Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuciyarta, domin ta mance ma da ta na da wata damuwa, tunda aka mata maganar Haidar, kuma aka danganta ta da shi na wani mu'amala. "Ai dole naji da shi." "Ina su Nussy da Rukky?" "Yanzun nan na gama waya da su wai suna hanya." "Allah ya kawo su lafiya, yanzu twelve ake nema, ya kamata a fara hennan ai, saboda lokaci yake ci, kuma ban so a yi dare sosai." "Tun tuni aka fara cancarawa mutane kina bacci, yanzu haka ana yin wa sauran sisters naki ne, waɗanda suke cikin ƙawaye, ina tunanin ma an gama yi wa Hidaya, wataƙila Safiyya ake yi wa." Jinjina kai Sadiya ta yi, sannan ta ce, "Wa ya san ma ko Salma ta dawo ko ba su dawo ba tukunna." "To ki ƙira layinta ki ji mana, ai dama ya kamata ki ƙirata, inma ta dawo ki mata sannu da dawowa, idan bata dawo ba ki mata a dawo lafiya, ba wai dan mutum zai maka ƙawance ka nuna iya amfaninsa ba kenan, yana da kyau ka damu da mutum", faɗin Zahra ta na danna na ta wayar. "Wannan haka yake ƙawata", Sadiya ta faɗa ta na gyaɗa kai, tare da cire wayarta a key, ta na ƙoƙarin shiga call log, sai idanuwanta suka sauƙa a kan message box da alamar an turo mata saƙo, har za ta yi ignoring sai kuma ta tuna ta aika wa Haidar saƙo, wataƙila kuma shi ne ya dawo mata da amsa, hakan ya sa ta shiga inbox nata da sauri, amma ta na shiga sai ta ga lambar Yaya Sadeeq wanda tayi saving da World best Yaayaa, a matakin farko saman layin Haidar, wanda hakan ke nuni da saƙon daga Yaya Sadeeq ne, da kamar za ta shiga ta duba, dan son ganin me ya turo, amma tsoro da fargabar abinda zai ce ya dakatar da ita, sai ma jikinta ya yi sanyi, idanuwanta na ƙoƙarin cikowa da ƙwalla ta fice a wajan messages ɗin ta shiga wajan ƙira, layin da tayi saving da friend Salma shi tayi dialing tare da kara wa a kunnenta, a zahirin ringing na wayar take saurare, amma a baɗini zuciyarta gaba ɗaya na ga saƙon Yaya Sadeeq da ta gani, ta na son buɗewa ta na kuma shakkar abinda idanuwanta ka iya gane mata. "Assalamu alaiki, amarya ba kya laifi ko kin kashe ɗan masu gida, amarya mai maganar sugar, amarsu ta Al-Sad, ya aka yi? Kina cikiyata ne?", muryar Salma daga ɗaya ɓangaren ya katse tunanin Sadiya, wacce bata ma san an ɗau ƙiran ba. "Hey amarsu kina ji na kuwa, are you there?" Salma ta sake yin magana, jin Sadiya ta yi shiru bata amsa ba. "Yes Salamatu darling ina jin ki, Ya Nasarawa? Ya kowa da kowa?" Sadiya ta faɗa tana sauƙe numfashi. "Lafiya alhamdulillahi, ba mu kai 10 minutes da isowa gida ba, zuwa Azahar zan shigo in sha Allah, su Zahran taki sun shigo ne?" "Eh, sun shigo ga ta nan ma", Sadiya ta faɗa ta na miƙa wa Zahra wayar. Zahra amsa ta yi suka gaisa da Salma cikin raha da tsokana, sannan Zahra ke jaddadawa Salma ta taho musu da tsarabarsu, daga haka suka yi sallama, Zahra ta miƙa wa Sadiya wayarta, ita ma suka yi sallama sannan ta katse ƙiran, har ta ajiye wayar sai kuma ta ɗauka, ta shiga inbox nata, runtse idanuwa ta yi gabanta na faɗuwa ta danna kan lambar Yaya Sadeeq, sannan a sanyaye ta fara buɗe idanuwanta cike da fargabar abinda za ta gani, a sanyaye ta fara karanta saƙon, idanuwanta na cikowa da ƙwalla, bata ankara ba har suka zubo a ƙoƙarinta na maidawa. Zahra da ke zaune a gefe idanuwanta a kan Sadiya ta na kallon duk move na ta, da mamaki ta ce, "Lafiya kuwa Sady?" Shiru, Sadiya ta yi nisa ba ta ji Zahra ba, hakan ya sa Zahra ta ɗan jijjiga hannun Sadiya tana faɗin, "Are you alright? Hawayen me kike yi? Menene a wayar?" Sadiya ba tare da ta share hawayenta ba ta ce, "am okay Zahra." Harara Zahra ta aika wa Sadiya sannan ta ce, "mai da ni jaririya mana ƴar rainin wayo, kina hawayen ne kika faɗa mini you're okay, a'a dai you're opay ne kin manta." Sadiya da take buƙatar yin kukanta ta sanar da wani abinda ke zuciyarta, sai kawai ta fashe da kuka tare da miƙa wa Zahra wayar, ita kuma ta amsa ba tare da ta bi ta kan kukan Sadiya ba, balle ta tsaya rarrashinta, dan ta fi so ta ji ba'asi idan na rarrashi ne tayi, idan na ƙara wa Sadiya wani zafin ne kuma sai ta ƙara mata, Zahra ta fara karanta text message ɗin a zuciya, sai da ta yi rabi sanna ta koma baya cike da mamaki, ta mayar da idanuwanta kan numbern kuma ta fahimci layin waye ne, sannan ta fara karantawa a fili «Assalamu alaiki, Halimatus Sa'adiyah na san zuwa lokacin da za ki karanta saƙon nan wataƙila na yi nisa zuwa inda na nufa, ban turo milk saƙo dan komai ba, ko a wani matsayi ba, sai dan na rarrashe ki na kuma ƙarfafa miki guiwa a matsayina na Yayanki cikin Umma ɗaya, ki mance da batun aure da ake yi tsakanina da ke, ki goge shi har abada domin nima na goge, kin sani ni mai sonki ne da son farincikinki a ko da yaushe, dan hakan ina mai roƙonki da ki yi haƙuri, ki sake ki mance komai ki yi hidindimunki yadda ya kamata cikin farin ciki da annashuwa, Aliyu Haidar za ki aura da yardar Allah kamar yadda kike so, nima kuma ina taya ki son abinda kike so, haka ya sa zan dawo domin walittar aurenki yadda kika buƙata, Yaayanki Abubakar Sadeeq, duniyarki». Zahra ta karanta saƙon ta kuma maimaitawa ya fi sau uku, amma ta kasa fahimtar me ma saƙon yake nufi, ga Sadiya kuma sai risgar kukanta take yi, kamar wacce idan Zahra ta karanta sake tunzura kukan nata take yi. Zahra kamo hannun Sadiya ta yi tare da cewa, "Ban fahimta ba Sady, ki yi mini bayani dalla-dalla plss, me saƙon yake nufi," Sadiya cikin kuka ta ce, "Abinda kika gani haka yake Zahra, kar mamaki ya sa ki kasa fahimta, haka abin yake, ko nima na shiga ruɗu da mamaki fiye da ke, tun daga ranar da naji wannan labarin har yau, kuma har yau na kasa fahimta, na kasa yarda na kuma kasa amincewa, domin ban ga dalilin hakan ba." Zahra zuba wa Sadiya da ke kuka idanuwa ta yi na wasu daƙiƙu, can kuma ta amshi wayar ta sake karanta saƙon, sai kuma kaman mai koyon magana da haɗa kalmomi ta ce, "Yaya Sadeeq ya na sonki kenan? Har ma ana maganar aurenku, haka saƙon yake nufi kenan?" Jinjina kai Sadiya ta yi alamar eh haka ne, amma bata ce komai ba. Da mamaki Zahra ta ce, "Shi kuma Haidar fa? Al-Sad naki fa? Kenan ba da shi ake shirin auren ba...", maganar Zahra ne ya katse saboda kukan Sadiya da ya tsananta. Cikin tsananin kuka Sadiya ta ce, "Ni ma ban sani ba, ban sani ba Zahra, ban san da wa ake hidimar biki na ba, Zahra am just breathing but deep down inside am burning, my heart is bursting and broken in to billions pieces, my chest is hurting me Zahra, bansan wa ake shirin miƙa wa stairing rayuwata ba, Haidar ko Yaya Sadeeq, i don't know, ina cikin wani hali, ina tsaka mai wuya", cikin kuka Sadiya ke maganar kamar za ta shiɗe, ga wani irin azababben ciwon kai da ke addabarta. Zahra cike da tausayin ƙawarta ta kama hannayenta duka, da sansanyar murya ta lallashi da ƙwarara guiwa ta ce, "It's okay Sady, just calm down and stop this crazy crying, saboda kuka ba zai ba ki mafita ba, you'll just end up with hardest headache, just explain to me everything, and I'll help you to find a solution, indai laluɓo mafita bata fi ƙarfinmu ba." Cikin kuka Sadiya ta labarta wa Zahra komai from a to z, daga ranar da suka fara maganar da Khausar har ta sanar mata son ta da Yaya Sadeeq yake yi, wanda wai shi yayi sanadin ciwonsa, har zuwa komai da ya faru har dai zuwa yanzu da suke magana, sannan ta ɗaura da cewa, "Zahra ban san ya zan yi ba, Yaya Umar da Mama sun dage, musamman Yaya Umar ba ya ta ni ta Amininsa yake yi, na samu Abba da maganar na amince kamar yadda suka buƙata, amma Zahra wallahi Abba mahaifi ne na ƙwarai, ya fahimci abinda ke zuciyata daban da abinda na furta a bakina, Zahra i only love Haidar, shi kawai nake so da maganar aure ko soyayya, wani kallo daban nake yi wa Yaya Sadeeq, wanda wani lokacin har nake ba shi matsayin mahaifi saboda ɗawainiya da hidimar da yake yi da mu musamman ni, Zahra ina son a fahimce ni, i can't take, bear or believe the fact that Yaya Sadeeq will lay his finger on my body, da sunan wani relationship ta masu aure i can't wallahi, har abada ba zan iya ba, ni wai da Yaya Sadeeq ake tsammani na iya shiga ɗaki ɗaya da shi, gado ɗaya a matsayin masu aure, what are they expecting? Hmmn, ba zan iya ba atou, ban shirya ba kuma ba zan taɓa shiryawa ba har abada, ba abinda zan iya bari ya shiga tsakaninmu, na haramta wa kaina auren Yaya..." Da sauri Zahra ta toshewa Sadiya da ke magana cikin kuka baki, tana girgiza kai ta ce, "Don't you dare say this Sady, kar ki faɗa haka dan Allah, ki dai zuba wa sarautar Allah ido, ki jira ki ga ikonsa da zai gudana." Sadiya cikin muryar kuka ta ce, "Are you trying to tell me you're not supporting me? I can't believe it Zahra, ke ma kina goyon bayan wannan abinda yake ba me yiwuwa ba kenan?" Taƙaitaccen murmushi Zahra ta yi, with seriousness face ta ce, "Sady am not supporting you and am not opposing you also, abu ɗaya na sani, shi ne you have no specific reason for all what you've just said, ba ki da ƙwaƙƙwaran dalili ko hujja, dan haka don't you dare try to act or says you'll fight with your destiny, just pray ki miƙa wa Allah lamuranki, duk abinda ya baki ki amsa ki gode kuma." Ɓata fiska Sadiya ta yi, murya da gunji-gunjin kuka ta harari Zahra tare da cewa, "Ban ce miki zan yaƙi ƙaddara ba Zahra, domin ni ba jahila ba ce kin sani, musulma ce ni kuma mumina, na yarda da ƙaddara kuma na yarda da addu'a, shiyasa nake addu'a Allah ya mallaka mini Haidar domin shi nake so, da shi na ji na gani zan iya rayuwa, ba na ƙin Yaya Sadeeq, kawai dai matsayin Yaya Sadeeq a gare ni ba zan iya masa kallon miji ba." Zahra ma hararar Sadiya ta yi tare da cewa, "okay, ba za ki iya yi wa Yaya Sadeeq kallon miji ba, amma shi Haidar za ki iya masa ko? Wait Sady let me ask you, da me Haidar ya fi Yaya Sadeeq? Me Yaya Sadeeq ya rasa da ba za a iya masa kallon miji ba?" Sadiya dakatar da kukanta ta yi, tare da haɗe fiska ta janye hannayenta a na Zahra, ba ta bai wa Zahra amsa ba ta matsa gefe. Taɓe baki Zahra ta yi tare da ɗage kafaɗa alamar abinda Sadiya ta yi bai dame ta ba, ta gyara zamanta tare da cewa, "Sady in kin so ki haɗe fiskarki ta fi ta dodo haɗewa da muni, wallahi sai na faɗa miki gaskiya, ke ana ga hanya kina runtse ido saboda ke bi ta can ce ko, to wallahi har zuciyata har ƙoƙon rai na, ni ma ina bayan su Mama, ni ban taɓa ganin aibun Yaya Sadeeq ba, ba na nufin ina ƙin Al-Sad na ki ko wani abun, amma dai wallahil Azim kun fi dacewa da Yaya Sadeeq, ke Yaya Sadeeq naki duniya ne fa, ke kin fi kowa sanin irin yadda yake son ki yake riritaki, ai wallahi ko a baya da nake maganarki da shi, har kike ganin kamar wasa ne ki ɓata rai, to ina yin shiru ne na bar shi a wasa, saboda banson muna jan magana da ke ko mu samu damuwa, amma ko lokacin har raina da gaske nake yi, Sady Yaya Sadeeq miji ne na kece raini, miji ne a gare ki wanda idan kika aure sa, ke da kanki kin san cewa Allah ya sallameki sai dai ki nemi wani abun kuma, domin duk bauta da yi nan yi can da muke yi saboda mu dace mu samu aljanna ne, kuma kika auri Yaya Sadeeq ina da tabbacin duk da dai ƙalubale da ke a cikin rayuwar aure, da har ya kasance tamkar gidan soja marmari daga nesa idan ka shiga abinda za ka tarar daban, da abinda kake hange, to duk da haka a yadda Yaya Sadeeq ke ƙaunarki, tun kamun tafiya ta yi nisa aje ko ina zai ɗaga miki ƙafa ki samu aljannarki, ke kamun ma ki gama rigimarki ki ba sa haƙƙinsa na san tuni ya lamunce miki tsakaninki da aljanna mutuwa ce kawai, balle kuma idan kika gama rigimar ya samu nitsuwa ai sai dai a ce Yaya Sadeeq ya zaunce, don na san fa sai kin yi rigima kamun a ba sa haƙƙin nasa", cikin raha da tausasa murya Zahra ta ƙarisa maganar da ta soma shi cikin ko in kula da haushi. "Mtswww!", Sadiya ta ja dogon tsaki tare da sake aika wa Zahra mugun harara, a hasale ta ce, "Zahra na ga alamar kina yin Yaya Sadeeq ɗin nan, to dan Allah ki aure sa, ai za ki iya fasa auren wanda kike tare da shi ki auri Yaya Sadeeq, domin na ji na gaji Al-Sad nake so, kuma kika sake danganta wata mu'amala tsakanina da Yaya Sadeeq wallahi zan miki rashin mutunci." "Ohh! To Allah na tuba rashin mutunci na nawa kuma ni Zahra'u, Sady kin jima ba ki yi mini rashin mutuncin ba wallahi, ke kin mance tijarar da kika dinga mini a baya dan wai na haɗa ki da shi, ke fa taimakonki za a yi idan aka aura miki shi wallahi, kuma da kike cewa na aure sa, ai Yaya Sadeeq son kowa ne ƙin wanda kuma ya rasa, ke kin sani sai dai ki take saninki dan naga abinda kike fama da shi a yanzu kenan, kuma abu ne mai sauƙi a wajena na bar wanda nake tare da shi na auri Yaya Sadeeq, muddin aka ce Yaya Sadeeq yana ƙaunata ko da kuwa rabin ƙaunar da yake miki ne Sady, amma dai a yanzu duk wacce ta auri Yaya Sadeeq ma to ta kinkimo wa kanta dutsen dala ba gammo ne kawai, domin fa ko gangar jikinsa bata aura ba balle zuciyarsa, da gangar jikin da zuciyar na san ya jima da mallaka miki, indai a yacce nake ganin komai da yadda kika faɗa mini ne, Sady please you have to think about it, choose wisely, rayuwar aure fa ba wasa ba, rayuwa ce da ake fata har mutuwa, ba wai ta ka je ka dawo within sati, wata ko shekara ba", cikin kwantacciyar murya Zahra ta ƙarisa maganar. "Hmmn!, in dai na kintata daidai, to Zahra ki na bayan maganar Yaya Sadeeq kenan, amma dan munafurci shi ne ɗazu kika ce ba kya bayan kowa, munafuka kawai, to wai ya kuke so na yi da Al-Sad na?", Sadiya ta ƙarishe maganar ta na harara Zahra, kuma idanuwanta suna cikowa da ƙwalla. Zahra sake kwantar da murya ta yi, tare da cewa, "Ƙawata gaskiya ce na faɗa miki ba na bayan kowa, ni mai son ki da alkairi ce kawai kamar yadda su Mama suke son ki da alkairi, na ce miki ki yi addu'a ki miƙa wa Allah lamuranki, ki zuba wa sarautar sa ido, ki kuma amshi duk abinda ya zaɓar miki domin wallahi shi ne alkairinki, idan ma kuma ba haka ba, ki tsananta istihara kamun ki tsayar da guda ɗaya, Al-Sad na ki ya na sonki ki na son shi mun sani mun yarda, Yaya Sadeeq ya na ƙaunarki matuƙa." "Ba gaskiya kike faɗa mini ba Zahra, son zuciyarki kike faɗa mini, domin duk maganarki ya karkata ne a kan Yaya Sadeeq", faɗin Sadiya rai ba daɗi. Murmushi Zahra ta yi, ta ce, "Ba son zuciya ba, ko ma menene ki faɗa ba komai, don ba ki yi laifi ba, na fi son ki da Yaya Sadeeq Allah ma ya sani, kuma dama ai shawara ce kike nema da mafita, sannan na ba ki shawaran, mafitar ma sai na nemo miki yadda za ki sallame Haidar cikin aminci ki aure Yaya Sadeeq ɗin ki, ku sha ruwan ƙauna." "Allah ya isa tsakanina da ke Zahra, wallahi na faɗa miki ki bar haɗa ni da Yaya Sadeeq kina kwatanta wata mu'amala, ba na so wallahi ran mutum zai ɓaci, kuma shawara indai ta ki ce, to na yafe duniya da lahira ba na buƙata, mafitar ma dama a wajan Allah nake nema kuma zan cigaba da nema a wajansa, dan haka ki fita tsabgata, munafuka kawai aniyarki ta bi ki, ni ina jin ma dai bakinku ɗaya da Yaya Umar, to ko da sallamar Haidar zai kasance fansar numfashina na ƙarshe ne a rayuwa, to wallahi da kai na ba zan sallami Haidar ba, sai dai numfashin nawa ya tafi na mutu kowa ya huta, amma ba zan taɓa sanar da Haidar wani abu ba, kuma ba zan bari wani ya sanar da shi ba in sha Allah, ko ma wace mugunta za a mana sai dai a yi bai sani ba, ya ji daga baya....", muryar Sadiya ne ya fara rawa, hawaye suka fara zubo mata. Zahra idanuwa kawai ta zuba wa Sadiya ta kasa ce mata komai, ganin abinda ta ke yi kamar mai aljanun kuka. Sadiya matsowa kusa da Zahra ta yi, ta riƙo hannayenta, hawaye na zubo mata ta na kuka ta ce, "Zahra wannan abun ya fi komai damuna, Zahra wai Yaya Umar zai samu Haidar da kansa ya sanar da Haidar sun fasa ba shi aurena, Zahra wannan wani irin cin fiska ne dan Allah? Zahra idan suka yi haka sun kyauta mini? Ba ma iya ni kai na ba, wallahi har su basu kyautawa kansu ba, za su zubar da kimarsu da darajarsu ne a banza,  amma Yaya Umar idanuwansa sun kulle ba ya kallon duk haka, damuwarsa kawai Amininsa, Zahra wai fa har kayan da ya kawo duk za a mayar masa." Cikin sigar rarrashi Zahra ta sakar wa Sadiya guntun murmushin ƙwarara guiwa, sannan ta girgiza kai ta kwantar da murya ta ce, "Ba a kyauta wa Haidar ba har da ke ma, amma Sady ki sani abinda duk haƙuri bai bayar ba, to rashin haƙuri ba ya bayarwa, Sady tun farko na faɗa miki ki yi addu'a, ki kai wa Allah kukanki, sannan ki zuba wa sarautarsa ido, ki jira ki ga abinda duk zai faru, amma ko ma menene to ki karɓa hannu bibbiyu kuma ki gode domin wallahi shi ne alkairi a gare ki, Allah ba ya zaɓar mana abinda ba alkairi gare mu ba, ko da abun ya mana daɗi ne ko ciwo, to fa alkairi ne, wataƙila daɗin na jarabawa, haka ciwon ma na jarabtar imaninmu ne, duk idan muka yi haƙuri muka daure muka amshi ƙaddararmu sai ki ga alkairi mai ɗumbin yawa bayan haka, sannan ga tarin lada wajan mahaliccinmu, Sady ki yi haƙuri ki bar damun kan ki da tashin hankalinki, Allah ya na tare da mai haƙuri kuma mai miƙa masa lamuransa." Sadiya gyaɗa wa Zahra kai ta yi, alamar ta ji kuma ta yarda ta aminta, duk da a zuciyarta fatan Allah ya zaɓar mata Haidar take yi, sai sa ta nisa sannan ta ce, "Tafiyar Yaya Sadeeq ya na damuna Zahra, ina jin kunyan Abba da Umma da Aunty Khausar, Zahra na san kowa zai ga kamar ban da hujja, amma duk wanda ya fahimceni zai mini uzuri, ina yi wa Yaya Sadeeq ne kallon duniyata, mahaifin da na rasa, zai iya cutuwa a zamanmu, Zahra ba zan iya bai wa Yaya Sadeeq haƙƙin auratayya ba", Sadiya ta ƙarishe maganar siraran hawaye na silalo mata, ta kuma yi ƙasa da kai ta runtse ido, kunyar furta maganar ma take yi kamar ta na gaban Yaya Sadeeq ɗin ne, ga kuma wani irin harbawa da zuciyarta ta yi, wani abu ya tsarga jikinta gaba ɗaya, maganar Zahra ne ya katse mata wannan yanayi, ta ɗago ta na kallon Zahra. Sai da Zahra ta numfasa sannan ta ce, "Komai da komai ki miƙa shi ga Allah Sady, tabbas ina son ki da Yaya Sadeeq har rai na, amma ina son ki da abinda kike so Al-Sad, amma ki dinga saka wa a zuciyarki, hatta da Ƙur'ani mai girma da tsarki, ya sanar mana kana iya son abu ya zame sharri gare ka, kuma ka na iya ƙin abu ya zame alkairi gare ka, na san ba ƙin Yaya Sadeeq kike yi ba, kuma na fahimceki duk da ke kin ƙi fahimtar kowa, kuma dai ba na nufin komai a kan Haidar, amma ki dogara da Allah zai iya miki a komai Sady." Nauyayyar ajiyar zuciya Sadiya ta sauƙe, tare da gyaɗa kai, murya a sanyaye ta ce, "Na gode Zahra, ina addu'a kuma zan ci gaba da yi, Allah ya saka miki da alkairi, amma ki taya ni da addu'a Allah ya sa Haidar ne zaɓin mahaliccina", ta ƙarishe faɗa ta na fece hanci tare da share hawaye. Kallo ɗaya Zahra ta yi wa Sadiya, ta girgiza kai kawai, a fili ta amsa mata da, "Amin ƙawata", amma a zuciya cewa ta yi, "Allah ya tabbatar da alkairi, Allah kuma ya sa Yaya Sadeeq ne alkairinki." Daga haka Zahra ta ci gaba da rarrashin Sady, suna kan jajanta lamarin, har suka koma kan batun event na su na yau, duk da a zuciyar Sadiya a maƙale tunanin Haidar da Sadeeq ne. Zuwa azahar Salma da sauran ƙawaye, Nussy da Rukky duk suka shigo, sai da suka yi sallah sannan aka yi musu jan lalle, daga nan kuma aka fara shirye-shiryen Henna partyn. *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD @Uwarbatoorl96 ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [30/12/2025, 10:18] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 💔NAUYIN BAKI....👄💔                Na            Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠 اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 Hey masu darajar habibties, ina mai farin cikin sanar da ku daga wannan shafi sai shafi na ƙarshe, mun kammala book 1 da ya kasance free kenan, maza me kuke jira? Ku hanzarta biyan 500 naku kacal domin a ƙarisa wannan tafiya da ku, kun fi kowa sanin yanzu muka fara labarinnan, abubuwa da dama suna gaba, kar ku sake a baku labari, sannan idan littafi ya kammala 1000 zai koma in sha Allah. 9161720046 Harira salihu isah opay Shaidar biya ta 09161720046. Sai da ku masu daraja habibties na Uwar Batoorl ❤️🫶 🅿️ 47 _ 48 ⭐️ Shirin Henna partyn suke yi ba kama hannun yaro, kasancewar Salma makeup artist, ita ta cancarawa Sadiya kwalliya mai matuƙar kyau, amma very simple makeup ne.   Rigar da aka yi wa ɗinkin buba da single zani, a cikinsu Sadiya ta haɗe, ta yi matuƙar kyau, kuma zanin ya amsheta dan na yarensu ne, ga shi akwai ratsi-ratsin yellow, aka mata ɗauri mai kyau daidai shigarta da kwalliyarta, sannan ta yafa fallen zanin a matsayin mayafi, hakan ya sake fidda haɗewanta da kyawun da ta yi, kamar ka sace ta ka gudu, banda hotuna da videos ba abinda ake mata, kowa sai yaba kyawun da ta yi yake yi. A compound na gidan Abba aka musu decoration na Henna partyn, daga kan darduman da aka yi wallpaper da shi har zuwa balloons da aka sake ƙawata wajan da su, duk kalolin kayan jikin amaryan da ƙawayenta ne, har kumbon da aka jera a wajan zaman amarya da kuma a wajan zaman ƙawaye.   Wajan ba ƙaramin kyau da haɗuwa yayi ba, ga speakers da suke ta ba da sautin bugun waƙoƙi, akwai camera man's

Chapter 29 of 32