Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bacci ya yi gaba da shi. Washe gari kamar yadda Hajiya ta ce, da wuri jama'arta suka fara taruwa, zuwa azahar duk waɗanda ta sanar wa sun hallara, danginta da na Alhaji, da kuma abokanan arziƙi da ƙawayenta, suka sako kaya a gaba suka nufo gidan su Sadiya cikin motoci. Kaya ne niƙi-niƙi a set guda na akwati orange color, da kuma set na handmade gift packaging basket na saƙa, wanda ake wrapping nashi da shining net mai kyau da flowers, kayaki ne masu kuɗi da kyau babu na wasa, duk da a haka sai da Alhaji ya yi ƙorafi ganin set guda na akwati da kuma handmade packaging basket, wanda suka yi da Hajiyar duk set bibbiyu za a haɗa, amma kuma abinda Hajiya ta faɗa, ya sanya shi zuba mata ido tare da girgiza kai kawai bai sake cewa komai ba, lamarinta kullum gaba-gaba yake yi, ga shi dai kamar ta daidaita komai ta bari, amma ashe ba haka bane, shi dai nashi ido, zai kalli yadda komai zai tafi, amma dai yana yi musu fatan alkairi, musannan wa ɗan shi. A gidan Mama tawagar kawo kaya suka samu masauƙi, inda aka cika su da ashirin da bakwai na arziƙi, wanda kayan ciye-ciye da sauransu duk daga gidan Abba ne, dan aunty Kulu ko da ta sanar da Mama batun kawo lefe da suka yi magana da Sadiya, Mama shiru ta yi bata kuma cewa komai ba, amma ranta ba daɗi sam, haka ya sa ko da Umma ta shigo su gaisa da su aunty Kulu, sai aunty Kulu ta sanar wa Umma, ita kuma Umma ta sa Khausar ta taya ta suka shirya komai da ya kamata, bayan ta sanar wa Abba za a kawo kaya, kuma yayi Allah sanya albarka tare da bayar da ƙudin da ake bayarwa na tukuicin masu kawo kayan. Su Umma sun yaba kaya sosai-sosai da su aunty Kulu, cikin mutunci da raha suka rabu da masu kawo kayan, suka kama hanya suka tafi, su kuma suka zauna kallon kaya suna santi, dan tabbas ba ƙarya an kashe Naira a wannan lefe, Mama dai ƙala bata ce ba, maƙota suka ci gaba da shigowa suna kallo ana sanya albarka.   Mama ta ce da aunty Kulu zuwa dare su tattara kaya su mayar gidan Abba, idan ya gani sai a ajiye kayan a can, duk waɗanda suka zo daga baya su je can su kalla, aunty Kulu ta amsa kuma ta yaba da karar da Mama ta yi wa su Umma. ⭐️ Ƴan kai kaya da suka koma, ba abinda suke yi sai yabon irin tarban da aka musu, Hajiya dai tana jin su amma bata ce komai ba, domin ta jima da sanin wani abu ba iyayen Sadiya ke yi ba, maƙotansu ne iyayen abokin Yayan Sadiya, a kan haka kuma ta shirya shirinta daban da za ta ƙaddamar, daga haka aka yi ƴan hira, aka kuma kassafa abinda aka ba su na tukuici, sannan kowa ya kama hanya ya koma gidanshi, Nihal tana cikin masu kai kaya, ta yaba da komai na dangin Sadiya, ta kuma ji babu daɗi da ta nemi ganin Sadiya amma bata samu hakan ba, ita dai fatan ta Allah ya taro Hajiya da batun Husna, su Sadiya da Ya Haidar su zauna lafiya su sha soyayyarsu. Haidar kuwa yana samun tabbacin isar kayan aurenshi da kuma IV ga Sadiya daga bakin Nihal, ba ƙaramin farinciki da nishaɗi yake ciki ba, ji yake kawai ya mallaki Sadiya, shedu ne kawai suka rage, hakan ya sa ya yiwa Nihal tukuici, yana kuma mai jin kamar ya ƙira Sadiya, amma fushin da yake yi da ita haka kawai yake sake hauhawa a zuciyar shi, sai kawai ya basar da batun ƙiranta, ya tsaya ganin iya gudun ruwanta za ta ƙira shi ko kuwa fushi ta yi ita ma. ⭐️ Ɓangaren Sadeeq da Umar, washe-gari da wuri suka wuce office, bayan Umar ya sake buga wa Sadiya warning da safe a kan, kada ya dawo gidan ya samu wani magana bayan ta Sadeeq, hakan kuwa ba ƙaramin sake sanya ta a damuwa yayi ba, sanin yau za a kawo lefe, shiyasa ta wuni tana ɓoye kanta a ɗaki, ƙarshe ma a sace ta fice ta wuce gidan Umma, ko Khausar da Umma basu san shigowarta ba suna aikin abun bai wa masu kawo kaya, da farko sashin Yaya Sadeeq ta yi niyan zuwa dan sanar da shi gaskiyar irin soyayyar da take mishi, ta san zai fahimceta kuma shi ne kawai zai iya cetonta daga Yaya Umar, amma ta samu Yaya Sadeeq baya nan, haka ya sa ta zauna a nan sashin shi, kawai ta kasa kunnuwa dan taji shigowar Abba ta mishi magana, duk da ɗaya bata san me za ta ce mishi ba, a nan sashin ta yi azahar da la'asar, a kitchen na Yaya Sadeeq ta samu abu ta sanya wa cikinta, dan ji take tsakanin jiya da yau, ulcer na barazanar yi mata mugun kamu, ga shi ta zabge kamar wacce ta yi wata tana jinya, idanuwanta duk sun kumbura sun yi luhu-luhu da su. Har goshin magrib sannan ta ji motsin shigowar Abba, hakan ya sa ta fito da sauri, yana ƙoƙarin haurawa step's ta tsaya a tsakiyar palourn, kanta a ƙasa ta ce, "Abba sannu da dawowa." Abba na murmushi ya juyo tare da cewa, "Yauwa auta, sannunmu ko." Sake duƙar da kanta ƙasa ta yi, tana murza yatsunta, domin ta rasa me ma za ta fara cewa. Abba da har ya juya, jin shiru alamar bata wuce ta zauna ba ko tafiya, sai ya dakata tare da juyowa, daga yadda take tsaye ya fahimci akwai magana a bakinta, hakan ya sa ya ce, "Yanzu dawowa na auta, bari na yi sallah sai mu yi maganar da ke tafe da ke ko." Jinjina kai Sadiya ta yi, tana mai jin salama a zuciyarta gefe guda, dama-dama take ji, da Abba ya fahimci tana tafe da magana, sai dai a yanzu ne take jin rashin kyautawarta, da kuma ganin tsantsar gaskiyar Mama da take cewa bata ji kunyar Abba ba, da ta nuna mishi bata yarda da batun yaron shi ba. Wannan tunani ya sanya Sadiya sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, tana jin lallai-lallai cikin biyu dole a yi ɗaya, ko ta jure wa ko ma menene daga Haidar, ko kuwa ta jure wa ko ma menene daga Yaya Umar, amma ko ba dan Yaya Umar ba, ko dan su Abba za ta amsa wa batun Yaya Sadeeq a yau, ko hakan na nufin komai gare ta ne, za ta amsa wa Abba cewa Yaya Sadeeq ta zaɓa, da shi ta aminta, ko da zuciyarta za ta fashe ne saboda yankar ƙaunar da ta mata, tsakaninta da zuciyar Haidar. *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD @uwarbatoorl96. ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚[22/12/2025, 09:15] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 💔NAUYIN BAKI....👄💔 Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠 اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 41 _ 42 ⭐️ Sadiya sai da ta gama zancen zucinta, sannan ta sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya tare da haurawa benen, kai tsaye ɗakin Umma ta nufa, a can ta yi alwala tare da gabatar da nata sallahn magrib ɗin. Daidai Abba ya dawo masallaci, su Umma da Khausar ma suka shigo, dawowarsu daga gidan Mama kenan, bayan gama ƴar hira da suka tsaya yi, bayan tafiyar masu kawo lefe. Khausar ce ta ɗan rusunar da kai tare da cewa, "Sannu da dawowa Abba." "Yauwa auntyn Abba." Nayla ma sannu ta yi wa Abba tana lafe a jikin Khausar, dan Najla tana can gidan Mama tare da yaran baƙin da suka zo, dan wasu mutanen ma sun zo yau, bayan su aunty Kulu da suka zo jiya. Umma sannu ta yiwa Abba, ya amsa yana faɗin, "Uwar amarya har baƙin naku sun koma kenan?" "Eh Abban yara, sun koma tun ɗazu, mun ɗan tsaya hira ne ma, ka san jama'a sun fara zuwa." "Ma sha Allah, yadda Allah ya kawo su lafiya, muna fatan a fara hidima lafiya a kammala lafiya, kuma Allah ya mayar da su gidajensu lafiya." "Amin Ya Rabbi", Umma da Khausar suka haɗa baki wajan amsawa. Abba haurawa yayi bene, tare da nufar ɗakin Umma, sai da ya tsaya yayi sallama Sadiya ta yi masa iso, sannan ya shiga ɗakin. Daga bakin gado Abba ya zauna, yana kallon Sadiya da ke zaune kan darduma kan ta a ƙasa, sai da Abba ya amsa sannu da shigowa da ta masa, sannan ya ce, "Auta ina sauraranki, me ke tafe da ke?" Sadiya ƙasa tayi da kanta, yatsun hannunta take wasa da su, ta kasa cewa komai, kunyar Abba a gefe guda, ga kuma tuƙuƙi da ɗaci a ɗaya gefe guda na zuciyarta, abinda ta yanke a zuciyarta za ta furta a yanzu, shi ne kuskure mafi girma da za ta aikata a duniyarta, amma za ta aikata hakan ko da zai kawo ƙarshen numfashinta ne. "Ina sauraranki auta, faɗa wa Abbanki abinda ke zuciyarki, Abba zai fahimceki in sha Allah, ki daina jin shakka, kunya ko tsoron faɗawa Abbanki duk abinda ke damunki", Abba ya ƙarishe maganar cikin sigar rarrashi. Sake yin ƙasa da kai Sadiya tayi, tana buɗe baki idanuwanta suka ciko da ƙwalla, muryarta na rawa ta ce, "Abba ba na nufin da Haidar na aminta, na faɗi cewa duk abinda kuka zaɓa mini na amsa ne, saboda...I.. ina..ina..nufin..Ya.ya Sadeeq, da...da shi na yarda", Sadiya ta faɗa tana mai fashewa da kuka mara sauti, hawaye suna sintiri a kumatunta. Abba idanuwa kawai ya zuba wa Sadiya, domin duk ƙasa da take yi da kanta da kuma shanye kukanta, ya fahimci halin da take ciki, wadda hakan ya sake shaida masa abinda ke zuciyarta, ya san kawai ta furta abinda ta furta yanzu ne a baki ba wai har zuci ba. "Maman Abubakar", wani ɓangare na zuciyarsa ya furta haka, duk yadda za a yi Maman Abubakar ce ta sanya ta dawowa da wannar magana, tunda su Umar ya gama magana da su tun jiya an wuce wajan. Sai da Abba ya numfasa sannan ya ce, "share hawayenki auta, abinda kike so in sha Allah shi zan miki", iya haka Abba ya faɗa kawai ya tashi ya fita a ɗakin, domin zuciyarsa ta gama amanna da cewa Maman Abubakar ce ta matsa wa auta, kuma zai yi wa tufkar hanci a yau yau ba sai gobe ba. Sadiya tana tabbatar da ficewar Abba a ɗakin, kawai ta fashe da kuka tare da haɗe kanta da guiwa ta shiga rerawa mai sauti, tabbas ta saya wa kanta tikitin zubar da ƙwalla, yanzu ta fara kuka in dai har ƙaddara ta damƙa wa Yaya Sadeeq igiyoyin aurenta. ** Umma da Khausar suna zaune a palourn sai ga Sadeeq ya shigo, sannu da gida ya musu, Khausar ta masa sannu da dawowa, ya amsa sannan ya wuce sashinsa, ba jimawa Khalid da Sa'ad suka shigo, Sa'ad ma sannu ya yiwa su Umma ya wuce ɗakinsa kai tsaye, Khalid kuma a kan sofa mai ɗaukar mutun biyu ya zauna, tare da yin baje-baje ya kishingiɗa yana cewa, "Gaskiya aiki da wahala." Umma girgiza kai kawai ta yi tare da cewa, "Allah ya shirya mini kai Khalid." Khausar ta ce, "Amin dai Umma, dan wannan son jiki irin na Khalid sai da addu'ar shiriya, wannan ƙorafi da yake yi, idan wani ya ji zai ɗauka ko rodi suke ɗaga wa a wajan aikin." "Aunty Khausar ba za ki gane bane, amma dai Allah ya shiryani kamar yadda Umma tayi addu'a." "To Amin, da sauƙi tunda kai da kanka ka san kana buƙatar addu'ar shiriya." Khalid tashuwa yayi ya wuce ɗakinsa, yana dariyar kallon da Umma ke bin sa da shi. Girgiza kai kawai Umma tayi, daidai Abba ya yi ƙiranta, tana ɗaukar ƙiran ya sanar mata ta tura Khausar ta ƙira masa Maman Abubakar, ita kuma ta zo ta same shi. Ba ɓata lokaci Umma tayi duk yadda Abba ya ce, khausar ta wuce ƙiran Mama, ita kuma ta haura sama ta wuce ɗakinsa kai tsaye, tana shiga da sallama ya amsa mata, kai tsaye ta ƙarasa inda yake zaune daga gaban gado a kan lallausar darduma mai ɗan girma, sai da Umma ta zauna sannan ta ce, "Barka da hutawa Abban yara, farincikin Halimatu." Abba nauyayyar numfashi ya sauƙe, yana mai jin dama-dama a yanayinsa, sannan cikin dattijuwar muryarsa ya ce, "Halimatu." "Na'am Abban Khausar", Umma ta amsa cikin sassanyar murya, cike da ladabi da ƙauna. "Halimatu, sam-sam ba na son kukan yarinyar nan Sadiya, shi aure bauta ne, wadda ake so bawa ya yi cikin son ransa, ta yadda zai yi haƙuri ya ɗauki duk wata ƙalubale ko ƙaddarar da Allah ya rubuto masa, tunda ba wanda zai bugi ƙirji ya ce yau ga auren da babu ƙalubale a cikinsa, rayuwar ma gaba ɗayanta cikin jarabawa ake tafiya, sai dai abun kamar yatsunmu ne, dole wani ya fi wani ba daidai suke ba, kowa da kalar ƙalubalensa, amma kuma mu iyaye wani zubin muna tsananta wa ƴaƴanmu ƙaddararsu da ƙalubalensu ne bisa hangenmu, ko son zuciyoyinmu." Sai da Abba ya numfasa, sannan ya ci gaba da cewa, "Na fahimci Maman Abubakar, amma ina son ita ma ta fahimce ni, Abubakar yarona ne, kuma sosai-sosai nake son maganarsa da Sadiya, domin na shiga cikin damuwa matsananciya na ciwon da ya kwanta, a lokacin da Umar ya same ni da batun dalilin ciwonsa, na ji ina ma wata daban yake so ba auta ba, to da duk yadda zan yi zan ƙoƙarta wajan samar masa abinda zuciyarsa ke so, amma kuma Sadiya ma ƴa take a wajena, yadda zan so wa Abubakar abinda yake so, ita ma haka zan so mata, kuma alamu sun nuna Aliyu take so, da shi hankalinta ya fi kwanciya, ban yi mamakin haka ba dan na san za a rina wai kare da hauka, to har ila yau Maman Sadeeq bata fahimce ni ba, ita ƴa mace mafi ƙololuwar alhaƙinta da za ka ɗauka a rayuwa, wadda zai daumawar da ita cikin ƙunci da ciwo da damuwa, shi ne ka aura mata wanda ba ta so, ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ya kamata a ce Maman Abubakar ta fahimce ni yadda ya kamata, domin ba zan bari Abubakar ya auri Sadiya ba, ban hangi hakan zai zama adalci ga Sadiya ba duk kuwa da alkairin da zai iya kasancewa a cikin auren, sannan ko shi Aliyu da yardar Allah akwai alkairi a zamansu in sha Allah", cikin kamala Abba ya ƙarishe maganar. Umma sai da ta numfasa, cikin tausayin yaran, da kuma gasƙata maganar Abba, sannan ta ce, "Tabbas Abban yara maganarka dutse, kuma ina fata yadda na fahimceka, ita ma Maman Sadeeq ta fahimceka, ba wanda ya isa ya zartar da abinda Allah bai nufa ba, idan aka bi komai a sannu, in dai auta rabon Sadeeq ce to za ta aure shi, in kuma Haidar ne wanda Allah ya zaɓar mata to dole shi za ta aura ba yadda muka iya, sai dai mu bi da addu'a da fatan alkairi." "Yauwa Halimatu, na ji daɗi sosai da kika fahimce ni." Daga haka Abba da Umma suka ci gaba da tattaunawa a kan lamarin, duk da suna son ɗan su kuma suna tausayinsa, amma a bar wa Allah komai a ga abinda zai faru, a haka suka yi matsaya. Sai da aka ƙira sallar isha'i sannan Abba ya miƙe ya fito dan wucewa masallaci, Umma kuma ta shige toilet dan ta ɗauro alwala ta gabatar da nata. Bayan Abba ya sauƙo daga benen, a palourn ƙasa ya haɗu da duka yaran nasa, su ma sun fito da niyar zuwa masallaci, duk gaishe shi suka yi cikin girmamawa da nitsuwa, ya amsa sannan suka jera suka fice, Sadeeq na a gefen Abba, sai Khalid da Sa'ad suna a bayansu. *** Sadiya sai da tayi kukanta mai isarta, sannan ta lallaɓa ta miƙe ta wuce toilet na Umma, wanko fiska tayi ta fito a sanyaye ta fice a ɗakin, cikin sa a bata haɗu da kowa ba har ta fice a palourn, a compound ɗin ne kawai ta haɗu da mai gadi, har ya mata Allah sanya alkairi, amsawa tayi ta fice a gidan, ta nufi gidansu cikin sansanyar tafiyarta. *** Khausar ko da ta je ƙiran Mama, sai da ta tsaya aka haɗe kayan lefen da mutane suka gama kallo, sannan aka jidi kayan aka nufo gidan Abba, Mama ta mara musu baya, sun shigowa gidan da sallama amma ba kowa a palourn, saboda Abba sun fice masallaci, Umma kuma tana salla a can ɗakin Abba. Waje suka samu suka zauna, ba jimawa Umma ta sauƙo daga benen, tun tana kan stairs ɗin take sakin murmushi, ganin su Mama da kayan lefen, har ta ƙaraso cikin palourn tana murmusawa, sannan ta samu waje ta zauna daga gefen Mama tana faɗin, "Sannunku da shigowa, sannunku da ƙoƙari." Duk amsawa Umma suka yi da murmushi a kan fiskokinsu su ma, sannan suka sake gaisawa duk da sun gaisa da ta shiga ɗazu suka tarbi masu kawo kaya. "Maman Sadeeq kin saka bayin Allah a wahala kawai, ina laifin ki bari Sa'ad da Khalid su jido kayan, ko kuwa shi Abban nasu ya je can ya kalla", Umma ta faɗa da murmushi mai cike da yaba karar da Mama ta musu. "A ƙyale autan maza ya huta, ranan ce mini yayi ya gaji a wajan aiki kaman zai rasu haka yake ji", faɗin Mama. Umma na ƴar dariya ta ce, "Ai Khalid ba ya rabo da abin dariya wallahi, ko ɗazu ma sai da ya raba hali sannan ya yi gaba." Duk jama'ar palourn ma ƴar darawa suka yi, suna cikin ɗan hira jefi-jefi sai ga Abba ya shigo da sallama, duk amsawa suka yi, Khausar ce ta fara yi wa Abba sannu da shigowa sannan ta miƙe ta wuce upstairs dan gabatar da sallar isha'i. "Sannu da shigowa Abban yara", Mama ta faɗa cikin mutuntawa. Abba murmushi yalwace a fiskarsa, ya samu waje ya zauna sannan ya ce, "Yauwa Maman Abubakar, baƙinmu sannunku da shigowa sannunku da gajiyar hanya, fatan an iso lafiya? Ya aka baro sauran ƴan uwan?" Cikin mutuntawa su aunty Kulu suka haɗa baki wajan amsawa Abba, sun zo lafiya kuma kowa na lafiya, suna isar musu da saƙon gaisuwa, sannan suka tambaya fatan sun same su lafiya. Abba na murmushi ya ce, "Duk muna lafiya sai godiya, sannunku bayin Allah." Godiya suka yi wa Abba, sannan suka miƙe dan su koma gidan Mama, Abba yana murmushi ya sake jaddada na shi godiyar, tare da fatan yadda suka zo lafiya, Allah ya sa a gama komai lafiya su koma lafiya, duk da amin suka amsa sannan suka fice. Mama da ke zaune bata bi su sun fice ba ta ce, "Wai baffanun nasu da Kawunai sai ranar Juma'a za su shigo, amma suna miƙo muku saƙon gaisuwa." Murmushi Abba ya yi, tare da cewa, "Muna amsawa ƙwarai, muna kuma godiya, wannan karar da suka mana ta a ɗaura auren a nan ba sai an je wajansu ba, Allah ya saka da alkairi ya bar zumunci har aljanna, Allah ya kawo su lafiya, za a shirya komai in sha Allah kamun su iso." "Allah ya amince Abban yara, mu ne da godiya kam, Allah ya saka da mafificin alkairi." "Amin Maman Abubakar, Allah ya kuma jaddada rahama ga marigayi." "Amin Ya Hayyu Ya Qayyum", Mama ta amsa tana lumshe ido, tare da sauƙe ajiyar zuciya, ko da yaushe tana kasancewa ne a cikin tunani da kewar mijinta kuma uban ƴaƴanta, amma a yanzu da batun auren Sadiya ya tashi har ya matso, tana jin kewarsa da tunaninsa fiye da ko yaushe, lallai akwai ciwo a rashin miji, musamman wadda ya kasance na gari, bango kuma jigo ga rayuwar iyalansa, amma da ikon Allah, Allahn ya amsa wa marigayin addu'ar shi, Allah ya jiɓanci lamuran iyalansa ko da babu ran shi, lallai Allah shi ne majiɓancin rayuwar kowa, sai godiya ga Allah. Ɗan shiru na wasu daƙiƙu palourn yayi, Mama na duniyar tunanin mijinta, Abba na nasa lissafin, Umma ma tana nata lissafin. Abba ne ya katse shirun ta hanyar yin gyaran murya tare da cewa, "Maman Abubakar na aika a ƙiraki ne a kan maganar auta." Sai da Mama ta ja numfashi sannan ta gyara zama, tana yalwata fiskarta da murmushi ta ce, "Ina saurara uban amarya." "Maman Abubakar dan Allah a bar matsawa Sadiya a kan wannan maganar, mu bar komai a yadda yake, in Allah ya sa Abubakar ne rabonta, to cikin ikon shi za a ɗaura da Abubakar ɗin, idan kuma Allah ya rubuto shi Aliyu ne rabonta, to da yardar shi da Aliyun za a ɗaura ba yadda muka iya." Sai da Abba yayi shiru na wasu daƙiƙu sannan ya ɗaura da cewa, "Auta ta kuma zuwa yau ta same ni da maganar Abubakar, ta nuna shi take nufi ba Aliyu ba, sai dai duk da kasancewana namiji, to matsayin mahaifi da nake da shi ya ba ni damar karantar zuciyarta duk da bata furta ba, na fahimci auta Aliyu take so har a zuciyarta, amma tunda naji ta yi maganar Abubakar na tabbata aikinki ne Maman Abubakar, domin shi Abubakar ɗin da Umaru duk mun gama magana da su, komai ya wuce sun fahimta sun kuma yi haƙuri, dan haka a karo na biyu wadda nake fata ya zama na ƙarshe, ina roƙon ki bar maganar Abubakar, da a ce babu Aliyu a zuciyar auta, zan goyi bayan a aura mata Abubakar za su daidaita daga baya, amma a yanzu da take da wani a zuciyarta to ina ba da shawara da kuma umarni a barta ta auri wanda ke zuciyarta, idan ba haka ba garin neman gira za a iya rasa ido." "A a Abban yara, ku ne fa kuke ganin Sadiya ba ta son mai babban suna, amma tana son shi kawai ta kasa fahimta ne, na tabbata kuma aka yi auren za ta fahimta a sannu, kuma ko da na dage a kan aurenta da mai babban suna gata nake son mata, domin abinda babba ya hanga shi yaro ko ya hau rimi ba ya hangowa, sannan kuma Sadiya yarinya ce budurwa, wacce a wannan matakin da take, to alhaƙin zaɓar mata miji a kan iyaye yake." "Haka ne Maman Abubakar, maganarki duk ba ta yadawa, gata kike son ki mata, kuma alhaƙin zaɓar mata miji na hannunmu, amma kuma idan muka koma baya a zamanin Manzon Allah SAW, akwai kissa a dangane da irin wannan ƙulli, akwai yarinyar da aka yi haka da ita, mahaifinta ya zaɓar mata miji ya aurar da ita, amma ta ƙi, aka dinga kai ruwa rana har abu ya kai gaban Annabi SAW, ko da Annabi ya tambayi ba'asin shari'ar ta su, mahaifin ya kawo hujjar alhaƙin da iyaye ke da shi na zaɓar wa yarinya miji a matakin budurcinta, da aka koma kan ita yarinyar kuma dan jin ta bakinta, sai ta kawo hujjarta na, ba ta ja da alhaƙin da iyaye ke da shi na zaɓarwa yaransu mazaje, amma kuma akwai matakin da idan yarinya ta kai, to ko budurwace a barta ta tsayar da miji da kanta, irinsu kenan, kuma wannan amsar da ta bayar ya gamsar har ya sa aka ja layi a ƙasar maganarta, wasu shekaru ko matakin wayewa idan yarinya budurwa ta kai, maslaha shi ne a barta ta zaɓi miji da kanta, kawai a taya ta da addu'a a kuma bincika cancantar shi mijin, kuma a wannan shari'ar ta su, Annabi ya bai wa ita yarinyar dama idan ta so a bar auren, idan kuma ta so a warware, yarinyar ta amshi auren amma ita damuwarta iyaye su dinga kiyaye a wani mataki ya kamata su tilastawa yaransu da kuma a wani mataki ne bai kamata su tilasta musu ba." Sai da Abba ya numfasa sannan ya ci gaba da cewa, "Idan kika duba wannan kissar da kyau, akwai abin lura, wanda da dama a zamin yau mu iyaye muna runtse ido daga shi, kuma sanadin runtse idonmu muke jefa yaranmu a ƙuncin rayuwa da damuwa, ƙalubale iri da kala sai yaranmu su dinga fiskanta a gidan aure, duk da a zahiri ƙaddararsu ce haka, amma a salsala har da mu muka zama sila muka kuma taimaka wajan tsunduma yaranmu a ƙangin rayuwa, ba na nufin Abubakar zai cutar da auta idan aka aura musu juna, kamar yadda

Chapter 26 of 32