tashi."
"Amin Umaru yaron kirki."
"Umma barka da safiya, ya ayyuka ya kwanan baƙin Abuja?"
"Alhamdulillah Umar, baƙin Abuja kuwa suna can wajan Maman Sadeeq, dan ko Abbanku bai gansu ba har yanzu."
"Wai a can suka kwana dama? Na ɗauka a nan ne fa shiyasa na zo nan kai tsaye, dan na duba su."
"Kar ka ce mini dai daga asibitin kake yanzu haka?" Umma ta tambaya cikin kulawa.
"Eh Umma, yanzu dawowana kenan na shigo nan dan na duba su kamun na wuce na huta."
"Allah ya maka albarka Umar, Allah ya baka ladan zumunci, zo nan ka zauna ka karya, khausar kam ba jimawa na san za ta shigo ita da fitinannun yaranta, kwana ne daman dole sai gidan Maman Sadeeq, ita za ta iya da fitinarsu ni ba zan iya ba, dama Sadiya ce auta kuma ita ma shirin aurar da ita nake, ai ba ni ba ƴan dugui-duguin yara, kowa ya riƙe kayansa ba ruwana da jikoki."
"Kishi dai kike Halimatu, kin ga yara kaman yaran turawa", faɗin Abba.
Umma taɓe baki tayi tare da cewa, "To muma ai da haskenmu sai godiya, haske irin nawa ma shi ne daidai, nasu ya wuce daidai yara kaman na masu jajayen kunnuwa."
Umar yana ƴar dariya ya ƙarasa kan darduman da Abba ke zaune, daga gefe ya zauna, Umma na ƙoƙarin saka mishi abun karyawan, sai Abba ya ce, "A a, Halimatu bar shi mu ci tare, saka hannunka mu ci ko Umaru."
"Cikin girmamawa Umar yayi ƙasa da kai, tare da wanke hannunshi ya saka a kwanon Abba suka soma ci tare.
Umma sai kan mita take, sai da Abba ya ce ta ƙyalesu haka su karya, su bi dokar shiru ta cin abinci, sannan Umma ta yi shiru, miƙewa tayi ma ta haura sama.
Kusan a tare Abba da Umar suka cire hannu a kwanon, duk wanke hannu suka yi suka sha ruwa, sannan Umar ya muskuta tare da cewa, "Abba ku yi haƙuri fa, har yanzu ina kan bincikan abinda yake ɓoye mana ne, in sha Allah in dai na gano zan sanar da ku a kan lokaci."
"Ba komai Umar, Allah ya taimaka Allah yayi albarka, ni kam ai tunda na tuntuɓe shi ya nuna mini ba komai, Ummanku da Mamanku ma duk suka tambayeshi amma ya ce ba komai, tuni na ce su ƙyale shi, kowa ya fita harkarshi idan tayi tsami ma ji."
"Ba za tayi tsami ba ma Abba, da yardan Allah zan bincika kuma zan sanar da ku."
"To Umar, muna saurara, Allah kuma ya sa mu ji alkairi."
"Khairan in sha Allah Abba."
"Amin Ya Rabbi."
⭐️
RAYFIELD
SADIYA POV
***
Sadiya suna game da Najla a wayarta har aka ƙira isha'i, tashuwa suka yi tare suka shige banɗakin da ke ɗakin Sadiyar, suka ɗauro alwala suka fito suka yi sallah, ba su jima da idarwa ba Haidar ya ƙira, cikin shauƙi da bege suke waya cike da ƙaunar juna, da kuma fatan wannan sati ta zago cikin aminci, su mallaki juna.
Najla rikici ta sanya kan cewa sai Sadiya ta bata waya, ita ma za tayi waya da uncle H, da yake Haidar na jiyo rigimar Najla sai ya ce da Sadiya ta bata wayar, ba musu Sadiya ta miƙa wa Najla waya, ita kuma ta miƙe ta fice, ɗakin Mama ta nufa, da sallama ta shiga bayan Mama ta amsa ta bata izinin shigowa.
Idanuwanta ta fara baza wa a ɗakin na son ganin ta ina Khausar za ta ɓullo, ganin babu ita a ko wani kusurwa na ɗakin, sai ta ce, "Mama ina Aunty? Ko tana banɗaki ne?"
"A a, sun fita da Yayanki Umar, zai kai ta, ta samu ta dubo jikin ɗan uwanta.'
Rausayar da kai Sadiya tayi, tana jin wani abu a zuciya, ina ma ita ce aka yiwa wannan gata na a kaita ta dubo Yaya Sadeeq, lallai wannan lalura tata bata kyauta mata ba ko kaɗan.
Sai da ta numfasa sannan ta ce, "Amma ai Mama ba kwana a can za tayi ba ko?"
"Wani kwana kuma ni Rabi bayan ga Umar, lokacin da mai babbban sunan ma bai san wa ke a kanshi ba, Umar ke fama ya hana mu wuni balle kwana, inaga yanzu kuma da mai babban suna ya ke a hayyacinshi, ana saka ran samun sallama a kwanakin nan."
Wani irin farin ciki ne ya lulluɓe Sadiya, jin batun za a yi discharge na Yaya Sadeeq, hakan ya sanya ta washe baki, tare da addu'an Allah ya ƙara mishi ƙarfin jiki, a sallameshi gobe-goben nan.
Da Amin Mama ta amsa, sannan Sadiya ta ce, "wa zai dawo da Aunty Khausar fa?"
"Khalid zai dawo da ita", faɗin Mama cikin gajiya da tambayoyin Sadiya.
Sai da Sadiya ta kuma yin tambaye-tambayenta, sannan ta juya ta koma ɗakinta, ta samu Najla sun gama waya da Haidar har ta katse ƙiran, Sadiya girgiza kai kawai tayi tare da sanya mata albarka, wayar ta ɗauka tare da ƙiran ƙawarta Zahra akan ta shigo gobe, sai da suka yi sallama sannan ta aje wayar ta shige toilet, ko kamun ta fito har Najla tayi bacci, hakan ya sanya tana fitowa ta wuce kai tsaye ta gyara wa Najla kwanciya, ta tofe su da addu'an bacci, ta wuce ita ma tayi shirin kwanciyar.
Wayarta ta ɗauka tare da aika wa Haidar ƙira tana kwanciya, ringing guda yayi ya katse tare da ƙiranta, ta ɗauka ta yi sallaman da zazzaƙar muryarta, shi kuwa ya amsa cikin murya mai amo da ɗumbin ƙaunarta, akan shirye-shiryen bikin suka yi magana, sannan ya sanar mata za a kawo lefe a satin, kuma zai kawo mata IV, duk Allah sanya albarka tayi tare da addu'an a kawo lafiya.
Khausar da sallama ta shigo gidan, sai da ta kulle ko ina sannan ta wuce ɗakin Mama, "Assalamu alaikum", ta yi sallama a sanyaye.
Mama daga ciki ta amsa, "Wa'alaikissalam shigo mana Khausar, har kun dawo kenan?"
"Eh mun dawo Mama", ta faɗa yayin da take shiga ɗakin.
"Ma sha Allah, ya jikin nashi?"
"Da sauƙi sosai Mama, yana gaisheku ma."
"To madallah da mai babban suna, muna amsawa, amma ya naga yanayinki haka? Ko dai wani abun ne?"
"A a, ba komai Mama, kawai gajiya ce", Khausar ta faɗa cikin son ɓoye abinda take lissafawa ita ma.
"Ai kam dole ki gaji Khausar, tunda kuka zo baki huta ba, sai ki je ki samu ki watsa ruwa ki kwanta a huta, yaran nan nasan sun yi bacci tunda na jisu shiru, dan daman bai jima ba Sadiya ta zo duba ki."
"To Mama, mu kwana lafiya."
Mama ta ce, "Allahu ya sa Khausar, Allahu ya hutacce ku gajiya"
"Amin Ya Rabbi Mama", daga haka ta juya ta fice.
Da kallo Mama ta bi Khausar ɗin, tana lissafin ko yanayin jikin Sadeeq ne, ya sanya jikinta yin sanyi, "a hakan ma wai dan baki kalleshi lokacin da yake maƙale da na'urori ba, ai dai mun ga abu kuma bama fatan sake ganin irin haka, a kan kowa ma balle a kan mai babban suna, Allahu dai ya sa a sallamo shi zuwa gobe", faɗin Mama a fili, sai da ta gama jimamin lamarin sannan ta yi duk abinda za tayi ta kwanta.
Khausar da sallama ta shiga ɗakin Sadiya, wanda Sadiyar na jin sallaman tayi wa Haidar sai da safe ta katse ƙiran, tare da amsa sallaman Khausar tana cewa, "Sannu da dawowa Aunty."
"Yauwa small Mum, sannu da ƙoƙari, na barki da rigimammun nan ko."
"Ba komai aunty, ai sun jima da yin bacci ma, nima ke nake jira da nayi baccin."
"To yi baccinki amarya mai maganar sugar, nima bari na shirya na kwanta duk na gaji."
Sadiya miƙawa Khausar nata kayan baccin tayi, Khausar ta amsa ta shige toilet, sai da ta watsa ruwa mai zafi sannan ta shirya ta fito, basu tsaya wani hira ba suka bi lafiyan gado, tare da yin addu'an bacci, ba jimawa bacci yayi gaba da Sadiya, ita kuma Khausar sai da ta tsaya lissafe-lissafe da Tunane-tunanenta sannan ɓarawon bacci yayi gaba da ita.
Washe gari bayan sun yi sallahn asuba, Khausar bacci ta koma, Sadiya kuma ta fice dan musu abin kari, Mama ta hanata ita tayi da kanta, sai wanke-wanke da ƴan share-share kawai Sadiya tayi, zuwa bakwai sun kammala komai, Mama ta ce da Sadiya, "Je ki taso su, suzo su karya ku samu ku wuce wajan Umman taku."
"To Mama", faɗin Sadiya da ta juya ta nufi ɗakinta.
Ta samu Najla kam ta tashi idonta biyu, Nayla da khausar ne suke bacci, tashin Khausar tayi tare da sanar da ita abinda Mama ta ce, khausar ta tashi zaune tana karanto addu'an tashi a bacci, sannan ta ce, "Ai gaskiyan Mama, kin ga jiya tunda muka taho bamu leƙa su ba, bamu haɗu da Abba ba", ta ƙarishe maganar tare da tashin Nayla, ita ma cikin gwalantinta tayi addu'an tashi a bacci, Sadiya ta tusa su a gaba ta musu wanka ta musu brush, daman Najla tayi sallah tare da su Sadiya da Asuba, Nayla kuma yanzu ana gama mata wanka ta yi alwalanta na shirme wai za ta yi sallah, Najla na dariya ta ce, "You're late fa baby Nayla, seven ta yi."
Nayla tura baki tayi ita sai ta yi sallah, haka ta tsaya a kan darduma ba hijabi tayi sallahn wanda koyo take, sai da ta idar sannan Sadiya ta shiryata ita ma dan ta gama da Najla, Khausar ma fitowarta toilet kenan ta watsa ruwa, shiryawa tayi, Sadiya ma ta fito toilet ta shirya sannan suka fita palourn.
Da Khausar da yaran kaf gaishe da Mama suka yi, tare da yi mata sannu da aiki, Mama ta amsa tana tambayarsu fatan gajiya ta warware.
"Alhamdulillahi ba gajiya Mama", Khausar ta faɗi tana murmushi.
Najla ta ce, "granny bamu gaji ba ai."
"To madallah haka ake so", Mama ta faɗa tana ƴar dariya.
A tsakiyar palourn suka zazzauna suka karya, bayan sun kammala Sadiya ta tattare komai Najla na taya ta, sai da ta mayar da komai kitchen, ta kuma tsaya ta wanke abubuwan da suka ɓata, sannan ta fito ta ɗauki Nayla, ta riƙe hannun Najla, Khausar ta tashi suka yi wa Mama sai anjima suka fice a gidan.
Da sallama suka shigo palourn, Abba da Umar suka amsa musu, Abba na washe baki cikin farin cikin ganin ƴar ta shi da jikokinshi ya ce, "Lale maraba da amarena."
Najla da gudu ta ƙarasa jikin Abba, Nayla ma yanzu kam har da ita, Sadiya ta sauƙeta ta ƙarasa, duk suka rungume Abba suna faɗin, "oyoyo."
Sadiya zama tayi a ƙasa daga gefe, domin su Abba ma a ƙasan suke zaune har yanzu a kan darduman.
"Ku ɗaga mini uba kar ku ƙarasa mini shi", faɗin Khausar da ta isa ga Abba ita ma, daga gefenshi ta zauna.
Abba na ƴar dariya ya ce, "Barni su ƙarasa ni Auntyn Abba, ai daman saurane ni, su nake jira, kuma tunda sun zo duniya har na gansu, ai alhamdulillah sai addu'an Allah ya sa mu tafi a sa a."
"Amin Abba", Umar ya faɗa a sanyaye.
Khausar ta ce, "Da saura fa Abba, ga na Yaya Sadeeq, Uncle U, Sa'ad, Khalid ga small Mum duka, ai duk su ma da yardan Allah sai kun ga nasu yaran, dan haka kar su ƙarasa mana kai dan su sun ganka."
"Allah ya muku albarka, fatan kun zo lafiya? Ya kuka baro mai gidan da sauran jama'a?", faɗin Abba yana dafa kan Khausar, fiskarshi yalwace da murmushi, domin soyayyar Abba ga Khausar na daban ne kaf cikin yaranshi, Abba mutum ne mai son ƴaƴa mata, sai kuma Allah ya bashi maza har uku mace ɗaya, shiyasa Abba ke ƙaunar Sadiya kamar ƴar da ya haifa.
"Amin Abba, duk suna lafiya suna gaidaku", Khausar ta faɗa cikin ƙaunar mahaifin nata.
"Gaisuwa ya iso, kuma mun amsa, madalla, sannunku ko, auta ƙaraso nan ki gai da Abba kema", Abba ya faɗa yana yi wa Sadiya nuni da ɗaya gefen nashi.
Miƙewa Sadiya tayi kanta a ƙasa ta koma ɗaya gefen Abba ta zauna tare da cewa, "Barka da safiya Abba, fatan antashi lafiya? Ya gajiyan aiki? Ya jiki jiki mai daɗi?"
Abba dafa kan Sadiya yayi ita ma da ɗaya hannunshi, sannan yana murmushi ya ce, "Duk alhamdulillah auta, jiki sai godiya, ya kwanan yaranki da auntynki? Fatan sun iso lafiya?"
"Alhamdulillahi Abba", Sadiya ta amsa cikin girmamawa.
"To ma sha Allah, Rabbi ya muku albarka, Allah ya raya ku ya tabbatar da duk alkairan rayuwarku, Allah ya albarkaci zuri'arku da kuke da da waɗanda za ku samu nan gaba, Allah ya sa ki shiga gidanki a sa'a, Allah ya sa sai mutuwa za ta raba ku, duk ya ƙara muku zaman lafiya a gidajenku, rayuwa da mutum ƴar haƙuri ce, balle kuma rayuwar aure, sai kuna haƙuri ko, Allah ya baku lada ya baku aljanna mu da ku duka dan isar Annabi SAW.
"Sallallahu Alaihi Wasallam", duk su ukun suka haɗa baki wajan amsawa, har ma da Najla da Nayla.
Khausar mai da dubanta ga Umar tayi tare da cewa, "Barka da safiya uncle U, fatan andawo lafiya? Ya mai jiki?"
Umar amsa wa khausar gaisuwan yayi, sannan Sadiya ma ta gaishe shi ya amsa mata, su Najla ma suka gaishe shi ya amsa.
Khausar ta ce, "Ina Umma fa?"
"Ummanku tana ɗaki", Abba ya bata amsa.
Khausar da Sadiya miƙewa suka yi, suka nufi upstairs wajan Umma, Umar cewa yayi, "Sister in kin fito ina jiranki a sashin Sadeeq."
"To uncle U", Khausar ta amsa mishi.
Da sallama su Sadiya suka shiga ɗakin, Umma da ke kimtse-kimtse ta amsa musu tare da cewa, "An samu shigowa kenan? Ina rigimammun?"
Sadiya zama tayi a bakin gado, Khausar ta zauna a stool na mirror, Sadiya ta ce, "Umma rigimammu suna can suna baza wa Abba rigima mai capacity."
"Rigima mai fakasiti dai, mijina ba abinda zai yi da su."
"Shikkenan ai Umma, idan ya bi su Abuja babu ruwanmu."
"Ko ya bi su ma zai dawo", faɗin Umma da ta kammala abinda take yi.
"Ina kwana Umma."
"Lafiya Alhamdulillahi Khausar, ya gajiya-gajiya?"
"Gajiya ta bi lafiya Umma."
"Ma sha Allah, ashe jiya Umar ya kai ki asibiti, haka dawowan Khalid yake faɗa mana tare kuka dawo."
"Eh Umma."
Umma ta ce, "Kada ki wani damu kanki, ai ya ji sauƙi ma, in sha Allah muna sa ran za a sallamoshi a kwanakin nan."
"Allah ya amince."
"Amin Ya Rabbi."
"Bari na je uncle U na jirana za muyi magana", Khausar ta faɗi tana nufar ƙofa.
"To ku magantu lafiya, ke da Umar ai ƙus-ƙus naku baya ƙarewa."
Khausar na dariya ta fice, sannan Sadiya ta gaishe da Umma ta amsa, Umma ta ce, "Maza mu je a yi gyaran yau."
Sadiya ba musu ta miƙe tare da wucewa toilet, kayan jikinta ta cire ta ɗaura towel sannan ta sanya zumbulelen hijabi ta fito, tare suka fice da Umma, ɗakin da suke gyare-gyaren suka shiga, Umma ta zage ta cigaba da gyara ɗiyarta, abubuwan da take bata ta sha dangin maganin sanyi da sauransu duk ta bata, sannan ta aje wa Khausar saura ita ma ta taɓa.
Khausar tana sauƙowa ƙasa ta samu Abba da su Nayla, suna ta cika shi da surutu yana biye musu, labarai suke kallo a tashar bbc, duk abinda aka ce sai sun tambayi Abba ƙarin bayani, shi kuma sai ya amsa musu.
"Abba suna ta cika ka da surutu", faɗin Khausar da ke ƙoƙarin bin hanyar da zai sada ta da sashin Sadeeq.
"Tambayoyi suke mini nake basu amsa, musamman Najla, kinga kuwa idan tana da wayon riƙe amsar, to za su amfaneta a gaba", faɗin Abba, wanda kuma haka ne, ilimi da sanin tarihi na ga kakanunmu da iyayenmu, sai kuma bincike ta hanyar karanta tsoffin takardun tarihi a ma'adana takaddu(libraries).
Khausar a tashi lafiya ta yiwa Abba sannan ta shige, ƴar corner ce da za ta sada ka da corridor madaidaici, sai ƙofan palourn Sadeeq, palournsa haɗaɗɗe ne kuma mai girma, akwai dinning area saboda Sadeeq ma'abocin cin abinci a sama ne, ba kasafai yake cin abinci a ƙasa ba, akwai kitchen madaidaici a palourn, wanda ba wai a gine yake kaman ɗaki ba, kitchen cabinet ne kawai a wajan da sauran abubuwan buƙata, wajan a zagaye da glass kana palourn za ka hangi kitchen ɗin, kuma duk abinda mutum ke yi a kitchen ɗin za ka gani daga palourn, dan ba girki yake ya dafa abinci ba, shayi da coffee kawai yake haɗa abinsa a wajan, domin ba zai iya har ya je kitchen na Umma ba, bai da ƙanwa mace balle ta ke kawo mishi, dan Khausar rabin zamanta a Abuja ne wajan takwararta yayar Abba, ƙannenshi maza kuma duk stabgarsu suke, Umma kuma ɗakinta a upstairs yake balle ta ɗauki nauyin kawo mishi, hawa da sauƙa aiki ne, shiyasa yake da keɓataccen kitchen nashi a sashinshi.
Ɗakuna uku ne a sashin, ɗakin gym nashi, sai ɗakin karatu wanda yake kaman ɗan uwan library kaman office, a ciki yake wasu ayyukanshi da zane-zanenshi da duk abinda ya shafi aikinshi ko karatu, sai kuma ɗakin baccinshi, sashin Sadeeq ya haɗu matuƙar haɗuwa.
Da sallama Khausar ta shigo palourn, wanda yake tsaf-tsaf sai tashin ƙamshi yake yi, dan Umma da kanta take zuwa ta gyara mishi sashen nashi, Sadeeq mutum ne mai tsafta sosai-sosai.
Umar da ke zaune a ɗaya daga cikin attajiran kujerun da ke palourn yana danna wayarshi, amsa sallamar Khausar yayi, ta samu waje ta zauna, suka sake gaisawa sannan duk suka yi shiru, sai da Umar ya kammala abinda yake a waya sanna ya kashe ta ya ajiye, cikin nitsuwa da dukkan hankali ya ce, "Ina muka kwana da maganar jiya? Kin fahimci wani abu saɓanin wanda kika faɗa jiya?"
Ajiyan zuciya Khausar ta sauƙe, sannan ta ce, "Uncle U, na kasa yarda da abinda zuciyata ke lissafo mini, bayan duk bayanin da ka mini, da kuma bayanin da Khalid ya mini game da small Mum da halin da take ciki, wanda har a yanzu da take ƙoƙarin nuna ba komai, muddin mutum ya mata farin sani to ya san akwai komai tana dannewa ne kawai, kuma na fi tunanin Umma ce ta shawo kan hakan, dan Mama ko ta small Mum ɗin bata yi."
"Me zuciyar taki ke lissafo miki?", Umar ya tambaya cike da fatan kar ya zamana shi kaɗai yake wannan zargin, domin wani sashi na zuciyarshi na faɗa mishi kamar gaskiya Sadeeq ya faɗa ba komai, tunda har yana iya dubanshi ya ce ya ba shi hujja, kamar da ƙamshin gaskiyarshi.
Khausar ta ce, "Uncle U, duk da dai kowa ya san irin shaƙuwa da ke tsakanin Yaya Sadeeq da small Mum, shaƙuwa ce ta haƙiƙa da ƙaunar juna wacce muke mata kallon ta Yaya da ƙanwa ce kawai, daga mu kuma har su a tunani na haka muke kallo, sai dai kuma ashe daga mu har su ɗin bamu sani ba, zuƙatarsu ba a iya ƙaunar Yaya da ƙanwa ta tsayar da su ba, zuciyoyinsu na ƙaunar junansu ta muradin kasancewa abokanan rayuwan juna, suna ƙaunar junarsu ƙauna ta masoya ba tare da sun sani ba ko sun ankara, kuma ga shi a wannan mataki da ake ciki Allah ne kawai ya san menene mafita."
Umar murmushi yayi mai ciwo na abinda Sadeeq ya aikata, sannan ya ce, "Kin fahimci abinda nake son ki fahimta, domin na tabbatar da abinda nake zargi kada ya kasance ni kaɗai nake zargin hakan, sai dai kuma sister mu ne kawai bamu san da ƙaunar ba, wataƙila da ita Sadiya, amma shi Sadeeq ya san da ƙaunar da yake yiwa Sadiya ta masoya, amma ya ɓoye, har ya shige gaba aka bai wa Haidar ita, ya shige gaba aka yi shirin aure da komai, at the end ga shi ya kasa jurewa, soyayyar ta ka da shi yana neman mutuwa ya sanya mutane asara, am still wondering what on earth Sadeeq is trying to do? Na kasa yarda na kasa fahimta, shakku da mamaki sun ƙi barina sister, hujja nake son na gani ƙuru-ƙuru da idanuwana, amma na rasa ta yaya kuma a ina? Ga shi Sadeeq denying yake kan cewa ba haka ba, he even told me to prove my evidence akan haka......", yanda suka yi jiya ya kwashe ya faɗa mata.
Murmushi mai mamaki ita ma Khausar ɗin tayi, sannan ta ce, "Biri yayi kama da mutum, uncle U, ni bana buƙatar hujja ma wallahi, Yaya Sadeeq soyayyar masoya ta aure yake yi wa small Mum ba iya ta Yaya da ƙanwa ba."
"Hujjan yana da amfani sister, domin ta haka ne za mu titsiye shi, sannan a sanar da su Abba mu san me ake ciki kar lokaci ya ƙure, Sadeeq bai da hankali zai cigaba da denying ne idan ba hujja, i know him very well kema kuma kin san shi."
"Amma tsakani da Allah yaushe Yaya Sadeeq ya fara ƙaunar small Mum? Anya ba bayan an tsayar da maganarta da Haidar bane ya fahimci shi ma sonta yake?"
"Bana tunanin haka sister, domin ba zai yi haka ba tunda ya san is not good, na fi tunani before hakan ne, amma dalilinshi na ƙin faɗa nake son ji, dalilin shi na tsaya wa Haidar ma ina son ji, me ma zai sa duk yayi haka? Kuma yaushe ma ya fara yiwa wannan shirmammiyar irin wannan soyayya? Meyasa ya ɓoye mini bayan bama ɓoyewa junanmu ko wani irin sirri?"
Numfasawa Khausar tayi tare da cewa, "Dole to akwai hujja, za a samu hujja uncle U, mu bincika da kyau, kai ka duba ɗakin ayyukanshi, ni na duba bedroom nashi, domin ɗakin gym nashi bana tunanin za mu samu komai a can, tunda kai ma kana shiga, ai da za ka ci karo da wani abun."
Umar jinjina kai yayi tare da cewa, "Hakan za a yi, dan yau ba zan koma asibiti ba sai dare, kuma so nake na tafi mishi da hujja, gobe Monday da yardar Allah, shikkenan kuma an shige week na bikin, duk yadda za a yi dai bana son lokaci ya ƙure."
Khausar miƙewa tayi tare da nufar ɗakin Sadeeq, da sallama ta shiga, ko ina tsaf-tsaf, tsayawa tayi a tsakiyar ɗakin tana duba ta ina ya kamata ta fara.
Kai tsaye bedside drawers nashi ta nufa, ta buɗe ta birkice abubuwan da ke ciki amma babu komai, ta koma side na mirror, drawern nan ma ba komai, ƙasan gado ta koma ta duba, katifa ma ta ɗage ta duba, duban gaske ta cigaba da yiwa ɗakin, amma ba wasu tarkace da za a ce mutum ya ɓoye wani abu a ciki, closet nashi ne abu na ƙarshe da ta duba, ba komai ciki sai wani madaidaicin box a rufe, sai an saka code ake buɗewa, kasancewan bata samu komai ba da take nema, sai ta ɗauko box ɗin ta fito da shi ta san may be wani abu mai muhimmanci ne a ciki, wataƙila ma su samu hujja a ciki.
Umar ya bincike ɗakin ayyukan Sadeeq tass, duk da dama ɗakin ba baƙonshi ba ne, bai samu komai ba, sai dai akwai drawer guda ɗaya da ke kulle, kuma sama ƙasa babu key, hakan ya sanya ya ƙyale ya fice a ɗakin, gym room nashi ya shige, nan ma dai ba baƙonshi ba ne, ya bincike tass amma a nan ya samu ƙaramin frame na photon Sadiya, ɗauka yayi tare da jujjuya shi a hannunshi, kamar zai ajiye sai kuma ya fasa ya fito da shi.
Sun ɗau lokaci sosai a bincike-bincikensu, ko da Umar ya fito Khausar ma ta fito, duk waje suka samu suka zauna, Umar ya miƙa wa Khausar frame ɗin yana faɗin, "Ga iya abinda na samu, and na san Sadeeq zai kare kanshi a kan wannan frame ɗin."
"Wataƙila a cikin box nan kuma a asamu abinda ba zai iya kare kanshi da shi ba", Khausar ta faɗi tana miƙa wa Umar box ɗin.
Amsa yayi tare da ƙarewa box ɗin kallo, sannan ya murmusa yana jin tabbas dai ba za a rasa abu a ciki ba, code ɗin ya fara gwadawa, «Waziri», abinda ya fara gwadawa, sannan ya gwada sunan Sadeeq duka, ya gwada date of birth na Sadeeq amma dukka ba daidai ba.
Khausar ta ce, "To ka gwada sunan small Mum mana."
«Sadiya», «Halima», duk Umar ya gwada amma bai buɗu ba, date of birth na Sadiya ma bai buɗe ba, numfashi mai nauyi Umar ya sauƙe tare da cewa, "Me kike tunanin zai saka?"
"Nima sunanta nake tunani dama, kuma ga shi bai yi ba, amma miƙo na gwada ko zai buɗu.
Umar miƙa mata box ɗin yayi ta amsa, amma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 32