Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jin Umar a zuciyanta haka take jin Sadeeq, hidiman da Sadeeq yake yi da su da alkairai da ɗawainiya, to ko yaron cikinta ne muddin ba na kirki bane to ba zai yi mata wannan hidima ba, tsakaninsu da Sadeeq sai addu'a da fatan alkairi, domin shi ɗin yaron kirki ne, nagartaccen mutum kuma wanda ya san ya kamata, yaro mai biyayya da hankali, Abubakar Sadeeq babban mutum. Wannan tunani da Mama take a zuciyanta shiyasa ma sam bata ji me Umma da Sadiya suke faɗa ba, sai da Umma ta ƙira sunanta, sannan a ɗan firgice ta amsa tare da miƙewa tana faɗin, "Ummansu bari mu tafi kar ruwa ya sauƙo, kinga garin sai walƙiya ake ga cida, zuwa safiya in sha Allah za mu shigo sai mu wuce asibitin tare." Jinjina kai Umma tayi ta ce, "To Allah ya kai mu da rai da lafiya Maman Sadeeq, Allah ya saka da alkairi, Allah ya bar zumunci da zaman tare, madallah." Ɗan murmusawa Mama tayi tare da amsawa da Amin, sannan ta dubi Sadiya ta ce, "Tashi mu tafi to uwar son jiki." Sadiya da sauri ta girgiza kai tare da cewa, "A a Mama, a nan zan kwana nikam, kar ki makara a tafi wajan Yaya Sadeeqna ba da ni ba." "Allah ya tashe mu lafiya, dan ba biye miki zan yi nayi magana da darennan ba ga halin da ake ciki, kuma ga hadari a gari ruwa na shirin sauƙowa", faɗin Mama tana miƙewa. Umma murmushin ƙarfin hali tayi tare da cewa, "A isa gida lafiya Maman Sadeeq, auta dai yau wajan Umma za ta kwana, dama ta kwana biyu bata kwana nan ba." Mama sai da safe ta musu ta juya ta fice ita ɗaya, cikin nitsuwa take tafe har ta isa gida, dai-dai lokacin ruwa ya sauƙo. Sai da ta kulle ko ina sannan ta shige banɗaki ta ɗauro alwala, nafila ta yi tare da jero addu'oi wa mamacin mijinta da ƴar ta da kuma magabatan da suka riga mu gidan gaskiya, sannan wa Sadeeq da sauran marassa lafiya gida da asibi, sai wa ƴaƴanta da sauran al'umman Annabi SAW, sai kuma kanta, sai da ta shafa addu'an sannan ta kwanta a madaidaicin gadonta. A ɓangaren Sadiya da Umma, sai da Umma ta rarrasheta sannan suka haura saman bene, ɗakin Umma suka shige, Sadiya ce ta fara shigewa banɗaki ta ɗauro alwala ta fito, sannan Umma ma ta shiga ta yo alwalan ta fito, kusan raba daren suka yi suna nafila da nemawa Sadeeq lafiya wajan Allah maɗaukakin Sarki, Sadiya sai da ta ɗau wayan Umma ta aika saƙo sannan ta ci-gaba da jan carbin da take. ⭐️ PLATEU JOS Old Government Residence Area(GRA). Street 003 H NO: 015 ALIYU HAIDAR POV *** Wani katafaren haɗaɗɗen gida ne, wanda girmansa da haɗuwarsa suka shahara matuƙa, don kallo guda za ka wa gidan ka tabbatar na masu yatsu da yawa ne, don za ka tabbata mamallakan gidan sun kai sun kawo, gidan gidane iya gida, harabar gidan na da matuƙar girma, wanda hasken fitilu ya haska shi tamkar rana ba dare ba, a ƙiyaci kuma dai-dai wannan lokaci zai iya kai tara da mintuna zuwa goma na daren. Ginin gidan ya tsaru matuƙa ta yanda dole a jinjinawa wanda ya zana da waɗanda suka gina gidan, ginin upstairs ne amma ba mai tsayi sosai ba, kaman dai duplex, a sashin da ke gefe a ƙasa, wani haɗaɗɗen palour ne wanda yake ɗauke da manyan kujeru masu matuƙar tsada, kana ganin tsarin palourn ka san sashin namiji ne, saboda ba wasu abubuwan hayaniya a palourn, sashin na da ɗakuna biyu kawai, ɗaya daga ciki mai ƙofa irin ta glass, tsararren ɗaki ne kuma shima bai da hayaniyan kayaki da yawa, daga makeken gadon da ya gaji da kyau, sai ɓangaren da ke manne da mirror a bango da abubuwan buƙata kaman su mayuka da turaruka da sauransu, sai kujeru biyu da ɗan madaidaicin centre table a tsakiya, ga centre carpet mai matuƙar taushi kaman auduga, sai wani ƙofa daga can gefe, wanda in aka shige shi farko closet ne mazubin kaya, daga cikin closet ɗin kuma ƙofan toilet ne a gefe, komai na sashin ya haɗu matuƙa gaya. Haɗaɗɗen matashi ne ke zaune a ɗaya daga cikin kujerun da ke tsararren ɗakin, sanye yake vest fari ƙal da short shi ma fari ƙal mai roɗi-roɗin baƙi, zaune yake ya bai wa ƙofa baya, yana fiskantar taga(window), hannunsa guda riƙe da wayarsa mai mashahurin kuɗi ta yayi, waya irin wacce sai manya isassu ke riƙe wa, da ɗaya hannunsa yake touching fiskar wayar, yana ta faman dialing wani layi da yayi saving da SWEET AL-SAD da emoji na heart da hug da kiss, a zaunen da yake bai shige bayan minti biyar ba kawai da suka gama waya da ita, ta ce masa Mama ta shigo bari su yi magana ta kashe wayan, shikkenan shiru har yanzu ya ƙira ya kai sau goma amma bata ɗaukan ƙira, baya yayi ya jingina da jikin kujeran yana ɗan taune leɓensa cikin rashin madafa, basu saba sallama da ita haka ba, bata saba mishi irin haka ba, ba zai kuma iya bacci bai yi sallama da ita ba, anya lafiya? Ƙira tara ya yiwa Sadiya amma bata ɗauka ba, Sadiyar da bai taɓa mata ƙira uku ba, lafiya ba zai taɓa sanya Sadiya ta ƙi ɗaukan ƙiransa ba duk tsanani, kuma ko a wanni irin hali, ya kuma sani Sadiya ba za ta kasance a lafiya kuma a hayyacinta sannan waya na a tare da ita bata ɗau ƙiransa ba, dole a kwai wani abun. Kammala tuna haka da yayi ya sanya shi miƙewa a hanzarce cikin jarumta, da nufin ya shirya ya je dubo Sadiya ko lafiya?..... *** JUMA'AT KAREEM. Masu daraja habibties ku kasance da alƙalamin Uwar Batoorl, domin wannan tafiyan na daban ne, na musamman ne, za ku shaida haka da yardan Rabbi. # Hareeyh # 09161720046 # 08146334243 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: 💔NAUYIN BAKI....👄💔 Na Uwar Batoorl. ***MASU TALLA ƘOFA A BUƊE TAKE, KU HANZARTA DOMIN AYI INGANTACCIYAR TAFIYARNAN DA HAJARKU, KU KAWO TALLANKU CIKIN AMINCI A TALLATA MUKU SHI CIKIN ANNASHUWA DA SHAUƘI, KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAMBA 09161720046.** 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠 اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 WANNAN PAGE NAKU NE. Maman Ihsan. Dr Seeyert 🅿️ 6 _ 10 ⭐️ Yana miƙewa ya juyo tare da nufo ƙofan da zai sada shi da closet nashi. Haɗaɗɗen gaye ne maƙura wanda kana ganinsa ka san kuɗi da jin daɗi sun samu ɗaurin wajan zama a tattare da shi, tsayinsa dai-dai haka ma jikinsa dai-dai, gashin kansa da ya tara a kwance suke a gyare sun sha askin matasa masu ji da kuɗi da aji da kyau, banda sheki da ƙamshi ba abinda gashin kan nasa ke yi, ga wani saje mai style da gashi dai-dai ɓakiƙƙirin, har zuwa gemunsa da gashin yake dai-dai ba za a ce babu ba kuma ba za a ce ya tara ba, haka ma kasumbarsa dai-dai a gyare, ya zagaye madaidaicin bakinsa mai ɗauke da laɓɓu masu matuƙar kyau da taushi, saboda man da yake shafa musu da kuma tauna su da yake idan yana nufin wani abu, to haka lip's ɗin nasa suka yi ja suka amshe sa sosai, saboda yana da hasken fata haske mai ratsin yellow-yellow, idanuwansa madaidaita ne gwanin sha'awa da iya kallo, idan ya shanye su yayi wa mace wani irin kallo to lokaci guda za ta akfa cikin kogin ƙaunarsa tsundum, da haka yake sharholiyansa wajan gwara kan ƴan mata yana wasa da zuciyoyinsu kaman ƙwallan ƙafa, amma babu wacce ta ishe sa kallo, asali ma shi ba mutum bane mai iya magana biyu, uku ko ya wuce haka da mace, yana da aji sosai-sosai ko cikin abokanansa, domin yana da ƙwarjina ga izza ga kuɗi ga kyau ga ilimi. Jallabiya fara ƙall ya sanya ya fito a closet ɗin, a kan mini centre table da ke tsakanin kujerun ya ɗau keyn motarsa da wayarsa da ya ajiye, daga haka ya juya cikin tafiyar jarumta ya fice a ɗakin, sai dai yana fitowa main palourn ya ci karo da dattijuwar matar da daga ganinta ko ba a faɗa ha kasan mahaifiyarsa ce, duba da yanayin da suke da juna, sanye take da kayan bacci ta ɗaura after dress a kai da ya kulle yanayin kayan baccin nata, hannunta ɗauke da ƙaramar tray, tun da ta fito hanyan kitchen nasu ta hangi fitowansa a sashinsa, hakan ya sanya ta ƙaraso palourn cikin sauri tare da tararsa, kallonsa tayi sama da ƙasa sannan ta haɗe fiska ta ce, "Haidar ina za ka da daren nan?" Haɗaɗɗen matashin da ta ambaci Haidar a matsayin sunansa, marairaice fiska yayi tare da sanya lip nasa a tsakankanin haƙoransa, kaɗan ya cija yana fatan kar Hajiyarsu ta hana shi fita, saboda ba zai iya bacci cikin salama ba tare da ji daga Sadiya ba. Maimaita tambayar tayi ta kuma ɗaura da faɗin, "Yanda na gankan nan nasan fita za ka yi, to inma baka da amsan bani ne sai ka yi maza ka juya ka koma ciki, idan ka kuskura ka ce za ka fita da darennan sai na haɗa ka da Alhaji kuma ka san sauran, fitan daren nan ba ƙaunarsa muke ba, koma menene tun da har goma ta gota kuma kai ma ka shigo gida baka yi ba, sai ka ɗau na Annabawa ka koma ka kwanta, zuwa safiya da rai da lafiya sai ka je ka yi", tana gama faɗan haka, juyawa ta yi ta wuce ta tafi abinta, bata tsaya jiran amsarsa ba, tunda ta san ba amsar zai bayar ba, shegen iyayi ne da shi magana sai ya ga dama. Haidar da sauri ya taune lip nasa da ƙarfi tare da lumshe idanuwansa, sai kuma ya buɗe su tare da bin hanyan da Hajiyarsu ta bi da kallo, ya juya kenan zai nufi sashinsa sai ya jiyo muryan ɗaya daga cikin ƙannensa tana ƙiran sunansa. Wata kyakkyawar matashiya ce mai hasken fata, kuma mara jiki, sai dai tana da kyau dai-dai da kuma shape dai-dai ƙiran jikinta, sanye take da pyjamas riga da wando, rigan mai dogon hannu mai bottons sai wandon dogo har ƙasa, kayan suna da kauri sosai dan cotton ne, kanta a rufe da net cap hannunta riƙe da tsadaddiyar wayanta, tun tana saman bene ta hangi Haidar da Hajiya kuma ta ga alaman fita zai yi, sannan Hajiya ta hana shi, ganin zai juya a zafafe ya sanya ta ƙiran sunansa, "Ya Haidar", ta ƙira sunanshi tana ƙarisa sauƙowa a step's ɗin tare da nufo shi, da siririyar muryarta ta ce, "Ya Haidar coffee kake so ne?", ta yi tambayar ne dan kar ya gane ta ga abinda ya faru tsakaninsa da Hajiya, yanzu ta samu ya kuma ƙullatanta a rai, ta gode Allah kwana biyu tunda aka yi maganan bikinsa da Sadiyarsa, shikkenan ta samu salama ya fara sakar mata fiska har ya saurareta, yanzu ma da ya tsaya ai ita ce da godiya. Haidar a taƙaice ya juyo tare da mata kallon baya buƙatar komai ya gode, sannan ya cigaba da tafiyansa ya nufi part nasa yana jin kaman ya dinga ihu saboda taƙaici, shi ayi-ayo ma sati ukunnan su zo a aura masa Sadynsa shikkenan ya huta. Matashiyar budurwan narai-narai tayi da idanuwa kaman za tayi kuka, a sanyaye ta ce, "Ni Husna na gode wa Allah, ko kaɗan bana burge Ya Haidar, ba abinda zan masa na masa gwaninta, anya a haka Ya Haidar zai so ni har yayi second wife da ni kaman yanda su Hajiya suke cewa? Tun ya Haidar bai kasance ƙarƙashin inuwan aure da Sadiya ba bana gabansa, inaga idan suka kasance ma'aurata, zan iya samun matsuguni a tsakanin masoya biyunnan kuwa? Allah kar ka ɗaura mini abinda bazan iya ba, son Ya Haidar da ƙaunarsa za su illatani", ta ƙarishe faɗa tana share guntun ƙwallan da ya zubo mata, dan ta yiwa Hajiya alƙawarin ba za ta sake kuka akan haka ba. Daga haka ta juya dan ta fasa yin abinda ya fito da ita daman, sama ta haura tare da wucewa ɗakinta. Haidar ko da ya koma sashinsa jallabiyan ya cire ya rataya a kan kujera, sannan ya zauna tare da jingina da jikin kujera ya lumshe idanuwansa, har dare ya raba yana a haka kuma bai yi bacci ba, can wajan ƙarfe ɗayan dare sha biyu ya gota ya ji ƙaran shigowan saƙo wayansa, ko da ya duba daga Sadiya ne amma da layin Umma, sai sannan ya samu salama a zuciyarsa ya wuce ya kwanta saboda a take wani irin bacci ya rufe shi. ***MASU TALLA ƘOFA A BUƊE TAKE, KU HANZARTA DOMIN AYI INGANTACCIYAR TAFIYARNAN DA HAJARKU, KU KAWO TALLANKU CIKIN AMINCI A TALLATA MUKU SHI CIKIN ANNASHUWA DA SHAUƘI, KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAMBA 09161720046.** ⭐️ ABUBAKAR SADEEQ POV *** Su Abba suna zaune shiru jigum-jigum, bayan awanni likitocin suka fito, suna tafe suna cire face mask da handsglove, tare da cire handkerchief daga aljihun labcoat na jikinsu suna share fiska, sauran likitocin biyu wucewa suka yi, ɗaya ne yayi da su Abba magana, murya ba amo ya ce, "Ƙu biyo ni." Abba da Umar ne suka miƙe tare da rufa wa likitan baya, Khalid da Sa'ad suka zauna a wajan bisa umurnin Abba. Likitan jagora ya yiwa su Abba har ƙofan office na likitan da ya kasance babbansu, da hannu ya yiwa su Abba nuni da su shiga, knocking suka yi aka basu daman shiga suka shige, sannan shi kuma likitan yayi gaba ya wuce nashi office ɗin. Da excuse su Abba suka shiga, sun samu dai-dai likitan ya dire goran ruwan da ya gama kwankwaɗa, fiska a sake ya yiwa su Abba nuni da kujeru ya ce, "Alhaji ga waje ku zauna." Abba da Umar zama suka yi, sannan suka haɗa baki wajan yiwa likitan barka, tare da mishi sannu da aiki, likita ƴar murmushi guntu yayi tare da godiya sannan ya jawo file nasu na katin da suka yanka, cewa yayi, "Alhaji ku ne kuka kawo Abubakar Salihu Waziri ko?" Jinjina kai Umar da Abba suka yi a tare, dogon numfashi likitan ya ja tare da gyara zamansa, sai da yayi ƴan rubuce-rubuce sannan ya ɗago, cikin yanayi na alhini amma mai cike da ƙarfafa guiwa ya ce, "Alhamdulillah mun samu daman yin nasara wajan ceto numfashin patient namu, sai dai ya faɗa dogon suma, kuma ba za mu iya faɗan ga lokacin farkawansa ba, idan muka ce to tabbas mun yi ƙarya, domin abu ne wanda sai yanda Allah ya so ya kuma yanke, idan Allah ya so a yau-yau sai ya farfaɗo, wataƙila zuwa gobe, wataƙila kuma sati guda, wasu ma suna iya kwashe shekaru a wannan yanayin bisa yanda Allah ya tsara wa ko wanne bawansa, abinda ya kamata dai mu dage da addu'a, sannan muma duk wani taimako da ya kamata mu ba shi za mu bayar, Allah ya tashi kafaɗunsa." Daga Abba har Umar gumi suka soma sharcewa, a fili suke maimaita kalman, "Innalillahi wa Inna ilaihiraji'un³", Likitan girgiza kai yayi cikin ƙarfafa guiwa ya ce, "Ba abun a ɗaga hankali bane Alhaji, abu ne na a miƙa komai ga Allah a dage da addu'a, cikin ikon Allah da yardansa sai ku ga tun ba a je ko ina ba ya farka, ba abun mamaki bane a cikin iko da zati irin na ubangiji sai ku ji ya farka yanzu cikin darennan, ka ga mu bincikenmu da aikinmu ga abinda ya nuna, amma fa idan muka roƙi Allah mai ƙudurar kun-fa-yakunu sai kaga tsantsar iko irin tasa, da ya ce abu ya kasance sai kawai ya kasance, to addu'a shi ne kawai, amma ba abin ɗaga hankali a nan." Abba jinjina kai yayi cikin gamsuwa da nitsuwa na tunatarwan da likita ya musu, yana sauƙe ajiyan zuciya ya ce, "To Allah yayi ikonsa ya tashi kafaɗun Abubakar cikin gaggawa." "Amin summa amin", likita da Umar suka haɗa baki wajan amsa hakan, sannan likita ya ɗaura da cewa, "Sai kuma zuciyarsa da yanayin yanda take bugawa kaman akwai wani abu, amma dai in sha Allah duk kar ku damu bakomai da yardan Allah sai alkairi, za muyi duk abinda ya kamata in Allah ya so ya amince." Jinjina kai Abba yayi , likitan ya cigaba da musu bayani, suka gode tare da bashi hannu duk suka yi musabaha, sannan suka miƙe suka fice, suna fita a office ɗin sai Abba ya dafa kafaɗan Umar, wanda hakan ya sanya Umar sauƙe ajiyan zuciya tare da rage tafiyarsa, ya zamana suna jerawa da Abba, murya cike da ƙarfafawa Abba ya ce, "Abubakar zai tashi da wuri in sha Allah, kar ka damu sam-sam, idan iyayenku mata suka nazarci wani damuwa a tattare da kai to su ma damuwan za su saka a ransu, mu dage da addu'a kawai kaman yanda likita ya bamu shawara, Allah ya muku albarka ya shige mana gaba duka." "In sha Allah!, Amin Abba", Umar ya amsa yana mai tattaro sauran ƙwarin guiwan da ya rage masa. Sa'ad da Khalid suna zaune a wajan har sauran likitocin cikin suka fito suka wuce, suna zaune shiru har su Abba suka dawo, Sa'ad ne yayi hanzarin cewa, "Abba me liktan ya ce wai? Fatan dai jikin da sauƙi?" "Da sauƙi Alhamdulillah, farkawansa za mu jira kawai", Umar ya faɗa yana ɗan sake fiska, Abba kuma ya jinjina musu kai alaman tabbaci ga abinda Umar ya faɗa, duk ajiyan zuciya suka sauƙe suna hamdala, tare da fatan Allah ya farkar da shi lafiya. Duk a zaune suka kwana, musamman Sa'ad da Khalid a zaune suka yi bacci, Abba da Umar ruwa suka fice suka nemo suka yi alwala, waje mai kyau suka samu suka yi nafila da addu'o'i sannan suka koma wajan su Sa'ad, Umar benci ya nemo wa Abba wai ya kwanta, ba musu Abba ya kwanta saboda jikin girma sai a hankali ba kaman ta yara ba, ba wani bacci Abba yayi ba amma dai dama-dama, shi Umar kuma a zaunen ya kwana ko runtsawa bai yi ba. Ƙiran sallahn farko shi ya tada su duka, ficewa suka yi suka nufi masallaci, ko da suka idar da sallahn a can suka zauna har gari ya ɗan yi haske, sannan suka koma ciki, Umar ne ya ce da Sa'ad ya mayar da Abba gida, ko da Abba ya ce a'a, Umar roƙonsa yayi a kan ya koma gida ya huta shi zai kula da Sadeeq in sha Allah, Abba albarka ya sanya musu duka, sannan shi da Sa'ad suka fito suka shige mota, Sa'ad ya ja su sai gida, suna tafe a hanya Sa'ad ya ce, "Abba daman kai ma ko jiya ai wahalar da kanka kawai ka yi, amma indai Yaya Umar yana nan to ya wadatar da koma menene ga Yaya Sadeeq, haka idan Yaya Sadeeq yana nan to ya wadatar da koma menene ga Yaya Umar, wannan abota tasu sai addu'an Allah ya basu ladarta har a aljanna." "Amin summa amin Sa'adu, Allah ya muku albarka duka." Ko da su Abba suka isa gida, sun samu Umma da Sadiya har sun haɗa abubuwan da za su asibiti da shi, saboda jiyan ba wani bacci suka samu suka yi ba, Sadiya tana tura wa Zakinta saƙo da wayan Umma ta aje ta cigaba da jero addu'oi ga Yaya Sadeeq nata, ko ɓarawon bacci bai ɗauke su ba ita da Umma, ƙiran farko suka miƙe, ana shiga sallah suka yi suka yi azkar da sauransu, sannan Sadiya ta fice ta shiga kitchen a gurguje ta haɗa duk abinda ya kamata. Umma ta kammala shiryawa ta fito palourn tana ƙwala wa Sadiya ƙira a kan tazo ta je ta shirya, Sadiya ta fito kitchen kenan sai ga su Abba sun shigo, da sauri ta fara leƙe-leƙen bayansu tana addu'an Allah ya sa Yaya Sadeeq nata ya warke kenan andawo da shi, amma sai bata ganshi ba, muryan Sa'ad ne ya dakatar da ita daga kukan da take son yi, cewa yayi, "Ƙanwar Yaya Sadeeq ya naga idanuwanki haka?" Sadiya narai-narai tayi da idanuwanta tare da faɗin, "Ina Yaya Sadeeqna?" Sa'ad zai yi magana sai Abba ya ja kunnenshi, tare da cewa, "Yayanki na lafiya auta, kwantar da hankalinki kuka ya ƙare." Ajiyan zuciya Sadiya ta sauƙe tana haɗiye kukanta, a sanyaye ta durƙusa tare da gaishe da Abba tana tambayan ya jikin Yayanta, Abba ya amsa yana murmushi tare da sanya mata albarka, sannan ya wuce ya haura sama Umma kuma ta mara masa baya, ɗakinsa suka nufa kai tsaye. Sadiya a sanyaye ta gaishe da Sa'ad, ya amsa yana murmushi tare da cewa, "Kwantar da hankalinki amaryar Haidar kuma ƙanwar Sadeeq, Yaya Sadeeq yana can asibiti amma jikinsa da sauƙi sosai, farkawanshi kawai ake jira in sha Allah, yana farkawa za ki gansa a gida." Sai sannan Sadiya tayi guntun murmushi tare da muƙewa tsaye, tana faɗin, "Allah ya sa to yanzu haka ma ya farka, shikkenan ba za mu je asibiti ba ni da Umma, Yaya Sadeeqna ya zo ya karya a gida." Sa'ad murmushi yayi tare da cewa, "Matsoraciya kawai, ni na rasa kalan tsoronki da asibiti, Allah ya taro ki amarsu ta ango ƙanwar Yaya Sadeeq", ya ƙarishe faɗa yana bin corridorn da zai sada shi da ɗakin shi. Sadiya sama ta haura ta wuce ɗakin Umma ta shiga wanka, a nitse a sanyaye take komai har ta kammala shiryawa, sannan ta ɗau wayan Umma, ganin har takwas ake nema, aika wa layin Zakinta ƙira tayi, yana ɗauka ta shagwaɓe murya tare da yi masa sallama, ya amsa a nashi ɓangaren tare da tambayanta lafiya kuwa jiya, ai Sadiya kaman mai jiran ƙiris daman, nan da nan ta fara hawaye, cikin shagwaɓa take sanar da shi Yaya Sadeeq ne ba lafiya, kasancewan ya san Yaya Sadeeq ɗin da irin alaƙar tsakaninsu, dan yana mutunta Yaya Sadeeq sosai kaman dai Yaya Umar, kusan zai iya cewa Yaya Sadeeq ne ya shige gaba a duk lamuransu, har maganan aurensu ta kankama ta yi ƙargo, yanzu haka ya rage saura sati biyu da kwanaki shida, cikin yanayi da siga ta lallashi mai ciƙe da ƙauna da tausayi ya dinga tausanta, ita kuwa ta dinga zuba shagwaɓarta, ba tare da sun ankare ba har suka cinye awa guda suna waya, lokacin da ƙiran ya yanke saboda ya cika awa ne, shi ya ankarar da Sadiya maganan zuwa asibiti, da sauri ta miƙe, tana ƙoƙarin ficewa ƙiran Zakinta ya kuma shigowa wayan Umma, inda aka yi saving da Haidar, da sauri ta dawo ta ɗauka tare da cewa, "My Al-Sad za muje asibiti da su Umma, muyi waya daga baya, byee", ta katse ƙiran bata tsaya sauraran amsarsa ba, da sauri ta fice ta sauƙo palourn ƙasa, amma sai dai bata tarar da basket da ta bari na kai wa asibiti ba, tana ƙoƙarin juwa ta koma sama ta dubo Umma, sai Sa'ad da ya fito daga kitchen ya ce, "Koma ki cigaba da bai wa furenki bayi amarsu, Umma da Mama sun jima da tafiya asibiti ai, inajin Umma na faɗin kina waya su je kawai." Wani irin ɓata fiska Sadiya tayi tare da juyawa tana kuka ta haura step's ɗin, Sa'ad yana murmushi ya ce, "Kiyi kuka a hankali dai dan Abba yana saman yana bacci dan ya huta jiya bai yi ba." Sadiya a tunzure ta dakata tare da juyowa, baki a kumbure ta ce, "Bana so Yaya Sa'ad." "To na bari ƙanwar Yaya Sadeeq, amma dai kema kinsan laluranki ta zuwa asibiti, in za ki haƙura ki haƙura kar ki tashi Abba a bacci da wannan murya naki kaman jare, aka je da ke asibiti ai sai lalurarki ta tashi, kema a kama jinyarki kaman Yaya Sadeeq ɗin." Sadiya ƙara ɓata fiska tayi tare da cewa, "koma mutuwa zan yi ni ba ruwan kowa sai naje wajan Yaya Sadeeqna, kuma Haidar zan ƙira ya zo ya kai ni." Sa'ad ɗage kafaɗa yayi tare da faɗin ita

Chapter 2 of 32