ya fahimci Hajiya za ta hana su rawar gaban hantsi ne kawai, in ba haka ba akan me Sadiya za ta zauna a wannan sashin, sannan bugu da ƙari Haidar har ma da Alhaji sun gano manufar Hajiya na asali, da ta hana a saka furniture's a ɗaya ɗakin sashin Haidar, wato dai rashin mutunci ta shiryawa surkuwarta tun fil azal, wadda suke da tabbacin da Husna ce to ba za ta yi mata haka ba, shi dai Haidar Allah ya kyauta ya bi lamarin da shi, yayin da ya samu Alhaji ya kanainayeshi a kan shi ba zai iya zama da Sadiya a wannan sashin ba, kunyar su zai ji, rigima dai ya saka wa Alhaji kamar ɗan goye, sai da Alhaji yayi dariya mai isar shi, sannan ya ce, "Allah ya shirya mini kai Aliyu, wato dai dan baka samu waje bane, amma da ka samu waje da ba ƙaramin taƙadirin shagwaɓaɓɓe za a yi ba, ji abinda kake kamar ba ƙanne gare ka waɗanda ake shirin aurar wa ba." Haidar dai yana kan zuba wa Alhaji rigimarshi, ta dole Alhaji ya amince a kan ya ji zai yi magana da Hajiya, ba za su zauna a asalin sashinshi ba, amma za su zauna a part da ke gefen nasu, tunda dama ba part ɗaya bane a cikin gidan, Haidar ba haka ya so ba, amma kuma da babu gwanda ba daɗi, da dai su zauna a sashinshi da ke part na Hajiya, ya gwammace su zauna a ɗaya part ɗin su kaɗai, sai su sake gwanda-gwanda, daga ƙarshe dai haka suka yanke, inda Alhaji sai da ya kai ruwa rana da Hajiya sosai sannan ta amince, amma ta amince ne bisa wani ƙudurin nata wanda ta sanar da Alhaji, ya rasa bakin magana kawai ya zuba mata ido tare da fatan Allah ya kyauta, ya kuma tabbatar da alkairi kawai. Alhaji ya bi Hajiya a kai lefe ya fi sau shurin masaki, ya bi ta har ranshi ya ɓaci amma sai kwana-kwana take yi, har dai ya yi tafiya ƙasar China, ya kwashe kwanaki sannan ya dawo a jiya Lahadi dare-dare, inda yau litinin aka tashi ya kama a cikin satin biki kenan. Dama tun Alhaji na can China, Haidar ya matsa mishi da batun yaushe za a kai kaya, ga shi za a shiga satin biki a fara events kaya basu isa ga amarya ba, ga kuma shi sai shan kunya yake yi, kullum ce mata yake masu lefe na zuwa amma shiru, Hajiya ta ƙi bari a kai, wannan ya sa Alhaji ya dawo a fusace, tun daren jiya da ya dawo har wayewan garin yau faɗa yake, dole Hajiya ta dinga ƙiran bayin Allah tana sanar da su gobe talata za a kai kayan auren Haidar, sannan ta faɗa wa Alhajin a gobe za a kai sai Haidar ɗin ya sanar da Sadiya, ai kuwa Alhaji na sanar da Haidar shi kuwa ya ɗauki waya ya aika wa Sadiya ƙira dan sanar mata. ⭐️ ABUBAKAR SADEEQ POV      *** Sadeeq shi ne bai tashi bacci ba sai da ƙarfe uku ta yi, bacci yayi sosai, kuma ko da ya tashin, da ya samu ya watsa ruwa, sosai ya ji kuzari a jikinshi, sai ya shirya cikin black shirt da black 3quater, ya kuma feshe turarenshi mai masifaffen ƙamshin sanya nitsuwa da shauƙi.   Sadeeq da kanshi ya gyara ɗakinshi bayan ya idar da sallan azahar, sannan ya kuma fito ya haɗa tea mai rai da lafiya a side glass kitchen nashi, sai da ya koma palourn shi ya zauna sanna ya fara sipping tea ɗin cikin nitsuwa da aji, da ya kammala sha ya maida cup ɗin kitchen ya wanke abinda duk ya yi aiki da shi, kallonshi ya kai ga agogon da ke maƙale a rantsattsiyar hannunshi, ganin lokaci sai ya ɗau wayarshi ya nufi fitowa a sashinshi dan ya ƙarisa masallaci ya samu jam'in la'asar tunda ya rasa na azahar. Khausar ko da ta iso gidan, ba kowa a palourn, da kamar za ta yi sashin Sadeeq, da ta tuna Umar ya ce yana bacci ne, sai kawai ta fasa ta haura upstairs ɗakin Umma, da sallama ta shiga inda ta hangi Umma zaune kan sallaya tana jan carbi, ƙarisawa ta yi ta zauna a gefen gado, tare da cewa, "Barka da rana Umma." "Yauwa Khausar barkanmu, ya wunin yaran? Ya Mamanku da Auta, duk da dai su kan sun shigo da safe ke ce baki samu shigowa ba." "Duk kowa lafiya Umma." "Ina fatan dai auta ta bar kukan?", Umma ta tambaya cikin kulawa ga Sadiya. Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe, sannan ta ce, "Na dai baro ta tana bacci Umma, amma daga yadda numfashinta ke sauƙa na san ta ci kuka har ta gode wa Allah, dan Mama ta ce daga ni har ita ba mai lallashin small Mum, ai gata aka mata da za a aura mata Yaya Sadeeq ɗin, ni wallahi tausayi ma small Mum ke bani." Daga ita har Sadeeq abun a tausaya musu ne, Maman Sadeeq ta ɗauka ko auta ta yarda wato, shiyasa har ta fara ƙiran yaronta ango, to ta mayar da wuƙar ciki Abba ya ce Haidar za a bai wa auta in sha Allah." Cikin damuwa da kuma tausayin Sadeeq, Khausar ta ce, "Umma meyasa wai? Ko small Mum ta ce bata yarda bane? Amma kuma daga yanayin kukanta ya nuna kamar ta ce mishi Yaya Sadeeq ta zaɓa. Umma gauron numfashi ta ja cike da tausayin ɗan nata, ta ce, "Auta bata bai wa Abbanku amsa ba, amma tabbas daga yanayinta ya fahimci amsarta, Haidar ne a ranta, idan aka ce a aura wa Sadeeq ita, to daga shi har ita kawai cutar da su za a yi, Abbanku ma cewa yayi kada a kuma ta da maganar ya kashe ta, dan ya rantse dama muddin bata yarda ba to ba zai aura ma Sadeeq itan ba." Khausar ta ce, "Shi kuma uncle U ya ce ko mutuwa small Mum za ta yi sai ta auri Yaya Sadeeq, ga Abba ya rantse ba zai bai wa Yaya Sadeeq ba, yau ya za a yi ni Khausaratu, wannan lamari yana damuna yana ƙulle mini kai yana bani tausayi, so so ne duk da an ce son kai shi ne asalin so, nasan na fi tausayin small Mum dan ita ke a tsaka mai wuya, ita ke cikin asalin damuwa, sannan sai tausayin Yaya Sadeeq saboda Allah ya gani ina son Yayana ya auri small Mum, sun dace sosai, daga shi har ita son kowa ne ƙin wanda ya rasa, amma kuma a adalci irin tawa da zuciya ta musulunci ina mugun tausayin Haidar, yana son small Mum ita ma tana ƙaunarshi, Ya Rabbi ga wannan lamura gare ka, ka yi mana mafita ka sanyaya komai cikin aminci, ka tabbatar da abinda yake mafi alkairi, Allah ka sanyaya zuƙata ka ba da haƙuri." "Amin Ya Rabbil izzati", Mama ta amsa zuciyarta cike da damuwa da tausayin yaran nata duka, dan ita ma tana tausayin Haidar. *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [13/12/2025, 12:24] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 💔NAUYIN BAKI....👄💔 Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠 اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 39 _ 40 ⭐️ Khausar ficewa a ɗakin ta yi ta wuce sashin Sadeeq, ganin azahar ta yi tana tunanin ko zuwa sannan ya tashi a baccin, amma ko da ta duba bai tashi ba, hakan ya sa ta ja mishi ƙofa ta fito ta dawo wajan Umma, suka ci gaba da jujjuya lamarin da jimami. *** Sadeeq idanuwanshi a kan wayarshi ya iso cikin palourn, hakan ya sa bai lura da kowa a palourn ba ya ɗauka ko suna sama. "Sannu da fitowa Yaya Sadeeq", Khausar ta faɗa tana washe baki. Maganar Khausar ya sa Sadeeq ya sanya wayarshi a aljihu, tare da ɗagowa yana sakin ƙayataccen guntun murmushi, ya taka a sannu har ya ƙarisa inda Khausar da Umma ke zaune, a wajan ƙafar Umma ya zauna a ƙasa tare da ɗaura kan shi a saman cinyar Umma, cikin haɗaɗɗiyar muryarshi ya ce, "Barka da hutawa Ummanmu." Idanuwan Umma cikowa suka yi da ƙwalla na tausayin Sadeeq, amma tayi ƙoƙarin mai da su, tare da ɗaura hannunta a kan shi, kwantaccen gashin kanshi mara yalwa ta shafa, tare da cewa, "Barkanmu Sadeeq, barka da dawowa daga asibiti, sannunka da tashuwa, Allah ya maka albarka, Allah ƙara maka lafiya da haƙuri da jumriya, Allah ya tabbatar da abinda yake mafi alkairi a rayuwarka Sadeeq, Allah ya zame gatanka kuma majiɓancin dukka lamuranka, Allah ya tsare ka da tsarewarshi ya kare ka da kariyarshi, Allah ya baka tsawon kwana mu ga ƴaƴanka, Allah ya sa da kai da ƴan uwanka duk ku sanya ni a gidana na gaskiya, ka yi haƙuri Sadeeq, ka bai wa zuciyarka haƙuri ka kuma sanya mata salama, Allah na tare da mai haƙuri, kuma duk abinda ka ga baka samu ba a rayuwa, to dama tun fil'azal wannan abu baya rubuce a ƙaddararka ne, amma muddin Allah ya rubuta maka samun abu, to ko ana ha maza ha mata sai ka samu, ka miƙa lamuranka ga Allah Sadeeq, kuma duk abinda Allah ya yi kai dai ka gode mishi ka kuma sanya imaninka a kai hakan ne alkairi gare ka, addininka da ma zuri'arka." Lumshe idanuwa Sadeeq ya yi, wani irin nitsuwa ne da ƙwarin guiwa ke ratsa shi, tabbas uwa jigo ce a rayuwa, addu'ar uwa rahama ce ga lamura, duk tsawon shekarun da yayi yana dakon so, bai taɓa jin makamanciyar natsuwar da yake ji a yanzu a zuciyarshi ba, duk da kuwa yana tunatar da kanshi karɓar ƙaddara ko wacce iri ce, amma dai yau da abin yake daga bakin Umma, ya fi sanya shi natsuwa. Hawayen da Umma ke ƙoƙarin haɗiye wa ne ya gangaro tare da ɗiga a bayan wuyan Sadeeq, hakan ya sanya Sadeeq ɗagowa da sauri, girgiza kan shi ya soma yana faɗin, "Umma kukan me kuma? Dan Allah kada ku mana kuka Umma, khairan da yardar Rabbi." Umma share hawayen ta yi tare da murmushin ƙwarara guiwa, kamar yadda ya yi magana kuma yake kallonta cikin ƙwarara guiwa, tana murmushin ƙarfin hali ta ce, "Ina matuƙar son ka da auta, na fi kowa baƙin cikin ɓoyewan da ka yi, amma duk da haka ina addu'a muddin ku alkairi ne ga juna to Allah ya mallaka muku junanku, idan ba alkairi ba kuma to Allah ya ba ku haƙuri." "Amin Umma", Sadeeq ya faɗa yana duƙar da kai tare da shafa bayan wuyanshi. Khausar da ke gefe ita ma tana share ƙwallan cewa ta yi, "In sha Allah ma su alkairi ne ga juna Umma, wallahi Yaya Sadeeq ya fi dacewa ya auri small Mum, Allah dai ya iya mana da abinda ba za mu iya ba." "Amin Khausar", Umma ta amsa. Sadeeq ta wutsiyar ido ya kalli Khausar, ya ɗan murmusa tare da cewa, "the cry don't fit you, so ki bar wa jikokin Abba su yi", a taƙaice yayi maganar, kuma da sigar raha duk da babu hakan sosai a fiskarshi, sai dai a zuciyarshi kawai wanda ke cike da ƙaunar mahaifiyarshi da tilon ƴar uwarshi. Umma ta ce, "Ai kuwa ta bar wa masu jajayen kunnuwa su yi, ita ta girma ai." Sadeeq a taƙaice ya ce, "Afuwan Umma." Murmushi Umma ta yi tare da shafa kan Sadeeq, saboda ta gane a kan maganar Sadiya yake bata haƙuri, hakan ya sanya ta ce, "Allah ya yi albarka ya shige mana gaba Sadeeq." "Amin Umma", ya amsa yana miƙewa tsaye, tare da sake duba agogon da ke maƙale a rantsattsiyar hannunshi, sai da ya numfasa sannan ya ce, "Masallaci zan wuce Umma, daga nan zan yi gida na gai da Mama." "Ya kamata kam ka leƙa Mamarka, dan yau saboda kai har da asubanci, ta bugo mana sammako, wannan Mama taka kana bata wahala Sadeeq", Umma ta faɗa tana ƴar murmushi na yaba soyayyar Mama ga Sadeeq. Shi ma Sadeeq murmushin ya yi, bai kuma cewa komai ba ya musu sai ya dawo, ya juya ya fice cikin ingirman tafiyarshi mai burgewa, masallacin ya wuce kai tsaye, kamun a ta da sallah ya dinga gaisawa da jama'a, waɗanda suka san Sadeeq ba lafiya, suka dinga mishi jaje tare da fatan ƙarin sauƙi, dan Sadeeq mai jama'a ne sosai, mutuntawa da girmamawa da kuma gaisuwa su ne tsakaninshi da kusan kowa a anguwar, duk dai wanda suka san juna. Ana idar da sallah, bayan shafa addu'a, Sadeeq ya fito masallaci ya nufi gidan Mama, cikin wannan takun nashi mai kama da na izza da ƙasaita yake tafe har ya isa ƙofar gidan, wanda ke da madaidaicin ƙaramin gate dan motar Umar, da kuma ƙaramar ƙofa ta shiga. Ƙaramar ƙofar Sadeeq ya tura da bismilla ya shiga da sallama a ƙasan maƙoshin shi, sai da ya ɗan tsaya jim a madaidaicin filin tsakar gidan, murmushi yayi cike da kewar gidan da yake ji tamkar shi ne nasu, saboda yadda yake ƙaunar ahalin mamallakan gidan, son da yake yi wa Amininshi Umar, da kuma son da yake yiwa Mama da ya ɗauketa tamkar mahaifiyar da ta haifeshi, waɗannan soyayyar ne suka haɗe suka rikiɗe suka koma ƙauna a kan Sadiya, ƙauna yake yi wa Sadiya irin wadda baki ba zai taɓa iya furta adadinshi ba, shiyasa ya zaɓi yin shiru, domin duk kalmomin duniya ba za su faɗi kwatan-kwacin yadda yake jin ƙaunar Sadiya ba, amma yana da tabbacin muddin Allah ya nufa kuma ya mallaka mishi ita, zai shayar da ita madarar ƙauna da zumar soyayya, zai yi ƙoƙarin fayyace mata dukkan ƙaunarshi a bayyane kuma a aikace, ba tare da ya wahalar da kunnuwanta wajan saurara ba, a jikinta da kuma zuciyarta za ta ji hakan ta kuma yarda ta aminta ya fi kowa son ta. Wani irin murmushi mai taɓa rai Sadeeq ya saki, murmushi irin wadda idan wani aka yi wa, to zai ɗau shekara da shekaru bai mance da murmushin ba, a yanayi na natsuwa da kamewa ya ƙarasa har bakin ƙofar palourn, knocking yayi tare da yin sallama. ⭐️ SADIYA POV Baccinta take yi har aka yi azahar, sai da lokaci ya gota sannan ta tashi, toilet ta wuce kai tsaye ta watsa ruwa sannan ta ɗauro alwala ta fito, mai ta shafa kawai da turare, ta zira dogon riga mara nauyi ta sanya hijabinta ta tayar da sallah, tana cikin sallah Mama ta shigo ɗakin, ganin Sadiyar na sallah sai Mama ta juya ta fice. Sadiya ko da ta idar da sallan, dogon addu'a ta yi sosai tana kuka, roƙon Allah ta ke ya sanyaya wa kowa zuciyarshi, ita dai a barta da Haidar nata shi take so, ba za ta iya zaman aure da Sadeeq ba, ta ɗau lokaci tana addu'a sannan ta shafa tare da lafewa a kan darduman ta kwanta tana mai da numfashin kukan da take yi, yunwa take ji yana nuƙurƙusarta, amma ba za ta fita cin abinci ba, domin ba iya Umma da Abba take kunya ba, har Khausar tana kunyarta, kuma tana tsoron Mama da Yaya Umar tunda ta fi kowa kwana da sanin irin yadda suka ɗauki Yaya Sadeeq nata, "Allah ka mini mafita ka barni da Haidar", ta faɗa cikin muryar kuka, tana nan a kwance a wajan har aka ƙira la'asar, bata tashi ba sai da masallaci suka idar, sannan ta tashi cikin rashin ƙwarin jiki ta tayar da nata sallahn. Mama ko da ta fice a ɗakin Sadiya, samu ta yi ƙanwarta Hauwa Kulu na ƙiranta a waya, hakan ya sa ta ɗauka suka yi magana, ƙanwar tata ke sanar mata suna hanya sun kusa isowa, a iso lafiya Mama ta musu sannan ta katse wayar, ta shige kitchen dan ƙara sanwar dare tunda baƙin yau za su fara zuwa. Bayan Mama ta kammala an ƙira la'asar ta wuce ɗakinta ta yi sallah tare da masallaci, tana idarwa ta shafa addu'ointa, sannan ta miƙe ta fito ta nufi ɗakin Sadiya cikin taƙaicin rashin fitowan Sadiya tun da jimawa, balle ta ci abinci. Da sallama Mama ta shiga ɗakin, yanzu ma samun Sadiya tayi tana sallah kamar dai ɗazu, guntun ƙwafa tayi tare da cewa, "Maza kina idar da sallahn to ki fito ki ci abinci, yunwa dai ba ƙanwata ba ce kuma ba ƙanwar babanki ba", daga faɗin haka Mama ta juya ta fice, dan ta koma ɗaki kar su Najla su mata ɓarna. Knocking na ƙofa Mama ta jiyo, da kuma sallama wanda ba ta jiyo muryar sosai ba, hakan ya sa ta dakata tare da amsa sallamar tana faɗin, "A shigo." *** Sadeeq sai da ya lumshe ido ya sauƙe numfashi, sannan ya buɗe ya tura ƙofar ya shiga da wata sallamar, kan shi a ƙasa. Mama washe baki ta yi kamar gonar auduga, ko wacce aka yi wa bishara da kujerar makka, har ta ma rasa abinda za ta faɗa saboda farin cikin ganin shi da kuma murna. Sadeeq ƙarasawa yayi cikin palourn tare da zama a ƙasa, da haɗaɗɗiyar muryarshi ya ce, "Barka da rana Mamana." Sai sannan Mama ta samu abun faɗa, zama tayi a kujera tana kan murmushi, ta ce, "Ma sha Allahu, alhamdulillah, barka babana, sannu da jiki, Allah dai ya ƙara sauƙi da ƙarfin jiki, Allah kuma ya sa kaffara ne, Allah ya tsare gaba, Allah kuma ya yi albarka mai babban suna." "Amin Ya Rabbi Mama, fatan an wuni lafiya?" "Lafiya alhamdulillahi sai godiya mai babban suna, ni da nake batun zuwa duba ka, sai kuma ka zo da kanka kenan, to Allah ya maka albarka babana." "Amin Ya Rabbi Mama", Sadeeq ya faɗa yana duƙar da kai ƙasa. Mama tana murmushi ta ce, "Tunda mun gaisa ai sai ka tashi ka zauna a sama ko, wannan sanyin ƙasan kuma dama lafiya bata ishe ka ba." "Babu komai Mama", faɗin Sadeeq a taƙaice. Sai da ya numfasa sannan ya ce, "Mama a mini afuwa." Murmushi Mama ta yi, dan ta fahimci a kan me yake nufi, hakan ya sanya ta ce, "Ba komai mai babban suna ya wuce ai, amma dai sam-sam bamu ji daɗi ba har Ummanku, Babana kana da iko da Sadiya yadda Umar ke da iko da ita, amma bamu ji daɗin wannan abinda ka yi ba sam, abu ne wanda ya fi komai sauƙi amma ka mayar da shi mai wahala, abinda ni ya mini rashin daɗin shi ne har kana cikin damuwa a kan haka, amma muka kasa fahimta kai kuma ka kasa sanar mana, duk sai ina ganin laifin kaina da gazawa a matsayin uwa a gare ku, tunda na kasa fahimtar me ke a zuciyoyinku har abu ya kusa lalacewa, amma godiya ya tabbata ga Allah da abun bai ida lalacewa ba, muna da sauran dama, kuma in sha Allah za mu taya ku da addu'a da komai har wannan abu ya yiwu." Sadeeq kan shi a ƙasa ya ce, "Allah ya saka da alkairi Mama, Allah kuma ya ji ƙan magabatanmu, Allah ya tabbatar da abinda yake mafi alkairi." "Amin Ya Rabbi mai babban suna." "Ayoyo big uncle", Najla da Nayla suka faɗa lokacin da suka iso palourn, a shirye suke tsaf dan dama Mama ta musu wanka ta basu abinci ta shiryasu da suka tashi bacci. Sadeeq buɗe musu hannu ya yi suka faɗa jikinshi, sannan ya amsa gaisuwansu har Nayla me gwalanti(tsamin baki irin ta yara masu ƙananun shekaru). Mama gaba ɗaya mancewa ta yi da wata Sadiya, akan bata fito cin abinci ba, hirarsu suka dinga yi da Sadeeq, sai da Najla ta dubi Mama ta ce, "Granny where's mummy and small Mum?" Mama ta ce, "Mamanku tana gidan Abba, Sadiya kuma tana ɗaki." Da Nayla da Najla duk ɗakin suka nufa da sauri wajan Sadiya, sun shiga sun same ta a kwance a kan darduma, Nayla ta kwanta a jikinta tana mata rigima, Najla kuma wajan fiskarta ta je tana leƙawa, da sauri ta ce, "Small Mum you're crying, what's wrong? Did granny hit you?" Sadiya bata ba wa Najla amsa ba, ƙoƙarin tsagaita kukanta ta yi da kuma hawayen, saboda Nayla na ƙoƙarin leƙo fiskarta, ga shi Najla ta kyaɓe fiska, ko kamun Sadiya

Chapter 24 of 32