Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
anjima, sannan ya sanar da Abba da Umma da dare. Numfashi Khausar tare da cewa, "Yaya Sadeeq bai kyauta ba uncle U." "Shiyasa na mishi tas ban raga mishi ba, domin wannan munafurtata yayi." "Amma uncle U, wani hanzari ba gudu ba, ita small Mum fa? Ya kamata a ji ta bakinta, ka ga kuma Yaya Sadeeq ya ce in ba amincewarta ba zai aure ta ba, kuma gaskiya ina tunanin za a iya samun issue da ita." Umar girgiza kai yayi tare da cewa, "Ki ƙyale ta shirmammiyar nan, ita ma tana son shi sarai, daga kalamanta kana ji ka san tana son shi." "Amma bata fahimci tana son shi ba uncle U, small Mum yarinya ce kuma Haidar ne first love nata, dole sai an fahimtar da ita cikin lallami da salama, in ba haka ba kai ka san matsayin da ta bai wa Haidar da irin son da take mishi." "Wa zai tsaya lallasan Sadiyar? To ko Sadeeq da ya ɗauko wa kanshi hanyar mutuwa ban lallashe shi ba, ko za ta mutu Sadeeq za ta aura, yaushe ma na fara wasar musu da Sadiya? Ki bar hasaso wani matsala daga gare ta, domin Sadeeq ɗin dai shi ne mijinta, su je can daga baya sai ya fahimtar da ita da kanshi, ya kuma lallasheta dan daman shi ke jure shirirtarta da shirme, tunda shi ya sangartata." "Uncle U, batun soyayya ya wuce duk yadda kake tunani, balle ga irin small Mum yarinya ƙarama, dole sai an fahimtar da ita." "To ke sai ki fahimtar da ita, domin ni yiwa su Abba magana ne a gabana yanzu, in ta so ta fahimceki in ta so ta ƙi fahimta, sai dai ta ganta a gidan Sadeeq." Khausar numfashi ta sauƙe mai nauyi, tare da cewa, "Allah ya rufa asiri ma uncle U, Allah ya sa ta fahimtar dai ,sai abun ya fi armashi." "Ita ta sani in bai yi armashi ba, mu dai muka ɗaura musu aure shikkenan, shi kuma idan ya so ya je ya cigaba da zama mata soko, ko kuma ya biye mata ya sako ta, ta zo ta auri wanda take son in dai ta nuna bata son shi." "Yanzu duk ba wannan ba, batun su Abba", Khausar ta faɗa cikin son kawar da wancan shafin, domin ta jima da sani a kan Sadeeq Umar ba abinda ba zai yi ba, kuma idan ya ce zai nuna zuciyarshi da ikonshi, to za a samu jibgegen matsala. "Yanzu zan fara yi da Mama magana, zuwa muka dawo sallahn isha'i ko magrib sai nayi wa Abba bayani na maida mishi har da yadda muka yi da Mama." "A shawarce dai ka bar Mama da kanta ta je ta samu Abban su yi magana ta fahimta." "Kar ki damu sister, na san yadda zan fitowa Abba ya dube mu, in ya so sai a bai wa mutanen Haidar ɗin haƙuri." "Shikkenan uncle U, ba damuwa Allah ya shige mana gaba, ya tabbatar da alkairi, kuma duk abinda ya tsara ya biyo baya, Allah ya bamu zuciyar ɗauka daga mu har su masoyan." "Amin Ya Hayyu Ya Qayyum." Daga haka ɗan tattaunawa suka yi, sannan suka fice a motar, Umar ya kulle abarshi suka nufi ciki da sallama, kasancewar la'asar ta yi, to ba kowa a palourn, Mama na ɗakinta tana salla, Sadiya na nata ɗakin tare da ƙawarta Zahra da su Najla. Umar ɗakinshi ya wuce ya ɗauro alwala ya zo ya fice masallaci, Khausar kuma ta wuce ɗakin Sadiya, tana shiga Nayla ta taso ta mata oyoyo, Najla dai sannu da shigowa ta mata ta amsa, Sadiya ta ce, "Aunty sannan da shigowa." "Yauwa small Mum amarya, ashe har cheif best ɗin ta iso?" Zahra na murmushi ta ce, "Na samu isowa Aunty, fatan kun zo lafiya?" "Lafiya Alhamdulillahi Zahra amare, kinsan an ce ƙawar amarya ma amarya ce, wataƙila cikin abokanaye wani yayi wuff da ke, nan da satanni mu kuma zuwa Jos shan biki." Ƙasa da kai Zahra tayi tana murmushi, sai Sadiya ce ta ce, "Ai aunty ita ma tana da tsayayye, kawai sai mun samu admission ta fara zuwa school sannan za a yi auren, dan Abbanta ya fi so ta fara karatun kamun ta shiga daga ciki." "Da gaskiyarshi ai, yanzu rashin tabbas irin na mazan zamanin yau, ai gwanda ƴar ka ta kama dahir, dan ba a yarda da alƙawarin maza, suna mallakar yarinya su fara gwada ikonsu da rashin mutunci, wasu har ya kai ga rashin kunya ga iyaye ko saki, Allah dai ya rufa asiri ya kyauta, amma duk indai har aka ce ka riga ka fara kamun aka yi auren to ma sha Allah, komai zai zo da sauƙi duk kuwa yadda mutum ya kai ga rashin kirkinsa." "Haka ne wallahi aunty, Allah dai ya shige mana gaba", faɗin Zahra, domin ta ga tabbacin zancen Khausar, akan wata cousin sisternsu da har yanzu ake fafatawa. "Amin Zahra, ya kika baro su Umma da kowa." "Duk suna lafiya suna gaida ku." "Ma sha Allah", Khausar ta faɗa tana nufar toilet. "Aunty kin gama bayani, to ni kuma fa kar dai Al-Sad ya mini halin maza", Sadiya ta faɗa tana langwaɓar da kai. "Idan ya miki shikkenan kin huta, dama Yaya Sadeeq ke so ki yi karatu ai ke ba so kike ba, balle ma Haidar ba zai yi haka ba in sha Allah, in kuma yayi to Yaya Sadeeq da uncle U sun ishe shi tuwo da miya", Khausar ta ƙarishe faɗa tare da shigewa toilet bakinta ɗauke da addu'a. Zahra ƙasa-ƙasa ta ce, "Wallahi gaskiyan Aunty ba kya son karatu, amma dai duk da haka ki daina lissafo wani abu mara kyau daga mijinki tun ba ki shiga ba, is not good." "Ke dalla malama kauce, barmu mu da muka kusa shiga daga ciki muyi bayani, idan kina son ki zauna lafiya a gidanki, to ki saka a ranki namiji is capable of doing anything, zai iya yin komai, kinga ko gani kika yi yayi, ko kuma aka baki labari yayi, ko kuma ya aikata miki wani abun, to hankalinki kwance daman kin tsammaci zai yi hakan ba zai dame ki sosai ba." "Hmmm!, kuma fa da gaskiyarki Sady, Allah dai ya ƙarawa waɗanda suke ciki haƙuri da zaman lafiya, ku masu shirin shiga Allah ya sa ku shiga a sa a ku zauna lafiya har mutuwa, mu ma kuma Allah tabbatar da alkairi da na gari mu shiga a sa'ar." "Amin Aminiyas", daga haka suka cigaba da shirye-shiryensu, wanda za su fara ranar Wednesday Henna day, Thursday Nupe day, Friday walima sai ɗaurin aure ranar Saturday. Khausar tana fitowa ta kabbara salla, Sadiya ma toilet ɗin ta shige ta ɗauro alwala, ta fito ta kabbara salla, Zahra dai tana zaune dan fashin salla take.   Najla ma alwalan ta yi ta zo ta bi sahun Sadiya, Nayla kuka ta fara wai ita ma salla, Zahra ce ta ɗauketa ta kai ta toilet ta mata alwala, sannan ita ma tayi salla kunnen kowa ya huta. Umar ko da ya dawo masallaci, ɗakin Mama ya wuce kai tsaye, da sallama ya shiga bayan ta amsa ta bashi iznin shigowa.   Waje ya samu ya zauna tare da mata barka da gida. Mama da ke zaune kan sallaya ta ce, "Yauwa Umar, ya labarin jikin mai babban suna? Yau duk baka leƙa shi ba tunda ka dawo da safe." "Abba ne ya ce in zauna a gida Mama, amma zuwa dare zan koma mu kwana kamar ko yaushe." "To ma sha Allahu, Rabbi ya yi muku albarka duka, Allahu ya tashi kafaɗun mai babban suna a sallamo mana shi da wuri." "In sha Allah a cikin kwanaki biyun nan za a sallameshi, na leƙa shi ɗazu, ina dawowa wajanshi na wuce masallaci, shigowana yanzu kenan, kuma na baro shi jikin da sauƙi sosai." "Alhamdulillah, amma wannan abu yayi mini daɗi, Allah ya ƙara mishi lafiya." "Amin Mama, uhmn dama akwai maganar da nake so muyi akan Sadeeq ɗin", Umar ya faɗa yana yin ƙasa da kan shi. Gyara zama Mama tayi tare da fiskantar Umar ta ce, "Ina saurararka Umar." "Mama akwai matsala, amma in kuka yi haƙuri kuka fahimcemu, kuma kuka mana uzuri to matsalar ba babba ba ce, tabbas bamu kyauta ba, amma dan Allah a fahimce mu." Mama cikin rashin gane kwana-kwanar Umar ta ce, "Wannan dogon labarin ba ni fahimtar shi, je kai tsaye ka faɗa mini menene, tunda ka ce a kan mai babban suna ne, ai dole zan fahimta na muku uzuri, ina jin ka." "Mama dama akan ciwon da yayi ne, asalin abinda ke damunshi." "Menene asalin abinda ke damunshi? Me ya kayar mini da yaro lokaci guda? Faɗa mini ina saurara, domin abinda muke ta mararin ji kenan, dan mu san ta yadda za mu ɓullowa lamarin, mu samu muyi wa tufkar hanci", Mama ta faɗa cikin ɗaukin son jin damuwar Sadeeq dan su nema mishi mafita. "Soyayyar Sadiya ce tayi sanadin faɗuwar Sadeeq", Umar ya faɗa yana mai ɗagowa dan kallon reaction na Mama, da kuma ya ji me za ta ce. Cikin rashin fahimta Mama ta ce, "Ban gane ba Umar, ban fahimci me ka ce ba." "Mama Sadeeq yana son Sadiya, kuma ya jima yana son ta, domin soyayyar Sadiyar ce ma tayi sanadin ciwon da yake yi." "Sadiya dai Sadiyar da na sani ita mai babban suna yake so? Kuma har sanadin soyayyarta ne yake a cikin wannan hali?" "Eh Mama", Umar ya faɗa yana jinjina kai almar tabbaci. Mama shiru tayi na wasu mintuna, idanuwanta tsurr a kan Umar, sai ta ce, "Amma saboda ba ka da hankali, kana sane da duk wannan, shi ne har sai yanzu kake sanar mana? Da mai babban suna ya mutu kuma shikkenan ba za ka faɗa mana ba ko? To da wallahi ba zan yafe maka ba Umar..." Da sauri Umar ya katse Mama ta hanyar cewa, "ki yi haƙuri Mama dan Allah, wallahi nima sai yau nake sanin gaskiyar, da a ce na san a kan Sadiya ce da ko ni da kaina na biya sadaki an ɗaura musu aure, Allah nima yau nake sani, kuma ke na fara sanarwa yanzu, sai zuwa anjima zan sanar da su Abba a san me ake ciki." Mama kallon rashin yarda da cewa wai sai yau ya sani take jifarshi da shi, fiskarta a haɗe tamau, tana ƙoƙarin buɗe baki ta sake yin magana, Umar ya yi sauri katse ta, ta hanyar girgiza kai tare da cewa, "Wallahi Mama da gaske nake.............", Tiryan-tiryan ya labarta mata komai duk yadda aka yi, amma ya ɓoye mata wasu abubuwan da zai sa ta ji haushin Sadeeq, wanda za ta tausaya mishi har ta shige gaba a yi auren kawai ya sanar mata, kuma yayi nasara domin Mama ƙwarai ta tausaya wa Sadeeq, har da ƴar ƙwallarta ta ce, "Allah sarki, mai babban suna ba laifinka kawai bane, har da namu da muka kasa harbo cewa kana son Sadiya, yadda kake bata kulawa da ɗawainiya da ita da komai, dama ya kamata mu fahimci son ta kake a matsayinmu na manya, amma ba mu kawo hakan ba har kana ƙoƙarin rasa rayuwarka, a kan wacce kake da cikakken ikon mallakarta, ka yafe mu, kuma in sha Allah muddin ni ce na haifi Sadiya ba wani ya haifar mini ita ba, to Sadiya matarka ce da yardar Allah." Umar wani irin wawan ajiyar zuciya ya sauƙe, yana jin quite relief, duk da daman ya san hakan ne za ta iya faruwa, domin Mama tana matuƙar ƙaunar Sadeeq, a nitse ya ce, "Zan je mu yi magana da su Abba zuwa anjima, in ya so sai a san yadda za a yi da su Haidar, Allah ya sa kada a samu damuwa." "Amin Umar, kuma in sha Allah ba damuwar da za a samu, ni ce fa na haifi abata, kuma na ce na bai wa mai babban suna ita duniya da lahira, ai ko shi Haidar ɗin ma zai tausaya wa babana tunda dai har ƙoƙarin rasa rayuwarsa yake yi saboda ita, irin wannar ƙauna da babana ke yiwa Sadiya, in bata aure shi ba ai ta yi rashi, namiji ya zaɓi farin cikinka a kan nashi, namiji ya so ka da dukkan komai nashi, ai muddin ba halin banza mace za ta nuna wa namiji ba, irin wannan ai sai mata sun dinga nuni da ita, suna addu'a da fatan da su ne a matsayinta, dan ba a ƙin mutum sai dai a ƙi halinshi, duk yadda miji zai so mace, idan tayi halin kirki na arziƙi barkanta, idan tayi ta tsiya kuma za ta gani a ƙwaryar tuwonta, kuma iya sanina daidai gwargwado halin kirki muka koyar da Sadiya." "In sha Allah ma lafiya lau za su zauna ba komai Mama, Sadiya ai kawai a barta da shirme da shiririta, amma in ba haka ba tana da hankali daidai." Jinjina kai Mama tayi tare da cewa, "To Allah ya tabbar da alkairi ya ƙara wa mai babban suna lafiya, shi kuma Haidar ɗin Allah ya ba shi haƙuri, dan ta Sadiya bana jin komai dan already tana ƙaunar babana, kuma duk inda aka shaƙu ake ƙaunar juna, dan lamarin aure ya shigo ciki ba komai bane." "Ni ma abinda na ce kenan, amma Khausar ta dage wai sai an fahimtar da Sadiyar." "Eh duk da akwai shaƙuwa da ƙauna tsakaninsu, amma tana da haƙƙin a fahimtar da ita, zan kuma mata magana dan ina da tabbacin Sadiya ba za ta musa ba." Jinjina kai Umar yayi cike da gamsuwa da hasashen Mama, domin ko shi haka yake hasashe, ƙauna da shaƙuwar da ke tsakanin Sadiya da Sadeeq ai a bayyane yake, sai dai fatan alkairi, dan ma dai duk hankalin mutane yayi nisa ne, kuma ba wanda ya taɓa lissafo haka, Allah ya kauda wa kowa basirar tuna wannan, in ba haka ba da an fahimci soyayyar su ko ba su furta ba. Tattaunawa Mama da Umar suka yi, musamman a kan danginsu da suke saka ran za su fara zuwa daga gobe litinin, duk da ba wani nisa sosai na a zo a gani bane tsakanin Jos da Minna amma dai akwai masu zuwa da wuri, musamman dangin Mama, dan daga dangin Mama har na Babansu mutanen Niger Minna ne, duk yarensu guda Nupawa ne. Daga haka Umar ya tashi ya fice, ɗakinshi ya wuce ya jawo ayyukansu na company ya fara dubawa. Sadiya da Zahra sun gama shirya komai in da Khausar ta gyara musu, sannan suka ƙira sauran ƙawayen da wayar Sadiya, conference call suka yi, dan ƙawaye shida ta tsaida, uku duk school mate's nata ne, Zahra tana cikinsu, sai guda ɗaya mai suna Salma, ita kuma ƴar anguwarsu ce, amma presently bata nan, sun yi tafiya zuwa Nasarawa sai Wednesday za su dawo ranar da za a fara events, sai kuma sauran biyu daga dangi, ɗaya ƴar ƙanwar Mama, ɗaya kuma ƴar ƙanwar Baba. Goshin magrib Zahra ta yi ma Mama da Khausar sallama, Sadiya ta raka ta zuwa bakin hanya ta samu mashine ta yi gida, Mama sai faɗa take akan Zahra bata tsaya an idar da magrib ba tukunna, don daga Sadiya har ƙawayenta sun san dokar Yaya Sadeeq, babu fita goshin magrib, irin Sadiya kam ma muddin aka yi magrib to ba inda take zuwa sai ko idan gidan Umma, nan ma Sadeeq faɗa yake wai ranar da za ta kwana wajan Umma to ta tafi tun kamun magrib, ranar da ta kuskura kuma ta je anguwa ta kai magrib to kashinta ya bushe. Sai da suka ida sallar magrib suna zaune duk kan darduma jiran a ƙira isha'i, Khausar da kuma Sadiya har da asu Najla, Khausar ce ta numfasa tare da cewa, "Small Mum." "Na'am aunty", Sadiya ta faɗa tana tsayar da danna counter da take yi, saboda yanayin sautin muryan Khausar, ya nuna magana za ta yi ta serious. Khausar jim kaɗan ta yi shiru, sai can ta ce, "Small Mum ban san ya za ki ɗauki lamarin ba, amma dai kamun na miki dalla-dalla, bari na baki a dunƙule na ga ko za ki fahimci wani abu, amma kada ki mana gurguwar fahimta, muna sonki kuma muna sonki da alkairi, muna kuma miki addu'an samun duk abinda yake mafi alkairi a rayuwarki." "Amin aunty, na san ba za ku so ni da abinda zai cutar da ni ba." "Yauwa small Mum tawa, kinsan Yaya Sadeeq da ya faɗi aka kai shi asibiti me likitoci suka ce?" "A a aunty", faɗin Sadiya tana girgiza kai. *** Umma da Abba duk idanuwa suka zuba wa Umar, cikin rashin fahimtar me yake faɗa. Umma na ƙoƙarin magana Abba ya rigata ta hanyar cewa, "Umaru bana son shirme da shiririta, kana cewa auta shirmammiya, kai yanzu me kake yi? Abubakar ɗin ne ya ce maka Halimatu yake so? Yaushe kuka yi haka da shi? Kai duk ma ba wannan ba, a ina ka taɓa jin an nemi aure cikin aure ko a wasa?" Umar Marairaicewa yayi, tare da sake yin ƙasa da kai, cikin muryar magiya da sigar tabbatarwa ya ce, "Wallahi Abba Sadeeq yana son Sadiya, kuma ai ba wani neman aure kan nema tunda....." Abba cikin haɗe rai ya katse Umar, tare da cewa, "Ba na son shirme Umaru, ka tashi ka bani waje, ba mai maidamu ƙananun yara, auta da yardar Allah Aliyu za ta aura, daga kai har Abubakar ɗin ku bar wasar kwaikwayonku, domin ba zan ba shi auren Halimatu ba, ya mutu ɗin, Allah ya ji ƙan shi muma duk hanyar muka kama." Da wani irin sauri Umar ya ɗago kan shi jin furucin Abba, Umma ƙasa tayi da kanta ta ma rasa me za ta fara tunawa, Umar na ƙoƙarin magana, Abba ya dakatar da shi tare da ɗaga mishi hannu ya ce, "Tashi ka je na gama magana, ba zan bai wa Abubakar auren auta ba, Aliyu za ta aura." *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD @Uwarbatoorl96 ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 💔NAUYIN BAKI....👄💔        Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠     اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 WANNAN PAGE NAKI NE     Maman Muhammad, Hajiyata mai capacity. 🅿️ 31 _ 32 ⭐️ Umar yana sababben aikinshi da system (dama shi ko a company field nashi kenan, dan shi computer science ya karanta, he's both computer engineer and software engineer). Bai tashi a wajan ba sai da aka fara ƙiraye-ƙirayen sallahn magrib, hakan ya sanya ya ajiye system ɗin ya rufe, kana ya miƙe ya shige toilet nashi ya ɗauro alwala, a madaidaicin closet nashi ya ciro jallabiya ya sanya, ya feshe jikinshi da daddaɗar turarenshi.   Umar haɗaɗɗe ne matuƙa, komai nashi cikin tsafta da aji yake yi, duk da kasancewar gidansu madaidaici kuma na rufin asiri, amma ɗakinshi na da ɗan girma, inda yake da gadonshi isashshe mai taushi, wanda ke kasancewa a malmale cikin tausasshen bedsheet ko da yaushe, saboda Umar akwai tsafta, dan har Mama watarana ta kan ce mishi, "Umar da matarka ce za ta ke maka wanki to da ta shiga uku, wannan ƙalƙale-ƙalƙalen naka da yawa yake". Shi dai Umar sai dai ya murmusa, domin ya san gaskiya Mama take faɗi, tunda ga shi ko yanzu ma ya cire jallabiyan da ya shigo da shi, wani ya saka. Akwai Sofa a ɗakin nashi, one-one seater guda biyu da centre table a tsakaninsu, daga gefe akwai madaidaicin fridge, sai mirror, sai closet nashi madaidaici, da kuma studying table da kujerarshi, inda yake adana systems da files da sauran abubuwan da suka shafi aikinshi ko na karatu.     Ɗakin nashi ba hayani sosai, kuma a ƙayace yake matuƙa, centre carpet mai laushi da ke lailaye a tsakiyar ɗakin, sai ya haska ɗakin sosai, ƙamshi da haɗuwar ɗakin Umar, idan suka haɗu da kana tsaye a kan wannan carpet ɗin, sai ka kusa mance inda kake. Yana kammala feshe turarenshi ya ɗau wayarshi ya fice a ɗakin, ba kowa a palourn nasu hakan ya sanya ya fice kai tsaye, a ƙafa ya ƙarisa masallacin, yana isa Abba na isowa, musabaha suka yi da Abba sannan ya mishi barka da fitowa, suka shige masallaci suka bi sahu, a ka kabbara cikin jam'i aka yi sallah, bayan an idar sun shafa addu'a sai Abba ya miƙe yana faɗin, "Bari mu shiga ciki kamun isha'i ya yi", alamar dai akwai uzurin da zai hana Abba jiran isha'i. Umar ma miƙewa ya yi tare da cewa, "Dama akwai maganar da za mu yi Abba mai muhimmanci." "To bismilla mu je Umaru." Suna tafe Umar na ta ƙoƙarin yi wa Abba bayani cikin kwana-kwana, amma Abba bai fahimta ba, har suka ƙarasa ciki, Umar ya tsaya daga palourn ƙasa, Abba kuma ya haura sama, ba jimawa ya dawo, zama yayi a kujeran da ke kallon wanda Umar ke zaune, sannan ya ce, "Ina sauraranka Umaru." Umar ya buɗe baki cikin ƙarfin guiwar sanar da Abba kai tsaye, sai ga Umma na sauƙowa daga stairs da hijabi jikinta, alamar ita ma idar da sallanta kenan, murmushi Umar yayi, tare da cewa, "Barka da fitowa Umma." "Yauwa Umar, barkanmu, ya wunin yau ɗin? Fatan ka huta da kyau?", Umma ta ƙarishe maganar tana zama a kujeran da Abba ke zaune mai ɗaukar mutum uku." "Alhamdulillah Umma, sai godiya." "Ma sha Allah, haka ake so Umar, Allah ya muku albarka, sai haƙuri kuma da rayuwa, musamman mata, maƙota da kuma abokanan kasuwanci." "In sha Allah Umma", ya amsa yana murmushi dan ɗazu Khausar ta faɗa mishi yadda suka yi da Umma. Abba gyaran murya yayi tare da cewa, "Umar ina sauraranka." Ƙasa Umar yayi da kan shi, a nitse ya ce, "Abba dan Allah a dube mu a kuma lamunce mana a yafe mana", yana gama faɗin haka ya yi shiru.     Amma jin su Abba basu ce komai ba sai ya numfasa tare da sake cewa, "Sadeeq yana son Sadiya, kuma soyayyarta shi ne sanadin ciwon da yake ciki, Abba kuma wallahi za mu iya rasa Sadeeq muddin bai samu Sadiya ba, tun sadda ya farka sanadin zuwan Sadiya asibiti, da wasu abubuwa da suka dinga faruwa suka ɗarsa mini zargin haka a zuciyata, har dai na ce maka in sha Allah zan bincika abinda yake ɓoyewa, to wallahi Abba sai yau na gano soyayyar Sadiya ce da yake ɓoyewa, ya zama maƙasudin komai." Abba da Umma daman da farko sun yi shiru ne, sun zuba wa Umar ido saboda basu fahimci yafiyar da ya fara nema ba kamun bayani, amma yanzu da suka ji abinda ya ce, kamun Abba ya ce wani abu, Umma ta ce, "Shi Sadeeq ɗin ne yake son Auta? Da gaske ko da wasa Umar?" Umar ƙasa yayi da kai tare da cewa, "Wallahi Umma da gaske ne, kuma dan Allah a taimaka mana." Umma da Abba duk idanuwa suka zuba wa Umar, cikin rashin fahimtar me yake faɗa kuma me yake nufi da a taimaka musu, tabbas sun ji me ya ce, amma ba su fahimta ba har sannan, domin mamakin maganar suke. Umma na ƙoƙarin sake yin magana sai Abba ya rigata ta hanyar cewa, "Umaru bana son shirme da shiririta, kana cewa auta shirmammiya, kai yanzu me kake yi? Abubakar ɗin ne ya ce maka Halimatu yake so? Yaushe kuka yi haka da shi? Kai duk ma ba wannan ba, a ina ka taɓa jin an nemi aure cikin neman aure ko a wasa?" Umar Marairaicewa yayi, tare da sake yin ƙasa da kai, cikin muryar magiya da sigar tabbatarwa ya ce, "Wallahi Abba Sadeeq yana son Sadiya, kuma ai ba wani neman aure kan nema tunda....." Abba cikin haɗe rai ya katse Umar, tare da cewa, "Ba na son shirme Umaru, ka tashi ka bani waje, ba mai maidamu ƙananun yara, auta da yardar Allah Aliyu za ta aura, daga kai har Abubakar ɗin ku bar wasar kwaikwayonku, domin ba zan ba shi auren Halimatu ba, ya mutu ɗin, Allah ya ji ƙan shi muma duk hanyar muka kama." Da wani irin sauri Umar ya ɗago kan shi jin furucin Abba, Umma ƙasa tayi da kanta ta ma rasa me za ta fara tunawa, Umar na ƙoƙarin magana, Abba ya dakatar da shi tare da ɗaga mishi hannu ya ce, "Tashi ka je na gama magana, ba zan bai wa Abubakar auren auta ba, Aliyu za ta aura." Umar rau-rau-rau yayi da idanuwa alamar magiya, amma Abba haɗe fiskarshi yayi bai ko sake kallon inda Umar ke zaune ba, Umma kallon Abba ta yi, sannan ta kuma mayar da idanuwanta

Chapter 18 of 32