Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kayan lefe ta sa ya kawo, Sadiya ta gama rena mutane wallahi, ina mata magana ma yarinyar nan ta yi mini shiru, bansan ranar da muka fara wannan wasar da ita ba, kuma bata san duk tausaya mata nake ba, amma ita tafi kowa sanin idan na ce zan dake ta to zan mata rauni ne kawai, dan haka ba zan dake ta ba amma za ta auri Sadeeq ko taƙi ko ta so, ni nan zan ɗaura musu aure ko da su Abba sun ƙi, shi kuma Haidar ɗin zan ji da lamarinsa." Mama gyara zamanta tayi tare da cewa, "Yanzu ma ai daga wajan Abban naku nake, shiyasa ma nake nemanta mu yi magana." "Wai ya suka yi da Abban?", Umar ya tambaya dan son jin ya ake ciki, duk da a ɓangarensa bai da damuwa da kowa, dan ya riga ya gama yanke yadda komai zai tafi ya aurawa Sadeeq ita. Muryar Mama cike da damuwar rashin fahimtar da Abba ya mata, ta ce, "Sadiya ta same shi da maganar mai babban suna, duk da ta furta masa ta amince, amma shi ya fahimci kamar tilasta mata nayi, amma a zuciyarta Haidar ne, shiyasa ya ce ba zai aura wa mai babban suna ita ba, duk damuwar Abbanku farincikinta ne kamar dai shi mai babban suna, duk da hujjojinsa da maganganunsa gaskiya ne, amma ba lallai su yi aiki a kan mai babban suna ba, ina da tabbacin in sha Allah ana yin auren za su daidaita." "Shiyasa na yanke ko ma yaya ne zan ɗaura musu aure, indai Sadeeq ne to lafiya za su zauna su daidaita kansu", faɗin Umar. Mama ta ce, "Nima hakan nake hange da yardar Allah, kuma ke ma Sadiya ai da naki, me yasa za ki nuna Haidar ne a zuciyarki?  wai ke kam butulu ce? Kin mance alkairin mai babban suna ko? Kina so ki kasance a cikin bayi masu saka alkairi da sharri ko?" Sadiya da kanta ke ƙasa hawaye ta fara, ta kasa cewa Mama komai, sai da Umar ya daka mata tsawa, sannan ta yi saurin girgiza kai, cikin muryan kuka ta ce, "A'a Mama, wallahi gudun saka alkairi da sharri shiyasa nake faɗar iya gaskiyata, Allah kallon Yayan da muka fito ciki ɗaya nake yi wa Yaya Sadeeq, Mama da fa gabar na bayar gwanda gabar na hana....." A tsawace Umar ya ce, "Keeee!" Maganar Sadiya ne ya katse saboda tsawar da Umar ya kuma yi mata, kamar zai rufe ta da duka, har sai da ta zabura ta yi baya da rarrafe tana kuka mai sauti. "Kee, zan tattakaki wallahi, har ana magana kina magana, wato idan an yi auren kina shirin ƙulla mugunta ko, to wallahi kin ji na rantse miki da Allahn da yake shi ɗaya ba wani bayan shi, kuma bai da abokin tarayya, Sadiya idan kika kuskura har aka yi auren nan kuma na samu labarin kina musguna wa Sadeeq, ko kina masa shirirtar da kika saba, wallahil Azim Sadiya sai na lahira ya fi ki jin daɗi, kar ma a ce na fahimci Sadeeq ba ya samun kwanciyar hankali da nitsuwa daga gare ki, hmmm!", Umar ya ƙarishe maganarsa yana mai yin ƙwafa, ba tare da ya sake cewa komai ba, sai azababben kallon jan kunnen da yake aika wa Sadiya, mai nuni da yana iya mata bugun sakwarar legas. Sadiya ta na ganin kallon da Umar ke  jifanta da shi, ta duƙar da kanta ƙasa, tare da ci gaba da yin kukanta, Mama kuma da kallo ta bi Umar har ya fice a ɗakin, dan alamu sun nuna ya ƙufula sosai ya kai wuya, wadda hakan ke nuni da idan ya ci gaba da zama a ɗakin to zai iya rufe Sadiya da duka Cikin muryar kuka Sadiya ta ce,"Mama kun ƙi fahimtata...", sai dai Sadiya bata kai ga ƙarisa maganar ba, Mama ta katse ta. Mama na girgiza kai ta ce, "Ba wanda ya ƙi fahimtarki ko ya kasa fahimtarki, ke ce dai Sadiya kika runtse idanuwanki, kika ƙi kallon gatan da ake son a miki, Sadiya ina hanga miki alkairan da ko dutsen dala kika haura ba za ki hanga ba, akwai tarin alkairai a auren mai babban suna, Sadiya rayuwar aure ta wuce duk tunaninki, ba iya soyayya ba ce rayuwar aure, Sadiya dole kina buƙatar wanda zai yi haƙuri da ke, ya miki uzuri, ya ƙaunace ki a ko wani hali, Sadiya aure ibada ne kuma babu ibadar da ake yi da sauƙi, dole kina buƙatar namijin da zai yi miki sadaukarwa, namijin da ba zai duba rauninki ko gazawanki ya take miki aljannarki ba, ban san ta ya zan fayyace miki wasu abubuwan Sadiya, amma ki sani lallai rayuwar aure ya wuce duk tunaninki da hasashenki, rayuwar aure kamar dai gidan soja ne, marmari daga nesa, sai ka shiga ciki ka tarar da abubuwan da kake tsammani ba haka suke ba, a wannan hali da kuma yanayi shiyasa nake miki kwaɗayi da fatan auren mai babban suna, na ji daɗi sosai da kika shaida wa Abbanku kin amince da Babana, kuma ina fata za ki cire damuwar da zai kawo zargi a zuciyoyi daga fiskarki da yanayinki, Allah ya miki albarka, Allah ya sa ki shiga a sa'a, Allah ya zaunar da ku lafiya har mutuwa, Allah ya baku zuri'a masu albarka." Sai da Mama ta numfasa, sannan ta miƙe daga zaunen da take, ta tako har inda Sadiya ke durƙushe, dafa kan Sadiya ta yi, ta na murmushi ta ce, "Allahu ya yi miki albarka Halimatu Sadiya, Allah ya baki zuri'a masu albarka da biyayya", iya haka Mama ta faɗa ta taka ta fice a ɗakin. Mama na ficewa Sadiya ta ɗaura hannunta a ka, tare da fashewa da wani irin mahaukacin ihu da kuka, har da birgima da shure-shure take yi da ƙafafuwanta, ihu take yi bil haƙƙi kamar wacce aka yi wa mutuwa, ko da yake a wajan duk wata mace, a mata mutuwa ya fi mata sauƙi, fiye da a aura mata wanda bata so ko kuwa ba ta tunanin iya haɗa duk wata alaƙa ta auratayya da shi. Abu mafi ciwo ga Sadiya shi ne da kowa ya ƙi fahimtarta ko saurarta, sannan abinda take jin ko da sama da ƙasa za su haɗe ba za ta ɗauka ba, shi ne a samu Haidar da maganar za a aurawa Yaya Sadeeq ita, ba za ta aminta da wannan cin fiskar ba, gwanda su aurar da ita bai sani ba akan su sanar da shi gaba da gaba, ba za ta bari a yi hakan ba. (Easy dai Sady beb😂🥱). ⭐️   ABUBAKAR  SADEEQ POV Yana ficewa a gidan ya rage saurin tafiyarsa, saboda kamawar da zuciyarsa ta yi, jiri-jiri yake ji.   Yana tafe yana haɗa hanya, har ya samu ya kai kansa ƙofar gidansu, sai da ya jingina da ƙaramar ƙofar, sannan ya tura ya shiga, mai gadi da su Hammadu direba suka yi masa sannu da shigowa, ya amsa a taƙaice ya wuce ciki. Mai gadi da su Hammadu direba da kallo suka bi Sadeeq, har ya shige ciki, a sanyaye duk suka yi masa fatan samun sauƙi, da kuma na Allah ya dubi lamuransa, domin daga yanayin yadda ya amsa musu, sun fahimci ƙaramin Alhaji ba lafiya ba, dan shi mutum ne mai fara'a da sake fiska gare su, duk da kaf yaran gidan ba mai wulaƙanta su, amma kuma shi nasa fara'ar daban ne, sai addu'a suka bi sa da shi. Sadeeq da sallama ciki-ciki ya shiga palourn, idanuwansa suka sauƙa a kan Khalid da ke zaune dirsham a gaban akwatuna, da kayaki kamar za a buɗe sabon kanti. "Sannu da shigowa Yaya Sadeeq", faɗin Sa'ad cikin girmamawa, yana mai zuba wa Sadeeq idanuwansa, dan ya fahimci kamar yanayinsa ba daidai ba. Kamun Sadeeq ya samu zarafin amsawa Sa'ad sannun da ya masa, shi ma Khalid ɗin ya jeho nasa maganar yana murmushi, "Sannu da shigowa Yaya Sadeeq namu Yayan amarya." Sai da Khalid ya ɗan washe baki ya dara, sannan kuma ya ɗaura da cewa, "Yaya Sadeeq ga lefen ƙanwarka an kawo ɗazu, ka ƙaraso mu gani mu sa albarka." Sadeeq ji yayi abinda ke kama masa ƙahon zuciya, ya tsananta, hakan ya sanya ba tare da ya kai wa inda su Khalid suke zaune kallo na biyu ba, balle ya amsa musu, ya wuce abinsa kai tsaye sashinsa, yana shiga ya wuce wajan fridge da ke a palournsa, ruwa mai matsakaicin sanyi ya ɗauko, sannan ya koma kan sofa ya zauna, sai da ya sha ruwan daidai, sannan ya kwanta tare da cire rigarsa da yake jin kamar ya na yi masa shamaƙi da shaƙar iska ne a gangar jikinsa, lumshe idanuwansa da suka jima da rinewa ya yi, wani irin zafi yake ji tamkar wanda ke wajan da babu mashiga iska, ciki-ciki Sadeeq ya furta, "Ya ilahil ajib, Ya Rabbi kai ka ɗaura mini ka jarabceni, ka kawo mini sauƙi." Khalid ganin Sadeeq ya wuce bai ce musu komai ba, a sanyaye ya ce, "Yaya Sadeeq yau da miskilan nasa yake ji a gaban goshi, yo ko ma dai menene to sun fi kusa da Sadiya, idan taji bai kalla kayan lefenta ba, na tabbata rigima da daru kaf za ta tsayar masa, namu ido Yaya Sa'ad." "Mtsww!", Sa'ad ya ja guntun tsaki tare da aika wa Khalid harara, sannan ya ce, "Kai dai an yi bahulkumi wallahi, yanzu a ce ko da yaushe bakinka ba fullstop ba birki, ba ka gane yanayin mutum sam-sam, ba ka banbannce lokacin da za ka yi dogon magana ko raha da mutum, da kuma lokacin da bai kamata kayi ba", faɗin Sa'ad yana kan hararar Khalid cikin haushi, dan shi ya fahimci yanayin Yaya Sadeeq akwai wani abun. Khalid ya ce, "Ni to ai ban san wani abu na damunsa ba, kuma na ga lefen Sadiya mutumiyarsa ce ai." "To daman ya za'a yi ka sani ka kai ajiyar hankali da wayonka." Khalid ɓata fiska yayi, tare da fara tattara kayan, wai ya ji haushi ya fasa kallo, domin shi ma ya damu da damuwar da ke damun Yaya Sadeeq. Sa'ad da Khalid suna zaune haka ba jimawa Umar ya shigo, sannu da shigowa suka masa ya amsa musu a taƙaice, sannan ya wuce sashin Sadeeq kai tsaye. Sa'ad da harara ya bi Khalid, sannan yana ƙwafa ya tashi ya wuce ɗakinsa, zuciyarsa cike fal da fatan alkairi ga Yaya Sadeeq, yana ji a jikinsa kuma kamar maganar Sadiya ce, dan haka ya ƙudurci raya daren yau da nafila, dan taya ɗan uwanshi addu'a, Allah ya mallaka masa abincin ruhinsa. Khalid tattare kayan ya yi, sannan ya kulle akwatunan, ya kai su ya jere  a keɓantaccen wajan da Umma ta faɗa, shi ma ya wuce ɗakinsa, zuciyarsa babu daɗi sam, dan su wasu irin ƴan uwane masu matuƙar ƙaunar junansu, da girmama junansu, da kuma damuwa da damuwar junansu, indai addu'a Abba da Umma suka musu na Allah ya haɗa kan su, to sai hamdala dan addu'ar su ta amsu, idan kuma Allah ne ya dube su da idon rahama ya musu arziƙin haɗin kan yaran nasu, to nan ma sai godiya, dan babban arziƙi ne wanda kowa ke nema ido rufe, amma ba ko wacce zuri'a Allah ke azurtawa da haɗin kan ba. Umar da sallama ya shiga sashin Sadeeq, amma Sadeeq da ke kwance idanuwa a rufe sam-sam bai ma ji sallamar ba balle ya amsa, dan ya yi nisa a duniyar tunani da kuma ciwon da yake ji, ya kunna ac ya ƙure, ya kuma kunna fanka, amma duk zafi yake ji ta yacce numfashi ma da ƙyar yake yi, dan haka yayi nisa yana ƙoƙarin ficewa a hayyacinsa, har sai da Umar ya ƙarisa ya ɗan taɓa sa, sannan a ɗan firgice Sadeeq ya buɗe jajayen idanuwansa, hakan ya sa Umar ya ɗan tsaya ya yi jim yana kallonsa. "Kawo mini maganina da ruwa," faɗin Sadeeq yana ɗan kawar da fiskarshi dan kar Umar ya fahimci halin da yake ciki, sai dai ya makaro domin Umar tuni ya lura, amma bai ce komai ba har ya kawo wa Sadeeq magungunanshi, ya ɓalle masa su ya miƙa masa, sai da Sadeeq ya lallaɓa ya tashi ya zauna yana mai ɗan cije baki, saboda kamawar da ƙahon zuciyarsa ke yi har sannan, cikin dauriya ya samu ya kora maganin, sannan Umar ya tattara ya mayar da magungunan, ya dawo ya rage gudun ac da na fanka, sanna ya zauna yana fiskantar Sadeeq, cikin kuluwa ya ce, "What's wrong with you again bro? Sadiya ce right?", with seriousness face Umar ya yi tambayar. Sadeeq gyara zamanshi yayi tare da lafewa a jikin sofa, Umar na rufe baki ya girgiza kai, da calmness voice ya ce, "No bro, ba Sa'adiyah ba ce, dan raha muka yi da ita muka rabu lafiya, shigowa na ne kawai naji jikina ba daɗi." Sai da Umar yayi taking deep breath sannan ya ce, "Allah ya rufa asiri, Allah ya ƙara sauƙi, but please bro ka cire komai a ranka, komai zai zama daidai kuma yadda ake so in sha Allah." Sadeeq gyaɗa kai kawai ya yi ba tare da ya kuma cewa komai ba, dan a yanzu da Umma yake buƙatar yin magana kawai, Amininsa da kuma Mama abokiyar shawararsa, har Abba da ma ita Sadiyar kanta, duk daga masu supporting batun auren, sai masu ƙi, shi kuma a yanzu yana so ne ya daure da gaske fiye da a farko, yana buƙatar mai ƙwarara masa guiwa ne, kuma ya san Umma ce kawai za ta masa hakan, sai dai kuma ko Khausar, amma ba ya buƙatar yin dogon magana da Umar a yanzu, dan shi da kansa ya riga ya gama yanke ba zai auri Sadiya ba no matter how, ko da hakan na nufin zai fansar da rayuwarsa ne, he'll risk his life for her happiness, wannan alƙawarinsa ne. Umar da kallo yake bin Sadeeq, cikin zuciyarsa yana raya da a ce Sadiya ce ta kuma yin sanadin wannan ciwon, to da ya ba ta mamaki ya bai wa kowa mamaki, ba mai hana shi ɗaura musu aure a gobe sai ikon Allah da tsananin rabo. Suna zaune shiru-shiru har lokaci ya ja, sannan Sadeeq ya lallaɓa ya wuce bedroom nasa, watsa ruwa ya yi tare da yin shirin kwanciya ya kwanta, ba jimawa bacci yayi gaba da shi, kasancewar akwai maganin da ke saka bacci a magungunansa.   Umar ma yana nan zaune a palourn yana ɗan duba wayarsa, sai da ya ga an jima Sadeeq bai fito ba, sannan ya miƙe ya bi sa ɗakin, ganin yana bacci sai ya wuce bathroom shi ma, dan dama nan ɗin ba baƙonsa ba ne, wani lokaci ya kan kwana idan suka yi wani aiki tare har dare, ko kuma watarana shi Sadeeq ɗin ya kwana a can gidan Mama su yi aikin a can. Umar yana fitowa ya shirya bacci shi ma ya kwanta a ɗaya edge na gadon, ba jimawa baccin gajiya yayi gaba da shi. ⭐️      SADIYA POV Ta na kwance a nan tsakar ɗakin Umar ta na rusa kukanta har bacci ya yi gaba da ita, bata farka ba sai goshin asuba, ganin ɗakin da ta yi bacci, da sauri ta kai dubanta zuwa ga kan gadonsa ƙirjinta na bugawa, sai dai wayam ta gani babu shi, har kan sofa, har toilet bata ji alamar yana ciki ba, sai da ta tuna ya fice ko ya kwana a wajan Yaya Sadeeq ne, sannan ta yi taking deep breath tana hamdala da Allah ya rufa mata asiri, sannan ta miƙe jiki a sanyaye, dan ji take kamar ba jikinta ba kamar wacce aka yi wa duka, a haka ta samu ta fice a ɗakin, kai tsaye ta wuce ɗakinta, da sallama ta murɗa handle ɗin a hankali ta shige, sallamar ma ciki-ciki ta yi, gudun kar ta tashi masu bacci. Toilet ta wuce kai tsaye, ta watsa ruwa mai zafi ko za ta ji dama-dama a jikinta, sannan ta ɗauro alwala ta fito, turare da mai ta shafawa jikinta, sannan ta sanya riga mara nauyi, ta shumfiɗa darduma ta gabatar da nafila, ta yi addu'a sosai-sosai, ta kuma yi kuka sosai mara sauti, har sai da aka ƙira sallar asuba sannan ta tsagaita da nafilfilun, ta tsaya jan carbi, sai da aka shiga masallaci sannan ta miƙe ta bi jam'i, zuwa lokacin sauran mutanen ɗakin nata sun fara tashuwa dan yin sallah. Sadiya na idar da sallah, ta shafa addu'anta, tare da laluɓar wayarta ta tura wa Haidar saƙon ƙaunarsa da take yi da kewarsa da take yi, sannan ta kashe wayarta ta kwanta.    ⭐️ ABUBAKAR SADEEQ POV Ana ƙiran salla suka tashi shi da Umar ɗin, sai da suka gabatar da nafila sannan suka fito dan zuwa masallaci, a palourn suka haɗu da Abba da su Sa'ad, duk barka da safiya suka yi wa Abba da junansu, sannan suka fice du suka wuce masallaci, bayan an idar da sallah sun yi addu'oi sun fito, duk suka gaishe da Abba nan ma da junansu, sannan Umar ya wuce gidan Mama. Su Sadeeq suna shiga gida su Sa'ad kowa ya wuce ɗakinsa, Abba ya haura saman bene, shi kuma Sadeeq ya zauna a palourn, kishingiɗa yayi a kujera har ya fara gyangyaɗawa sai ya ji sautin muryan Umma. "Sadeeq lafiya dai ko?" Umma da ke ƙarasowa cikin palourn ta tambaya, dan tun kamun ta gama sauƙowa a benen ta fahimci Sadeeq ne a palourn, ta kuma yi mamaki. Sadeeq tashuwa yayi zaune, yanan daidaita yanayin fiskarsa ya ce, "Lafiya Umma, daman ina jiran sauƙowanku ne." "Ka tsaya jiran sauƙowana, maimakon ka ƙirani a waya, ko kuma ka ce da Abbanku ya ƙira maka ni, ina ce tare kuka dawo a masallaci?" "Eh Umma", iya haka Sadeeq ya amsa mata a taƙaice. Umma ƙarasowa tayi ta zauna a kujerar da ke kallon wanda Sadeeq ke kai, sannan ta ce, "Idan ma tunaninka ina salla ne, ai tare muka idar tunda jam'i na bi, ba na son irin jiran nan Sadeeq, ka ga yanzu ma har ka faɗar mini da gaba, Sadeeq sam-sam ba na son ganinka a irin wannan yanayin yana matuƙar damuna, ya kamata ka cigaba da ɗaukar ƙaddara kamar yadda ka fara tun farko, ka yi haƙuri, ka daure ka jure, komai ka ga ya faru to muƙaddari ne daga Allah, rayuwa tamkar zaren ƙaddara take ba mai tsinka ta sai Allah, ba kuma wanda ya san gobensa sai Allahn da ya halicce shi, haka sanin abinda ka iya faruwa a gobe, wannan ma a bar wa Allah, damuwarka tana damun mu, indai akan auta ne ka sha kuruminka ka miƙa wa Allah lamarin, muddin ita rabonka ce ba wanda ya isa ya dakatar ko ya hana, idan kuma ba rabonka ba ce, to ko duk duniya za mu taru mu ba ka ita, to ba za ka mallaketa ba tunda Allah bai ƙaddara hakan ba", cikin rarrashi da kuma nuni da tunatarwa Umma ta yi maganar. Sadeeq sai da ya ja numfashi ya busar da iska mai ɗumi, sannan ya gyara zama tare da cewa, "Umma ina lafiya, ba komai, sannan duk wannan na nusar da kai na, yanzu damuwata ɗaya ne." "Menene damuwarka Sadeeq?" Umma ta tambaya cikin kuluwa. "Sa'adiyah", Sadeeq ya faɗa underneath his breath. Umma da kallon rashin fahimta ta bi shi, sannan ta ce, "Kamar auta ka ambata ko? To dama tun asali menene damuwar taka idan ba ita ba? Sadeeq dole fa ka sanya haƙuri da salama a zuciyarka." "I know Umma, and that's what am trying to do, batun aurenta da Umar ke yi shi ne damuwata." "Me kenan kake nufi?" "Umma ba na son maganar kawai, Umma ba na son a ke maganar da ya shafi akwai abu a zuciyata dangane da Sa'adiyah, she's my little sister, a sister from you, ƙanwar da kika haifeni kuma kika haifeta, haka kawai nake son ji", Sadeeq ya faɗa yana yin ƙasa da kansa tare da taune leɓensa da ƙarfi, saboda yadda maganar Sadiya ke masa amsakuwwa a kunne, kamar yanzu take furta masa maganar da ke shaida abinda ke zuciyarta, furucin da ke nuni da ba ta son shi ba ta ƙaunarsa, Haidar ne zaɓinta shi ta zaɓa, faɗar wannan magana daga bakinsa, yana ji ne kamar zai ƙarisa maganar yare da ficewar numfashinsa na ƙarshe. *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD @Uwarbatoorl ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [28/12/2025, 08:27] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 💔NAUYIN BAKI....👄💔        Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠     اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 45 _ 46 ⭐️ "Sadeeq", Umma ta ƙira sunan shi jin ya yi shiru. "Na'am Umma"; ya amsa in a gentle and calm voice. "Duk da abubuwan da suka faru kuma suke kan faruwa suna mini babu daɗi a zuciya, saboda daga ni har Abbanku ƙannenka da kowa ma mun so lamarinka da Sadiya, amma kuma mun yi imani abinda Allah ya nufa shi yake faruwa, dan haka na ji daɗi da ka haƙura za ka cire komai a ranka, hakan ba ƙaramar sukuni zai samar mana ba, Allah ya maka albarka ya agazawa lamuranka, zan ci gaba da yi maka addu'a, khairan in sha Allah." "Amin Umma, muna fatan hakan, Allah ya amsa addu'oi." "Amin Ya Hayyu Ya Qayyum", Umma ta amsa, sannan ta ɗaura da rarrashi tare da ban haƙuri, da shawarwari ga Sadeeq, sun jima sosai dan basu ankara ba har agogon da ke maƙale a palourn ya buga, gari kuma ya yi haske tangararan, Sadeeq sai da ya gaishe da Umma sannan ya miƙe ya wuce sashinsa, dama-dama yake ji a zuciyarsa na abinda ya kama masa ƙahon zuciya, domin ko da ya sha magani, da ya tashi da asuba ba sosai ya sake shi ba, amma yanzu ya sake sa yana jin daidai, damuwarsa kawai kada ko Umar ne ya sake yi masa batun bikin, kuma yana sane da yau laraba za su fara shagalin biki, hakan ya sanya, ya zauna tare da turawa Sadiya saƙo, sannan ya shirya tafiya, dan dama akwai issue da yake da shi a Adamawa, kuma zai ɗauke sa har ranar Juma'a sannan ya dawo. Sadeeq ba tare da ya yiwa kowa sallama ba, ya sanya kayakinsa a mota, karyawa ma bai tsaya yi ba, zuwa bakwai da rabi ya fice a gidan, da motarsa ya kama hanyar Adamawa. Ko da jama'ar gidan suka fito, ganin bai zo an karya da shi ba, Khalid ya dubo shi ba ya sashinsa, sai suka ɗauka ko ya tafi wajan aiki ne, daga haka suka zauna suka karya, sannan kowa ya wuce ya shirya ya fito ya kama hanyar wajan nasa aikin. ⭐️ Umar ko da ya koma gidan, yana shiga ɗakinsa ya wuce kan gado, ba jimawa bacci yayi gaba da shi, bai farka ba sai takwas da mintuna, ya tashi ya samu an jere masa abun karyawa, wanda yake da tabbacin aikin Mama ne.   Toilet ya wuce ya wanko bakinsa ya fito ya karya, sannan ya koma yayi wanka ya fito ya shirya dan zuwa aiki, shi ne bai bar gidan ba sai wajajen ƙarfe tara, bai tsaya bi ta gidan Abba ba, dan ya san zuwa lokacin Sadeeq ya jima a office tunda mutum ne mara wasa da aiki sam-sam. Jama'a tun da garin Allah ya waye ake ta hada-hada, amarya Sadiya ta na can ta na tiƙar bacci, ita ce ba ta tashi ba sai wajajan sha ɗaya, ko da ta farka wanka ta shiga, ta na fitowa ta wuce ta shafa manta, ta sanya kaya simple, ta fesa turare, bakin gadonta ta koma ta zauna, kasancewar ba kowa a ɗakin sai ita kawai, wayarta ta jawo ta kunna, ta na ƙoƙarin shiga call log aka turo ƙofar ɗakin aka shigo da sallama, da sauri ta ɗago kanta ta na sakin murmushi tare da cewa, "Wai yanzu nake shirin ƙiranki ai." Zahra ƴar dariya ta yi tare da ƙarisowa ta zauna a gefen gadon ita ma, sannan ta ce, "Ni kam tun ƙarfe goma ina gidan nan ai, kawai na barki ki yi bacci ne ki huta da kyau, abinka da amarya ai dole a huce gajiya tun kamun hidima, kar abin ya miki yawa ga kuma wanda Haidar zai ƙara miki ba ɗaga ƙafa." "Ke dai za ki ji da shi", faɗin Sadiya ta na murmushi wanda yake har

Chapter 28 of 32