Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba za ki zo ki gaida ni ba, kin maƙale wa mamanki ko", faɗin Umma tana kallon Nayla da ta ƙara lafewa jikin Sadiya da kyau. "Umma za ta gaidaki amma sai zuwa anjima, ta fi so ta fara gai da Abba ne, kinsan Miji na gaba da kishiya." "Ta je can ta yi kishi da Maman babanta ba dai ni ba, kuma ba kallar mini miji za ta yi ba, da farinta kamar ƴar turawa, fatan kun iso lafiya? Ya hanyan? Ya mai gidan naki?" "Alhamdulillahi Umma yana gaida ku", Khausar ta faɗi tana dariya. "Amma dai daman yau baka je ma'aikatar taku ba ko?" Umma ta faɗi idanuwanta a kan Umar. "A a Umma, na je daga can ma na wuce ɗauko su." "Na ɗauka ai wannan ruwa da ya kawo sanyi ma sha Allah, ko ya hana ka fita." "A a Umma." "Assalamu alaikum, sannunku da zuwa Maman Najla", faɗin ma'aikaciyar gidan, da ta aje trayn ruwa da drinks a gaban Khausar. Du amsa sallaman suka yi, sannan Khausar ta murmusa tare da cewa, "Yauwa Mama Saude, sannunku da ƙoƙari, ya bayan kwana biyu? Ya iyalai?" "Alhamdulillah Maman Najla, amaren Alhaji Abba sannunku da zuwa ko", ta faɗa tana sakar wa su Najla murmushi, sannan ta musu sallama ta wuce ta koma sashinsu na ma'aikata. Umma cewa ta yi, "Mama Saude ki bar haɗa mini miji da waɗannan online product's ɗin." Du murmusawa suka yi, sannan Najla da Nayla suka sauƙo suka ƙarasa wajan Mamarsu, drink ɗin ta ba su ita ma ta sha, duk yaran biyu sai da suka yi bismilla sannan suka sha, sannan ita ma ta sha, duk suka yi hamdala. Umar miƙewa yayi tare da cewa, "Bari na koma wajan aiki Umma, sister a huta gajiya da kyau, anjima zan zo muyi maganar, sannan za mu fita tare." Umma ta ce, "To Allah ya taimaka Umar, a dawo lafiya." "A dawo lafiya uncle U, Allah kai mu anjiman", faɗin Khausar tana jinjina kai. "Uncle U byee, ka kawo mana tsaraba", faɗin Najla tana mishi bye da hannunta, Nayla ma waving na hannu ta mishi, ya amsa musu sannan ya fice. Sai sannan Sadiya ta samu sarari tare da miƙe wa ta koma gefen Khausar tana jaddada mata kewansu da tayi, Khausar kuwa sai tsokanar Sadiya take wai amarya mai maganar sugar. Abinci Mama Saude ta kawo wa su Khausar, suka ci suka yi hamdala, sannan ta miƙe tana faɗin, "Umma bari mu je wajan Mama." "To a dawo lafiya ku gaidata." Sadiya miƙewa tsaye tayi tana cewa, "Aunty Khausar da dai mun bari zuwa anjima, Allah yanzu da akwai rana fa, kinsan aka yi ruwa to rana fitowa yake da gaske, kuma ma ko hutawa ba kuyi ba." "Ni fa ban ce sai kin bi mu ba small Mum, kiyi zamanki wajan Umma, mu dai wajan Mama za mu, inyaso sai mu huta a can." "Akwai rana fa Aunty." Umma ta ce, "A a auta, ƙyalesu su je can su cika ta da karambanin su, daman waɗannan yaran naku masu ƙiriniyar ba shiryawa da su zan yi ba." Sadiya ranƙwafowa tayi ta ɗauki Nayla ta kama hannun Najla, rufawa Khausar da ta kusa ficewa baya suka yi, Sadiya na faɗin, "Umma na tafi da yaran nawa." "Ku sauƙa lafiya, ku gaishe ta." Ɗan ɗaga ƙafa Sadiya tayi suka iso Khausar, jerawa suka yi, suna tafe Sadiya da Khausar na hira, Najla kuma tana kalle-kalle tare da nuna wa Sadiya wani yaro da ke wucewa a keke, Sadiya na amsa mata sama-sama. Akan yadda suka tsara events ita da ƙawayenta Khausar ke tambaya, Sadiya bayani ta mata, Khausar ta sauya wasu tsarin tare da gyara wasu abubuwan, har suka shiga harabar madaidaicin gidan suna zancen su, "Assalamu alaikum", Khausar da Sadiya da yaran duka suka yi sallama a ƙofar shiga palourn gidan. Mama daga ciki amsa musu tayi tare da basu izinin shigowa, sannan suka tura ƙofan suka shiga, Najla sake hannun Sadiya tayi ta nufi Mama da gudu, su kuma suka ƙarasa kowa ya zauna a kujera, Nayla na lafe jikin Sadiya har yanzu. "Manya-manyan baƙi mutan Abuja", faɗin Mama da ta ɗaga Najla ta ɗaura ta a cinya.   Najla surutu ta fara yiwa Mama tare da isar mata da saƙon gaisuwan daddynsu. Mama ta ce, "Mun amsa gaisuwa sosai, sannunku da hanya." Khausar na murmushi cikin girmamawa ta ce, "Mama mun same ku lafiya?" "Lafiya sai godiya Khausar, ya kuka baro mai gidan? Ya maƙota? Sannunku da hanya ko." "Duk suna gaishe ku." "To ma sha Allah." "Sannu da gida Mama", Sadiya ta faɗa tana ƴar dariya. "Kin yiwa ƙannen babanki da ke zuwa dariya, me ma ya kawo ki gidana? Maza tashi ki koma wajan Ummanki ku fama", faɗin Mama tana haɗe fiska. "Allah ya baki haƙuri Mama." "Idan ya bani ki ƙwace." Khausar ƴar dariya tayi ita ma, tare da cewa, "Amarya fa bata laifi Mama,  a mata afuwa." "Amaren ƙwarai ne basa laifi, wannan shirmammiyar ai sai dai addu'an shiriya kawai ga Sadiya." Tura baki Sadiya tayi tana ɓata fiska.   "Lah small Mum ma bata ji, mummy ki mata bulala ita ma", faɗin Najla. Duk dariya maganan Najla ya basu, sai suka dara, daga nan Mama da Khausar suka bige da hira, Sadiya ta tashi ta tafi kitchen, kunu ta samo sauran wanda aka kai wa Sadeeq asibiti, sai ta ɗibo musu dukansu, yaran suka amsa kuwa suka kafa kai sai sha kawai. A nan wajan Mama suka wuni har bayan magrib, Sadiya ce ta fice ta je ta ɗauko wa su Khausar abinda za su buƙata na shirin kwanciya ita da yara, bayan ta dawo ta shirya su, Nayla ba jimawa bacci ya ɗauke ta, Sadiya da Najla suna game a wayarta. Mama da Khausar suna tare a palour har Umar ya shigo, bayan sun mishi sannu da dawowa ya wuce ya je ya watsa ruwa ya shirya, ko da ya fito zama yayi yana cin tuwo suna magana da Khausar, dan Mama ta wuce ɗaki ta ba su waje. "Uncle U ban gane me kake faɗa mini ba, wai shi Yaya Sadeeq ɗin ne yake asibiti har tsawon sati biyu? Kuma ban da labari." "Abba ne ya ce kar a faɗa miki domin bamu ɗauki matsalar babba ba ce za ta kai har kwanaki haka yana asibiti, duk da alhamdulillahi tunda a satin bikin nan muke sa ran sallama in sha Allah." "Jikin nashi da sauƙi kenan? To ma sha Allah, Allah ya ƙara afuwa, amma in za ka tafi ai za mu je tare ko?" "In sha Allah, domin shi ne fitan da ɗazu na ce miki za muyi." "To Uncle U, ka kammala sai mu je ɗin na dubo shi, Allah ya sa su sallameshi gobe." "Amin sister." "Daman shi ne maganar da ka ce za muyi? Mene ne zan taya ka bincikawa kuma?" "Ba maganar ba kenan, za muyi ta idan muna tafiya", Umar ya faɗa yana kai ruwa bakinshi. "Amma Uncle U me ke damun Yaya Sadeeq ɗin?, sam naji na damu hankalina ya tashi, Yaya Sadeeq ɗin da ba zan iya tuna when last yayi ciwo ba, shi ne wai har yayi good two weeks a hospital, shi da duk tsananin ciwonshi a tsaye yake yi har ya kammala, amma a ce har ya kwanta a asibiti har kwanaki haka." "A kan abinda ke damunshi ɗin za mu yi magana, kuma ki taya ni bincikowa." "To Allah ya bamu sa a, shi kuma Allah ya ba shi lafiya." Da, "Amin", Umar ya amsa, sannan ya wanke hannunshi, ya tattare kwanukan ya kai kitchen sannan ya fito yana faɗin, "Bari na je masallaci nayi salla, kamun na dawo ki yi sai mu wuce." Amsawa Khausar tayi sannan Umar ya fice, ita kuma ta miƙe ta shige ɗakin Mama, a nan tayi sallahn dan ba ta son hayaniyar su Najla, tunda Allah ya taimaketa sun zo gida ga Sadiya bari ita ma ta huta, amma in ba haka ba ka biye wa yara dan ta su, tun suna ciki kai kaɗai za ka ke fama da su, haka in sun zo duniyar ma kai kaɗai ba hutu sam, ita kuwa ba za ta iya ba, tunda sun zo duniya, Allah kuma ya sa ga al'umman Annabi ai sai a taya ta fama da su, shiyasa ko a Abuja ranar da daddynsu baya nan tana kai su neighbour, muddin ba makaranta, idan da makaranta kuma wuni Najla take gwanda Nayla zuwa twelve ta dawo. Jiyo sallaman Umar a palour, shi ya sanya Khausar miƙewa tare da gyara hijabin jikinta tana faɗin, "Mama bari mu je asibiti mu dawo." "Da Umar ɗin ko?" "Eh Mama." "To a dawo lafiya, Allah ya tsare, a gaishe da mai babban suna, Allah ya ƙara mishi lafiya da ƙarfin jiki, muna addu'an a sallamo mana shi gobe ya dawo." "Allah ya amince Mama", faɗin Khausar da ta juya ta fice a ɗakin, sannu da shigowa ta yiwa Umar, ya amsa tare da ƙarasawa yayi wa Mama sai da safe, ko da ta tambayeshi wa zai dawo da Khausar, ya sanar mata su Sa'ad za su dawo da ita, Allah tsare hanya ta musu, sannan yayi gaba Khausar ta rufa mishi baya, mazaunin direba ya shige, ita kuma ta shiga gefen direba, ya ja motar suma bar anguwar. Umar yana tuƙi, ya fara magana idanuwanshi na a kan hanya, "Dare-dare wajan ƙarfe goma har na kammala komai na yi shirin kwanciya sai ga ƙiran Khalid, na ɗauka kenan yake sanar mini da halin da Sadeeq ke ciki ba ya ko motsi, hakan ya sanya cikin kiɗimewa da sauri na sanar da Mama na fito, mun kamo Sadeeq mun fito da shi sai ga Sa'ad, ya jawo mu a mota ya kawo mu asibiti, likitoci sun jima ƙwarai a kan shi, kamun suke sanar mana da ya faɗa doguwar suma, saboda wani abu da ya dame shi a rai sosai, har dai suke faɗin yanayin zuciyarshi na tafiya ba daidai ba, mun ɗauka zai kai watanni ko shekara ma kamun ya farka, kamar yadda suka ce lokutan da dogon suma ke ɗaukar mutum, amma cikin ikon Allah a sati guda sai ga shi ya farka, a ranar da su Abba suka taho da Sadiya asibiti bayan mun yanke a zo da ita, ina tsaye a wajan, ina ɗakin na ga motsawan Sadeeq, bayan jikinshi ya rikice likitoci sun yi ƙoƙarinsu, da yardan Allah ya dawo daidai ya zamana ya farka, nan ma likita ya mana bayanin dole akwai abinda ya ji ko ya raɓe shi wanda yake so ko yake ƙi, da hakan yayi sanadin farfaɗowanshi, sannan sun shawarce mu da mu tuntuɓe shi ko akwai abinda yake buƙata yake ɓoye mana, ko akwai abinda ke damunshi yake ɓoye mana, a iya bayanin da na miki na farko me kika fahimta?" Wani nauyayyan numfashi Khausar ta sauƙe, idanuwanta har sun cika da ƙwalla, sannan ta ce, "Tabbas idan mutum ya rasa tunaninsa, likitoci kan ba da shawarar yana mu'amala da abubuwan da yayi kamun ya rasa tunaninshi hakan na taimakawa tunanin ya dawo, haka kuma idan mutum ya faɗa doguwar suma, wani abu da yake so ko yake a zuciyarshi yana taimakawa wajan farfaɗowarshi da yardan Allah, Yaya Sadeeq yana ji da small Mum sosai-sosai, lallai-lallai ta ba da gudumawa wajan farfaɗowarshi." Murmushin gefen baki Umar yayi tare da cewa, "Abba ya same shi da maganar ya faɗa me ke damunshi ko me yake so, kaman zai faɗa sai kuma ya fasa, nima na same shi da maganar ..............", yadda suka yi da Sadeeq da dare ranan ya labarta mata. Sai da ya numfasa sannan ya ɗaura da cewa, "Me kika kuma fahimta? Me kuma kike hasashe." "Gaskiya Yaya Sadeeq na ji da small Mum sosai, komai dai ita, komai damuwarshi ita", Khausar ta kammala maganar daidai sun iso cikin asibitin. Umar taɓe baki yayi kawai, sai da ya daidaita sawayen motar, suka fito ya kulle motarshi, sannan suka nufi ciki yana faɗin, "Har yanzu tunaninki bai je inda nake so ya je ba, amma kiyi tunani da kyau, domin gobe nake son ki taya ni bincike ɗakinshi kaf da kyau, dole sai na samo hujjar nuna wa su Mama abinda yake damunshi." "To Uncle U, Allah ya kai mu da rai da lafiya, Assalamu alaikum", Khausar ta ƙarishe maganar da yin sallama saboda sun iso ƙofar ɗakin. Daga ciki Khalid ya amsa, sannan suka shiga, washe baki Khalid yayi yana faɗin, "Aunty ku ne a gari oyoyo, ina yaran Uncle?" "Autan maza na Umma mu ne a garinku fa, su Najla suna can gidan Mama wajan small Mum suna gaishe ka." "Sannu da dawowa Yaya Umar, ya aikin?" "Alhamdulillah, ga ni nidai aikin bai kashe ni ba." "Daman ai aiki ba ya kashe babba, sai yara irina." Khausar na dariya ta ce, "Kai ne yaro?" "Eh Aunty, yanzu Abba ya gama faɗan haka ma kamun suka tafi shi da Yaya Sa'ad." Girgiza kai Umar yayi tare da samun waje ya zauna, Khausar ta ce, "Allah ya shirya ka autan maza, 24 ai a wani wajan da matar ka har da yaranka." "Amin Aunty babba, our one and only aunty, nima ɗin ina jin Abba aure zai mini, amma fa shi zai ciyar da mu da komai." Murmushi Khausar tayi tare da yi wa Sadeeq da ya fito a toilet yanzu sannu, fitowanshi ne ya hana ta kula shirmen Khalid. Sadeeq bai yi mamakin ganin Khausar ba, sai dai ganinta ya kuma bugar mishi da zuciya, domin tuni ne gare shi a kan kusantowar rasa Sadiya da zai yi, duk da zuciyarshi ta kama amma haka ya daure, tare da ƙaƙalo murmushin dole, ya ƙara gado ya zauna tare da faɗin, "Welcome sister.' "Thank you Yaya, fatan mun same ku lafiya? Ya ƙarfin jiki?" Ta ƙarishe maganar cikin matuƙar nuna kulawa, dan a duniya Khausar tana bala'in ƙaunar Yayanta, duk da kasancewarta saƙonshi(wacce take bin shi), amma ba komai na rigima tsakaninsu sai ƙaunar juna da girmama shi da take yi, kamar yadda ita ma na ƙasa da ita suke girmamata. "Alhamdulillah! Na warke.?", ya faɗa a taƙaice. Cikin girmamawa ta ce, "Haka muke so Yaya, Allah ya ƙara ƙarfin jiki, bama fata a yi bikin small Mum Yaya Sadeeq namu na asibiti." "Uhm!", iya haka Sadeeq ya faɗa tare da kallon Umar, shi ma Umar ɗin Sadeeq yake kallo, amma suna haɗa ido ya ɓata fiska ya kawar da ido, Sadeeq murmushi yayi kawai ya kwanta tare da lumshe ido. Khausar amsa hiran Khalid take yi, wanda duk na barkwanci ne dariya yake saka su, sai da lokaci ya ɗan ja, sannan Umar ya ce, "Khalid ku koma gida lokaci ya tafi." Da sauri Khalid ya miƙe tare da sara hannu ya ƙame irin yanda sojoji ke yiwa ogamninsu, a ƙamen ya ce, "Ok Sir." Girgiza kai Umar yayi ya ce, "Allah ya taro ka." "Kai dai Khalid ba ka rabo da abin dariya wallahi, ashe kun koma sojoji kai da uncle U ba mu da labari?", faɗin Khausar. "Ai ni tunda Yaya Umar ya raba ni da gingimammun ayyukan da suka nemi hallaka ni, sara mishi ya zame mini dole, dan ya fi mini soja." "To Parrot ku tafi dare na yi", faɗin Umar. Khausar Allah ya ƙara sauƙi ta yiwa Sadeeq,  sannan ta musu sai da safe, bayan ta amsa maganar Umar na jaddada mata da yayi da safe za su yi magana idan ya shigo, daga haka suka fice ita da Khalid, suka shige mota ya ja su sai gida, yana labarta mata rikici da rigimar Sadiya, da ƙyar Umma ta shawo kanta ta haƙure ta cigaba da walwala yadda ta saba.   Khausar na sauraran Khalid ne, yayin da take sake jujjuya maganganun Umar da na Khalid ɗin duka a zuciyarta, tana son lissafo abinda yake so ta fahimta, a ƙofar gidan Mama ya aje ta tare da mata sai da safe ta shige, sannan shi ma ya wuce gida. ⭐️ PLATEU SPECIALIST HOSPITAL. ABUBAKAR SADEEQ POV      *** Bayan tafiyar su Khausar ba jimawa, Sadeeq ya muskuta, without opening his eyes ya fara magana in a gentle way, "Malam me kake ɓata wa fiska haka? Wa ya taɓo ka?" Umar sarai ya ji abinda Sadeeq ya faɗa, duk da murya ƙasa-ƙasa yayi maganar, amma ko ci kanka bai ce mishi ba, ci gaba yayi da danna wayarshi. "Malam am talking to you", ya faɗa yana  buɗe gajiyayyun idanuwanshi, tare da watsa su wa Umar. Fiska a haɗe Umar ya ce, "Ohh! Wai ni kake yiwa magana? I thought you're talking with your self ne ai." Sadeeq taɓe baki yayi tare da ɗage kafaɗa irin abinda Umar yayi bai dame shi ba, sannan ya ce, "what's wrong with you?" "Hmmn! Kai fa kana da renin hankali sosai Sadeeq, da kake tambayar what's wrong with me, didn't i told you? Da nake magana ranan ba mahaukaci tuɓuran ka mayar da ni ba, and yanzu kana tambayana what's wrong, haukar kake son na cigaba da yi kenan?" "That day am not okay, something is wrong with my heart, shiyasa ban ce maka komai ba, but now am okay you can tell me what's making you doing cow face this day's." Umar hararan Sadeeq yayi tare da cewa, "Kai ke yin fiskar shanu ba ni ba malam, sannan kuma zuciyarka ai ba za ka taɓa jin daɗinta ba muddin baka faɗa wa mutane me ke damunka ba, don barin kashi a ciki ba ta maganin yunwa, dan Allah ko ba za ka faɗa wa kowa ba, ni ka faɗa mini, mene ne ke damunka? Kai fa baka san yadda aka kawo ka asibitin nan ba shiyasa kake wannan ɓoye-ɓoyen, badon ikon Allah ba da yanzu mun jima da yin sadakan bakwai naka saura sadakar arba'in." Guntun murmushi Sadeeq yayi, yana jin ko ba su yi ba ma suna daf da yi, a fili kuma ya ce, "Thank God for his miracle and ina da sauran numfashi na, so ka daina damun kanka lafiya lau ba komai kawai stress ne, amma am okay now as you can see, waɗannan likitocin ma ya kamata su sallameni." "Wallahi Sadeeq renin hankalinka yana da yawa, to ko ka faɗa mini me ke damunka ko kar ka faɗa mini duk ɗaya, domin zan gano ko ma menene i promise you this, and you know me very well, when it come's to investigation, bana wasa sai na binciko duk abinda na sanya a gaba." Sadeeq lumshe idanuwanshi yayi tare da cewa, "Am okay malam." "Huh! Kana son wacce ke shirin auren wani ne kake a lafiya? Kana ɓoye ƙaunar wacce kake da cikakken iko da ita ne kake lafiya? Ko lafiya ne zai sanya ka nemi kashe kanka bayan ka san mahaifiyar wacce kake ƙoƙarin kashe kanka a kanta, a matsayin jininta ta ɗaukeka? Ɗan cikinta da za ta iya mishi komai ta mallaka mishi komai, wannan ne lafiya? Ko lafiya ne zai sanya ka ci amanar abotar wanda ya ɗauke ka a babu na biyunka a duniya? Sam-sam ba ka da lafiya Sadeeq, kuma zan tabbatar maka da haka", Umar ya faɗa zuciyarshi na ƙuna, domin indai hasashen shi gaskiya ne, to Sadeeq bai kyauta mishi ba, bai kyauta wa Mama ba balle kuma Sadiya da kanta da take mutuwar son shi. Wani irin bugu zuciyar Sadeeq ta yi, har sai da ya buɗe ido tare da tashi zaune, kallon Umar yayi, amma yana ganin wani irin kallon da Umar ke jifarshi da shi ya kau da kai, zuciyarshi na bugawa da sauri matuƙa, cikin rarrabewan magana ya haɗo kalmomin bakinshi tare da cewa, "what..did.. you ..mean? Me kake nufi Umar?" Umar da ke kan kallon Sadeeq rai a haɗe, cikin harzuƙa da gajiya da renin wayon Sadeeq ya ce, "Ina nufin abinda ka ji, kuma abinda ka ke riƙe da shi a zuciyarka, ina nufin abinda kake ɓoye mini ni da kowa ma, hmmn! Sadeeq kenan." Sadeeq cikin son danne abinda yake ji a zuciyarshi da bugun da zuciyarshi ke yi ya ce, "Enough Umar, bana nufin komai lafiya nake." "Soyayyar Sadiya da ke shirin auren Aliyu ba zai barka ka kasance a lafiya ba." Wani irin kallo Sadeeq ke jefawa Umar, yayin da shi ma Umar ɗin ke jifan Sadeeq da kalar nashi kallon rai a matuƙar ɓace. Sadeeq a dake, a taƙaice ya ce, "Look Umar.... *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD @Uwarbatoorl96 ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 💔NAUYIN BAKI....👄💔        Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠     اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 25 _ 26 ⭐️ Sadeeq ya ce, "look Umar, ba na son irin wasan nan, na rasa wacce zan so sai Sadiya ƙanwarmu? Sannan ma idan ina sonta me zai hanani sanar maka ko ita ɗin? Haba Umar..." Umar katse Sadeeq yayi ta hanyar cewa, "Abinda nake ta lissafawa ina tunawa kenan, kana son Sadiya me zai sa ka ɓoye ko ka ƙi faɗa mini? Sadiya fa taka ce ƙanwarka ce, me zai sa har ka kasa sanar mata ita ma?" Guntun dariyar da ya fi kuka ciwo Sadeeq yayi, domin kana ganin dariyar ka san ba daga zuciya bace, ta son danne damuwa ce, a dake ya ce, "Dole ka lissafa Umar, how on earth will you even think about this? How it's be possible ka ce Sadiya nake so? Ko kana da hujja ne?" "I'll make sure that i give you a surprise Sadeeq, zan baka hujja kuwa, this is my promise", iya haka Umar ya faɗa ya gyara yayi kwanciyarshi.    Sadeeq ma kwantawar yayi, amma da matuƙar mamakin har me ya kawo wannan zargin a zuciyar Umar? Ko de yayi making move ɗin da ya fallasa abinda ke zuciyarshi ne without his knowing? In ba haka ba ya aka yi Umar yayi wannan maganar? Tunane-tunanen da Sadeeq ya dinga yi kenan, har baccin da ya fi kowa iya sata ya sace shi. Umar kuwa mamakin ƙarfin hali da zuciya irin na Sadeeq yake yi, domin from his look, word's and even his sound, sun nuna alamar tabbaci ga zarginshi, amma dai tunda ya tambayeshi hujja, to zai tabbatar da ya mishi presenting na hujjarshi zuwa gobe ma kuwa da yardar Allah, shi ma Umar da wannan alwashi bacci yayi gaba da shi. Washe-gari da safe bayan sun idar da sallar asuba, ya kwanan jikinshi kawai Umar ya tambayeshi, daga haka ya fice a ɗakin, har likita ya shigo duba jikin Sadeeq ɗin Umar bai dawo ba, shi ne bai shigo ɗakin ba sai da su Khalid suka iso sannan ya shigo tare da su, nan ma bai yi mintuna talatin masu kyau ba ya fice, motarshi ya ja yayi gida, bai tsaya gidan Mama ba, kai tsaye gidan su Sadeeq ya wuce dan duk tunaninshi anan Khausar ta kwana. Horn yayi mai gadi ya buɗe mishi ya shige, mai gadin ɗaga mishi gaisuwa yayi ya amsa, sannan ya parker motar a ma'adana motoci ya fito ya nufi cikin gidan, da sallama ya shiga palourn, Umma da Abba suka amsa mishi, kasancewar ranar Sunday ce to ba zuwa wajan aiki, Abba na gida zai huta, Sa'ad da Khalid kuma suna asibiti wajan Sadeeq. "Ah! Umaru har an taho kenan? Ma sha Allah,  Rabbi ya muka albarka Umaru, Allah ya ƙara haɗa kawunanku ya bar zumunci, hidima da kake da Sadeeq sai dai Allah ya saka maka da mafificin alkairinshi", Abba ya faɗa cikin tsantsar jin daɗi da godiya ga Allah, da yaronshi Sadeeq yayi dacen aboki kuma Amini irin Umar. "Amin dan Nabiyur-rahmati, ai Umar ba mai saka mishi sai Allah, kirkin Umar ko Sadeeq bai da shi", Umma ma ta faɗa hakan cike da alfahari da zumuntar su. Umar cikin girmamawa yayi ƙasa da kai, yana godiya ga Allah da haɗuwar zumuncinsu da waɗannan bayin Allah, a duniya duk kirkin da zai yiwa Sadeeq ko su Abba, ba zai taɓa yi musu rabin abinda suka musu na alkairi ba a rayuwa, Allah ne mai mutan-mutani, to su Abba suna cikin gun-gun mutanen kirki da Allah ya yi a doron ƙasa, "Barka da Safiya Abba, fatan an tashi lafiya? Ya gajiyan aiki? Fatan jiya kun dawo lafiya?" "Lafiya Alhamdulillahi Umaru, gajiya kuwa kai ne da gajiya ai, kai ne asibiti, kai ne gida, kai ne company, ranan Sa'adu ya ce mini har wajan nashi aikin ka leƙa, nasan ka je duba ko yana shirme ne, Allah dai yayi albarka Umaru, amma ya kamata yau Lahadi ka wuni a gida ka huta." "Ma sha Allah, Allah ya ƙara lafiya da abinda lafiya za ta mora Abba, in Allah ya yarda zan wuni a gida kaman yadda ka ce, Allah ya sa kar buƙatar fita ya

Chapter 14 of 32