mai ɗauke da manyan mayatattun idanuwa dai-dai shi, ga dogon hancin shi mai tsayi, ga jajayen laɓɓuna, sannan girar shi a cike take, idanuwanshi wasu irin idanuwa ne masu cike da ƙwarjini da cikar zati, kallonka idan yana yi normal ma sai ka tsargu, balle idan a ce kallon da ma'anar da take nufi, idanuwa ne kaman na zaki kaman na damisa, yana da faffaɗan ƙirji da cikinshi kamamme wanda, ko vest yake sanye da shi kana iya hango 6pack nashi, a taƙaice dai Sadeeq haɗaɗɗene kuma dirarrene maƙura matuƙar lamba na ɗaya.
Sadeeq da kanshi ya lallaɓa cikin rashin ƙarfjin jiki har ya shige toilet ɗin shi kaɗai, saboda ƙarfin hali da jarumta irin ta gwarazan maza, dan da wani lusarin namijin ne ko mace ke jin ciwon da yake ji, to da ko yatsa ba za su iya motsawa ba balle su tsaya a kan diga-digansu.
Sai da ya kama ruwa sannan ya kuskure baki ya ɗauro alwala ya fito, darduman da Umma ta miƙe ya nufa, yana ƙarisawa kai, Umar ya miƙo mishi cup na tea mai kauri da ƙamshi da ya haɗa mishi, sai dai sam-sam ba sugar, saboda Sadeeq ba ma'abocin ta'ammali da abinda ya shafi zaƙi ba ne, a cewar shi zaƙi na illata lafiya da kuzarin namiji, shi kuma bai shirya zama lusari a maganan soshalewa ba(bed thing's).
Yauwa iyaye a kula fa sosai-sosai, wannan yawan bai wa ƴaƴa zaƙi ba gata bane, musamman ƴaƴa maza, duk da su ma matan yana musu illa, amma ga maza ya fi illa, minti, sugar, zuma ko chocolate masu zaƙi ga yara ba wani gata bane, domin zaƙi ba ƙaramin gudumawa yake badawa ba wajan kassara ƙarfi da lafiyar Monster(Sandar girma), sai ku ga mutum ya girma ya zo shi ba basir ba shi ba sanyi ba na a zo a gani, amma duk ya zama sai a hankali, ƴar mutane manage take, to dan Allah abar cutar da bayin Allah, a cuci ɗa a cuci surka, da sayan kayan zaƙi banza-banza wa yara gwanda ko fruits a dinga saya musu ta dai-dai kuɗinsu, a maimakon minti ko wani abun ƙwalaman ta ɗari ko fin haka, ai gwanda ka saya wa yaro Lemu, Mango ko Ayaba, sai ya fi mishi amfani da ƙara lafiya a jiki fiye da zaƙin da ke cutarwa.
Sadeeq kallo guda ya yiwa cup ɗin ya kawar da kai, amma kamun ya ida dai-daita tsayuwarshi Umma ta ce, "Amshi ka sha kamun ka yi sallar, ai ko hadisin Malam bahaushe mai ulcer, a kan ce ci na gaba da sallah, kuma ai banga kuskuren hakan ba, dan akan mutum ya tsaya gaban mahaliccinshi, yunwa na ƙwaƙwalarshi ya kasa yin sallah cikin nitsuwa da dai-daita ai gwanda ya tsaya yayi maganin yunwar tukunna, tunda nitsuwa da dai-daituwa a cikin sallah dai ɗaya ne daga cikin farillan sallah, dan haka hadisin Malam bahaushe na kan hanya, yunwa za ta sa ka yi raka'a uku a matsayin huɗu, ko biyar a matsayin uku."
Sadeeq amsan cup ɗin yayi tare da lallaɓawa ya zauna, dan al'adanshi ce, baya cin abu ko shan abu a tsaye, yana dai bin hadisin da ke ladaftarwa da hani ga shan abu a tsaye.
Sai da ya zauna sannan ya sanya cup ɗin a bakinshi da bismillah, bai sauƙe cup ɗin ba sai da ya kwankwaɗe tea ɗin duka, dan magana ta gaskiya Sadeeq sam-sam baya wasa da maganan cikin shi, da safe ko da rana zai zage ne yayi wa abincin ruf dugu, ci guda gayya, zai ci ne ya cika cikinshi kaman me, amma zuwa dare ba lallai ya sanya abu mai yawa ko nauyi a bakinshi ba, sai kuma wani safiyan ko ranan.
"Ko kai fa, ai a irin cin ka nasan yunwa yana nan ya maka katutu a ciki, sati guda ba ci ba sha sai abinda aka baka ta drip ko na'ura, Allah dai ya raba bawa da wahala, Allah ya ƙara maka lafiya", faɗin Umma tana gyara zamanta.
Sadeeq dai bai ce ko ƙala ba, aje kofin yayi, tare da yi wa Umar kallon da ya fahimci nufinshi, dan bottle water ya miƙo mishi bayan ya buɗe mishi, amsa yayi ya sha a madadin kuskure baki, sannan ya aje goran ya ta da sallah, kaman yanda Umma ta ambaci sati yana a kwance, haka ya lallaɓa ya jera sallahn la'asar na kwanaki shida dan na cikon bakwai ɗin yayi la'asar nashi har isha'i ma, bayan isha'i ne ya faɗi, a daddafe cike da dauriya ya ida sallahn a tsaye, dan jiri yake ji sosai da rashin ƙarfin jiki.
Umma ɗiba wa Sadeeq abinci ta yi, tare da ɓalla masa magun-guna kaman yanda Umar ya gwada mata prescription ɗin, tana kallamawa ta zauna jiran Sadeeq ya ida addu'oinshi, bayan ta ce Umar ya ƙira mata layin Abba.
Sadeeq yana shafa addu'anshi, Umma ta ɗauko plate da ta cika da farar shinkafa da miyar stew da ya ji kifaye ta aje a gabanshi, sannan ta miƙa mishi magun-gunan ya sanya hannu ya amsa, kallo ɗaya ya yiwa plate ɗin ya tabbatar ba zai iya cin shinkafa ba a yanda yake jin ƙirjinshi, hakan ya sanya ya miƙa hannu ya ɗauko bottle water da ya aje, ya watsa magun-guna bakinshi ya bi da ruwa.
Umma cewa tayi, "Sadeeq, abincinfa? Ai kamata yayi ka ci kamun ka sha maganin."
Sadeeq cikin rashin son magananshi ya ce, "Kunu zan iya sha", a taƙaice yayi maganan yana mai lumshe idanuwanshi.
Umar da duk yake kallonsu yake jin su, ƴar murmushi ya saki domin sai yanzu yake jin kanshi dai-dai, lallai Aminin shi ya farfaɗo, kuma da alama da sauƙi tunda ga shi ya fara raba kaɗan daga halayensa na miskilanci, dan daman shi ya sa Sadeeq ba cin abincin zai yi ba dan ya riga ya sha ruwa bayan ya sha tea, a tsarinshi tea kawai yake sha kamun cin abinci, muddin ya sha ruwa to ya ƙoshi da koma menene, ida ya soma shan tea ya ɗuma hanjinshi sai ya kuma cika su da abinci, sannan ya kuma shan ruwan zafin, sai bayan wasu mintuna sannan ya sha ruwa, Sadeeq ba ƙaramin kula da lafiyarshi yake yi ba.
Umar cewa yayi, "Umma layin Abba ba ya tafiya."
"To ƙira mini Mamanku, ko za ta yi kunun ta bai wa direba ya kawo", Umma ta faɗa tana ɗage plate ɗin a gaban Sadeeq.
Umar dialing na layin Mama ya yi, sai da ya kusa tsinkewa sannan aka ɗauka dai-dai ya miƙa wa Umma waya.
Umma na kara wayan a kunnenta ta jiyo sallaman Sadiya a ɗaya ɓangaren, cikin siririyar sansanyar muryarta mai nuni da tana ciki ciwo.
"Wa'alaikissalam Auta, ya jikin naki?" Faɗin Umma cike da kulawa.
Sadeeq jin Umma ta ambaci Auta, a nitse ciki kewanta ya buɗe idanuwanshi tare da ƙure su a kan wayar Umar da ke kare a kunnen Umma, gani yake kaman zai hago fiskarta a wayar,sannan ya baza kunnuwanshi da kyau ko zai samu ya jiyo rantsattsiyar siririyar zazzaƙar muryarta.
⭐️
ALIYU HAIDAR POV
***
Tsaye yake a gaban side na mirror da ke a hamshaƙin ɗakin nashi, sanye yake da ƙananun kaya, tsadaddun riga da wando, ya kammala shirinsa ya gyara kwantaccen baƙin gashin kan shi, wani gawurtaccen ƙamshi kawai ke tashi a jikinshi.
Riƙe yake da p-cap nashi yana ƙoƙarin maƙala agogonsa a hannunshi, yana kammmala maƙala agogon, ya sanya hannunshi guda ya gyara kwanciyar gashin kanshi, sai da ya kalli kan shi da kyau, sannan ya juya, hannunshi guda riƙe da p-cap nashi, ɗaya kuma riƙe da wayarshi, cikin takun ƙasaita da izza da aji ya fice a ɗakin, ko da ya iso main palournsu, samun iyayenshi yayi duk har ƙannenshi a danƙareren dining area nasu, ɗan ɓata fiska yayi dan baya so zama cikinsu da yawa haka, shi ba son yawan hayaniya da surutun ƙannensan nan yake ba....
Maganan Hajiya ne ya katse masa zancen zucin da yake yi.
"Yauwa Haidar ƙaraso mu karya, sanin halinka ya sa ba mu tsaya jiranka ba, Nimra da Husna za su wuce school", Hajiya tayi maganan tana kai cup na tea bakinta.
Haidar tsayuwa yayi har kusan mintuna biyu, dan sai da mahaifinsu da suke ƙira da Alhaji, ya ɗan waigo tare da cewa, "Ƙaraso mana Aliyu."
Cikin aji da isa Haidar ya soma takawa har ya isa dinning ɗin.
Husna ce ta miƙe ta ja mishi kujera da sauri, ba tare da ya ko kalleta ba balle ya ce wani abu, ya zauna fiskanshi a haɗe.
Husna bata zauna ba sai da ta zuba mishi abinda ta san yana so, ta kuma haɗa mishi tea, sai da ta kammala haɗa mishi komai sannan ta koma ta zauna.
Haidar murya ba amo cike da girmamawa ya ce, "Barka da safiya Alhaji."
Murmushi Alhaji ya sakar wa tilon ɗan shi namiji, Aliyu Haidar Zaki, sannan ya ce, "Ka karya tukunna Aliyu."
Jinjina wa Alhaji kai yayi, sannan ya kuma cewa, "Barka da safiya Hajiya."
"Yauwa Haidar, fatan ka tashi lafiya?" Faɗin Hajiya tana aika mishi da kallon da ya san ma'anar shi.
"Alhamdulillah", Haidar ya amsa a taƙaice tare da yin ƙasa da kai ya fara karyawanshi, bai bi ta kan kallon da Hajiya take mishi ba, dan ya san labarin gizo bai wuce na ƙoƙi, dan Husna ta yi serving nashi sai ya mata godiya ko saka albarka, to shi da yake kawo kayan abinci wani lokacin gode mishi ake yi ne? Da nemo abinci da dafawa ai ba haɗi, nemowa ne mai wahala, girkawa da ko a kwance sai a girka....
"Good morning Ya Haidar", kyawawan ƴammatan da ke a dinning ɗin, duka suka haɗa baki wajan gaida shi, Nimra, Nihal and Husna.
Gaisuwan su ne ya katse mishi zancen da yake a zuci, hakan ya sanya ya ɗan haɗe fiska, a taƙaice ya ce, "morning", daga haka bai sake ko ɗago kai ya kalli kowa ba balle ya ce wani abu, karyawanshi yake yi.
Duk kusan lokaci guda suka aje cokula da cup's na hannayensu, dukkansu a dinning ɗin har Haidar da ya zo daga baya yayi joining nasu.
Hajiya tana goge bakinta da tissue ta ce, "Yauwa tunda duk kun gama lokaci ɗaya, sai ku ɗau abinda za ku ɗauka Haidar ya yi dropping naku a school kamun ya wuce, ai fita za ka yi yanzu ba?", ta ƙarishe maganan idanuwanta a kan Haidar.
Haidar ɓata fiska yayi tare da cewa, "Hajiya shi direban nasu me amfaninshi?"
Kamun Hajiya ta ce wani abu, Alhaji ya tari numfashinta ta hanyar cewa, "Nimra and Husna oya go and get ready, direba ya kai ku as usual."
Nihal na murmushi ƙasa-ƙasa ta ce, "that'll be more better for you guys, than ku biyewa Hajiya wai Ya Haidar yayi dropping naku."
Husna da Nimra da suke age mate's kaman twin's, miƙe wa suka yi suka haura sama, da yake a shirye suke already, to mayafi da handbags da read materials nasu suka ɗauka suka sauƙo palourn, sallama suka yiwa su Hajiya sannan suka fice.
Hajiya ce ta bi su da kallo tana murmushi ta ce, "Allah ya tsare mini ku my babies, Allah ya dawo da ku lafiya."
Da, "Amin", Alhaji da Nihal suka amsa.
Nihal ta ɗaura da cewa, "Hajiya ki daina ɗaure wa ƴan biyunki wajan zama da kyau atou, or else they already knew the consequences."
Kallon zan saɓa miki, Hajiya ta bi Nihal da shi, sannan ta ce, "get out of my eye's Nihal, if not i will stand and give you a dirty slap, naga dai yarannan ba abinda suka tare miki ko?"
Nihal na dariya ta miƙe tare da cewa, "Allah baki haƙuri Hajiya, amma ke da ƴan biyun naki ne ai kuke da neman ta da zaune tsaye, Alhaji a dawo lafiya, Ya Haidar a dawo lafiya, my regards to Aunty Sady", ta ƙarishe faɗa tare da barin dinning ɗin tana danne dariyarta, har ta haura sama ta wuce ɗakin da yake nata, sannan fa ta kwanta a haɗaɗɗen gadonta ta dinga dariyanta, she see no way da Hajiya za ta ke forcing Ya Haidar akan Husna, though she's supporting the fact that ya auri Husna tunda cousin ta su ce, but that's not mean everything has to do with force, love is love if he loves her or he'll loves her in future, nothing can change that, and if he doesn't love her and he'll forever not love her, force can't change that, Allah ya kyauta kawai ya sa Hajiya ta gane gaskiya, a fili Nihal ta ce, "Anyway I like Aunty Sady tun da Ya Haidar na son abarsa, Allah tabbatar da alkairi."
Hajiya ƙwafa tayi bayan Nihal ta bar dinning ɗin, sannan ta dawo da idanuwanta ga Haidar, shi ma nashi rabon na kallon ta aika mishi, sannan ta ce, "Haidar keep on doing the hell you're doing don't stop, but I want you to know one thing Husna dai sai ka aureta ko ka ƙi ko ka so, kai ko mutuwa nayi sai ka aureta in sha Allah, even death can't stops you from marrying Husna, yarinya ƴar marainiya kuma ƴar uwanka shaƙiƙiya, she care's about you alot and duk abinda ya dame ka ya dame ta, kullum ƙoƙarin yarinyar nan ta faranta maka ta yi ɗawainiya da kai, but you that you're not leaving with soft and kindest heart like normal Humans leave with, da yake zuciyar mutanen baya gare ka, to ko sau ɗaya ba za ka tausashi zuciyarka a kanta ba,you can't look with pity to her, to tun wuri in za ka tausashi zuciyarka ya fi maka ka taushi zuciyarka, dan auran Husna ka yi ka gama, kar ka ga na ɗaga maka ƙafa saboda shirmen soyayya ya rufe maka ido, to ka gama shirmen ai ana auran shikkenan ko? So you most marry Husna....", faɗan da take yi ne ya katse saboda dakatar da ita da Alhaji yayi.
Ta hanyar cewa,"Hajiya what is is this? If i could remember, na dakatar da ire-iren waɗannan maganganun ko? How comes soyayya ne shirme? Ai da soyayya shirme ne to da ke da kanki ba kya a gidana, so i don't like this blaa blaa you're saying, tunda mun gama magana zai aureta daga baya to da Allah ki bar mini yaro ya ji da abubuwan da suke gabanshi tukunna, leave my son to rest and have peace", cikin faɗa-faɗa Alhaji ya ƙarishe maganan.
Sai da ya numfasa sannan ya kuma cewa, "Aliyu Haidar get to the palour and wait for me their, i have something to talk on it with you."
Haidar miƙewa yayi fiska ba yabo ba fallasa ya bar dinning area ɗin, a palourn ya samu waje ya zauna tare da ciro wayarshi, ganin lokaci ya tafi ƙarfe taƙwas ya gota har ana neman ƙarfe tara, layin Sweet Al-Sad ta shi yayi dialing, ko zai ji muryanta ya ji dama-dama na tafarfasar da zuciyarshi ke mishi, cause he's madly upset, Hajiya tana making nashi to hate's that stupid girl more, it's most to marry someone you don't have any feelings over him? Or it's most to marry two wives while you totally knows that ba za ka iya adalci a tsakaninsu ba, and that can lead you to face hukunci wajan Allah, wa zai so ya tashi incomplete a gaban mahaliccinshi?, "probably not me", faɗin Haidar a fili, with soo much annoying in his face.
Alhaji da ido ya bi Haidar har ya bar dinning ɗin, sannan ya juya ga Hajiya ya soma faɗa, "Aisha za mu samu damuwa da ke idan kika ce za ki takurawa yarona, ke wa ya miki dole? Auran soyayya muka yi sannan muka rayu cikin aminci bisa yarjewan Allah akan tsarinmu, shekaru talatin da shida muke nema da aure, akwai wanda ya matsa na miki kishiya? Ko ni na yi maganar yi miki kishiya? To wallahi tun wuri ki iya bakinki ki kama girmanki, idan kika bari matar da Aliyu zai aura ta ji fatan abokiyar zama kike mata tun bata shigo ba, to ba lallai ku shirya ba, kina da kishi kin san irin kishinku na mata, kuma kika zama surkuwar zamani to Allah zai haɗa ki da surkar zamani dai-dai ke, ki daina takurawa yaron nan, nayi magana da shi ya amince ba damuwa zai auri Husna daga baya, to idan kika matsa mishi zai iya sauya ra'ayi, ya kuma tsani ƴar uwanshi bisa ga takurarki, kina da sanin cewa ba a cusa wa mutum soyayya a dole ko? To ki bi komai a sannu ki bi lamura a hankali."
Hajiya ɓata fiska tayi tare da cewa, "Alhaji kai dai bayan ɗanka kake bi, ni kuma bayan yarinyar ƴar uwata nake bi, Haidar sai ya auri Husna in sha Allah, shi ne kawai."
"Allah ya shiryaki Aisha, sam-sam kin girma ma ba za ki sauya halinki na kafiya da ina faɗa kina faɗa ba, sannan ba za ki buɗe zuciyarki da kyau ki fahimci komai ba, Allah ya kyauta", iya haka Alhaji ya faɗa, sannan ya miƙe ya bar dinning ɗin, zuciyarshi sam ba daɗi, wasu abubuwa idan Hajiya tana yi mamaki take bashi, yaranta fa mata ne, idan ana musu abinda take ina za ta ji daɗi, Allah kawai ya dube shi ya kare masa yaranshi, ya shirya mishi matar shi, daman wannan a kullum shi ne daily du'a ɗin shi.
Haidar ya ƙira layin Sadiya ya fi sau abinda ya fi amma ba a ɗauka ba, gaba ɗaya hankalinshi ƙara ɗugunzuma yayi ya ƙara tashi, jiya lafiya-lafiya suka yi waya da ita akan yau za ta asibiti dubo Yaya Sadeeq, to ko dai sun je ne? Kar dai fa wani abu ya same ta, "Ilahi Rabbi!", ya furta yana dafe kan shi tare da busar da iska mai matuƙar zafi a bakinshi.
"Aliyu Haidar", Alhaji ya ƙira sunanshi yana zama a gefenshi, hakan ya sanya shi ya ɗago, cikin damuwa, ko da Alhaji ya ga haka ya ɗauka lamarin Hajiya ne, hakan ya sanya shi yin murmushin ƙarfafa guiwa tare da cewa, "In Allah ya amince, kuma muddin akwai alkairi a ciki, to nan da ƴan kwanakin da suka rage za ka mallaki Halimatu Sadiya, don't bother yourself about what Hajiya said, we've already talked on it with you right?, daga baya za a duba lamarin ƙanwarka Husna."
Haidar jinjina kai kawai yayi, tare da amsawa da Amin a zuciyarshi, he's just eager kwanakin da suka rage su ƙarato, gaba ɗaya tun da auren ya matso yake jin wani iri da yawan faɗuwan gaba, ya kuma tabbata idan ba ganin Sadiya yayi a gidanshi ba he won't totally be in peace, rigingimun Hajiya da wasu al'amuran da suke giftawa are giving him too much of headache, abinda ba ya shiga tsakaninshi da Sadiya a kwananin nan sai giftawa yake, sai ya mata ƙira kusan goma bata ɗauka ba, me ke shirin faruwa ne?
Alhaji ganin Haidar yayi shiru bai ce komai ba, numfashi ya sauƙe tare da taping na bayanshi cikin lallashi da son kwantar mishi da hankali, cewa yayi, "Aliyu Haidar, ka bar barin ƙananan abubuwa suna damunka har su sha maka kai, kayi addu'a da fatan alkairi kawai, duk abinda yake a rubuce kuma alkairi gare ka to zai iskeka da yardan Allah."
Jinjina kai Haidar yayi gami da sauƙe ajiyan zuciya, sannan ya ce, "In sha Allah Alhaji."
"Yauwa yaron kirki, Allah ya muku albarka duka, Allah ya kuma nuna mana bikinnan da rai da lafiya, ka ga ma sai aukin sanar da jama'a nake da baki, kuma ka san akwai mantuwa, ya kamata a week ɗin nan ayi preparing IV, saboda kar ya zama mutanenmu su mance date ɗin, ranar ya kasance sun yi scheduling wani abun, amma idan ya kasance mutum na tare da IV to zai ke tunashe shi, kuma koma menene zai yi ƙoƙari ya ga ya samu ƴar ƙafa ta zuwa halartan ɗaurin auren", Faɗin Alhaji.
Haidar jinjina kai yayi tare da cewa, "In Allah ya yarda zuwa gobe zan ji da wannan, yanzu dai dama zan je batun kayanmu da suka iso daga China ne."
Murmushi Alhaji yayi ya ce, "Allah ya maka albarka Aliyu, shikkenan ka hutacce ni, sai na samu na huta gajiyan Cairo, dan zaman jirgin nan ba ƙaramar shungulla bace, sannan mutum idan ya je ba zama yake yi ba kayi nan ka yi can."
Haidar ɗan taune leɓenshi yayi da ƴar guntun murmushi ya ce, "Alhaji shiyasa na ke cewa ka zauna ni sai naje ƙasashen wajan batun kayakin."
"A'a Aliyu, ai da kula da company, da jigile da daga garinnan zuwa wancan, da lissafe-lissafe ai sai kai ɗin, nikam da shekaru suka ja suka tafi ai sai su ƙarasa ni, gwanda dai na fama da zuwa ƙasashen wajen, tunda in na je ina buɗe ido da sauransu, in samu kuma nayi nishaɗi na sha iska da kyau, kai dai ka cigaba da ayyukan da kake yi, Allah ya dafa maka ya maka albarka, Allah ya sa wacce za ka aura ta zame maka tagari kuma alkairi, and may she be your Safe Place also your ComfortableZone."
"Amin Ya Rabbi, Allah ya ƙara lafiya ya ja kwana Alhaji", faɗin Aliyu da ke ƙoƙarin miƙewa, cause he got soo much releif on what he feels about maganganun Hajiya.
Alhaji na ƴar dariya ya ce, "Au wai ko kunyata ba ka ji? Shikkenan ai, Allah ya sa ta kula mini da kai sosai."
Haidar da murmushi ya miƙe tare da gyara shirt nashi, p-cap nashi na riƙe a hannunshi har yanzu, yana murmushin maganan Alhaji ya fice a palourn.
Alhajinshi kenan, mahaifinshi kuma abokin rahan shi, yana ƙaunar mahaifinshi sosai fiye da lissafi, saboda mahaifi ne na gari na ƙwarai kuma abun alfahari.
Arniyar haɗaɗɗiyar motarshi ya shiga ya mata key ya kama hanya, duk wata mota da za ta fito sabon yayi kuma tsadaddiya, to Haidar yana cikin jerin matasan da suke fara mallaka, saboda su ɗin suna da kumban susa, kuma a cikin harkokin business nasu shi da mahaifinshi, har da shigo da motoci.
Cool music yayi playing na Gyakie mai taken Forever, cikin aji yake tuƙin yana kuma bin waƙar, wanda in ka ji a bakinshi ka ce shi ya rera, yana bin waƙar ne cikin nishaɗi da kewar sweet Al-Sad, saboda duk zai yi playing wannan waƙa, he feels like she's by his side at that moment, shiyasa yake tsintar kanshi cikin shauƙi.
Alhaji yana ganin ficewan Haidar ya miƙe ya shige ɗakinshi dan ya huta, saboda jiya-jiya dawowanshi daga Cairo.
Hajiya kuma masu aiki ta ƙwala wa ƙira, sanar da su abinda za su girka na rana tayi, sannan ta miƙe ta mara wa Alhaji baya, masu aikin kuwa sai da suka tattare dinning ɗin, sannan suka wuce kitchen dan fara shirye-shiryen yin abinda Hajiya ta faɗa.
Hajiya da sallama ta shiga ɗakin, dai-dai Alhaji na rage kayan jikinshi, ƙarasawa tayi tare da kama mishi ta taya shi, a bakin haɗaɗɗen gadon nasu ya zauna, cikin gajiya da son ya samu ya huta ya ce, "Hajiya Aisha is there anything again?"
"Am so sorry Alhaji, pardon me please", faɗin Hajiya with soo much expression that reveals the love she has for her husband.
Ƴar murmushi Alhaji yayi tare da cewa, "Komai ya wuce, Allah ya miki albarka ke da yaranmu."
"Amin Alhajina", Hajiya ta faɗa tana murmushi.
Alhaji gyarawa yayi tare da kwanciya da bismillah, sannan ya ce, "love is not rubbish as you said, domin shi ya haɗa ni da ke har Allah ya bamu su Aliya har zuwa kan Nimra, dan haka ki sakar wa yarona mara, yanzu maganan lefe nake son a kai a week ɗin nan if he prepare the IV."
"In Allah ya yarda, yanda ka ce haka za a yi Alhaji."
"Ma sha Allah, bari na taɓa bacci na samu na huta, cause am super tired."
Hajiya a tashi lafiya ta mishi, tare da miƙewa ta fice ta ja mishi ƙofa, ɗakinta ta wuce ta ɗau wayarta ta aika wa layin ƙanwarta da suke business na zannuwa da sauransu ƙira, suna haɗa kayan aure ga duk customern da ya so, kuma kayakinsu akwai kyau da inganci sai dai akwai kuɗi, dan dama lamari ne na kuɗi, abu mai kyau siyen kanshi yake.
***
Za ku iya samun littafin a wannan manhajoji.
BAKANDAMIYA HIKAYA.
AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
WHATSAPP
09161720046
a kan Naira #500.
Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah.
# Hareeyh
# 09161720046
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 32