Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta sake fa, auren nan fa yanzu kwanaki ne kawai suka rage, bai kyautu ba sam jama'a su fara zuwa tana a irin wannan yanayi, balle kuma ayi auren tana a haka, ni wallahi na rasa ma tsakanin ita da Yaya Sadeeq ɗin wa na fi tausaya wa, gaba ɗaya ta damu da Yaya Sadeeq sosai, ta yacce har nake ganin ƙoƙarin Haidar, in da ace shi ba mutum mai fahimta bane ai da sun dinga samun damuwa a kan yanda ta ke damuwa da lamarin Yaya Sadeeq ɗin nan, ni wallahi har shi Haidar ɗin ma tausayinshi nake ji, duk su ukun tausayi suke bani." Umma wani nauyayyan ajiyan zuciya take sauƙe kawai, bata ce ƙala ba, domin ita ma akwai abinda ke damunta a zuciya amma sai gani da ido kawai, lamarin ne na yaran sai addu'a da fatan Allah ya shige musu gaba. Sa'ad jin Umma tayi shiru, ya kuma cewa, "Umma a dai duba lamarin Sadiya dan Allah, in har jikin Yaya Sadeeq ya ɗan ji dama-dama,  to kawai a dawo gida ya ƙarisa jinyan, idan ba haka ba da alama, ba za a gane kan Sadiya kuma shi yana asibiti ba." "Allah ya shige mana gaba kawai", faɗin Umma tana miƙewa ta wuce dinning. Da, "Amin", Sa'ad ya amsa yana mai cire wayarshi a key ya kunna data tare da yin baya ya jingina da kujera, ya shige WhatsApp nashi. Umma abinci ta saka wa kanta ta ci, sai da ta kammala tayi hamdala, sannan ta saka wa Sadiya ta nufi stairs, Sa'ad ya taso da sauri ya amshi plate ɗin yana faɗin,  "Umma bari na miƙa mata." Umma jinjina kai tayi tare da rufa mishi baya suka haura saman tare. Sadiya tana haurawa stairs ɗin ta shige ɗakin Umma da sallama, a can kan mirror ta hangi wayarta, hakan ya sa ta wuce kai tsaye ta ɗauki wayar sannan ta koma kan gado ta kwanta ba tare da ta cire hijabin jikinta ba, layin Haidar ta laluɓo ta aika mishi da ƙira bata ma tsaya duba tulin miss calls da aka mata ba, domin ta san kaso casa'in cikin ɗari duka zai kasance daga Haidar ɗin ne. Ringing guda ma bai gama cika ba Haidar ya ɗau ƙiran, domin wuni yayi yana bulayin nemanta a waya, ga shi ayyuka sun riƙe shi matuƙa bai samu daman zuwa har gida ba, hakan ya sanya ya wuni kaman mara lafiya, "Al-Sad, Are you alright?" Abinda ya fara faɗi kenan ba tare da ya ko tsaya yin sallama ba. Wani tausayin Haidar da soyayyan shi ne suka ƙara damalmale mata zuciya lokaci guda, anya ta yiwa kanta adalci kuwa? Ta yiwa Haidar adalci? Ta yiwa soyayyarsu adalci?... "Are you there? Is everything okay?", tambayan da Haidar ya kuma jeho mata kenan jin tayi shiru, kuma tambayan ne ya katse mata zancen zucin da take yi. Ajiyan zuciya ta sauƙe, cikin ƙarfin hali da son nuna mishi ba komai dan kar ya damu kanshi, cewa tayi, "Alhamdulillah, fatan ka wuni lafiya?" "Ba lafiya ba, no at all, how can i be fine without hearing from you? Ban ga ko text message daga ke ba for all the day, a simple text that'll let me know you're doing good, babu talk less of phone call, ta ya zan wuni lafiya Al-Sad? I guess you're joking right?" "Uhmn! Am sorry." "Don't sorry me, explaining nake so, domin ban yadda kina lafiya kuma komai dai-dai ba", Haidar ya ƙarishe maganan in a careful way,  saboda yana iya experiencing something is off with her, a voice nata da kuma yanayinta. Sadiya marairaice fiska tayi kaman tana a gabanshi, tare da cewa, "Kawai ciwon kai ne, amma ina lafiya." "You went to the hospital right?" "Umnn", ta amsa bakinta a ture har idanuwanta na kawo ƙwalla. "Hmmn! Fatan kina lafiya? And ya jikin Yaya Sadeeq ɗin?" Sai sannan ta maida ƙwallanta tare da cewa, "Ina lafiya,  shi ma jikinshi da sauƙi ya farka yau." "Ma sha Allah! Allah ya kara muku lafiya da marassa lafiya gaba ɗaya gida da asibiti." "Amin, Al-Sad." Sai sannan Haidar ya saki murmushi wanda ya taho daga zuciyarshi,  kuma tare da ajiyan zuciya, in a calm voice ya ce, "I love you soo very much sweet Al-Sad, please kar ki dinga mini irin haka, I can't take it, my heart won't bear it anymore, na jima da kassaruwa a soyayyarki, ina matuƙar ƙaunarki." "Am sorry mijin Sadiya, and I do love you too, more than yo do." Wani irin salihin murmushi Haidar ya saki a lokaci guda ya cije lip nashi, cikin shauƙinta ya rausayar da kai, murya a ƙasa ya ce, "In sha Allah, time shall prevail." Cunna baki Sadiya tayi tare da cewa, "Baka amince na fi sonka da yawa ba kenan?" "Nidai ban ce ba, kawai dai lokaci ne zai nuna mana, kuma Allah kai mu lokacin da rai da lafiya." "Amin Ya Rabbi." "Good girl, nayi kewanki sosai, saboda rashin ji daga gare ki aikin da zan gama zuwa azahar, sai da na kai kusan magrib ban kammala ba, you're my energy giver, indai ba kina son a fara yiwa Alhaji shiririta ba to kada ki kuma,  don next time kika kuma irin haka to wataƙila ma a yiwa Alhaji asaran wani abun." "A'a, Allah ya tsare ya kiyaye, in sha Allah wannan ne first and also last, ba zan kuma ba da yardan Allah, nima na wahala sosai da kewanka yau, kaman bazan kawo i yanzu da rai ba." Guntun dariya Haidar yayi tare da cewa, "ki bari sai mun haifa wa su Alhaji da su Mama jikoki, sannan sai kiyi maganan mutuwa." "Allah dai ya sa mu cika da imani kawai, amma ai mutuwan yanzu..." "Amin, amma da yardan Allah sai mun haife yaranmu mun rene su, sannan mu mutu tare ma", faɗin Haidar yana katse  magananta, kuma yayi dai-dai da ƙiran da aka mata ya gama ringing ya katse, bata bi ta kan call ɗin ba ta cigaba da wayanta, jiyo sallaman Umma ya sanya ta cewa, "1 minute Al-Sad,  Umma na kira na." "Okay, take care ko, inkin gama you should flash me." Gyaɗa kai tayi kaman yana kallonta ne, sannan ta katse ƙiran, tare da amsa sallaman Umma, "Wa'alaikissalam Umma in zo?" Umma da ta amshi plate ɗin ta ce da Sa'ad ya koma ƙasa angode, murɗa handle na ƙofan ɗakin tayi ta shigo,  dai-dai lokacin ƙiran Khalid ya kuma shigowa wayan Sadiya, tana ganin shi ne ta fasa tashuwa zuwa amsan plate da ke hannun Umma, sanin alƙawarin da ke tsakaninsu da Khalid ɗin ba ɓata lokaci ta ɗau ƙiran, ƴar siririyar muryanta na rawa ta ce, "Assalamu alaikum, Yaya Khalid ina Yaya Sadeeqna?" *** A ɓangaren su Sadeeq, daman Khalid na ganin ta ɗau ƙiran, cikin sauri ya mannawa Sadeeq wayan a kunnenshi, hakan ya sanya da sallaman da tayi da tambayan duk a kunnen Sadeeq, bai amsa sallaman ba, hannunshi ya kai ya dafe wayan, Khalid ya janye nashi hannun, ya miƙe ya koma saman ɗaya gadon da ke a gefe, ya zauna a gefen Umar. Sadeeq janye wayan yayi a kunnenshi da Khalid ya manna mishi, ya maida ɗaya kunnen, gyara kwanciyanshi yayi, sannan ya amsa sallaman da ta kuma yi muryanta na rawa jin anyi shiru, "Wa'alaikissalam", ya amsa a taƙaice muryanshi ba amo. "Yaayaana", Sadiya ta faɗi, muryanta cike da zumuɗi da farin cikin jin muryanshi da gaske. Wani iri Sadeeq ya ji sosai, da sunan da muryan duk sun daki zuciyarshi, hakan ya sanya shi kai ɗaya hannunshi saitin zuciyarshi yana shafawa, sai da ya ɗan ɗau lokaci kaman ba zai amsa mata ba, sai kuma ya ce, "Na'am Sa'adiyah", ya faɗi sunan in a sweetness voice,  tare da bai wa H na ƙarshe haƙƙinshi. Wani irin abu ne ya taho a tare da yanda ya ƙira sunanta da h na ƙarshe, ya soki ko wani sassa na jikinta, Sadiya tana rasa yanda Yaya Sadeeq ke ƙiran sunanta, tana da tabbacin ko balaraben mutum ba zai iya ƙiran sunanta ba yanda shi yake ƙira, tana ji ne duk duniya ba wanda ya kai shi iya ƙiran sunanta, idan ya ƙira ta sai ta ji wani abu ya tsirga mata daga tsakar kai, har tafin ƙaramin yatsar ƙafanta, ko da kuwa ya ƙirata bata amsa ba to ba wani abu mai motsawa a halittarta da ba ya amsa ƙiran Yaya Sadeeq, hatta ruhinta na amsa ƙiran Yaya Sadeeq ba iya bakinta ba. *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: I just published "Page 46 _ 50" of my story "💔NAUYIN BAKI👄💔 Na Uwar Batoorl"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=6923e9e7e481f7dec14f6b34 💔NAUYIN BAKI....👄💔        Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠     اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 WANNAN SHAFI NAKI NE Hafsat Umar. 🅿️ 19 _ 20 ⭐️ Sadeeq ko da ya ji tayi shiru, kuma yana iya jiyo sautin numfashinta alaman ba wai ƙiran ya katse bane, sai ya busar da iska mai ɗumi a bakinshi, gani yake kamar laifi ya mata tayi shiru, may be ta fara fahimtan zai rusa mata farin cikinta ne, ko may be yanda yayi magana ya mata ba daɗi, sassauta muryarshi ya yi sosai yayi ƙasa sosai, kamar mai raɗa ya ce, "Fatan kina lafiya?" Maganar Sadeeq shi ya dawo da Sadiya hayyacinta daga duniyar shauƙin yadda ya ƙira sunanta, murmushi ne ya yalwata sosai a fiskarta duk da yana ɗauke ne da rauni na tausayinshi da kewarshi, siririyar muryarta ta kwantar tare da cewa, "Alhamdulillah Yaayaana, fatan kai ma jikin ka da sauƙi?" "Na ji sauƙi sosai Sa'adiyah", ya faɗi yana murmushi mara sauti wanda ya fi kuka ciwo, domin ya san sauƙin dai na farkawanshi ne, bayan farkawanshi ba wani sauƙi da yake ji a zuciyarshi game da ita. "Alhamdulillahi ala kulli halin,  mun gode wa Allah Yaayaana,  naji daɗi sosai da kaji sauƙi, kuma na ji yanzu na nitsu, amma dai duk da haka ka dawo gida da wuri, ba za a barni na sake zuwa asibiti ba, kuma ba zan ji na nitsu sosai ba muddin ba ganinka nayi ana komai da kai ba, Yaayaana kai ne duniyata kai ne komai na, na fi jin ka a rai fiye da Yaya Umar wallahi, kwata-kwata ni bana son komai ya same ka, da kayi ciwo gwanda ma a ce ni nayi ya fi mini, dan Allah ka dawo gida Yaayaana, ina kewarka duk gidan ba daɗi." Maganganun Sadiya daɗa ƙara karya wa Sadeeq zuciya suke bata sani ba, sosai maganganunta ke raunata mishi zuciya, wani irin abu yake ji yana kekketa mishi zuciya, muddin ya cigaba da sauraran Sadiya, rauninsa zai fito fili, ba zai iya cigaba da danne zuciyarshi ba, murya a ɗan dake ya ce, "It's my time to sleep,  goodnight koh." Idanuwan Sadiya ne suka ciko da ƙwalla, bata gaji da jin muryarshi ba, bata gaji da ƙiran sunanta da ya ke yi ya mata daɗi fiye da kowa ba, kai ita so take ma tayi turning phone call ɗin in to video call, tana son ta kalleshi, suyi hira sosai, ya bata labari ya sanyata dariya, tana da tabbacin indai Yaya Sadeeq zai yi haka to a yau za ta warke ta ji ƙarfin jikinta, cikin muryan rauni mai nuni da tana daf da fashe mishi da kuka ta ce, "Yaayaana!." Sadeeq daga muryan Sadiya ya fahimci me take shirin yi, hakan ya sanya ya katse ƙiran ba tare da ya kuma ce mata komai ba, dole ya koya wa kanshi haƙuri da Sadiya, in ya cigaba da saurararta, to komai na gaf da faruwa. Khalid da sauri ya taso ya ƙaraso ya amshi wayarshi da Sadeeq ke miƙa mishi, sannan ya koma gefen Umar ya zauna yana jin ya sauƙe nauyin alƙawarin da ya mata. "Da wa yayi waya?", Umar ne ya jeho wa Khalid tambayar, idanuwanshi na a kan nashi wayar. "Sadiya ce Yaya Umar." Girar sama da ta ƙasa Umar ya haɗe tare da aika wa Khalid mugun kallo,  ya ɗaura da cewa, "Wa ya baka go ahead ɗin haɗa su a waya?" "Afuwan Yaya Umar,  wallahi duk ta ban tausayi ne, kuma na yi alƙawari shiyasa." "Next time ka kuma haɗa su a waya, ni da kai ne." "Ba za a kuma ba babban Yaya." Daga haka Khalid ya gyara yayi kwanciyarshi, Umar kuma ya cigaba da abinda yake yi a wayarshi. Shiru-shiru har lokaci ya ja sosai, Khalid har yayi bacci saboda gajiyar da ke a tare da shi, a ɓangaren Sadeeq ma baccin ne ya fara fisgarshi, saboda shiru da yanayin jikin, kuma cikin magungunan shi akwai na bacci. Umar sai da ya kammala duk abinda yake, sannan ya kulle datar shi yana mai kallon lokaci, wanda ke nuni da sha ɗaya saura, dare yayi sosai bai farga ba, locking na wayar yayi sannan ya sanya a aljihu ya miƙe daga bakin gadon ya ƙarasa gaban gadon da Sadeeq ke kwance, plastic chair ya jawo kusa da gadon sosai sannan ya zauna, cikin muryar da ke nuni da dukka hankalinshi na ga Sadeeq,  kuma magana yake so su yi mai muhimmanci, ya ce, "I guess you're not off right?" Sadeeq sarai baccin bai tafi da shi ba tukunna, tun motsawan Umar yana jin shi har yayi magana, bai bawa Umar amsa ba, domin bai da niyar bayarwa, sai haɗe fiskarshi da yayi. Umar ya fahimci sarai idon Sadeeq biyu tunda ya zauna, saboda daga yanayin numfashin da yake yi, it doesn't sound like for someone who's asleep. "Nasan idonka biyu, so kawai malam ka tashi muyi magana, dan in baka son kanka da lafiyarka to mu muna sonka muna son lafiyarka." Gajeren tsaki Sadeeq ya ja saboda baccin da ya fara fisgarshi, ga Umar na son ƙara mishi ciwon kai akan na zuciya, a ƙufule ya ce, "Me damuwarka da ni? Waya ce taka kuma ka amsa sai dai hakan ai bai hana ni waya da ita ba, duka kuma in ka fasa taɓa ta, kai ka san ciwo ba zai hanani rama mata ba." Guntun murmushi Umar yayi mara sauti tare da cewa, "Next time ko su Abba ba zan bari su haɗa ka da shirmammiyar nan ba." "You should stop me from going to home idan aka yi discharge na, that'll be better dan haka ne kawai za ka samu abinda kake so." "Ko ban hana ka komawa gida ba, ai nan da kwanaki za ta koma wani gidan." Wani irin dogon tsaki Sadeeq ya ja a mugun ƙufule cike da kishi da haushin Umar, dan ji yake kaman da gangan Umar ke faɗa mishi wannan magana, kai ba Umar kawai ba, gani yake duk wanda zai yi maganar auren Sadiya a gabanshi to da gayya yake yi, da gangan ake so a ƙarasa kassara mishi zuciya, "Hmmn!", ya faɗi kawai, da kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, sai sake tamke fiska da yayi ya lumshe ido, yana neman bacci yayi gaba da shi tun kamun zuciyarshi ta kai bango, ya saki layi a gaban Umar, wanda kuma ba ya fatan haka, soyayyar Sadiya sirrin shi ne, and he'll keep on hiding it, saboda ta samu farin cikinta, he sacrifice his own happiness for her, yana mata fatan kasancewa cikin farin ciki da abinda take so. Umar murmushi ya saki mai zurfi da sauti,  saboda yana noticing wani abu ne wanda yake son gano wa, duk da abun dai ƙara ɗaure mishi kai yake, murya a sake ba yabo ba fallasa ya ce, "Barin kashi a ciki baya maganin yunwa, you better utter what's in you than ka ta humming kai ba mai naƙuda ba." Sadeeq banza ya kuma yi da Umar,  hakan ya sanya Umar ya ce, "Sannan maganar duka sai na kirɓa Sadiya, keep this on back of your mind,  I'll make very sure that i deal with her, tana hauka ne za ta dinga yiwa mutane shiririta da yaranta, muna fama da addu'a ka warke sannan ta ke mayar wa mutane aiki baya, to in ka ji labarin na zane ta kayi zuciya ka warke ka dawo gida ka rama mata, I'll be very happy dan mun kwana biyu bamu gwada ƙwanji ba, sai naga da sauranka ko kuma ka zama rabi da rabi." "Indai ba a gode mata ba ai ba za a zane ta ko a dake ta ba, batun gwada ƙwanji kuma you should try me and see." "A gode mata a kan me? Akan shirme ko shiririta ko rashin hankali?" "Duk wanda ka zaɓa, dan naga dai ni ta dama ba kai ba, kai ai ba ka da damuwa da hakan", faɗin Sadeeq cikin jin haushi, ga Umar ya tasa shi gaba da maganganun banza, kuma dama ko da ba zai yi surutu da kowa ba, to banda Aminin shi Umar, ko Sadiya, su yana iya wuni ya kwana magana da su ba tare da ya gaji ba. Umar murmushin da shi kaɗai ya san ma'anarshi ya kuma saki sannan ya ce, "Ni kuwa nake da damuwa." "Your problem is your problem,  am not concern and i don't mind", faɗin Sadeeq yana taɓe baki saboda haushin Umar. Ɗage kafaɗa Umar yayi irin ko kaɗan abinda Sadeeq ya ce bai dame shi ba, sannan ya ce, "Damuwana kai ne bro, kai ne damuwana wallahi, you were painted and unconscious, in ba dan Allah ya kiyaye ba, wa yasan abinda zai faru, kasan irin damuwan da muka shiga? Umma, Abba,  Mama,  Sa'ad da Khalid, dan ma an ɓoye wa Khausar,  kai ka san da yanzu haka tana a asibitin nan tare da mu, duk da su Abba basu tambayeni akan abinda ke damunka ba, amma na tabbata suna mini kallon na san abinda ya faɗar da kai, i never expect this from you, wai ka ɓoye mini wani abu yana damunka, abinda har zai sa ka faɗi kaman mara numfashi a tattare da shi, i think there's no secret between us, ka san komai nawa na san komai naka, ashe am wrong, na fahimceka bai bai, yanda na ɗaukeka ba haka ka ɗauke ni ba, this is the last thing i never ever expect from you Sadeeq", Umar ya ƙarishe maganar cikin sautin da ke tabbatar da maƙurar rashin jin daɗin abinda Sadeeq ya mishi. "Huh, ita ɗin da baka sako sunanta ba bata damu bane? Ko ita ba mutum ba ce? Umar meyasa kake wa Sadiya haka? Ƙanwarmu ce fa tana da wasu bayan mu ne?", Sadeeq ya faɗi cikin son kawar da maganan Umar, saboda tabbas Umar gaskiya ya faɗa, amma ya san sai ran Umar ya fi haka ɓacci muddin ya ji gaskiya, gaskiyanma wai na son Sadiya da ke a zuciyarshi,  kuma ya ji daga lokacin da ya fara son ta. Umar murmushi guntu yayi, na ganin yanda Sadeeq ke cigaba da son shashantar da shi, ba tare da damuwar komai ba ya ce, "Sadiya ba a lissafata a jerin mutane, and soon za ta samu wasu bayanmu, tana aure shikkenan kuma an wuce wajan, so in za ka faɗa mini abinda na tambaya ka faɗa mini kawai ka bar yi mini corner, me ke damunka? Menene damuwarka? Me kake so? Me kake ɓoye mana? Kai ne baka da kowa bayan mu, idan ka faɗa mana komai, we'll help and support you, ko da kuwa financially support ne, in kuma da addu'a ne we'll pray for u also, idan kuma muna da right akan abinda kake buƙata za mu samar maka da abin muddin bai fi ƙarfinmu ba, ko kuwa baj saɓa wa addini ba." Maganganun Umar sun taɓa Sadeeq sosai, ya ji kaman ya faɗa abinda ke a ranshi, amma ba zai iya ba, ba zai taɓa faɗa ba, asali ma maganar Sadiya za ta yi aure ta samu wasu family, sake dulmiya mishi zuciya yayi cikin kogin ciwo da raunin rasa ta. Daga haka duk abinda Umar ya kuma faɗa, Sadeeq bai ce komai ba, har Umar ya gaji ya tashi ya wuce ya je ya kwanta, Sadeeq ma ba jimawa bacci yayi gaba da shi. Washe-gari bayan duk sun yi sallahn asuba, Umar ya ce da Khalid ya zauna wajan Sadeeq ɗin, shi zai je gida zai ya shirya, da kansa yau zai je wajan aikinsu, Khalid dan murna kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, dan da gaske yake ayyukan nan za su margaya shi, cikin jin daɗi ya ce, "Sai da kai Yaya Umar, a dawo lafiya, ina nan asibiti in ma ka ce kar na leƙa gida, to ba zan leƙa ba ina nan a asibiti." Umar guntun murmushi yayi ya ce, "Allah ya shiryaka Khalid,  idan Abba ya maka auren za mu ga wanda zai ke making kuɗi ya kular maka da matar da yaran da za ta haifa." Jinjina kai Khalid yayi tare da cewa, "Abba, ai Abba ne ma zai ciyar da mu daga ni har ita har jikokinshi, ai ni cima zaune ne wallahi, ɗan zaman kashe trouser, in dai har aka mini aure a haka ai sai Abba ya ciyar da mu, ku ma da kuka goyawa Abba baya, sai kuke mana kayan sallah, maganan outing,  kuɗin kashewa da sauransu, har Yaya Sa'ad sai yayi hidima da mu, Umma da Mama da Aunty Khausar da Sadiya kawai za mu ɗaga wa ƙafa, tun da su ma sai an basu suke samu." Umar girgiza kai yayi yana ƴar dariya ya ce, "Allah ya taro ka, nikam na wuce ka kula sosai", yana gama faɗin haka ya juya ya fice ba tare da ya ce da Sadeeq komai ba, dan tun jiya da suka yi magana, to yau tun bayan gaisuwan da suka yi ya tambayeshi ya jikinshi, to bai sake mishi magana ba. ⭐️ RAYFIELD      SADIYA POV         *** Sadiya tana jin alamar Sadeeq ya katse ƙiran sai ta aje wayar, hawayene masu ɗumi suka fara zirya a kumatunta, ba ta ko tantama Yaya Umar ne amshi wayan ya datse ƙiran, "Ya ake so nayi da rayuwata?" Ta faɗa cikin karyayyiyar murya, mai nuni da rashin daɗin da take ji a zuciyarta. Umma da ke tsaye tun shigowarta ta zuba wa Sadiya ido ta kuma kasa ƙarasowa ta zauna, sabboda tausayin Sadiya da kuma Sadeeq, dan ta fahimci da Sadeeq Sadiya ke waya, jin abinda Sadiya ta faɗi ne bayan ta dire wayan, ya sanya Umma ƙarasowa tana faɗin, "Ke da wa auta? Wa ya taɓa mini ke?" Sadiya kwantar da kanta tayi a kafaɗan Umma da ta zauna a gefenta, cikin muryar kuka da sheshsheƙa ta ce, "Umma ba fa ni na ɗaura wa kaina lalurar zuwa asibiti ba, asalima kullum cikin son yaƙar hakan nake yi, dalilin da ya sa na ce zan karanci science kenan, amma Yaya Sadeeq ya hana ni kuma na hanu, Umma kowa fa ya san yanda na ɗauki Yaya Sadeeq, wallahi ko Yaya Umar ba na jin shi a rai tamkar yanda nake jin Yaya Sadeeq, Umma nasan ba za a barni na sake komawa asibiti ba, shiyasa na sanya wa rai da zuciyata salama, amma magana a waya ma a ce Yaya Umar ya hana ni yi da Yaya Sadeeq, hakan ya kyautu dan Allah?" Umma hannunta ta kai take ɗan bubbuga bayan Sadiya alamar rarrashi, sannan ta ce, "Ki yi haƙuri Auta, ba a kyauta ba amma in sha Allah zan yiwa Umar magana, duk da ba ma fatan har biki ya zo Sadeeq bai dawo gida ba, amma in har Allah ya ƙaddari hakan ta faru, to ni da kai na zan kai ki asibitin wajanshi ya miki nasiha ko, amma fa duk haka zai faru ne akan yarjejeniya guda ɗaya." "Menene yarjejeniyar Umma?" Murya a sanyaye ta yi tambaya. Sai da Umma ta numfasa sannan ta ce, "Dole za ki sake kike walwala kamar yanda kike asali, za ki cire damuwar komai a zuciyarki ki saki ranki, hakan ne kawai zai sa kullum na haɗa ki da Sadeeq a waya ku gaisa kamun lokacin bikin idan Allah ya yi ya warke to, idan kuma bai warke ba sai na kai ki kaman yanda na ce in sha Allah." "In Allah ya yarda Umma zan saki rai na, walwalanma zan ƙoƙarta dan dai Yaya Sadeeqna baya nan kam ba walwala, amma zan ƙoƙarta nayi, kuma in sha Allah zai warke ya dawo gida kamun lokacin bikin." "Allah ya amince auta, Allah ya sa ya warke dan duk haka muke fata." "Amin Umma." "To maza ɗaga kanki ki fara cika yarjejeniyar tun yanzu, ki ci abinci sosai, kin ga duk kin bi

Chapter 11 of 32