Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta sani, amma dai ba inda za ta, ya gama faɗa ya wuce ɗakinsa, hannunsa riƙe da cup da ya haɗo tea, dan ya samu ya je ya sha ya shirya fita office tunda Abba na hutawa bai kamata duk su zauna a gida ba wanda ya je ba. Sadiya kuma tana kukanta ƙasa-ƙasa ta shige ɗakin Umma, wayan ta ɗauka tare da aikawa layin Haidar ƙira, bai ɗauka ba ya katse ya biyo ƙiran, tana gani ta ɗauka tare da fashewa da kukan shagwaɓa, hankali tashe a ɓangaren Haidar yake tambayarta me ya faru? Ya aka yi? Wani abu ya samu Yaya Sadeeq ɗin ne?, sai duk ta girgiza mishi kai tare da faɗa masa, su Umma ne suka tafi asibiti suka barta wai saboda tana waya kuma saboda bata son asibiti, cikin kukan ta ɗaura da cewa, "Amma ai Zakina idan kai ne a asibiti ko Mama ko Umma ko Abba ko Yaya Sadeeq ko Yaya Umar ai zan je ko?" Shiru tayi jim kaɗan alaman tana sauraran abinda Haidar ke faɗa. Yana gama maganansa ta jinjina kai tare da cewa, "Yo ai lokacin Yaya Khalid ne ba lafiya shiyasa naƙi zuwa, kuma ko Yaya Sa'ad ne ba zan je ba, amm ai idan ku da na lissafa ne dole naje ko zan mutu, nidai kawai ka zo ka kai ni asibiti na dubo Yaya Sadeeq." Haidar a ɓangarensa ajiyan zuciya ya sauƙe tare da aikin rarrashi kawai, yana ɗaya daga cikin abinda ke ƙara masa ƙaunar Sadiya, rigimarta da shagwaɓarta, ga shi kuma takan ji rarrashi, sannan Yaya Sadeeq ne da Umma suka shagwaɓata a yanda ya fahimta. Sai da ƙyar Haidar ya shawo kan Sadiya, a kan yanzu zai je yiwa Alhaji wani aike, sai zuwa anjima zai zo ya ɗauke ta su tafi asibitin, daga haka kuma ta yarda suka yi sallama bayan kalaman soyayya da ƙauna da suka yi musaya, masu matuƙar taushi da ratsa zuciya da gangar jikin masoya, bayan sun yi sallama a wajan Sadiya ta ɓingire ba jimawa baccin da bata samu yi jiya ba yayi gaba da ita. Umma da Mama direba ne ya kai su asibitin, ko da suka isa Khalid ne ya zo ya musu jagora har sashin da suke da Sadeeq, Umar cikin girmamawa da biyayya, ya gaishe da iyayen nasa duka Umma da Mama, suka amsa tare da tambayar mai jiki, Umar fiska ba yabo ba fallasa ya sanar musu jiki da sauƙi Alhamdulillah, likita bai jima da baro wajan Sadeeq ɗin ba, har da ƴar guntun murmushi na yaƙe ya saki tare da cewa, "Likitan ya ce bakomai yanzu farkawansa kawai za a jira." Umma da Mama ajiyan zuciya suka sauƙe tare da masa fatan farkawa lafiya, Khalid ne ya ja basket ɗin ya fara zuba wa kannsa abin da zai sanya a cikinsa, Umar kuma wucewa yayi su Umma suka rufa masa baya har ɗakin da Sadeeq ke a kwance, hancinsa maƙale da oxygen da kuma wasu na'urori jone a ƙirjinsa waɗanda suke daga wata ƴar na'ura kaman computer, sannan an ɗaura masa drip yatsansa na hannu mai drip ɗin da ɗan wani abu kaman pil a maƙale. Umma da Mama duk suna ganin yanayin da Sadeeq yake ciki a kwance kaman ba shi ba, duk sai jikinsu ya kuma sanyi, kaman ba Sadeeq ingarma jarumi kuma dirarren namiji ba, lallai a duniya mutum bai da maƙiyi irin ciwo, duk ƙiyayyar da maƙiyi zai maka muddin ba zai iya ɗaura maka ciwo ba to da sauƙi, ƙiyayyarsa bata cika ƙiyayya ba, sai fatan Allah bai wa marassa lafiya na gida da asibiti lafiya. Umar cikin dabara ya nusar da su Umma komai, ya kuma ɗaura da tunatar da su komai daga Allah ne kuma sai sanda Allah ya so, hakan ya sa ba su ɗaga hankalinsu sosai ba duk da suna a dame, har azahar suna nan, sai da suka yi salla sannan Umar ya ce su koma gida su huta kawai, ba musu Mama da Umma suka shige mota har da Khalid, direba ya ja su sai gida, suna tafe a hanya Umma da Mama a baya, Khalid a kujeran gefen mazaunin direba, Umma ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa, "Ai gwanda da bamu taho da auta ba, da yanzu haka wani zancen ake ba wannan ba." Mama ƴar murmushi tayi tare da cewa, "Na rasa irin ƙiyayyar dake tsakanin Sadiya da asibiti." "Ai da ta wannan ne ma da sauƙi, da anzo da ita ta kalli abubuwan da ke jone a jikin Yaya Sadeeq nata ai da an samu akasi", faɗin Umma. Mama cewa tayi, "Tabbas da ita ma may be ta kama jinyar, wannan ƴa da Yayan nata ina ji ai sai dai a haɗe su a kai su gidan Aiyun tare." Umma murmushi tayi mai kyau tare da cewa, "Aikwa dai da abu bai yi kyau ba sam, amarya da jinya ina abu ya haɗu, aka kuma kai Sadiya da Sadeeq gidan Aliyu ai a ranan zai fatattako su duka." Mama ƴar dariya tayi tare da cewa, "Allah dai ya tashi kafaɗun mai babban suna, ya kuma nuna mana bikin da rai da lafiya." "Amin Maman Sadeeq, dan aka yi auren auta babu Sadeeq ai na tabbata ba zai sake kulamu ba duk fushi zai yi da mu, dan inaga wani abun na Sadeeq ya mayar da auta kaman ƴar cikinsa, kaman shi ya haifar mini ita." Mama dariya tayi tare da addu'an alkairi da fatan sauƙi ga Sadeeq, tare da na alkairi ga su Umma na karamcinsu gare su, Umma ta girgiza kai kawai ba komai ai an riga an zama ɗaya. A ƙofan gidan su Umar direba ya fara tsayuwa, Mama ta sauƙa ta shige madaidaicin haɗaɗɗen gidansu, sannan direba ya wuce da Umma nasu katafaren gidan, ko da Umma ta leƙa ɗakinta, samun Sadiya tayi har lokacin tana bacci, ja mata ƙofa tayi ta wuce ɗakin mijinta, tarar da Abba tayi dai-dai lokacin ya tashi, sannu da tashuwa ta masa shi kuma ya amsa ya mata sannu da dawowa, tare da tambayarta jikin Sadeeq, ta amsa da sauƙi, addu'an Allah ƙara sauƙi yayi sannan ya miƙe ya wuce toilet, ruwa ya watsa sannan ya ɗauro alwala ya fito, a ɗakin yayi sallahnsa, yana idarwa ya shirya a gaggauce, tare da Umma suka sauƙo ƙasa, abincinma sama-sama ya ci, yana kammalawa ya mata sallama ya fice, saboda yana da meeting da wasu baƙi abokanan kasuwancinsu daga ƙasar waje, ga kuma za a kawo mai a gidan mansa da yake kula da shi, kuma yana son zuwa asibitin ya dubo jikin Sadeeq ɗin. Umma sai da ta kammala sannan ta wuce sama, ɗakinta ta koma ta tashi Sadiya, ba jan magana Sadiya ta wuce ta ɗauro alwala ta fito ta tayar da sallahnta, sai da ta idar sannan Umma ta ja hannunta zuwa ɗakin da suke abubuwan gyaran jiki da sauransu, Umma soma dirje Sadiya tayi tana turarata, tana kule da yanda Sadiya ke cunna baki alaman fushi, kuma tasan ba zai wuce a kan an tafi asibiti an barta bane, hakan dai bai sanya Umma ta ce mata komai ba, ci-gaba da mata abubuwan da suka dace tayi har zuwa la'asar, sannan ta haɗa mata ruwan ɗumi mai turaruka iri da kala ta wanke jikinta ta ɗaura alwala, duk sallan la'asar ɗin suka yi, Sadiya ta wuce ta cika wa kanta ciki da fruits da yaji haɗi, daman ita ba gwanar cin abinci sosai bane, musamman da yamma ko da dare, gwanda da safe da kuma rana idan ba za ta kwanta ba, to tana cin abinci sosai kuma mai nauyi. # Hareeyh # 09161720046 # 08146334243 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: 💔NAUYIN BAKI....👄💔 Na Uwar Batoorl. ***MASU TALLA ƘOFA A BUƊE TAKE, KU HANZARTA DOMIN AYI INGANTACCIYAR TAFIYARNAN DA HAJARKU, KU KAWO TALLANKU CIKIN AMINCI A TALLATA MUKU SHI CIKIN ANNASHUWA DA SHAUƘI, KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAMBA 09161720046.** 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠 اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 WANNAN PAGE NAKI NE. Waleedah graphic, madallah da ke, Allah ya saka da alkairi. 🅿️ 11 _ 15 ⭐️ Sai goshin magrib sannan Sadiya suka kuma waya da Haidar ya shaida mata yana hanya, hakan ya sanya ta sanar da Umma, sannan ta shirya cikin riga da skirt na leshi ruwan ɗorawa(yellow), ba ƙaramar karɓan kalar fatarta yayi ba, saboda ita Sadiya ba za a sanyata a layin farare tass ba, haka kuma ba za a sanya ta a jerin masu duhun fata ba ko da kuwa chocolate color ne, fatarta bai da duhu tana da haskenta dai-dai, amma ba fayau ba. Sadiya kyakkyawar matashiya ce mai kimanin shekaru goma sha takwas da haihuwa, ƙiranta ƙira ne irin ta manyan mata, domin ita ba siririya sosai bace, ƴar duma-duma ce kuma tana da dukiyar fulaninta dai-dai jikinta, haka ƙugunta cikansa da bajewansa ya tafi da yanayin jikinta, domin idan ka kalleta ka rantse ta haura shekaru ashirin, duk da halayyarta da sangartarta za su tabbatar maka a sha takwas ɗin take, ko kayi tunanin bata ida kai wa hakan ba ma. Sadiya tana da tsayi mara hayaniya wanda ya ƙawata dirinta da kyawunta, idanuwanta farare ne tass haka baƙin ciki ma baƙine wuluk, hancinta bai cika tsayi sosai ba, amma ba za a ƙirata mai yankakken hanci ba, lip's nata ya dace ƙwarai da kalar fiskanta, domin irin lip's da suke nan peach da zanen baƙi a ƙasansu ne sama da ƙasa, da yawa waɗansu a yanzu sukan yi aiki da lipstick da kajol dan su fenta laɓɓunsu irin haka, musamman ga ma'abota cuɗanya da manhajar tiktok, amma ita Sadiya naturally haka Allah yayi mata lip's nata, shiya take da sansanyar kyau matuƙa, a kallo guda idan ka mata za ka gane tana da kyau dan kyakkyawan ce, amma a kallo guda baka kalli ko rabin kyawunta ba, sai ka tsura mata idanuwa za ka tabbatar da irinsu ake cewa, ko ba kwalliya suna da kyau, saboda Allah yayi halitta ƙwarai ma sha Allah, ko ita da kanta aka ce ta halicci kanta, to ba za ta yi kyau kamar haka ba, dimple take da shi gefe guda, ga tambatsetsen wushiryanta da idan ta murmusa kaman ta dauwama a haka ana kallonta, gashin girarta sun cika sosai har sun haɗe a ɗan sirrance, gashin idanuwanta kuwa zara-zara suke kaman wacce ta ƙara da na shago, amma haka abinta yake daga Allah, tun daga gashin da ke kwance a sajenta da gaban goshinta zai tabbatar maka da ita ɗin mai gashi ce, tana da tsayin gashin kai da cika duka, wanda ya sauƙa har bayanta, gashin kuma akwai laushi, domin sanadin laushinsa har kusan kwatan gashinta yayi farin gashi( furfura), dama shi furfura abubuwa uku zuwa huɗu ke kawo shi, laushin gashi na kawo furfura, wahala da rashin nitsuwa na kawo furfuwa, akwai furfura ta baiwa, sannan furfura na stufa wanda idan lokaci yayi, wasu kamun su koma ga Allah ba za ka tsinci baƙin gashi ko guda ɗaya a kansu ba duk ya koma fari, yawan tsinkewan zuciya na damuwa ko wata fitinar ita ce musabbabin fara kawo furfura, kamun mutum ya gama tsufa duk gashinsa sun koma farare, Rabbi ka jiɓanci lamuranmu ka iya mana a ko ina a ko wanni mataki, duk masu damuwa Allah ka yaye musu, masu buƙata Rabbi ka biya musu ka sa mu dace duniya da lahira alfarman Annabi SAW. Saboda fari da gashin Sadiya yake yi ya sanya Yaya Sadeeq nata ke sanya mata baƙin dayis a kanta, Sadiya kyakkyawa ce sosai-sosai, idan muka ce za mu cigaba da zayyano haɗuwanta to za mu ɗau lokaci mai tsayi a kan hakan. Tana gama sanya leshinta ruwan ɗorawa, ta naɗe gashin kanta da ke a kunce ta kame da ribbom sannan ta ɗan lanƙwasa shi, ɗauri tayi irin wanda ke zama a goshi ya fito da gashin mutum ta ƙasa, ɗaurin kuma ya amshe ta matuƙa, sannan ta sanya hijabinta zumbulele har ƙasa(kin kwafsa mana Sadee🤌wannan kwalliya ina laifin mayafi😂). Takalmi flat ta sanya, sam-sam bata sanya turare ba, domin wanda ke tashi a jikinta yanzu ma, dan ba yanda ta iya ne da ba za ta je ga Haidar da ƙamshin a haka ba. Tana fitowa da Umma ta ci karo a palourn, Umma na murmushi ta ce, "Ma sha Allah, Halimatu ta Haidar in sha Allah, irin wannan kyawu haka Auta, kaman fa irin kun zo gaishe da mu da angon naki, irin kin fito za ki bi shi ku koma gidanku, kar fa idan kika fice mu neme ki mu rasa ya ɗauka tare da shi kuka zo." Sadiya ƴar guntun murmushi tayi da ya bayyana dimple nata da wushiryanta, matuƙar kyau ta yi duk da ba asalin murmushi ne wanda ke daga zuciyarta ba, dan indai Yaya Sadeeq zai yi ciwo to tabbas bata da nitsuwa har sai ya samu lafiya, yanzu kuwa abun da yawa ya taru mata ga shi an ƙi zuwa asibiti da ita kuma bata san wanne asibiti bane aka kai shi. Umma ganin Sadiya ta tsaya bata tafi ba, kuma bata ce komai ba, sai murmushi ne kwance a kyakkyawan fiskanta, wanda Umma take da tabbaccin murmushin yaƙe ne, cikin sigar tsokana hallau ta ce, "Auta maza a je a dawo da wuri kinsan wannan zancen daren an hana ki, Allah ma dai ya nuna mana ƴan kwanakin da suka rage da rai da lafiya, muyi mu miƙa ki, shi ma ya huta da sintirin kai wa da kawo wa." Sadiya cunna baki tayi kawai ta fice a palourn, kai tsaye parking lot ta nufa, dan daman ko da yaushe ya zo nan ne wajan hiransu a sarari, kuma yana isowa ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan zai kawo mishi plastic chair's, Haidar ya zauna ya jiranyi fitowan sarauniyar ta shi. Yanzun ma hakan ne kaman ko yaushe, tana fitowa haraban gidan, ta hango sa zaune inda suka saba zama, ɗan tsayawa tayi na ƴan sekonnni idanuwanta a kansa, banda murmushi ba abinda take saki, wani irin ƙaunarsa da soyayyarsa ke ƙara dulmiyeta duk sanda za ta yi tozali da shi, ko kuwa za ta ji haɗaɗɗiyar muryarsa, ji take ba lallai ta iya rayuwa ba Haidar ba, domin soyayyarshi ya zame mata tamkar numfashi, lallai in babu Haidar a rayuwarta to rayuwar bata da ma'ana balle amfani. Sai da ta gama tsayuwan sannan ta fara takawa cikin tafiyarta mai ɗaukan hankali, cikin nitsuwa da salo wanda wasu ke masa kallon rigima, amma ga waɗanda suka san Sadiya, to tabbas sun san asali haka tafiyarta yake tun tana ƴar tatsitsiyarta. Ɓangaren Haidar tun kamun Sadiya ta iso ya mace da murmushin da ke kwance a fiskanta, Sadiya kyakkyawa ce kuma murmushi na mata kyau, murmushinta na kunce masa lissafi wataƙila shiyasa take yawan masa dan ta ci-gaba da sanya shi yana matowa kan ƙaunarta da ya jima da yin nisa, domin in har za a ce soyayyar Sadiya mafarki ne a gare shi, to har ranar ƙarshe baya fatan ya farka daga wannann mafarkin, Sadiya duniyar soyayyar shi ce. Sadiya na ƙarasowa, Haidar ya gyara mata kujeran da za ta zauna, sannan ya miƙe tsaye kyawawan idanuwanshi na jefinta da kallon ƙauna mai narka zuciya masoyiya, da tausasshiyar muryanshi ya ce, "Barka da fitowa ranki shi daɗe amarya mai jiran gado." Sadiya da sauri ta sanya tafin hannayenta duka biyu ta rufe fiskanta tana tura baki, sai da ta zauna sannan ta ƙara cunna bakin kuma har sannan hannayenta na rufe da fiskanta. Haidar ƴar murmushi yayi mai aji sannan ya zauna bayan ta zauna, ɗan ƙasa-ƙasa yayi da murya ya ce, "My Al-Sad Amarsu ta ango." Sunan da Haidar ya ambata shi ya sanya ta sake faɗaɗa kyakkyawan murmushinta, wannan kam daga zuciya ne, domin ya ambaci suna mafi soyuwa a gareta, sunan da ta zauna ta dinga lissafi da nazari har ta haɗa abinta da kanta, Al-Sad, Aliyun Sadiya ko kuwa Sadiyan Aliyu. Idanuwanta ta ɗan kawar gefe saboda kunyansa na zolayan da ya tsiri mata tun da aka sanya ranan bikin nasu, a shauƙance ta ce, "Fatan Zakina ya iso lafiya? Ya aka baro su Hajiya da su Nimra?" "Na iso lafiya Alhamdulillah Zakanyata, su Hajiya da yarannan duk suna lafiya, sun ce na gaidaki." Sadiya wani irin juya idanuwanta tayi tare da yi masa wani kallon love me sanya numfashi ɗaukewa, bakinta ta ɗan ɗana irin bata so fa, ta kuma cewa, "Ba wata Zakanya, ni a ce da ni sunana kawai." Aliyu Haidar mutum ne da bai cika son surutu ba ko kuwa magana ɗaya biyu har uku da mace, amma a kan Sadiya za ka ɗauka shi parrot ne, idan yana hira da ita mancewa yake da wani rashin son yawan magananshi, mancewa yake da ajinsa da komai indai yana a tare da Sadiya, a zahiri ko a waya. Cikin zolayarta ya ce, "Indai Aliyu Zaki ne, to Sadiyarsa Zakanya ce." Rigima Sadiya ta fara, aikin lallashi ya ga Haidar, domin daga haka ta ɗaura da rigimar zuwa asibitin da ba a je da ita ba, ga shi shima Haidar ɗin bai zo da wuri ba, lallashi dai ya yi dole, yana tambayanta wani asibiti aka kai shi sai su je tare, Sadiya tana taɓune fiska cikin shagwaɓa ta ce bata so, tunda bai zo da wuri ba ita ba inda za ta bi shi, za su je tare da Abba. Da ƙyar dai Haidar ya lallashi Sahibarsa, da muggan kalaman ƙauna da ta soyayya, har dai ta haƙura aka koma murmusawa. Ganin ana ƙiraye-ƙirayen magrib ya sanya Haidar ɗan rusunar da kai, cike da salon soyayya irin ta Sarki ga Sarauniya ya ce, "Idan ranki shi daɗe ta amince mini, ta mini izini, fatan zan iya tafiya?" Murmushi mai zurfi da kyau Sadiya ta yi, a duniyarta salon Haidar da ƙaunarsa suna burgeta, suna sanyata shauƙi matuƙa, tana jin kanta ta daban, irin ta fi ko wacce mace sa'a da dace, tana jin ba wacce take samun ƙauna da kulawa da salo irin wanda take samu daga Haidar, hakan ke ninka mata ƙaunarsa ta ji ba za ta taɓa iya bai wa wani namiji dama ba bayan shi, tunda Haidar ya sace zuciyarta, shikkenan ta daina kallon sauran maza a wasu abun zuwa gabas. Haidar sake maimaita neman izinin tafiya yayi, sai sannan ta ɗan tsagaita murmushin ta shagwaɓe fiska, da siririyar muryanta ta ce, "Wai tafiya tun yanzu?" "Eh Sarauniyar duniyata da zuciyata, amma fa sai kin amince", ya ƙarishe faɗa yana rusunar da kai, alaman abinda dai take so shi za a yi. Sadiya langwaɓar da kai tayi ta ce, "Nidai bana so ka tafi, Allah ni ban gaji da ganinka ba Al-Sad, kawai ka fasa tafiyan." "Nima banason in tafi a karan kaina, nima banƙi mu dawwama haka ina kallon kyakkyawan fiskanki mai sanya ni nistuwa da farinciki ba, ina kuma sauraran muryanki da ke kore mini damuwa da gajiya, ke ɗin tamkar maganin da ake ƙira antibiotics ne a rayuwata, kina kore komai kina maganin cutuka da dama, my Al-Sad ba za ki taɓa fahimta ko gane adadin ƙaunar da nake miki ba, sai ranar da hijabin shingen da ke a tsakaninmu ya yaye, igiyuna suka zamana a kanki, zan tarairayeki, zan shagwaɓaki fiye da yanda kike, zan so ki na ƙaunace kuma zan zauna da ke a ko wanni hali, zan cigaba da mayar da ke Sarauniya har ki ƙere wa sauran mata, ki zama ta daban a cikin dubunni, and zan tabbatar a sanda kike a gidana, baki kasance cikin kewa, yunwa ko ƙishin ganin Zakinki ba, ko da yaushe kina ƙira, kina buƙata, kina muradi, ko a zuciyarki kika ji hakan to tabbas za kiyi tozali da Al-Sad naki, in sha Allah." Lumshe ido Sadiya tayi, ta kasa cewa komai ma, lallai aure shi ne ribar soyayya, duk wanda ya jahilci soyayya a kan ta fi daɗi a waje to lallai bai san asalin yanda soyayya take ba, a lokacin da masoyi da masoyiyarsa suka yi nisa a lambun ƙauna, ba su da burin da ya wuce jin su kusa da juna, idan a waje ne to lallai akwai hijabi a tsakankaninsu muddin masu tsoron Allah da kiyaye dokokinsa ne, amma idan sun ribaci soyayya zai kasance ba komai ne a tsakani sai shauƙi da zuciyoyinsu, idan Haidar na tsuma ta da soyayyarsa sai taji kaman ta rungumesa ta dinga masa godiya da jaddada masa tana ƙaunarsa fiye da haka, amma ba hali ba dama dole sai sun jira wannan hijabin shingen ta yaye, lallai soyayya ma jarabawa ce, sai wanda Allah ya so, kuma mai rabo da tsoron Allah yake kiyayeta yake haye jarabawar lafiya. Haidar yatsunsa guda biyu yayi clashing a saitin idanuwan Sadiya da suke a lumshe, da tausasshiyar muryansa ya ce, "Can I leave sweet Al-Sad?" Sadiya bata da wani option na sake yin rigima domin ya gama narka mata zuciya, jinjina masa kai kawai ta yi matsayin amsan zai iya tafiya, sannan a sanyaye da sulɓi ta buɗe kyawawan idanuwanta, duk da kunyansa da take ji amma ta daure, tana kallon fiskansa ta ce, "Al-Sad ina ƙaunarka da yawa, please ka kula sosai-sosai, kar ka karya mini zuciya, kar ka guje ni, kar ka sauya mini, kar ka......", ta dakata saboda ƙwallan da suka cika idanuwanta. Haidar numfashi ya ja tare da lumshe nasa idanuwan ya kuma buɗe su, a yanayi na zayyane abinda ke a ransa ya ce, "Ina kishinki, ina matuƙar kishinki, ina da zazzafan kishi, amma ban taɓa gwada miki hakan ba saboda na yarda da ke na kuma aminta da ke, shirin aure muke, nan da sati biyu da kwanaki shida da yardan Allah, war haka kina a cikin gidana kuma da igigoyin aurena a kanki, ban taɓa ji a raina akwai wani bayan ni ba a gare ki, kuma ina da tabbaci a kan haka kaman yanda kema kike da tabbacin ke kaɗai ce mace mai matuƙar sa'a, da kika ƙeta duk matakan tsaro kika zubda duk makaman tsaro da kuma na'urorin tsaro har kika yi nasarar shigewa zuciyata kika cika ko ina, Al-Sad ban taɓa kawo wani abu mara kyau a tsakaninmu ba ko tarayyanmu domin nasan da yardan Allah ba komai, muddin ayyuka suna tafiya da niyya ne to lallai niyanmu mai kyau ne, kuma Allah zai tallafa mana wajan cikan niyanmu da burinmu, kibar maganan karya zuciya domin ban taɓa kawo shi a rayuwar da za mu yi ba, ban taɓa yaudara ba kuma bazan fara a kan matar da zan aura ba, kaman yanda ba zan kwatantaki da hakan ba, tunda nasan nine mutum na farko kuma na ƙarshe da kika so har kika shirya miƙa mini amanar kanki, kika amince kika bani dama na zama jagora a gare ki, mijinki, masoyinki, uban ƴaƴanki in sha Allah, kuma da akwai lissafin sauyawa a tsakaninmu da bamu kai wannan mataki da muke ba, kece kawai kuma kin wadatar, bazan guje ki ba kaman yanda nasan ba za ki taɓa gudu na ba, Al-Sad ina da wani irin yaƙini a kanki da imani da bana lissafin rabuwa ko sauyi ko yaudara, duk da nasan a ko wanni zama akwai rabuwa, kaman yanda a ko wanni rayuwa akwai mutuwa, amma bana lissafin rabuwa wa ni da ke, nafi lissafin ko mutuwa ce sai dai ta ɗauke mu tare lokaci guda in sha Allah, so kibar irin waɗannan maganganun, kar su ma fara shiga tsakaninmu, yanzu mu planning za mu ɗaura da yi kawai da kuma addu'a, planning yanda za muyi rayuwa a gidanmu, da yanda za mu reni babynmu idan Allah ya bamu, i can't wait to see that day, ace kina ɗauke da babyna a cikinki and da yardan Allah za ki haife mini babyn da kanki", ya ƙarishe maganan yana saakin wani irin hamshaƙin murmushi tare da lumshe idanuwansa ya ɗan yi baya ya jingina da jikin plastic chairn, ya wara hannayensa tare da sanya hannu guda ya kama saitin zuciyarsa. Sadiya da sauri cikin kunya da soyayya ta miƙe, a sanyaye take tafiya har tana harɗewa, saboda sauri take son yi amma kuma ba za ta iya sauri irin yanda wasu ke yi kaman za su ɓace ba, ko

Chapter 3 of 32